Ashirin Da Bakwai
Koda Ramlah ta karasa cikin gidan da wani kyakyawan murmushin kan fuskarta. Ita dai har ga Allah indai har suna fira da Dr Aliyu Allah ya sani har kasan ranta take jin dadin abun. Gashi ya iya murmushi, tunowa da drama dinsu ta dazu yasa tayi yar guntuwar dariya, bata lura Lubnah na wajen ba saidai taji maganarta, "Toh fah, yau soyayyar har bayan an dawo gida?" Da hanzari ta juya tana kallonta sai ta zaro ido. "Ji Lubnah, wake soyayyar to?"
Lubnah na hanyar wucewa dakinta tayi yar dariya, "Nidai bance komai ba, kardai ki bari diyar bawan Allah ta gane. Wannan irin kauna da ake ma ubanta ta kusa yin yawa." Ramlah dai kallonta kawai takeyi. Ita bata musa ba sanna ita batace eh ba. "Tana ma ina?"
"Tana wajen Mama, kinsan Mama da yara. Bari inje in dan watsa ruwa kafin maghrib yayi." Daga mata kai Ramlah tayi kafin ta juya ta nufi hanyar dakin Mama. Da sallama bakinta ta shiga dakin ai kuwa kafin ta rufe baki Hafsah ta rugo ta rungumeta. "Ammi, tun dazu inata jiranki, kun gama magana da Abba?"
Murmushi Ramlah ta mata tana lura da yarda Mama take kallonsu itama da wani murmushi kwance kan fuskarta, ba sai ka tambaya ba daka gani zaka san ma'anar shi. "Mama tana nan ta cika ki da surutu ko?" Janyo Hafsah tayi jikinta suka zauna kan kujera sannan suka gaisa da Mama, dan tun safe sai yanzu suka kara haduwa.
"Aa nikau ina yar albarka zata cikani da surutu? Firar school ake ta mani tun dazu ko Hafsah?" Yar dariya irinta yara Hafsah tayi kafin ta mike tsaye, "Zo muje mu bar Mama ta huta, anjima sai azo ayi fira ko Hafsah?" Daga haka suka bar dakin, ita kuwa Mama har kasan ranta addu'a take Allah yasa wadannan mutane sune sanadiyar samuwar dawwamammen farin ciki a rayuwar Ramlah.
Saida sukaje daki tukun Ramlah ta lura jakar kayanta har an kawota, "Aunty Lubnah ce ta kawo maki jakar ki nan?" Yar dariya tayi irinta yara idan sunyi abunda basu kyauta ba, "Dakinta ta kaita, wai can wajenta zan rika kwana. Ni kuma na fara kuka nace dole saidai wajenki, shine fa ta maido man wai munyi fada kuma ta kaini wajen Mama." Dariya Ramlah ta fara, "Anjima zamuje a bata hakuri ko? Ko kinaso ta ki baki toy din ne?" Girgiza mata kai tayi da hanzari. Daga haka suka cigaba da labari ita dai Ramlah babu abunda takeyi sai dariya, dan kusan rabin labarin duk wasan yara ne. Sai dunyi fira sunyi fira sai ta tuno labarin da Dr ya bata, ko ya sukayi rayuwa? Tanaso taji sauran labarin amma kuma batasan jin abunda ya faru, kuma daga gani ko dan ta rikice Dr yana iya cewa zai fadi mata.
Tare sukayi sallah, ita Ramlah har mamakin wayon Hafsah take dukda cewar Hanan ma kusan haka take kamar ba karamar yarinya ba. Sai can bayan sallar isha'i suka sauka kasa don cin abincin tare, dan kuwa wayar Ramlah dama tana hannun Hafsah babu abunda take bugawa sai game.
Dukansu zama sukayi kan dining din aka zuba abinci, dakyar Ramlah ta samu ta karbi wayarta tukunna Hafsah ta dan ci abinci, karshe dai sai cookies ta dauko mata da yar madara, wanda hakan da tayi sai ya tuna mata bataga Rayyan ba tun rabuwar da sukayi a shago. Lubnah na shigowa kitchen din ta fara magana, "Lubnah mutuminki bai shigo cin abinci ba, ko zaki kai mashi?"
Kasake Lubnah tayi tana kallonta, tana san tayi hakan amma kuma batasan ta ina zata fara ba. A hankali ta fara girgiza kai alamar bazatayi ba. "Aa, Ramlah. Kila ya koshi ne ko? Kawai sai naje nace mashi naga baka ci abinci ba gashi na kawo maka? Kema ai kinsan bai yiwuwa ko?" Yar dariya Ramlah tayi tana kai mata dukan wasa, "Wai ke duk lokacin da ake san a gyara abu lokacin ne bai maki ko? Anshi, na gama hada maki tray din kai mishi kawai zakiyi. Ki dan tsaya kuyi labari..." Zata kara wata gardamar Ramlah ta aje mata tray din saman hannu tana jan hannun Hafsah. "Hafsah kima Aunty Lubnah saida safe."
"Saida safe Aunty Lubnah, karki manta alkawarina." Guiwa sake Lubnah tama Hafsah murmushi, "Bazan manta ba Hafsah, kiyi bacci ki aje game dinnan kinji?" Daga haka suka fita kitchen din tana mata dariyar mugunta, "To amaryar gobe, a dai dawo da wuri dan Allah, kar inji kar in gani." Lubnah bataji ta kanta in baccin dariyar da tayi a hankali, dan ita ji take kamar kar takai amma tasan Ramlah zataji haushi kuma ko ba komai wannan ma wani hanya ne da zaisa su kara fahimtar juna. A hankali jiki a sabule ta fita daga falon ta nufi hanyar part dinshi gabanta na faduwa kadan kadan.
Saida tazo bakin kofa ta fara roko Allah yasa ma ace yayi bacci ta koma hankalinta kwance. A hankali ta kwankwasa kofa har zata juya taji an bude, idanunsu cikin na juna yana kallonta alamar bai taba tunanin ganinta a wannan lokacin ba. Gyaran murya tayi tukunna ta fara magana, "Naga bakazo kaci abinci bane, halan aiki ne yayi maka yawa?"
Duk yadda Rayyan ya kai ga bakin rai bai cika nunawa ba, balle ita bama ita ta mishi ba. Wacce ma ta mishin batasan tayi ba. "Kinsan mutanen namu, gani nima da kiuyar aiki sai abu yazo deadline. Shigo mana." Murmushi ya mata wanda hakan yasa ta dan rage danasanin zuwan da tayi. Saida ta zauna saman kujera a cikin falon tukunna taga yadda yayi watsi da takardu ga system dinshi kunne gefe guda.
Janyo tray din yayi gefenshi ya fara cin abinci, "Amma fa nagode sosai wallahi, inda kinsan yunwar da nakeji da tun dazu ma zaki kawo man." Dariya tayi ta fara tattara takardun waje daya, "In kana ma takardu haka Rayyan sai ka nemi wata ka rasa ai." Kallonta kawai yake har ta kammala tattara su waje daya ta koma ta zauna, lokacin har ya fara koshi saidai lemun yake dan sha kadan kadan.
"Kinyi wani shiru shiru dake, lafiya ko?" Maganar da yayi ne yasa ta dago ta kalleshi, sai ma a lokacin ta lura ashe ya dade ita yake kallo. Dan gyara dankwalinta tayi kafin ta fara magana, "Lafiya lau fa, jira nake ka gama cin abincin sai ka fada man meke damunka." Ya akai ta gane wani abu na damunshi? "Har kin gani, Lubnah?" Ajiyar zuciya ta sauke tana daga kai, "Har na gani Rayyan."
To yanzu shi me zaice mata? Maganar yace dan yaga Ramlah da Dr Aliyu tare duk ma bata taso ba, tunda su dukansu sunsan abunda yasa babanshi ya hanashi zama gidanshi, kuma wani abun mamaki har yau basu taba maganar da juna ba. Maybe yau ya kamata suyi, gara shi koma menene ayi a gama ya gaji da wannan abun dake tokare mashi zuciya game da Ramlah. Saida ya rufe system din tashi tukunna ya juyo yana kallonta, "Waya mukayi da Baba dazu," sai kuma ya danyi yar dariya alamar baisan ta ina zai fara mata bayani ba, "Tambaya ta yayi yanda muke ciki." Ba karya ya mata, tunda sunyi wayar amma kuma shi inma ba yanzu ba ya manta sunyi din.
"Ya muke ciki da me?"
Daga kallon da yake mata kadai ya isa ya tabbatar mata da cewar yasan ta gane abunda yake nufi amma ta maze, saida yayi yar dariya tukunna ya bata amsa, yana hade hannuwa waje daya, "Aure mana, Lubnah. Ba aure zasu mana ba? Ni sai yanzu naga nayi kuskure bamu taba maganar dake ba, bansan ko kinada wanda kikeso ba kuma babu wanda ya tambayi ra'ayinki." Inda ace tasan maganar da zasuyi kenan Allah ya sani da ko gigin zuwa bangaren nan bazatayi ba. Yanzu ta ina zata fara? Ko kallonshi ma bata iyayi.
Ganin yanda tayi shiru tana yan kame kame yasa Rayyan kara yin dariya, "Lubnah kunya kuma? Da rasa kunyar kawarki na nan ai da ta tayaki magana." Hararar wasa ta balla mashi jin ya zagi Ramlah, "Ayi hakuri. Yanzu dai taimaka man ki aje kunyar nan muyi magana, kinji?" Saida ta sauke ajiyar zuciya tukunna tayi magana, "Yanzu ya kakeso nace? Ai da Mama tasan akwai da bazata yarda ba tun farko ko?" Zuciyarta dukan ukku ukku take, ji take kaman idan ta kara minti daya a wajen tana ma iya fada mashi tana sanshi.
Da hanzari ta mike tsaye, "Yanzu kaga dare yayi, ko sai mu ida maganar gobe da safe?" Kallonta kawai yake baice komai ba, nazarta yanayin dake fuskarta yake. Ya akayi bai taba lura ba? Bazaice tana sanshi ba kai tsaye amma kuma idan yanzu akace gobe za'a daura masu aure Lubnah bazata taba yin fushi akan hakan ba.
Tasowa yayi ya rakata har bakin kofa, "To ai baki ce mun kina sona ba kuma zaki tafi. Haka za'ayi auren?" Da za'a auna zuciyarta to tabbas ta buga, dan dagowa tayi a hankali, "Dama mace ke cewa tana san namiji?" Fitowa sukayi a tare zai rakata cikin gidan, "Aa, amma ai ni gidanku nake zaune already, kodan wannan ai kinman kara ko?" Tsayawa sukayi suna fuskantar juna, "To yanzu dai sai mun gama magana goben, kayi tunani nima zanyi nawa. Idan mun yanke shawara daya sai mu fada masu, idan bamu yanke bama duk sai mu fada masu, Mama nima ta dade tana mun maganar." Tunda ta fara magana yake kallonta, har ga Allah Lubnah kyakyawa ce sosai, amma shi baisan ya akayi bayajin abunda yakeji game da Ramlah tattare da ita ba. "To Lubnah, saida safe?" Daga mashi kai tayi, amma bai bar wajen ba har saida ta shiga cikin gidan ya jiyo karar rufe kofarta tukunna ya juya. Yanzu shi me ya kaishi fara wannan magana? gashi nan ya kulle kanshi da kanshi.
Lubnah kuwa tana rufe kofa da hanzari ta ruga dakin Ramlah, bata damu da ko tayi bacci, dan yanzu zuciyarta take mata zillow kamar zata fito idan ba maganar ta fidda ba bazata taba jin dadi ba. Bakinta kamar gonar auduga haka ta bude dakin ko kwankwasawa batayi ba ta iske ta rungume da Hafsah tayi bacci tana waya. Zama tayi gefen gadon tana kallon, "Dr ne? Dan Allah ya taimaka man minti biyar, in ban fada maki ba mutuwa zanyi." Ramlah na dariya tayi excusing dinta ta kashe wayar.
"Gaya man, halan yace yana sanki?"
Wani irin ihun murna da tsalle Lubnah ta fara, tun acan dama danne kanta takeyi, "Aure, Ramlah! Wayyo zuciya zan mutu! Ke wai maganar aure, ina zansa raina?!" Saida Ramlah ta lallaba ta aje Hafsah tukunna ta mike suka fara tsallen tare rungume da juna, dariyarsu kau kila har dakin Mama ana jiyota.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top