Chapter 2✓


MEERAL 💗
Page 2

ASALIN SU

Malam Yusuf bukar shine sunan mahaifinta, asalinsu fulanin mambilane dake garin taraba, malam Yusuf ya girmane gaban maihaifinsa, Dan tun yanada shekara 18 Allah yama mahaifiyarsa rasuwa,tun bayan rasuwar maihaifiyar Yusuf, maihaifinsa malam bukar bai sake aure ba sai ya maida kula da ɗansa main abin da ke gabansa dan yana so ya ginasa gudun kar yayi rayuwar Kunci da maraici, mutane kan faɗa masa ƙarin Aure shine zai cire sa daga tunanin da yake amma yaƙi saurarar kowa, tunanin sa idan ya Auri wadda zata gallaza masa fa?
amma kash..
Ita rayuwa kana naka ne Allah na nasa, kuma Allah bai barin wani dan wani yaji daɗi,
Yusuf nada shekaru 20 Allah ya dauki ran maihaifinasa yayi kuka yayi baƙin ciki dan ba ida Wanda zai juya ya kalla a ciki rugar awwah yace wannan nasane sai kanwar maihaifinsa Yawaro, Wadda ita kuma bata kyaunarsa ko kaɗan Domin a ganinta saboda shine bata cin dukiyar dan uwan nata yanda ya kamata dan ita Sam bata yarda bai dashi ba.. Zaman nasa dadi ba dadi ya jure dai har ya ƙara shekara a garin a shekaran da yayi ne a kayi auransa da ma'amah(faɗime) Dan dama sun jima tare..watansu biyu da aure yayan ke shawaran barin garin Shima da kyar dan sai da a kasha gwagwarmaya da dangin ma'amah...

shanu bakwai daya gada gun mahaifinsa ya siyar da Dan abun da ba a rasa ba suka fita daga garin,

Garin kano ya nufa dan sosai ya keda bukatar ya fita daga mambila, hayar gida Mai daki biyu kitchen sai bandaki ya kama musu anan anguwan rijiyar zaki,
A hankali ya fara juya Yan kudin daya ke dasu ta hanyar saro kayan miya kadan ya siyar, a haka yake rufa ma kansa da iyalinsa asiri.
Shekararsu daya a garin Allah ya azurtasu da santaleliyar ɗiya, malam yusuf yayi murna sosai da kyautar da Allah ya basu dan haka ya dau san duniya ya ɗoraaa yar tasu wacce taci suna MEERAL,,
malam yusuf ya dau burin duniya ya dora kan meeral, ya jima yana ɗaukawa kansa Alkawarin bata rayuwa Mai inganci da ilimi islama Dana boko da Ikon Allah.
Haka kuwa akayi dan sosai ya dage Wajen bata ilimi mai kyau. FA'AN ya samar mata duk da yawan fees ɗin su bai yi kasa a gwiwaba buga nan buga can a haka ake ta fama.
har ta gama both FA'AN nursery, primary &junior sec sch...ma'amah ta sake samun ɗiya mace wace taci Suna Asia, haka rayuwa ta cigaba da tafiyan musu dadi ba dadi, malam Yusuf yana yar sana'ar sa wacce Allah yasa masa hannu a ciki..
Lokacin shigan meeral ss1 ya nema mata federal goverment college kano.. Kwanci tashi bawuya tagama fgc..
Result ya fito kuma Alhamdulilah da grade Mai kyau ta fita.. Iyayenta sunyi farin ciki sosai,. tayi taking jamb exam kuma tayi sa'a ta samu 220.above scores din da take nema dan ita burinta ta karanci business administration, tayi applying bayero university suka bata cikin yardar Allah,,

Lokaci na tafiya sannu sannu ba wuya gun Allah... shekara tazo lokaci yazo Wanda meeral ta kamala karatun ta a jamiar bayero university.. shekarace wadda ta kasance ta farin cikinsu haka zalika ta bakin ciki saboda shekarace Wadda ta gama, makaranta,,kuma ta rasa mahaifi ya rasune dalilin brain cancer da ya jima dashi bai sani ba.. Shekarar ta zame musu baƙa dalilin faɗuwar katangar da su keda musaman ma'amah wacce bata san ina zata sa kanta ba.ya tafi ya barta da nauyin yara biyu kuma duka mata....

Kulli nafsin zaikatul maut, musan Kowane rai zai ɗanɗani zafin mutuwa. Wani Uwa , wani uba , wani ɗa, wani ƴaru wa wani ɗan uwa, wani mata , wata miji, da zafi da daci amma Allah subahanahu wata'ala cikin hikimarsa zai sa maka dan gana da hakuri da juriya, hakata kasance da faɗime ta rungumi hakuri da dangana na rashi mijinta. Kuma ta kuduri niyar kula da yaran nata biyu.. Amma yawan tunani da damuwa ya haifar mata da matsalan zuciya..

Sauda dama meeral kan zauna tana bata baki akan takwantar da hankalinta tana gama bautar ƙasa Zata samu aikin, yarda kula da ma'amah da Asia da kuma kuɗin magani ba zai masu wuya ba.. duk a tunanin ta tunda ta fita da result mai kyau hakan ba zai wuya ba,tunanin ta lokaci guda zata iya samun aiki da takardun ta. Amma kash ƙasartamu yanzu ba wai ka gama karatun ba aikin.
Saida tayi shekara da gama bautar kasar amma shiru aiki yaki samuwa.. Sai ta zuba ma sarautar Allah ido although she's trying so hard taga ta samu mafaka.
Aikin waitress tacsamu ta hanyar wata kawarta a anan wani restaurant dake Cikin sabongari.. Shima da kyar ma'amah ta barta dan a cewarta ai miral din baza ta iya ba.. Miral saita nuna mata da zaman nasu haka ai gwara tayi tunda ita ma'amah ba wata sanaa take ba kuma ga yanayin matsalarta hakazalika gakuma karatun Asia. dan haka sai ma'amah ta hakura tabi yar tata da aduaa......
Wanan kenan

Yo hope y'all like..
Don't forget to vote , follow, comment, &share it means alot
Love y'all 😍xoxo
Chuchujay

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top