Chapter 15✓
Sis you dont need to talk to him one last time for closure let that shit go!!
Meeral❤
Page 15
Sipping tea take a hankali tana juya wayanta a hannunta tunani take yarda Zayn yayi mugun raina mata hankali ace zaiyi tafiya amma a matsayinta na matar gida sai dai ya tura mata text message akan tasa a kulle koina in dare yayi shi zai yi week baya gida.
Wani huci ta fitar ta ƙara sipping tea ɗinta ,ita a ganinta ai ko ba soyayya tsakaninsu ba ya dauketa ba komai ba.
Tunani ta faɗa yarda zaman nasu ya koma tunda yayi raping ɗinta suke wasan buya almost 3 weeks kenan dan Inda yasan zai ganta a guri to bai zuwa dan yanzu gudun rainin da yake hangowa a idonta yake, inda ita kuma Miral gani take ai yama raina mata hankali yayi raping nata sannan ya ringa mata acting kaman wani kashi ya aje, in tsautsayi ya saka suka hadu yaita bata rai kenan,
Cup din ta kai kitchen tana wankewa thought Iri iri a ranta "tunda ka tafi ai nima banata zama kaman wata prisoner cikin gida ba walh mutum yayi kaɗan, kuma zai zo har cikin gidan nan ya tarar dani" magana take tayi ita kadai har ta gama yan ayukanta.
Wanka tayi ta shirya cikin red atampa mai kwaliyyan white manyan flower rigaa da skirt ,plain simple hijab tasaka ,hand bag ɗinta ta dauka ta kulle front door,
Peter driver ta hango da Musa gate man suna hira, da sauri Peter ya taso "madam sannunka da fitawa inane zakaje "ya faɗa cikin hausansa da bai clear ba..
ɗan gaba tayi yana binta a baya "sannu da fitowo hajia" cewan Musa gate man
" yauwa sannu Musa sanunku da aiki"
" Madam make I carry the car come wey you dey go"? Peter yas ake tambayanta..
"Peter kabarsa ba sai ka dauko Mota ba ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo"
"But madam oga say make i no allow you waka for leg,If you need anything we dey me and musa we go help kuku, its our work "ya ƙarasa yana yake mata baki.
Musa ma yace haka ne hajia inda aikene kikawo ai sai aje.
Cikin kosawa tace masu ai kar su damu tayi magana da Zayn dan tana san ta dan wasa kafane.
Koda ta fita napep ta tare ya kaita anguwan su saima,sosai saima tayi murnan zuwan ta kaman zata maidata ciki duk da tayi mamaki, hiran yaushe gamo su kai tayi da tuna baya ba tare da wani ya kawo maganar Aurenta ba ko dalilin fitowarta a yanzun.
Ba ita ta koma gida ba sai daf da magrib.
da daddare tana kwance tana tunanin zuwa gida washe gari dan tayi missing maamah da Asia.
*******
Bangaren Zayn kuwa aikine na gaggawane ya taso masa a company ɗinsa na abuja, so without thinking twice kawai yacshirya dan tafiya, koda ya fito daga part ɗinsa ya nufa nata ,a hankali ya buɗe dakinta ya shiga yat arar da Ita tana bacci peacefully gudun kar ya tashe ta ya saka kawai yayi pecking forehead ɗinta ya jamata blanket ya tafi,
Sai da ya isa abj sannan ya tura nata text akan tafiyan nasa.
Fitowansa kenan daga wanka daure yake da pure white towel, he was busy drying his hair sai ji yayi an yi hugging bareback dinsa,
"holly shit" ya faɗa a ɗan tsorace dan bai bar kowa a cikin parlour ba bare har cikin bedroom.
Yar dariya tayi irinta rikakkun whores ɗinnan,
"baby look at how scared you are"
dan gyaran murya yayi yana san yayi calming kansa dan sosai ransa ya ɓaci da ganin ta.
"Ruffy what the hell are you doing here?" mai ya kawo kinan ?beside ya a kai kika shigo gidannan har cikin bedroom dina?".
"Baby what do you mean" karasowa inda yake ta fara da wani seductive look ,"shi'kenan kuma bazan zo inda masoyina yake ba, a kano kace mun your reputation saboda kowa yasan kana da mata, amma mene, kaga a Abuja daga ni sai kai ba mai cewa saboda mene,no paparazzi no fams no wannan mayyar matar naka.ta ƙarasa maganan tana wani shafasa.
ɗan ture ta yayi yabi ta da wani irritating look Naji yanzu kije parlour lemmi dress up inna fito sai muyi maganan.
"Baby let me dress you up"
"No" ya faɗa yana ɓata rai wanda ganin hakan yasa ta fita dan Sarai tasan halin Zayn din idan bayasan nonsense yanzu zai cimata mutunci...
Tsaki ya saka da ta fita, zama yayi kan stool yana brushing hair ɗinsa da fingers in frustration oh God"
Dark formal pants ya saka da white shirt an rubuta PERFECT da black rubutu bold, Spraying jikin sa yayi da perfs masu kamshi, sannan ya fita dan dole ma ta bar masa gida yanzun nan.
Zaune ya ganta ta wani harde kafafu tana cin fruits daga Ita sai wata banzan riga mai spaghetti hands ta cire blazer din saman kai kace a gidanta take.
Tana ganinsa ta taso "baby you look so damn hot "da sauri ta ƙaraso zata taɓasa
Kauce wa yayi kaman zata shafa masa kashi" ruffy ki zauna muyi maganan mutunci ba wannan ba please ,ya a kai kikasan ina abuja" ya tambayeta,
grapes ya ɗauka cikin fruits ɗin da takeci ya kai baki yana binta da ido alamun yana jiran amsan tambayan daya mata.
"Okay Naji ta koma ta zauna" Farouk na tambaya ya fada mun kana abuja so dama ina son zuwa abujan kuma sai ga babban dalili ya taso kasan aguna you are before anything else magana take tana wani kashe masa ido..
"I will surely skin you alive Farouk ya faɗa under his breath,
"Baby mai kace she asked,,,
Bakomai yanzu dai abinda na ke so dake kizo ki tafi akwai inda zanje zan kiraki.
Charaf ta karɓa da baby zan bika mana.
No bazakiba yavata amsa kaitsaye beside nibanasan kikarazuwa gidan nan ma inbani na nemekiba..
sosai ranta yabacci amma gudun nasa baccin ran sai ta shanye nata dan bata san plan dinsa tashirya nasamunsa wannan Karan ya ruguje,
"Ok baby Naji zan tafi take care Peck" ta basa a cheeks sannan ta kwashe tarkacenta ta fita.
Zaman yayi kan kujera yana sauke ajiyan zuciya yana mai tuna shi ya bata access da gidan,wayansa ya ciro ya kira Farouk ,ringing ɗaya ya ɗauka yana mai faɗin "Hello yane man ya akayinne".
"Ubanka a kayi "yafada a fusace
Dariya Farouk ya kyalkyale da "kace mun tazo mutuniyar kenan, shaka mun mai ya faru ko na sha ƙama Miral nima..
Sosai ya ƙara kullar da mutumin nasa.
"Walh in ka sake mun irin haka billahillazi saina faffallawa yarinya mari"
Wata mahaukaciyar dariya Farouk ya ƙara ."Allah mutumina dan rantse"
Ganin idan ya biyesa kunnasa zai tayi ne ya saka ya kashe wayan.,baiyi minti biyar da ajewavba wani kiran ya shigo masa ,number Peter ya gani so kawai ya ɗaga saninsa akwai wani abu muddin ya kira sa" hello Peter ya akai"
"Good evening oga "
"Evening "ya amsa sa kai tsaye. "Mai yafaru"
Emm Peter yaɗan fara Kame kame. oga I wan tell you something but please I take God beg you don't tell madam sey na me tell you"
Gabansa ne ya faɗi jin abin da Peter yace so cikin tsawa yace" za ka faɗa munne ko sai nayi firing dinka"
"Oga dama madam ya fita tun safe bashi ya dawo gida ba sai to 6 oga I beg madam say make I take her but she refused ."
Bai ƙarasa jin maganan Peter ba yayi hanging up
Layinta ya fara nema sai da yayi mata 5 missed call sannan ta dauka tana mai faɗin Hello, kanta rufe baki muryansa ya katseta,
"gidan ubanwa kike zuwa ,wanne dan iskan ne yake hure miki kunnen fita? wato dama ni kike jira kuga bana kusa ku cigaba da iskancin ku ko?
Wani takaici ta ji ya rufeta dan baa taɓa faɗa mata maganan wai tana isakanci da wani ba sai yau.
Gyara kwanciya tayi sannan ta fara basa amsa.
"Ai kasan dama shi dan iska kallan kowa yake a dan iska kuma duk abin da yake haka yake ganin kowama shi ya keyi ,inma iskancin nakeyi ai agunka na koya, kuma kai ɗin shaida ne lokacin da ka bajemun naka isakanci da akuyancin i manne ka sameni ba a buɗe ba.
Kafin ya sake magana tayi hanging up sannan ta kashe wayanta,Sosai maganan nata ya zafe sa amma in tasan wani ai bata san wani ba.
Wayan ammi ya kira,Cikin ladabi ya gaisheta sannan ya faɗa mata dawowansa bazai iyu nan kusa ba dan company ɗin nasa yana bukatansa so yazun Farouk ne in charge of na kano,Kara marairaice murya yayi please ammi I need my wife near me,ki saka Adeel ya kawo ta nan Abuja cos ayyuka sun sha mun kai da yawa.
Dariya irin na manya ammi tayi "jaarin yaro kai da matanka ba wanda zai hanaka ɗaukanta, insha Allah zan sa Adeel ya kawota.
Godiya yayi ma ammi sannan ya kashe wayan.
Maamah ya kira ya faɗa mata maganan tafiyan, sosai ta masa addua da fatan alkhairi.
*****washe gari Adeel yazo yamata maganar tafiyan sosai tayi mamaki amma sai bata nuna ba tayi kaman dama tasan da tafiyan,wato tanan ya bulo kenan.
Ranan gida tasa Adeel ya kaita sosai maamah tama nasihohi mai ratsa jiki akan tabi mijinta ,haka ma gun ammi cikin fasaha irinta manya ta mata yan nasihohi wanda sosai suka shigeta,
Bayan kwana uku da abun ranan Monday da safe suka bi flight ɗin Abuja.
**********************
Sosai take karema gidan kallo dan ba karamun haduwa yayi ba wani infinity circular pool ta hango which had a background of light blue water sunata clashing against each other,sosai take yaba tsarin gidan very huge and well decorated.
"Auntyn mu bismillah" muryan adeel ya dawo da ita, girma da kyau ɗin parlour din bazai fasaltu ba bata gama Santin gidan ba taga ruffy tana saukowa daga staircase kaman an korota, Kallon kallo suka bi juna dashi,Adeel ma kasa rufe baki yayi sai ware ido yake yaga ta ina Zayn zai fito.
"ke wa kika barma Jakan ki?" Kasa ƙarasawa yayi gani ƙaninsa da matansa.
************
dont forget to share, comment, vote & follow Chuchujay
I love y'all xoxo
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top