Chapter 11✓

Page 11
MEERAL
Abubuwa da yawa sun faru bayan barin maamah daga asibiti ciki kuwa harda manya da suka shiga cikin maganan auren Zayn da Miral, Inda maamah tace lallai sai dai aje can mambila gun mahaifinta tunda sudin ba wasu yan uwa suke da a garin ba,
Sun saka rana akan za suje cikin watan nan inda itavkuma maamah tace zasutafi a satin dan ta fara cimma iyayennata da maganan taga yaza su ƙare dan ita kanta tasan bata kyauta ba da bata sake nemansu ba dan rabanta dasu tun miral nada shekara daya shima saida ta matsa Malam Yusuf ya barta amma da sharadin shi bazashi ba..
*
Sauri take ta shiga office ɗinta dan batasan haɗuwa dashi Kasancewan yau din Friday ba wani yalwar mutane a company din sai taji dadi dan ba wanda zai san tazo bare a faɗa masa dan taga ƙarfin halin nasa yayi yawa bata kai ga auresa dinba amma ya bata dokan In dai zata fita dole sai ta sanar masa saboda shi baya san ace fiancee ɗinsa tana fita any how ba girmansa bane, yarda ta bar office ɗin haka yake sai dai gyarasa da a keyi kullum amma komai yana nan inda ta ajesu, yan abubuwan da suka kasance nata ta zo dauka dan satin ta na wajen uku kenan da barin aiki saboda Zayn yace shi ba zai lamunta ba saboda ita din tasace although yace shi ba Santa yake ba amma fa ba zai lamunci yana shirin aurentaba amma wasu suna kalleta abun ma ya zama kaman cin fuska a gunsa, musamman wannan heavy behind din nata dake shouting Nicki minaj yafi komai tsone masa ido.

hankali ta nakan wayanta tana duba message ɗin da ya shigo mata kenan, Gware taji tayi da wani hard chest.. "Och sorry" suka faɗa a tare dagowa tayi eyes dinsu suvkayi locking ita tana kokarin fitowa shi kuma yana kokarin shiga.
Wani kyau yaga ta masa sosai so yakasa ɗauke idonsa a kanta ita kuma so take ta wuce amma Ya tare mata hanya and taga alaman kaman suna different world ne yanzun,Sanye take cikin wata yellow blouse mai santsi then simple long black pencil skirt jikinta black veil ta daura ma kanta den ta dauko black jacket mai laushi sabida sanyi da ake yi ,black Zara heels ne ƙafanta sai backing back data goya ,
"excuse me "
ta faɗa da ɗan karfi wanda shi ya dawo dashi duniyan sa na ainayi, simple make up nata tayi applying amma ba ƙaramin kyau tayi ba dan kowane Ya kalleta yasan ita din mai kyauce

"Mai ya kawo ki nan "ya:tambayeta yana san ya basar da wamcan halin da ya shiga .
"kuma nace miki bana:san wannan shigan in zakivfita am a highly man of upper class bai kamata ace wasu can waje sunsan Yaya yanayin tsarin fiancee na yake ba, ba ajina bane".

Ita dai jinsa kawai take dan ba taga wani aibu a shigantaba hasalima ai tafi wannan shegiyan karuwan nasa dressing decently.

"dama ina son zanje gida na sameki ko baki zo ba,  gobene zaku mambila ko?
ɗaga masa kai tayi .

"I hate body language bana so na sha faɗa miki inace kina da baki answer me my friend"

"Eh ta amsa a takaice dan ita yau she's not into his damn fights,bata da ƙarfin kula sa.
"Inason za muje gun ammi ne"

"Naam' ido ta zaro tana Kallansa. k
"Kasan mai kake cewa kuwa ni dai gaskiya da kunyana"

Kallanta yayi a wani lalace." ke stop acting kaman wani romantic relationship ne tsakanina dake oo wani kinajin kunya ke wai mai sirika ba ,I repeat it don't fall for me saboda I wont catch you never,kada kice ban faɗa Miki ba, Allah ma shaida nane.

Maganan sosai Ya zafe ta amma bata nuna ba ɗan murmushin rainin hankali ta masa "to da an faɗamaka kana da wani qualities dana keso a namiji ne, wlh baka dashi ai kai din bakakaiba,Kuma ka sani ni bani nake tura kai a kan ka aureni ba kai kanace, yanzu kayi lissafi na kuɗin ka da kakashe kagan inban biyaka ba."

"Kan uba"ya faɗa da wani irin murya, "lalaima yarinyar nan ai wlh bari kiji bakin alkalami ya bushe ai tun lokacin da kikasa Hannu a papern nan from that very moment kika zama MINE, You are my property.

Hissing tayi under her breath tayi gaba tabarsa,dan kalmar ita property ɗinsa ce tafi komai shaƙa mata ,da kyar ta yarda ya maidata gida.

Washe gari da sassafe suka dau hanyan mambila,yarda  maamah tayi tsamanin iyayen nata ba haka ta gani ba dan kuwa kaman zasu maidata ciki ita da yaran nata,kan Kace mene yan uwa da abokan arziki sun taru kowa yana murnan zuwansun, kawo wannan kawo wancan inna wuro kam mahaifiyan maamah bakinta har kunne dan murna, Baffanta ma kam abun ba a magana, Asia har tsiya ta fara ma maamah dama suna da wannan gatan amma suke garin da dagasu sai su ni wlh badan makaranta bama zamana zan"
. Baffa kam washe baki yayi "wlh kuwa amaryar ga ɗaki can na gyare maka shi"
duk suka kwashe da dariya Asia na cewa..
"wlh baffa ni dai macene bavnamiji ba kake cemun wani kai.
" Jairin yaro"
duka sa dariya cikin nishadi kana ganinsu kasan suna cikin farin..
Dangi sosai suka zaga har saida suka gaji dan mama yar dangi ce sosai.. Kwanan su biyu kanwan mama inno dije tazo dan ita tana aure ne a nijar..
Koda maamah Tama baffa maganan auren miral din ba ƙaramin murna yiyi ba da cewan dama ai tama wuce lokacin aure insha Allah in magabatan sa sunzo bazasu tafi ba sai an daura, saura wancan yaron yana nuna Asia da baki ,bara jauro yazo sai Ya kawo shanunsa manyan ciki biyu sai a hadashi da ita,
baki Asia ta rike .
"laa inna kiji min Wannan tsohon mijin naki fa ,yarinya yar charas kamanni ace za'amin aure ko makaranta bangamaba wlh da sake.

Dariya yayi sosai yana kiranta ja'ira dan shi kam baffa yana son tsokanan Asia dan sosai yarinyan ke da shiga rai.

Koda magabatan Zayn suka zo baffa ya basu bukatansa nasan a daura auren in yaso in anje can sayi shagalin bikinsun, sosai yaji dadi wanga batu dan haka a take ya bada sadaki na naira dubu ɗari aka daura Auren Zayn Zaid da Miral Yusuf Bukar..

Koda aka faɗama Miral ɗin kuka kawai ta saka na tunanin halin da zata shiga, yan uwantan kam da suka taru su kayi ta mata shakiyanci akan ai itatace tana so..
Zayn kam da Adeel na faɗa masa bata rai yayi irin ina ruwansan nan, gyara tsayuwa Adeel yayi ,"big bro ni na rasa gane wannan gulma irin taka, kanaso kana kai wa market.
Hannu Ya kaicmasa ya kauce yana dariyan shakiyanci,he can't help it,tsakanin su idan suna abu zaka rantse abokai ne,
Koda ya shiga ɗakinsa wani farin ciki from no where yaji ya rufesa ya rasa dalili,yasan hanyar da yayi approaching wajen samunta bai kamata ba,wani bangaren kuma yakan jaddada masa ƙaddararsu ce.

Sosai ackayi shagalin bikin a mambila, sunyi al adu dayawa na fulani gwanin shaawa,Inno dije sosai ta gyarata inda ita kuma take ganin rashin amfanin hakan dan dashi da babu duk daya dan duk ranan ma da yazo inda take sai ta fasa masa kai.

Watansu wajen guda a garin Sannan su kayi shirin komawa kano, kudi baffa ya bama maamah yace ama Miral kayan daki dan baffa mutum ne irin masu kudin fulanin nan,bata ƙi tasa ba ta karɓa.

Tare suka tafi da inno dije da yarta salima sai yayan yayayun maamah maza zainab Aisha da Khadija,After sun komane maamah tayi nata gayyan.

Gogan kam abokansane suka haɗa masa party har wajen Kala uku dan sunce ai yawane bikin d mighty zayn ba wani cashewa, bachelor party suka fara sanan lunching shima da kyar Miral ta hallata ,dinner ne ya rage wanda yau da dare za ayi.

Adeel ya aiko ya kawo mata dinner gown ɗin, wata pink simple gown ce mai masifan kyau da heels da jakansu.
da ƙyar ta yarda aka mata makeup shima sai da yan uwan nata suka matsa Asia ne kan gaba tanata Didi please.
Yanmatan amarya sunyi dressing cikin ankon lace material maroon mai kyau an masa kwaliyyan milk, su Saima kan manyan ƙawaye an kashe kyau ba kadan ba,Su carina ma anfito kai ka rantse duk sune yarda da saje dasu.
Kana ganin Asia kaga amara kirjin biki itace yinan yican sosai itama tayi gayyan kawayenta dan gurin ta ba ƙaramin show off Auren nan ya kankaro mata ba.,Around 8 angwaye sukazo daukansu,Adeel ne ya kai Miral motan ango muryan Asia yaji :
"to aikuwa sai kaji dani tunda ka rabanicda didee na"

" Oh madam baki tafi ba Ashe wayyo gimbiyata kinji yarda kuwa wani abu ya soke zuciyata"
safe Chest ɗinsa yayi irin mashin ya soke sa,haushi abin ya bata mutuƙa ,kamar ana ankaɗata ta juya ta bar gurin,a baya Ya biya yanata harzukata.

Miral kam tana shiga motan Kamshin turarnsa ya mata sallama sosai taga ya mata kyau cikin ash gitzner ɗinsa da tasha tsadadden aiki Ya gyara hair dinsa ya sha kyau sannan ya ɗora masa hula, quarter million ɗinsa sai dake Ƙara fito da hasken fuskansa yasha gyara sai sheki yake,ita kanta tasan duk inda kyau yake da gayu to Zayn ya wuce nan dream din kowace macene amma ban da ita ta faɗa a ranta.
Shima nasa bangaren kyan da tayi yake yabawa danji yake kaman yayi shekaru bai ganta ba ga wani haske da fatanta tayi sai sheki take ji yake kaman ya taɓa dan yasan zactayi laushi,Shiru ne ya ratsa cikin motan har suka isa gun dinner din, gun yasha kwalliyan pink and ash sosai aka kashe kudi wajen tsaragun.

Hand ɗinta cikin arms ɗinsa haka suka shiga gun yayin da flower girls suna ganbasu suna watsa fure,.

Dinner ta fita dan Sosai a kaci a kasha aka danse a gun ,dollar kam sunyi kuka dan in banjemin's abokan ango suka ringa liki,
Mc ne yayi announcing amarya da ango su yanka cake, Ita ta fara yankawa tasa masa a baki den turn ɗinsa, kato ya gutsoro,dan ja da baya tayi ,mc kam ya dage sai koɗa ango yake haka na nanu ango ba zai bar amaryasan da yunwa ba blah blah.

Tura mata yayi gashi ya mata yawa,  duk ya ɓata mata baki ,a zuciyarta sai ɓacinsa take dan  tasan da salan mugunta yayi hakan. Hannunta taji ya rike then ya jawota jikinsa , tunani take mai kuma zai mata, bata ankaraba saijin lips ɗinsa tayi Kannata as if his life depend on it tas yayi licking cream din daya ɓatata.

Ihu gurin ya ɗauka da tafii,
" Damn my first kiss "wani mugun takaici taji ya rufeta kaman ta wankesa da mari wani bagaren kuma mamakin munafurci irin nasa take dan koda zata rantse akan ba soyayya tsakaninsu ba mai yarda, dan turesa tayi in a style tana basa wata harara ƙasa ƙasa shi kuma yana bata wani smirk na rainin hankali irin kaɗan kika gani ɗinnan.

After an tashine wajen 12 sannan ya maidata gida shima sai dayacgama rarraina mata hankali da threatening Kala Kala na intazo gidan sa zata gane kurenta.
Washe gari kam aka kaita gidan Mr Zayn Zaid wanda take jin kamar an buɗe rijiyar wuta ne an tsoma ta an rufe.

Koya zaman nasu zai kasance??

Xoxo love y'all ❤

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top