SHA DAYA | PRESENT
****
Hannun ta ta saka ta toshe bakinta saboda dariya. Shi kuma kawai sai ya qura mata idanunsa masu kyaun gaske. Idanun da suka kasance suna rudar yan mata tun yana dan samari.
"Salmah kenan." Ya fada yana jinjina kai. Har zuwa lokacin bata dena dariya ba. Tun da yake da ita bai taba sanin tana da wannan bangaren a tattare da ita ba. Kullum fuskarta ba yabo ba fallasa kawai sai wataran ta danyi murmushi wanda a iya lebenta kawai yake tsayawa.
"Dariyar ta isa haka nan Matar sheikh." Dum! Kalmar ta doki kunnen Salmah wadda nan take ta dena dariyar.
"Matar sheikh kuma?" Ta maimaita tana tuno wannan littafin. Gaba daya sai taji lissafin yaqi haduwa.
"Eh mana ko sunan baiyi miki ba? Ni ba Sheikh bane? Kinga matata ta zama matar Sheikh ko kuwa?" Ya dage mata gira.
"Hakane." Ta fada tana sadda kanta kasa.
"Yawancin matan abokanai na haka suke kiran kansu da shi. Amma ke fa?" Shiru tayi.
"Toh ai kai malami na ne wanda nake neman shawarwari a wajen sa. Babu wata alaqa tsakaninmu." Wannan karan Sheikh Salim ne ya sheqe da dariya. Lallai ma yarinyar nan. Duk irin kallon da take masa har cikin kwayar idonsa tana nufi bashi da wata ma'ana.
"Toh shikenan ai. Zan yi kokari naga na nemi mata kwana kusa." Zuciyar Salmah ce ta shiga rawa. Gaba daya taji wani irin yanayi mara dadin gaske ya mamaye ta. Meye hakan?
Muryarta tun tana maqogaronta ta fara karyewa amma bata sani ba.
"Toh Allah ya baku zaman lafiya idan ka samu." Ta miqe tana tattara littafan ta, tana saka su a jakarta. Har wani yaji yaji idonta yake mata. Ji takeyi kamar kawai ta sa abu wanda zai ragewa idonshi kyau saoboda kar wata macen ta gani.
"Ina zaki je kuma muna hira abun mu?" Qara saurin rufe zif din jakarta tayi ta dago ta kalle shi. Hadiya tayi amma duk da haka taji wani abu ya tokare mata wuya.
"Class zanje." Ta fada a takaice tana juyawa. Hade hannayensa yayi ya dora su akan kirjinsa yana jijjiga kansa. Har zai bita kuma sai ya fasa ya tsaya ya kare mata kallo har ta wuce. Murmushi kawai yayi.
"Mata?" Ya sake girgiza kansa yayinda Jamilah ta fado masa a rai. Nan da nan sai yaji kwalla tazo idon sa.
****
Jamilah.
Page 6;
leave me alone!
Nayi kuka cikin wannan daren kuma cikin kukan nake ta gwada kiransa amma bata shiga. Ko kadan zuciyata bata saka min wani abu mara kyau ba. Ni dai fatana daya, Allah yasa lafiya qalau yake.
Yanda naga rana haka naga dare. Fuska ta ta kumbura sosai. Ciwon da kai na yake kuwa har sai da na zata tarwatsewa yake shirin yi. Haka nayi ta jinya ni kadai ba wanda ya damu. Ina ta murna ai kwana biyar din da akace zanyi tayi. Sai na ga kawai an bude kofar daki na a sako min akwatuna na suka gangaro cikin dakin. Nan na fahimci dai kulle ake min. Abun duniya ya ishe ni. Babu wanda yake min magana.
Iya kar a kawo min magani a ajiye shikenan. Amma ko sannu babu me ce min gashi kuma kwana hudu kenan rabona da shi.
Ranar na shirya nace zanje gidan Maami aka hana ni. Nace zanje nayi rijista na NYSC shima aka ce sai wata shekarar. Qarshe ma dai wayar tawa karbeta akayi.
Duk wadannan abubuwan basu saka naji na rage son shi ba. Idanun sa kawai nake gani cikin nawa duk sanda na rufe idanuwa na.
Kullum a cikin duba kalanda nake ina kirga sauran kwanakin da suka rage su Umma da Abba su koma kasar waje. Da dan biro na nake yiwa kwankin alamu har ya zama saura sati daya. A sannan gaba daya damuwata ta ragu sosai tunda nasan na kusa samun yancin kai.
Ina ta planning yanda zan hadu da sheikh idan suka tafi. A yanzun komai ya sauko domin a tunanin su na manta da shi tunda har anyi wata biyu.
Sai dai zuciyata ta kan yimin zafi idan naga ai ko yunkurin nema na Sheikh baiyi ba.
"Tashi ki shirya!" Na tsinci muryar Abba. In shirya kuma? Naje ina? Allah yasa wajen Maami zai kai ni.
"Wannan karan ba Brighton zamu je ba. Kin manta na gama? Shekara biyar ne dama. Amma na samu wani temporary aikin a Egypt. Zamu fara Umrah, in da hali zamu dubai sai mu wuce Egypt daga can." Ban san sanda na daka tsalle ba ina ta murna. My dream was to visit the holy city and the ancient city of Egypt. Oh my Allah! Kai wannan abu yayi mun dadi.
Ban ma ji ragowar abunda suke cewa ba kawai na tafi na sako hijab mukaje aka mun visa. Tun da muka dawo baki na ya bude ina ta surutu.
"Ilham! Egypt for real?" Na tafa hannu na sannan nayi tagumi dreamily ina fluttering lashes dina.
"Kin yi sa'a zaki. Abba ce baki je." Tabe baki nayi ina kwaikwayonta.
"Kinga karki fasa min kunne da wannan gurbatacciyar hausar taki. Tunda dai inajin turanci ai kawai ki min da yaren da zan gane abunda kike cewa." Duk wannan abun da nayi bai hana ta sake gwada yi min bayani da Hausa ba. Da na gaji da jin ta kawai na bar mata wajen.
******
Muna ta shirye shirye. Ashe gaba daya family zamu tafi. Har big sis ma da mijinta da kuma babyn ta za'a je. Naji dadi sosai duk sai damuwata ta kwanta amma deep down, it's embedded in my heart.
"Finally!" Naji big sis ta fada daga baya na. Na juya na kalleta.
"Finally what?"
"Kin rabu da wannan yaron. Addu'a ta ta karbu."
"Ya Fiddy kenan. He might be miles a way from me. A thousand miles away yanda ko kwalla masa kira nayi na zai ji ba amma kuma har yanzu yana nan." Na shafa gefen hagu na kirjina ina nuna mata saitin zuciyata.
"Allah ya yaye miki. Amma ni kam kauyancin nan naki mamaki yake ban." Ban ce komai ba, na miqa mata hannu na karbi baby Aayan da yake ta barci. Har muka kusa karasawa airport bamu sake cewa komai ba. A hanya kawai kallon sleeping figure din Aayan nake ina hasko yanda nawa dan zaiyi in akayi auren mu da sheikh. Sauran sai hirar su kawai sukeyi ni dai kam na tafi duniyar tunani.
Motsin Aayan ne ya saka na daga ido naga an zo. Fitowa muka farayi aka yi abubuwan da za'a yi sai jirgi wanda bai sauka ko ina ba sai a Jiddah.
****
Bayan munyi umra haka Abba yayi ta yawo da mu. Rannan yace zamuje wajen wani abokin sa a jami'atul madina. Yace mana tun suna yara abokin yake son zama malami. Kuma a yanzu hakan ma yana visiting lecturing a jami'ar madina. Sosai muka ji abun ya burge mu ni kuwa sai yashe haqori nake saboda Sheikh dina ma so burin sa kenan.
Muna tafe muna hira har cikin makarantar. Tsayawa bayanin ginin ma wahala ce kawai dan ba zata kwatantu yanda ya kamata ba.
Takalmi na ne ya tsinke na tsaya lallabawa su kuma duk basu lura ba suna ta hira. Ina ta kwada musu kira amma sam ba su ji ba. Hakan yasa kawai na cire takalman na rungume su na fara saurin kamo su.
"Assalamu alaikum." Naji an min sallama. Wani saurayi ne dogon gaske gashi fari tas amma duk da haka kana mishi kallo daya kasan ba balarabe bane.
"Wa'alaikumus salam." Na amsa ina kallon gaba na yayinda su Abba suka min nisa.
"Nawfal Akhiy!" Naji muryar sa. Wallahi na zata gizo kawai take min shiyasa ko daga kaina banyi ba.
"Na'am Muhammad Akhiy ha anaa, ra'aitu bintan Jameelah." Ba wani larabci na iya sosai ba amma na gane abunda yace saboda mu'allim dinmu yana mana larabci jefi jefi.
Yana karasowa ya kalle ni, nima sai na daga kai na kalle shi. Tsakanin ni da shi ban san waye yafi mamakin ganin wani ba. Wato ina can ina ta fama da kaina shi yana Madinah yana jin dadi. Bani da lokacin tambaya ko karatu yake ko akasin haka. Ni dai kawai na tsinci kaina da fushi dashi sosai.
"Jameelah!" Ya fada yanda gaba daya naji sunan ya shige ni ta ko wacce kofar jikina. Amma sai na qudurtawa zuciyata ba zan nuna hakan ba. I truly missed him beyond my inscribing capability. Nasan zaiyi tunanin zanyi tafi nayi tsalle koma na rungume shi duk da ban taba yin hakan ba.
Dauke kaina nayi. Shi kuma Nawfal kawai takalmin sa naga ya cire ya bani. Babu musu akan idon Sheikh na karba na saka.
"Shukran Akhiy Nawfal." Na juya zan tafi kamar ban ga Sheikh ba. Mamaki ma ya hana shi motsi.
Ina juyawa naji Nawfal ya tambaye shi ko ya sanni ne. Yace masa eh. Bai qara da komai ba ya biyo ni.
Yana ta kiran suna na naqi juyawa sam. Ya qara saurinsa yayin da Nawfal din kawai ya juya. Takalmin Nawfal yamin girma sosai shiyasa na kasa gudu saboda tsoron kar na fadi.
"Jameelah listen!" Naji ya fisgo hannu na. Sai naji zuciyata tayi rauni.
Fisgewa nayi. "No Sheikh!" Na cigaba da tafiya ta.
Sake biyo ni yayi naga idan na biye masa mukayi yar tsere to ni zan sha wahala tunda ban taba zuwa makarantar ba. Hankali na take ta tashi da naga babu su Abba babu alamar su. Juyawa nayi naga bani da nisa da gate. Ajiyar zuciya nayi, ko ba komai sai na koma na jira su nasan dole zasu fito.
"Meelaty, please. Dan Allah ki tsaya kiji," daga masa hannu nayi irin kalar wanda Abba yayi min. Kai na a kasa yake. Bana jin zan iya kallon fuskarsa balle na saka ido na a cikin nasa. Ina da tabbacin zuciyata yaudara ta zatayi in har na hada ido dashi domin idon yana tafiya dani.
"Bayani zan miki Meelaty." Yayi kasa da muryar sa. Wannan karan ma ji nayi gaba daya jini na yana tsinkewa, zuciyata tana yunkurin yafe masa.
"Ka kyale ni. Just leave me alone Salim. Leave me alone!" Ina fadan haka, kuka ya kwace mun. Da gudu na bace masa da gani. Ban juyo ba har na isa get. Nan na samu waje na durqushe na fara hawaye. Wannan soyayya tana wahalar dani.
Gaskiya ne; na haukace. Babu tantama; na sakarce. Babu shakka; na dolence kuma na kauyence duk a sunan soyayya.
****
Ganin security kawai yayi ya harde hannu yana kallonsa. Danshin da yaji a fuskarsa ya gane hawaye ne suke tsiyaya. Shi kuwa dan tsohon da yake sanye da uniform rasa abunyi yayi.
"Malam kafi minti goma anan kana ta zubar hawaye. Me yake faruwa?" Firgigit ya dawo daga tunanin da yake sannan ya runtse idonsa. Ji yake kamar yanzu abun yake faruwa. Sai kawai yaji kamar abunda ya faru tsakaninsa da Jameelah ne zai maimaita kansa tunda gashi Salmah ma tayi tafiyarta ta bar shi a tsaye.
Yasan cewa security officer ya gane shi saboda haka, bai ba shi amsa ba ya shiga mota kawai ya kunna AC. Ya jima kafin ya tayar da motar yaje har bakin faculty din su Salmah. Faculty of earth and environmental science. Jiranta zaiyi har su tashi. Ba zai bari tarihi ya maimaita kansa ba.
Ba zai bari ya yi sakaci irin na da ba. Ba zai bari abunda Sheikh Salim na bogi yayi ya shafi real Sheikh Salim ba. Da haka ya kifa kansa akan sitiyari yana jira su tashi.
****
Toh....
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top