HUDU | PRESENT

Dedicated to Halimatuuu_____

***

"Kai Yaya!" Salmah ta fada tana dariya. Yau kam duk sanda mutum ya gifta zaiji dariyar ta saboda Yaya Farouq yazo hutu. A jami'ar dake Sokoto yake karatu kuma a halin yanzu saura zango daya ya kammala.

Shine wanda jininsu yazo daya. Wanda take jin zata iya fada masa komai da komai.

"Bari in wuce masallaci." Ya dubi agogonshi gami da miqewa. Murmushi Salmah tayi tare da cewa idan ya dawo yayi mata magana su cigaba da hira.

"Yau baki har kunne." Ummah ta qarasa shigowa falon tana tsokanar Salmah. Bata tanka ba saidai yar dariya da tayi kafin ta wuce cikin daki.

Tana zuwa tayi alwala tayi sallah. Tana idarwa wayarta ta fara ruri. Dan tsaki tayi kafin ta sa hannu ta dauka.

"Ranki ya dade." A ka fada daga dayan gefen. Wani tsaki taji yazo mata amma ta hadiye shi. Ko duba waye ya kira batayi ba amma daga jin kalaman farko tasan likita ne. Wai shi meye damuwarsa da rayuwarta?

"Hello? Bana ji." Ta katse tun kafin yace wani abu. Ace mutum sai naci? Ita kam ta tsani irin haka a rayuwa. Kowa kawai yayi rayuwarsa ba tare da ya takurawa wani ba.

Let everyone mind their businesses without poking nose in the affairs of others. Urgh! Was that too much to ask?

Girgiza kan ta tayi ta haye saman gado. Ita gabadaya ranta ma ya baci sai taji bata son fita falon. Dama ita fushin ta a kusa yake.

Zaman kusan mintuna da yawa tayi ta juya wannan ta juya wancan. A take ta tuno da littafin nan. Yau kam babu wanda zai hana ta karantawa.

Kofa taje ta rufe, ta dawo ta janyo jakar ta inda littafin yake. Daukowa tayi ta sake hayewa gado ta kishingida kafin ta bude fejikan taga yawansu.

Gani tayi littafin a cike yake taf. Lallai yau tana da aikin yi a gabanta. Kamar me shirin karanta Qur'an harda wata bismillahr ta da jan dogon numfashi.

Assalamu alaikum warahmatullah.

Page 1: The beginning of it all.

1998.

Watarana ne dai ba zan iya tuna kwanan watan ba amma dai nasan a watan September ne sanda muka zo hutu Nigeria. Mun yan Nigeria ne ciki da baya. Asalin yan Katsina ta Dikko. Kasancewar Abba yana aiki da wata kungiya yasa aka yi masa transfer zuwa Brighton. Temporary transfer ce saboda shekara biyar kawai zamuyi. A lokacin ina yarinya yar shekara sha hudu.

Nice ta biyun qarshe a gidan mu. Yaya Nasir ne na farko, sai Yaya Fiddausi, sai ni Jamilah sai yar autar mu Ilhaam. Tsakani na da Ilham akwai tazara sosai hakan yasa nakeji da shagwaba sosai ba kadan ba.

Ranar kuwa munje gidan Hajiya, kakarmu ta wajen mahaifin mu a Katsina. Bayan mun gaysa sai na fice waje domin ganin gari. Ba wuya abun naga wasu yaran maqwabtan ta kamar sa'anni na zasu tafi talla.

"Dan Allah zan bi ku." Na roqe su. Abun mamaki sai suka fara musu, ko wacce tana cewa ita zan bi. Wadda tafi su tsafta na kalla nace nikam ita ce kawa ta. Bani da kyamar kusantar talaka amma kuma bana son kazanta ko kadan.

Farantin gyadar ta ta sauke ta bani ta ce idan ina so na dauki kulli daya kafin mu tafi. Tambayar ta nayi idan babu matsala a hakan tace iyi. Duk da hakan dai nace zan biya in mun komo gida.

Ganin muna tafiya a jere gwanin sha'awa yasa nace don Allah nima a bani faranti na riqe tawa gyadar. Babu musu kam suka bani.

Tafiya muke yi muna asiye gyada har muka iso bakin titi inda na ga da mai mota ya sauke gilashin motar sa za'a fara guje guje.

Bazaka taba ganin irin wannan a Brighton ba. Asali ma idan aka ga mutum yayi kamar bara yake ko talla akan titi kama shi a keyi.

A gaban wata mota muka tsaya inda mai tuqin yayi kiran mu. A guje na qarasa shiyasa na dan dafa motar ina haaki. Abunka da wadda bata saba ba.

A haka dai cikin lokaci kadan muka siyar da gyada muka koma gida. Na sha fada sosai har ma an kusa duka na amma ban damu ba because I had a lotta fun out there. I didn't care about what Ummah and Abba did to me.

Ko da mukazo tafiya sai naji dama a barni. Ko yunkurin tambaya banyi ba saboda nasan ba abu ne me yuiwa ba. A haka muka tattara muka koma. Rayuwa ta cigaba da tafiya har na kammala high school. A lokacin ne na tayar da rigima sosai nace ni akan dole a Nigeria zanyi jami'a idan ba haka ba kuma zan kai qarar mahaifana nace sunyi violating rights dina. Dama qawaye na sun sha gaya mun da ace sune suke rayuwar gidan mu da tuni sun mutu saboda takura. Wasu acikin su su ka nuna min cewar zan iya kai qara idan aka takurawa rayuwa ta.

Da wannan dalilin yasa Abba kawai yace zaifi dacewa a mayar da ni Nigeria gidan kakata saboda da alama idan na cigaba da rayuwa tare dasu kuma na girma zan yi fitina. Domin kuwa ina shiga shekara sha takwas zan buqaci a ware mun gida.

Ba abi ta abunda Umma zata ce ba aka tattara mun komai nawa sai Nigeria. Murna kamar inyi me. Wani abun haushi shine duk wadannan masu tallar sunyi aure sun dena talla. Wasun su ma har yara sun ajiye. Ban ji dadi ba amma dai haka na haqura. Duk sai naji kuma bana jin dadin zaman saboda kaka ta ba mai magana bace.

A haka dai a ka fara fafutukar samo min admission a jami'ar da ke nan Katsina. Na samu na fara zuwa inda nake karantar mass communication.

A lokackin kuwa SHIEKH malami ne. Yana koyarwa a department na Islamic studies. Lokacin yana tashen quruciyarsa, saurayi ne kyakkyawa na ajin farko don kuwa yan mata tururuwa suke yi akan sa. Shi kuma kamar ba malami ba, yana da kallon mata da kula su. Hakan yasa gaba daya nikam naji na tsane shi. Gashi kuma yana da gadara da nuna isa.

Taya na san hakan koh? Aminiyata Hadiza tana bala'in son shi. Kullum takan fito kofar department dinmu ta zauna ta jira ya fito daga faculty dinsu ya wuce a motar sa.

A lokacin mutane da dama basu mallaki mota ba musamman ma malaman makaranta. Naji ana cewa mahaifinsa mai kudin gaske ne.

Toh da wannan haukar Hadizah, rannan sai ta yi masa girki taci kwalliya sosai tace nayi mata rakiya zuwa ofis dinsa. Ban tsaya musu ba saboda nasan ba zata sauya ra'ayinta a kan shi ba. Bayan mun gama lecture muka shirya mukaje.

A bakin qofa muka tsaya Hadiza tana ta faman addua kamar babu gobe. Nice ma na kwankwansa kofar yace mu shiga. Ko da muka shiga wasu mata biyu muka gani suna ta fari da ido suna dariya shi kuma yana aiki a laptop dinsa. Tabe baki nayi na samu gefe na kame a wata couch.

Hadiza ce ta gayshe shi. Nikam ko kallan sa banyi ba.

"Ya akayi ne?" Ya tambaya yana wani yatsina fuska.

"Emm, Malam daman... Nace ko wadannan zasu iya bamu waje?" Ta fada tana nuna yan matan da suke zaune a gaban teburin sa. Harara suke shiga aika mata ita kuwa ko kula su bata yi ba.

"Ke kuma ofis din na gidan ku ne da kika samu waje kika zauna? Ko na baki izinin zama ne?" Yi nayi tamkar banji ba. Lallai ma mutumin nan yana ji da wulaqanci. Duk Hadizah ce ta janyo mana.

Littafi na na cigaba da dubawa har ma wani lokacin ina tuntsurewa da dariya kamar irin na tuno abu. Kunsan yanda dariya take da cin rai.

"Get out of my office!" Ya wani daka tsawa. Ko gigau banyi ba.

"Zaki fita ko sai rai ya baci?" Hakan da ya fada neh ya saka wata er dariya ta zo min. Rufe littafin nayi a hankali sannan na kalle shi.

"Wai da ni kake?" Na tsare shi da idanuwa kamar yanda naga yana kallo na shima. Kafin yace wani abu, nayi bakin qofa na tsaya.

"Dalla malama dauki lalataccen abincin ki kiyi gaba. Da fuska tamkar ta biri." Ya jefi Hadizah da wadannan kalaman. Eh toh, ta bani tausayi saboda haka naga idonta ya fara ruwa yayinda hannun ta ke ta rawa. A hankali ta dauki flask din tana neman fita inda ni kuma na tsaya a bakin kofar ina sake tattauna maganar da ya gaya mata a cikin raina.

Taka wa nayi har inda yake da niyar masifa. Yan matan da suke zaune ne suka gaji sukace zasu tafi.

Ko amsa bai ba su ba.

"Kai waye da zaka zagi halittar Allah?" Na fada ina nuna shi da yatsa na.

"Ki sauke hannunki. Bana son raini." Ya fada cikin muryar da take nunawa cewa umarni yake ban.

"Sai ka sauke idan zaka iya!" Na fada cikin tsiwa. Kafin na qarasa rufe baki na, har yau kama hannu na ya matse.

Hadizah ce tayi saurin qarasowa daidai inda muke.

"Haba..." Ta fara magana.

"Stay out of this Hadizah." Na fada cikin raunanniyar murya domin kuwa na fara nadamar rashin kunyar da nayi masa. Yayi mun riqo mai zafin gaske. Da kyar nake riqe hawaye na.

"Kisan wa da wa zaki dinga yiwa rashin kunya amma banda ni!" Ya kafe ni da idanuwan sa wanda sai da nayi da na sanin kallan cikin su. Ya bani tsoro sosai.

"Fita!" Ya sake ni yana nuna kofa. Kamar wacce ake kunnawa da batir, haka na nufi kofa ba tare da nayi musu ba. A hankali naji yayi wata 'yar dariyar mugunta. Ban kula ba, na kama hannun Hadizah muka fice.

Salmah ce tayi ajiyar zuciya tana yar dariya. Ashe ma kurin Jamilahn na qarya ne. Nisawa tayi da zummar cigaba sai wayarta tayi kara. Kamar kar ta duba sai kuma ta dauka.

Baquwar number ta gani. Sallama tayi ta kara a kunnenta.

"Hehehe kina tunanin bana iya binciko duk inda kika shiga a fadin duniyar nan?" Kamar wadda aka zubawa qanqara haka ta daskare a wajen. Ba zata taba mantawa da mai wannan muryar ba. Innalillahi wa inna ilaihirajiun.

"Kina mamaki ko? Zan zo har gidan da kike gobe." Kafin tayi magana, ya kashe wayar. Wani wahalallen kuka ne ya kwace mata. Yau kam ta shiga uku. Wanda ta gujewa shekarar da ta gabata shi yake son dawowa. Wanda ya zama sanadiyyar hargitsewar rayuwarta.

Yanzu ya zata yi idan su Ummah suka ji? Dafe kanta tayi tana kuka mai tsuma zuciya. Kamar ko da yaushe ji tayi tana da buqatar ta sha syrup ko ta samu sauqi.

Da sauri ta sauko daga kan gado tana neman inda ta ajiye. Wayar ta ce ta qara yin qara ta duba taga Salim neh yake kiranta. Wanda take karanta labarin sa mintuna kadan da suka wuce ba tare da ta sani ba saboda sam har yau bata fahimci shine wannan sheikh din ba.

Daukar wayar sa tana matuqar faranta mata rai.

It has started becoming her new addiction, which she was oblivious to.

"Assalamu alaikum." Ta fada gami da komawa saman gado. A hankali ya fahimci tana cikin damuwa. Haka yayi ta Jan ta da hira har dare yayi sosai. Lokacin kuwa, Salmah ta manta  da wani kiran waya da ya firgitata.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top