GOMA | JAMILAH'S POV

Jamilah.
Page 5;
The disappointment.

Bayan mun gama magana da Umma, bamu cigaba da hira ba nayi sauri na tashi ina jin raina duk wani iri amma daga baya sai naji sanyi. Nasan sheikh dina zai basu mamaki duk kansu.

Ina shiga daki, na watsa ruwa nayi sallah na haye kan gado. Waya ta na zaro a kasan filo inda daman nan ne mazauninta. Nan take zuciyata ta fara tsalle a kirjina ina jin dadi. Na juya na juya na rasa ta ina ma zan gaya masa ana son ganin sa a gidan mu. Ni dai gaba daya farin ciki ya hana ni wani tunani mai kyau.

Danna kiran kawai nayi wataqila idan ya dauka na samu abun cewa. Har ta kusa katsewa sannan ya dauka. Bayan mun gaisa sai muka danyi shiru kowa ya na tunani irin nasa.

Can dabara ta fado min. "Albishirinka!" Na fada ina fadada murmushin fuska ta kamar wadda yake gani.

"Goro, meye?" Ya fada a daqile. Gaba daya sai naji gwiwata ta sage. The little courage I gathered within me flew into nothing. Na neme shi na rasa.

"Haba dan Allah. Ai ba haka ake yi ba. This your response just killed my vibe. Na fasa fadan abun da nayi niyya ma." Kit na kashe wayar na mirgina daya barin gadon. A hankali naji wasu hawaye sun taho amma ko kadan ban san dalilin zuwansu ba.

Na sani Sheikh ya tsani mutum ya kashe masa waya ko da kuwa kai ka kira shi, shiyasa na kashe saboda yaji haushi na. Ina kwance abun duniya ya ishe ni sai ga kiransa ya shigo. Hannu na yana rawar murna na dauka ina kallon wayar. Zuciyata ta rada min kar na dauka. Wani bangaren kuwa tunzura ni yake na dauka. Ban san ya akayi ba sai ki nayi na dauki kiran na kara a kunne na.

"Kiyi hakuri." Murmushi nayi na tabe baki. Sai da na sosa kaina sannan na shagwabe fuska.

"Ni ban hakura."

"Haba Matar sheikh, so kike a ji kanmu ne? Yauwa gaya mun meye albishir din? Nasan babban goro ne. Um? Yauwa yan mata." Qarshen maganar ne ya ban dariya.

"To yan maza." Dariya yayi mai qaramin sauti kafin naji yayi shiru. Da dukkan alamu ni yake jira. Hadiye yawun bakina nayi kafin nayi gyaran murya.

"Dazu munyi magana da Umma akan ka."

"Bata amince ba ko?" Shiru nayi, ina nazari.

"Nace bata yarda dani ba ko? Kamar yadda kowa baya so na ko?" Ban ce komai ba har yanzu.

"Ki min magana mana." A wannan gabar, dariya ta kufce mun. Sai da nayi mai isata sannan nayi shiru. Na san har cikin sa ya kada.

"Ance ka zo gobe." Ban jira amsarsa ba, na kashe ina murmushi. Pillow dina nayi hugging very tight feeling as if my chest wanted to burst open. Kamar zuciyata zata fito saboda yanayin da na tsinci kaina.

'Karfe nawa zaka zo?' Na tura masa saqo. Sai bayan kusan awa daya, sannan ma har barci ya fara fisgata sannan ya bani amsa wai zai zo bayan sallar isha'i. Ban ba shi amsa ba, na kifa wayar sai barci.

****

Da sassafe na tashi na sanar da Umma da zuwan sheikh saboda ta fadawa Abba da wuri. Bayan na gaya mata ne an gama komai na aikace aikacen gida sai tace a hadawa Sheikh abinci. Ta tambayeni wani kalar abinci yake so na tsaya sosa qeya.

"Ban fahimci shirun da kikayi ba. Kina nufin baki san me yafi so na ko me? Wannan wace irin soyayya kikeyi ne? I love you, I love you kawai kika sani ko? Ko ba shi kike son aura bane?" Ni dai yau Umma ta ritsa ni kuma ta saka ni a tarko. Na bude baki na yafi sau a kirga amma sam na rasa abun cewa.

"Na sani daman despite your age, baki san meye soyayya ba kawai hauka kikeyi Jameelah. Baki da hankali." A karo na farko na amince da bani da hankalin. Saboda da an kalle ni za'a ga alamun haka saboda duk nayi wani sororo a gaban Umma. Idona ya raina fatata. Na yarda bani da hankali amma haukar tawa ta son da nake ma Sheikh ne.

If I only I knew I was really crazy in the reality, things would've been easier in the future. Amma na makara!

"Umma shi bai fiya son abinci ba fa. Ya fi son fruits, a gidan su ma fa fruits da veggies ake ci yawancin lokuta. Kuma baya cin naman kaza. In short, he's a vegetarian." Ban san ya akayi ba, kawai wannan qaryar ta fado min kuma na shararawa Umma ita.

Bata kulani ba ita da Mrs Ruth suka cigaba da girke girken su.

Juyawa nayi kawai na koma daki. Littafi na dauka na bude wai dan na dauke hankalina from the hassle of what just happened amma sam na kasa karanta komai.

Kawai tuno yanda Umma tace mun bani da hankali nake yi. Shin da gaske ne? Waya ta na jawo na kira yaya.

Yana dauka ko gaishe shi banyi ba.

"Yaya is it true?" Sai da ya danyi jim kafin yayi magana.

"What?"

"That I'm crazy? Like Umma tace wai hauka nakeyi kuma bani da hankali. Yaya dama ni mahaukaciya ce ban sani ba? Yaya ta ya ake gane mutum mahaukaci ne? Wayyo Allah ashe duk inda nake zuwa kallon mahaukaciya ake min? I'm doomed yaya." Tsaki kawai naji yayi.

"Magana da yawa a lokaci daya, yawan surutu da tambayoyi duk alamar hauka ne." Ya amsa min.

"Wayyo Allah na shiga aljanna na makale. Yaya yanzu haukacewa zan yi?" Na sake tambaya.

"Zama ki fito ne. Sakarya kawai." Sai ya kashe wayar.

Mahaukaciya, mara hankali, sakarya? Duk ni kadai a yau. Yau dai da alama ta hannun hagu na tashi.

Ina cikin jujjuya maganganun a kai na sai Ilham ta shigo. Janyota nayi ta zauna kusa dani.

"Ilham am I crazy? Wai bani da hankali?" Shiru tayi.

"Gashi dai saura yan kwanki ki shiga shekara ashirin amma sis ba zan boye miki ba. Kin koma kamar yar shekara goma tun da kika hadu da mutumin nan. You used to be smart but now I can't help but describe you as dullard." Doluwa kuma? Oh ni Jameelah yau naga ta kaina. Yanzu ita kuma doluwa zata kira ni da shi. Da na hada sai naga yau nayi sabbin sunaye har hudu. Kallon da na watsa mata ne yasa tayi saurin barin dakin.

"Ya Allah!" Na fada ina kwanciya akan gado. Ba zan ma kira big sis ba kafin ita ma ta fada mun nata sabon sunan da ta rada min. Wai ko hada baki suka yi ne? A haka dai na rufe idanuwa na. Na dade a kwance ina hutawa kafin barci ya dauke ni.

Ban tashi ba sai wajen Maghrib. Nayi sallah na fara karatun qurani har zuwa lokacin isha. Da isha tayi, nayi sallah na watsa ruwa sannan na saka kaya.

Falo na samu kowa yana zaune. Gefe kawai na zauna duk aka zuba min ido. Da alama dai so suke ince ko gashi a hanya ko kuma ya qaraso.

Banyi ko daya daga ciki ba.

****

Zaune Salim yake a cikin abokansa ana ta hira kamar ba shi ake jira a can gidansu Jamilah ba.

"Sheikh wai ni kuwa yarinyar nan kana son ta kuwa? In baka so ka bamu hanya kawai." Mudassir ya tambaya. Bai yi aune ba yaji Salim ya kai masa naushi.

"Baka da hankali!" Salim din ya fada yana miqewa ya bar wajen yayinda sauran abokan suka riqe Mudassir kuma suka bi Salim da ido.

Ko da ya qarasa cikin gida, bai tarar da kowa ba a haraba saboda haka daki ya wuce kai tsaye. Yana zuwa ya kunna wayar sa wadda ya kashe tun da rana. Saqonnin Jameelah ne tun daga barka da safiya har zuwa tambayarsa ko lafiya qalau yake. Ko zai iya zuwa ko ba zai iya zuwa ba.

Shi kam kara kashe wayar yayi, zuciyar sa na masa zafi yayinda ya tuno kiran wayar da ya amsa na qarshe kafin ya kashe wayar. Kiran da gaba daya ya ruguza masa lissafi ya rasa kuma ta inda zai fara kama shi.

Tsaki yayi kawai ya kwanta.

****

Shiru shiru har tara tayi babu shi babu dalilinsa. Har tsakar gida na fita dubawa ko zan ganshi amma babu alamar sa.

"Kinga irinta ko? Na gaya miki yaron bashi da mutunci. Kalli inda ya shanya mu kamar wasu sa'o'insa. Sai kije kiyiwa Abban bayani dan bani da lokacin jin haukar ki." Jikina ba qaramin sanyi yayi ba.

Da wanne zanji? Da rashin samun sa a waya ko da fadan Umma?

A haka dai na lallaba naje na durqusa gaban Abba. Tun kafin nace komai naga ya daga mun hannu. Hannun nasa nabi da ido sannan kuma na kalli fuskarsa inda naga babu alamar wasa a tattare da ita. Idonsa yayi jaa. Abba baya son raini komai kankantarsa.

"Kar kice mun komai. Ina so ki bude kunnenki da kyau ki saurare ni. Daga yau babu ke babu shi. Yaron banga alama yasan me ne girmama magabata ba."

"Amma Abba..." Hannun sa ne ya sake katseni.

"Ki bace mun da gani. Jameelah I don't want to see you here in the next minute!" Ya daka mun wata tsawa wanda na san qarar ta ne ya kada ni har dakina.

Ina shiga na kullo kofa sai kuka. Wannan wace irin rayuwa ce? Wai meye laifinsa ne? Ni har yau ban ga ko daya ba! Wataqila yana can ma bashi da lafiya. Wataqila yana asibiti amma duk basu duba wannan ba. Allah sarki sheikh dina.

'Ina tare da kai ko yaushe kuma zan cigaba da yi maka uzuri a kowanne hali!' Na fada da qarfi ina sake fashewa da kuka.

****

Nidai ba abunda zance illa "Sannu fa, Jamilah." Ku fa?

A dinga vote da comment sai na samu qarfin gwiwan yin typing a kai kai.

Wadanda suke iya qoqarinsu wajen bin labarin daki daki, da voting har comment ma, ina miqo saqon godiya. Na gode!

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top