BIYU | PRESENT

Assalamu alaikum.

Let's do the tag thingy. Tag our friends in the comment section. And share on our social medias.
Thank you.

Dedicated to Saadah_Mohd.🌷

****

A hankali jikinta ya fara motsi, tana jujjuyawa kamar jikin nata ciwo yake. Hasken rana da ya bullo ta windo ne ya haske mata ido hakan yasa ta kasa bude idon nata da wuri.

Sai da ta dan bude daya a hankali, sannan ta kalli hannunta wanda taji yana mata zafi zafi sai ta ankara ma allurar qarin ruwa ce a jikinta. Zumbur ta tashi a tsorace tana kallon gefen ta inda wata mata itama take barci.

Me ya kawo ni asibiti? Ta tambayi kanta tana kalle kalle kamar wacce ta samu tabin hankali. A hankali ta fara tuna abun da ya faru.

Runtse idonta tayi cikin fargaba. Allah yasa dai ba'a fadawa su Ummah dalilin sumar ta ba. Tana cikin wannan tunani ne zai taga an bude kofa.

Likita ne, wani saurayi kyakkyawa da zai wuce shekara talatin ba ya qaraso wajen ta yana dan murmushi. Kau da kai tayi domin ita a duniyar nan babu wanda tafi tsana kamar namiji. Musamman ma idan yana nuna mata kula Sai taji duk ta tsani mutum.

"Sannu ko? Ya jikin malama...?" Ya qarasa tambayar yana neman yaji sunan ta.

"Lafiya lau. Ina su Umma?" Ta tambaya ba tare da ta bashi amsar tambayar ba. Kafin ta sake yin maganar sai ga iyayen nata sun shigo.

"Alhamdulillah. Likita me ka gani a test din?" Ummah ta tambaya gami da rungume Salmahn.

"Gajiya ceh, depression, da kuma..." Sai ya mayar da kallonsa zuwa Salmah.

Kallon da yake mata ne yasa ta sha jinin jikinta. Bata ankara ba taji zuciyarta na dukan uku uku a lokaci guda. Yau idan likitan nan ya tona mata asiri ya zatayi? Tab lallai yau tana cikin matsala.

Itama kallonshi ta shiga yi tana me roqon sa ta idonta. Murmushi yayi, haka kawai sai taji hankalinta ya dan kwanta.

Allah dai yasa bazai kwafsa ba.

"Sai kuma wataqila rashin barci. Amma ga magunguna da zaki siyo a waje Ummah." Ya miqa mata wata takarda. Da sauri Ummah ta karba tayi waje ya rage daga Salmah sai likitan sai wasu masu jinyar kuma.

Zagayo wa yayi, ya duba gudun ruwan da ake kara mata kafin ya gyara muryar sa.

"Me yasa kika sha qwaya?" Ya tambaya cikin wani irin salo da yasa jikinta ya fara rawa. Bata taba samun wanda yayi mata wannan tambayar ba kuma ba tajin zata iya bayar da amsar tambayar ko da kuwa tilasta ta za'ayi.

Kallon ta yayi, ya tabe bakin shi kafin ya sake magana. "Idan baki fada ba fa zan gaya wa Ummah saboda naga alama kamar basu san halin da kike ciki ba." A razane ta daga kanta tana kallon shi. Gaba daya ma ta rasa ta yanda zata yi mishi magana. Itakam ta sani cewa idan Ummah taji labarin nan kwanan ta ya qare.

The day Ummah will find out that she was using drugs was her biggest nightmare. She would do all it takes taga cewa ta boye wannan halin nata.

Gyaran muryan da likitan yayi ne ya saka ta dawo daga duniyar tunani. Toh yanzu shi me yake so tace masa?

"Ehmm, daman... Dan Allah ko zaka iya mantawa da wannan tambayar?" Ta fada a hankali. Shi kuwa likitan kallon fuskarta yakeyi sosai yana mamakin me zai saka kyakkyawar yarinya kamar ita shan qwaya.

"Da alama dai so kike su Ummah suji labari. Then, it will be easier." Ya juya zai fita sai ga Ummah nan ta shigo.

Hadiyan yawu Salmahn tayi tare da hade hannayan ta biyu a boye tana roqon shi. Gyada kai kawai yayi ya juya ya fita yana tausayin ta sosai.

"An gaya miki boko ba addini bace amma kin qi ji. Shin yaushe zaki dena karatun hauka ne? Ko sai kin kai kanki kabari kafin lokacin ki ne?" Ummah tasha yi mata fada akan zaman daki wanda take tunanin idan Salmahn ta zauna to karatu takeyi.

"Ummah idan na fadi kuma fada zakui min fa." Ta fada a shagwabe tana turo baki. Ita kam Salmah tana sane da duk abinda takeyi. Wasu lokutan ma sai ta sha qwayar ta ta kwanta, sai ta kifa littafi akan fuskarta dan ayi zaton ko karatu ne ya saka ta barci. Lokuta da yawa kuma rike littafin take hannu. Ita kuma Ummah da ta leqa dakin ta ganta da littafi, sai tausayinta ya kamata.

If only she knows the truth.

Sun danyi shiru ne, aka turo kofar dakin a hankali. Gaba daya suka mayar da kallonsu zuwa qofa.

Anty Samirah maqociyarsu su ka gani ta shigo da manya manya filasai da alama abinci ta kawo. Anty Samirah mace ce mai kirki da son taimako. Ita daman bata da da ko ya ko daya, da wannan dalilin yasa take son ko wani yaro ko yarinya. Sannan kuma idan taga mutum babu lafiya tana iya qoqarin ta taga ta taimake shi.

"Anty Samirah ina wuni." Salmah ta gaisheta bayan sun gama gaisawa da Ummah.

"Lafiya lau, ya jikin?"

"Da sauqi."

"Toh Allah ya qara sauqi." Ta fada tana zuba musu abinci. A haka sukaci suna hira. Da yamma tayi aka sallami Salmah ta tafi gida. Amma fa kafin ayi musu sallamar sai da likitan yayi dabara ya karbi nambar Salmah. Ranta bai so ba amma saboda kar Ummah tayi magana ya sa ta bashi.

****

Bayan kwana biyu Salmah ta warware sarai har ma taje gidan kitso ta dawo. Suna zaune suna cin abincin dare neh sai Muhammad ya gyara murya yace.

"Ummah misali ace wadda nakeso tana shan qwaya zaki barni na aure ta?" Duuum. Salmah taji gabanta ya fadi musamman ma da taga kallonta yake.

When you're guilty... You know. Lol.

Ummah ceh ta buga salati sannan ta riqe haba tace, "Er qwaya! Tazo tana maka maye a gida? Allah ya kiyaye."

"Toh misali ace yaudarata tayi sai bayan na aureta na gane. Kuma ko a gidansu ma ba wanda ya sani fa?" Wai meye hakan ne? Me yasa yake son ci mata mutunci ne? Shi babu rufin asiri a lamarinsa?

Salmah's heart was literally burning and threatening to break it's confines.

"Wallahi sakinta zaka yi babu ruwana domin ba zaka gurbata tarbiyan yaranka tun wuri ba." Ummah ta fada tana gatsine.

Salmah ce ta gaji da jin zancen. A masife ta fara magana bata sani ba.

"Haba dan Allah dan annabi. Ku ka san ko meye zai kasance dalilin shiga halin da take? Ko kuwa littafin qaddara a hannun ta yake? Gaskiya Ku sake tunani." Har ta ida maganar numfashinta yana sama sama.

"Ke kuma meye na tsarguwa?" Muhammad din ya jefe ta da tambayar da ta sa hantar cikin ta ta kada.

"Ni ban tsargu ba. Kawai akwai wadda na sani ne... Amma kar ka damu ba sai kaji labarinta ba." Ta fada gami da miqewa tabar abincin a wajen.

The place suffocates her!

Tana shigewa daki, ta zauna ta fara rusa kuka har barci yayi gaba da ita.

****

Washe gari Salmah tayi iya qoqarin ta ta tabbatar basu hadu da Muhammad ba ko a wajen cin abinci. A gaggauce ta shirya ta fice saboda daman lakcar safe ce da ita.

Tana zuwa makaranta ta tarar da qawayen nata zaune a qasan wata bishiya suna hira. Tayi mamakin ganin su bayan kamata yayi ace suna aji a wannan lokacin.

"Yoo girls!" Ta qarasa tana daga musu hannu.

"Kunji sabuwar sallama daga wajen uztaziyar cikin mu. Yoo Salmah ya kike?" Sa'ada ta tambaya in a sarcastic way. Salmah ce ta harare ta kafin ta zauna. Ita ta rasa me yasa Sa'adatu take yi mata irin wannan abun.

"Ya kuka zauna anan?" Ta tambaya tana kallon gefe inda taga wasu fuskokin da ta sani.

"Ai an fasa lecture yau. Kinsan ashe malaman nan basu tafi ba. So, yau ma zasu sake lakca karfe goma shine muka fito nan saboda ana can ana yiwa tiyatar kwalliya kamar wanda za'ayi wani biki. Hmm." Raudah ta bayar da amsa tana dage girarta hade da yatsina fuska.

Salmah wadda ta ji dalilin ne ya saka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki. Tabbas ko Ummah bata tilasta ta zama ba tana son zama.

"Yanzu wannan sheikha zata ce sai mun zauna." Sukayi wa Salmah gatse.

"Babu dole fah. Zaku iya tafiya." Ta fada ranta a bace.

"Salmah matso kiji dan Allah." Matsawa tayi kusa da Raudah tana jira taji me Raudah zata gaya mata.

"Ko kina da abun?" Tsaki Salmah tayi ta zata ma wani abun kirki za'a gaya mata. Sai kawai ayi mata zancen syrup. Ita Allah ya sani ba'a son ranta takeyi ba kawai saboda ya riga ya zame mata jiki ne.

"Dallah malama ki rabu dani." Ta tunkude kawar ta ta.

"Ke da anyi maganar abun sai ki kama turbune fuska. Ni na dora miki?" Wasa wasa sai fada ya barke tsakanin su har ma da sauran. Baram baram sukayi dasu. Salmah barin wajen tayi tana sharar qwalla.

Ji tayi kamar ta fasa ihu a lokacin amma sai ta danne zuciyarta ta wuce masallaci ta zauna kafin lokacin zuwan malaman yayi.

***

Kamar wancen lokacin, yau ma an cika maqil ko ina mutane ne. Wannan karan kuwa Salmah a gaba ta zauna.

Ba a jima ba malamai suka zo suka fara gabatar da kansu a karo na biyu. Sunyi lakca me ratsa zuciya sosai har yasa da yawan mutane suka share hawaye.

Salmah kuwa ji tayi gabadaya duniyar batayi mata dadi. Malamin da ta tun a wancen karan ya birgeta wato SHEIKH MUHAMMAD SALIM ya dade yana magana. A qarshe ya fara karanto suratul mu'uminun yana fassarawa.

"Allah yace qad aflahal mu'uminun wato lallai mumuninai sunyi nasara. Allah dai tsaya a nan ba sai da ya fada mana su waye mumunai. Ya jama'ar wajen nan ku bani hankalin ku kuji ko kuna cikin mutanen nan." Ya fada yana kallon ko wace fuskar da idon sa yake iya gani.

A hankali idonsa ya fada kan Salmah wadda da ka kalleta kasan hankali ta a tashe yake. Sadda kanshi qasa yayi ya cigaba.

"Allah ta'alah ya qara da cewa Alladhina hum fi salatihim kashi'un. Wannan ayar ba wai ta tsaya kan maganar masu yin Sallah ba. A'a, idan kana sallahr kana yin ta da tsoran Allah? Ma'ana idan kana yi kana qaddarawa a gaban ubangiji kake? Shin kana tara hankalin ka waje daya ko kuma kawai yi kake kana tunanin abun duniya? Ya dan uwa, minti biyar kacal ya ishe ka kayi sallah raka'a hudu. Idan har zaka iya awa biyu kana hira me zai rage ka idan ka cire minti biyar? Wasu sai ka ga ma Sallahr kawai yi sukeyi dan kar ace basuyi ba."

"Idan kana Sallah, kana nutsuwa kaji karatun sallar na ratsa ko wacce kofar jikinki ko da kuwa baka gane abunda kake cewa? Shin idan kana Sallah kana karatun a nutse ko kuwa karatu kake kamar sautin injin markade, birrrrrrrrrrr birrrrrrrrr." Dariya aka kwashe da ita kafin ya cigaba.

"Wallahi akwai watarana na fito zanje masallaci na tarar da wasu samari a gefen titi suna hira. Har na je na dawo. Ko da na dawo na tarar basu tashi ba sai nayi musu magana. Nace kunyi Sallah kuwa sukace basuyi ba. Na tambayi dalili. Wa'iyazubillah. Kun san me suka ce min?

Wai customer sai da bashi. A lokacin sai da naji wani ciwon kai. Wato a duniyar nan akwai wanda yake tunanin in yayi Sallah saboda jin dadin Allah ne. Shin bamu san cewa Sallahr nan da duk sauran ibadu kan mu mukeyiwa ba?

Har takai ta kawo wani idan kana masa wa'azi kana cewa yaji tsoran Allah ce maka zaiyi wai no space. Dan Allah wannan wace irin lalacewa ce haka? Muji tsoran Allah mu gyara tun kafin lokaci yayi halinsa.

"Allah ya qara da cewa Wallazina hum anilagwi mu'uridun. Wadanda suke basa kusantar munanan kalamai."

"Yan uwana musulmai, muna cikin wani hali a wannan zamanin. Zagi, ashar, batsa duk sunyi yawa kuma an dauke su ba komai ba. Yanzu sai ka ga wani ance masa ubanka amma dariya zaka ga yana yi. Kaji ana fxck you amma cika zai dinga yi yana botsewa a lallai shi ya burge an kira shi da shege. Me yake faruwa? Ina muka bar tarbiyar mu? Shin bama so mu kasance cikin muminai wadanda sukayi nasara?" Ya fada muryar sa na rawa yana neman ya fara kuka.

Nan da nan dalibai suka fara Allahu Akbar kafin ya cigaba.

"Yanzu kuma ya zame mana jiki. Muyi gulma, muyi annamimanci, munafurci, cin naman mutum duk ba tare da jin komai ba. Abun har ya kai ga kaga yan uwan juna, uwa daya uba daya suna gulmar junan su ina ga bare? A hakan muke so mu shiga aljanna? 'Yan uwa ku tuna cewa ranar alkiyama Allah zai iya yafe maka wani abun wanda ya ke tsakanin ka dashi amma banda haqqin wani. Yau idan akace kaci naman mutum yazo yaqi yafe maka ya zaka yi? Mu sake tunani ayyuhal ikwaat." Ya matse kwallarsa ya cigaba da fassara har sai da yazo qarshen bayanin siffar muminai.

Yace " Lallai wadannan da muka lissafo sune magadan aljannah firdausi. Sune wadanda zasu shige ta har abada. Ya dan uwa, yanzu zabi ya rage naka. Ka zauna kayi tunani. Kai mumini neh? Idan ka ga kana da wata matsala sai kayi hanzarin gyarawa tun kafin lokaci ya qure domin idan lokacin mutuwar rai tazo Allah baya qara ko da kuwa sakan daya ne." A lokacin da ya rufe lakcar tashi hawaye yake sosai har sai da ya samu wajen zama.

Salmah kuwa gaba daya mutuwar zaune tayi domin gaba daya abunda ya lissafo babu wanda takeyi. Eh toh, tana Sallah amma banda kamar yanda ya kwatanta ba. Dungure dungure takeyi. Wasu lokutan ma tv na gefe tana Sallah tana jin abunda ake fada. Wasu lokutan kuma Allah Allah take ta idar ta koma kan gado.

Yanzu ya zata yi? A hankali dai lokaci ya qare malamai sukayi jawabin bankwana suka fara fita.

Salmah wadda qafarta tayi sanyi ne, ta bisu a hankali ta samu sheikh din da ya fi burgeta.

"Ya sheikh." Ta fada. Ai kuwa tayi sa'a yaji ta. Gaisawa sukayi kafin tace tana buqatar number sa saboda zata so yin magana dashi akan wasu abubuwa.

Bude jakar sa yayi ya ciro wasu kati guda biyu ya bata.

"Ya sunan malamar?"

"Salmah." Ta fada a taqaice tana jin wani irin yanayi a zuciyarta.

"Salmah." Shi ma ya fada. Har tsakiyan kanta taji sunan. Ya fade shi tamkar a bakin sa aka tsara sunan. Ko wani harafi sai da ya bashi haqqinsa. Ita kam bata taba jin dadin sunan ta ba sai yau.

"Nagode ya sheikh." Gyada kai yayi ya tafi. Yana matsawa sai taga ya yarda wani koren littafi me ban sha'awa. Dauka tayi ta bi bayan sa da zimmar bashi sai ta neme shi ta rasa.

Bude fejin farko tayi taga wani rubutu mai kyaun gaske.

Suna na Jamilah wadda aka fi sani da MATAR SHEIKH wannan shine tarihin rayuwa ta tun daga farko har zuwa aurenmu da sheikh.

Gudun zuciyarta ne ya qaru tayi saurin rufewa gami da jefa shi a cikin jakarta. Har ta koma gida tana tunanin lakcar yau da akayi da kuma koren littafin dake Jakarta.

******

Woah! A long chappie it is.

How was it?

Ga salmah ga sheikh, ga kuma koren littafi. Toh fah😌🤔

Don't forget to Vote, comment, share.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top