BAKWAI | PRESENT

***

Kwana biyu Salmah ba ta je makaranta ba haka kuma yar maganar ma da takeyi ta dena. Har ma dena fitowa tsakar gida tayi saidai in an kira ta ta yi shara ko wani abun, tana yi zata koma daki. Ummah tayi mamaki ganin canjawar Salmah lokaci daya. Gaba daya babu walwala a tare da ita kuma babu dan wannan murmushin da ta saba duk da daman baya kaiwa zuci. Muhammad ma yayi mamaki domin duk takalar ta da fada da yayi bata kula shi ba sam. Ummah ta tambayeta me yake damunta. Da farko tace bakomai, daga baya tace ciwon kai. Haka akan dole aka saka ta shan magani.

Abba kam yayi tafiya wajen kasuwancin sa wato Cotonou saboda haka bai san abunda yake faruwa ba kuma Ummah bata yi yunqurin fada masa a waya ba.

A kan gadonta wanda zama akan sa ya zaman mata al'ada take. A can qarshen gadon ta takure waje daya tare da runtse idonta tana jin wani radadi yana zagayawa dukka sassan jikinta. Idan ba zata manta ba, irin wannan abun taji ya saka ta fada halin da ta ke ciki.

Yanzun tunani kala kala take yi a ranta. Ji takeyi kamar ta dauki ranta kowa ma ya huta gaba daya. Idonta a rufe ta fara laluben wayar ta har sai da ta ji ta taba ta sannan ta janyo ta zuwa gabanta. Har yanzu bata bude idon ba. Domin gani takeyi kamar idon ta budesu, babu wanda zata gani illa fuskar da tafi tsana a duniya.

Wato fuskar Mansur.

A lalube ta danna number Salim ta kara wayar a kunnenta. Wataqila yin magana dashi yasa taji dadi. Wataqila ya fada mata kalaman da zasu sanyaya mata zuciya. A haka dai har wayar ta tsinke bai daga ba. Sai a sannan ta daga kai ta duba agogo. Karfe bakwai da rabi ta kusa. Dai dai lokacin sallar isha bayan ita a lokacin ma ko sallar magariba ba tayi ba. Tunawa tayi da abunda wannan SHEIKH din ya gaya mata tayi. Ta tuna sanda ta tura masa saqo nasiha yayi mata doguwa.

A lokacin ta shiga hankalinta yanzu kuma nasihar ta bi dayan kunnen ta ta fice. Ya gaya mata a duk sanda take cikin damuwa, ta samu tayi sallah ko raka'a biyu ce zata samu sassauci. Idan ba zata iya hakan ba, ko iya alwalar ce tayi. In itama ta gagara, to ta karanta qurani ko kuma ta dinga salati ba adadi a cikin ranta.

Salmah ce ta dan yi murmushin takaici a lokacin. Dan ko sallar farillar ma ba'ayinta yanda ta dace ina kuma ga nafila?

Sallah ita ce farko a rayuwar mutum. Ita ce abu na farko da za'a fara dubawa a littafin mutum ranar hisabi. Sallah ita ce ta farko a shikashikan musulinci bayan shahada. Kenan idan mutum baya sallah ya zama ba shida babancin da wanda ba musulmi ba.

Sannan an bayar da misalin wasu mutane wanda zasu tashi a cikin wuta ranar qiyama idan aka tambaye su dalilin shigar su wuta, zasu ce— mun kasance cikin wadanda basa sallah.

Qalu lam naaku minal-musallin.

Sallahr nan dai ita take hani daga mummunan aiki.

Innas-salata tanha anil fahsha'i wal munkar...

Yayin da mutum ya ga rayuwa bata tafiyar masa dai dai yanda yaso, abu na farko shine ya fara duba yanayin sallar sa; tun daga tsarki zuwa alwala. Ance sallah itace mabudi ko mukullin aljanna, mabudin sallah kuma shine tsafta da tsarki. Ashe kenan idan alwalar mutum bata yi kyau ba, sallar ma ba zata yi yadda ake so ba.

Salmah har yanzu bata fahimci haka ba. Bata gane cewa ya kamata ta gyara sallarta ba, tayi ta cikin nutsuwa da lumana. Kawai dai jefi jefi tana tuna lakcar da ta zauna rannan. Toh idan ta tuna sai jikinta yayi sanyi.

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin ciwon kai na damunta. Daurewa tayi, sannan tayi saurin saukowa daga saman gadon ta shiga bandaki tayi alwala domin yin sallar farillar da bata yi ba ma tukun.

Ta idar da maghriba kenan taji an turo kofar dakin. Ummah ta gani tsaye da kwanon abinci a hannun ta.

Ganin Salmah akan dadduma ya saka Ummah ta danji dadi a ranta.

"Ga abinci kici. Gone zamu je asibiti a duba lafiyarki." Zare hijabin jikinta tayi, ta linke sannan ta zauna a gefen gado.

"Ummah ni fa ba sai anje wani asibiti ba. Gobe ma zanje makaranta domin na ji sauki." Ta fada tana tabe baki sannan ta qaqalo wani murmushi ta sanya a fuskarta duk dan Ummahn ta yarda da ita.

"Toh shikenan. Allah ya qara lafiya." Gyada kawai ta samu tayi tare da juyawa daga saitin fuskar Ummah.

"Sai da safe Ummah."

"Ki tabbatar kinci abincin nan fa. Zan zo anjima naga ko kinci in ba haka ba kuma na turo miki Muhammad ya gamu da ke." Yar dariya tayi.

"Zanci." A takaice ta fada tana kade gadonta.

"Ana karkade gidan ne?" Ummah ta fada a sigar tsokana.

"Gida kuma Ummah. Wani gida?"

"Ga shi nan kina kadewa. Ai ke gado ne gidan ki. Inaga ko a tsakiyar titi aka ajiye miki gado kwanciyarki zakiyi ba tare da kin gane a kan titi kike ba ma." Dariya Salmah tayi. Ita ma Ummah ta danyi kafin ta juya.

Har ta fice daga dakin sai kuma ta dawo kamar ta tuna wani abun.

"Salmah!" A firgice Salmah ta dago kanta. Idanunta wanda har sun canja kala tun da jimawa, ta sauke akan na Ummah.

"Na'am Ummah." Sai da ta hadiye wani abu kafin ta bayar da amsar.

Shiru taji Ummah tayi. Ita kuwa Ummah tunanin abunda zata fada takeyi. Kar taje ba zaiyiwa Salmah dadi ba saboda ita kawai na mace ce mai son fada ba. Amma yaro sai da fadan lokaci zuwa lokaci saboda tsaro. Yaro idan ya tashi bai saba da fada ba, yana zamantowa mai wata iriyar hallaya. Kowa ni mahaifi yana son dansa kawai daurewa yake yayi fadan ko dan tarbiyar dansa ta inganta. Tuna hakan ne yasa ta yiwa Salmah da alamar tazo ta zauna kusa da ita.

"Me yake damunki?" Kamar yanda Ummah tayi tsammani, girgiza kanta tayi.

"Ki dena ce min babu komai bayan kwayar idonki taqi gaskaka hakan. Abunda fuskar ki take nunawa baiyi daidai da abunda bakin ki yake furtawa ba Salmah. A ina matsalar take?" Hawaye ne suka taru a idon Salmah. Duk yanda taso ta boye su, sai da suka zubo.

A zafafe ta share su.

"Ana miki wani abun da bakya so ne a gidan nan? Nice? Muhammad ne? Ko Abba? Ni bana so naganki a cikin halin nan sai naga kamar bana kyauta miki. Tun da kin dage ba zaki fada min me yake faruwa ba inaso dan Allah ki dena damuwa. Ko sai na kira Yaya Karime ne?" Jin an ambaci wannan sunan yasa Salmah saurin yankare haqoranta.

"Ummah dan Allah ki bari. Kalli kiga, na miki alqawari ba zaki sake ganin hawaye na ba amma karki sake min maganarta." Murmushi ne ya kufce wa Ummah. Dama tana sane ta fadi hakan.

"Toh yayi kyau. Allah ya qara lafiya." Ummah ta fada tana miqewa domin ta fita. Ta san ruwan zafin da ta dora zata sha kunu ya tafasa.

Har ta fita sai ta hango wata kwalba ta gangaro daga qarqashin gado. Har zata wuce sai ta dawo. Ta dauki kwalbar.

Salmah kam ta mayar da idonta rufe sai jin muryar Ummah tayi.

"Salmah meye wannan?" Zuciyar Salmah sai da ta kusan fitowa.

****

Toh fah😁
Ya kuke gani?
Meye damuwar Salmah?
Meye tsakanin ta da Mansur? Da Yaya Karime?

Follow MATAR SHEIKH
Follow AeshaKabir.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top