9.

Hello y'all. Sorry for the long wait.
Here's a short chapter. Enjoy!!❤

9.

Da yammacin wata ranar larana Fareeha na falo tana goge uniform dinsu na boko. Sati mai zuwa inshaAllah sukeda niyyar komawa. Umma ce ta daga labule ta shigo.

"Sannu Adda"

"Yauwa Umma"

Ta samu waje ta zauna akan kujera. "In kin gama Abbanku yana nemanki"

Nan da nan ta mike. "Na ma gama"

A falon shi ta sameshi yana karatun Alqur'ani. Da tayi sallama ta shiga ta samu waje ta zauna. Tana zaune sai da ya gama karanta shafin sannan ya rufe ya dubeta.

"Adda ana ta shirin komawa makaranta ko?"

Ta gyada kai "Eh Abba"

"Toh Allah ya kaimu Allah kuma ya bada sa'a"

"Ameen"

"Ina neman wata alfarma a wajenki"

Murmushi ya kubce mata. "Abba alfarma kuma? A wajena? Ni a suwa?"

Hakan ya bashi dariya. "Ke a me sunan Mamana"

Ta sake murmusawa.

"Naji labari a wajen Ummanki wai bakya son zuwa karatu kano"

Ta dan ji wani dim.

"Kawai dai bana so nayi nisa da gida ne. Kuma naji Bappah yace wai makarantar kwana ce"

Abba ya jinjina kai. "Tabbas hakane. Shiyasa nace Ina neman alfarma a wajenki. Ina so kije ki gwada zana jarabawar shiga babban aji a makarantar. Idan Allah yasa kinci sai kije"

Zuciyarta ta qara bugu.

Abunda da take gudu shine dai ya faru. Dama dai tun dawowata daga Kano tana jira daya daga cikin iyayen nata ya dago da maganar makarantar to da taga an kwana biyu ba wanda ya mata zancen sai tayi tunanin ko sun riga sun yanke shawarar cewa bazata je bane? Ashe ba haka abun yake ba.

"Abba da na dauka cewa kafi so na zauna a nan"

"Nayi tunanin hakan. Amma yanzu wasi abubuwan sun bullo kuma danayi nazari me tsawo sai naga ba laifi idan kinje. Ni dai kawai bukata ta shine ki je ki gwada zana jarabawar shiga."

Ta hidiyi yawu mai daci.

"To Abba"

"Yauwa Addana. Allah ya miki albarka"

Idonta suka kawo hawaye wanda bata san dalilinsu ba. "Ameeen Abba"

Haka ta karasa wunin ranar gaba daya jikinta ba kwari. Ga shi Umma ta ce ta shirya kayanta da daddare washegari Bappah Dattijo zai zo daurin aure, idan zai koma tare zasu koma tunda jarabawar ranar asabar ne. Duk ta rasa abinda ke mata dadi.

Haka dai ta daddafa ta shirya kaya Kala uku don bata fata ta wuce Sunday a Kano.

Washegari kuwa bayan sallar Juma'ah sai ga Bappan ya shigo. A gidan yaci abincin rana. Sun dade suna tattaunawa da Abba kafin daga bisani yace ta fito su tafi.

Har da dan guntun kukanta haka ta fito ranta baya so.

Dayake ita kadai ce a baya shi yana gaba tareda driver sai ta sha baccinta iya son ranta. Bata tashi ba sai da suka tsaya sallah a Darki.

Anti Mami kam da ta ganta ba sai tsokana ba. Wai dama ta sani bata tafi ba sai da ta tsaya ta yi jarabawar.

"To yanzu meye amfani kinje gida kinyi kwana goma kin sake dawowa."

Idonta sukayi ja. "Anti Mami ki barni haka dan Allah"

Anti Mami tayi dariya. "Wai sai kace wanda za'a kaita prison. Ni ban gane wanann kuncin ba fa"

Haka dai tayi ta zolayarta.

Dawowar su Anisa ne ya sa ta dan sake jiki don tayi ta mata hirar makarantar da za su je din. Da Fareeha ta nuna mata kamar tana fargabar zana jarabawar sai ta kwantar mata da hankali.

"InshaAllah zata da sauki. Karki damu"

Da dare kafin su kwanta Bappah ya samesu a falon Anti Bebi. Ya sanar dasu cewa shi da kanshi zai kai su wajen zana jarabawar sannan ya musu Addu'ar samun nasara.

Tunda ta farka sallar Asuba bacci ya kaurace daga idonta. Don haka sai ta yi wanka kawai ta shirya cikin riga da skirt na atampa.

Anti Mami dake kwance ta dan juyo ta kalleta don safa da marwan da take a dakin ya tasheta.

"Adda fitar taku fa se takwas"

Fareeha tayi ajiyar zuciya. "Na kasa bacci ne wallahi"

"Ki kwantar da hankalinki. Kiyi Addu'a kuma. InshaAllah akwai alkhairi a ciki"

Gyada mata kai kawai tayi ta fita a dakin.

Amina ta samu a kitchen tana fere doya. Kujera ta jawo itama ta sa hannu. Nan da nan suka gama suka daura doyar. Amina ta dauki tsintsiya ta wuce parlor domin ta fara shara ita kuma Fareeha ta fara wanke wanke. Ba shi da yawa don an yi na dare jiya kafin su kwanta.

Ta gama tayi mopping din kitchen din sai ta sauke doyar ta fara shirin soya ta da kwai.

"Fareeha da sassafen nan? Ke da kike da exams" fadar Anti Bebi kenan da ta shigo ta sameta.

Tayi murmushi sannan ta gaisheta cikin girmamawa. Ta ce mata ta je ta zauna Amina zata karasa.

"Bakomai Mama zan iya"

Haka ta hakura ta barta inda ita kuma ta shiga shirya wa Bappah kayan shayinsa. Kafin ta gama Fareeha tayi kasko biyu don haka ta shirya masa breakfast dinshi tsab.

Karfe takwas dai-dai suka bar gida sai Rijiyar Zaki inda makarantar take. Lokacin jarabawar karfe tara. Dayake sun isa da wuri sai Bappah yace a dan zagaya dasu suga makarantar.

Ba laifi tana da kyau sosai. Ko daga tsare-tsaren ginin da kuma shukokin fulawowi ta ko ina. Komai an yi shi dai dai da zamani. Suna da isasshun ajujuwa da labs (physics, chemistry, biology, computer da catering labs) sannan suna da babban library wanda yake makil da litattafai masu matukar amfani a duk wanni fannin daya shafi ilimi. Bugu da Kari suna da Babban masallaci da kuma islamiyya. Abun ya birge Bappah sosai.

Lokacin da suka shiga jarabawa sai ya barsu ya tafi gidan wani abokinsa a Janbulo.

Bayan tafiyar su Anisa da Fareeha Anti Mami ta tashi ta kintsa kamar yadda ta saba. Tayi wa Ahmadi wanka sannan itama tayi. Ta gyara dakin tsab ta saka turaren wuta sannan ta fita ta karya.

Dawowarta daki ta samu missed call har guda biyar daga wajen Umma don ta bar wayar tana caji.

Tana murmushi ta zauna bakin gado yayinda ta ke kiran layin Umman.

"Hajiya Umma har kin fara kewar 'yar taki ne" abunda ta fara fada kenan da Umma ta dauki wayar.

"Mami ina ta kiranki ina kika shiga" Umma ta fada a gigice.

"Umma me ya faru?"

"Mami Mukhtar ne"

Nan da nan taji zuciyarta ta sauya bugu. Ta mike tsaye. "Me ya same shi?"

"Yau da safen nan ya zo gidan nan wai yana nemanki."

Gumi ya tsatstsafo mata. "Yana nema na kuma Umma?"

"Muma dai abun ya bamu mamaki. Don yayi kamar ba a hayyacinsa yake ba. Da mukace bakya garin ma kamar zai mana kuka"

Hawaye suka ciko mata a ido. Shin me ke shirin faruwa?

"Yanzu dai ina tunanin yana hanyar Kano zuwa wajenki. Na de kira Bappah ban sameshi ba shiyasa kikaga ina ta kiranki babu kakkautawa. Kije ki sanar da shi halin da ake ciki"

"Umme meke shirin faruwa?" Yanzu kam ta riga ta fara kuka. "Meyasa yake nemana?"

"Mami kiyita Addu'a. Koma menene alkhairi ne inshaAllah. Ki sa a ranki duk abunda Allah ya aiko miki zai zama alkhairi a gareki kinji ko?"

Ta gyada kai tana kokarin share hawayenta. "To Umma"

"Yanzu dai ki fada wa Bappah yanda ake ciki"

"Baya gida. Shi ya kai su Adda makarantar."

"To zan cigaba da neman sa a waya. Zamuyi ta Addu'a. Allah ya tabbatar mana da alkhairi "

"Ameen"

Ta nemi nutsuwa ta rasa a ranta gaba daya. Ta shiga kiran sunayen Allah tana ta zagaya dakin.
Ita dai tasan tunda al'amarin nan yafaru ba abunda take sai Addu'a Allah ya fidda ita lafiya kuma ya kawo mata nutsuwa da kwanciyar hankali. Toh Alhamdulillah kam hankalinta ya fara kwanciya amma tun ranar da ya kirata a kitchen da daddare ta shiga sabon babin wani tunanin. Yanzu ga abinda ya biyo baya kuma.

Ta zauna a bakin gado tana share hawayen da suka gagara tsayawa. Allah ne kadai yasan boyayyan al'amarin da ke cikin wannan abu.

Daf da Azahar su Anisa suka dawo gida. Sunsha hirarsu a mota akan yanda jarabawar ta kasance da kuma kyaun makarantar dukda ma dai Rabin hirar Anisa ne da Babanta suke yi, Fareeha sai dai in an tambayeta ta bada amsa.

Hankalinsa duk yana gida domin wayar daya samu akan Mukhtar da abokinsa sunzo ganinsa, amma hakan bai hanashi hira da 'yayan nashi ba.

Ya tsaya a Yahuza ya saya musu kaza da Habib youghurt.

"Ga wannan ku rage pressure din da kuka shiga lokacin exams din" ya fada yana mika wa kowwacensu leda daya .

Anisa tayi dariya. "Ni dama ba wata pressure lafiya kalau na rubuta"

Fareeha kuwa cewa tayi "Mungode Bappah"

"Yauwa Fareeha" ya juya wajen Anisa yace "To ke tunda jarabawar bata baki wahala ba a bani kazata"

Nan da nan ta rungume ledar "A'a Baba ta danyi wahala fa kadan"

Fareeha bata san lokacin da wata dariya ta kwace mata ba. Shima Bappahn dariyar yakeyi.

A haka suka koma gida cikin nishadi.

A kofar gida Bappah ya tarar da  Mukhtar da abokinsa suna zaune jugum jugum kaman wanda akayi wa mutuwa.

Cikin girmamawa suka gaisa sannan ya musu iso zuwa parlonsa.

Cikin gida ya shigo ya sami Anti Bebi.

"Kinada labarin bakin na da sukazo kuwa?"

Anti ta yi ajiyar zuciya. "Ina da shi. Ni nace a ce musu su tsaya a waje"

Ya hade hannayensa a kan kirjinsa yana jiran karin bayani daga gareta.

"Fisabilillah Baban Samha, yaron nan ya sakota cikin dare ta dawo gida da danyen baby, bai san cin su ba bai san shansu ba sannan kuka nemeshi akan yazo ayi magana yaki zuwa, shi ne sai yanzu daya ga ta kusa gama idda zai wani zo yace yana son ganinta? Ko yana tunanin bata da gata ne?"

Ya girgiza kanshi a yayinda wani dan guntun murmushi ya ziyarci labbansa. "Shatu am" Ya kira sunanta a hankali. "Ai in mutum ya nufeka da sharri kai kuma sai ka yi masa alkhairi. We are not going to stoop to his level. Tunda mu ya wulakanta mu, sai mu karramashi. Mu nuna masa ba duka aka taru aka zama daya ba ko?"

Ta jinjina kai.

Ya dafa kafadarta. "Yanzu dai kiyi hakuri ki sa a kawo musu ruwa da abinci ko. Sun kwaso hanya"

Ta mike tayi hanyar kitchen din tana magana kasa kasa. Yo ita tace su kwaso hanya da tsakar ranar nan su taho?

Zuciyar Fareeha na bugu ta shiga dakin don tana ganin Ya Mukhtar a kofar gida ta san ba lafiya ba. Yanayin data ganshi; yayi baki ya rame ga wata kasumba daya tara, duk sai taji tausayinshi ya kamata.

Bata sameta a dakin ba amma ganin Ahmadi a kan gado da kuma motsin data ji a bandaki ya bata tabbacin cewa Anti Mami ce a ciki.

Ta zauna a bakin gado ta riko Ahmadi wanda ke ta gwalatun sa ta fara mishi wasa.

Anti Mamin ta fito a bandaki idonta sunyi ja da alamar kuka tasha.

"Anti Mami...."

Tayi saurin girgiza mata kai. Hakan yasa ta hadiye abun da takeson fada mata.

Sallaya ta jawo tare da hijabinta ta fuskanci kibla. Ko da ta tada kabbara, wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata. Ganin haka sai Fareeha ta dauki Ahmadi suka fita a dakin don bazata jure ganin ta a haka ba. Ita ma sai ta fara kukan. Wanda a halin yanzu ba wani amfani gareshi ba.

Dakinsu Anisa ta wuce inda Anisan ke ta bawa yayarta labarin jarabawar tasu. Ta samu waje a gefen gadon ta zauna itama a ka shiga yin hirar da ita. Ta ma manta da batun kazar da aka saya musu sai da taga Anisa da Fadilan suna ci ta tuno ta bar nata a parlor. Haka ta koma ta dauko ta kawo musu tace ita ta koshi.

Abu kamar wasa tana idar da nafilarta Anti Bebi ta shigo tace Bappah yace ta shirya gobe zasu wuce Azare tareda Fareeha.

"Anti me ya faru?"

Antin tayi ajiyar zuciya. "Lamarin babba ne Mami. Maganar dai sai kunje can din. Ke dai kawai kiyita Addu'a Allah ya zaba miki abinda yafi alkhairi"

Ta gyada kai kawai ta kwantar da kanta a jikin gado.

Sai la'asar Fareeha ta shigo dakin ta sameta akan sallaya tana bacci. Ahmadi ma yayi bacci don haka ta kwantar da shi a kan gado ta shiga bandaki tayi alwala.

Data fito sai taga ta farka.

"Sannu Anti Mami" abun da kawai ta iya furta mata kenan.

Anti Mami tayi murmushi wanda banu annuri a tattare da shi. "In kinyi sallah ki tayani shiri. Bappah yace tare zamu koma gobe"

Ta na fadin haka ta wuceta ta shiga bandakin.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top