8.


Sati daya da zuwan Fareeha Kano a wata ranar alhamis da daddare Anti Bebi ta shigo dakin da suke kwana ita da Anti Mami ta sanar musu cewa zasuyi bakuwa washegarin ranar.

"Kanwar Mama ce da take zama a America" cewar Anti Bebi a yayinda ta zauna a bakin gadon"Ta dan jima bata zo ba ne yanzu kuma jikin Hajiyar su yayi tsanani shine zata zo duba ta"

Anti Mami ta jinjina zancen "Allah sarki. Allah ya kawota lafiya"

"Ameen Ameen. InshaAllah wajen goma zata iso dayake jirgin nasu a Abuja zai sauka da asuba, so zata shigo wani jirgin zuwa nan"

Fareeha dai shiru tayi tana rike da Ahmadi a hannunta wanda yayi bacci tuntuni.

"Ina so ku taimaka min wajen shirya mata abinci tunda kunga su Anisa zasu tafi makaranta da safe"

"To Anti me da me za'ayi?"

Anti Bebi ta gyara zama. "An dai kawo kaji so ina tunanin muyi farfesu. Sannan ko za mu kara da Masa da miyar taushe. Sai ayi Kunun gyada ko kuwa?"

Anti Mami ta jinjina kai "Eh hakan ma yayi"

"To saura Lunch. Me zamuyi?"

Su ka danyi shiru kafin Anti Mami tace "Tunda kin ce ba'a nan take ba kuma ta dade bata zo ba ko za'a mata wani abincin gargajiya wanda ba kasafai zata same shi ba a can?"

"Eh kuma hakane. Ina tunanin ayi sakwara amma kar aikin yayi yawa ko?"

Anti Mami ta girgiza kai hade da yin wani guntun murmushi "Ba matsala Anti inshaAllah zamu iya. Fareeha zata taya mu"

Anti Bebi ta mayar da kallon ta kan Fareeha sai taga yarinyar ta mata murmushi alamar cewa babu komai.

"To Alhamdulillah. Allah ya kaimu goben. Mami ni da ke zamuyi breakfast sai Fareeha tayi kunun gyada. Sai Amina ta tayaki ko?"

Fareeha ta gyada kai. "Allah ya kaimu"

Hakan kuwa akayi, ana sallar Asuba suka shiga kicin aka fara aiki ba kakkautawa. Su Anisa ma suka saka hannu suka taya. Karfe bakwai tana yi kuma suka karya suka yi shirin makaranta driver ya mika su. Fareeha ta gama kunun gyada tsaf sannan aka hada ta da yanka fruits.

Ba bata lokaci suka kammala komai sai aka bar Amina da Fareeha su karasa wanke-wanke da goge kitchen. Anti Bebi ta shiga wanka bayan ta bar wa driver sako cewa nan da wasu lokuta zai mika ta airport zata dauko bakuwa.

Ko da ta fito karfe tara ta dan gota don haka da sauri ta kimtsa suka fi ce. Mami suka kara gyara gidan aka saka turaren wuta sannan suma suka yi wanka. Sai a lokacin ne suka samu sukunin karyawa.

Wata annashuwa da bata san daga inda ta zo ba taji ta lullubeta a lokacin da ta shaki iskar garin Kano. Bahaushe yayi gaskiya da ya ce duk wanda ya bar gida, gida ya barshi.

Dan siririn murmushi ne a dauke a kan fuskarta a lokacinda take tura dan karamin akwatinta wanda tayi hand luggage dashi zuwa wajen daukan sauran kayan ta.

Fasinjojin da suko shigo jirgin tare da su duk sunyi cirko-cirko kowa yana jiran kayansa a wajen Baggage Claim. Zuwa wani dan lokaci kayan suka fara zuwa suna tahowa ta conveyor belt. Idonta na kai har sai da ta hango nata kayan. Tayi kokarin jawosu saidai sun yi nauyi. Wani mutum ta samu ya tayata kafin kayan su wuce. Sai a lokacin ta kara jin dama da Muazzam dinta suka taho.

Mutumin ya jejjara mata su a trolley. Ta mishi godiya mai dimbin yawa kafin ta nufi hanyar fita.

Batayi minti biyar da fitowa ba ta hango Anti Bebi tana isowa gareta. Cikin daukin ganin juna suka rungume junansu suna dariya.

"Oyoyo Mama Amma" Anti Bebi ta fada lokacin da ta ke kokarin karban jakar hannun Amma.

Murmushin da ya kasa kaucewa daga fuskarta ta kara fadadawa tana fadin "Bebi na sameku lafiya?"

"Lafiya Alhamdulillah." Ta kalli trolley din Amman mai shake da akwatuna "Mama Amma wannan kayan naki da kin taho da Kanina ya tayaki dakonsu ai"

Suka fashe da dariya "Zan ce mishi kin canja mishi suna zuwa Dan Dako"

Direban Anti Bebin ne yayi sauri ya karaso ya tura trolley din Amman.

Hira sukeyi sosai a mota har isarsu gidan.

Su Baba Habu ne masu taya sauke kayan Mama Amman. Tana ta zolayarshi wai yaga amaryarsa yana so ya nuna bajintarsa (tunda jika yake a wajenta).

Shigowarta ke da wuya Fareeha da Anti Mami su ka shigo don suyi mata sannu da zuwa.

Anti Bebi ta gabatar dasu gareta.

"Mami kanwar Babansu Ashraf ce. Fareeha kuma 'yar kanwar sa ce"

Amma ta jinjina kai "Masha Allah. Sannunku ko 'yan albarka."

Wanka ta shiga yi, kafin ta fito kuwa an jera abinci a falon Anti. Komai yaji dai dai gwargwado. Bayan ta shirya tayi nafila ta zauna cin abincin. Wayarta ce a hannunta tana canja simcard dinta zuwa na Nigeria wanda ta siya a airport. Sim din na hawa ta saka kati.

Muazzam ta kira.

Kamar yana jiran kiran nata kuwa bugu biyu ya dauka.

"Hajiya Amma daga zuwa Nigeria sai kuma ki manta da ni?"

Tayi murmushi yayin da ta kai kofin kunun gyada bakinta. "Yanzu nake fada wa Bebi nace nasan abunda zaka fara fada kenan"

"You know me so well"

Ta jinina kai "Oh yes I do"

"Yaya hanya? Hope kun isa lafiya?"

"Lafiya Alhamdulillah. Ka dawo gida ne ko kana wajen aiki?"

Muazzam ya gyara kwanciyar shi akan doguwar kujeran falonsa."Gani a gida fa. Yaya Anti Bebin?"

"Tana nan lafiya. Ta hadani da lodin abinci. Idan na dawo bazaka ganeni ba saboda kibar da zan hada"

Yayi dariya. "Ni dai ba zan yi rakiya zuwa gym ba."

Suka cigaba da hirarsu gwanin sha'awa har ta kusa cinye abinci. Da taji alamar katinta ya kusa karewa ta mishi sallama ta kashe wayar.

Ta ji dadin abincin sosai. Ta jinjina wa Anti Bebi da kokarinta da kuma nuna kulawarta a gareta.

Anayin azahar da ta kwanta bacci bata farka ba sai biyar na yamma. Tafiya ce tayi mai tsawo ga gajiya sun hadu mata dole baccin yazo da nauyi.

Wanka ta sake yi sannan tayi sallar La'asar. Bata tashi a kan sallayar ta ba har akai kiran Maghreb. Bayan ta idar da sallah Anti ta shigo dakin.

"Sannu Mama am. Kin dauko gajiya"

Amma tayi murmushi "Ai ba'a magana. Yanzun ma naji kaman wani baccin ne yake kokarin zuwa saceni"

"To gaskiya yayi hakuri sai kin ci abinci"

Ta tashi ta nade hijabin da tayi sallar dashi. "Dagaske dai so kike na kamo ki Kiba ko?"

Anti tayi dariya "Da ke da Ummata ban san waye kibar nan tafi damunsa ba. Ni kuma sakayau nake jina"

Amma ta jinjina kai "Saheeh"

Sukayi dariya. "Ga abincin nan a parlor ko a shigo miki da shi ciki?"

"Ba matsala gani nan fitowa"

"Toh" ta tashi "Barin ce su Anisa suzo ku gaisa. Tun dazu suke ta sintiri a dakin nan wai suga ko kin tashi"

Dayake tasan ba lallai Amman ta so abinci mai nauyi ba da daddaren don haka samosa aka soya se akayi chicken cream soup. Anisa ce ta gasa garlic bread din.

Ita dai Fareeha a rayuwarta ranar ne ta fara ganin an saka madara a miya. Amma kuma daga baya data dandana sai taji yayi mata dadi.

Suna zaune a kitchen din suna hirarsu ita da Anisa da Anti Mami ne Anti Bebi ta shigo ta samesu.

"Sannunku da aiki"

"Yauwa sannu Mama" duka suka amsa.

"Kunci abincin dai ko?"

Suka amsa mata da 'eh'

"Anisa ki zo ku gaisa da Mama Amma. Ta tashi a bacci"

Da sauri Anisan ta sauko daga kan freezer inda ta ke zaune akai.

"Ina Fadila kuma?"

"Tana daki. Barin kirata" Anisa ta fada lokacinda ta fice daga kitchen

Anti Mami tayi ajiyar zuciya lokacinda aka bar musu kitchen din daga ita sai Fareeha.

Kamar daga sama sai suka ji ringing din waya daga kan cupboard. Fareeha tayi saurin mikewa don karar wayar Anti Mamin ne. Ita a tunaninta ma ko Ummanta ce, don sun kirata da rana basu sameta ba. Ganin bakuwar lamba sai ta mika wa Anti Mami wayar. Ta duba ita ma taga bata san lambar ba.

Da sallama a bakinta ta amsa wayar.

Shiru ne ya biyo baya kafin nan taji an kira sunanta da muryar da ko a mafarki taji ta san ta waye.

Kirjinta ne taji yana dukan uku-uku. Idanunta suka ciko da hawaye.

Ta kira wayarshi yafi a kirga tunda abun ya faru, amma be dauka ba. Daga karshe ma idan ta kira sai ta ji ta a kashe. Bappah Dattijo ma ba kokarin da bai yi ba don a samo shi suzo su zauna ayi magana amma abun ya ci tura. Daga baya ma ce wa akayi ya bar garin gaba daya. Waliyyinsa ma bai san inda ya shiga ba.

"Mukhtar?"

Fareeha ma da taji furucin Anti Mamin sai da gabanta ya fadi.

Dif! wayar ta dauke. Ta cire ta daga kunnenta ta duba. Ya katse kiran. Ta sake kira amma sai taji wayar a kashe.

Hawayen da ta ke ta rikewa taji sun zubo mata ga wani zafi da kirjinta yake yi a lokacin.

Dankwalinta ta jawo ta rufe fuskarta a lokacinda wani kuka mai karfi ya kwace mata. Ita kanta ba ta san dalilin kukan nata ba.

Bata ankara ba taji ta cikiin rikon Fareeha. Ta rike ta cikin lokaci mai tsawo yayinda ta ke ta kuka me daci. Tayi kukanta ma'ishi sannan ta tashi ta wanke fuskarta a sink din kitchen din.

Ba wanda yace dan uwansa komai haka suka fito a kitchen din suka koma dakinsu.

Kusa da Ahmadi wanda yake bacci ta kwanta. Ta kalli fuskar yaron wanda banbancinsa da babansa kadan ne. Nan take tsausayinsa ya kamata. Shin yana da rabon sanin babansa kuwa?

******

Fareeha na ta shirye-shiryen komawa Azare. Da alamu kamar ta kosa ta koma. Dama ita tana da wahalar sabo. Kuma in ta saba na dan wani lokaci ne.

Dama abunda ya sa ta dade don taji Umma tace su Inayaah zasu zo ne. To daga baya Abba se yace su zauna kawai kar su cikawa Bappan gidan shi.

Da tace zata tafi Anti Mami tayi ta rokonta akan ta kara sati. Da kyar ta shawo kanta ta samu ta kara wasu kwanaki.

Tana kwance a daki itada Ahmadi suna ta gwalatunsu sai ga Amina mai aiki ta yi sallama ta shigo.

"Anti Fareeha kizo inji Baba" kawai tace ta juya.

Anti Mami da ke bakin wardrobe tana jera kaya tayi dariya tace "Oh su Adda tafiya ta kankama fa tunda Bappah yayi kira"

Tayi murmushi ta yafa dan karamin mayafi tana fadin "Ni dai yanzu ko me zakice bazan zauna ba wallahi"

"Ai naga alama kin kosa. Ko dai akwai wani da yake jiran ki ne a Azaren?"

Ta zaro ido hade da dafe kirjinta "Iyeh??? Rufamin asiri Anti Mami kar Bappah yaji labari. Nashi ga uku ni Hauwa'u"

Anti Mami dariya har da kwanciya a kasa. Haka ta fice ta barta tana ta kyakyatawa.

Da yake yau weekend ne kaf wunin a gida Bappahn yayi.

A falo ta sameshi yana shan tea ga kuma AC yana dan buso shi. Labarai ake watsowa a tashar Aljazeera wanda da alama hankalinsa ba wajen yake ba don idonsa na kan computer din da ke cinyarsa yana daddanawa da hannu daya, hannun dayan kuma na rike da kofin shayinsa.

Tayi sallama ta shiga ya amsa. Wuri ta samu a bakin carpet ta zauna.

"Dawo nan" yayi mata nuni da kujerar da ke fuskantar shi. Ba musu ta koma wajen.

"Jiya munyi waya da Babanki"

Ba wani dalili haka kawai taji gabanta ya fadi.

"Munyi magana da shi mai tsawo akan inaso ki dawo garin nan da karatu. Akwai wata makarantar kwana ta 'yan mata wacce ta shahara a karatun boko dana addini, kuma Ina sha'awar Anisa ta koma nan itama shi ne nayi tunanin na hadaku ku biyu tunda Fadila ta riga tayi nisa a nata karatun."

Dum dum dum, haka zuciyar ta take ta bugawa.

"To amma ya nuna min yafi son karatunki a can kina kusa da gida. Nayi iya kokarina don na shawo kanshi amma bai yarje min ba."

Ta gyara zama domin sai taji gumi yana tsatsaffo mata.

"Ina so na ji ta bakinki ne in dai har ke kina son ki zo nan din kiyi karatu, to watakil in yaji daga bakinki ya bawa maganar muhummanci. Yanzu yanaga kamar inaso in cusa miki abin dan dole ne. All I'm asking is, are you interested?"

Kallon yatsunta take wanda ke nade akan cinyar ta.

Bata tunanin zata iya barin gida na tsawon lokaci. Hutun nan ma data zo yaya aka kare?

Duk wani irin kulawa da jajircewa Bappah Dattijo ya nuna mata ita ta kannenta. Dawainiyar da ya ke da su kadai ya isa ace ta amince da duk wani abun da ya zo mata da shi. Dangin babanta ma wanda al'amuransu ya rataya a wuyansu basa kula dasu kamar yanda yake kula dasu.

Amma in ta tuna Ummanta, sai taji kamar baza ta iya ba. Wa ze na tayata aiki to?

"Karki damu. Ita ma Umman naki zata so ace kin samu ilimi me inganci a wannan bigire na rayuwarki"

Sai a lokacin ta fahimci cewa maganar da ta keyi a zuci ta fito fili.

Ta rankwafar da kai. "To Bappah a ban dama mu tattauna da su idan naje gida"

Ya jinjina kai. "Ba matsala. Ko me kuka yanke zan kira naji. Gobe inshaAllah zamuje kiga Yayan ki sai su Anisa su rakaki gida ko?"

Duk sai ta rikice ma. Bilal din zasu je gani? Su Anisan har Azare zasu rakata? Ta rasa wace tambaya daya zata mishi. Kawai sai tace "Toh Allah ya kaimu. Nagode Bappah"

Tana zuwa daki kuwa ta bawa Anti Mami labarin yanda sukayi da Bappan.

Anti Mami tace "Ni dai zan baki shawara in dai Abba ya tambayeki raayinki kice kina so. Kar ki bari wannan opportunity ya kubuce miki. Ita ma Umman da za ki tanbayeta zata so ace kin sami ilmi mai inganci"

"Bappan ma haka yace"

"Ke da kawai kiyi ta Addu'a. Allah ya zaba miki mafi alkhairi"

"Amin Anti Mami. Nagode".

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top