7.
Azare, Nigeria
Yau kwana hudu kenan da tafiyar Bilal Kano shi da Bappah Dattijo. Umma duk sai taji gidan ya mata shiru tunda ba wanda zatayi wa fada ko ta tada hankalinta akanshi. Musamman ma yau da su Fareeha suka tafi islamiyya ga Abba tun bayan asuba daya koma bacci bai tashi ba.
Sai ta samu kanta da yin aikace-aikacen da ba kasafai takeyi ba don kawai ta samu abunyi saboda in ta zauna hakan tunani zata shiga yi. Abun da kuma bata son yi kenan.
Ta gama 'yan abubuwan da zatayi sannan ta daura abincin rana. Daya ke masu zuwa gaishe da Abban sun dan dauke kafa sai tayi abincin dan daidai. Zuwa sha biyu yaran zasu dawo a Islamiyya bataso su dawo ba abinci.
"Lami" Abba ya kirata daga falon shi.
Ba laifi kwana biyu jikin yayi sauki don haka yanzu sai aka tattare shimfidin kwanciyar tasa aka mayar daki sannan aka sake gyara falon. Yanzu ya kan zauna akan kujerarsa wasu lokutan kuma ya kishingida a kasa.
Alhamdulillah har ya kan taba hira da abokansa masu zuwa dubiya. Da daddare kuma zai saurari radio ko kuma ya ce su Inaayah su zo su taya shi hira.
Ta shigo da sallama ta samu waje ta zauna a gefensa.
"Ga ni Abba"
A hankali ya jawo hannunta na dama ya damke a hannunsa na hagu. Wani dumi ya lullube zuciyarta.
"Na gode" ya furta idon sa na cikin nata idon.
Ba sai yayi wani dogon bayani ba, tasan me ya ke nufi.
Yawu ne ya kafe a bakin ta ta rasa me zata ce. Kai kawai ta gyada sannan ta sunkuyar da kanta.
Da taga bashi da niyyar sakin hannun nata sai ta zame a hankali.
"Na bar abinci akan wuta" abinda ta ce da taga ya mata kallon tuhuma.
Bai ce komai ba ta tashi ta koma kitchen din.
Duk sai taji jikinta ya mata lakwas. Ta samu ta karasa abincin.
Azahar ta gabato dan haka ta shiga bandakinsa ta hada mishi ruwan alwala.
"Zo ki kamani" ya fada mata yana mika hannunsa a lokacin da ta ce ya tashi yayi alwala.
Murmushi dauke a fuskarta tace "Haba Abba, yaushe rabon da a maka jagoranci? Ina ce jikin da sauki yanzu?"
Ya kafeta da ido "To laifi ne Dan nace kizo ki dagani?"
"A'a ni bance ba"
Ba musu ta karasa wajensa ta riko hannun nasa. Har wani jingina yayi a jikinta wai shi a dole baya jin dadin jikin nasa. Dariya ta ke son yi amma ta gintse. Har kofar bandakin ta rakashi sannan ta dawo.
Fareeha tayi sallama suka shigo.
"Umma sannu da aiki"
"Sannu Adda am. Ya makaranta?"
Fareeha ta cire hijabinta ta lankaya a wuyanta "Alhamdulillah"
A daidai lokacin Qulsoom da Inaayah suka shigo da gudu.
"Ku kuma babu sallama?" Addan tasu ta watsa musu wani kallo.
Inaayah bata tsaya jin ta ba ma ta kara shigewa ciki da gudu. Qulsoom tayi sallama sannan ta wuce ciki.
"Kuje kuyi sallah kuzo kuci abinci" inji Umma.
Fareeha ta gyada kai ta bi bayan kannenta. Wanka duka sukayi dayake basu samu sunyi da safe ba sun makara. Fareeha ta jika uniform uniform nasu sannan suka zo sukaci abinci domin sai da sukayi sallah a islamiyyar kafin suka dawo gida.
Tana wanki ne ta ji sallamar kawarta Hafsatu. Dama tace mata zasuzo da mamanta duba Abban nasu don tun da aka sallamoshi sau daya tazo kuma ita kadai ne.
Ta dauraye hannunta ta tarbo su zuwa falonsu. Cikin ladabi ta gaida Maman Hafsatun sannan ta shiga kitchen Dan kawo mata ruwa. Ta saka pure water guda uku a faranti da kofuna guda biyu sai ta Fanta guda daya wacce daga cikib kayan dubiya aka kawo musu kuma ita kadai ta rage.
Tana ajiyewa a gabansu ta shiga falon Abba domin ta sanarwa Umma zuwan bakin nasu. Ta same ta suna zaune da Abba a kan kafet suna cin abinci. Abun duk sai yayi mata wani iri don ta dade bata ga hakan daga garesu ba.
Suka amsa sallamarta yayinda Umma ta kara da cewa "Naga kin wuce da baki. Su waye?"
"Hafsa ne da Mamanta sun zo gaida Abba"
Umma tayi murmushi tana kokarin tashi. "Ayyah Allah sarki. Barin zo mu gaisa"
Abba yayi saurin dakatar da ita. "Zauna mu karasa." Ga Fareeha kuma sai yace "Kice musu tana zuwa su dan yi hakuri"
Kai kawai ta gyada masa ta juya ta koma falon nasu.
Hira sukeyi jifa-jifa suna saka Maman Hafsatu a ciki duk da dai hirar bata wuce ta makaranta ba. Umma tayi sallama ta shigo.
Suka gaisa, Maman Hafsatu ta tambayeta me jiki. Ta amsa da sauki sannan ta rakata falon Abban shi ma ta gaishe shi. Su dan yi hira anan ma sannan ta ce zasu tafi. Ta ajiyewa Umma dubu uku a kan kujera akan a saya Abba fruits. Umma ta mata godiya.
Har bakin titi Fareeha ta rakasu. Sai da suka sami abun hawa sannan ta juyo ta dawo.
Kamar daga sama taga mutum a gabanta. Warin taba ya daki hancinta nan da nan taji hankalinta ya tashi.
"Ya ne?"
Ta daga ido ta kalli me maganar. Tabbas tana ganin fuskarshi jifa-jifa amma ko sunansa bata sani ba.
"Malam lafiya?"
"Ina kuwa lafiya baby. Dama wallahi yayanki ne ya min iyaka" ya taho kaman zai hada jikinsa da nata tayi saurin ja da baya. "Amma na samu labari ya fece shi ne nace to ya? Zan samu shiga ne a wajenki? Ko kuwa?"
Addu'o'i kawai take ta kwararowa a zuciyarta yayinda ta kare Kankame hijabinta.
"Kayi hakuri. Ana jira na a gida" da kyar ta furta wadannan kalmomin.
Zai sake magana sai ga wani yazo ya talle keyarsa ta baya. "Kai Dan iska. Ana ta nemanka a shago ashe nan kayo."
Shi ma dai mai talle keyar duk kalarsu daya.
Ya ja hannunsa. "Wuce muje dallah mu nemo kudi me za'ayi da wata mace"
Ai suna wucewa da ta falfala a guje ba ita ta tsaya ba sai a tsakar gidan su.
Umma ta leko daga kitchen. "Lafiya Adda? Yau kece da gudu?"
Tana haki ta karasa bakin famfo. Ta wanke fuskarta sannan ta sha ruwa.
"Me ya faru?"
Ta girgiza kai. "Kare ne ya biyoni"
Umma ta lura dai kaman ba gaskiya ta fada mata ba amma se ta kyaleta.
"Umma wa ya karasa wankin?"
Sai a lokacin ma ta lura da uniform dinsu da aka shanya akan igiya suna ta digar da ruwa a simintin tsakar gidan.
"Ni ce. Kije ki huta an jima zan aikeku kasuwar kaji ku dubo min Innayo."
"Sannu nagode."
Da sukayi la'asar Umma ta hadasu da kudin Napep da kuma yajin tafarnuwa da na daddawa su kaiwa yayarta Innayo.
Duk da su uku suke tafiya amma Fareeha sai raba idanu take ko zata ga mutnanen dazu. Sai da suka shiga Napep sannan ta saki ajiyar zuciya.
Ranar litinin da safe Umma na zaune a tsakar gida suna waya da Anti Mami yayinda take tsince waken abincin rana, taji an yi sallama a kofar gida. Ta zaro hijabinta ta saka da zummar taje taga waye sai gashi ma ya shigo ciki. Baba Zubairu ne.
Suka gaisa sannan ta karasa da shi wajen Abban. Ta karanci kamar akwai damuwa a tattare dashi amma ba ta ce komai ba ta koma kitchen ta hado mishi kayan tea da sauran masan da aka soya da safe.
Har ta kawo ta ajiye a gaban shi bai ce komai na in banda gaisuwar da sukayi dazu.
Ta duba dakin Abban taga ko ya tashi sai ta samu ya shiga bandaki.
Ta fito tayi wa Baba Zubairu bayani amma sai taga kamar hankalinshi baya wajen.
"Baba Zubairu lafiya dai ko?"
Sai a lokacin ya dago ya kalleta. Ta hango wani abu a idonsa amma ta kasa gane ko menene.
"Na samu mummunan labari jiya da dare. Abokiyar zaman ki zaa kaita asibiti Kano neman magani hatsari ya ritsa da su motar ta kama da wuta"
Kafafunta suka gagara riketa sai ji tayi ta zame ta zauna.
"Allah ya mata rasuwa"
Innalillahi wa inna ilaihi raajiun.
Hawaye taji suna bin fuskarta wanda bata san dalilin zubar su ba.
A haka Abban ya fito ya samesu.
Shima da aka bashi labarin abunda ya faru sai jikinshi ya mutu.
Tabbas ya tambayi Mariya a lokacin da ya fara samun sauki kuma Umman ta sanar da shi cewa bata jin dadi. Toh Allah da ikon sa kuma tun lokacin basu sake zancen nata ba.
Yanzu kuma da labarin rasuwarta ya riskeshi sai ya rasa me yakeji game da hakan. Shekara shida suka yi da Mariya a matsayin matarsa amma a yanzu ya rasa takamemen abun da zai tuna ta da shi wanda ta mishi ma kyautatawa ko kuma sanya shi farin ciki.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mata Addu'a a ranshi. Allah ya gafarta mata kuma Allah ya yafe mata kura-kurenta.
Haka suka yi jugum-jugum a falon kowa da abunda ya ke sakawa a zuciyarsa.
Ita Umma tausayin yaran Mama Mariyan ne ya kamata. Dama can ubansu ya rasu sun taso basu sanshi ba. Akazo Abba ya aureta ya maye musu gurbinsa. Toh gashi yanzu itama Maman nasu ta tafi ta barsu. Wayyo Allah duniya!
Daga karshe dai suka yanke shawarar zuwa Bulkachuwa taaziyyah bayan sallar Azahar. Kafin nan yaran sun dawo a makaranta sai tace suje gidan Maman Walid su zauna kafin su dawo.
Wunin ranar dai haka sukayi shi ba wani kumari.
****
Fareeha ce ta fara yin hutun makaranta domin sun zana Jarabawar JSCE. Don haka Umma tace taje Kano ta gano mata Anti Mami. Su Qulsoom da Inayah hadda kukansu lokacin da zata tafi. Umma tace su ma idan sunyi hutu zasu je in ya so sai su dawo tare.
Baffa Dattijo ne ya turo direba tareda dan sa Abubakar wanda suke cewa Baba Habu sukazo daukanta.
Umma ta cikata da guzuri ta kaiwa matar gidan. Su tsintsiyar laushi da garin kunu da su daddawa da kuka da garin danwake da garin tamba. Haka aka cika boot din motar makil da Bonita na garin. Sannan ta yi masar gero ita ma a kaiwa Bappan dan ta san yana so.
Karfe sha daya na rana a Kano ta musu.
Gidan Bappan da ke Sharada suka wuce kai tsaye. Dama dai ita Fareeha sau biyu ta taba zuwa tunda take. Zuwanta na farko tana yarinya sunzo duba kakarta a asibiti lokacin an kwantar da ita a Aminu Kano. Zuwan ta na biyu kuma bikin 'yar kawar Umma shima an kusa shekara uku yanzu. Don haka sai taga gidan ya kara canza mata.
Tun da can daman anyi gidan ne na karamin iyali wato daki uku da falo daya da kuma gareji. To da yaran suka fara girma sai aka gyara garejin aka maida shi dakin mai gidan sai ya bar musu sauran dakuna ukun. A haka a haka har akazo aka gina boy's quarters a baya yara mazan suka koma can. Sai aka sake wani gyaran a cikin gidan aka kara wani falon ta wajen dakin Anti Bebi wato matar gidan. Yanzu haka dakuna hudu ne a cikin gidan da falo biyu. Sannan kuma anyi wani kicin ta waje da wajen yin wanke-wanke.
Dayake duk 'yan matan gidan suna makaranta Anti Mami da Anti Bebi suka samu a gidan sai mai aikinsu. Cikin fara'a da murna Anti Bebi ta tarbeta. Dama ba laifi tana da fara'a da kyautatawa jama'a. Matsalarta daya bata cika shiga cikin mutane ba. Ko taro ake a dangi idan taje bata dadewa take dawowa gida. Wannan yasa dangin mijin ta suke ganin kaman tana da girman kai.
Asalin sunan ta Aishatu kuma 'yar Misau ce. Sun hadu da Bappah a bikin kawarta shima kuma angon abokinsa ne. Soyayya mai karfi ta kullu a tsakaninsu kuma babu wani bata lokaci akayi aurensu. A gidan sa ta karasa karatunta na secondary tayi degree har ma tayi masters. Suna zaune cikin kwanciyar hankali da kyautatawa juna. 'Yaya biyar ne a tsakaninsu. Maza biyu; Muhammad Ashraf da Abubakar da kuma mata uku; Samha, Fadila da Anisa. Ashraf yana kokarin kammala degree dinsa na biyu a kasar Jamus sai Samha da ke binsa ita kuma tana karanta Law a Jami'ar Bayero. Abubakar na aji daya a FUD da ke dutse yana karanta Microbiology. Fadila da Anisa sune kusan sa'annin Fareeha don sune suke secondary.
Anti Mami kasa rufe bakin ta tayi tsabar murnar ganin Fareeha. Duk da irin mutuntawa dake tsakaninta da 'yayan yayan nata amma ta kasa sakewa tsawon lokacin nan. Yanzu kuwa da taga fuskar da ta sani duk sai dadi ya mamayeta.
Dakin da aka sauketa wanda shine dakin Samha anan ta yi wa Fareehan masauki.
Fareeha sai taga Antin nata kamar ta dan kara haske tayi fes. Sai dai har yanzu kana hango damuwa a tattare da ita. Tana rike da Ahmadi a hannunta wanda ya ke ta shan baccinsa. Shima sai taga ya kara girma sosai Tubarkallah Masha Allah.
Sun kira Umma domin su sanar da ita isowar Fareehan lafiya. Ta gaisa da Abban su da kuma kannenta sannan sukayi sallama.
Amina mai aiki ce tayi sallama ta shigo dakin.
"Anti tace wai kiyi sallah sai kizo ga abinci a falo an kawo"
Fareeha ta gyada kai "Toh nagode". Ta mika wa Anti Mami Ahmadi sannan ta tashi ta shiga bandaki ta dauro alwala.
Shinkafa da miya ne akayi sai salad wanda yaji kayan lambu. A gefe kuma an yanka kankana da abarba sai jug me dauke da zobo me sanyi.
A plate daya suka zuba ita da Anti Mami suna ci suna hira har su Fadila suka dawo a makaranta. Suma sun ji dadin ganin Fareeha don sun jima ba su hadu ba. Dama sallah ne yawanci ya ke kaisu Azaren inda suke haduwa, to kwana biyu basu je ba a Kano suke yi don yawanci dangin maman nasu a kano suke kuma sunfi sabawa dasu. Shi Bappah be damu ba kowacce sallah se yaje ko da su ko ba su. Amma su dai kam zumuncin sai a waya.
Da yamma bayan ya dawo a wajen aiki ya kirata falon shi suka gaisa.
"Yaya jikin Abban naku?"
Kan ta kasa ta amsa "Da sauki Alhamdulillah."
"Ba dai wata matsala ko?"
Ta girgiza kai alamar babu.
"To Alhamdulillah. Naga mamanki ta hado ki da tsaraba kala-kala. Zan kirata na mata godiya inshaAllah. Yaushe jarabawarku zata fito?"
"Inaga sai mun koma"
"To Allah ya tabbatar da alheri. Ina so ki saki jikinki anan kin ji. Nasan kun dade baku hadu da 'yan uwanki ba kar hakan yasa ki ja baya dasu. Nan ma gidan ku ne kinji ko?"
"To Bappah. Nagode"
"Bakomai. Ki cewa Mama nace a kawo min shayi"
Ta amsa da to sannan ta fita zuwa falon Maman.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top