6.
Disclaimer: Please read previous chapter again to avoid confusion. Me sef I had to read it again 😅
6.
Muazzam bai yi shirin dawowa gida ba sai bayan la'asar. Hakan ma Mujahid yana ta mishi mita wai daga zuwa zai tafi. Ya dai bashi hakuri yace yana da wasu uzurirrika ne. Shi da Aisha suka mishi rakiya har kofar gida tare da sake tuna mishi zasu kawo masa Hidaya.
Da murmushi a bakinshi ya fita a gidan.
Sai da ya tsaya yayi sallah sannan ya wuce Subway Station.
Yana zaune yana dan danne danne a wayarsa ne yaga email ya shigo mishi. Ya lura kuma cewa ba daga wajen aiki bane. Don haka ya yanke shawarar sai ya koma gida zai karanta.
Saukarsu da wuya, ya yi tattaki zuwa wani bakery wanda ya shahara wajen yin samfurin biredi iri daban wanda suka samo asali daga kasashe daban-daban na duniya. Layi ne a gaban wajen da ake yin oda, don haka shi ma ya bi layin har yazo kanshi. Croissants da Baguette ya ce ya ke so. Aka fada mishi kudin su ya mika katinsa. Bayan an cire kudin aka bashi rasiti ya karasa gurin wanda zai bashi odarsa ya mika masa rasitin. Bayan mutumin da ke bayan kanta ya karanta abunda ke jikin rasitin sai ya dauko masa duk abubuwan da ya bukata ya saka masa a brown paper bag ya mika masa. Da murmushi dauke a fuskarsa ya ce ya gode sannan ya fita.
Bata tsammace shi a wannan yammacin ba don haka da ta bude kofar ta ganshi tsaye sai da ta dan kankance idon ta alamar tambaya.
"Are you okay?" Ta tambayeshi.
Bai bata amsa ba ya jawo ta barin jikinshi suka qarasa cikin falon nata. Kwamfyutarta ya gani a ajiye akan kujera ga kuma wasu takaddu ta bazasu a kan kafet. Da alama tana aiki ya katse ta.
"Na je Long Island ne, shi ne nace bari na tsaya mu gaisa kafin na karasa gida" ya bata amsa yayinda ya wuce zuwa kitchen din ta. Plate ya samo ya zuba Croissants din a ciki sannan ya dauko fresh milk cikin fridge ya zuba a kofi ya fito.
Ta maida kwamfyutar kan cinyoyinta tana nazarin abun da ke kai. "Yaya su ke?"
"Lafiya kalau. Su na gaishe ki"
Ta ji dadin cewa yanzu har yana fita ziyara wajen abokai amma bata nuna masa hakan ba.
Shiru ya biyo baya, shi yana cin abincin sa ita kuma tana aikinta. Bayan wani dan lokaci ta kammala sannan ta kashe kwamfyutar ta ajiye ta gefe. Ta zare gilashin idonta ta dan mutsutsuka su sannan ta dube shi.
"Ina da tafiya zuwa Najeriya"
Ya dago ya kalleta, amma bai ce komai ba. Yana jira ta mishi karin bayani.
"Jikin Mama Amina ne yayi tsanani. Ina so naje na dubo ta."
Ya sunkuyar da kai.
Mama Amina ita ce mariqiyar Ammansa tun lokacin da mahaifiyar ra ta rasu. Idan bai manta ba ma kamar ita ce ta yaye shi. A iya saninsa, ba shi da wata Kaka ta wajen uwa kamar Mama Aminan.
"Allah sarki. Allah ubangiji ya tashi kafadunta."
"Ameen"
"Yaushe ne tafiyar?"
Ta nisa tare da nutsewa cikin kujerar tata mai taushi. "Next month. Ina tunani ko zaka rakani?"
Ya hadiye wani abu mai daci. Baya tunanin zai iya haduwa da kowa a yanayin da ya ke ciki. Tabbas idan suka gamu da 'yan uwansa- wanda dole hakan sai ya faru, yayi amanna sai sun mishi ta'aziyya duk da kuwa an shafe kusan wata shida da rasuwar. Shi kuma a halin yanzu ba abin da baya son ji a rayuwar sa kamar a tuna masa da cewa Najma ta rasu.
Bai san meyasa ya ke jin hakan ba. Amma therapist din sa ta ce saboda ba a taba masa mutuwa da ta jijjigashi kamar wannan bane. Domin lokacin da Babansa ma ya rasu shekararsa shida a duniya. Bazai iya tuna zafin mutuwar koma yayi kuka. Amma wasu lokutan yakan farka cikin dare yaji ba Wanda yake son gani a duniyan nan kaman Najma. Idan ya tuno bata nan kuwa haka zaiji numfashinsa ya sarke ga wata wuta da take ruruwa a kirjinshi.
Imam Hamid, limamin masallacinsu yace masa yayi tawakkali. Amma meye tawakkalin? Shi a ganinshi zaman daya ke a duniyan nan ma tawakalli ne. To kiris ya rage ya kashe kansa. Amma dai Alhamdulillah hakan bai faruba.
"Amma I'm sorry" ya furta a hankali. "In kinje zamu yi waya da Mama Aminan. Amma bazan iya zuwa ba"
Bata yi mamakin hakan daga gare shi ba. Don haka ta gyada kai sannan ta miqe. "Are you staying for dinner? Dashishi zanyi da taushe"
Ya gyada mata kai.
"Good" kawai tace sannan ta wuce kitchen din.
Ya dan zauna shiru na wasu lokuta yana sake-sake kafin nan ya tashi ya bi bayanta. Ya karasa wajen sink din ya karbi Colander din hannunta wanda ke kunshe da allayaho a ciki ya fara wankewa. Murmushi tayi kawai ta koma ta dauko yankakkiyar kabewar ta da ke cikin ziploc ta fara shirin sarrafata.
A nutse suke ayyukan nasu kafin nan daga baya Amman ta fara jan shi da hira har ya warware.
Nan da nan suka gama abincin. A nan kicin din suka zauna suka ci a kwano daya.
Shi ya musu jam'i suka gabatar da sallar maghriba sannan ya Mata sallama akan zai wuce bayan ta hada shi da shirgin stew da kuma frozen Samosas.
"Mu'azzam" ta kira sunanshi a hankali.
Ya dago ya kalleta.
"Ina so ka daure ka yi hakuri kuma ka kara tawakkali akan wanda kake yanzun. Allah ya san da kai Mu'azzam. Ka cire damuwan nan a ranka. Yaya kake tunanin nake ji a matsayina na mahaifiyarka idan na ganka a wannann yanayin? Nima damuwa nake kara shiga"
Cikin ruwan sanyi ya jawo hannunta ya dunkule a cikin nashi. "Wallahil azeem Amma ba abunda nake gudu a duniyan nan kamar na saki a cikin damuwa ko na bata miki rai"
"Nasan da haka. Kuma ina alfahari da kai akan hakan. Amma hankalina ya kasa kwanciya. I know you've come a long way fighting this grief, amma ina so ka kara kokari. Yanzu tunanina yanda zan tafi na barka a halin da kake ciki. Ga tafiya ta kama ni dole"
"Amma relax. I'm going to be fine InshaAllah"
"Ni dai idan ban ga wani muhimmin change ba a tatttare da kai to gaskiya ticket biyu zan siya. Kafata kafarka. Tun wuri ma ka fara shirin daukar hutu a wajen aiki"
Murmushi ya kubce mishi. "Amma ban Dade da komawa aikin ba dai. Bai dace kuma na sake daukan wani hutu ba in the same year"
Ta galla masa harara. "Oho dai. Think about what I said. Na gaji da wannan tashin hakalin"
"Wayyo Ammata kiyi hakuri to" ya fada yana dariya tare da rungume ta.
Ta dan bugi kafadarsa. "Na ki na yi hakurin"
Da kyar dai ya samu ta sassauto akan tafiya Najeriya tare da shi din.
Har bakin kofa ta rakashi tana kallo har sai da ya sha kwana sannan ta jawo kofar ta ta dawo ciki.
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke kafin tayi addu'a ga Rabbil izzati da ya yaye wa dan nata duk wata damuwa ya kuma kawo mishi sauki a duk lamuran sa da ya sa a gaba.
Har ga Allah da tana da yadda zata yi da ta cire duk wata damuwa a zuciyar Mu'azzam ta kwashe ta ta dawo da ita kanta. Amma bata da wannann halin. Iyaka kawai ta mishi addu'a kuma ta tallafa mishi ta kuma kara jawo shi jikinta.
****
Azare, Nigeria
Tana kwance a gefen katifar ta sa. Sallar Asuba ta idar ko Azkar dinta bata gama ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Sama-sama taji ana kiran sunan ta kafin nan ta bude ido.
Yanzun ma shi ya ke kiran na ta. "Lami" ya sake fada a hankali har yana jan hijabin jikinta.
Tsam! ta tashi tana ganin ikon Allah.
Suka hada ido ta ji wani abu ya makale mata a makoshi.
"Na gaji" ya fada a hankali. ".....da kwanciya"
Kallonshi kawai takeyi ta kasa gane mafarki ne ko gaske.
"Ki taimaka min" ya furzar da iska a hankali. "........in tashi zaune"
Wasu hawaye da bata san daga inda suka zo ba kawai taji suna zubo mata. Ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciya. Kukan nata ne ya jawo hankalin Fareeha da ke kicin tana kokarin dafa musu ruwan wanka.
"Umma?" ta kira ta cikin damuwa lokacin da ta shigo falon da sauri.
Umma kam ta rufe fuska da hijabi sai kuka take. Ita bata taimaka mishi ya tashin ba, kuma bata ce komai ba.
"Adda"
Ai itama sai da zuciyar ta ta kada data ji ya furta sunan nata. Mamaki ya bayyana karara a fuskar ta.
"Na'am?"
Ya yafito ta da hannunsa akan ta matso.
Kafafunta ta ji sun mata nauyi. Kafin ta karasa gare sa Umma tayi yunkuri ta tallafo sa ta tada shi zaune. Duk a lokacin bata daina kukan ba. Filon da ya ke kwance a kai ta saka mishi a bayanshi sannan ta mike ta fice a falon.
"Zo" ya sake yafito ta da hannunsa. Sai a lokacin ta lura da yanda karan hannun nasa ya rama ga dogayen yatsun sa sun sake zama sirara. Hawaye suka ciko a idon ta.
"Gani Abba" ta samu ta furta da kyar bayan ta tsuguna a gabansa.
Ya nuna kafafunsa. "Matsa min"
Hannayenta na rawa ta kai ga kafafun nasa da basu da maraba da kasusuwa. Ashe haka Abban ya rame?
"Ciwo .......suke min"
"Sannu Abba" abun da ta tsinci kan ta da fada kenan. Ya gyada mata kai inda ita kuma ta shiga aikin yi masa tausa.
Gaba daya jikin ta yayi sanyi. Sai take ji ma kamar baza ta iya zuwa makaranta ba yau.
Umma kam dakin ta ta shiga ta zauna dabas a kan Kafet. Hawaye babu kakkautawa ga wani malolo a makogwaro ta kasa hadiye shi ta gagara amayo shi.
Yau ina zata saka ranta? Wannan abun da takeji farin ciki ne ko meye? Meyasa ta kasa daina zubda hawaye?
Ya Rabbi Ya Rabbi.
Da kyar da rarrafe, fuska duk hawaye ta fito a dakin. Ta daddafa ta karasa bakin famfo tayi alwala sannan ta dawo ta tada kabbara. Ita kanta bata san raka'a nawa tayi ba, ta dai tsinci kanta a sujjadar karshe ta mai fashewa da kuka kuma tana yi wa Allah kirari da yabo.
A hankali ta shigo falon, wannann karon fuskar ta fayau babu tsoro ko firgici. Hasali ma, wani dan guntun murmushi ne a makale a labbanta lokacin da ta samu Fareeha tana bashi ruwa a baki.
"Adda yau ba makaranta ne?" Ta tambaye ta bayan ta samu waje ta zaune a kusa da Abban nasu.
Fareeha ta ajiye kofin sannan ta daga ido ta kalli Umman nata. "Umma wani iri nake ji". Ta fada a sanyaye yayin da ruwa ya taru a kurmin idon ta. Umma ta gyada mata kai alamar ta fahimci yanayin da ta shiga. Ta sunkuyar da kai gudun kar hawayen su zubo kuma Umman ta gani "Bari dai na tashi su Inaayah suyi wanka su shirya" ta fada da sauri tare da zummar mikewa.
Umma ta tari numfashin ta "Ki barsu kawai. Duk ku huta yau tunda gobe Asabar"
Gyada kai kawai tayi ta fita a falon. A tsakar gidan ta sulale ta zauna tare da kifa kanta a kan cinyoyinta. Baka jiyo sautin kukan nata amma hawayen da ke zuba daya na bin daya zai bawa mutum mamaki. Ita kanta Fareehar ta manta yaushe rabon da tayi irin wannan kukan.
Yau Abban ta ne ya kira sunanta? Ya ce ta masa tausa? Har ma ya sha ruwa daga hannunta.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Uangijin talikai, Mai kowa Mai komai.
Sai da ta sha kukan ta ya ishe ta sannan ta bude famfo ta wanke fuskarta ta koma dakin su ta kwanta luf kusa da kannen ta. Amma sai dai har wajen bakwai da rabi idon ta biyu in banda juyi da sake-sake ba abunda takeyi.
Umma kam gari yana dan wayewa ta kira Baba Zubairu ta sanar dashi halin da ake ciki. Ya ce Mata ta tsammaci zuwansa a ranar.
Misalin takwas da rabi, su Inayaah da Qulsoom suka shigo gaida Umma.
"Adda tace baza mu je makaranta ba yau. Me ya faru?" Qulsoom ta tambaya.
Umma tayi murmushi "Nace kawai ku zauna a gida ku huta."
Inayaah tayi wani ihun jin dadi har sai da Abbansu ya farka. Umma ta doka mata tsawa a lokacinda Abban ya sauke idanunsa a kan Qulsoom.
"Ummu" ya kira ta a hankali.
Ita ma dai sai da jikinta yayi sanyi don bata tsammaci hakan ba. Ta dan kikkifta idanunta tana tunanin anya shi ne ya kira sunanta ko dai kawai kunnennta ne ya jiyo mata haka?
"Ummu"
"Abba? Abba ka warke ne?"
Hankulan Inayaah da Umma suka koma kansu.
Murmushi ya kakalo tare da gyada kai.
Umma ta taimaka mishi ya zauna sannan ta saka mishi pillow a bayanshi ya jingina.
"Akwai abun da kakeso?"
"Kunu" ya furta a hankali.
Ta janyo flask din da ke gefen katifar tasa ta zuba mishi lafiyayyen kunun tsamiya a kofi. Ta koma kusa dashi ta fara bashi yana sha a hankali.
"Ku je ku tashi Adda azo a san a bun da za'a daura"
Jikinsu duk a sanyaye suka koma daki inda Fareeha take kwance. Bata ma san lokacinda baccin ya kwashe ta ba.
"Adda ki tashi Abba fa ya warke" Inaayah ta fada tana jijjiga ta.
Ta dan bude idon ta ta kallesu.
"Har ya kira sunana" Inji Qulsoom.
Fareeha ta lumshe idon ta ta sake bude su. Ashe dai dazun ba mafarki bane tayi. Wani abu taji cikin zuciyar ta. Shi ba farin ciki ba kuma shi ba bakin ciki ba.
Isti'aza tayi sannan ta tashi.
"Umma tace me za mu ci?"
"Bari na je na gani ko akwai sauran flour sai na mana danwake"
Hijabi ta saka ta zo wajen famfo ta wanke fuskar ta kafin nan ta duba kitchen din. Flour bata da yawa amma zata ishe su. Cikin lokaci kalilan ta kwaba ta jefa danwaken. Umma ta bawa su Qulsoom naira dari biyu suka siyo lettuce da tumatur a bakin titi.
Umma ce da kanta ta wanke lettuce din ta yanka kanana. Inayah aka bari da hada yaji tana daka shi a turmin karfe. Suna ta hirar su sai ga Bilal yayi sallama ya shigo.
Tun da Asuba da taji fitar shi sai yanzu ya dawo gidan.
"Umman ina kwana?" Ya gaisheta yayin da ta zauna a dan dandamalin bakin famfo.
"Lafiya Alhamdulillah. Ya na ganka sai yanzu?"
Su Fareeha basu barshi ya amsa tambayar tata ba suka fara jefo mishi gaisuwa. Ya lura yau din suna cikin fara'a.
Ya masa musu sannan ya juya ya kalli Umman nasa.
"Na tsaya ne munyi karatu daga nan kuma sai na tsaya wajen mai shayi"
Ran ta fari kal. Taji dadin ganin wannan canjin daga wajenshi.
"Masha Allah. Allah ya bada sa'a. Ga danwake nan idan zaka ci"
"Na koshi gaskiya. Sai dai anjima"
Suka dan yi shiru. Da Fareeha ta lura kaman yana so yayi wa Umman magana amma ba a gabansu ba, sai ta dauki tray din abincin nasu ta ja kannennta zuwa daki.
"Munyi waya da Baffa jiya"
Umma tayi shiru tana jiran ta ji me zece.
"Ya ce na shirya idan yazo zai kwana biyu sai mu koma tare. Da Abba nada isashen lafiya da sai suyi maganar amma yanzu yace kawai naje din kafin na canja shawara"
Ta gyada kai. "Toh Allah ya sa a dace. Abban naku ma yau jikin da sauqi. Ka shiga ku gaisa"
Mamaki ne ya kamashi a lokacin da yayi sallama ya shiga falon kuma yaji an amsa.
"Malam Bilal"
Wani abu ya tokare mishi a makoshi. Bazai iya tuno yaushe rabon da Abban nasu ya kirashi da wannan sunan ba. Don Kafin ya kwanta rashin lafiya ma kullum yana cikin mishi fada. Amma yau gashi har fara'a yake mishi kuma ya kirashi da sunan da ya fi so a duniya.
"Na'am Abba"
Ya samu waje ya zauna a gefen Kafet. "Yaya jikin?"
Ya lumshe ido hade da jingine kanshi a akan pillow. "Alhamdulillah"
Kamar daga sama suka jiyo muryar Bappah Dattijo yana sallama daga kofar gida. Umma ce ta fito a kicin ta karasa kofar gidan domin ta shigo da shi ciki.
Duk suka zauna a falon aka gaggaisa. Fara'ar Umma yasa Baffan yaji wani sanyi a ranshi don har ga Allah kullum ya ganta cikin damuwa sai yaji ba dadi a ranshi. Kuma yana iya kokarinshi ya ga ya cire Mata duk wata damuwa amma wasu abubuwan sunfi karfin shi.
Ta mishi tayin danwake ya ce ya karya a gidan abokinshi da ke nan GRA kafin ya karaso gidan nasu.
Duk da haka dai ta shiga kicin ta dama mishi kunu ta kawo mishi.
Su Fareeha suka zo suka gaishe shi aka dan taba hira kafin nan suka watse suka bar Mazan a falo.
Anan Baffan ya sanar da Abba hukuncin da Bilal ya yanke wa kanshi na zuwa gidan horo wato rehab.
Kwalla suka cika idon Abban.
"To Dattijo ai duk wani abunda kace dangane da rayuwar Bilal ba zan hanaka ba ko kuma inyi jayayya dakai. Ka mishi abunda ni na kasa yi masa. Ni dai kawai sai da na taya shi da Addua Allah ya bashi sa'an abunda yaje nema. Kai kuma Allah ya saka maka da aljannar firdaus."
Suka amsa da Ameen.
Bayan tafiyar Baffa Dattijo kuma sai da Baba Zubairu ya iso. Nan ma aka sake gaggaisawa. Baba Zubairu yaji dadin ganin yanayin jikin dan uwan nasa.
Duk yadda Abban yaso ya fita sallar Jumuah amma Umma da Baba Zubairu sukace sam babu inda zaije. Da kyar dai ya daddafa Umma ta taimaka mai ya shiga bandaki akayi wanka. Wankan ma a zaune akayi shi. Umma ta mishi gyaran fuska ta shirya shi cikin farar shadda.
Ita kanta sai da zuciyar ta tayi tsalle data kare masa kallo. Ta shimfida masa sallaya a falon nashi bayan Fareeha ta share ta saka turaren wuta na tsinke. Ya zauna ta ajiye mishi littafin Azkar dinshi a gabanshi kafin nann itama ta je ta yi nata wankan.
Bayan ta fito ta shirya suka shiga kicin da yaran aka yi tuwon semo da miyar busashiyar kubewa.
An sauko masallaci lafiya. Baba Zubairu a nan gidan yaci abincin rana kafin nan suka sake fita shi da Bilal din akan ze mishi rakiya.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top