5.
Kamar yadda Malam Kabiru yayi alqawari, kullum da safe zaizo. Zai zauna a falon yayi ta karatu daga baya kuma yayi Addua a ruwa sai a bawa Abban yasha. Da farko yana Shan ruwan sai amai, amma Alhamdulillah a hankali sai ya dena aman.
Wankansa, kashinsa da fitsarinshi duk aikin Umma ne. Ita zata mishi alwala, sannan ta gyara mai kwanciyarsa don fuskantar qibla. Bata san ko yana sallar ba, don wani lokaci zaka ga kamar gangar jikinsa ce ke duniya, ruhinsa kuma yana wani waje daban. Amma a hakan bata fidda rai ba, kullum yana cikin alwala da Shan ruwan Addua. A dalilin Malam Kabirun ne yasa ta dan kwantarda hankalinta, ita ma ta dan murmure dukda kullum kwana take tana sallah.
Gaba daya dawainiyar yaran ta barsu a hannun Fareeha, dama tun da can tana dan taimaka mata. Toh yanzu ita kanyi komai a gidan tun daga abincin safe har shirya qannen nata zuwa makaranta. Haka kuma idan sun dawo zata tabbata sunyi wanka sunci abinci sannan ta jiqa uniform dinsu kafin nan ta tasa qeyarsu zuwa islamiyyah. Da dare ma ita take taya su homework, sai ta tabbata sunyi bacci sannan ita ma zata runtsa.
Tana jin tausayin Umman nata, da irin wahalar Abban nasu da ta ke sha, shiyasa ma bata nuna gajiyawar ta game da ayyukan gidan da ta keyi. Har cikin ranta tasan cewa da Umma ce zata kwanta jinya, tabbas Abba bazai mata kwatankwacin abunda take mishi a yanzu ba. Bata tunanin ko kwatan rabi ma ze iyayi don a iya tasowarta bazata iya tuna rana daya da Abban ya nuna kulawarsa a bayyane ga Umman ba. Bata san ko in suna tare su biyu yana nunawa ba, amma ita dai ba a taba yi a kan idonta ba.
Hakan ne ya sata tunanin shin, dama haka ne yake faruwa idan anyi aure? Ko kuma wasu auren ne suke zuwa a haka? Toh ga dai Anti Mami ita kam qarewa ma sakin ta akayi aka barta da yaron da ko shayar dashi bata gama yi ba. Tana jin yawancin 'yan ajinsu suna cewa idan sun zama JSCE zasuyi aure. Toh meye ne a cikin auren da har suke so haka? Wahala ce kawai zakaje kasha, kayi ta bauta wa miji ka haifa mishi 'yaya ya kasa tayaka riqesu. Shikenan kai baka da rayuwa sai ta wani? Toh gaskiya in dai haka ne ma ita bazatayi aure ba a rayuwarta. Ta ga irin wahalar da Anti Mami da kuma Umma suka sha don haka tayi wa kanta alqawarin bazata taba sa kanta a irin wannan alqawari. Su Qulsoon da Inayaah zasuyi in har suna so, amma ita kam ba ita ba aure. Karatun nan ne sai tayi shi kuma sai ta zama abun alfahari a gurin Ummanta. Zata dauke mata duk wani nauyi kuma zata faranta ma ta in har Allah ya ara mata lokacin.
Da wannan tunanin ta tura qofar falon Abban tayi sallama ta shiga. Umma na zaune akan sallaya da alama ta idar da sallar walaha ne. Dayake yau Sunday ba makaranta, tun da ta shigo ta gaishe da Umman sai ta koma ta je tayi wankin kayansu harda na Umman ma. Sai yanzu ne data gama shanya ta shigo wajen Umman.
"Umma me za a dafa?" Ta tambayeta a hankali.
Ido Umman ta qura mata tana qara ganin quruciyar yarinyar a fuskarta har ma a jikinta. Anya ta yi wa kanta adalci kuwa da ta bar 'yarta a irin wannan hali?
"Adda ki dan huta mana. Kinyi aiki dayawa yau" ta fadi cike da kulawa "Akwai canji a hannuna sai a siyo shinkafa da wake a ci ko? Ko wani abun kikeso?"
Ta dan yi shiru. Ita kam har cikin ranta bata son abincin siyarwa. Amma tunda Umman ta ce haka, hakan za ayi.
"Aa ba komai Umma. Bari inje in daura ruwan Kunun Abba"
Umma ta girgiza kai "Je ki huta Adda. In na tashi zan daura da kaina"
"Toh" tace kawai ta juya ta fice a falon.
Wayar Umma ce tayi ringing, ta duba kuwa taga Anti Mami ce. Ta dauka tare da yin sallama.
"Wa Alaikum salam Umma ina kwana?" Mamin ta fada murya can qasa-qasa
"Lafiya lau Mami. Ya kuke?"
Hawaye ne suka gangaro wa Mamin. Tana so ta fada wa Umma irin halin da take ciki tunda Bappah Dattijo ya tafi wani aiki South Africa, amma kuma bata so ta tayar mata da hankali. Cikin nutsuwa ta amsa mata da "Lafiya Alhamdulillah Umma. Ya jikin Abban Bilal?"
"Da sauqi Alhamdulillah. Yana zama ma yanzun"
Suka cigaba da dan hirarsu zuwa wani lokaci sannan Mamin tace "Umma zan iya dawowa idan na gama idda ta?"
Shiru ne ya biyo baya kafin kuma Umman tace "Wani abunne ya faru Mami? Ko Bappan ne yace ki dawo in kin gama?"
Idonta ya kawo hawaye "Aa Umma. Kawai dai kinga ba sabawa mukayi da ita matar gidan ba kuma zanfi sakewa a nan din...."
"Toh Mami tun farko ba ni na kaiki ba kinga kuwa ba zan ce ki dawo ba ko? In Bappan ya dawo sai ki tambaye shi, in ya yadda ki taho nan din sai ki taho. Amma dai da kinyi haquri kin zauna kinga can din ba Wanda ya sanki, nan kuwa mutane zasuyi ta surutu."
Mami tayi shiru tana juya zancen a kwanyar ta .
Ta nisa, hadi da cewa "Toh Umma. In ya dawo zamuyi maganar. A gaida su Adda. Allah ya qara sauqi"
Umma ta amsa da "Ameen" kafin ta yanke wayar.
Yamma liqis Umma na zaune a tsakar gida tana kallon su Fareeha suna tankaden garin da za'ayi tuwon dare da shi. Kamar daga sama Bilal yayi sallama ya shigo gidan. Sai da gaban Umma ya fadi. Ta ma kasa amsa shi. Su Fareeha kam sai ido suka bishi da shi.
Har gaban Umman ya zo ya tsuguna. Wani wari ya daki hancin ta, idonta har wani yaji-yaji ya fara yi. Bata Ankara ba sai taga ya fara zubda hawaye.
"Umma......" ya fadi a hankali sai kuma ya fashe da kuka. Ai babu shiri Fareeha ta ajiye rariyar hannunta ta ja hannun Qulsoom sukayi cikin daki. Alamu sun nuna baya hayyacinsa, don haka bada ita za ayi wannan dramar ba.
Shiru Umman tayi, its ma kukan ne ya ke kokarin kwace mata amma ta daure. Su biyu a tsakar gidan, yasha kukanshi son ranshi sannan ya share hawayenshi.
"Umma na gaji. Ki cece ni" abunda ya ce kenan yayinda yake jan mijina.
Wani abu ya tokare mata makoshi ga wani zazzafan hawaye dake barazanar zubowa. Ta hadiyi yawu sannan ta ce "Bilal wani taimako zan maka bayan Addu'ar da na ke maka dare da rana?"
Wasu hawayen suka sake zubowa. "To Umma bansan ya zanyi ba. Ko wacce rana idan na farka sai naji na tsani kaina amma maimakon canji, sai in saka fadawa cikin halaka. Na rasa yadda zan saka raina"
Tausayinshi ya kama ta. Tambayoyi ne fal cikin ranta, amma ta rasa ta inda zata fara mishi su saboda son shi da ta ke ji a ranta. Shin duk tsawon kwanakin nan, ina ya shiga? Ba yau farau ba, amma a iya saninta in ya kwana a waje yakan dawo gida washegari. Wannan karon kuma ba haka abun yake ba.
Numfashi ta ja, tareda alkwarin zata tuhume shi idan ya dawo dai-dai kuma ta nema masa mafita. Don a gaskiyar lamari suna bukatar tsayayyen namiji a gidan a halin yanzu.
Ta dafa hannunshi da ke dunqule a gwiwowinsa. "Ka saka a ranka cewa wannan jarabawa ce ta Ubangiji, kuma InshaAllah shi zai fitar da kai a cikinta. Abinda nakeso da kai yanzu shi ne ka tashi kaje kayi wanka kuma ka yi duk sallolin da suka wuceka a kwanakin nan"
Shiru ya biyo baya, kafin nan ya mike a hankali, fuskarsa kaca-kaca da hawaye yayi hanyar dakinsa. Duk abunda ke faruwa akan idon Fareeha. A ranta tace "Allah dai yasa wannan shine dalilin shiriyarsa"
Da daddare dukkansu suka zauna a falon Abban suka ci abinci. Dukda dai ba wata hirar kirki akayi ba amma abu yayi wa Umma dadi a ranta. Abun farin cikine ka juya kaga duk 'yayan daka haifa da ransu kuma da lafiyarsu. Tayi godiya da tasbihi wa Ubangiji kuma ta rokeshi da ya azurta mata mijinta da isashiyar lafiya.
A ranar kwana tayi bata runtsa ba. In banda salolli ba abunda take. Ta sha kukan ta son ran ta, ta na mika roqonta da bukatunta zuwa ga Rabbal Izzati.
Bayan sallar Asuba Fareeha ta dora musu ruwan wanka dana kunu. Ita tayi wa Inayah wanka sannan ita ma tayi. Lokacin da Qulsoom ta fito a nata wankan har Fariha ta gama musu dumame kuma ta dama kunu. Suka karya suka yi shirin makaranta.
Fitar su makaranta da kadan sai ga wayar Bappah Dattijo. Da sallama a bakinta ta amsa. Ya amsa mata tare da tambayar jikin Abban Bilal. Idon ta ya kai kan marar lafiyan da ke sharar bacci tun asuba.
"Ya fara samun sauki Alhamdulillah" amsar da ta bayar kenan.
"Toh Masha Allah. Yanzu ina kan hanyar koma wa Kano, idan Allah ya kaimu gobe zan shigo Azaren in duba jikin nashi"
"Allah ya kaimu. Allah ya kiyaye hanya"
Ya amsa da "Amin Amin. A gaida yaran duka"
Sukayi sallama ta katse wayar. Motsin Bilal ne ya fargar da ita daga tunanin da ta fada. Ya shigo falon ya zauna kusa da ita suka gaisa. Sai a lokacin taga wani bala'in ramewar da yayi. Cikin ranta ta ke Adduar Allah ya yaye mishi duk abunda yake damunshi.
"Tashi kaje kaci abinci. Fareeha tayi dumame"
Ya girgiza kai "Shayi kawai zan sha"
Shiru ya biyo baya kafin nan ya sake cewa "Ina so naje Kano gobe InshaAllah"
Cike da mamaki take kallonshi "Meya faru?"
"Ina so na je wajen Bappah Dattijo. Rehab nakeso a kaini" kansa a qasa yake maganar.
Umma ta jinjina kai "Kunyi maganar da shi ne?"
"A'a bamuyi ba. Ina tunanin in muka hadu face to face zaifi ba wa maganar muhimmanci"
Lallai shiriyar Ubangiji ta fara sauka akan Bilal, tunanin da Umman tayi kenan. "To ka bari mana gobe InshaAllah shima yace yana hanya. In yazo sai ku tafi tare ko?"
Ya miqe tsaye tare da sanya hannunsa cikin aljihu "Allah ya kaimu."
Tace "Ameen"
Daga nan ya wuce kicin din. Tana jin kwaramniyarsa har ya gama tafasa ruwa ya hada shayin sa ya wuce daki. Daga nan kuma sai taji gidan yayi tsit.
Tana zaune a wajen har goma saura, yunwa ta fara nukurkusan ta. Ta duba taga Abban Bilal din bashida alamun tashi, sai tayi hanyar kicin din itama domin neman abinda za ta ci. Sauran dumamen su Inayah ta juye a plate ko sake dumama wa bata yi ba ta janyo flask din kunun ta tsiyaya a cup ta dawo falon. Tana zama aka doka sallama a bakin qofa. Kamar bazata amsa ba saboda ta yi zaman cin abinci ne, saidai ta lalumo hijabin ta ta saka sannan ta amsa sallamar.
Maza ne su biyu suka shigo, dukkaninsu bakin fuska ne a gareta. Tashi tayi daga tabarmar da ta ke zaune ta koma kusa da Abban Bilal inda su kuma suka zauna a inda ta tashin. Suka gaisa har sukayi mata 'ya mai jiki',sai dai fuskan bakin babu annuri.
Cikin karfin hali tace "Sai dai ban ganeba daga ina ne ?"
Babban yayi magana cikin sanyin murya. "Mu 'yan uwan abokiyar zaman ki ne Mariya, daga Bulkachuwa"
"Allah sarki" abinda Umman tace kenan. "Dafatan duk kowa lafiya"
"Babu lafiya fa"
Gaban Umma ya fadi dam.
"Kwanaki biyun nan da suka wuce munyi su ne a cikin kunci domin 'yar uwarmu ta shiga wani hali." Ya dan gyara zama sannan ya cigaba. "Ciwo ne ya kamata wanda daga farko aka kasa gane kansa. To yanzu abun kuma ya juye ya zama kaman aljanu kaman ciwon hauka."
"Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un" wasu hawaye suka taru a idon Umma.
"To dai a cikin 'yan sumbatunta ne takan ce ace miki ki yafe mata. Da muka ga abun ya ci tura shi ne muka zo da kanmu don nema mata yafiya a wajenki ko Allah zai sa ta samu waraka. Wala'Allah alhakin ki ne ya daddaureta ya mayar da ita haka"
Umma ta kasa magana sai kuka. Ta rasa me ke mata dadi. Da wanne zata ji?
Dayan mutumin da tunda suka gaisa be sake cewa komai ba yai magana. "Baiwar Allah ba kuka zakiyi ba. Ki taimaka mana ki yafe wa Mariya ko Allah zai yafe mata itama kafin ta koma gareshi"
Cikin kuka Umma ta furta cewar "Na yafe mata duniya da lahira. Na yafe wa Mariya"
Suka yi ajiyar zuciya gami da cewa "Muma Allah ya yafe mana baki daya"
Su ka ci gaba da bata haquri har suka samu ta daina kukan.
Har bakin qofa ta rakasu, tare da musu alqawarin zata zo har Bulkachuwan idan jikin Abban yayi sauqi don ta duba Mama Mariyan.
Ai wunin ranar Umma kasa komai tayi. Karin kumallon nata ma sai ture shi gefe tayi ta zabga uban tagumi. Shin wai ina zata saka ranta?
Ya Hayyu ya Qayyum.
Tana zaune a wajen tana saqe-saqe. Abban Bilal ya farka. Ta taimaka masa ya dan tashi zaune. Ta gogge masa jikinsa sannan cikin dabara ta sauya shimfidar. Ta canza mishi kaya ta mishi alwala sannan ta fuskantarshi zuwa gabas. Ita ma alwala ta dauro sannan ta tada kabbarar sallar Azahar.
Tana idarwa su Inayah suna sallama. Ta amsa musu a yayinda suka shigo falon dukkansu.
"Sannunku da dawowa"
Inayah ta gangara kan cinyar Umman tayi likimo. Ta shafa kanta tana murmushi "Yaya dai?"
"Umma yunwa nakeji"
Umman ta bude baki zatayi magana kenan sai ga Walid yayi sallama da foodflask guda biyu a hannunshi. Ko cire uniform dinshi ma beyi ba. Ya durqusa ya gaida Umman sanna ya ajiye foodflask din yace inji mamanshi.
"Maman Walid kam bata gajiya. Kace mata mungode Allah ya saka da alkhairi"
"Amin"
Qulsoom ce ta dauki flasks din ta kai kicin sannan ta zo ta fatattaki Inayah akan ta je ta canja kayanta sannan tazo taci abincin.
Sai wajen biyu saura Fareeha ta shigo. Duk ta gaji tasha rana. Sama sama suka gaisa da Umma ta debi ruwa a famfo ta yi bandaki. Sai da ta wanke uniform dinta sannan tayi wanka ta dauro alwala. Ta shanya uniform din ta a tsakar gidan sannan ta wuce daki ta shirya tayi sallah. A lokacin har su Qulsoom sun gama cin abincinsu suna kwance a falo suna jiran lokacin islamiyyah yayi.
Sai a lokacin Bilal ya fito a dakinshi. Tashin sa kenan daga bacci tun bayan yasha tea da safe. Bakin famfo yaje yayi alwala sannan ya koma daki yayi sallar Azahar din.
Da Ummah taji shiru bai fito ba sai tace Inayah taje tace mishi yazo yaci abinci.
"Nikam tsoro nake kar ya dake ni" ta fadi hadi da turo bakinta
"In ya dakeki nikuma zan rama miki"
Ranta dai baya so haka ta miqe kamar wacce qwai ya fashe mata a ciki ta qarasa dakin nasa ta kwankwasa kofa. Da ta ji shiru sai ta dawo tace wa Umma bacci yake. Bata yadda ba sai da ta tashi da kanta taje ta duba sai ta ganshi a kan sallaya yanata sharar baccin kuwa. A ranta tace Allah yasa baccin lafiya ne.
Bayan Sallar la'asar duk suka watse sai islamiyyah. Ummah ta dan share gidan sannan ta daura tuwon dare. Jefi-jefi takan leka falon Abban Bilal sai ta tarar dashi yanda ta barshi a zaune yana kallon bango. Haka dai har ta gama tuwon ta da miyar kuka. Tayi wanke wanke sannan ta daura ruwan wanka. Yana tafasa ta juye a bokiti ta nufi dakin Bilal.
"Maza maza tashi. Wannan baccin asarar ya isa haka." Ta fadi tana jan hannunshi.
Ya farka idonshi sunyi ja.
"Tashi mana"
Ya tabune fuska ya tashi zaune. "Umma ni fa bacci bai isheni ba"
"Kasan karfe nawa kuwa yanzu? Biyar da rabi fa. Ko sallar La'asar bakayi ba ka wani ce min bacci be isheka ba" ta qara jan hannunshi har sai da ta Mike tsaye. "Ga ruwa nan na kawo maka na wanka. Ka je kayi wanka ka wuce masallaci."
Daga nan ta fice ta barshi a tsaye.
Tana cikin bawa Abban nashi kunu ta ji yazo ya wuce ya shige bandaki. Ba da jimawa ba ya fito ya wuce daki.
Dai-dai lokacin da su Qulsoom ke dawowa a islamiyyah lokacin shi kuma ya fita zuwa masallaci.
Sai da sukayi sallah suka ci abinci sannan Umma ta hadasu da flask din Maman Walid ta ce su kai mata kuma su mata godiya. Hakan kuwa akayi.
*******************************
Long Island, New York
Karfe biyu da rabi agogon falon ya nuna a lokacin da Muazzam ya danna kararrawar qofar gidan. Ba da jimawa ba aka bude masa kofar. Murmushi ne ya kwace masa a yayinda abokin nasa ya cafke hannunsa a cikin nasa.
"Shahararrun marasa kirkin sun iso" abunda Mujahid yace kenan cikin zolaya.
"Da ni da kai bansan waye bashi da kirkin ba"
Suna dariya suka shiga gidan. Muazzam ya tsaya ya cire takalmsansa tareda lankaya coat dinsa da muffler dinsa a jikin hanger kafin suka karasa cikin parlor din. Baby din Mujahid wacce bata kai shekara daya ba tana kwance akan baby cot dinta tana sharar bacci. Nan da nan Muazzam ya karasa wajen ya daukota ya rungume a jikin sa.
"Is this Hidaya? Haka ta girma?"
Mujahid ya tabe baki "Ai na dauka ma bazaka gane ta ba. Rabon da ka ganta fa tun muna asibiti"
"Kamin afuwa mutumina. These past few months have been really hard" Muazzam ya fadi tare da langwabar da kansa "Yanzu haka ma daga wajen therapist dina nake"
Gaba daya sai Mujahid yaji babu dadi. Domin a gaskiya Muazzam ya cancanci a masa uzuri. Mutuwar matarsa yayi bala'in juya masa rayuwarsa. Addu'ar mahaifiyarsa ce kawai da rahamar Ubangiji suke taimakonsa don ba don haka ba Allah kadai yasan irin halin da zai shiga.
Yanzu an shafe wajen wata shida kenan amma kullum yana jin mutuwar Najmah sabuwa fil a ransa. Musamman idan ya farka a kan gadonsu ya ganshi shi kadai. Ko ya shiga bandaki ya lura cewa babu shower gel dinta ko hair brush dinta. Ko kuma ya duba closet yaga babu kayanta a ciki. Wannan dalili yasa ya canja gida. Amma hakan bai kawo wani canji sosai ba a tattare dashi. Illa ma sai yaji yana kewar tsohon gidan nasu.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya. Yana nan yana aikinsa na tukin jirgi. Kuma ko wani asabar sukan hadu da Amminsa suje grocery shopping ko kuma ya rakata saloon ko wani dai abu haka. Wasu lokutan ma su kan qarasa Manhattan su shiga wannan restaurant din su fita su je wannan shagon suyita yawace-yawace suna nuna kamar cewa su baqi ne wanda suka zo yawon bude ido(tourists).
Hakan yakan yi wa Ammi matukar dadi idan ta ganshi yana farin ciki yana walwala dukda tasan cewa yana cikin tsananin damuwa. Samo masa therapist din da ta yi ya taimaka kwarai domin yanzu damuwar tasa ta ragu kuma yakan fita yaje yayi basketball da abokansa kuma yanzu yana yin exercise.
An ce dama komai lokaci ne. Ita dai fatan ta Allah ya kawo wa Muazzam dinta mata wacce zata tausaya mishi kuma ta soshi ko da rabin rabin son da Najmah ta mishi ne. Tasan cewa maganar aure ba yanzu ba, amma tana fata abun zai kasance nan kusa ne.
Matar Mujahid mai suna Aisha ne tayi sallama ta shigo parlorn da tray na kayan shayi a hannunta. Ta ajiye akan coffee table din sannan suka gaisa da Muazzam.
"Ai nikam na dauka ka yaye mu ne. Shiru shiru babu kai babu labarinka"
Muazzam ya danyi murmushi "To yanzu dai tunda gani nazo sai amin afuwa"
"Afuwar da za a maka shine kayi babysitting Hidaya for a week"
Dariya yayi sosai tareda kara rungume baby din a jikinsa. "This is the best job in the world ,you know right?"
Mujahid ya tabe baki "For you ba. Wai kasan kalar fitinan yarinyar nan kuwa?"
"Duk wannan ba damuna zaiyi ba InshaAllah. I'm in"
Aisha tayo murmushi "Ni wasa ma nake maka Uncle Muazzam. Ina ni ina barinka da rigimammiyar nan. Kana so Amminka ta kaini kara kenan"
Sukayi dariya dukkansu sannan ta koma kicin domin ta cigaba da ayyukan ta.
Mujahid da Muazzam suka zauna domin shan tea. Duk da haka Hidaya na hannunsa tana shan bacci abun ta.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top