4.
Salaaam Alaikum everyone. Sorry for my silence.
4.
Abban Bilal bai farka ba sai washegari da Asuba. Umma kam kwana tayi tana roqon Allah ya ceci ran mijinta. Daga qarshe haqura tayi ta kira Balaraba ta sanar da su Fareeha halin da ake ciki. Inaayaah kam har da kukanta wai zata taho. Ta dai basu haquri tace su tayasu da Addua. Dada ma tayi jajen abun. Ta yi wa Umma alqawarin cewa gari yana wayewa Balaraba zata rako yaran insha Allah.
Fitar da tayi zuwa bandaki domin ta kama ruwa kuma tayi alwala ne ya farkar da Abban Bilal din. Ta dawo kenan tana qoqarin fuskantar alqibla kawai sai taga idonshi a kanta. Gabanta yayi mummunar faduwa. Suka tsaya suna kallon kallo. Abubuwa da ta dade bataji game dashi ba taji sun taru wake daya sun dunqule a can cikin zuciyatrta. Da qyar bakinta ya motsa
"Sannu Abban Bilal. Ya jikin?"
Kai kawai ya iya daga mata saboda wani azababben zafi da ya keji tun daga qaramar yatsar qafarshi har zuwa qasan kanshi. Sake runtse idonshi yake ko hakan zai sama mishi sauqin ciwon dayakeji amma kamar an qara rura wutar ciwon.
Ta dan dafa gadon tana matsowa kusa dashi. "Akwai abinda kakeso? Ko in kira doctor?"
Kasa motsawa yayi balle ma ya bude baki ya fada mata irin azabar dayake sha. Wata ajiyar zuciya ta saki kafin nan ya bude idanuwan nashi ya sauke su a kanta.
"Sannu. Sannu kaji" abinda tace kenan domin ta karanto abunda ke kwance a cikin idanuwan nashi.
Ya dan gyada mata kai kadan.
"Me kakeso? In baka ruwa kasha? Ko in taimaka maka ka zauna?" Ita kanta bata san daga ina wadannan tambayoyin suke zuwa mata ba, kawai ta tsinci kanta da yi mishi su.
Bai bata amsa ba illa lalumo hannunta da yayi ya damqe cikin nashi ko zai samu sauqin azabar dayakeji din. Wani baqon abu taji ya ziyarci dukkan ilahirin jikinta har yana barazanar fasa mata kwanya.
Shikuwa sake lumshe idon nashi yayi. Tana durqushe a wajen hannunshi na cikin nata har wani baccin ya sake daukeshi. A hankali ta zare hannun nata sannan ta tashi ta gabatar da sallar Asuba domin har lokaci ma ya wuce.
Ta na nan zaune a kan sallayar har nurses sukayi canjin shift; 'yan dare suka saki aikinsu wa 'yan safe. Wata nurse ta shigo dakin tana dudduba marasa lafiyan har ta iso gadon nasu. Suka gaisa ta tambayeta ya mai jiki ta amsa da lafiya hadi da sanar mata cewa har ya farka dazun. Nurse ta danyi wasu rubuce rubuce a jikin wani littafi dake maqale a kan gadon sannan ta cire mishi ledar jini da ta drip din wanda tuni duk sun qare.
"Doctor zai shigo nan da one hour insha Allah " fadar nurse din kafin ta mata sallama ta fita.
Fitar nurse din keda wuya saiga kira yana shigowa wayar Umman. Maman Walid ce don haka tayi saurin dauka. Suka gaisa ta tambayi mai jiki tace da sauqi.
"Umma ko akwai wani abunda kikeso in kawo muku daga gidan? Ina tura yara makaranta nima zan taho insha Allah"
Umma ta nisa tana jinjina qoqarin maqociyar tasu. "Babu komai Maman Walid. Dama kinyi zamanki basai kinzo ba"
"A'a Umma ga abinci kari har na dafa ai ya kamata kici wani abu a cikinki indai kema ba jinyar kikeso ki fara ba"
Dan guntun murmushi ya kubce mata. "Toh mungode. Sai kinzo"
Har zata katse wayan ta dakatar da ita.
"Nikam Baban Walid yace miki ko yaga Bilal? Tun jiya fa na kasa samunshi a waya na fada wa Baban Walid din yace ze nemeshi a unguwa"
Maman Walid ta danyi jim. Bata son sanar da Umman halin da ake ciki domin hankalinta ne sai qara tashi. Ita ce ma ta hana Baban Walid din kiran Umman, don da shi niyyar shi ya sanar mata halin da ake ciki.
Wato a daren ranar da abun ya faru Bilal din da wasu abokansa suka samu matsala da wasu yara 'yan matsango. Sunyi rikici sosai har aka kira 'yan sanda suka kwashe su. To yawancin 'yan dabar su Bilal din sun samu sun gudu, 'yan matsangon ne dai aka kamasu da yawansu ciki kuwa har da ogan su. Shine sauran yaran ogan wanda basu fada hannun hukuma ba suka biyo Bilal din har gida, a tunaninsu yana gidan. Suka shiga domin su mishi dan banzan duka su Kakkarya shi. Akayi rashin sa'a baya nan sai Abban. Su kuma suka ga bazasu yi aikin banza ba shine shima Abban suka dan lallasa shi, wai don in Bilal din yazo ya gani ya tsorata.
Maman Walid ta yi ajiyar zuciya. Yanzu idan Umma taji wannan labarin ai hankalinta ne zai qara tashi. Don haka kawai tace "Umma kinga kuwa bamuyi maganar dashi ba. Amma insha Allah in ya dawo a aiki zan tambayeshi."
Wasu hawaye suka taru a idon Umman. Yau ina dan ta tilo guda ya shiga?
"Toh. Allah ya kaimu" kawai tace sai ta katse wayar.
Tsabar nisan da tayi a kogin tunani bata ji gaisuwar da Dakta Yusuf yake mata ba sai da ya sake yi mata wata sannan ta dago ta kalleshi.
Tashi daya yaji tausayin matar ya kamashi. Duk ta rame ta jeme a qanqanin lokaci.
"Nurse ta ce min ya farka dazu" ya fadi bayan sun gama gaisawa. Littafin da nurse din tayi rubutu a jiki yake sake dubawa yana jinjina kai.
"Yanzu zan aiko a canja mishi ledar fitsari. Sannan zan rubuta muku wasu magunguna da zakije ki karbo a pharmacy. In ya tashi a bashi ruwan shayi ko kunu ko dai wani abu mai ruwa-ruwa amma banda abinci mai nauyi"
Umma ta amsa da "Toh likita. An gode "
Ya rubuta magungunan sannan ya miqa mata takardar ya nufi wani gadon domin duba sauran peshan din dake dakin.
Tana fitowa a ward din Maman Walid na isowa. Suka sake wata sabuwar gaisuwar. Tace mata zata je ta karbo magani sai ta dawo ta ci abincin data kawo. Maman Walid ta amsa da to sannan ta shimfida 'yar tabarmar data zo da ita.
Umma na dawowa daga karbo maganin ta hango su Fariha da sauran yaran zaune wajen Maman Walid din. Kafin ta qarasa Inayaaah ta taho da gudu ta fada jikinta. Nan da nan ta barke da kuka.
"Umma me ya sami Abba? Ciwon da yawa ne? Ya tashi?Ina de ba mutuwa zaiyi ba?" Ta jero mata tambayoyi kamar an aikota. Umma ta shafa kanta ta dan janyeta daga jikinta tace
"Inayaah banson kukan nan ya isa haka. Abbanku zai samu sauqi da iznin Allah. Ki mishi Addua kinji?"
Kai ta daga mata sannan ta sa hannu ta share hawayen nata. Tare su ka qarasa wajen sauran. Bayan sun gaisheta suka tambayi jikin Abban nasu. Ta amsa da sauqi.
Tare sukaci abincin da Maman Walid din ta kawo. Dafa dukan dankalin turawa ne yasha kayan lambu se kuma bread data kawo da kuma flask cikeda shayi wanda yasha kayan qamshi.
Bayan sun kamalla Umma ta umurce su da su koma gida su zauna da Maman Walid har sai yamma tayi lokacin visiting hours sai su dawo su ga Abban nasu, tana fata lokacin ya dan ji dama-dama. Hakan kuwa akayi. Su la tattara suka tafi bayan sun bar mata shayi da bredin.
Komawa tayi ta zauna a gefen gadon nashi. Ta lura an canza mishi ledar fitsarin dake jikinshi kuma har nayi dressing dinkin nashi an sauya bandeji. Kamar yadda ya zame mata jiki, Adduoi ta rinqa yi a cikin ranta har ma a bayyane, tana Adduar Allah ya kawo wa mijin nata sauqi kuma ya bayyana mata Bilal dinta. A haka har bacci ya kwasheta.
*****
Abu kamar wasa, ciwon Abban Bilal din ya warke tas amma saida me? Wani ciwon ne kuma ya sake bijirowa. Ba ya iya magana, ga wani zazzafan zazzabi dayake mamaye shi duk wata safiya. Idan zazzabin ya sauka kuma sai ya jiqe sharaf da gumi, yayi ta karkarwar sanyi. Su kansu likitocin sun kasa gano maqasudin abunda yake damun sa.
Mama Mariya kam bata dawo ba, illa ma sai turowa tayi aka kwashi 'yayanta aka tafi dasu. A cewarta, ita ma rashin lafiya ne ya kamata bazata iya doguwar tafiya ba. Tsabar takaici ma Umma rasa abinda zata ce mata tayi. Haka yaran suka tattara suka tafi bayan sunzo sun ga Abban. Daman tunda aka kawoshi sau biyu suka zo, kuma duk lokutan dasuke zuwa bacci yake. Ranar da sukazo yimishi sallama ma baisan waye yake kanshi ba saboda tsabar azabar daya ke sha.
Yayanshi dake Hadejia, wanda suke kira da Baba Zubairu ne yazo domin ganin jikin nashi. Yana zuwa kuwa yace zai canja mishi asibiti su koma asibitin Malam dake Kano domin jikin ya qara tsanani kuma likitoci sun kasa komai a kai in banda allurar bacci da ake dirka masa sai kuma drip dayake sha don in yaci abinci baya minti biyar sai amai. Daga kunun gyada sai tea shikenan abunda yake ci.
Idan kaga Umma sai kace ita ce marar lafiyar saboda tsabar ramewar data yi gashi duk ta yamushe. Hankalinta ne ta kasa kwantar dashi. Ga miji ba lafiya, ga Bilal yanzu kusan satinshi uku a hannun 'yan sanda. Ta rasa me ke mata dadi. A asibitin take kusan wuni, sai wajen la'asar idan Fareeha tazo sai ta koma gida tayi wanka ta ci abinci ta dan runtsa. Da anyi sallar isha Baban Walid zai dawo da ita sai ya maida Fareeha gida.
Kusan kullum Doctor Yusuf yana zuwa ya gaisheta kuma ya tambayi jikin Abban dukda yanzu shi din ba peshan dinshi bane. Shi kanshi ya girgiza da lamarin.
Wata rana da safe daya je sai Umman take sanar dashi Baba Zubairu yace za a maida shi Kano domin a yi mishi wasu gwaje-gwaje don a gano matsalar.
Dakta Yusuf ya jinjina kai sannan yace "Hakan ma yayi daidai. Amma Umma ga shawara"
Umma ta gyara zama "ina ji Dakta"
"Me zai hana a dangana da addu'o'i da ruqiyyah? Don inaga abun kamar harda sihiri a ciki."
Gaban Umma ne ya fadi taji wani malolon abu ya kafeta mata qirji.
Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un. Sihiri?
"Akwai wani Malami dana sani a irin wannan fannin ya qware. Ina ga kafin kuje Kano din sai a jarraba a gani mai yiwuwa a samu nasara"
Shiru tayi na dan wasu lokuta tana juya maganar tashi kafin ta amsa da "Toh Dakta. Insha Allah sai a gwada a gani. Allah ya sa a dace"
Ya ce "Ameen. Duk sanda zaku koma gida sai ki sanar min insha Allah sai na kaiku wajenshi"
Hawayen da suka taru a idon ta take qoqarin hadiyewa amma sai da suka zubo. Zuciyarta ta yi mata daci.
Tausayinta ne ya qara kama Dakta. baI qara cewa komai ba ya fice saga ward din. Baya tantama wannan aikin sihiri ne. Don yasha cin karo da irin wannan matsalolin. Zakaga mutum yazo asibiti a kasa gane me ke damunshi, ga ciwo ya qi ci ya qi cinyewa, amma ana zuwa ana ruqiyyah sai kaga an fara samun sauqi. Ba wai be yadda da maganin asibitin bane, a'a. Wani lokacin kawai abun yana fin qarfin ilimin mutum sai a dangana da ayoyin ubangiji.
Bayan kwana biyu da maganar su da Dakta sai ga Baba Zubairu ya sake dawowa. Umma ta fada mishi abinda likitan yace. Ya jinjina kai.
"Nima nayi tunanin hakan, amma sai ban ce komai ba dan kar inyi hanzari. Da na so ace sai yaje Kanon idan ba a daceba sai ayi ruqiyyar, ya kika gani?"
Kanta a qasa tace "Toh akan aje ana qara kashe wani kudin ba gwamma an gwada wannan dinba tukunna?"
Baba Zubairu yayi na'am da shawarar nata. Washegari yazo da mota aka debesu. Motar Dakta na gaba suna binta har gidan Malam Kabiru, Malamin da zai yi musu ruqiyyar a can unguwar Rijiyar 'yan wanki. A mota aka bar Abban inda shi Malan din ya fito daga gida ya dubashi. Ya tabbatar cewa Sihiri ne amma kuma ya dade yana tare dashi. Dalilin dayasa kuwa yake wannan ciwo shine Sihirin ne yake qoqarin karyewa wasu kuma suna qoqarin dora shi shiyasa yake ta ciwo babu qarewa.
Umma sai Kuka. Ta rasa inda zata saka kanta domin kwata kwata bata kawo wanann a ranta ba. Yanzu wanene zaiyi wa mijinta wannan danyen aikin? Anya mutane suna tunanin haduwarsu da Allah? Wannan wani irin rashin Imani ne?
Malam Kabiru yace a maida shi gida gobe sa safe zaizo da ruwan Addua kuma zai mishi ruqiyyah insha Allah zai samu sauqi. Kafin su tafi ya bawa Umma wasu adduoi yace ta tofa a ruwa ta mishi alwala dasu kafin ya kwanta.
Jikinsu a sanyaye duk suka koma gida. Yaran duka suna gidan Maman Walid don haka tana zuwa ta bude sashen nashi ta fara sharewa dukda Fareeha ta dan share sama-sama. Ta wanke bandakin ta goge ko ina sannan Baba Zubairu ya tayata suka kwantar dashi a kan katifar data shinfida a tsakiyar falon.
Sai a lokacin Maman Walid suka shigo da su Qulsoom hannunsu riqeda kulolin abinci.
"Maman Walid ke kam bakya gajiya? Yanzu kam ai na dawo gida sai ki bar dawainiyar haka ko?"
Fuskarta dauke da murmushi tace "Haba Umma ba wata dawainiya ai an zama daya. Ya jikin Abban?"
"Toh Alhamdulillah." Kawai tace. Tana so ta mata zancen sihirin amma kuma sai taga ba huriminta bane.
Ta barsu a nan falon da yaran ta wuce dakinta domin ta dan watsa ruwa tayi sallar Azahar.
Fareeha ce suka shigo gidan tareda Walid da qanwarshi Walida. Sun dawo kenan a makaranta suka samu gidan su Walid din a kulle shine suka taho nan din.
Suka qarasa cikin palon Abban inda kowa yake. Ta durqusa ta gaida Baba Zubairu wanda ke zaune can nesa a kan kujera fuskarshi cikeda damuwa, ga abinci Maman Walid ta zuba amma ya gaagara ci. Sama-sama ya amsa mata ya cigaba da tunanin da ya fada.
Ta maida kallon ta zuwa ga Mahaifinta dake kwance a kan katifa, rai kwa-kwai, mutu kwa-kwai. Ta manta rabon da taji muryarshi a cikin kunnuwanta, da taga idanunshi a cikin nata. Ta sani babu shaquwa a tsakaninta dashi, amma Mahaifinta ne shi, kuma tana sonshi tana tausayinshi. Shiyasa yanzun data ganshi taji wasu hawaye suna barazanar zubo mata. Da sauri ta miqe ta nufi sashensu.
Ta dauka hawayen nata sun qare, ashe akwai saura. Don duk tsawon lokutan da take zama dashi a asibiti idan Umma taje gida ba abunda takeyi sai Kuka. Wani lokacin har haushi kanta takeji. Meyasa takeyi mishi kuka bayan shi baI damu da ita ba? Meyasa takejin shi a cikin ranta bayan shi ba haka yakeji ba a nashi ran?
"Adda har kun taso?" muryar Umma ce ta katse Mata tunanin da ta ke. A lokacin kuma ta ankare cewa hawaye ne malala a kwance a fuskarta. Don haka tayi saurin dauke kai tana nufar hanyar dakinsu tareda fadin "Eh Umma. Bari na canza kaya in fito" tare da jawo qofar ta rufe ruf.
Sarai Umma taga hawayen nata saidai bata da abinda za ta ce mata. Ita dinma a halin yanzu rarrashi take buqata da ban baki. Gaba daya duniyar ta jagule mata. Saidai bata son taga 'yar tata a cikin damuwa. Tana da qarancin shekarun da bai kamata ace ta na wasu tunanin da sunfi qarfin qwaqwalwarta ba. Yanzu ne lokacinda daya kama ta ace tana cikin farin ciki kuma ba ta tareda wani damuwa a ranta illa abinda ya shafi karantunta da addininta. Amma saidai an samu akasin hakan. Tausayin 'yar tata ya sake kama ta.
Sam bata damu da su Qulsoom da Inayaah ba, domin su yara ne kuma basa saka abu a ransu kamar yadda ita Fareehar ta ke sakawa. Ido ta lumshe, tana roqon Allah ya basu sa'ar cin wannan jarabawar.
Falon ta koma ita ma ta zuba abincin ta fara ci suna hira sama-sama da Maman Walid da yaran. Suna nan zaune har Baba Zubairu ya gama ya ce shi zai wuce amma zai dawo bayan kwana biyu. Umma ta mishi Allah kiyaye tareda godiyar dawainiyar da yayi dasu. Sukayi sallama ya fita.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top