34.


Hello my loves ❤.  A cigaba da hakuri da ni please and manage this chapter.




34.

"Yanzu Adda sai yaushe?"

Dariya ce ta kusa ta kubce mata a lokaci guda kuma taji kamar ta fashe da kuka.

A wasu 'yan shekaru a baya haka suka zauna a tsakar gidan nan ita da Maman Walid tana tambayar ta yaushe zata dawo idan ta koma makaranta. A lokacin kam tana da amsar da zata bata. Amma a halin yanzu, bata da shi.

Tun da Mu'azzam ya samu labarin yajin aikin da aka shiga na kungiyar malamai ta jami'o'i wato ASUU, yace to tayi maza-maza ta hada nata ya nata ta taho. An yi rashin sa'a ne ma ya cinye duk hutun sa na shekara a dalilin sintirin da yayi tayi a tsakani amma babu makawa da shi da kan shi zai zo ya tafi da ita. Ticket din nata ma one way ya siya mata.

Kallon lallen da Hafsatu take zana mata tayi tare da ajiyar zuciya ta ce. "Hmmm Maman Walid nima ban sani ba. Sai dai abun da Allah yayi kawai"

Tana ji a cikin ranta in har ta tafi to dawowar ta zaiyi wuya.

Shi gogan ma shirin maida makarantar tata can America gaba daya yake. Shi murna yake yi ma saboda an shiga yajin aikin. Don kwata-kwata basu saka ran sake haduwa ba sai nan da wasu 'yan watanni idan ta samu hutu. Sai gashi kuma Allah ya juya lamarin.

Maman Walid ta jinjina kai.
"Allah sarki Adda. Auren kenan fa. Tun da kike nasan baki taba tunanin ko da barin garin nan ba, sai gashi kasar ma gaba daya zaki bari.To dai in an tafi kar a manta da mu. A rike zumunci dan Allah. Nasan da wuya, amma ayi kokari Adda kinji?"

Nan da nan hawaye suka taru a kurmin idon ta. Ita ta isa ta manta da Maman Walid bayan irin kalar halaccin da ta musu. Ai ba ta isa ba.

Hafsatu ta dago ta kalleta tana dariya tace "Maman Walid kiyi shiru fa kar ta fashe mana da kuka a nan yanzu muji saukar jirage ta ko ina"

Dariya suka saka su biyun in da ita kuma Fareeha ke hararar Hafsatun.

Haka suka gama lallen suna dan taba hirarsu.

Sai bayan la'asar tukunna Hafsatu ta tafi bayan ta wanke mata lallen. Tubarkallah Masha Allah yayi kyau matuka. Ga fatar ta nan sai sheki takeyi da sulbi don kafin ta taho Azare sai da Anti Bebi ta kaita a ka mata gyaran jiki na tsawon sati biyu.

Ita kanta sai da taji canji a tattare da ita.

Tana share tsakar gidan bayan tafiyar Maman Walid ne Abba yayi sallama ya shigo.

Ledar Viva dake hannunsa ta yi sauri taje ta karba.

"Kaji ne nace ko zaki masa dambu ki tafi masa da shi?"

Sunkuyar da kai tayi tana murmushi. Allah sarki Abban ta. Dukda larurar dayake fama da ita, amma hakan bai sa ya dena musu dawainiya ba.

"Abba angode Allah ya saka da alkhairi ya kara budi."

Ya amsa da "Ameeen" kafin ya shige falon sa.

Tana cikin tafasa kajin Umma da Anti Mami suka dawo. Sun je dubo Daada ne a Shira ta danyi ciwo na kwana biyu har aka kwantar da ita a asibiti amma jikin da sauki yanzu Alhamdulillah. Fareehan ma ta so ta bi su amma Umma ta hana wai salon yawo ne kawai tun da dai mijin ta gida yace tazo bai ce ta je har wani garin ba kuma.

Leda cike da kwalam suka kawo mata wai inji Daadar. Haka tayi ta budewa tana ta murna. Su yajin tafarnuwa ne da daddawar miya da busashiyar kubewa da dai sauran abubuwan mutanenmu na kauye. Sai kuma chin-chin, gyada amaro da aya mai siga.

"Ke yanzu aka bude akwatin ki aka ga daddawar miya ai hana ki tafiya za'a yi" Anti Mami ta fada tana mata dariya.

Fareeha tayi narai-narai da ido. "Adda Samha fa tace baza'a kwace ba in dai nayi wrapping dinsu da kyau"

Anti Mami ta jinjina kai "To ni dai ba ruwana. In da rabon sun hanaki tafiya to"

"Kai Mami ki dena tsorata ta mana" Umma ta fada tana gintse dariyar ta ganin yanda Fareehar duk ta zama kalar tausayi.

Umma ce ta tuke mata dambun tass. Abun ka da ba yawa bane dashi kan ta gama rabawa 'yan kannen nata ladan ganin ido har ya kusa rabi. Haka ta nannade shi a jarida ta tusa a akwati.

Washegari karfe goma na safe direban Bappah Dattijo ya iso.

Fareeha kuka har da majina haka suka rabu da 'yan gidan su. Ko ranar da aka daura mata aure batayi irin kukan da tayi a yau ba. Ko don wancan lokacin ta san zasu sake haduwa ne, wannan karon kuma bata san yaushe zasu sake ganin juna ba. Su Qulsoom kam sai da aka banbare su a jikinta.

Haka aka taru a kofar gidan ana ta koke-koke.

Da kyar dai Anti Mami ta samu ta cusa ta a mota suka kama hanya.

Tun Anti Mami na lallashin ta har ta gaji ita ma ta zuba mata ido.

Gidan Ammah ya sauke su don kusan duk wasu kayan ta da zata bukata ta dawo da su gidan.

Aunty Zu suka samu don Amman tayi tafiya zuwa Jos. Prof ne ya saka sunanta a wani Kwas na National Institute for Policy and Strategic Studies, aka ci sa'a kuma akayi approving to shi ne ta je don tayi rajista.

Bayan sunyi sallah sun ci abinci aka shiga wani sabon packing don washegari zasu wuce Abuja ita da Anti Mamin.

Ita kam tsabar kukan data sha zazzabi ne ya rufeta don haka Aunty Zu ta bata magani tace ta kwanta su zasu mata packing din.

Sai dab da Maghreb ta farka. Shima kiran daya shigo wayar ta ne ya tashe ta. Sai da tayi sallolinta tukunna ta kira shi.

"Jikinne har yanzu?" Ya tambaya bayan sun gaisa.

Dan guntun murmushi tayi tace "Ho! Nikam duk motsi na sai an sanar maka ne?"

Shima murmushin yayi. "To na bada amanar zuciya ta ba dole a sanar min da dukkan motsin ta ba? In ta buga fa?"

Ita kam ta godewa Allah da ya hadata da mutum irin Mu'azzam. Mutum sai bala'in zaro zance haka ko nauyi basa mishi.

Juya idon ta tayi kaman yana gabanta tace "Naga alama ai. To yanzu dai na ji sauki Alhamdulillah. Calm down"

Hakan ya bashi dariya. "Ai da alama kam kin ji sauki. Kin gama shirin dai ko?"

"Eh na gama. Su Aunty Zu sun taya ni"

"Kai amma sun kyauta. Allah ya saka musu da alkhairi"

Sun dan taba hira kafin nan ya mata sallama bayan ya cika ta da kalamai masu sanyaya zuciya.

Tana ajiye wayar kuma sai ga kiran Ammah ya shigo. Gaisawa sukayi sannan Amman tace mata anjima Aliy zai kawo mata sako.

"Na bawa Zuwaira ma wasu kayan sanyi nace ta baki idan kinzo. Kinsan yanzu sanyi ya kankama sosai a can"

"To Ammah Nagode Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen Ameen. Kin kammala duk wani shiri dai ko?"

"Eh Ammah nagama"

"In dai akwai wani abun ki fada fa. Kar kiji komai"

Sunkuyar da kai tayi kaman tana gaban ta tace "Wallahi Ammah babu komai. Mungode da dawainiya Allah ya saka da alkhairi"

Bayan Isha sai ga Aliy Mastoor ya kawo mata sakon a envelope. Kudi ne Ammah ta bashi akan ya canja ya kawo wa Fareehar. Dayake British Airways zata bi don haka akwai tsayawa a Landan, shi ne Amman ta bayar a canja mata Pounds ta sha ruwa a Airport din kafin ta shiga wani jirgin zuwa New York.

Ai yana tafiya ta dauki waya ta kirata. Godiya kan godiya haka suka gama wayar Ammah tana ta saka mata albarka da addu'o'i masu kyau.

Karfe shi hudu da rabi na yamma a filin jirgin Malam Aminu Kano tayi musu.

Fareeha taga jama'ar da sukazo mata rakiya sai abun ya bata dariya. Bappah Dattijo da ilahirin zuriyarsa suka taho har da Ya Ashraf da Wafiyya, ga Samha da maigidan ta. Mota uku sukayi gaba dayan su. Ga kuma Prof da Aliy Mastoor da kannensa shi ma. Anti Balaraba ba haka ta tattaro kan iyalan ta suka taho.

Sallama dai taki karewa har sai da sukaga lokaci yana nema ya kure musu sannan aka rabu.

Wannan karon dai Fareeha bata yi kuka ba don ana wasa ana dariya aka rabu kowa yana mata fatan alkhairi da son barka.

Direba aka turo daga gidan wani abokin Bappah yazo ya dauke su a Airport. Lokacin da ta zo intabiyu din visa ma a gidan ta sauka dukda a lokacin masu gidan basa nan sun je Umrah.

To yanzu ma dai da suka zo ance basa nan sun tafi Egypt graduation din daya daga cikin 'yayan gidan.

Sun sami abinci da masauki mai kyau sosai. Dukda cewar jirgin Fareeha na safe ne hakan bai hana su hira da Anti Mami ba har asuba. Yawanci dai shawarwari tayi ta bata da kuma addu'o'i da zasu taimaka mata.

"Yanzu ne zaku fara zaman aure Adda. Wannan da kukayi na dan lokacin nan sharar fage ne kawai. Hakurin nan dai da mukayi ta nanata miki a baya, yanzu ne zaki ga dalilin daya sa muke fada miki hakan"

Idon ta cike da bacci haka ta daddafa tayi sallar asuba sannan tayi wanka ta shirya. Dama matar gidan ta riga ta sanar da masu aikin zancen tafiyar tata don haka tana fitowa a wanka mai aiki ta shigo tace ta hada musu breakfast a falo. Godiya ta mata sannan ta maida kallon ta kan Anti Mami wacce tun bayan da tayi sallah take ta sharbar bacci.

"Anti Mami ki tashi ki shirya fa kar mu makara"

Wani juyi tayi kafin ta bude ido daya tace "Ai inaga kawai anan zamuyi sallama don bana tunanin zan iya rakaki har airport."

Kasake ta tsaya tana kallonta. "Haba Anti Mami kar kiyi min haka. So kike in tafi ni kadai? To naki flight din fa?"

"Ni ki kyaleni, zan ce wa Bappah sai gobe a canja min ticket din"

Wani abu Fareeha ta hadiya kafin nan ta juya ta fara shiri. Bata sake ce mata komai ba ta fita falo ta fara karyawa. Daurewa kawai take yi amma wani abun da ya makale mata a makoshi in ba'a ci sa'a ba in ta hadiye shi to kuka ne ze biyo bayan sa.

Ta na cikin sake-sake ne sai ga Anti Mami ta fito a shirye tsaf sai zabga kamshi take.

Kallon Fareeha tayi sannan ta fashe da dariya. "Ni dadi na dake baki san wasa ba wallahi. Ki saki ranki dan Allah kar fuskarki ta kone don dai ta fara tafasa kam"

Dukda bata ji dadin wasan Anti Mamin ba amma dai taji sanyi a ranta jin cewar ba ita kadai zata tafi ba.

A tsanake suka gama sannan suka dau haramar tafiya.

Karamin akwatin ta dama kawai ta shigo da shi a jiyan don sauran kayan nata duka a boot din motar ta bar su don haka shi kawai ta jawo suka fito.

Har gaban kofar international departures Anti Mami ta rakata. Ganin dai rakiya tazo karshe fa hawaye suka ce salamu alaikum. Duk dauriyar Anti Mami ita ma sai da ta zubda su. Haka suka rungume juna babu mai lallashin dan uwan sa.

Sai da sukayi mai isarsu sannan Anti Mami ta sake ta.

"Zanyi kewarki matuka Adda. Ina mai miki fatan alkhairi da addu'ar Allah yasa wannan tafiyar ta kasance mai dinbin alkhairai a cikinta. Allah yasa muna da rabon sake haduwa"

"Ameeen"

Haka suka rabu kowa ya kama hanyar sa.

Kanta har ciwo yake saboda rashin bacci da kuma kukan da ta kasa dainawa. Har ta yi checking in ta hau sama ta samu waje ta zauna a waiting lounge bata dena kuka ba.

Kiran Mu'azzam ne ma yasa ta dan tsagaita saboda ta san shi yanzu hankalin shi zai tashi.

"Kin gama komai ko? Ba wata matsala?"

Gyada masa kai tayi sai kuma ta tuno cewa ba ganin ta yake ba, don haka ta amsa da "Babu"

"To Masha Allah. Allah ya kiyaye hanya ya kawo ku lafiya"

"Ameen"

"I can't wait to see you"

Shiru ta mishi kawai don idan ta cigaba da magana wani sabon kukan ne zai dawo.

Murmushi yayi mai sauti. "Ayi hakuri a dena kukan nan my love. Girma ne yazo miki, sai hakuri. Kowa ma da haka ya girma"

Haka ya cigaba da lallashin ta har aka fara kiran su boarding. Addu'o'i ya mata kafin nan suka yi sallama.

Tana shiga jirgi ta cusa dan karamin akwatin ta a sama sannan ta zauna. Umma ta kira sukayi sallama sannan Anti Bebi da Ammah. Su Hafsatu da Yusrah kam text message ta bi su dashi sannan ta saka wayar ta a flight mode.

Wani bacci ne ya dauke ta a lokacin da suka tashi, ko da aka tashe ta ma lokacin da aka fara raba abinci, cikin magagi taci abincin ta cigaba da baccinta.

Duk yadda ta so taga gari a lokacin da jirgi ke sauka hakan ya gagara don ji kawai tayi ana cewa sun iso filin jirgin Heathrow da ke birnin Landan.

Sai da ta gama duk wasu biyebiye daya kama ta tayi a bisa ka'ida sannan ta shiga neman wajen sallah. Cikin sa'a kuwa ta samu. Sallolin azahar da la'asar ta gabatar sannan ta fito don neman abun sawa a bakin salati.

Pan(£) dari Ammah ta bata na shan ruwa a Airport. Sai da ta zo siyayya ne ma ta gane cewa ba karamin kudi ta bata ba.

Pizza ta siya 'yar karama sai shayi don ta turara 'yan hanjinta.

Waje ta samu ta zauna ita da 'yan tarkacen ta sannan ta jona wayarta da WiFi din filin jirgin. Ko minti daya ba'a yi ba sai ga wayar shi nan ta shigo.

"Kun sauka lafiya? Ba wata matsala dai ko? Ki na dai terminal dinki ko?"

Murmushi ta sakar mishi "Ka kwantar da hankalin ka inshaAllah bazan bata ba fa"

"Ban baki labarin wanda suka shiga jirgin Abidjan ba a maimakon jirgin Abuja ko?"

Dariya tayi tana hadiye abincin ta. "Ka bani labari yafi a kirga. Na tabbatar maka cewa jirgin New York zan shigo ba jirgin wata kasar ba. Zan zo maka in one piece"

Ajiyar zuciya yayi. "Allah yasa. Kinyi sallah?"

"Eh"

"Abinci fa"

"Shi nake ci yanzu"

"To Alhamdulillah."

Hira sukayi tayi har sai da ya zo shiga nashi jirgin tukunna sukayi sallama.

Sako ta tura wa su Anti Mami da Yusrah cewar sun sauka lafiya suna jiran sauyin jirgi.

Bacci take so tayi a lokacin amma in ta tuno labarin da Mu'azzam ya bata sai ta wartsake. Idan ta bata a filin jirgin nan babu me ceton ta sai Allah. Don haka ware idon ta tayi duk bayan dan wasu lokuta tana duba allon sama taga ta wani gate za'a saka jirgin nasu.

Haka ta shafe kusan awa da rabi tukunna can daga baya taga ya bullo. Nan da nan ta tattara shirginta don gangarawa gate din da taga an saka a jiki.

Sai da ta isa wajen taga ashe sai an shiga jirgin kasa ma (tube) kafin a isa gate din.

Yau take ganin ikon Allah. Wani irin girma filin jirgin yake da shi to?

Bata gama ganin ikon Allah ba ma sai da ta shiga jirgin. Jirgin dai da aka kwaso su daga Najeriya bai kai wannan kyau ba ko kadan. Sai yanzu ne ma ta fahimci abun da ake nufi da Business Class.

Shigar dare sukayi wa birnin New York.

Tsawon lokaci suka shafe wajen jiran kayayyakin su kafin nan ta nufi inda yace su hadu.

Duk da na'urar dumama waje da ke ciki  filin jirgin hakan bai sai taji tsananin sanyin da ake a garin ba.

Sweater data riko tayi saurin sakawa tana cusa hannayenta a cikin aljihun ta amma ko kadan bata samu sauki ba. Rarraba idanu ta shiga yi ko zata hango shi amma bata ga ko mai kama da shi ba.

Laluba jakarta ta hau yi tana nemar wayarta don ta sake nemanshi.

Kamar daga sama taji wani dumi ya lullubeta. Kamshin turaren da ya ziyarci hancin ta ne yasa ta san shi dinne a bayan ta.

A hankali ya lulluba mata kwat din sa kafin na  ya juyo da ita tana fuskantar shi.

Bata san tayi kewar sa har haka ba sai da ta gan shi tsaye gaban ta ya cika mata ido da zuciyar ta da kyawun halittar sa. Yana sanye ne cikin uniform dinsa na aiki, hakan ya kara masa kwarjini da haiba. Zuciyar ta ta cika sumtum tana barazanar fashewa.

Wai wannan din nata ne? Mijin ta ne?

Murmushi mai taushi ya sakar mata kafin ya hada ta da kirjinsa.

"Welcome home Wifey"

Wani gwauron numfashi ta sauke tare da zagaye hannayenta a faffadan bayan sa. A lokaci guda kuma hawaye masu dumi suka gangaro zuwa kan kuncin ta.

"I've missed you. So much" ya fada murya kasa-kasa. Shima daurewa kawai yayi amma da ya zubar da ta sa kwallar.

Sun shafe kusan mintina uku a haka kafin nan ya dago ya sake sakar mata wani murmushin. Hannunsa daya yasa yana share mata hawaye dayan kuma yana kara riketa a jikin sa sosai.

"Kin gwammace kiyi kuka akan kice I missed you too ko?"

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi. Ko don wannan zolayar tasa ma ai dole tayi kewar sa.

Sarke hannayensu yayi a cikin na juna yana gyara mata zaman kwat din tasa a kafadar ta.

"Yaya hanya? Ina de baki sha wahala ba ko?"

Girgiza masa kai kawai tayi don harshen ta ya mata nauyi. Jin ta take kamar ba a duniya ba.

Murmushi ya sake yi mata kafin ya maida duban sa kan trolley din nata.

"Ana ta zumbura min baki ba'a so a zo shine kuma na ga an lodo kaya haka? Ashe dai ana so ake kaiwa kasuwa"

Ta kankance idanunta a kanshi.

Wannan kallon da take mishi yana daya daga cikin ababen da yayi kewa a tattare da ita.

Yayi dariya yana kamo hannunta, daya hannun nasa kuma ya sa ya fara tura trolley din.

Suna fitowa wajen motoci taga taxi kala-kala suna fake suna jiran fasinja. Yana daga hannunsa sai ga guda daya tazo inda suke ta ja ta faka. Direban ya fito ya loda kaya a bayan boot din sannan su biyun suka shiga baya. Ya sanar da direban inda zai kaisu sannan su ka fara tafiya.

Ko bayan sun shiga motar, bai cire hannunsa a cikin nata ba. Haka ya ringa bi da babbar yatsar sa yana tisa zanen lallen da aka mata.

Fareeha de shidewa ne kawai batayi ba a lokacin. Da ba dan hirar da yake jan ta da shi ba kam da bata san yaya zatayi ba.

Maimakon taga sun tsaya a wajen gidaje ko makamancin hakan sai taba direban ya kaisu hotel.

Kallon sa take da mamaki har yayi checking dinsu in.

"Ki dena kallo ma kamar na sato ki" ya rada mata a yayin da suka shiga elevator. "Ina so ki samu the full New York experience shiyasa na kawo ki nan. Amma in hakan be miki ba gobe sai mu koma gida"

Da sauri ta girgiza masa kai "A'a ni ban ce ba kawai de dama karin bayani na ke nema"

"To bayanin nawa ya gamsar da ke?"

Gyada masa kai tayi tana murmushi.

Fareeha bata san me ake cewa saukar aradu ba sai da taga ma'aikatan hotel din sun gama shigo da kayan su sun jawo kofa tukunna taji wani abu ya tsaga daga saman kanta zuwa tafin kafanta.

Duk da cewa dakin Suite ne ma'ana ciki da falo ne, hakan bai sa taga kankantar sa ba don gaba daya ji take iskar da ta ke shaka ita da shi ta musu kadan.

Mu'azzam ya lura da yanda gaba daya yanayin ta ya canza don babu abun da fuskarta take nunawa sai tsananin tashin hankali a lokacin.

Ajiye jakar sa yayi a kujera mafi kusa da shi yayi mata nuni da dakin yace
"Ki shiga mana, yaya kika tsaya anan?"

Wani abu mai nauyi ta hadiya kafin ta taka zuwa ciki. Tana jin shi yana bin ta a baya wanda hakan ya kara haddasa mata bugun zuciya.

Kofar da ta raba tsakanin falon da dakin ya jawo yana fadin "Ki kimtsa, ni zan dan fita. Akwai menu a kan dresser..." ya nuna mata shi "Idan akwai abun da kikeso sai ki fada min in saka a kawo miki"

Kai kawai ta gyada mishi. Jawo kofar yayi ya fice.

Wani gwauron numfashi ya sake a lokacin da ya shiga elevator din. Ya lura da yanda gaba daya ta takure ganin su biyu ne a dakin.

Har ga Allah bashi da niyyar yi mata komai. Hakan ne ma ya sa ya kama musu suite saboda niyyar shi ya kwana a falo. To amma yanzu yana tunanin ko ya kama wani dakin ne karami sai ita ta kwana anan din?

Kai ina.!! Matar sa ce fa. Ba zai bar ta ta kwana ita kadai ba a garin da bata da kowa sai shi.

Kasa ya sauka zuwa basement in da vending machines din otel din suke. Ruwa ya ciro da granola bars da dan chewing gum sannan ya zauna a wasu 'yan tebura da aka ajiye a wajen yana dan daddana wayarsa. Yana so ya koma amma sai ya tabbatar ta gama kimtsawa tukunna.

A fannin Fareeha kuwa jiki babu kwari ta bude akwatin ta ta fara neman jakar kayan wankanta da su towel da kayan barci. Ko tsaya wa yaba kyau da fasalin dakin bata yi ba ma. Ita dai Allah Allah take tayi wanka ta shirya kafin ya dawo.

Zata iya cewa bata taba yin wanka a minti biyu ba a rayuwar ta sai a ranar. Sauri sauri ta yi alwala ta wanke bakinta. A cikin bandakin ta shirya sannan ta zumbula babban hijabi akan kayan baccinta na riga da wando wanda a cikin kayan da Ammah ta shirgo mata su ta dauko.

Ko bayan ta fito da ta ga baya dakin ta ji wani sanyi a ranta.

Tana kan sake shirya akwatin nata sai ga shi ya shigo da sallama. A hankali ta amsa masa.

"Kinyi sallar ne?" Ya tambayeta bayan ya ajiye tarkacen daya shigo da su akan dresser.

"A'a bansan ina ne kibla ba"

Wayar sa ya ciro ya duba kafin ya ciro sallaya a bagpack din sa ya shimfida mata dai-dai kiblar.

Yana nan zaune har ta idar da sallar. Ya so ya shiga wanka shima don a gajiye yake amma baya son ya razana ta dayawa don haka ya jira.

"Kin duba menu din?"

Kwantar da kanta tayi a jikin gadon tace "A'a fa. Bana jin yunwa"

Murmushi ya sakar mata. "Duk jetlag dinne hala. Ko tea bazaki sha ba?"

Ta girgiza masa kai.

"Ruwa fa?"

Sake girgiza masa kai tayi. Idanunta har sun fara rufewa.

"To ki tashi ki kwanta ko"

"Uhum. Minti daya" ta fada tana kara rufe ido.

Shiriricewa yayi wajen kallon ta yana yin tasbihi wa ubangiji. A kullum idan ya kalleta sai yaga kamar kara kyau take yi. Yau kam ma yaga har wani shining take ga wani santsi da yaji fatarta take.

Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.

Shi kam yaji dadin sa.

Ganin bata da niyyar tashi yasa ya shiga bandakin shima ya dan watsa ruwa. Har ya fito ya shirya tana nan jingine da gado tana baccin gajiya.

Kashe wutar dakin yayi kafin nan ya rankwafo yasa hannu yana kokarin dagata.

Wani irin razana tayi hakan yasa tayi saurin mikewa tare da yin baya-baya har tana kokarin faduwa.

Da sauri ya riko hannunta yana fadin "Fareeha ni ne. Mu'azzam ne. Don't be scared"

Dukunkunewa tayi cikin hijabinta ta kauda kanta gefe. Har yanzu zuciyar ta bata dena lugude ba don wani mafarki tayi mummuna kuma bata ankara ba kawai taji mutum ya sunkume ta.

"Ki hau gado ki kwanta. Kiyi Addu'a kuma kinji? Sai da safe." Yana fadin haka ya jawo mata kofa ya koma kan doguwar kujera ya zauna yana maida numfashi.

Kansa ya sanya cikin hannayen sa.

Lallai akwai aiki a gaban sa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top