33.
Salaam guys! Ya mukaji da abun da ke faruwa a Gaza da ma duniyar baki daya? Allah ya kawo karshe abunnan da alkhairi and May Allah continue to keep the Muslim Ummah safe from oppressors. Ameen.
Bari mu leka gidan Ashraf da Wafiyya muga meke wakana.
33.
Karfe tara da rabi har da minti biyar agogon dake manne a jikin bango ya nuna.
Ashraf ya sauke ajiyar zuciya tare da mikewa ya shiga kitchen din. Ya ga alama Wafiyya bata da niyyar dawowa don haka ya shiga nema wa kansa abin da zai ci.
In da sabo yanzu kam har ya saba don tun da ta koma zuwa shagonsu yawanci sai ya dawo gida ya samu bata nan. Tun yana jiran ta ta dawo ta nema masa abinci har yazo yanzu yana dawowa yaga bata nan to zai nema wa kansa mafita.
Freezer ya bude ya lelleka ko zai ga sauran abincin da zai dumama. Couscous ya gani a cikin wata container wanda akayi shekaranjiya. Ya dauko ya saka a microwave sannan ya hau soya kwai.
Sai da ya kammala ya fito falo ya zauna tukunna yaji tsayuwar motar ta.
Yana jin shigowar su ita da kanwar ta Mumtaz, bai ce musu komai ba.
"Ina wuni Ya Ashraf?" Mumtaz din ta fada tana shigowa niki-niki da ledojin souvenir a hannunta.
A hankali ya dago ya kalleta tare da kakalo murmushi ya amsa da "Lafiya Mumtaz. Sannunku da dawowa"
Gyada kai tayi ta wuce dakin da tayi masauki.
Tsawon sati uku kenan yanzu da ta fara zama a gidan nashi tunda suka samu sabani da daya daga cikin matan babanta har aka kai ga yin dambe, shine da Baban ya tsawatar mata ita kuma taji haushi ta tattaro ta dawo gidan yayar ta.
Shi dai Ashraf ya je ya bawa mahaifin nasu hakuri kuma yace ya hakura, bai dai san dalilin daya sa har yanzun bata tattara kayan ta ta koma gidan su ba.
"Hayaat ka ganmu sai yanzu ko? Wallahi souvenirs muka tsaya rabawa a haka ma wasu ban samesu ba sai taho musu da shi nayi gobe na basu"
A karo na biyu Ashraf ya dago da kansa daga kan abincin sa ya fuskanci matar sa wanda ke tsaye a wajen kofa tana kokarin cire takalminta mai tsini.
Har yanzu makeup din ta yana nan daram a fuskarta kamar ba'a shafe awowi da yin sa ba. Jambakin nan radau akan lebbanta.
Bin shigar da ke jikin ta yayi da kallo.
Lokacin da suka rabu da safe doguwar Abaya ce a jikin ta. Yanzu kuwa wani hadadden leshi ne a jikinta ruwan goro wanda aka masa dinkin fitted gown. Yana tsammanin shine ankon bikin don irin sa ne a jikin Mumtaz.
Dinkin yayi mata kyau matuka gashi kalar leshin ya sake fito da hasken fatar ta.
A ranshi yake tunanin idan shi mijin ta ya shiririce haka wajen kallon ta, to maza nawa ne a yau suka samu damar yin haka?. Saurin kauda tunanin yayi a ranshi dalilin wata tafarfasa da yaji zuciyar sa ta fara yi.
Jinjina kai yayi kawai ya kurbe sauran juice dinshi dake cikin kofi kafin ya mike ya shiga kitchen din dan mayar da plate din sa.
"Hayaati ina ta maka magana ka share ni" Ya jiyo muryar ta a bayan shi. "Ko duk gajiyar office dinne?"
Girgiza mata kai yayi alamar yana bukatar ta kyaleshi.
Tun ba yau ba ta san cewa idan ran sa ya baci baya son ta cika shi da surutu, amma sam taki koya. Idan yaci gaba da tsayuwa a wajen zai iya furta abun da zai yi nadama don haka ya rabata ya fice a kitchen din. Yana isa dakin sa ya saka mukulli ya shige bandaki.
Sai da ya watsa ruwa ya saka kayan bacci tukunna yayi shaf'i da wutr. Yana idar wa kuwa aka dauke wuta. Cikin dan kankanin lokaci compound dinsu ya karade da karar generator kowa ya kunna na gidan sa.
Wafiyya taga shiru bai fito ya kunna musu Gen ba don haka ta nufi dakin don ganin me ya hana sa fitowa.
Jin kofar da mukulli yasa ta hau kwankwasawa.
Yana jin ta kamar ba zai bude ba, haka dai ya taso ya bude.
Hasken torchlight din wayar ta ne ya tallafa mata wajen ganin hade ran da yayi don haka ta dan shagwabe fuska tace "Naga an dauke wuta kuma shiru baka zo ka kunna mana Gen ba shi ne nazo naga ko lafiya?"
Dauke kan sa yayi a kan ta yana kokarin tura kofar yace "Lafiya. Bacci nake ji ne"
Hannun ta ta kai gefen fuskar sa ta ce "To Hayaat ka dan kunna mana mu kikkimtsa sai ka kashe. Minti talatin ma ya ishemu"
Janye fuskarsa yayi daga hannunta yana watsa mata wani kallo. "Ku haska da wayoyinku. Ni na gaji kwanciya zanyi" yana fadin haka ya juya ya bar ta tsaye a wajen da sakakken baki.
Har gobe bazata dena ganin sabbin abubuwa a tare da shi ba. Wasu su bata mamaki, wasu su kara sa mata son shi a cikin zuciyar ta, wasu kuma su bata haushi. Musamman ma dai wannan.
Ya ma za'a yi yace ba zai kunna musu generator ba? Kawai don an bata masa rai a wani wajen shi ne zaizo ya huce a kanta? Sai yau ne tayi da na sanin rashin iya kunna gen dinnan.
Kwafa tayi ta juya ta koma kitchen in da ta bar Mumtaz wacce ke kokarin tafasa musu indomie.
"Ya naji shiru?" Mumtaz din ta tambaya tana watsa sausage din da ta yanka a cikin tukunyar.
Wafiyya ta dan kakalo murmushi tace "Ashe wai babu mai a gen dinne. Kuma yanzu dare yayi balle yaje ya siyo. Watakil kafin mu gama ma a dawo da wutan"
Mumtaz dai gyada mata kai kawai tayi don bata gamsu da bayanin da ta yi mata ba. Ta lura tun da suka shigo Ashraf din yake wani cika yana batse wa shiyasa tun da ta gaishe shi ta shige daki abun ta.
Haka suka gama dafe-dafen nasu suka cinye sannan suka tattare kitchen din kafin kowa tayi dakin ta.
Yana jin ta tana ta kwaramniya a toilet duk wai don ya tashi, bata san ma shi idon shi biyu ba don yanda ran shi yake suya baya tunanin zai iya yin bacci ma.
Tsaf ta gama wankan ta shirya cikin rigar baccinta mai laushi. Tana kwanciya a kan gadon kuwa suka dawo da wuta, gaba daya dakin ya gauraye da hasken lantarki.
Juyowa tayi suka hada ido kafin ta juya masa baya ta rufawa kanta bargo.
"Wutan fa?" Ya tambayeta ganin bata da niyyar tashi.
"Ni bacci nake ji. In ta dame ka ka kashe mana" ta amsa ba tare da ta juyo ta kalle shi ba.
Shiru yayi na dan wasu lokuta don ita tana tunanin ma ko ya koma baccin ne, sai kawai taji ya tashi ya kashe wutan.
Tabe bakin ta tayi ta sake jan bargo. Ai da be tashi ya kashe ba yau sai de su kwana da wuta tangararan a kansu. Dan ma dai Mumtaz tana nan da yau a dakin ta zata kwana.
Washegari haka suka tashi kowa rai a jagule. Dayake weekend ne bayan Ashraf ya dawo daga masallaci sai ya koma ya kwanta don ya dan sake runtsawa.
Wajajen tara yaji kaman ana tashin shi.
Yana bude ido suka yi ido hudu da Wafiyya.
Tayi wankanta fes tana sanye da wani leshi yellow da fari an masa dinkin bubu me kyau. Dankwalin nan ya zauna a kanta kai kace inji ne ya daura mata shi. Fuskar ta fayau babu komai sai dan lip gloss dinta da yake sheki. Ga sarka ta gwal ta saka wanda ta dace da leshin.
"Dama zan ce maka zamu tafi ne" ta fada a sanyaye.
Tashi zaune yayi yana mutsutsuka ido. "Zaku tafi ina?"
Kallon sa take wani iri. "Gidan su Kwaise mana. Yau ne fa daurin aure Hayat"
Nan da nan ya daure fuska. "Ba inda zaki je" ya fada tare da mikewa ya shige bandaki.
Jin maganar tayi kaman saukar aradu a ka. Ba inda zata je?
Gefen gadon ta samu ta zauna yayin da wani ciwon kai ya bijiro mata lokaci guda.
Tsawon watannin nan da suka shafe tare daidai da rana daya bai taba hanata fita ba sai yau. Karin abun takaicin ma ya rasa ranar da zai mata haka sai ranar daurin auren aminiyarta.
To me ta mishi har haka da zai mata wannan hukunci mai tsanani? Ko a mafarki bata taba tunanin ze mata haka ba.
Fitowar shi a bandakin ne ya sa tayi saurin dago kanta daga kogin tunanin data fada.
"Hayati....."
Saurin katse ta yayi yana fadin "Meye abun karyawa?"
Jin shirun datayi ne yasa ya jiyo daga inda yake tsaye a gaban wardrobe yana neman kayan sakawa.
Ganin yanayin fuskar ta ya tabbatar masa da cewa bata yi abun karyawar da shi ba.
Jinjina kai ya maida hankalin sa wajen saka kaya.
"Hayati kayi hakuri dan Allah. Idan wani abun nayi maka ka yafe min amma kar ka hanani fita dan Allah." Hawaye har ya fara taruwa a kurmin idon ta.
Kankance idon shi yayi a kanta. "Damuwanki kenan a yanzu Wafiyya? Your biggest worry a halin yanzu shi ne ki tafi bikin kawarki ba tare da kin tsaya kin ji ko akwai abun da nake bukata ba? Ba ki ma damu kiji dalilin fushi na ba, har kina da karfin gwiwan shiryawa ki sake wani fitan."
Hawayen da take ta kokarin boyewa suka wanke mata fuska.
"Yanzu meye na kuka?" Ya tambaya yana harde hannayen sa a gaban kirjinsa.
Cikin sheshsheka ta ke cewa "Kayi hakuri bansan fitan danayi zai bata maka rai ba. Naga dai tun saura wata uku bikinnan nake ta maka tuni...."
Daga kansa sama yayi wani haushin ta yana kara mamaye shi.
"Wafiyya are you dumb? Duk zancen nan danake hankalinki yana kan bikinnan har yanzu wato. Bakima gane me nake nufi ba ko?"
Share hawayen ta tayi tana girgiza masa kai. "To menene nayi maka da kake min haka? Wallahi Kwaise baza ta ji dadi ba idan ban je ba. Kaga Lagos za'a kaita, ban san ranar da zamu sake haduwa ba"
Tsaki ya ja yana nufar kofar fita a dakin. "Idan Kwaise taga dama ta ce a fasa daura mata aure tunda bazaki je ba. Karshen rashin jin dadi kenan. In the meantime, ki zauna kiyi tunanin lefin ki kafin na dawo"
Yana fadin haka ya rufo kofar dakin da karfin gaske. Mumtaz da ke falo tun dazu tana jiran Yayar tata sai da ta tsorata ganin shi. Kafin ta bude baki ta gaishe shi ma har ya fita a gidan.
Wafiyya ce ta fito tana kuka tace mata ta tafi kawai zata biyo ta daga baya kuma ta bawa Kwaise hakuri.
Mumtaz na tambayarta meya faru ta juya ta koma daki ba tare da ta bata amsa ba. Fadawa tayi kan gado ta fashe da wani sabon kukan. Sai da ta sha kukan ta mai isar ta sannan ta tashi ta sake yin wanka.
Tana fitowa taji wayar ta tana kara. Ko ba'a fada mata ba tasan Kwaise ce ke kira. Kashe wayar tayi gaba daya ta cilla ta kan gado.
Shiryawa tayi cikin kaya masu sauki sannan ta hau gyare gidan.
Har sha biyu babu Ashraf babu labarin shi. Tasan ko ta kira shi ma ba amsawa zaiyi ba don haka ta shiga kitchen ta fara shirin yin abincin rana.
Sai wajen biyu da rabi ya dawo.
Tana kwance a dakin Mumtaz bata leko ba don har a lokacin haushin sa take ji.
Wanka ya sake yi tukunna ya fito falon ya zauna.
"Wafiyya"
Sai da ya kira ta sau uku tukunna ta fito ba tare da ta amsa ba. Ganin ta tsaya a kofar dakin ba ta ce masa komai ba yace "Zo ki zauna magana zamuyi"
Samun waje tayi ta zauna a gefen shi.
Hannunta ya riko cikin nasa. "I'm sorry" ya furta a hankali. "I'm sorry I called you dumb"
Ai kaman jira take ya furta hakan, nan ta fashe masa da kuka.
Barin ta yayi ta yi mai isar ta tukunna ya cigaba da magana. "Tsawon lokacin nan dana fita, kinyi tunanin da nace kiyi?"
Gyada masa kai tayi tana share hawaye ta.
"And?..."
"Saboda ban dawo da wuri bane shine kake fushi?"
Tsayawa yayi yana kallon ta don yanzu kam dariya ta ke kokarin saka shi.
"Ko ba haka bane?"
Dan siririn murmushi yayi kafin nan ya gyada kansa. "Yana daya daga cikin dalilan daya sa nake fushi. Amma babban abun shi ne yanda bayan kin dawo din baki ma nuna cewa kinyi kuskure ba. And also shigar da kikayi zuwa wajen bikin ya kara bata mun rai. A matsayin ki ta matar aure bai cancanci ki rinka saka kaya irin wannan ba. Hakan kuma bai ishe ki ba still, yau da safe kuma ina nuna miki bacin raina amma ke hankalin ki sam baya ma kaina, yana kan bikin kawar ki. Duk se naji baki ma dauke ni da aurenmu da muhimmanci ba. Shi yasa na fusata sosai"
Runtse idon ta tayi kafin ta bude su a kan fuskarsa. Nan ta marairaice fuska ta shiga bashi hakuri.
Ita sam bata san girman laifin ta ya kai har haka ba don gaba daya idon ta ya rufe. Tabbas a jiyan kam bata shi ta ke ba, ta Kwaisen ta take. Don yadda ta mata hidima a bikin ta, haka ita ma ta yi alkawarin zatayi a nata don tsabar hidimar da Kwaisen tayi sai da Ashraf ya kira ta musamman bayan bikin nasu ya mata bangajiya. Dalilin ma da yasa ya barta ta je bikin kenan.
A rashin sanin ta kuwa, a kokarin faranta wa kawarta ta je ta bakanta wa mijinta.
Cikin lokaci kalilan sai gasu sun zauna suna cin abinci a kwano daya. Mata da miji kenan, sai Allah..
******
Short Chapter, ayi hakuri please.
Vote vote vote and comment.
Taku a kullum,
Miryamah
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top