32.
This chapter is so far my favorite. Jama'a I love loooovvvveeee. Allah ya bar mana love🥰🥰🥰.
32.
"Wannan fa a ina za'a saka?" Yusrah ta tambaya hannunta rike da wani agogo me kyau. Dukkansu suka daga ido suka kalli agogon da ke manne a bangon falon sannan suka sake kallon na hannun nata. Dukka biyun sunyi kyau kuma sun cancanci a saka su a parlor din.
Anty Zu ta kalli Fareeha sannan tace "Ko a sa miki shi a daki?"
Fareeha ta danyi guntun murmushi wanda ke cike da gajiya ta ce "Ko a ina ma aka saka Anti ba matsala"
Yusrah ta tabe baki "Se da mukace ki zauna ai kar ki taho, gashi yanzu kinzo kina ta wani mashangwale"
Aunty Zu ta kalleta ta gefen ido. "Oh ni Zuwaira. Ke kam bakin ki baya taba shiru ko?"
Yusrah bata bada amsa ba ta wuce da agogon daya daga cikin dakunan da suka gama shiryawa don ta kafa shi. Idan ba don kayan sunyi yawa ba ma yaushe ake wani kafa agogo a daki?
Kaya ne gasu nan an rasa yanda za'a yi da su; Bappah Dattijo ya siya Baba Zubairu ya siya ga oga kwata-kwata Mu'azzam shima ya siyo su.
A jiya aka bashi mukullan gidan wanda daya daga cikin gidajen Prof ne ya bashi aro don ya kasa samun irin gidan daya ke so. A jiyan kuma ya tattaro masu gyaran wuta da na famfo aka canja mishi wutace da socket din gidan da kuma kan famfuna da su sink da shadda ma duk sake su akayi. Har karfe sha daya yana tsaye akan kafafun shi yana jiran masu fenti su gama nasu aikin.
Abincin daren da yake yawan zuwa ci a gidan Ammah ma jiya be samu yaje ba se hotel dinshi ya koma ya sha tea da cookies ya kwanta.
Yau kuwa suna iso wa gidan da safe suka same shi shima ya riga da yazo da akori kura an dora mata kayan wuta dangin su firij da talabijin da freezer da injin wanki.
Haka Fareeha ta tsaya tana kallon su suna ta sauke kaya. Ba'a gama wannan ba kuma sai ga Anti Bebi ita ma ta iso da mota shake da kayan katako wanda kana gani kasan showroom kawai ta shiga ta zabo su.
Aiki suka shiga yi babu kakkautawa don a ranar Mu'azzam yace yake so ta tare.
Tun safe suke ta aiki gashi yanzu har an fara kiraye-kirayen sallar Maghreb. Gajiya iya gajiya sun gama yi amma Alhamdulillah sun ci karfin aikin kuma komai yayi daidai. Abubuwan da ba'a karasa ba kadan ne kuma ko gobe ma zasu iya karasawa.
Alwala Fareeha ta shiga tayi kafin ta fito ta kabbara sallah. Tun kafin ta idar ta ji shigowar shi yana yi wa su Anti Zu sannu da aiki.
Tana idar wa kuwa sai gashi ya shigo.
"Sannu da dawowa" ta furta a hankali bayan ta kammala azkar dinta na bayan sallah.
Dagowa yayi daga kallon da yake wa wayar sa ya kalleta. Kankance idon sa da yayi a kanta yasa hantar cikin ta kadawa. Rabon da yayi mata wannan kallon tun ranar da suka fara haduwa taki karban kyautar daya bata.
Kafin ta bude baki ya mike yana fadin "In kin gama kizo"
Ta saba idan tayi farilla tana tashi ta kara da Nafila, yau kam tashi tayi ta nade sallayar sannan ta bi bayan shi.
Ta zaci a falo ze tsaya kawai sai taga ya kama hanyar waje.
Nan da nan zuciyar ta ta sauya bugu.
Anti Balaraba data idar da sallah a falon dauke ido tayi kaman bata gansu ba har suka fice.
Sai da ya isa wajen mota tukunna ya bude kofar fasinja. Ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace "Shiga"
Wani abu ta hadiye a wuyan ta kafin ta shiga motar ya turo kofar ya rufe.
Har ya zagayo ya shiga mazaunin direban zuciyar ta bata dena lugude ba.
"Ya mukayi dake?"
A hankali ta dago ido ta kalleshi. Ya hade gira fuskar sa babu alamar wasa. Kallon daya ke mata har yafi na dazu tayar mata da hankali.
Kwakwalwar ta ne ta fara tariyo mata abubuwan da Anti Mami ta ringa karanta mata. Yaya ma ake lallashin miji?
"Kayi ha....."
Saurin daga mata hannu yayi yana dakatar da ita.
"Ki bani amsa. Yaya mukayi dake?"
"Kace idan na gama ganin gidan na koma gidan Ammah na jira ka" ta fada murya kasa-kasa.
"Shi ne na zo na sameki hadda ke ake buga ķusa, a sauke wannan a dora wancan ko?"
Ai ita ta zaci dazu da ya kawo musu abincin rana be lura da ita ba lokacin da suke ta faman kwale-kwale a kitchen ita da Yusrah. Ashe ya ganta.
"Wa ya aike ki ma in the first place? Kin taba ganin amaryar da aka je jeren ta da ita?"
Tsuru-tsuru tayi kaman barawo a tsakiyar mata.
Tasan tayi laifi na kin bin umurnin sa, amma bata ga laifin ta ba don tazo ta taya su jere.
Idan aka cire Anty Zu, duk sauran sai da ta sansu tukunna ma ta san da zamansa a duniya. Sai da suka zama 'yan uwa a gare ta tukunna suka zama sirikan ta, don haka bata ga dalilin daya sa zata zauna a gida ba suzo suna tikar aiki ba tare da tazo ta taya su ba.
Lokacin da ake ta aikin ma ita ji tayi kaman ba na gidan ta bane don zagewa sukayi suna ta hira a tsakaninsu. Har mantawa ma tayi cewa wai ita ce amaryar.
Amma da ta tsaya a gidan Ammah ai wuni zatayi a daki tana boyon Ammah don ita kam har yanzu nauyin ta take ji.
Gwamma da ta zo nan aka yi aikin da ita kuma ta dan sarara ita ma.
Bata fito ta fada masa duk wannan ba, hasali ma kara shagwabe fuskar ta tayi don karatun Anti Mami ya fara dawo mata.
Tattaro nutsuwar ta tayi da dan sauran karfin halin da ya rage mata ta fara magana cikin sanyin murya kamar me shirin yin kuka.
"Dan Allah kayi hakuri, wallahi ban dauka ran ka ze baci ba akan haka. Nayi kuskure na karbi laifi na, kamin duk wani hukuncin da zaka min amma dan Allah ka saki ranka. Wannan fade-faden sam be dace da mijina ba"
Sake baki yayi ya tsaya yana kallonta.
Lallai ma yarinyar nan. Me take kokarin yi haka?
Bai gama shan mamakin ta ba se ji yayi ta cigaba da cewa. "Ni dai mijina ba haka yake ba. Yana da fara'a da dariya da son tsokana, baya fada. Ka dawo min da abuna dan wannan kam bansan waye bane"
Dariya ce ta kusa kubce masa amma yayi sauri gintse.
Dauke idon sa yayi daga kanta yana kunna motar.
A hankali tace "Ka hakura?" don taga alamar kamar ta fara yin nasara a kansa.
"Yimin shiru" ya fada da wani miskilin murmushi akan labbansa, idon sa akan gate din gidan da me gadin ke kokarin budewa.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin ya saki ran nasa kamar yanda ta bukata. Har ta koma ta zauna da kyau a cikin kujerar sai kuma wani karatu ya sake fado mata.
Hannunsa da ke kan console ta jawo tana sarke yatsun sa cikin nata. Ba shi kadai ba, ita kanta sai da tayi mamakin aikata hakan da ta yi.
"Nagode Mine" ta furta a hankali.
Juyowa yayi da sauri ya kalleta na 'yan wasu dakikai, kafin wani murmushi ya bayyana a fuskar shi.
Yarinyar nan so take ta kashe shi, don a halin yanzu ya ma manta dalilin fadan dayake tayi dazun.
Cigaba da tukin yayi, jefi-jefi ya kan juya ya kalleta ko kuma ya sake dumtse hannayen nasu.
A kofar wani wajen cin abinci yayi parking kafin ya juyo ya kalleta.
"Me zaki ci?"
Sai a lokacin ma ta tuno rabon ta da abinci tun da safe. Abincin da ya kawo da rana daga gidan Ammah ko ta kanshi bata bi ba.
Lumshe ido tayi kafin ta sake bude su a kan shi.
"Duk abun da aka samu."
Girgiza mata kai yayi. "Tell me what you want"
Shiru tayi na dan wani lokaci kafin tace "To abu me sauki dai haka ko snacks. Don banjin zan iya cin abinci me nauyi na gaji"
Cire hannun sa yayi cikin nata yana watso mata harara. "Ko waye ya jawo gajiyar oho"
Dariya take yi kasa-kasa har ya fita a motar.
Sai bayan ya shige ciki ta lura cewa ma bata fito da wayar ta ba. Tasan yanzu Yusrah tana nan tana ta zabga mita. Idan ta koma kuwa zata sha tsokana.
Be jima ba se gashi ya dawo da ledoji baja-baja. Yana shigowa kamshi ya cika mata hanci.
Sai da ya zauna da kyau kafin ya fara bubbude robobin takeway din. Soyayyan dankali ne a cikin daya sai chicken nuggets, spring rolls da samosa a sauran. Daya ledar kuma ruwa ne da lemo mai sanyi.
Dankalin ya miko mata bayan ya saka mata nuggets din a gefe. Karba tayi hade da mishi godiya ta fara ci.
Yana kokarin bude mata ketchup din da ke cikin ledarsa ya juyo yaga har ta kusa cinye rabi.
"Yaushe rabon ki da abinci?"
Hadiye abincin bakin ta tayi sannan tace "In de fada zaka mun to bazan fada maka ba"
Girgiza kai kawai yayi yana dariya. "Allah ya shiryeki Faree"
"Ameen"
Haka suka ci abincin a mota suna hira har suka kammala. Komawa yayi ya karbo mata ice cream; dama yayi oda gudun kar ya narke da wuri ne yasa be karbo dazun ba.
"Ina naka?" Ta tambaya bayan taga ya tada motar yana kokarin yin ribas.
"Ni ban siya ba. Se de in za'a sammin"
Kallon sa tayi ta gefen ido tana jin yanda sanyin madarar ke gangarawa cikin makogoranta. Idan ma da wasa ya fada to ya shirya shan mamakin ta yau.
Ganin spoon din da yayi daidai bakin sa ya saka shi dauke idon shi akan tukin da yake ya mayar da kallon sa gare ta.
Da taga ya ki bude bakin nasa sai tayi yunkurin janye hannunta. Da sauri ya dakatar da ita tare da shanye ice cream din da ke cikin spoon din.
Haka ta cigaba da bashi sai da yace ya isa tukunna.
"Yau me ya same ki ne kam?"
Cigaba da shan ice cream din ta take. "Me ka gani?"
"Naga yau ko dan tsiwar nan ma ba'a min ba. Infact naga har wani lovey dovey ake ta min"
Dariya tayi kafin tace "Wai duk de rarrashin ka nake ta yi fa."
Ya jinjina kai. "No wonder. Naji har wani sabon suna aka saka min"
Sunkuyar da kai tayi tana murmushi. Ita duk se yanzu ma take jin kunyar abun da ta tafka.
Ta dade da saka mishi wannan sunan a zuciyar ta kawai furta wa ne bata yi ba, sai a yau ta samu kwarin gwiwar yin hakan.
Hannunsa me dumi ya sanya cikin nata me sanyi kafin ya kai hannun bakin sa ya manna mishi sassanyar sumba. "I love it" ya furta a hankali.
Zuciyar ta ce taji ta cika tam da farin ciki.
Bata iya ce mishi komai ba har ya maida su gida.
Har ta ja mabudin kofar da niyyar fita kawai taji kofar taki buduwa, juyo wa tayi ta kalleshi don neman karin bayani.
Yanayin data ga fuskar sa ya sa ta jin wani abu ya dira a zuciyar ta.
A hankali ya juyo gaba daya ya zuba mata kyawawan idanun sa masu kunce mata lissafi.
"Faree" ya kira ta a sanyaye.
Kasa amsa mishi tayi kawai ta tsaya tana kallon shi.
Hannayenta biyu ya riko ya damke su cikin nasa.
"I'm sorry I couldn't give you a proper wedding and a proper home"
Kallon sa take kaman ya sha wani abu. Saura kiris ma ta fashe da dariya don a ganinta kwata-kwata be san me yake fada ba.
"And I'm sorry zan tafi na barki ba tare da na bamu chance din gina sabuwar rayuwar mu ba. Ki gafarce ni"
Girgiza kan ta ta shiga yi a take kuma wasu hawaye suka wanke mata fuska.
"Ka dena cewa haka dan Allah." Ta kara kankame hannayen nasu. "Ka sani cewa bayan Iyayena kaine mutumin daya gama mun komai a rayuwa. Ka so ni a lokacin da nake ga ni ba abar so bace. Hakan bai ishe ka ba, ka kasa zaune ka kasa tsaye, sai da ka lullube ni ka martaba ni ka maida ni matar ka. Idan nace baka gama mun komai ba a rayuwa nayi maka butulci."
Dagowa tayi tana sanya jajayen idanunta a cikin nashi wanda suma suna dab da zubar da hawayen.
"Gidannan da duk abun da yake cikin shi basu dame ni ba. Kai ne a gaba na. Kai ne komai na. You're my proper wedding and my proper home."
Hada ta yayi da kirjin shi yana jin kamar zuciyar shi zata fito waje saboda wani zaburar data ke yi a dalilin yarinyar nan.
Ya ilaaahi!. Tabbas she will be the death of him.
Sake fashe mishi tayi da kuka tana kara kankame shi.
Rarrashin ta ya shiga yi duk da shi ma a lokacin yana bukatar me rarrashin sa idan ya tuna cewa gobe ze tafi ya barta.
Daidai kunnenta ya ke fadin "Idan bakiyi shiru ba zan ciji bakin kukan"
Ba se ya sake fada ba ai, nan da nan ta bar jikin shi ta koma ta zauna tana share hawayenta da gefen hijabin ta. Bata fasa ba kuwa sai da ta dan watso masa harara saboda dariyar dayake mata.
Mika hannunsa yayi ya tayata share hawayen. "Allah nagode maka da ka bani mata me tsiwa"
Turo bakin ta tayi tana fadin "To ba kai bane kake sani nake tsi....."
Numfashin ta ne taji yana barazanar daukewa jin abun da yake wakana. Yau ta shiga ukun ta menene haka?
Mu'azzam kuwa sai da ya aiwatar da abun da ya dade yana niyyar yi har ma da kari kafin ya saki fuskar ta yana hada goshin su waje guda.
Yadda take maida numfashi shima haka yake mayarwa.
"What were you saying?" Ya fada yana mata wannan murmushin gefen leben nasa.
Saurin ture shi tayi tana rufe fuskarta da hijabin ta.
"Uncle Captain Dan Allah ka bari"
"Lallai yarinyar nan so kike na sake ko? Ina aka kai sabon sunan nawa?"
Ai nan da nan ta shiga magiya. Haba wa me Mu'azzam zeyi in banda dariya.
Zuciyar shi cike da farin ciki. A lokacin sai yaji dama su dawwama a haka.
Sai da yayi me isar sa tukunna ya maida nutsuwar sa kan ta.
"Faree gobe fa zan tafi" ya fada cikin wani yanayin da ya sa taji kaman ta sake fashewa da kuka.
Lokacin da ya fada dazun ma ta jishi, kawai bata so ta saka abun a ranta ne a lokacin. Bata so tunanin rabuwar su ya bata wannan yanayin da suke ciki na farin ciki.
"Karfe nawa ne tafiyan?" Ta tsinci kan ta da tambaya.
"Karfe bakwai jirginmu zai tashi zuwa Abuja. Amma tafiyar jibi ne da safe inshaAllah"
Sauke numfashi tayi tana daidaita zuciyar ta.
"Allah ya kaimu. Allah ya kaika lafiya ya kuma bada sa'ar abun da aka je nema"
Dauke idon shi yayi akan ta don yanda zuciyarshi ta cunkushe waje guda. "Ameeen Fareeha ta." Bude lock din motar yayi. "Dare yana kara yi. Muje in rakaki"
Kafin ma tayi yunkurin fitowa a motar har ya zagayo ya bude mata. Haka suka jera har kofar falon.
Kaman wasu marasa gaskiya suka shiga falon sadaf-sadaf.
Yusrah dake kwance a kan carpet tana daddana wayarta ta dago tana kallon su da murmushi a fuskar ta.
"Ai har ina shirin kiran Mama in ce a zo a daukemu don masu gidan ma sun gudu sun bar mana gidan, sai ga ku."
Zama Muazzam yayi akan hannun kujerar da tafi kusa da shi yace "Kiyi hakuri dai ki karasa ladan ki Mamana."
Tashi tayi tana gyara zaman mayafin ta tace "Ni karka min wani wayo. Ana koma wa makaranta gidan mu zan koma"
A ranshi Muzzam yace shima da ba dan makarantar ba da gobe da matar sa zai tafi abin sa.
Haka ya shiga bata hakuri tana dariya ta shige ciki abin ta.
"Sai da safe?"
Dago wa yayi ya kalli Fareehar wacce ke tsaye tun shigowar su.
Sai da ya kare mata kallo tsaf yana adana fuskarta a cikin zuciyar shi kafin ya mike yana mata murmushi ya iso dab da ita yace "I had a great time today. Nagode"
Kallon shi take ita ma tana murmushi.
Lallai ma Uncle Captain dinnan. Ai ita ce ma yakamata tace ta gode bayan duk wannan hidimar da ya gama yi akanta.
"Ni ce de da godiya Mine. Hidima akan hidima na ma rasa wace godiyar zan maka specifically. Allah ya saka da alkhairi ya kara budi"
Shiriricewa yayi wajen kallon ta.
"Sake fada naji"
Sarai ta gano shi don haka ta jefa mishi wani kallo.
"Duk surutun nan dana yi abun da kaji kawai kenan?"
Daga mata gira yayi alamar eh.
Juya idon ta tayi alamar kosawa da tsokanar ta shi.
"Mine" ta maimaitawa kamar yanda ya bukata.
Sunkuyowa yayi ya sumbaci goshin ta wanda hakan ya haddasa mata mutuwar kwakwalwa. Daidai kunnenta ya furta "Yours" kafin yaja da baya yana aika mata wasu sakonni da idanun shi.
Har ya ja kofar ya fita a falon bata matsa daga inda take tsaye ba.
"Yau kwanan tsaye zamuyi ne?" muryar Yusrah ta jiyo a bayanta.
Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi. "Yusrah dan Allah ki kyaleni na yau de kam, na gaji wallahi"
Dariya Yusrah ta shiga yi. "Oh wai su Adda ne ake love da Uncle Captain. Uncle Captain de da ake gaisawa da shi. Gashi yana kokarin saki kwanan tsaye"
Bin ta tayi zata dake ta ita kuwa ta saka gudu sai daki. Ihun su ne ya tashi Anty Zu daga bacci nan kuwa ta shiga surfa musu fada. Sumui-sumui Fareeha ta wuce daki don tayi shirin bacci inda ta bar Yusrah da Anty Zu wacce har a lokacin bata dena fadan ba.
Washegari wajajen karfe bakwai sai ga matar Prof ta zo musu da abin kari. Dama jiya da yamma data taso daga aiki ta tsaya sun gaisa har da guzurin drinks din ta. To yanzu kuma se gashi ta kawo musu abin karin kumallo.
A tsatsaye suka gaisa don tana sauri zata wuce office.
Sai da suka karasa sauran ayyukan da ba'a gama ba jiya sannan sukayi wanka suka zauna suka karya.
Suna gamawa kuwa Yusrah ta fara shirin zuwa gida don zata dauko wasu kayan nata. Mu'azzam ya sanar mata cewa ranar litinin zata yi wa Fareeha rakiya zuwa Bauchi domin ayi mata passport. Ya so ayi mata a Kanon amma kuma Baba Zubairu yace akwai wanda ya sani anan immigration office na Bauchi wanda ze musu shi cikin sauri.
Kafin goma tayi ma har ta fice a gidan ya saura daga Fareeha sai Anty Zu wacce ta koma bacci don kusan tafi kowa aikatuwa a jiya.
Falo ta dawo ta dan kunna TV ko ze rage mata shirun da take ji. Wayar ta ta dauko don ta kira Umma ta bata labarin tarewarta. A jiya sunyi waya akan cewa an samu gida har ma ta mata addu'ar sanya alheri. To tun sannan basu sake magana ba.
Tana kokarin kira kawai sai ga wayar Umman ta shigo.
Da fara'a a fuskar ta ta amsa kawai se taji Umman ta hau masifa.
"Yanzu Adda Fisabilillahi abin da kikayi yayi daidai kenan? Haka akeyi?"
Ai nan da nan ta gyara zama ta fara zare ido. Yau ta banin ta. Me tayi kuma?
"Umma me ya faru?"
"Zan saba miki yanzunnan. Ace mai gidanki zezo shi ne bazaki kira ni ki fada min ba in shirya, kin barni se kame-kame nake a gidan nan na rasa me zan bashi gashi yara duk sun tafi makaranta ma balle na aika a siyo min wani abun. Baki kyauta min ba wallahi ko kadan"
Bata ma da bakin da zata fara ce mata ita kanta bata san da zuwan nasa ba dan haka ta shiga aikin bada hak'uri.
Umma dai tabe baki tayi ta kashe wayar ta tacigaba da dama kunun gyadar ta. Wayar Fareehar ce ta sake shigowa. Katse wa tayi hade da kashe wayar ma gaba daya. Ranta ya riga yagama baci yanzu kuma se ta sakko kafin ta iya amsa wayar ta.
Tagumi Fareeha ta zabga jin Umma ta kashe wayar gaba daya.
Amma lallai sai a gaida Unce Captain. Bata san hawa ba bata san sauka ba yaje ya janyo mata masifa.Yo ita data san ze je ma ai da ta makale masa sun tafi tare.
Tsabar abu irin nasa ma ace tsawon lokacin da suke shafe tare a daren jiya ya kasa sanar mata cewa yau da safe zai je Azare, sai kawai ta ji shi a can.
Tsaki taja tana kashe TV din.
Ita ba'aje da ita ba, gashi ya je ya jangwamo mata fadan Umma. Wannan abu goma da ashirin haka.
Wunin ranar haka tayi shi kaf rai ba dadi. Ko da ya kira ta ma daga baya bata nuna masa cewa ta san yaje ba, shi ma kuma be fada ba.
Bayan la'asar kuwa sai gasu nan shi da Aaliy Mastoor da wata kanwar shi Umaimah. A falo suka baje suna ta hirar su da Anty Zu.
Fareeha kam tun da ta kawo musu ruwa suka gaisa da Aaliy da Umaimah sai ta koma gefe tayi shiru tana danna wayar ta. Tana sane sarai da idon sa a kanta taki dagowa ta kalleshi.
Can dai taji Aaliy ya ce "Yakamata fa mu kama hanya kar kayi missing flight din ka"
Anty Zu ce ta juyo ta kalleta. "Ki je ki shirya sai ku je ko?"
Mikewa tayi ta shige daki. Ita da tayi niyyar ma kar tayi masa rakiya kawai de rashin sanin yaushe zasu sake haduwa ne yasa ta dan sassauto. Har dan gift ta hada mishi amma yanzu ta ma fasa bayar wa.
Tana tsaye a gaban wardrobe dinta tana tunanin ta canja kaya ne ko kuma ta daura Abaya akan na jikin nata, sai kawai ta ji shi a bayanta. Nan da nan kuwa turaren shi ya gauraye ko ina.
Kan shi ya kwantar akan kafadar ta yana rada mata "I'm sorry".
Duk wata hanyar narke mata zuciya ya sani, amma hakan be sa ta yasar da makaman yakin ta ba.
Sai da ta tattaro duka nustuwar ta kafin nan tace "Wani abun ne ya faru?"
Juyo da ita yayi suna fuskantar juna.
"Idan nace miki ni kaina bansan zanyi tafiyar ba se yau da safe zaki yadda?"
Shiru tayi tana cigaba da kallon sa.
"Nima kawai tashi nayi naji yakamata ace kafin na tafi naje nayi wa Umma da Abba godiya da suka gwangwaje ni da kyakyawar mata mai bala'in sona mai kuma sakani farin ciki da annashuwa"
Tun kafin ya karasa ma ta fara jefo mishi harara.
Hada ta yayi da kirjin sa yana dariya yace "Kin zaci ke kadai kika iya zakin baki ne?"
Dariyar ita ma take yi ganin ya rama abin da ta mishi jiya ne.
Dago wa tayi tana kallon shi tace "Amma de ko da text ne da ka min ka fada min. Baka ga fadan da Umma ta rinka sirfa min ba wai ban sanar mata ba gashi surukin ta yazo ta rasa abin da zata bashi. Ina zaman zamana ka jawo min fushin Umma"
Rike fuskarta yayi cikin tafukan hannun sa. "Kiyi hakuri Faree na sha'afa ne wallahi. Da nasan hakan zata faru da na baki heads up. Ki bar Umma kuma ni da kaina zan bata hakuri zata sassauto inshaAllah"
"In bata sassauto ba ma kaikam kayi mata nisa ai. Ni ne zan kwana a ciki"
Sumbatar kumatun ta yayi. "Dan Allah ki huce Faree bana so mu rabu haka kina jin haushina".
Yadda yayi maganar ya bata tausayi hakan yasa ta zagaye hannayenta ta bayansa ta kwantar da kanta a kan kirjinsa.
"Ni ba haushin ka nake ji ba. Kawai dai raina ya dan sosu ne dama. Amma yanzu komai ya wuce"
Sake rike ta yayi shima yana haddace bugun zuciyar ta a kwanyar sa.
Sun dade a haka kafin ya saketa don ya bata dama ta shirya.
Yana tsaye a wajen ta zaro Abayar ta baķa wanda duk a cikin siyayyar da yayi mata ne a 'yan kwanakin nan ta saka ta. Hoda ta dan murza da lip gloss kafin nan ta nade mayafin a kanta.
Da murmushi a fuskar sa yake kallon ta har ta gama. In ban da jarabawa irin ta ubangiji bai ga dalilin da zai sa ya sa kafa ya tafi ya barta ba amma babu yadda ya iya.
Kama hannunta yayi suka fita a dakin.
Har sun isa falon kawai taji kamar bata kyauta ba. Don haka tace ya jira ta tana zuwa. Koma wa dakin tayi ta bar shi a tsaye a wajen. Su Aaliy kam har sun fita ma su kawai suke jira.
Dawowa tayi da wata 'yar gift bag a hannun ta. Sako ne Sajida ta aiko mata a ciki kwanaki kuma jakar ta mata kyau sosai shine tayi ta ajiyar ta har Allah ya kawo ranar da itama zata bayar da ita.
Mika masa tayi kanta a kasa tace "Ga wannan ba yawa. Ban samu time na shirya da kyau ba"
Tsayawa yayi yana kallon ta da mamaki. A lokaci guda kuma sai ya tuno a wasu 'yan watannin baya shima haka ya tsaya a gabanta a ranar daya fara ganinta ya mika mata tasa kyautar.
Sai gashi yanzu itama tana masa. Shin ita ma a lokacin ta ji abin da yake ji yanzu?
Da ita da kyautar gaba daya ya hada waje guda ya rungumesu.
"Faree idan kika cigaba da melting heart dina haka zaki karya min zuciya. I won't be able to leave"
Wasu hawaye ne suka taru a idon ta wanda na zallan farin ciki ne.
"In aka koreka a aiki babu ruwan diyar Malam Abubakar"
Dago wa yayi yana lakace mata hanci "Da ruwanki ma har da tsakin ki"
Dariya tayi ta juya don ta nufi kofa taji ya dakatar da ita.
"I didn't get you anything" ya fada hade da tattare girar sa.
Ji tayi kaman ta rike kafadun shi ta jijjiga shi don ya dawo hayyacin sa. Shin ko ya manta da kudaden da ya barar a 'yan kwanakin nan ne da ya ke cewa be bata komai ba? Da ya duba gift bag din ma yaga abun da ke ciki watakil ya mata dariya.
"Hidimar da kayi akaina a 'yan kwanakin nan ma sun isa Mine. It's enough"
Girgiza mata kai yayi. "Wancan daban. Wannan daban.".
Ta bude baki zatayi masa musu suka ji horn din Aaliy.
Anty Zu ta leko tace "Zaku makara fa. Abun da tare zaku tafi ba se ku karasa zancen a hanya ba?"
Haka sukayi sauri suka shige motar. Ita da shi a baya, Aaliy da Umaimah a gaba.
Har suka isa airport din yana ta tunanin me ze bata. Har tambayanta yayi ko akwai wani abun da take so tace mishi ita kam babu komai.
Sai da taga ya damu ya damu tukunna tace to ya bata turaren sa.
"Turare na dai?"
Ta gyada masa kai "A wajen ka kawai na taba jin kamshin sa."
Haka ya kwantar da akwati a tsakiyar parking lot ya bude ya dauko mata turarukan sa guda biyu ya danka mata su.
Sallama sukayi tunda ba'a bari wanda ba matafiyi ba ya shiga cikin airport din.
"Sai munyi waya" yace da ita yana dan rike hannunta.
"Allah ya kaiku lafiya"
"Ameen" Wani abu me nauyi ne ya danne masa zuciya. Da kyar ya iya furta "Take care" Kafin ya juya ya nufi departures lounge.
Suna tsaye a wajen har ya shige kafin su ma suka shiga mota suka kama hanyar gida.
Ita dai Fareeha har suka isa gida bata sake cewa uffan ba. Gaba daya ji tayi kaman an sace wani abu a zuciyar ta wanda bata san ranar da za'a maido mata da shi ba.
Bayan tayi sallar Maghreb taga sakon sa akan cewar sun tashi. Kamar kullum dai Addu'a ta masa.
Sake neman lambar Umma tayi, ta ko ci sa'a ta same ta a bude. Tana dauka kuwa ta hau bata hakuri. Abun ka da ďa da uwa, kan kace me sun dinke.
Nan Fareeha ta shiga bata labarin gidan da irin hidimar da su Anti Bebi suka yi mata. Labari yayi dadi har ta kuskure tace da ita ma akayi jeren. Ai kuwa fada ya dawo sabo fil.
Ta inda Umma take shiga bata nan take fita ba.
Ai Fareeha se ta rasa bakin bada hakuri. Haka ta karaci fadan ta ta kashe wayar.
"Ni ma dai da dogon baki na" ta fada tana tashi don kabbara sallar Isha.
Bata jima da idar wa ba kuwa sai ga Yusrah nan ta shigo.
"Har kin sa na fara tunanin ko ta can ta can bazaki sake dawowa ba ne"
Yusrah ta tabe baki tana jingine dan karamin akwatin ta a jikin bango. "Inaaa. Ai ni da ke kuma mutu ka raba takalmin kaza. Yadda Ya Mu'azzam ya kakaba min ke, babu ranar yakice ki"
Girgiza kai tayi tana dariya. "Kyaji da shi dai. Ni yunwa nakeji barin je na nemi abin da zan ci"
Sai da Mu'azzam yayi sallah ya ci abinci tukunna ya dauko gift bag din don ya duba abunda ke ciki.
Mamaki ne ya kama shi ganin leda ce guda cike da gullisuwa da alawar madara.
A iya hirar da sukayi da Fareeha kafin auren su zai iya cewa so daya ya taba furta mata kaunar da yake yiwa su gullisuwa. Shi ya ma manta da zancen. Ashe ita abun yana ranta.
Zaro ledar yayi don ya bude ya ci yaji sai ga wata takarda ta fado daga ciki. Yana budewa idon sa sukayi tozali da kyakyawan rubutun matar sa.
Wasika ce 'yar gajeruwa ta masa tana mai mishi godiya akan dinbin alkhairan da yayi mata tare da yi masa addu'ar samun nasara a rayuwa. Bata kammala ba kuwa sai da ta sake jadadda masa matsayin sa a zuciyar ta.
'You're my proper wedding and my proper home. I love you'
Hawaye ne yaji sun cika masa idanu.
Fareeha ta gama kashe shi. Ta ciro zuciyar shi daga kirjin sa da damke ta a hannunta. Ba shi kuma da sauran wani abu. Sai yadda tayi da shi.
Ikon Allah ne kawai ya sa yake zaune a hotel room dinsa a wannan lokacin. Amma da ba dan haka ba a daren nan zai iya komawa Kano don kawai shima ya sake jadadda mata matsayin ta a tashi zuciyar.
So kenan. Ga dadi ga zogi.
*******************
Swimming swimming in this chapter🥰🥰🥰.
Leave a pink heart for my babies please.
Taku a kullum,
Miryamah.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top