31.
Can na hango wani comment wai ana cewa those that have my contact should start calling me 🤣. Nace babbar magana. Barin zo nayi updating kafin a fara sallama a kofar gidan mu a na nema na a dalilin labarin Fareeha da Uncle Captain dinta.
Assalamu Alaikum my darlings ❤. Ba ni da kalaman da zanyi amfani da su wajen baku hakuri. Life happened. I didn't know it'd take this long before I updated another chapter, but here we are.
Please accept this as a token of apology. I really do hope you love this chapter.
31.
Abun mamaki sun bar Azare shiru-shiru kamar ba biki ake ba, suna isa Kano sai ga jama'a cike a gidan Ammah, har sai da tayi mamakin yanda aka tarkato kan jama'ar ganin cewa auren yazo bagtatan.
Motar su na tsayawa aka bude murfin kofar baya sai ga Yusrah ta leko kai.
"Wa nake gani haka kamar amaryar Uncle Captain ?"
Fareeha ta banka mata harara, hakan yasa Yusrah tuntsure wa da dariya.
"Su Uncle Captain za'a sha tsiwa kam. Yanzu ni dai lullube fuskarki na rakaki ciki"
Hannunta Yusrah ta mika mata ta taimaka mata ta fito a motar kanta a kasa. Nan da nan sauran jama'ar da ke harabar gidan suka zagayeta ana ta maraba da zuwan amarya.
Har falon Ammah suka rakata inda Amman ita ma ke zagaye da jama'arta.
Sanya ta tayi cikin rikon ta tana mai farin ciki da shigowar Fareeha cikin zuri'ar ta. Addu'o'i ta jero mata kafin nan ta zaunar da ita akan kujerar da ta tashi akai. Anti Bebi ce tazo ta zauna kusa da ita tana dan dafa kafadar ta. A hankali ta rada mata 'Barakallahu lakuma wa Baraka alaikuma wa jama'a baynakuma fii khair'.
Zata iya cewa a lokacin kaf wajen bayan Ammah a farin ciki sai ita.
Tun bayan da Ashraf yayi aure ta shiga zullumi kan batun yarinyar. Dama shi ne take tunanin zai taimaka mata kan kudurin da ta dauka akan Fareehar, sai gashi shi kuma ba hakan yake tunani ba.
Ashe ashe Allah ya shirya wani babban lamari a kansu. Gashi yanzu Fareeha ta zama matar kaninta.
Allah kenan. Shi ba ruwanShi.
Bayan an gama shigowa kowa ya natsa sai Anti Balaraba ta fara jawabi da godiya wa Allah da ya nuna musu wannan ranar tare da yin 'yar takaitacciyar naseeha zuwa ga amarya.
Fareeha dai tana kudundune cikin mayafi ta ma kasa dagowa taga su waye a falon.
Haka dai tayi ta jin muryoyi kowacce da dan guntun shawarar da zata bayar hade kuma da yin addu'a.
Bayan an kammala aka shigar da amarya daga ciki domin ta yi sallah ta dan huta.
Tun da suka shiga dakin kuwa Yusrah ta kasa barin ta ta sha iska in banda zolaya ba abinda take mata.
"Nikam ba ce min kikai babu komai tsakanin ku ba? Har da ce min wai gaisawa kawai kuke. Gashi yanzu gaisuwa ta kawo mu zuwa nan"
Fadila ce ta zungureta amma hakan bai sa tayi shiru ba.
Fareeha dai kawai murmushi tayi don kwata-kwata bata da karfin mayar mata da martani a lokacin don gaba daya jikinta wani sanyi yayi.
Bandaki ta shiga tayi alwala ta zo ta gabatar da sallar la'asar. Tana idarwa kuwa sai ga shi an fara kiran Maghreb don haka ta tashi ta sauke farali.
Anti Balaraba ce ta shigo dakin tare da wata mata da Fareeha ta lura suna kama da Ammah.
"Yusrah ku je ku shigo mata da abinci idan ta ci sai ku tayata shiryawa." Anti Balaraba ta fada tana ajiye wata leda me kyau a kan gadon dakin. "Ga wannan ki saka inji angon ki"
Wata kunya ce ta kamata tayi saurin sadda kanta kasa.
Da kyar ta samu ta ci abincin don sam bata jin cin komai. Har wani zazzabi zazzabi ne ma taji yana kokarin kamata.
Sai da su Yusrah suka fita da kwanukan ne ta samu sukunin lalubo wayarta don ta kira su Umma tace mata sun iso lafiya.
Bugu biyu aka dauka.
"Adda?" muryar Inayaah ta doki kunnuwanta.
"Na'am Inayaah"
Wani kuka Inayar ta fashe da shi wanda ya razana Fareehar.
"Adda shi ne kika tafi ba sallama? Meyasa zaki tafi ki barmu? Anti Mami tace wai kin tafi har abada. Har abada fa Adda? Har abada dayawa sosai dan Allah ki dawo mucigaba da zamanmu...."
Idon ta ne taji itama ya ciko da hawaye ga wata dariya da ke kokarin kwace mata duk a lokaci daya.
"Ya Salaam! Inayah ni ban tafi har abada ba ina nan zuwa inshaAllah kinji ko? Anti Mami tsokanarki kawai take yi. Wani sati ma tace zaku zo ai inshaAllah. Ki kwantar da hankalinki kinji?"
Da kyar ta samu ta dena kukan tukunna ta kai wa Umma wayar wacce ke kwance a daki tun bayan la'asar. Har ga Allah tun da su Fareeha suka tafi ta ji kaman an shiga zuciyar ta an sace wani abu mai muhimmanci a cikin ta. Gaba daya taji gidan ya mata shiru dukda cewa su Qulsoom suna ta hayaniya a tsakani.
Jin Inayaah tace Fareeha ce a kan layi yasa ta tashi daga kwanciyar da tayi ta karbi wayar.
Bayan sun gaisa take sanar mata cewa ai Mu'azzam ma ya kira yace sun isa lafiya.
Wayencewa Fareeha tayi kamar bata ji maganar Umman ba ta hau yi mata wata hirar daban. Ganin surutun yaki karewa yasa Umma tayi mata sallama ta katse wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta cire wayar daga kunnenta. Idon ta ne ya kai kan ledar da ke kan gadon. Tana so ta dauko ta duba koma menene amma kuma kunya take ji don bata san me ta kunsa ba. Bata kuma so a ga zumudin ta don har yanzu akwai jama'a a gidan suna ta kai komo a tsakani.
Shigowar Yusrah ne yasa ta kauda tunanin a ranta.
"Ki tashi fa ki shirya Uncle Captain dinki yana hanya"
Kwafa tayi ta tashi ta nufi inda kayan ta suke. Nan ba da jimawa ba zata fara mayar wa Yusrah da martani don da alamu bata da niyyar sarara mata.
Karamin akwatin ta jawo ta bude ta cire duk abun da zata bukata ta shige bandaki da niyyar yin wanka.
Bayan ta fito ta shafe jikinta da mai da Kulachcham mai sanyin kamshi sannan ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ruwan hoda da fari.
Bata kammala shiryawa ba su Fadeela suka shigo don sanar da ita cewa Ango fa ya iso.
Nan taji zuciyarta ta fara sassarfa a kirjinta.
Fadila ta jawo ledar kan gadon inda ta fito da wata rantsatsiyar luffaya ruwan hoda da gwal. Kallo daya zaka yi mata kasan cewa an barar da kudi wajen siyan ta.
"Kai Masha Allah Kawuna ya iya zabe gaskiya. Perfect match" Fadila ta fada tana jingina Lufayyar a jikin Fareeha. Ita kanta Fareehar sai da ta yaba da kyan ta da kuma yadda ta dace da kayan jikinta.
Su suka tayata karasa shiryawa suka feshe ta da turaren da bata san daga ina suka samo shi ba mai sanyin kamshi sannan suka ja ta zuwa falon Ammah.
Ana fito da ita kuwa wasu tsoffi da ke falon suka hau guda, masu hoto kuma suka fara aikin su.
Wata sabuwar gudar aka sake rangada wa tare da yi wa ango maraba da shigowa. Ba tare da bata lokaci ba su Fadila da sauran 'yan matan da ke wajen suka tare ta wai su a dole se an fanshi amarya tukunna zasu bar ango ya bude mata fuska.
A lokacin ta tuna irin diramar da akayi a bikin Ya Ashraf da Wafiyya har tana ganin rashin dacewar hakan, ashe ita ma za'ayi haka a bikin ta.
Wani katon kwando suka ajiye a gabansu na fansar. Kan kace me kuwa abokan ango suka fara jefa rafar kudi a ciki. Goggonin sa ma ba'a bar su a baya ba. Nan da nan kwando ya cika dam. Sai da suka kammala sannan shima ya fito da rafar kudi a aljihunsa ya dora a sama. Wuri ya kacame da ihu da tafi, kowa sai san barka yake.
Aka buda waje ango ya iso ga amaryar sa.
Kamshin turaren sa ne ya fara mata salamu alaikum kafin ta ji dumin jikinsa a lokacin daya rankwafo don yaye lullubin da aka mata.
Tana jin sa yana karanto addu'o'i kafin ya kare da basmala tare da yaye mayafin lufayyar tata.
Wani sama-sama taji numfashin ta yakeyi a lokacin da idanunsu suka sarke a cikin na juna. Abubuwan data hango a cikin nasa idanun yasa tayi saurin sunkuyar da kanta tare da kokarin daidaita numfashinta.
Ba abunda da take ganin sai hasken flash din kyamarori da ta mai daukan hoto da masu wayar hannu. Kowa sai binsu yake da fatan alheri.
Zuciyar ta ce taji ta cika da farin ciki ganin yanda kowa ke murna da wannan auren da yazo babu shiri babu tsammani. Nan ta shiga yiwa Allah tasbihi da godiya bisa wannan ni'imar da yayi mata.
Hotuna aka shiga dauka babu kakkautawa kowa yana so yayi hoto da amarya da ango.
Duk wannan bidirin da ake idon Mu'azzam na kanta. Ya kasa yarda abun da yake gani a gabansa gaske ne. Gani yake kamar nan da wasu 'yan lokuta zai farka ya ganshi a dakin shi a New York. All this might be a dream.
Sai dai kuma abun ba haka yake ba fa. Da gasken gaske ya zama mijin Fareeha kuma ta zama matar sa.
Bai kara tabbatar da hakan ba kuwa sai da ya sarke hannayensa cikin nata, yaji yanda numfashinta ya tsaya cak saboda yanda abun yazo mata a bazata, yaji kuma yanda ta kankame hannun nasa daga baya wanda hakan ya kusa ya haddasa masa bugawar zuciya tsabar farin ciki.
Har aka gama daukar hotunan kuwa bai saki hannunta ba.
Ko bayan jama'a sun ragu kowa ya kama gabansa yana nan zaune a gefenta a kan doguwar kujerar falon Ammah.
Sai da su Anti Balaraba suka zazzare mishi ido ganin bashi da niyyar sake ta sannan ya sarara mata. Daga karshe ma kora shi suka yi akan dare yayi kuma amarya ta gaji da safe ya dawo su sake gaisawa.
Ya so ace ya samu ko da minti goma da ita ne su biyun su ba tare da hayaniyar mutane a tsakani ba, amma hakan bai samu ba.
Haka ya tattara kan 'yan uwan nasa(cousins dinsa) wanda sune suke a matsayin abokan sa suka bar gidan.
Wajajen sha daya da rabi kowa ya watse aka share wa Ammah gidan ta aka mayar da komai inda yake.
Fareeha ta sake yin wanka ta saka kayan baccin ta kafin ta bi lafiyar gado ta kwanta kusa da Yusrah wacce aka bar ta don ta tayata kwana. Akwai wata mata a tare dasu wanda taji suna kiranta da Anti Zu, da alama ita ce ke zama tare da Amman a gidan.
Har ta fara bacci ta ji wayar ta tana vibration. Ko kafin ta duba me kiran ta san shi ne yake kira.
Sai da ta leka kasa inda Anti Zu tayi shimfidi ta tabbatar bacci take tukkuna ta amsa wayar.
A hankali ta kara wayar a kunnenta. Cikin rada tace "Hello?"
Daga daya bangaren yayi murmushi mai sauti wanda ta jishi har cikin tafin kafanta. "Ba sai kin ce komai ba nasan ba ke kadai bace a daki. Just listen to me"
Gyada kai ta shiga yi kaman yana tsaye a gabanta.
"You looked so beautiful today" ya fada tare da sauke ajiyar zuciya. "And you smelled so good"
Runtse idon ta tayi jin wata kunya ta lullubeta.
"A ajiye Lufayyar nan za'a sake saka min ita ni kadai kinji ko?"
Zuciyar ta ce taji ta cika dam da wani irin yanayi sabo.
Murya kasa-kasa ta amsa mishi da "Toh"
"Kiyi hakuri na hanaki bacci, kawai naji bazan iya kwanciya ba tare da na fada miki abun da ke yawo a raina ba the moment I saw you"
Jin tayi tsit ya sake saka shi yin wani murmushi.
"Kiyi bacci Faree. Allah ya miki albarka ya bar min ke. Don't forget that I love you" Yana fadin haka ya kaste wayar.
Tayi bacci fa yace? Ina ita ina yin bacci bayan ya riga ya sauya mata bugun zuciya.
Dirowa tayi daga kan gadon ta shiga bandaki ta dauro alwala.
A cikin duhu tayi ta lalume har ta samo hijabin ta ta skirt din data cire na kayanta ta daura akan rigar baccin ta.
Nafila tayi raka'a biyu.
Lokaci ta dauka mai tsawo tana wa Allah kirari da godiya, sannan ta roke Shi da sunayenSa kyawawa kan ya sanya mata albarka da ni'ima mai tarin yawa a cikin rayuwar aurenta ya bata ikon kyautata wa mijin ta ya kuma kara dasa mishi son ta a cikin zuciyar ta.
Ba ita ta runtsa ba sai wajen karfe uku, hakan ma bata san lokacin da bacci ya dauketa akan sallaya ba.
Da safe bayan tayi wanka ta shirya ta shiga dakin Ammah suka gaisa. Da fara'a suka gama gaisuwar har ta tambayeta ko akwai abun da take bukata, tace mata babu.
Bayan ta koma daki sai ga Yusrah ta shigo mata da breakfast.
"Kinci albarkacin yau, amma gaskiya daga gobe bazan wani sake shigo miki da breakfast ba. Fitowa zakiyi muci tare ehe!"
Rankwashi taji me zafi ya sauka a tsakiyar kanta har sai da ta saki 'yar kara.
"Kaniyanki!" Anti Zu ta fada tana hararta. "Matar Kawun naki kike cewa haka? Ki bar ganin cewa kawaye kuke a da, yanzu matsayin Antinki take"
Yusrah ta turbune fuska yayin da Fareeha ke dariya kasa-kasa.
"Tunda abun hakane nikam zan koma gidan mu to inda aka san matsayi na"
Anti Zu ta ajiye flask din ruwan zafin da ta shigo da shi ta juyo ta kalleta "Ai baki isa ba tunda Mu'azzam yace ki zauna a wajen ta kuwa ba inda zakije. Wuce muje my friend!" Ta finciki hannunta sukayi fita.
Har a lokacin Fareeha bata dena dariya ba. Ta lura Anti Zu tana da son dirama.
Saukowa tayi ta hada tea sannan ta zuba soyayyar doya da sauce a plate. Abincin yayi dadi sosai don har sai da ta kara.
"Su Mama sun zo zamu tafi kasuwa sai mun dawo" Yusrah ta leko don yi mata sallama.
Nan da nan ta marairaice fuska ganin za'a bar ta daga ita sai Ammah da Anti Zu a gidan. Ko ba komai in Yusrah tana nan zasuyi fadan su su shirya, ita da su Ammah kam sai dai su yi ta wasan buya.
"Tafiya zakiyi ki barni?"
Wani kallo Yusrah ta mata. "Shagwaba zaki min ko me? Ki jira idan mijinki yazo sai ki mishi."
Ita ma mayar mata tayi da wani kallo.
Yusrah tayi dariya "Asha soyayya lafiya. Bye bye" ta na fadin haka ta fice.
Kai kawai ta girgiza ta cigaba da karyawanta.
Tana gamawa ta tattare komai ta kai kitchen. Ta samu komai tastas don haka ta hau wanke kwanukan data shigo da su. Ta gama tsaf ta jere su a kan rack sannan ta dawo daki ta zauna.
Wayar ta ta dauka ta kira Umma. Ita kadai a gida kowa ya tafi islamiyya Anti Mami kuma taje yin exams.
Hira suka dan taba sannan Umma ta kare da nasihohi da Addu'a kafin sukayi sallama.
Tana zaune a daki har gyangyadi ya fara dibar ta ganin cewa bata samu isashen bacci ba.
Sallamar shi kawai taji a bakin kofar dakin , wannan yasa tayi saurin bude ido.
Bata yi aune ba kawai ta ganshi tsulum cikin dakin. Nan da nan ta hau laluben dankwalin ta don rufe kanta.
"I..I...Ina kwana?"
Murmushi ne dauke a kan fuskarsa yana kare mata kallo. Idanun sa ke yawo akan ta yana kallon yanda kayan ta suka karbeta matuka.
Karaso wa yayi bakin gadon ya zauna tareda kai hannunsa kan dankwalin nata ya zame shi.
Ji tayi gaba daya numfashin ta ya sarke jin hannunsa cikin gashin ta.
"Meyasa zaki boyemin kanki? Ko kin manta matsayi na a wajen ki ne yanzu?" maganar tasa ta fito kamar rada-rada, hakan yasa taji gaba daya jikin ta ya mutu.
Bai jira ta bashi amsa ba ya jawo ta barin jikinsa. Nan da nan kamshin sa ya cika mata hanci.
"Kin tashi lafiya?" Yayi maganar daidai kunnenta.
Ita tama manta da gaisuwar da ta mishi a lokacin daya shigo, don haka gyada masa kai kawai tayi.
Murmushi yayi me sauti. "Fareeha kece kuwa? Ina kika kai min matata me bala'in tsiwa?"
Bata san lokacin da ta dago daga jikin sa ba ta banka masa wata harara.
Sake sanyata yayi a jikinsa yana dariya me cike da annashuwa. "There she is"
Sun dade a haka; ita tana sauraron bugun zuciyar sa shi kuma yana shakan sassanyar kamshin ta.
Sai da ya tattaro duka nutsuwar sa sannan ya ja da baya yana kare wa fuskar ta kallo.
"Kin karya?"
Gyada masa kai tayi.
"Shi ne ko ki jirani?"
Daga kai tayi ta kalli agogon dake manne a jikin bango sannan ta maida kallon ta gare shi. "Karfe sha daya fa Uncle Captain. Idan na jira ka ai yunwa ce zata kashe....."
Wani zafi ne taji ya ziyarci labbanta. Tayi saurin kai hannun ta wajen tare da zaro idanun ta.
"Meyasa zaka mintsine min baki?"
Shima yanzu hararar ta yake. "Ba nace bana son wannan sunan ba?"
Juya idon ta tayi wanda hakan yakara mata kyau a idanunsa.
Ita kam taga ta kanta. Tama manta sunyi wani zancen a canza masa suna. Shine hadda murde mata baki. Ai wannan ma cin zali ne. Daga aura masa ita har ya fara cin zalin ta.
"Eh din anci zalin"
Ware idon ta tayi akan shi. Bata ma san cewa maganar da take a zuciya ba har ta fito fili.
"Next time kika sake maimaita wa cizon bakin zanyi"
Har zata mayar masa da martani sai kwakwalwarta ta hasaso mata yadda za'ayi cizon, nan da nan wata kunya ta lullube ta. Ba shiri ta jawo dankwalin ta tana kokarin rufe fuskarta. "Dan Allah ka bari...."
Murmushi yayi yana janye hannunta daga fuskarta.
"Sai nayi maganin wannan kunyar taki. Yanzu dai tunda ba'a jira ni ba za'a iya min rakiya inje inci abincin?"
"Rakiya kuma? Su Amma fa suna falo"
"Ni dai lokacin dana shigo ban ga kowa ba. Ke dai idan baza ki rakani ba kawai ki fada, bana son kwanakwana"
Girgiza kai ta shiga yi tare da mikewa tana neman mayafin kayan nata. "A'a ni bance ba, muje na rakaka"
A dinning table suka zauna gefen juna. Tana kokarin jawo mug don hada mishi tea yayi saurin dakatar da ita.
"I just want your company." Yace da ita bayan ya karbi kofin a hannunta.
Tana kallon shi ya gama hada tea dinshi ya zuba abinci a plate.
"Zan iya sanin dalilin daya sa ake min wannan zazzafan kallon?" Ya yi maganar tare da yin murmushin gefen lebe.
'Yar karamar dariya tayi. "Kar ka min sharri ni ba wani zazzafan kallon dana ke maka."
Kurbar shayin sa yayi kafin yace "In kinyi ma ba wanda ze daure ki. I'm all yours"
Sunkuyar da kanta tayi tana jin dadin kalaman nasa.
Haka sukayi ta hira har ya kammala kafin nan ya shiga daki don yi wa Ammah sallama, ita kuma ta tattara kwanukan ta kai kitchen.
Tana cikin dauraye wa ta ji shi tsaye a bayan ta.
"Na ce wa Ammah ta bani aron ki muje house hunting ta ki"
Da sauri ta juyo a razane tana kallon shi. "Huh?"
Dariya ce ta kubce mishi ganin yanda ta rude lokaci daya. Jawota yayi jikin shi har tana jin jirin dariyar sa a nata kirjin.
"I love messing with you"
Dan ture shi tayi tana turo bakin ta jin cewa zolayar ta yake. "Allah ka dena min haka inba so kake nima na rama ba"
Shi baya ma jin abun da take fada, idon shi na kan bakinta. Sai da ta lura da hakan ta yi saurin juyawa tana kokarin boye murmushin ta. Hakan da ta yi yasa ya farga daga tunanin daya fada.
"To kiyi hakuri, I'm sorry" ya dafa kafadarta. "Yanzu dai a min addu'ar samun sa'a zanje neman gida"
Dama can ba fushi tayi ba don haka ta juyo da murmushi sanye a fuskar ta. "Allah ya kiyaye hanya ya kuma bada sa'ar abin da aka je nema"
Shafa gefen fuskarta yayi "Ameen Fareeha ta"
"Nagode da dawainiyar da kake tayi akaina. Ina rokon Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"
Kiris ya rage ya aiwatar da abun da yake ta kokarin danne zuciyar sa akai.
"Ameen. Nima nagode"
Haka sukayi sallama kowanne zuciyar shi cike da kaunar dan uwansa.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top