30.

Spoilerrrrrrrrrrr alertttttt.

This is the chapter where we get married y'all 👰🏽‍♀️🤍💍💐.



30.

Dawowarsu kenan daga gidan Mama Uwani. Tun bayan da ta gama jarabawa da ta dawo gida su Inaayah suke ta damun ta akan suna so suje don suma sunyi hutu a lokacin. A lokacin ne kuma aka sallamo Abba a asibiti don haka sai ta maida hankalin ta kacokam wajen taimakawa Umma kula da shi da kuma aikin gida.

Yau din sun tashi jikin da sauki don haka Umma ta ce su tattara suje su gano yayar tata don itama ta sha sintiri akan su tunda Abban ya kwanta.

A bakin layi mai keke napep din ya sauke su don haka takowa sukayi suka karaso.

Inaayah da Qulsoom sun rigata shigewa gida don su suna gaba ita kuma tana rike da hannun Ahmadi shiyasa bata tafiya da sauri.

Kamar daga sama taji ance "Hauwa"

Ko a mafarki ko a farke idan taji wannan muryar tasan waye mammalakin ta.

Sake kankame hannun Ahmadi tayi tana juyawa don ta tabbatar da abun da kunnuwanta suka jiye mata.

A lokacin ne kuma ta fahimci me hausawa suke nufi idan sunce mutum ya tsorata kamar yaga fatalwa, don kuwa abun da taji a lokacin da tayi ido hudu da Engineer Faruk ya wuce tsoro, ya wuce fargaba. Ba ta ma san da me zata kwatan ta shi ba.

"Innalillahi wa inna ilaihi raajiun" abun da ta iya furtawa kenan kawai.

Sakin hannun Ahmadi tayi inda shi kuma ya ruga gida da gudu.

A hankali Faruk ya fara takowa inda take, yayin da ita kuma ta fara ja da baya.

"Hauwa please ki tsaya muyi magana" muryarshi can kasa kamar me shirin yin kuka "awa ta biyu a nan ina jiran naga giftawarki saboda bani da karfin gwiwar shiga cikin gidanku"

"Me ya kawo ka nan?"

Jin tambayar tata yayi kamar ta watsa masa garwashin wuta.

"Wajen ki nazo"

Cigaba da kallon sa take kamar har yanzu bata gasgata shi dinne a gaban ta ba.

Ya karanci halin da ta shiga a lokacin don shima kusan hakan ne a wajen shi.

Ya cigaba da magana.

"Magana nazo muyi Hauwa. Please kiyi hakuri ki saurareni"

Wani abu ta hadiya mikit. Yaji-yaji takeji a idon ta wanda ya nuna alamun cewa kiris ya rage ta fara hawaye. Nan da nan kuwa ta danne su.

Ba shi da wannan matsayin a rayuwar ta da zata tsaya tana zubar kwalla saboda shi. Yayi kadan.

"Ina jinka"

Maganar da ya zo da ita bata cancanci suyi ta a tsaye a kofar gida ba amma yanda yaga yanayin ta yasan bata da niyyar ce masa ya shigo. Hasalima yana ganin idan ya tsaya bata lokaci to zata iya shigewa ta bar shi a wajen.

Shi kuma yazo ne da kudiri babba a ransa, kuma yana fatan ta saurare shi ko da kuwa na minti daya ne.

Ba tare da bata lokaci ba ya shiga bata hakuri akan irin rabuwar da sukayi da yadda bai neme ta ba tsawon lokacin nan da kuma karin bayani akan yadda dangin sa suka hana shi auren ta a bisa dalilin abun da ya faru da ita.

Tun da ya fara magana kawai jin shi take, sai da taji yace "I want you to give us a second chance Hauwa" tukunna ta dawo daga duniyar tunanin data fada.

"Me kace?"

"Wallahi daidai da rana daya ban ji na dena sonki ba Hauwa. Dare da rana kina raina. Tsawon watannin nan da aka shafe kullum da tunaninki nake bacci da shi nake tashi...."

Wata busashiyar dariya ce ta kubce mata wadda babu annashuwa a tare da ita.

Dariyar ta masa ciwo amma bai karaya ba, ya cigaba da surutun sa. "Ki yafe min Hauwa, ki bari mu dawo yadda muke dinmu a da. Tun da kika bar rayuwa ta Hauwa na rasa farin cikina. Ki yafe min please. Ki bani dama na wanke kaina na baki farin cikin dana kasa baki a baya. Ki bani dama na nemi auren ki a karo na biyu"

Harde hannunta tayi a kan kirjin ta tana kare mishi kallo. Yanzu abun nashi ma ya dena bata mamaki, dariya ma yake bata.

Wato duk inda kake tunanin maza sun kai a rainin hankali, to sun wuce nan. Bata san ma da me zata kwatanta abun da Faruk din yake ba.

"Hajiya ta yadda ka aure ni kenan yanzu? Ko kuma dai tawaye zaka mata?"

Tambayar ta dauke shi bazata, don sai da ya kare mata kallo yaga ko cewa daga bakin ta maganar ta fito.

Ta ido take bashi amsa, cewa Fareehar daya sani a da an canja ta. Wannan Fareeha 2.0 ce, kuma bata da kirki. Kuma bata daukar rainin hankali daga wajen maza irin sa.

Ajiyar zuciya yayi ya sunkuyar da kansa.

"Ta amince"

Yanzu kam dariya take masa bil hakki.

"Kai Masha Allah. Na maka murna wallahi. Amma meyasa ta amince yanzun? Me ya canja?"

Sai a lokacin yake dana sanin zuwan nasa don kwata-kwata ba haka ya hango maganar tasu zata kasance ba. Bai taba tsammanin a 'yan watannin nan Hauwar sa zata canja har haka ba har ta na mishi irin wannan maganar cike da gatse da rashin ganin girmansa. Yarinyar da da kowa kallon kwayar idon sa bata iya yi, amma yanzu se gasa mishi magana take?

"Yanzu wannan ba shi bane muhimmi, muyi maganar abun da ya fi muhimmanci"

Hade rai tayi kamar ba ita bace ta gama dariya yanzu.

"Wannan dinma yana da muhimmanci. Idan har kana so na baka dama a karo na biyu to zaiyi kyau ace babu wani boye-boye ko karya a tsakaninmu. Ta haka ne kawai zai sa na sake amince wa da kai a karo na biyu. Don haka ka fada min, meyasa Hajiya ta amince yanzu?"

Tauna gefen lebban sa yake yi yana tunanin ko ya sanar da ita ko kuma ya fasa, to amma kuma ga alama ta fara sakko wa kuma idan ya fada mata gaskiya ta yiwu ta sake amince wa da shi din.

"Dama can bayan ta hana aurenmu ta gindaya min sharadi akan idan dai ina so na aureki to se na dawo da tsohuwar matata wanda a lokacin ko wata biyar bata yi ba da fara zawarci. Dana nuna mata bani da niyyar yin hakan ne yasa ita ma ta yi kememe akan bata yarda na aureki ba.

To gaskiya yanzu naga bazan iya rayuwa babu ke ba Hauwa, shiyasa kawai na dawo da ita ex-wife din tawa kuma......"

Kallon da take masa ne ma yasa ya hadiye sauran kalaman nasa.

"Ikon Allah. To a tunaninka tsawon watannin nan dama zama nayi ina jiran ka gama cika umurnin ta sannan ka zo ka aure ni ko me? Saboda ance maka bani da masu sona ko kuma na damu danayi auren?"

Goshin sa ne ya tattare jin furucin ta. Anya kuwa ita ce ?

"Kace a tsawon watannin nan ka rasa farin cikin ka, ka san ni me na rasa?

Kaina na rasa Faruk. Ji nayi kamar gangar jikina ce kawai take nan amma ruhina yana wani wajen. Bana iya bacci bana iya cin abinci ba abun da yake mun dadi a duniya. Idan banda tunanin yanda zan kashe kaina ba abun da nakeyi. Kana ina lokacin?

Bayan nan mahaifina jigon rayuwata ya samu bugawar zuciya a dalilin fasa aure na dakayi...." daga kanta tayi saboda a lokacin taji wani matsanancin kuka yana kokarin kwace mata amma tayi saurin hadiye wa.

"Umma ta da ilahirin 'yan gidanmu babu wanda bai shiga tashin hankali ba a dalilin haka. Rayuwa ta mana baki kirin, muka rasa tudun dafawa. Amma cikin ikon Allah, sai gashi abubuwa sun zo da sauki. Da ba dan rahamar Ubangiji ba, bansan a wani yanayi zamu tsinci kanmu ba.

Don haka idan kana tunanin ka shiga kunci a dalilin rabuwarmu, then you have no idea. Baka san me kake fada ba"

Jikinsa ne yayi matukar sanyi jin kalaman nata. A lokacin ne kuma yaji ya kara tsanar kansa na rashin bibiyar mai take ciki bayan rabuwar su.

"Hauwa...."

Saurin dakatar da shi tayi ta na masa nuni da bakin titi. "Ina so ka juya kan motarka ka kama hanya ka koma inda ka fito tun kafin na furta maka abun da zanyi da na sanin fada. In ba haka ba kuma in tattaro maka 'yan dabar unguwar mu su cinna maka wuta da ga kai har motar taka" tana fadin haka ta juya ta shige gida.

Da kyar kafafunta suka kaita dakinsu inda ta fada kan gado ta fashe da matsanancin kuka.

Komai ya dawo mata sabo a lokacin.

Me yasa sai yanzu zai zo? Ina ya shiga a lokacin da ta fi bukatar sa? Meyasa zai zo ya tono mata abubuwan da take tunanin tayi nasarar binnewa? Meyasa zai sake shigowa rayuwar ta bayan tana kokarin maye gurbin sa da wanda a yanzu tana ganin shi yafi cancanta da wannan matsayin?

A haka Anti Mami tazo ta sameta. In da sabo ta saba ganin ta a irin wannan yanayin, amma haka ta daure ta tambayeta dalilin kukan nata.

Ko da ta sanar mata itama Anti Mamin sai da abun ya bata mata rai.

"Amma lallai sai a gaida Engineer. Shi a karan kanshi bai ji maganar ma ta mishi banbarakwai ba? Ai ko maza sun kare a duniya bazaki aure shi ba tunda dai bai duba zumuncin dake tsakaninsa da marigayi ba ya tafka mana rashin mutunci. Ki dena bata hawayenki a kanshi dan Allah. Ba shi da wannan matsayin kuma yanzu"

Da dare da Mu'azzam ya kira yaji muryarta kamar ta sha kuka sai tace mishi kawai bata jin dadi ne, kanta na dan mata ciwo. Bai yadda da zancen nata ba amma kawai sai ya bari a haka. Gajeruwar hira sukayi kafin nan ya mata sallama tare da addu'ar samun sauki.

Suna gama waya kuwa ya danna wa Anti Mami kira yana son karin bayani daga wajenta. Hajiya Anti Mami kuwa batayi wata-wata ba ta sanar da shi abin da ke faruwa.

Bayan kwana uku da zuwan Engineer suna zaune a daki tana yi wa Inaayah kalaba sai ga Qulsoom ta shigo tace ga Baba Zubairu yazo yana nemanta.

Tun da aka sallamo Abba baya kwana biyu sai yazo ya duba su. Har tausayi ma yake bata yanda yake ta sintiri a kansu. Sai dai kawai Allah ya bashi lada.

Shi da Umma ta samu a falon kowa yayi jugum jugum. Nan da nan kuwa ta sha jinin jikinta don ta san maganar ba karama bace.

Bayan sun gaisa ba tare da bata lokaci ba ya shiga yi mata bayanin dalilin kiran da yayi mata.

"Nasan kina da labarin cewa yaron nan dayake neman aurenki ya turo Bappansa wajena ko?"

Zuciyar ta ce ta ji ta sauya bugu.

A hankali ta gyada kanta.

"Tuntuni naso muyi maganar da ke amma kuma yanayin yanda abubuwa suka kasance kwana biyun nan yasa na dan jinkirta zancen. To amma yanzu lokaci yayi kuma da yakamata mu sake taso da shi.

Na samu labari cewa yace a dan jinkirta batun don kaman baki shirya ba, wanda hakan da yayin ya kyauta tunda be matsa miki ba.

Dama ni fatana shi ne idan kin gama jarabawa kin dawo se naji ra'ayinki akan batun. Idan karin lokaci ne kikeso to se a baki. Idan kuma shi dinne kwatakwata bakya so, sai a janye maganar gaba daya.

To sai kuma muka wayi gari da wannan jarabawar da Allah ya turo mana."

A ranta tace jarabawa babba ma kuwa. To gashi dai Abban yana samun sauki kullum, amma batun dawowar tunaninsa har yanzu shiru. Da suka je follow up likitan ya bada shawara kan ko za'a kai shi asibitin malam don yi masa psychotherapy. Da sukaji kudin da za'a ma sai aka bar zancen anan. Kudin da suka kashe ma kadai wajen jinyarsa a ICU har yanzu ba'a fanso su ba, don haka sai suka dukufa da Addu'a kawai.

Kamar abubuwa sun lafa don har yazo ya dena mata zancen 'mijin' nata ma.

To amma shekaranjiya da taje gaishe shi da safe sai cewa yayi "Mamana yanzu kam ai na samu sauki, yakamata kema ki koma dakinki ko?"

Tsabar tashin hankalin da ta shiga a ranar yasa ta ce wa Umma ko zata hada kayan ta ta koma Kano kawai, idan Abba ya dena ganinta watakil hankalin sa ya kwanta ya zaci ko ta koma 'dakin nata' ne da gaske.

Umma kam bata iya bata kwakwarar amsa ba don itama abun ya dameta. Dalilin daya sa ma tace suje gidan Mama Uwani ranar kenan ko ta dan shaki iska daban da ta gidan nasu.

Muryar Baba Zubairu ce ta dawo da ita daga tunanin data fada.

"Har ga Allah na so ace kina dawowa kuyi aurenku ke da yaron nan ko don kuwa Abbanki ya samu nutsuwar da mukeso duk ya samu. Ba irin nazarin da ban yi ba akan yanda zan samu na fahimtar da shi cewa ba'ayi aurenki ba, don har likitan sa na sake tuntuba amma ya gargade ni wajen yin hakan don idan kwakwalwarsa ta kasa amsar gaskiyar lamarin, zai iya haddasa masa wata buguwar zuciyar tunda a dalilin auren ne ya samu ta farkon.

Ina cikin tsaka mai wuya Mamana. Bani da wani buri daya wuce naga na cire ki daga halin da kika shiga na tashin hankalin nan. Amma kaina ya kulle, bani da wasu sauran dabaru.

Shiyasa na tara ku anan ke da Ummanki, idan kuna da wata mafita ko wata shawara ku fada min mu san yadda zamuyi mu shawo kan al'amarin nan"

Zuciyar ta ne taji ta yi mata nauyi jin yadda Baba Zubairun ya gama karaya. A kullum shine mai karfafa musu gwiwa da nuna musu cewa komai mai wucewa ne, to yau shi dinma gashi bukatar lallashi yakeyi. Mai share musu hawayen shima yau kuka yakeyi.

Hawaye suka cika taf a idanunta.

Lokaci yayi da itama yakama ta ta share mishi nashi hawayen.

"Na amince zanyi auren"

Ba Baba Zubairu da Umma kadai ba, ita kanta tayi mamakin furucin nata.

"Mamana" ya kirata a hankali "Ina so ki san cewa maganar danayi banyi ta don na tilasta miki aure a yanzu ba ne, na zo neman shawara da mafita ne a wajen ke da Ummanki"

Wani abu ta hadiya me daci. Maganganun da Faruk ya mata a ranar suna dawo mata tana jin wani zafi a ranta. Ta tuno cewa kusan a dalilin abun da yayi mata ne suka kawo wannan bigiren a rayuwar su. Bayan hakan kuma ko nadama beyi ba shine zaizo yace zai aure ta a matsayin matarsa ta biyu. Saboda shine autan maza.

"Adda" Umma ta kirata ganin kamar bata ma duniyar da suke ciki. Gaba daya hankalin ta na wani wajen.

A hankali ta dago ta kalleta.

"Farin cikinki shi ne abu mafi muhimmanci a yanzu. Kada ki duba halin da Abban ki yake ciki, ko halin da mu muke ciki, ki duba rayuwar da zakije ki fuskanta nan gaba. In ta Abbanki kike, ki sani cewa ba zai dawwama a haka ba, watarana zai tashi ya fahimci cewa abun da yake tsammani a kanki ba hakan bane, don haka kar kice zaki saka kanki a wani hali don kawai ki gasgata abun da shi ya kwallafa ran sa akai.

Idan kuma ta mu kike, menene bamu gani ba a rayuwar nan Adda? Duk zai zo ya wuce da iznin Allah. Don haka bana so ki yanke hukunci haka cikin....."

Ita ma farin cikin su take nema. Farantawar da za ta musu ya wadatar da nata farin cikin. Watakila a dalilin hakan Allah ya dubeta da idon Rahama ya mata sakayya da abinda yafi haka ma.

Dogon numfashi ta ja "Umma dagaske na amince. Dama abun da yasa da din nace a jinkirta ganin Abba yana coma ne shiyasa."

Gaba dayan su jikinsu ya kara sanyi jin furucin nata. Shiru ne ya gifta na dan wani lokaci kafin nan Baba Zubairu yace

"Ina so ki natsu kije kiyi tunani akai. Zuwa gobe zan tuntube ki"

Gyada masa kai tayi a hankali sannan ta tashi ta bar musu falon shi da Umma don su cigaba da tattaunawa.

Daren ranar bata yi bacci ba.

So take ta tashi tayi sallah ta kai wa Allah kukan ta amma ba hali don tana fashi. Don haka ta dauro alwala tazo ta zauna akan sallaya ta fara karatun alkur'ani.

Har Anti Mami ta shigo suka kwanta ita da Ahmadi bata tashi akan sallayar ba. Daga karshe dai sujjada tayi ta kai kukan ta ga Allah. Har sai da taji idonta sun fara rufewa sannan ta rarrafa ta kwanta. Batayi minti biyar da kwanciya ba kuwa sai gashi ana kiran assalatu.

Hakura tayi da baccin ta shiga tayi wanka kafin ta fito ta tada Anti Mami.

Har suka gama shirin makaranta suka watse a gidan bata samu ta runtsa ba. Ga shi kanta na mata wani matsanancin ciwo wanda tasan a dalilin rashin bacci ne.

Sai da ta share gidan tas tayi wanke-wanke tukunna ta koma ta kwanta amma sam ta gagara bacci. Tunani ne fal ranta.

Wayar ta ce tayi kara daga kan kafet in da ta saka ta a caji. Tashi tayi don duba me kiran nata don bata da niyyar amsa wayar kowa a halin da take ciki.

Lambar da ta gani a kan madubin wayar tata yasa hanjin cikinta kadawa. Lambar sa ce ta Najeriya, hakan kuma na nufin abu guda daya.

Hannunta har rawa yake tana kokarin cire wayar a caji.

Ko sallama batayi ba ta ce "Kar kace min zuwa kayi"

Daga daya bangaren Mu'azzam yayi murmushi yana sunkuyar da kanshi. "I couldn't help it".

Hawaye ne taji sun taru a idonta.

Oh ita Hauwa'u ya za tayi da bawan Allahn nan?

"Uncle Captain aikin ka fa?"

Shiru yayi na dan lokaci yana juya cokalin da ke cikin kofin shayin sa.

Wani yanayi ya tsinci kanshi a ciki wanda ya rasa da me zai kwatanta shi.

Tsawon kwanakin nan, inde ba ya aiki to yana zaune yana nazari kan yadda lamarin shi da ita ya kwabe.

Lokacin da yace mata zai janye maganar auren su ba karamin yaķi yayi da kansa ba. Duk da haka bai cire rai akan cewa za'a sake tado da maganar ba kwanan nan amma sai gashi ta zo mishi da labarin halin da Abba yake ciki tun farfadowarsa. Wannan labari ya sa shi cikin matsananciyar damuwa don ba irin tunanin da bai yi ba akai.

Sai gashi Anti Mami kuma ta kara hura wutar da ta sanar da shi cewa tsohon saurayin Fareehan ya dawo, har ma yana mata tayin aure.

A lokacin ne kuma ya fara hango kamar rabuwar shi da ita tazo.

Don tsoron sa daya, shine kar wancan mutumin ya sake komawa har ma maganar ta je wajen manya, don dai shi kam Abba bai san shi ba, Faruk ya sani. Zai iya sake bashi auren 'yar shi in yaso.

In hakan ta faru kuma, tashi ta kare. Bai san inda zai saka ranshi ba.

Ya kai ya kawo har yake tunanin ko ayar Allah ce ke aiki akansa, don ba irin nazarin da baiyi ba akan aya ta 3 dake cikin suratun Noor. Shin wannan ma jarabawa ce daga wajen Allah da ya daura masa son abunda ba zai taba iya samu ba saboda laifin daya tafka a baya?

Cikin dare zai tsinci kanshi a wani irin yanayi. Zuciyar shi zata cushe waje guda tayi masa nauyi, idon sa su cicciko da hawaye. Ya rasa inda zai saka ranshi yaji dadi.

Haka zai tashi yayi sallah raka'a biyu. Idan ya idar sai ya rasa abin da zai roki Allah don yana ganin har yanzu zunubansa suna yawo akansa, addu'o'in sa bazasu karbu ba.

"Allah na tuba. Allah ka yafe min. Allah na tuba" abun da kawai yake iya fada kenan koyaushe.

Ya riga ya gama saduda cewar in dai lamari ne na Fareeha, to komai kunce masa yake. Yanzu ma kasa hakuri yayi ya taho don ya samar wa zuciyar sa mafita. A karo na biyu yana so ya san ko cewa zai same ta din, ko kuma ba zai same tan ba.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin nan yace "You're more important than aiki na Faree"

Lumshe ido tayi, hawayen da suka taru a kurmin idon ta suka samu damar zubowa.

Ya ilaahil alameeen.

Wani abu take ji game da shi a lokacin wanda bata taba ji ba. Hannunta na dama ta saka akan kirjinta ko zuciyarta zata rage gudun da takeyi.

Jin shirun nata yayi yawa ya sa shi fadin. "Ina nan tafe gobe inshaAllah. Zanzo in duba Abba, sannan kuma akwai maganar da nakeso muyi"

Ba sai ya fada mata ba, ta riga ta san maganar da ta taso da shi. Tana so ta ce mishi ya nutsar da zuciyar sa ya kuma kwantar da hankalinsa cewar ba zai rasa ta ba, amma bata san da wasu kalamai zatayi amfani da su ba.

Don haka kawai sai tace "Allah ya kawo ka lafiya"

Yana jin yanda tayi maganar yasan kuka take. Ya runtse idon sa yana kokarin hana zuciyar sa jin zafin kukan nata. "Ameen" ya amsa hade da katse wayar.
Inda yaci gaba da jin kukan bai san me ze iya yi ba.


Karfe sha daya Baba Zubairu ya shigo gidan ya kuwa same ta a falon Umma.

A kwayar idanunta kawai yaga cewa ta riga da ta gama yanke shawara, ba batun komawa baya kuma.

"A jiya munyi magana da Ummanki idan har baki canja ra'ayinki ba zuwa yau, to ni zan wuce Kano mu hadu da Kawunki Dattijo a daura auren a can saboda bama so Abbanki ya sake rudewa ya zaci ko aure akan aure za'a miki."

Kanta yana ķasa ta kasa ce wa komai saboda luguden da zuciyar ta keyi.

"Se ki zauna cikin shiri. Munyi magana da Farfesa cewar in mun kammala magana da ke, gobe inshaAllah in an sauko a sallar Jumu'ah sai a daura, in yaso se ku taho ke da Bilal bayan an daura"

Shirun nata ya dan sosa mishi zuciya don haka sai ya koma lallashinta. "Ki kwantar da hankalinki Mamana kuma ki barwa Allah komai kinji? InshaAllah zabin da kikayi wa kanki ba zai cutar da ke ba. Kina tare da Allah, kuma kina tare da albarkar iyaye, baza ki taba tabewa ba. Yadda kika sadaukar da wani bari na rayuwarki don ki faranta mana, Allah kema ya faranta miki a rayuwar aurenki ya baki masu miki"

Ita kanta bata san yaushe ta fara kukan ba, ji tayi kawai ya dafa kanta yana cigaba da mata addu'o'i da fatan alheri.

Har ya bar falon bata motsa daga inda take ba. Tana jin su suna magana kasa-kasa da Umma a tsakar gida don kar Abba yaji kafin ya fice ya bar gidan.

"Adda kukan na ya isa haka. Idan kina yin sa sai naga kamar bada son ranki za'a yi abunnan ba. Yana sawa ina jin kaman ban kyauta miki ba"

Nan da nan ta dago kai ta fara share hawayenta "A'a Umma wallahi da son raina ne. Kar kiji komai dan Allah. Umma kin min komai a rayuwa idan nace baki kyauta min ba nayi wa Allah butulci"

Jin furucin diyar tata yasa itama hawaye suka taru a idon ta.

Oh Allah yarinyarta taga jarabawa kala-kala a 'yan shekarunta, ba ta da abun da zata ce sai dai tayi wa Allah godiya da a iya haka abun ya tsaya da kuma addu'ar Allah yasa wannan aure da za'ayi ya zama hanyar samun farin cikinta da ma aljannar ta baki daya.

Wunin ranar a daki tayi ta kasa tabuka komai don ji take kamar ba'a duniya ma take ba gaba daya.

**********************

Ranar Juma'ah sha daya ga watan Nuwamba a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai aka daura auren Ibrahim Mu'azzam Kabir da Hauwa'u Abubakar (Fareeha).

Lokacin da Anti Mami ta shigo dakin Umma ta sameta ta ce "An daura" ji tayi kamar a mafarki.

Kowa yasan kowace 'ya mace idan tana tasowa tana hasaso yanda aurenta zai kasance; shagulgulan da za'ayi, kayan da zata saka, mutanen da za'a gayyata da ma de sauran su. Wasu su kan faru wasu kuma basa faruwa.

Itama tayi ire-iren tunanin nan. Amma duk a cikin tunanin da tayi babu wanda yayi kama da halin da take ciki yanzu; ranar daurin aurenta, zaune a dakin Ummanta sanye da wata tsohuwar boubou, gidan shiru babu kowa saboda babu wanda aka fadawa gudun kar mutane su taru Abban ya zaci wani abunne ya faru.

Kuka take so tayi amma hawayen ma sun ki zuwa. Sai a lokacin ne ma ta fahimci ashe hawaye suna zuwa ne ma idan kana cikin nishadi, idan ka shiga wani tashin hankalin ma ba ka da sukunin yinsu.

Ba tare da bata lokaci ba Anti Mami ta sa ta shiga tayi wanka yayin da ita kuma ta tayata karasa packing din da takeyi tun jiya. Kayan ta ne rankatakaf Umma tace ta kwashe na kwashewa, wanda bazata tafi da su ba kuma a barwa su Qulsoom da Inaayah.

"Da gaske yanzu shikenan idan na tafi ba dawowa?" tambayar da tayi wa Anti Mami kenan lokacin data fito a wanka ta samu Anti Mami na zuge daya daga cikin akwati nan nata.

Anti Mami tayi murmushi. "Akwai dawowa mana Adda. Sai dai yanzu nan ba gidanku bane, kema kina da naki gidan don haka in kinzo a matsayin bakuwa zakizo"

Bata iya cewa komai ba saboda wani abu da ya makale mata a wuya.

A tsanake ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa kalar sararin samaniya da adon dorawa a jiki. Kwalli kawai ta saka sai man lebe ta sanya hijabinta wanda ya dace da kayan.

Sallah tayi raka'a biyu masu kyau sannan ta dade a sujudar ta tana rokon Allah da dukkan sunayenSa tsarkaka akan ya shige mata gaba akan wannan sabuwar rayuwar da zata shiga.

Tana idar da sallah sai ga Anti Mami ta shigo da murmushi a fuskarta tana mika mata waya.

"Ga mijinki"

Jin abun tayi banbarakwai, wai namiji da suna Hajara. Mijin ta wai? Ita ma wai tana da miji? Ya ilaaahi.

Hannu na rawa ta karbi wayar ta saka a kunnenta.

"Assalamu Alaikum"

Daga daya bangaren ya amsa mata muryarshi cikeda annashuwa. "Wa alaikum salam warahmatullah, Wifey"

Wani dumi ne taji ya lullube ilahirin jikinta.

"Kin gama avoiding din nawa ko kuma har yanzu da saura?"

Sunkuyar da kanta tayi kamar yana gabanta tace "Kayi hakuri". Abun da taga kawai ya dace tace kenan don tasan bata kyauta ba.

Tun jiya da Baba Zubairu ya kama hanyar Kano ta kashe wayar ta don a lokacin ji tayi bata son magana da kowa, so take kawai ita da zuciyar ta suyi hira. Tasan tabbas ya kira ta bila adadin bai sameta ba, tunda yanda batun auren yazo mata a bazata shima hakan yazo masa a bazata. Yanzunma tasan hakurin sa ne ya kare shiyasa ya kira ta wayar Anti Mami.

"Ai banyi fushi ba ma balle a bani hakuri. Kin taba ganin wanda yayi fushi a ranar aurensa?"

Murmushi tayi mai sauti wanda ya ji shi har cikin ranshi.

"Ban san ta yaya zan kwatanta miki halin da nake ciki ba a yanzu Fareeha. I am over the moon."

Yanda yake maganar sai taji kaman ya sammata kaso kadan daga cikin nashi farin cikin.

"Kinsan dalilin daya sa nazo Nigeria in the first place?"

"A'a"

"Nazo ne naji matsayata a rayuwarki tunda naji labarin cewa tsohon saurayin ki ya dawo. In fact, nayi tunanin ma cewa idan nazo ma breaking up kawai zamuyi.

Amma Allah cikin ikonSa, mai yin yadda yaso a lokacin daYa so, sai gashi labari ya canja. Cikin lokaci kalilan Ya canja labari, ni da nake tunanin na rasa ki har abada, sai gashi ya mallaka min ke a rana mai albarka.

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Wallahi na kasa dena yi wa Allah tasbihi Fareeha. Ki tayani mu gode maSa a kan wannan ni'imar da Ya mana"

Zuciyar Fareeha ta cika suntum jin kalamansa. Samsam bata hasaso wa kanta yin farin ciki ba a ranar nan, amma sai gashi Mu'azzam yana sata tana jin wasu abubuwa da bata san a ina zata kasafta su ba.

Murya kasa kasa tace "Alhamdulillahil lazi fadhallana ala katheerin min ibadihil mu'minin"

"Alhamdulillah. Allah ya bani ikon sauke nauyin da ke kaina Faree"

"Ameen"

"Allah kuma ya bani ikon faranta miki har karshen rayuwarmu"

Murmushin ta ya fadada "Ameen"

"Su Aaliy Mastoor da Baba Habu suna hanya in ma basu iso ba, zasu taho min da ke inshaAllah"

Zare ido tayi jin furucin sa. Ita da suke shirin zuwa tasha ita da Ya Bilal ashe shi har ya turo masu daukota.

"Uncle Captain...."

"Ehen!. Daga yau kuma sunana ba Uncle Captain ba."

"To me sunan ka?"

Ya juya idonsa. "Nima ban sani ba. A sama min wani sunan amma banda wannan. Ni ba Uncle dinki bane"

Yadda yayi maganar ya so ya bata dariya.

"Na bani na. Wani suna zan nemo maka kuma?"

"Kiyi tunani a hanyar ku ta tahowa, don nikam na tanadi sunayen da zan kiraki da su masu dinbin yawa"

Kunya ta kama ta, hakan yasa ta sunkuyar da kanta.

"To nagode. Allah ya saka da alkhairi"

"For what?"

"Daka turo masu dauka ta mana"

"Ki godewa Allah dan ma banzo da kaina ba."

Dariya tayi kafin ta katse wayar don tasan in de shine be ki suyi ta hira ba har ta isa Kano.

Sai bayan ta katse ne ma ta lura cewa wayar Anti Mami ce a hannunta don haka ta fita falo don ta mayar mata.

Nan ta samu Mama Uwani da Maman Walid sunzo don Umma ta sanar da su yau da safe cewar yau za'a daura auren.

A tsakiya suka sakata aka shiga yi mata naseeha wanda kusan dai duk tunatarwa ce. Duk yawancin abun da suka fada sun fada mata a lokacin da aka saka auren ta da Faruk; kusan wata daya suka shafe ana nasihar, ta yau daban ta gobe daban.

Ba'a jima ba su Baba Habu suka iso. Bayan sun sha ruwa an gaggaisa aka fito da kayan Fareehar don a saka a mota inda ita kuma ta shiga falon Abba don yi masa sallama.

Sai a lokacin ne tayi kuka jin yadda Abba yake ta jero mata addu'o'i da kalaman kwantar da hankali.

Taji tausayin shi matuka, kuma ita ma taji tausayin kanta don bata san abun da ke jiranta ba anan gaba.

Kuka take sosai lokacin da ta rungume Umma da Anti Mami. Suma addu'ar fatan alheri suka mata da samun albarka a aurenta.

"Ki share hawayenki muna nan tahowa ni da su Inaayah wani satin inshaAllah"

Ta ji takaicin cewa basuyi sallama da kannen nata ba, amma babu yadda ta iya.

Sun kama hanyar Kano tukunna ta kunna wayar ta. Sakonni kuwa suka mata salamu alaikum. Yawanci daga MTN ne da kuma gaisuwar Jumu'ah daga 'yan uwa da abokan arziki. Amma wanda suka fi yawa shine wanda Mu'azzam ya tutturo tsakanin jiya da yau.

'Ina kika shiga?'

'Can you believe this is happening?'

'Innalillahi I'm losing my mind'

'Faree na kasa bacci'

'Are you avoiding me?'

'Ko de auren dole za'a miki Fareeha? Kin fara bani tsoro'

'To koma auren dolen ne gaskiya sai dai kiyi hakuri there's no going back. I will make sure that this is the best auren dole you'll ever experience'

Wannan ya bata dariya sosai.

'Alhamdulillahi Alhamdulillah. Allah gatan bawa. Hauwa'u Abubakar I am finally finally yours. Ke ke kadai inshaAllah. Alhamdulillah'

Jikinta ne taji yayi dumi lokaci guda.

'I can't wait to see you Wifey. I love you. Immensely. From the depths of my heart.'

Kwantar da kanta tayi a jikin seat din yayin da wasu hawaye suka gangaro kan kuncin ta.

Babu tantama tasan wannan hawayen bana bakin ciki bane.

Ko da dan wannan farin cikin data samu na wannan lokacin aka barta, ta godewa Allah.

Alhamdulillah da Allah ya bata Mu'azzam. Tana fata ya zama haske a rayuwarta, ya kuma saukaka mata hanyar ta ta zuwa aljannah.

**********************
You guysssss. I'm in tears 😭❤.
I have no wordsssss. Please please drop hearts for my babies. May Allah bless their union Ameen.

Taku a kullum,
Miryaamah

PS: I think I won't be able to update anymore until mid September because I have like so many things going on right now and I have exams coming so I really need to get my head out of the fictional world and focus on reality. So inshaAllah zaku jini bayan na dawo hayyacina. Thank you for your unwavering support. I love love love you all fisabilillahi. Allah ya bar mun ku🤍.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top