3.
It's been a while. I'm really sorry.
3.
Ranar da Baffa Dattijo yazo, saida ya tsaya yaji bayani daga wajen Umma harda ma ita Anti Mamin. Don haka washegari da safe tareda Mamin suka bar garin zuwa Kano inda zata cigaba da iddarta a gidan sa. A cewar sa, wannan ne kadai abinda za'ayi wanda zai kade fitina tsakanin Umma da Abbansu Bilaal tunda har yace ta bar gidan. Umma bataso hakan ba, amma babu yadda ta iya.
Kamar daga sama ta ganshi. Shi da yace kwana hudu zaiyi sai gashi da hantsin ranar Alhamis.
Dayake duk yaran suna makaranta don haka ita kadai ce a falon tana sauraron rediyo. Shigowarshi ta razana ta don batayi tsammanin ganin shi a wannan lokacin ba.
Abun mamaki, da sallama a bakinshi ya shigo falon. Da qyar harshenta ya amsa sallamar tsabar kaduwa da kuma mamaki.
Ya samu waje ya zauna a kan 'yar kujerar falon. Umma ta zuba mishi ido. Mutuminda idan ya shigo falon a bakin qofa yake tsayawa yau shine harda zama. Yau tana ganin ikon ArRahamanu.
"Sannu da dawowa" Kawai tace a taqaice.
Kai ya gyada mata sannan ya cire hularsa. Sukayi shiru. Tana so ta tashi, ko da ruwa ne ta kawo masa amma tana tsoron kar ya gwasaleta. Don haka ta sake nade qafarta tana jiran jin alkaba'in daya shigo dashi.
"Ina Mariya?"
Jin tambayar tayi wata banbarakwai. Ita ke auren Mariya ne da zata san inda take? Ko kuwa dai da wata manufa yayi tambayar?
"Dama ba tare kukayi tafiyar ba?"
Idanu ya zubo mata kamar a lokacin ya fara ganin ta. Ya saukar da murya "Zuwa ina?"
Kasa gasgata abinda ke gabanta take. Wai yau Abban Bilal ne yake magana kamar an mishi saukan ruwan qanqara? Sai wani saukarda murya yake. Lafiyarsa kuwa? Koma dai meye manufarsa a shirye take da ta hadiye duk wani rashin mutunci.
Ta tabe baki. "Haka tace zata maka rakiya"
Ya yi wata doguwar ajiyar zuciya kafin ya miqe. Ya dauki hularsa, saidai bai maidata kanshi ba. "Idan bazaki damu ba keda yaran kuje Shira ku dan kwana biyu" ya fadi yayinda ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro 'yan dubu-dubu guda uku ya miqa mata "ga kudin mota sauran kuyi tsaraba".
Umma dai tsaya wa tayi tana jiran taji wani ya tabata ko wani dalilin da zai sa ta farka daga wannan mafarkin da ta keyi.
Dubu uku? Mene? Rabonta da....
"Ki karba mana"
Sai a lokacin ta dawo hayyacinta. Ya na nan tsaye ga kudin a hannunshi na dama yana miqa mata.
Hannu na rawa ta sa ta karba. "Angode"
Ya zura takalmansa "A gaida su Dada Yelwa" abinda yace kenan kafin ya fice daga sashen.
Ai yanda kasan an shukata haka ta zauna a wajen babu abunda bai zo ranta ba. Kodai bashida lafiya ne? Halan yaje an gano yana da wata mummunar cutar shine yake so ya lallabasu a rabu lafiya kafin ya mutu. Ko kuma dai wata muguntar yake shirin mata. Wataqil ma gidan zai siyar shine zaice taje gurin qanwar mahaifiyar ta ta.
Kanta ya kasa yin lissafin wannan al'amari. To gashi baice yaushe zata dawo ba. To zama zatayi har sai yace ta koma? Sa'ar ta daya su Lawiza a gidan Antinsu zasu kwana tunda washegari Mariyar zata dawo.
Ta nisa. Sam hankalinta bai kwanta da wannan tafiyar ba.
Allah shine masani akan komai.
Tana shiga daki sai ta dauro alwala. Sallah raka'a biyu ta gabatar, inda ta shafe lokaci mai tsayo tana addu'o'i cikin sujadarta. Roqon ubangiji take, wannan sabon al'amarin daya bullo, Allah ya sanya alkhairi a cikin sa. Kuma Allah ya bata ikon jure duk wani qalubale dazaizo ya wuce a 'yan wannan kwanakin. Hawaye jiqe a fuskarta a lokacinda ta sallame sallar. Ta sharesu, sannan ta jero wasu Azkaar din.
Zuciyarta ta mata sauqi bayan ta kammala. Don haka ta fara hada kayanta. Tunani iri-iri, na khairi da sharri sunzo mata amma duk tayi watsi dasu saboda nutsuwar da ta sauko mata.
Wajajen daya da rabi yaran suka dawo. Dama tuni ta tafasa musu taliya da miyar dage-dage sukaci sannan sukayi wanka. Fareeha ce ta shirya musu kayan nasu. Itama kanta ya kulle game da tafiyar gashi Umma bata mata wani cikakken bayani ba. Gashi gobe Jumu'ah akwai makaranta. Haka zasu haqura su tafi. Allah yasa dai ba wani abin bane ya sami Dada.
Wajajen qarfe uku sun shirya tsaf. Su Inayaah se murna ake za'aje ganin Daadama.
Umma ta shiga qofar Abban domin ta mishi sallama amma ta samu baya nan. Abinda ta dade batayi ba shi tayi. Taqaitaccen saqo ta tura mishi a waya tana sanar mishi cewar sun kama hanya. Ta kira Bilal a waya ta mishi kashedin cewa ya tabbata ya kwana a gida yau don batason a bar gidan ba kowa. A taqaice ya amsa da toh tareda addu'ar Allah kiyaye hanya.
Tashar dan Asabe mai Adaidaita sahu ya saukesu bayan sun tsaya a babbar kasuwa sun dan sayi tsaraba wa Daadan da sauran jama'ar gidan. Basu dade ba suka sami mota.
Qarfe hudu da rabi a Shira ta musu. Balaraba, 'yar bazawarar dake zama da Daadan ita suka samu a tsakar gida tana shara. Nan kuwa ta wurgar da tsintsiyar laushin ta yi kansu tana fadin 'lale marhabun'. Murmushi dauke duk a fuskokinsu suka isa gareta. Aka rungume juna. Inayaah kam saida aka dagata sama.
Hayaniyar da Daada ta jiyo a tsakar gidan ne ya saka ta daddafo ta fito daga dakinta.
"A'a Lami? Kune da almurun nan?"
Umma ta qarasa gareta ta riqo hannunta ta taimaka mata ta zauna akan tabarmar qofar dakin.
"Mune Daada. Ina wuni? Mun sameku qalau?"
Aka shiga gaishe-gaishe. Balaraba ta tayasu shigar da kayan su dakin ta dake gefen na Daadan sannan ta debo musu ruwa a randa a babban jug din qarfe. Kafin ayi haka ta zari hijabi akan igiya ta shiga maqota nemo awara da caccanga.
Nan ta barsu ana ta hira da Daada Yelwa. Inayaah sai tsokanarta take wai har yanzu bata miqewa kullum a durqushe kamar qwarya. Umma saida ta dan maketa, wai tana yiwa Daadanta ta tsiya. Sukayi dariya.
Bayan sallar maghreba 'yayan Balaraba Hassan da Hussaini suka dawo daga makarantar allo. Daada da Umma suna daki sun idarda sallah. Daada take tambayarta ko lafiya.
"Naga dai kamar yaran suna makaranta ko? Kuma na sanki bakya wasa da karatu, haka kawai bazaki tsigesu a makaranta ku taho nan ba"
Umma tayi murmushi yayinda ta tanqwashe kafarta. "Daada am banaso kina saka damuwa a ranki. Don dai kawai munzo sai kice wani abun ne ya faru? Toh babu abinda ya faru. Kawai naga kwana biyu bamuzo ba shine nace muzo mu kwan biyu. makarantar ba'a dade da komawa ba ma. Don haka don basuje na rana daya ba babu matsala insha Allah"
Daada ta kalleta tsaf, sannan ta jinjina kai.
"Toh Allah yasa. Maigidan lafiya dai ko?"
Umma ta hadiyi wani abu mai daci. Awa hudu kenan har yanzu bai bata amsar saqon data tura masa ba. Ko meyasa ma ta damu oho?.
"Lafiyarsa qalau. Yana gaishe ki. Alkamar nan ma da dabino shi yace a kawo miki"
Daada ta rausaya kai. "Allah sarki. Allah ya saka da alheri. Allah ya bude mishi qofofin arziqi"
"Ameen" kawai Umma tace sai kuma suka shiga wata hirar. Tanaso ta mata zancen Anti Mami, amma tunda taga Baffa Dattijo bai fada mata ba itama sai tayi shiru. Abune mafi sauqi Daada tanajin auren Mami ya mutu ta fashe da kuka. Daga nan kuma ba'a san me zai biyo baya ba.
Yaran kam suna dakin Balaraba Dan malele ne a tray yayi nasha-nasha da manja ga yajin tafarnuwa da su albasa. Ci kawai suke ana ta hira. Hassan da Hussaini suna ta basu dariya. Bayan sun kammala aka wawwanke hannaye aka yi sallar isha'i. Balaraba ta hau basu tatsuniya. Daya bayan daya bacci ya kwashesu. Fareeha ta taimaka mata wajen gyara musu kwanciya akan katifa. Ta musu addu'a ta shafa. Itama kwanciyar tayi.
Saidai bacci ya kasa ziyartar idanunta. Ta lula duniyar tunani. A ganinta tayi qanqanta ace tana fuskantar irin wannan al'amari a rayuwarta. Tunda take maganar arziki bata taba hadata da mahaifinta. Umma ta kan basu labarin cewa lokacin suna yara yana yawan wasa dasu. Wasu lokutan har daukansu yake ya fita suje su sha iska su dawo. Tambayar anan itace, me yasa yanzu baya sake musu fuska? Meyasa yanzu be damu da halin rayuwarsu ba? Be damu yasan meke faruwa a fannin karatunsu ba ko dai wani abu mai muhimmanci a rayuwarsu.
Wannan abu yana daure mata kai.
Tanajin yadda mutane suke bada labarin mahaifansu. Suce Baban su ya siya musu kaza da kaza, ko yayi musu wani abin alkhairin ko ya kyautata musu. Ita kam batada bakin bada wannan labarin. Don tunda tayi wayo ko alewa be taba bata ba balle aje ga manyan abubuwa.
Uwa uba ga cin mutuncin dayake yiwa Ummansu. Baiwar Allahn nan tana qoqari dasu. Cinsu shansu duk ita ce. Idan sun rasa wani abun zata yi qoqari taga sun sameshi. Amma duk wani alkaba'i a kanta yake saukewa.
Hawaye sukayi barazanar zubo mata.
Ko yaushe wannan zaman wake da manjan zaizo qarshe? Allah ya gani ita kam ta gaji. Don dai babu yadda ta iya ne.
Bata san sadda barawon ya saceta ba.
Washegari sassafe suka hau wanke-wanke da shara ita da Balaraba. Bayan sun kammala Balaraba ta barta da hada koko inda ita kuma taje siyo qosai da 'yar tsaala. Shine karin kumallon nasu.
Sun ci sun yi wanka kowa ya kintsa. Umma tace su je su gaida Goggonninsu da suke nan kusa. Ta aiki Hassan ya siyo mata kati don tun bayan asuba taga missed call din Baban Walid. A tunaninta Maman Walid ke nemanta shine ta yi amfani da wayar mijin nata. Dama wasu lokutan takanyi hakan.
Hassan yaje ya dawo babu kati a shagon kusa dasu. Ta yake shawarar idan sunje gidan Gwaggo Laraba sai ta duba anan.
Sun shirya kenan zasu fita wayar Umma tayi qara. Abbansu Bilaal ne. Gabanta yayi wani mummunan faduwa. Saida ta tattaro nutsuwarta sannan ta amsa.
"Salamu Alaikum"
Wata baquwar murya ce ta amsa. "Wa Alaikum salaam. Ina magana da Hajiya Lami ne?"
Hanjin cikin ta ya kada. "Eh ita ce. Wa ke magana?"
"Sunana Dakta Yusuf. Ina nan emergency unit a FMC Azare. An kawo maigidanki da misalin qarfe biyar na asuba. Barayi ne suka shiga gidan a daren jiya. An dai dan samu wani sabani a tsakaninsu. Amma sha'anin da sauqi tunda yana da rai. Amma yakamata kizo nan emergency ki........."
Ji tayi komai ya dauke. Kamar yadda nepa suke dauke wuta a tsakiyar fim. Qafarta ta mata nauyi. Don haka ta zube a nan tsakar dakin Daada. Wayar ta subuce a hannunta.
Ta lumshe ido.
Mafarki ta keyi ko? Kai saidai mafarki kam. Wannan irin baqin labari da safiyar Allah?
"Umma lafiya kike hawaye?" Qulsoom ta mata tambayar. Shigowarta dakin kenan domin taga shiru bata fito ba. Sai kuwa ta tsince ta a qasa dabas, hawaye na sintiri a fuskarta.
Umma ta taba fuskarta. Ai kuwa hawayen ne. Yaushe suka zubo?
Qulsoom ta tsorata. Don haka da gudu ta fita domin kiran sauran. Suzo Umma ba lafiya kuka take.
Sukayi cirko-cirko a kanta suna tambaya ko lafiya. Balaraba harda qoqarin yi mata fifita.
Umma dai ta kasa gane meke faruwa. Ta lalubo wayar ta ta wadda tuni ta rabe gida biyu a sanadin faduwar da tayi. Ta saka batir din ta kunna. Nan kuwa saqo ya shigo daga lambar Abban. Dakta Yusuf ne yake mata qarin bayani.
"Ku samo min mota" ta furta a hankali " zan koma Azare"
Su Fareeha suka kalleta cikeda mamaki.
"Umma wani abun ne ya faru?"
Ta girgiza kai a yayinda wasu hawayen masu bala'in zafi suka kwaranyo mata. "Ku kiramin mai Napep ya kaini tasha kawai" ta miqe a daddafe tareda sanya hijabinta.
A lokacin Daadama ta shigo dakin. Dama ta zagaya bandaki ne. Ganin su da tayi kowa da alamun damuwa a fuskarshi ya qara mata bugun zuciya.
"Lafiya?"
Umma tayi saurin riqe hannunta. "Lafiya Daada" ta qarasa da ita kan gado " waya akayi min wai barayi sun shiga gidan shine nakeso naje na ga yanayin abun."
"Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un" abunda duk suka furta kenan.
Daada ta kalleta "Shine kike kuka?"
Umma ta sake goge fuskarta "Daada ba dole nayi kuka ba. Sata fa! Me nake dashi ma balle anmin sata"
Daada ta jinjina kai. "Allah sarki. Dako sukayi miki. Zasu biyaki a lahira insha Allah. Allah ya dada karewa"
Duk 'yan dakin sukace Ameen.
"Umma zan biki" Fareeha ta furta lokacinda suka fito a dakin Daadan.
"Adda ki zauna da qannenki. Ni zanje na dawo yau insha Allah"
Ta riqe hannun mahaifiyar ta. "Kin tabbata ba wani abinda ya faru? Sata kawai sukayi?"
Wannan halin jin qwaqwaf din na Fareeha ta rasa a inda ta gado shi. Yarinya qarama amma abubuwa kadan ne suke wuce idonta. Tanada saurin gano bakin zaren lamari.
Umma ta numfasa. Wannan karon kam bazata barta ta ganota ba. Don haka ta qaqalo murmushi.
"Ba komai Adda. Idan naje zan kira a wayar Balaraba sai kuji halin da ake ciki. Ki tattara qannenki waje daya don Allah"
Fareeha ta mata rakiya zuwa bakin titi har sai da ta sami abun hawa sannan ta juyo ta dawo gida zuciyarta fal da tunani iri-iri.
Umma kam motarsu bata tashi da wuri ba. Bayan ta saka kati ta kira Maman Walid. Ashe dama kiranda ta mata bayan sallar asuba don ta sanar mata halinda ake ciki ne.
"Yanzu ma gamu nan a asibitin. Baban Walid ma yanzunnan ya koma gida." Inji Maman Walid din.
Umma ji take kamar ta zama tsuntsuwa.
"Yaya jikin nashi?"
"Ai wallahi Umma sun hana kowa shiga. Amma inaga idan kinzo za'a barki ki shiga. Don ba'a dade da dawo dashi daga dakin tiyata ba"
Tiyata? Subhanallah. Idonta suka cicciko da hawaye amma ta hadiye kukan.
"Kin kira Mama Mariya?"
Sai a lokacin ma ta tuno da ita. Nan ta yi wa Maman Walid sallama ta danna wa Mariya kira. Wayar tayi ta ringing shiru ba'a dauka ba. Don haka ta sake bugawa. Har sau uku tayi amma shiru. Ta tura mata taqaitaccen saqo akan ta dawo gidan ba lafiya.
Cikin sa'a motar tasu ta tashi.
Tunda ta tari abin hawa a bakin tasha tace ya kaita FMC take ta jero addu'o'i. Wasu ma bata san ta iya su sai a lokacin. Haka dai har ta isa asibitin.
Sauri-sauri ta qarasa jerin dakunan emergency din. A baranda ta samu Maman Walid zaune itada wasu mata guda biyu suma sun kawo marar lafiya. Suka gaisa sannan Maman Walid ta mata jagora zuwa wajen ma'aikatan asibitin dake bakin dakin.
Ta ce musu ita matarshi ce. Bayan dai sungama tambayoyinsu da sauran farillai aka barta ta shiga. Su bakwai ne a dakin , yana kan gadon qarshe an saka mishi qarin ruwa da.....jini? Subhanallah!
Qafafunta rawa suke a lokacinda ta qarasa wajenshi.
Idanuwansa rufe suke. Ga fuskarshi ta kumbura da alama sun mammakeshi. Ba qaton bandeji an nade gefen cikinshi dashi. Duk ya lalace.
Hawaye suka cika mata ido.
Bilal yana ina wannan danyan aikin ya faru?
Addu'o'i ne suke yawo a labbanta. Ta rinqa karantosu harsai da taji zuciyarta ta sassauta sannan ta samu waje ta zauna akan wata kujerar roba.
Ta share hawayenta kamin nan ta qura mishi ido. Wani tausayinshi ya mamayeta ga wani abu da batasan menene shi ba yana kai da komowa a cikin zuciyarta. Ta kira lambar Bilal ya fi a qirga amma taqi shiga. Abubuwa suka cunkushe mata a maqogoro. Addu'ar dai bata bar yinta ba domin da ita kadai ta dogara. Ita ce makaminta.
Tana zaune a wajen har likita ya zo. Dan saurayi bai wuce shekara 28 ba zuwa 29. Ya gabatar da kanshi a matsayin Dakta Yusuf kuma ya mata bayani cewa wuqa aka daba was Abban Bilal din a gefen cikin nashi. Hakan yasa ya zubda jini mai yawa domin lokacinda Baban Walid ya sameshi barayin sun dade da yin aika-aikar.
"Alhamdulillah dai wuqar bata huda mishi komai ba a cikin illa fatar shi wadda mun riga mun dinke." Cewar Dakta Yusuf. "Nanda wani dan lokaci zai farka insha Allah"
Umma ta share hawayenta. "Toh likita. Na gode. Allah ya saka da alkhairi. Amma wanene ya biya kudin tiyatar?"
Dakta Yusuf yayi guntun murmushi hadi da sosa qeyarsa. "Hajiya karki damu. Wani bawan Allah ne ya taimaka mishi"
Umma ta nisa. Na Allah basa qarewa a duniya.
"Allahu Akbar" ta jinjina kai. "Dan Allah ka hadani dashi na mishi godiya"
Ya sake yin murmushi "Toh insha Allah Hajiya. Allah ya qara mishi lfy. Sai dare insha Allah zan shigo"
Sukayi sallama ya qarasa zuwa duba wasu peshan din.
Har Azahar Abbansu Bilaal bai farka ba. Fitarta sallah ta ci karo da Maman Walid ta kawo musu abinci. Saida tayi sallar sannan ta zauna. Abincin dai cinsa kawai take amma batajin dadinshi. Tunaninta daya; ina Bilaal? Kodai barayin sun tafi dashi?
"Wai ya akayi Baban Walid ya sami Abban Bilaal din?" ta tambayi Maman Walid bayan ta kora shinkafa da waken da ruwa mai sanyi.
"Kinga Umma yaje masallaci da Asuba bai ganshi ba shine yace bari ya leqa yaga ko lafiya. Yayita sallama babu amsa shine ya kirashi a waya. Saiga waya tana ringing a bakin famfo. To anan ne ya gane ba lafiya ba ya qarasa dakin nasa ya sameshi nasha-nasha cikin jini"
"Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un" Umma ta fadi tareda hadiye wani abu me daci.
"Ai sa'a daya ma da ranshi. Godiyar dazamuyi wa ubangiji kenan. Amma kam abu beyi dadi ba"
Umma jinjina kai kawai tayi.
"Allah ya dada karewa dai" inji Maman Walid din. "Kuma fa Umma inaga babu abunda suka dauka"
Umma ta kalleta cikin mamaki. Wannan wani irin rashin imani ne? Ka shigo har cikin gidan mutum ka lahanta shi? Ba abinda ya maka?
"Toh ni da wannan zaluncin dama satar sukayi suka barshi da lafiyarshi" ta fada muryarta na rawa.
Maman Walid tadan dafata. "Insha Allah zai samu sauqi Umma. Kuma Allah zai biya mishi haqqinsa. Allah ya isar masa"
"Ameen" Umma ta fadi a sanyaye.
Sukayi shiru na dan wani lokaci. Kowa da irin tunanin dake yawo a ranshi.
"Mama Mariya shiru har yanzu ko lafiya?" Maman Walid tayi tambayar.
Umma ta girgiza kai "Toh Nima dai naga har yanzu bata kirani ba bayan missed calls din danayi mata gashi har saqo na tura mata amma shiru."
"Toh Allah yasa qalau"
Umma ta miqe tareda gyara zaman hijabinta. "Ameen. Bari in duba koya farka"
"Toh. Allah yasa a dace"
"Ameen"
*********
I know I know. I will go and update Alkyabba. 🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃🏽♀️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top