29.


29.

Da sallama a bakin sa ya shiga falon. Yana sauke idon shi a kanta ya tsaya cak ganin tashin hankalin da ke shimfide akan fuskarta. Ko sallamar ta shi ma kasa amsa masa ta yi, sai idanu data zuba mishi wanda babu komai a cikin su sai rudani.

Shi dai yasan da ya tashi a aiki ya tura mata sako akan cewa zai biya ta gidansu don haka ba zai samu dawowa da wuri ba. Kuma bayan da yayi sallar Maghreb ya sake tura mata wani sakon cewa zai dan yi dare. Don haka baya tunanin tashin hankalin dake bayyane akan fuskar ta na da alaka da rashin dawowar sa da wuri.

A hankali ya furta "Me ya faru?"

Wani abu mai nauyi Wafiyya ta hadiya kafin idanunta suka ciko da hawaye. "Ummi ce..."

Bata karasa maganar ba wani kuka ya kwace mata. Ai bai san lokacin da ya cike space din da ke tsakaninsu ba, ganinta kawai yayi a cikin rikonshi.

Kuka take sosai wanda hakan yasa hankalin sa ya tashi. Sai kuma a lokacin ne ma ya lura da cewa Ummi bata falon. Ba haka ya saba gani ba don tunda tazo gidan nan ne wajen zaman ta. Ganin hakan yasa zuciyar shi ta kara bugu.

"Kiyi shiru Wafee ki fada min meya sameta?" Ya tambayeta yana kokarin share hawayen da ya wanke mata fuska.

Cikin shesheka ta ke fadin "Tun safe wata kawar ta tazo ta dauke ta wai zasu je siyayyan kayan kitchen, shiru-shiru har la'asar banji ta ba na kira tace wai sun je salon wanke kai da yin lalle. To tun da lokacin kuma idan na kira wayar a kashe. Gashi har yanzu bata dawo ba"

Wani nannauyan numfashi Ashraf ya sauke.

Kai Ya Subhanallah.

Har ga Allah ya zaci wani mummunan abu ne ya samu Ummin don babu irin tunanin da bai yi ba a wannan lokacin, amma ashe abin ma da sauki.

Ya kalli Wafiyya ta kasan idonshi da guntun murmushi a bakinsa. "Yanzu dama saboda Ummi bata dawo bane shi ne kike kokarin bani heart attack?"

Kara kankame shi tayi tana matsar kwalla. "Kayi hakuri wallahi na tsora ta ne shiyasa."

"To shine hadda kuka? Ai Addu'a zakiyi Allah yasa ta dawo lafiya. Kuma ma dai Ummi kam ba bata zatayi a garin Kano ba, maybe wayar ce ta mutu. Don haka ki kwantar da hankalinki"

Ita ko ta san ba bata zatayi ba, kawai dai bata so ya gane cewa mahaifiyar tata ta bude wata sabuwar harkalla ce a yanzun don itama sai a safiyar yau dinnan ta fahimci hakan ganin an turo direba da katotuwar mota don a zo a dauketa.

Koke-koken da take duk dan kar Ashraf yayi tunanin wani abune idan Ummin ta dawo can dare, wanda kuma hakan take fata don idan ta sake ta kwana a wani wajen to ta zubar mata da mutunci a idon mijinta da ma zuri'arsa baki daya.

Sake narkewa tayi a jikinsa tana addu'ar Allah ya dawo da ita lafiya. Sannan kuma ta kudurci cewa a yau dinnan zasuyi maganar da suka dade basuyi ta ba, don ita kam bada ita za'ayi wannan aika-aikar ba. Ko ta bar mata gida ko ta koma inda ta fito, ita kam ta fara gajiya.

Cikin tausashiyar murya tace "In kawo maka tea? Nasan kaci abinci a gida"

Ya shafi gefen kumatunta. Wajen har yanzu da damshin hawayen ta. "Ya akayi kika san naci abinci a gida?"

"Kana ta warin miyar kuka"

Dariya ce ta kubce masa wanda ta ke jin shi har cikin bargonta. "Allah ya kamaki to ba ma miyar kuka naci ba"

"Ni dai abin da hancina ya jiye min kenan"

Ya lakaci hancin nata "Wannan hancin to ya fada miki karya. Yanzu dai bari naje nayi wanka don kin sa ma tsargu da kaina"

Ba'a son ranta ta bar jikin shi ba ta tashi ta shiga daki don hada masa ruwan wanka da kuma fidda masa kayan baccin sa. Bayan ta gama shirya komai tsaf ta bar shi don yayi wankan sai ta fito.

A falo sukayi kicibis.

Kallo daya ta mata ta wuce dakin da tayi masauki. Wafiyya bata jira komai ba ta biyo bayanta tare da turo kofar dakin tana saka mukulli a jiki.

Ummi ta dubi kofar sannan ta daga kai ta kalli 'yar tata. "Duka zaki min ne naga kin kulle kofa?" Ta tambaya a yayin da take warware mayafin jikinta wanda yasha jeren duwatsu masu walainiya da sheki.

"Ummi meyasa?" ta jefo mata tambayar kai tsaye.

Hajiya Huda ta tattare girarta tana cigaba da cire dankunnenta wanda suka dace da material din dake jikinta kalar sararin samaniya. "Meyasa me?"

"Meyasa sai da kikazo gidana? Meyasa bazaki gama harkokinki ba sannan kizo min?"

"Iyeh?" Ummi ta shiga tafa hannu tana salati "Wafiyya ni kikewa gorin gida? Kwata-kwata yaushe kika mallaki gidan da har zaki min iko akan shi?"

Wafiyya ta rufe idon ta tana hadiye wani abu mai daci.

Ta dade da sanin cewa mutum baya zabar iyayensa, kuma ko me suka zama a duniyan nan su ne dai iyayen naka baka isa ka canza su ba. Ita dai ga irin uwar da Allah ya bata.

Tun da tayi hankali ta san meye ciwon kanta ta fahimci dalilin daya sa mahaifinsu baya bari suje wajenta, ta fara mata wa'azi. Tun Ummin nata nayi kamar tana ji har ta kai ta kawo ta fara zagin ta a duk lokacin da ta ce mata Allah yace Annabi yace. Daga karshe dai sai da sukayi baran-baran Ummi tace ba ita ba su.

Kanwar Wafiyya, Mumtaz wacce a lokacin bata fahimci makasudin sabanin nasu ba ta so ta shirya su amma abun ya faskara. Sai da akayi wasu shekaru kafin nan Ummin ta sassauto ta fara neman su. A lokacin ta sanar musu cewa ta dena duk wasu dabi'un ta marasa kyau.

Amma daga baya da Wafiyya ta fahimci ba haka bane, sai ta hakura da nasihar ta koma yi mata Addu'a. Bata isa ta yanke alaka da ita ba tunda ita ce tayi sanadiyyar zuwan ta duniya. Kuma baza ta ce bata son ta ba don idan aka cire halayenta marasa kyau, akwai wasu masu kyau din wanda suke kara saka Wafiyya son mahaifiyar tata.

To amma yanzu kam abun ya fara wuce gona da iri.

"Ummi bana so muyi hayaniya dake a cikin daren nan. Amma ina rokonki dan girman Allah Ummi, ki duba darajar aurena ki taimakeni ki barni da mutuncin danake da shi a idon mijina. Idan kuma hakan ba zai yiwu ba, Ummi ki koma Abujanki. Mun gode da ziyara"

Tana fadin haka ta fice a dakin tareda jawo kofa.

Kitchen ta fada inda ta sha kukanta ma'ishi kafin nan ta wanke fuskanta a sink. Nan ta hau hade-haden shayi da dan abin tabawa ta wuce musu da shi daki.

Ta samu Ashraf ya fito a wanka har ma yayi nafilar sa ta shaf'i da witr.

"Ka min Addu'a ?" Ta tambaya tana ajiye tray din shayin qahwa datayi na larabawa wanda ta saka a 'yan kananun kofi masu ban sha'awa. A gefe ga cookies ga basbousa a dan karamin filet shima mai dan karen kyau.

A hankali ya tako rike da sallayar shi a hannu ya sumbaci saman kanta. "Kullum kina cikin Addu'a ta my love."

Dadi ya mamaye zuciyar ta.

"Nima kullum kana cikin tawa"

Jayota yayi jikin sa yana shakar sassanyar kamshin ta.


*******************


"How was the test?"

Fareeha ta lumshe ido tana jin yanda muryarshi ke saukar mata da wata nutsuwa.

Idan aka ce mata ta shiga uku to baza ta yi musu ba don yanda mutumin nan ya shiga zuciyar ta cikin lokaci kankani ya zauna daram-dam, abun ba zai daina bata mamaki da tsoro ba.

"Lafiya Alhamdulillah tayi sauki. Ya aiki? Kana ina yanzu?"

Murmushi yayi mai sauti wanda ta ji shi har cikin ranta. "Phoenix. At the airport. Nan da minti talatin zamu tashi. Na tsaya cin abinci ne"

A kanta ta lissafa lokaci sannan tace "Sai yanzu kake cin abinci?"

"Uhm"

"Ayyah sannu"

Yayi dariya "Meye abun sannu?"

"Naga wai har wajen tara baka ci abinci ba, shine ka ban tausayi"

Zuciyar sa ya ji ta matse. Ba wai don tace ya bata tausayi ba, sai don sanin cewa yanzu karfe taran ne a Arizona. Hakan na nuna cewa ta damu dashi kenan tunda har ta fara haddar world clock.

Dadi ya mamaye zuciyar sa.

"Yaushe zaku fara exams?"

Ta gyara kwanciyar data yi a kan gadon tana maida wayar zuwa kunnenta na dama. "Nan da sati uku"

Ya gyada kai yana kurban latte din shi. "That's good. How long will it take?"

"Sati uku shi ma. Akwai intervals a tsakani"

"Sai ayi hutu?"

Ta yi dariya. Yadda yayi tambayar kamar wani karamin yaro. "Eh sai ayi hutu"

"How long is the hutu?"

Zuciyar ta ta fara bugu. Kar dai zuwa zeyi? Ita kam bata tunanin zata iya sake tsayawa a gabanshi bayan haduwar su ta karshe.

A hankali ta amsa. "It depends. Dayake hutun session ne sunce four weeks. Amma komai zai iya faruwa a tsakani, zai iya karuwa"

Ya dan sosa girarsa yana tunanin yanda zai fada mata maganar da ya dade yakeson ya fada.

"Sati hudu ya isheki kiyi shiri?"

Goshinta ya tattare a rashin fahimtar tamabayar tasa. "Shirin me?"

"Auren mu"

Dif! taji numfashin ta ya dauke. In dai ba so yake ya kashe ta ba to bata ga dalilin da zai sa ya bijiro mata da irin wannan maganar ba a wannan lokacin.

Nan da nan ta tashi zaune. "Ehn?"

Abun ya bashi dariya. "Na tsorata ki ko?"

Tayi narai-narai da ido kamar yana kallonta tace "Dan Allah kace wasa kake"

"Bazan fada ba don ba wasan nake ba. Ke de kawai ki zauna cikin shiri idan kika koma gida hutu zakuyi magana da Baba Zubairu"

Me take shirin ji?

"Ni Hauwa'u na shiga uku a ina kasan Baba Zubairu?"

Yanzu kam dariya yakeyi sosai. "Baki shiga uku ba, ko daya ma baki shiga ba. Sannan ina neman auren ki ta yaya bazan san wanda zai bani ke ba?"

Hawaye taji sun cika mata ido.

"Uncle Captain Dan Allah kayi hakuri. Wayyo Allah na"

Sosai ta bashi dariya jin furucin nata. Yanda take rikicewa lokaci guda akan irin lamura yana sa jin wani sonta na kara ratsa shi. She is so adorable.

"Aurenki fa na ce zanyi Fareeha ba sace ki ba. Calm down" ya fada yana kokarin tsaida dariyar tasa.

Hakan daya fada yasa hawayenta gangarowa. "Please"

Ya rike lebbansa cikin hakoransa yana jin rokon da take mishi har cikin zuciyar sa "Meyasa?"

Ta hadiyi wani abu mai nauyi.

Ita kanta bata san me zata ce mishi guda daya ba don abubuwan da yawa.

Na farko ya mata shigar sauri, tana so ta kara fahimtar ko shi wanene tukunna kafin ma ta fara tunanin shiga wata sabuwar rayuwar da shi. Sannan muhimmin abun ma shi ne yanzu ita aure kwata kwata tsoro yake bata.

A ranta ta san cewa Mu'azzam ba zai cutar da ita ba, duk da wasu lokutan tana tunanin akasin hakan don haka ta yadda da Engr Faruk amma sai gashi daga karshe yazo ya dasa mata ciwo a zuciyarta.

A duk lokacin da tayi wannan tunanin sai wata zuciyar kuma tace mata Mu'azzam ba haka yake ba. A lokacin da Faruk ya tafi ya barta da tabo a zuciya, a lokacin da duniya ta mata kunci, a lokacin ne shi kuma Mu'azzam ya waiga yaga duk duniya babu wacce yake so sai ita, ya tsamo ta daga duhun data fada ya nuna mata cewa har yanzu ita din abar so ce.

Sai dai abinda bai sani ba shi ne har yanzu akwai sauran burbudin tabon abun da akayi mata a tattare da ita. Da shi take kwana da shi take tashi.

Wannan dalilin yasa take ganin ko da ta yi auren to wannan abun da takeji din zai zo ya zame mata matsala babba. Don duk yadda take tunanin watarana zata iya auren Mu'azzam, bata jin cewa zata iya kasencewa da shi ba tare da wancan abun da ya faru da ita a baya ba ya bijiro mata ba.

Hawaye ne suka ci gaba da zubo mata don ta rasa abin cewa.

Cikin sassanyar murya ya kira sunanta. "Fareeha"

Ta yi saurin hadiye kukan nata. "Na'am"

"Menene? Ki fada min"

Ta lumshe ido tana girgiza kanta duk da tasan cewa ba ganinta ya ke ba.

"Bakomai"

Ya karanci damuwa a muryar ta. Yana so ta bude masa zuciyar ta ya san me ke damunta, amma yasan har yanzu tafiyar ta su da saura.

Shi kanshi bai san menene ya shiga kanshi ba da har yayi wa kanin mahaifinsa Prof. Umar zancen Fareehar a watan da ya wuce, wannan yasa Prof din ya nemi wayar Baba Zubairu har suka tattauna lamarin.

Lamarin da yayi wa Baba Zubairun dadi matuka don kullum da tunanin Fareehar yake kwana yake tashi ganin yanda abubuwa suka rincabe mata lokaci guda. Sai gashi yanzu Allah yayi mata sauyi da mafificin alheri don yaji labarin komai a bakin Anti Mami kuma ta shaida mishi cewa yaron mutumin kwarai ne. Da ta sanar da shi cewa dan wajen Mama Ammah ne ma ya sake gasgata batun don baya manta alherin da dattijuwar ta musu a lokacin da dan uwansa ya kwanta a asibiti.

To yanzu ace irin wannan zuri'ar Fareeha zata shiga ai Alhamdulillah. Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki.

Jira yake kawai ta gama jarabawa sai yaji daga bakinta kafin su yi nasu shirin dan farfesa yace mishi su kam a shirye suke ko yaushe aka kirasu.

To yanzu gashi ita wacce ake ta daru a kan nata ta nuna alamun ba hakan takeso ba.

Mu'azzam ya ja dogon numfashi yana mikewa daga teburin tare da daukar hular sa wanda ta dace da uniform dinsa na matuka jirgi.

"Ina so kisan cewa bazan taba aikata  wani abu daya shafi rayuwarmu ba wanda ba kya so. Nasan nayi azarbabi wajen fara maganar aurenmu ba tare da ji daga gareki ba don haka kiyi hakuri na yi miki shisshigi"

"Uncle Captain ni bance...."

"Nasan ba ki ce ba amma na fahimci hakan a shirun da kikayi. Nasan bakiji dadi ba. Ki sani cewa ban yi hakan bane wai don ko opinion dinki bashi da muhimmanci a wajena ko wani abun, nayi ne kawai saboda Fareeha na kasa controlling feelings dina towards you. I am so in love with you, I can't wait to call you my wife. Wallahi ni ko bana kasar aka ce min kin zama tawa, hakan zai fi min komai dadi a rayuwa"

Kunya taji ta lullube ta wanda yasa ta runtse idanunta. Dadinta da shi kenan; yasan duk wata hanyar da zai toshe mata baki ya kuma hanata yin numfashi.

"Zan fada wa Uncle dina cewa a janye maganar zuwa lokacin da kika shirya."

Wani numfashi ta sauke wanda bata san tana rike da shi ba.

A hankali ta furta "Nagode"

"Hakan ba wai yana nufin ko na fasa bane. Ina kan baka na, kuma bazan zauna ba sai ranar da akace kin zama tawa"

Bata san lokacin da murmushi ya bayyana a fuskarta ba har ma ya fidda sauti.

Ji tayi kawai yace "Ina rokon Allah yasa na cigaba da saki yin irin wannan murmushin har karshen rayuwarmu"

A zuciyar ta ta amsa da 'Ameen' a fili kuwa tace "Zaka makara fa. Kar a baka query"

Yayi dariya yana saka hularsa a kansa tare da jan dan karamin akwatin sa. "Idan suka bani sai nace matata ce ta rikeni a waya"

Ho! Yau ita kam taga ta kanta.

"Uncle Captain sai anjima"

Ya sake yin wata dariyar. "Sai anjima Fareeha. Allah ya bar min ke"

*********

Karfe hudu saura suka fito a aji. Tun karfe daya suke ciki sai yanzu suka samu suka kammala. Irin malaman nan ne da basa zuwa aji sai an kusa fara jarabawa su zo su yi fixing lakcha. Abun da yakamata akace sun koyar a sati goma sha daya ko biyu, sai suce a kwana biyu zasu juye shi.

Ita dai Fareeha ta kasa gane irin wannan muguntar. Don in dai ba mugunta ba bata ga dalilin daya sa mutum yana karbar albashi ba amma ba zai zo ya sauke nauyin da ke kanshi ba a lokacin da aka kayyade mishi, sai lokaci ya kure yazo ya loda wa dalibai aiki.

Ko da me daya zasuji; karatun jarabawa ko kuwa zuwa lakcharsa?

Zaro wayar ta tayi a cikin jaka wacce ta saka a silent don ta duba lokaci. Dama dabi'ar ta ce in dai zata shiga aji to a silent take saka wayar ta.

Nan ta tsinci kira baja-baja a wayar tata. Hakan yasa ta razana ganin duk kiran daga Umma ne sai Anti Mami sai kuma Ya Ashraf.

Hannunta na rawa ta kai kan sunan Umma don ta sake kiranta sai ga kiran Ya Ashraf ya sake shigowa.

Tana dagawa taji yace "Kina ina?"

Da kyar ta iya furta "Ina makaranta"

"Eh nasan kina makaranta. Kina ta ina?"

Nan ta sanar da shi wajen da take. Ba'a yi minti uku ba sai gashi nan ya karaso. Tana ganin shi kawai taji hawaye sun wanke mata fuska.

"Meyafaru?" Ya tsareta da ido lokacin da ta shiga motar ta zauna.

Ta sa gefen hijabinta ta share hawayen ta. Ita dai tasan bai taba zuwa ya dauketa a makaranta ba haka kawai, gashi taga missed calls dayawa daga wajen Umma da Anti Mami. Don haka tasan kawai abun da ya faru. Abbanta ya tafi.

Kokarin share hawayen ta take amma kukan yaki tsayawa.

"Godiya ya kamata kiyi wa ubangiji ba kuka ba Fareeha. Abu ne da aka kwana ana Addu'a akai kuma sai gashi yanzu Allah ya amsa. Ki dena kukan nan dan Allah"

Juyowa tayi tana kallon shi da mamaki karara a fuskarta. Me yake nufi da furucin sa? Mahaifin ta ya mutu so yake ta yi ihun murna ko me?

Ganin kallon mamakin da take masa ne ya fahimci cewa bata ma san me ke faruwa ba don haka ya kara mata bayani.

"Dazu da Azahar Abba ya farfado daga Coma"

Sam kunnenta ya kasa gasgata abun da takeji.

Abbanta ya tashi? Ya ilaahil alameen.

Ai kaman an kara wa hawayen ta gudu, nan da nan gaban hijabinta ya jike. Daga karshe ma kife kanta tayi akan gwiwowinta.

Ashraf kasa ce mata komai yayi don ya san cewa a yanzu kam ba kukan bakin ciki takeyi ba.

Tsayawa yayi a Old Site suka dauki Yusrah wacce dama ya riga ya kirata akan ta samesu a wajen masallaci.

Kai tsaye hanyar fita gari ta nufa don kaf gidan nasu an watse an yi Azare. Wafiyya ma gidan Samha ya sauketa kafin yazo daukan kannen nasa.

Tunda kuwa suka fara tafiyar ba wanda yace komai a motar sai sautin radio kawai kakeji.

Ana kiraye-kirayen sallar Maghreb suka shiga garin. Kai tsaye gidan su Fareehar suka wuce. Anan suka tarar da Anti Bebi ita ma basu dade da isowa ba ita da Bappah Dattijo.

Umma na asibiti, Anti Mami ce kawai a gida da yaran.

Suna hada ido da ita kuwa ta fada jikinta sai wani sabon kukan. Ita ma Anti Mamin kuka take. Abu ne da aka cire tsammani akai amma sai gashi Allah ya kawo sauki.

Anti Bebi ce ta lallashe su da kyar sannan Fareeha da Yusrah suka shiga ciki don yin sallah. Sai a lokacin ne ma ta tuna cewa ko sallar la'asar batayi ba.

Bappah, Ya Bilal da Ya Ashraf suka shigo bayan sun dawo daga masallaci. Anan ne suke sanar da su cewa an canja wa Abban daki daga ICU ya koma amenity ward. Hakan na nuni da cewa da sauki kenan kuma an yi clearing dinshi zuwa gobe zai iya ganin mutane amma a halin yanzu Umma ce kawai aka bari a wajenshi.

Fareeha kam ranar batayi bacci ba. Haka ta raba dare tana sallah tana godewa Allah da ya dawo musu da mahaifinsu garesu.

Karfe takwas na safe a asibitin tayi musu gaba dayan su. Su Qulsoom ma duk da su akaje don Baba Zubairu cewa yayi a hakura da makarantar ranar.

Sai da suka jira likitansa tukunna yazo don yi musu wasu muhimman bayanai kamar yanda ya bukata.

"A bisa gwaje-gwajen da mukayi mishi a jiya mun fahimci cewa ya samu selective amnesia. Ba wani abun tada hankali bane, ya dan manta wasu abubuwa, wasu abubuwan kuma ya dan gauraye su, ma'ana yana mixing dinsu up. Hakan yakan faru idan an shiga coma.

Abin da nakeso da ku shine sai kun yi hakuri kuma kun bi shi a hankali, hakan ne zai nutsar da kwakwalwarsa waje guda har ma ya fara tuno abubuwa a yanda suke.

Amma idan akace sai an masa dole akan ya tuno wani abu ko kuma ayi wani musu da shi akan abin da ba haka yake ba, to zai iya jawo matsala sosai.

Idan akayi hakuri komai zai dawo daidai inshaAllah"

Bayan likita ya gama bayanin sa sukayi musabaha da su Bappah da Baba Zubairu kafin suka dunguma wajen Abban.

A zaune suka same shi a dakin wanda shi kadai ne a cikinsa ba tare da wasu majinyata ba. Ba sai an fada wa Fareeha ba ta san wannan aikin Bappah ne.

Umma ce a gefen sa da kofin kunu a hannunta wanda a daren jiya Ya Bilal ya kawo musu shi.

Abba kam ya rame dukda da din can ma shi ba mai kaurin jiki bane kamar Baba Zubairu, amma kana ganinsa kasan ya sha jinya.

Fuskar sa da fara'a yake amsa gaisuwar su.

Dama kafin su tafi asibiti sai da Anti Bebi ta gargadi Fareeha akan banda kuka, yanzu kuwa kokarin maida kwallar ta ganin da gaske dai Abban ya farka.

Ba mafarki bane, gashi nan a zahiri. Tana ganin shi, kuma ta na jin sa.

Allah sarki.

"Mamana"

Da sauri ta daga ido ta kalleshi. "Na'am Abba"

"Ya na ganki ke kadai? Ina maigidan naki?"

Shiru dakin yayi kaman babu kowa a cikinsa don duk cikinsu babu wanda yayi tsammanin jin hakan daga gareshi.

Fareeha kuwa daskarewa tayi a wajen don kwata-kwata ji tayi kwakwalwarta ta dena amfani.

Likita yace kar a tayar masa da hankali. Yace kar a tirsasa masa akan sai ya tuno wani abun.

Yanzu ita me zata ce mishi? Idan ta mishi karya, zuwa yaushe ne zai tuno cewa batayi aure ba? Zuwa yaushe ne zai tuno cewa fasa aurenta akayi kuma a dalilin hakan ne har ya kwanta ciwo?

Hawayen da take ta kokarin hadiye wa ne taji suna barazanar zubowa.

Kamar daga sama taji Umma tace "Yana nan zuwa shima inshaAllah. Ayyuka ne suka rikeshi. Yace a gaishe ka ai"

Abba yayi saurin gyada kai "Toh toh toh Masha Allah. Ya kyauta ai da ya barki kika taho"

"Yanzu dai jiki yayi karfi ko, zamu iya zuwa mu duba gona gobe?" Baba Zubairu yayi saurin fada don a mance da wannan maganar.

Abba ya kalleshi kasake "Yaya haka kuma? Daga samun sauki ka fara min zancen gona. In dai ba so kake ka karasa ni ba ka yi wa Allah ka bar ni na kara murmurewa"

Nan fa akayi dariya.

Daga inda take tsaye idanunta dana Umma suka sarke a cikin na juna. Tausayin su duka biyun taji a lokacin.

Akwai aiki babba a gabansu. Fatan ta kawai Allah ya basu ikon cin wannan jarabawar.

***************

Two words; Vote and Comment.

Taku a kullum,
Miryamah 🤍

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top