28.

Barkanmu da Sallah jama'a ta🤍. Allah ya karba mana ibadunmu yasa munyi karbabbe ameen ya mujeeb.
Here is the long awaited chapter. Even though it's half baked, I couldn't resist giving you guys a goron sallah.
Allah ya bar min ku ❤.


28.

MANHATTAN, NEW YORK

"Wai lafiyar ka kuwa?" Mujahid ya tambayeshi a lokacin da suke fitowa daga masallacin Masjid Manhattan inda suka gabatar da sallar Juma'ah.

Mu'azzam ya danyi murmushi yana sosa sajensa.

"Me ka gani?"

Mujahid ya daga girarsa guda daya "Ga abun da nake gani kuwa. Tun dazu sai murmushi kakeyi kai kadai kamar sabon kamu"

Murmushin Mu'azzam ya fadada "Sabon kamun ne ai" ya bashi amsa yana sanya hannayensa a aljihun jacket dinsa. Yanayin bazara wanda turawa ke kira da Fall shine ke karatowa don haka wasu lokutan akan yi iska mai sanyi da ratsa jiki shiyasa yanzu ya zama ma'abocin sanya jacket.

Mujahid ya girgiza kai jin amsar abokin nasa "Something smells very fishy. Tunda ka dawo na ga ka fara wani walwali kaman sabon ango. Ko dai ko dai?"

Yau sati daya kenan daya dawo daga Najeriya.

Idan aka ce a kwana bakwai dinnan a kan gajimare yake yawo bazai musa ba don gaba daya wani sakayau yake jin sa.

Abun kam yanzu ya dena bashi mamaki. Ya dade da karban lamarin Fareeha a matsayin alkhairi a rayuwarsa, amma bai kara kaimin rikon da yayi mata a zuciyar sa ba sai da ta furta masa da bakinta cewa ta amince da kudurinsa a kanta.

Ba kalmar so ta furta masa ba ko wani muhimmin abu, amma a lokacin ji yayi kaf duniya babu mai sa'a irinsa.

Ji yayi komai ya daidaita a rayuwarsa, don ya gama hango yadda zai cigaba da tsarata tare da Fareeha a cikinta. Babu tantama kuma yasan zatayi albarka.

Lallai abun da aka gina shi akan turbar Allah shi ne yake wanzar da natsuwa da kwanciyar hankali a koda yaushe.

A duk lokacin da yake makale da waya ya ke mata hira, sai yaji kaman an sake wani sabon Mu'azzam. Shi kanshi bai san cewa zuciyar shi zata taba son wata bayan Najmarsa ba, amma sai gashi kullum kara dilmiya yake akan Fareeha. Dariyarta, murmushin ta, kunyarta kai har ma da tsiwarta duk burgeshi suke. Musamman ma tsiwar ta. Wasu lokutan da gangan kawai zai kunno ta don kawai ta mishi wannan tsiwar, hakan na sashi nishadi matuka.

Ranan ta ga gano shi kuwa turbune fuska tayi kaman yana kallonta tace "Nifa gaskiya da ba haka nake ba Uncle Captain, kai ne ke sakani yawan masifa"

Dariya yayi a lokacin shima yace "Nima da can ba haka nakeba Fareeha, son ki ne ya maida ni haka"

Dif tayi kamar bata wuri.

Lokuta irin haka idan ya ji tayi irin wannan shirun dadi yakeji don yasan cewa kalaman shi suna tasiri a kanta. Nan bada jimawa ba kuma ita ma zata fara mayar masa da martani.

And he couldn't wait.

Tasbihi yayi wa ubangiji yayin da suka karasa takawa wajen motar Mujahid inda ya faka ta. Mahaifiyar Mujahid din ta gayyace su cin abincin rana a gidan ta don haka tare zasu wuce.

A hanyarsu ta tafiya abokin nasa yana ta bugun cikinsa don yaji mai ke faruwa da shi amma sam ya ki fada masa. Ya fi so sai magana tayi karfi tukunna ya sanar dashi. Kuma yana da yakinin cewa nan ba dadewa ba zatayi karfin. Burinsa kawai a mallaka masa Fareeha a matsayin matar sa. Don haka tana gama jarabawa zai tura kanin mahaifinsa yaje wajen Baba Zubairu; gemu yaga gemu.

***************

KANO, NIGERIA

"Hayati"

Ashraf ya dan lumshe ido yana juyawa akan kujerar da yake kai, muryar ta tana ratsa duka sassan jikinsa "Sai yanzu kikaga kirana?"

Wafiyya ta marairace murya "Kayi hakuri wallahi bana kusa da wayan ne shiyasa."

"Hm. Irin mamanta dinnan tazo ta manta da mijinta ko?" Ya fada muryarsa cike da zolaya.

Tayi dariya. "Ni na isa na manta dakai? In na manta da kai to ashe kuwa zan iya manta kaina"

Kaunar ta ne yaji tana kara ninkuwa a zuciyar shi. A kullum yana godewa Allah da ya bashi mata irin Wafiyya. Ga kyau ga iya ado ga iya kula da miji. Wasu lokutan har ji yake kaman mafarki yake saboda yanda take sashi farin ciki.

"To shikenan. Dama na kira naji yaya kike ne. Ki gaida Ummi. Nasan kafin na dawo watakila ta tafi"

Nan fa Wafiyya ta fara in'ina "Ehm dama....dama...dama kaga mun dade bamu hadu ba kuma gashi bata nan ma akayi bikinmu shine take tunanin ta dan kwana biyu anan din"

Shiru ne ya biyo baya bayan ta gama koro zancen nata.

Shi dai Ashraf tun da yake bai taba jin inda aka yi haka ba. Sati biyu da bikinsu surukar shi tazo musu kwana? Su da ko amarcin su ba su gama ba basu gama fahimtar juna ba? Ina aka taba yin haka?

Ya nisa yana dan kada kafafunsa kadan. "Okay bakomai. Akwai abun da kikeso in taho miki dashi idan zan dawo?"

Wafiyya ta saki wani numfashin da bata san ma tana rike da shi ba.

Ta san Ashraf na da saukin kai amma ko da wasa bata taba zaton cewa zai amince ba don itama da Ummin ta sanar da ita cewa hutu tazo mata sai ta ji abun banbarakwai.

Eh tabbas sunyi kewar juna don koda wasa babansu baya bari su je wajen ta, sai dai ita tazo ta gansu hakan ma sai a wani wajen amma ba a gidan shi ba.

Dalilin dayasa ma batayi rawar kan zuwa bikin ba don tana tsoron kar ayi mata wulakanci, sai dai ta bada guddumuwar ta mai tsoka sannan ta bi su da Addu'a.

To yanzu gashi sun hadu a inda babu wanda zai hana su haduwa, su sha hirarsu babu wanda zai ce musu komai. Hakan ba karamin dadi yayi wa Wafiyyar ba, sai dai batun kwanakin da zatayi a gidan tan ne take ta taradaddin su don akwai wasu halayen mahaifiyar tata da bata son Ashraf ya sani.

Ko ba komai yana ganin girmanta, yanzu idan tazo ta zauna mishi a gida ta nuna masa wani halin kuma girma ya zube fa? Shin darajar ta zai ragu a idon mijinta ko kuwa?

Sake sauke ajiyar zuciya tayi kafin nan tace "Babu komai. Allah ya dawo dakai lafiya"

"Ameen"

Ko da ya kaste wayar, sai da ya kara juya maganar a kwanyarsa. Wai Ummi zata kwana biyu? Kwana biyu rak ko kuma kwana biyun bahaushe?

Ya nisa.

Aiki ya same shi kuwa. Daga shi har Wafiyyar.

Cigaba da aikin sa yayi har zuwa lokacin tashi yayi. Sai da yayi sallar la'asar tukunna ya tsallaka kasuwar tarauni yayi wasu 'yan kananan siyayya kafin ya kama hanyar gida.

Da sallama a bakinsa ya tura kofar gidan nasa ya shiga.

"Wa alaikum salam" yaji muryar mahaifiyar Wafiyya ta amsa mishi. Sai da ya cire takalminsa tukunna ya karasa ciki.

Kwance ya sameta a kan doguwar kujera da remote a hannun ta. Idon ta na kan TV inda take kallon wani diramar Nollywood. Kanta babu dankwali, gashin kanta mai tsawo da sulbi wanda babu tantama daga nan Wafiyya tayi gado ta tufke shi ta zagayo da shi ta gaban wuyanta.

Saurin sauke idanunsa yayi yana zama akan kafet din parlor domin su gaisa.

"Malam Muhammadu, har an dawo?"

Bata tashi daga kwanciyar da tayi ba akan kujerar, haka zalika batayi yunkurin lullube kanta ba don ganin sa a cikin falon.

"Eh Ummi. Ina wuni? An zo lafiya?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah."

Suna cikin gaisawa Wafiyya ta fito a kicin. Fuskarta cike da fara'a ta karaso inda yake ta dauki ledojin da ke gabansa tana fadin "Sannu da dawowa"

Idon shi a kan duk wani motsinta. Tayi kyau sosai a cikin shigar ta na riga da siket na wata jar atampa. Dinkin ya mata kyau sosai ya kara fito da hasken ta.

"Yauwa sannu" ya amsa mata a hankali kafin nan ya tashi ya nufi dakinshi.

Baiyi minti biyu da shiga ba sai gashi ta biyo bayan shi da abinci akan tray.

"Ko na kai maka falo?" ta tambaya a marairaice.

Tsayawa yayi ya kallon yanda duk ta rasa abun yi. Sai abun yaso ya bashi dariya.

Idan ta kai mishi parlor kuma ina shi ina cin abinci a gaban Ummi.? Gashi bata ma ko muna alamun tashi daga wajen ba.

Kai kawai ya girgiza mata ya shige bandaki don ya watsa ruwa.

Kafin ya fito har ta ciro masa kayan da zai saka ta feshe su da turare ta ajiye akan gado.

Da alwalarsa ya fito don haka yana shiryawa masallaci ya wuce kai tsaye. Ko bayan ya dawo Ummi tana nan a inda ya barta, canjin daya gani shine kawai taci abinci don ga kwanukan nan a gabanta.

Sannu ce kawai ta gifta a tsakaninsu kafin ya wuce dakinsa don yaci nashi abincin shima.

A nan ya samu Wafiyya tana jiransa. Da alama anan ma tayi sallah don har a lokacin hijabin sallarta na jikinta.

Murmushi ta mishi a lokacin da suka hada ido, shima murmushin ya mata.

"Naga baka ci abincin bane. Ko wani abun kakeso?"

Zama yayi kusa da ita ya janyo ta jikinsa. "Ba abun da nakeso. Ke kawai nakeso"

Narkewa tayi a cikin rikonsa tana jin yanda zuciyarsa ke sassarfa a kirjinsa. Wani dadi ne ya kamata ganin cewa a dalilin ta ne zuciyar sa ke sauya bugu.

Sun dade a tare a haka ba mai cewa kowa komai kafin nan ya saketa.

Saukowa yayi a kan gadon ya fara bude flasks din don yaga abin da aka dafa. Har cikin zuciyar sa yana fatan yaga ba taliya bace amma ya makara. Ita din ce ma yau.

Ya dan ja numfashi kafin nan ya dauki plate dan ya zuba.

Har ga Allah ya gaji da cin taliyar nan. Kai duk wani dangin pasta ma ya fice masa a rai don tun da Wafiyya ta fara girki in banda macaroni, taliya da Couscous ba abinda take dafawa. Ranar har shiga store yayi ya leka yaga ko babu shinkafa ne, sai gata buhu guda ko budewa ba'ayi ba.

Sau dayawa yakan so ya mata magana amma sai ya fasa. Yana ganin kaman idan yayi hakan bai kyauta mata ba don ta kowani bangare bata rage shi da komai ba, fannin girkin ne de kawai.

Gashi kwana biyun nan yana sha'awar cin tuwo, amma ganin take-taken ta ya fahimci cewa kamar ba bata iya tuwon bane.

"Sauko mu ci" yace da ita bayan ya kai lomar taliyan bakinshi. Ba laifi tayi dadi don tasha kayan lambu da nikakken nama sai kamshi take, kawai dai ta fara ginsar sa ne.

Ba musu ta sauko suka fara ci. Bata yi loma uku ba sukaji an kwala mata kira daga falo. Ashraf kam sai da ya razana don baya tunanin ya taba ji anyi ihu haka a cikin gidansa. To yaushe zaiji daga shi sai 'yar matar sa?

Daga ido tayi ta kalleshi da wani yanayi.

Yayi 'yar dariya "Ya kike kallona? Baza ki je bane?"

Girgiza kai tayi tana ajiye cokalinta.

"Kayi hakuri yanzu zan je na dawo"

Gyada mata kai kawai yayi ya cigaba da cin abincin nasa.

Kafin ta dawo har ya fita sallan Isha.

A kitchen ya same ta bayan ya dawo daga masallaci tana dauraye kwanukan da suka yi amfani dasu.

"Ummi ta shiga ne?" Ya tambaya yana tsayawa dab da ita yana karban kwanon dake hannunta yana kifawa akan dish rack din dake kusa da shi.

Ta gyada kai "Na kai mata ruwan wanka. Kasan saboda ba amfani da dakin muke ba sai na manta ban kunna heater din ba. Shine aka sani dora ruwan zafi da daren nan" ta karashe maganar tana dan turo bakin ta.

Ashraf ya sunkuya ya dan sumbace ta kafin yayi murmushi.  "Aikin lada kikayi ai Wafee. Kema Allah ya baki masu miki"

Kunya ta kama ta. Can kasan makoshi tace "Ameen"

Tare suka karasa wanke-wanken sannan ya barta ta karasa kimtsa kicin din inda shi kuma ya koma daki dan ya sake watsa ruwa yayi shirin bacci.


*********

Ranar Jumu'ah karfe biyu ya tashi a aiki, kawai sai ya tsinci kansa da kama hanyar gidansu.

Tun bayan bikin sun je har sau biyu da Wafiyya, amma duk shigar dare sukayi kuma basu wani dade ba suka dawo gida.

Yanzun sai yaji yana kewar 'yan gidansu da hayaniyar su. Dukda shima yanzu gidan nashi cike yake da hayaniya a dalilin mutum guda.

Kwana na hudu kenan ake nema amma Hajiya Ummi bata ma fara zancen tafiya ba. Batun zama a falo kam ma Ashraf har ya hakura da shi. Kullum idan ya dawo idan suka gaisa zai wuce dakinsa.

Haka matar shi zata biyo shi da abinci su zauna su ci kaman wasu munafukai. Su da gidansu amma suna rayuwa kamar baki a cikinsa.

Ya saba idan ya dawo koyaushe Wafiyya tana kusa da shi, ko da nan da can ne baya so ta matsa. Yanzu ba dama ya riketa ko ya rungumeta sai dai idan sun kebe. Abun na ci mishi tuwo a kwarya kuma yana gab da daukar mataki.

Yanzu dai tuwo yakeson ci don ya dauki kudiri ko ba tuwo akayi yau a gidansu ba to sai fa an daura tukunya an tuka masa nasa.

Eh. Abun yayi tsanani har haka.

A farfajiyar ajiye motoci ya tarar da Babansa da wani abokinsa suna zaune a kujerun roba suna dan taba hira.

Sai da ya tsaya suka gaisa suka tambaye shi aiki da iyali sannan ya karasa ciki.

Yana sallama a falon Anti Bebi ya samu Samha da Fadila suna cin abinci. Wani dadi ne ya cika shi ganin tuwon shinkafa da miyar zogale ne suke ci. Ai ba shiri ya je kitchen ya wanko hannunsa yazo ya zauna ya sa hannu.

Ko bayan sun gama cin abincin anan falon suka baje kolin hira. Yusrah da Fareeha ma da suka dawo a makaranta suka jona.

Ba shi ya bar gidan ba sai bayan Isha.

Zuciyar sa fes ya nufi gidansa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top