27.

Inyeh!!!. Ku tafa min dan Allah😂

27.

Tsayawa sukayi kallon-kallo, kowa da abun da ke gudana a cikin ransa.

Shi dai Mu'azzam in banda tasbihi ga Allah babu abinda yakeyi. Nutsuwa ne da wani farin ciki yaji sun mamaye shi lokaci guda a dalilin ganin ta tsaye a gabanshi.

Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.

Wata guda kenan rabon da ta saurare shi, bai ma san ya akayi yayi hakuri har haka ba don yanda wani abu ke fizgar shi ji yayi kamar yayi tsuntsuwa yazo inda take ya fuskance ta.

Horon da ta mishi yayi tsanani matuka. Babu hanyar da bai bi wajen lallaminta amma ta kafe ta tsare, karshe dai abun da yake gudu shi ya faru. Blocking dinsa tayi.

Bata san hakan data yin ba kuwa kara tunzura shi tayi. Wannan ne dalilin daya sa ya kara jin dole-dole yazo ya same ta ya kalle ta cikin ido ya sanar mata da kudurinsa a kanta.

Ya san ya tafka kuskure wajen shigan saurin dayayi mata, yaso ace ya bita a hankali tukunna. Amma yayi gajen hakuri.

To yanzu dai koma menene, gashi nan yazo, kuma ba zai koma inda ya fito ba, sai ya aiwatar da abun da yayi niyya. Ko da kuwa ba yau bane.

Duk abun da zai faru, sai dai ya faru.

"Me kakeyi anan?" Ta furta a hankali.

Har yanzu zuciyarta bata daina sassarfa ba don sam ta kasa yarda da abunda take gani.

Murmushi yayi wanda ya kara masa kyau sannan yace "Wajen ki nazo". Ganin kallon rashin fahimtar da take mishi yasa shi karawa da "Nazo ne na bada hakuri akan laifin danayi miki wanda mind you, bansan menene ba. Amma dai punishment din ya isa haka dan Allah. Ayi min afuwa"

Kankance idon ta tayi akanshi wanda hakan yaso ya bashi dariya.

Bai san me yayi ba? Karar da ya kaita wajen Anti Mami kuma fa?

Gyara tsayuwar ta tayi sannan tace  "Ni ba abun da kayi min kawai dai...."

Ya karya wuyansa "Kawai dai me?"

Yanda ya tsare ta da idanunsan nan sai ta kasa fadin abun dayake ranta. Gaba daya sai taga ya mata wani kwarjini. Dukda dan durkusowar da yayi hakan bai sa sai ta daga kai take iya kallon shi cikin ido ba, don haka ta sunkuyar da kanta.

"Kayi hakuri idan abun da nayi ya bata maka rai. Kawai dai naga hakan danayi shi ya fi"

"Meyasa?"

Ta dan dago ta kalleshi kafin ta sake sunkuyar da kanta. "Saboda banga amfanin alakar mu ba"

Kallonta yakeyi a yayinda wani abu ke yawo a cikin zuciyarsa. Alakarsu bata da amfani fa tace? Lallai akwai aiki a gabansa.

Murmushin gefen lebe yayi yace "To za'a bani dama dan in nuna amfanin wannan alakar?"

Ji tayi kamar ta shake shi.

Ita ba karamar yarinya bace, don haka ta fara gano inda ya dosa.

Bazata iya bane kawai. Da wani ido zata kalli Anti Mami?

"Kayi hakuri dan Allah" muryarta har rawa takeyi kamar me shirin yin kuka.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daga kai ya kalli sama, sannan ya sauke.

"Mamish tace min zaki tafi gida gobe. Yaushe zaki dawo?"

To yanzu kuma rahoto ake bayar wa a kanta wato? Yau tana ga ikon Allah.

"Ban sa ranar dawowa ba. Mid semester break dinmu sati biyu ne, to kafin dai ya kare zan dawo inshaAllah"

Kwana uku take da niyyar yi idan ta je don suna dawowa da sati biyu zasu fara exams, tana so ta dawo ta yi karatu don wannan karon bata son carry over ko kwalli daya. Bata fada mishi hakan bane kawai don tana fata kafin ta dawo ya koma inda ya fito don da dukkan alamu ba wai yazo kasar bane da niyyar dadewa.

Koma yazo da niyyar dadewa shi ya sani. Bata da lokacin sa.

Jinjina kai yayi. "Allah ya kaimu"

"Amin"

Shiru ne ya biyo baya kafin nan yace "Kiyi hakuri na fito dake cikin daren nan"

Kiris ya rage ta juya idon ta. Sai yanzu yasan ya fito da ita cikin dare?

"Bakomai"

Mikewa yayi sosai daga jinginar da yayi a jikin motar sannan ya kwankwasa gilas din motar daidai wajen direba. Gani tayi an sauke gilas din wani saurayi ya dan leko. Murmushi ya sakar mata yana fadin "Barka da dare Antinmu"

Kasake tayi tana kallonsa yayin da Mu'azzam ya dan zungure shi.

"Barka kadai" ta furta a dakile.

Gani tayi ya miko wa Mu'azzam din wata 'yar jaka mai kama da gift bag.

"Gashi wannan tsarabarku ce ke da Yusrah. The trip was last minute so ban samu na tambayi me kikeso ba" Sai kuma yayi 'yar dariya "na manta ma ashe anyi blocking dina, ba damar tambayar ma"

Gaba daya ta rasa me ke mata dadi a lokacin. Ga haushin wancan mutumin da ya ce mata 'Antinmu' sannan shi kuma wannan harda wani guzurin tsarabar sa, gashi yazo yana ta mata murmushin sa mai kyau, ga dirin dariyar sa da ya shiga har cikin zuciyarta......

Innalillahi wa inna ilaihi raajiun.  Yau ta shiga ukun ta. Me ya hakan takeyi?

"Da ka barshi ma wallahi, mungode"

Wani kallon da yayi mata da ya nuna alamun cewa ba wasa yake da ita ba yasa ta saka hannu biyu ta karbi jakar babu shiri.

"Mungode" ta sake furtawa a hankali.

Ya dan saki ajiyar zuciya. "Nima nagode"

Dagowa tayi ta kalleshi har zata ce 'na me?' sai taga shima itan yake kallo da wannan kasalallen murmushin a fuskarsa.

Mutumin nan zai kasheta.

Kamar ba shi bane yanzu ya gama bata tsoro amma ji yadda yake mata sassanyar kallo?

Ta yi saurin ja da baya tana sunkuyar da kanta. "Sai da safe?"

Bata san meyasa maganar ta fito a bakinta da sigar tambaya ba.

Sake cusa hannayensa yayi cikin aljihunsa yana kallonta, yana so ya dauki hoton fuskarta a idanunsa ya adana shi a wani bangare na zuciyar shi dai ba san da shi ba a rayuwarsa sai yau.

Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.

"Sai da safe Fareeha. Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya"

Har cikin zuciyar ta taji dadin addu'ar sa. "Ameen. Ka gaida Mama Ammah"

Juya wa yayi yana kallon hanyar shiga gidan yace "Gata can ma tana tahowa"

Da sauri ta dago kanta ta dubi inda yake nunawa. Ile kuwa sai ga mahaifiyar sa na doso motar ita da Anti Bebi da Anti Balaraba. Ai kafin kace kwabo ta bace a wajen, nemanta kawai yayi ya rasa sai hango jelar mayafin ta yayi tana shigewa ta kofar baya.

Har suka iso wajen motar bai daina murmushi ba.

"Mu'azu idon ka kenan? Ashe zan sake ganinka?" cewar Anti Balaraba.

Ya dan sosa keyarsa yana dariya. "Ina wuni Ya Balaraba?"

"Ba wani ina wunin nan. Se kace wanda muka maka laifi. In ka tafi ko duriyarka ba'a ji, sai dai in ka zo. Gashi zuwan ma ba wani yi kakeyi ba."

Anti Bebi tayi dariya tace "To yanzu kam dai tunda Mama Ammah ta dawo ai zaki na ganinsa akai-akai."

Ammah dake kokarin shigewa motar tayi saurin cewa "A'a nifa ba dan ni yazo ba ingaya muku. Wani abun ne de ya kawo shi"

Musayar kallon da sukayi da Amman ya nuna cewa sun fara gano bakin zaren. Nan Anti Balaraba ta shiga washe baki. "Iyeh. To Masha Allah. Masha Allah. Tubarkallah."

Mu'azzam yaji wata kunya ta lullube shi. Don haka ba shiri ya musu sai da safe ya shige motar.

Aaliy Mastoor wanda yake dan kanin mahaifinsa ne ya ja motar suka fice a harabar gidan.

Zuciyar Fareeha bata dena bugu ba har ta shiga dakinsu.

Yau da su Anti Bebi sun ganta tsaye da shi me zasuyi tunani? Allah ya so ta.

Zarah dake ta danna waya lokacin da ta shigo tace "Zamu kwana gidan Adda Samhan ne yau ma ko kuma mu kwana anan? Naga an dan ragu a nan din"

Fareeha ta cire mayafinta ta fara fiffita da shi. AC din dakin a kunne yake amma gumi ne yake karyo mata.

"Duk yanda kukace. Ni inaga anan dinma zan kwana tunda gobe da safe zamu kama hanya inshaAllah"

Sai a lokacin Zarah ta dago ta kalleta jin yadda muryar ta ke fita kamar wanda ta yi tseren gudu "Lafiya?"

Girgiza kanta kawai tayi.

A daidai lokacin kuma Yusrah ta shigo dakin. "Jama'a ya batun abinci?"

Suka juya suna kallonta. "Ya batun abinci kuwa. Mun ci mun koshi"

"Ah! Shine baku jirani ba?"

Zarah ta harareta "Lallai ma yarinyar nan. Ki duba time fa kigani. Kusan awar ki daya a waje. Sai muyi ta jiranki har ki gama hirarki sannan muci abinci, yau ga kanwar babanmu"

Fareeha bata san lokacin da tayi dariya ba.

"To ni nasan time ya tafi ne ma?"

"Ina zaki san ya tafi idonki ya rufe"

Ta juya idonta "Kyaji dashi. Ni dai bari naje na nemo abinci"

"Allah yasa ki samu"

Sai da suka jira taci abincin tukunna suka nemi Baba Habu don ya mika su gidan Samha don ita tama dade da tafiya.

Haka suka saka Fareeha ta shirya jakar ta ta zuwa Azare akan da safen zata wuce tashar Mariri sai su hadu kawai da Ya Bilal da Qulsoom din a can.

Da suka zo kwanciya ne ta ke fadawa Yusrah cewa ta ajiye wani sako a cikin wardrobe dinta. "Idan na dawo zan miki bayani"

"Nifa bana son jan rai. Kuma kin sanni sarai zan iya budewa kafin ki dawo, dan haka kawai ki fada min"

Fareeha tayi murmushi. Ta san furucin nata duk salon wayo ne. "In baza ki iya hakura har sai na dawo ba to shikenan. Kiyi duk abun da kikeso dashi"

Yusrah ta dan tureta. Ta so ace taji bayanin amma Fareeha bata fada tarkon data dana mata ba "Baki hadu ba"

"E naji din"

**********

Umma tana gida lokacin da suka isa. Farin ciki wajen Fareeha baya misaltuwa. Ko da ta rungumeta, ji tayi idanunta sun cika tap da hawaye. Nan kuwa ta shiga yin kuka kaman an aiko ta.

Bilal hadda zungurin ta.

"Wannan idan baki suka shigo sai su zaci mun dauko ki daga prison ne ai. Kin dena kukan nan ko sai na kwade ki?"

Ta dan dago ta kalleshi idonta yayi fici-fici da hawaye tace "Yanzu dan kukan da mutum ya dade beyi ba ma baza'a barshi yayi ba?"

Umma tayi dariya tana kara damķe hannayenta cikin nata. Itama tayi kewarta sosai. "Yanzu Adda kukan har wani abun so ne da zakice a barki kiyi shi?"

Ta dan turo bakinta tana share hawayen nata da daya hannunta. "To ba shi bane hadda wani zungurina. Daga zuwan mutum za'a fara cin zalin sa"

"Baki ga cin zali ba ma tukunna" Bilal ya sake zungurinta.

Umma ta kwade hannunsa "Ya isheka kuma haka. Kazo ka wuce ka bamu waje".

Yana dariya ya shige dakin sa.

A tsakar gidan Umma ta shimfida musu tabarma suka baje ita da 'yayan nata gida biyu.

Inayaah ta raka Anti Mami da Ahmadi Jama'are ranar Jumu'ah don haka kwana biyun nan ita kadai ke wuni a gida babu kowa.

Asibitin ma da take zuwa ba ko yaushe ake barin ta tana ganinshi sai dai in suna bukatar a canja mishi kaya ko a goge mishi jikinshi shine zasu kirata. Don ta jaddada musu cewa ta fi so ace ita ce ke wannan dawainiyar da shi ko dan ta samu ladar jinya.

A irin wannan lokacin ne kawai ake bari tana kebewa da shi. Wani lokacin ta masa hira dukda tasan ba jinta yake ba, wani lokacin kuma tayi kukanta ma'ishi.

A kullum likitocin suna kara karfafa mata gwiwa kan cewa ba abun tada hankali bane, hakan yana faruwa duba da yanayin da Abban ya shiga.

Tana kokarin kwantar da hankalinta da kuma yin tawakkali. Sai dai wasu lokutan takan rasa ina zata saka ranta ta ji dadi.

Taga jarabawowi kala-kala a duniya, kuma da taimakon ubangiji tana cinye su. Wannan dinma tana fatan hakan.

Allah ya kawo musu dauki.

Sai bayan la'asar su Anti Mami suka shigo.

A bakin famfo suka sameta tana wanke kwanukan da sukaci abincin rana a ciki.

"Agogo sarkin aiki, daga dawowa har kin fara duty"

Murmushi tayi ta rungume ta "Oyoyo Anti Mami"

"Ni kar ki jikani da kumfan wanke-wankenki."

Suna dariya suka shiga falon Umma.

Anan aka baje tsarabar Jama'are.

Kayan ciye-ciye ne danginsu aya mai siga da su goruba Gwaggon Mukhtar ta bayar a kawowa Qulsoom sai kuma kayan kuka da su daddawa da kuma man shanu wa Umma.

Umma taji dadi sosai ganin cewa har yanzu Mami bata yanke zumunci da dangin mijinta ba dukda kuwa cewa a da anyi zama marar dadi, sai daga baya ne zaman yayi dadi. Ashe zaman ma ba mai dorewa bane, tunda ba'a dade ba Allah ya karbi wanda ake ta fada domin san.

Rayuwa kenan, kana naka Allah na nashi.

Tare duk suka raka Umma asibiti bayan Maghreb. Taso ace an barsu sun ganshi a yau din musamman ma dai Fareeha, amma masu aikin wajen sam suka hana. Haka suka hakura suka baro ta suka dawo gida.

Suna dawowa wayar Fareeha dake hannun Inaayah ta shiga ruri, ta ko miko mata wayar. Ta duba taga bakuwar lamba ce.

"Cigaba da game dinki kawai" tace tana shigewa daki don ta dan watsa ruwa.

Tana fitowa a wanka taga Inaayah a kan gado. "An sake kira fa Adda" Tana fadin haka sai ga wani kiran ya sake shigowa.

Dagawa tayi tare da zama a bakin gadon. "Hello?"

"Ina neman alfarma guda daya tak!" muryarshi ta daki kunnuwanta, wannan ya haddasa mata bugun zuciya mai rikitarwa. Nan da nan ta shiga rarraba idanu a dakin.

Ya cigaba da magana. "A taimaka kar ayi blocking wannan layin har zuwa ranar da zan koma please. Bana jin zan iya jure irin wancan horon bayan na riga da na sanya ki a idanuna"

Ehn? Me take shirin ji?

"Uncle Captain...."

"Please karki bani hakuri don bazan hakura ba Fareeha. Ban ga dalili ba. Ki bani dama kawai in nuna miki cewa alakar mu tana da muhimmanci"

Anti Mami tana falo. Zata iya shigowa a kowani lokaci. In ta zo ta ji shi yana wannan surutan fa?

Jikinta ya hau bari.

"Nima to ka bani dama in yi tunani dan Allah. Ka fara bani tsoro" ta fada da sigar roko. Ta fadi hakan ne kawai don ta samu ya kyaleta.

Wani tunani zata tsaya yi? Tun wuri ma ya nemi inda dare ya masa.

Wani abu yaji ya soki zuciyar sa. "Kiyi hakuri na zaburar dake, nima abunne ya min shigar bazata shiyasa kika ganni haka. But I promise you I'm not usually like this." Ya ja dogon numfashi. "How long do you need?"

Shirun da yaji tayi ne yasa ya kara nanata tambayar.

"Nima ban sani ba. Sai nayi shawara"

Ya dan mintsini karan hancinsa a rashin jin dadin kalamanta. "I'm not going to be the nice guy dazan ce miki ki debi dinbin lokacin da kikeso wajen yin tunani, don haka kawai ki bani lokaci nikuma nayi alkawari zan kyaleki har zuwa wannan lokacin"

Iyeh! Yau tana ganin ikon Allah.

"Shima duk zanyi tunani sai na sanar maka"

Yayi murmushi mai sauti. Yasan daman sai yasha wahala wajen shawo kanta, amma baiyi zaton abun zai kai har haka ba.

Shikam yaga ta kanshi. Tunda shi yace yaaji ya gani duk abun da aka masa ma dole ya shanye.

"Shikenan. I'll be expecting your call."

Ita ce ma zata kirashi? To tabbas yana ruwa, kusa da kada ma kuwa. Hnh!

Jin tayi shiru ya sa shi yi mata sallama. "Ki gaida Umma da sauran mutanen gida"

"Zasuji" ta na fadin haka tayi saurin kashe wayar tareda sakin wani gwauron numfashi. Waigawa tayi ta kalli kofa taga har yanzu dai a rufe take kuma ita kadai ce a dakin don tunda ta fara wayar Inaayah ta fice.

Yau da Anti Mami ta ji ta me zata ce mata? Ita yanzu duk yasa ma ta bi ta tsargu. Bata tunanin zata iya kallon ta a daren nan bayan bomaboman da ya gama saukar mata a yanzun. Don haka kayan bacci ta saka kawai ta bi lafiyar gado ta kwanta duk da kuwa ba baccin takeji ba.

Wasa-wasa ita da tazo da shirin yin kwana uku sai gata har kwana biyar bata ma da niyyar komawa. Hutun ta kawai takeyi tana sha'aninta. Hafsatu ma satin daya wuce suka samu hutu a makaranta don haka a gidansu take wuni.

Tun faruwar lamarin nan ita dai bata sake saka kafarta a layin su Hafsatu ba ma balle ta je gidansu, amma kawar tata kam kusan ko yaushe tana hanyar nasu gidan. Kuma kullum in zatazo sai ta kunso mata wani abun da tasan tana so.

Yanzuma zaune suke a tsakar gidan sun shimfida tabarma suna cin awarar da Hafsatun ta kawo danye inda ita kuma Fareehar ta soya musu ita tayi musu sauce din jajjage.

Bilal ne yayi sallama ya shigo sannan ya kalli yadda suka baje suna ta hidimarsu.

Hafsatu ta gaishe shi ya amsa sannan yace "Ko zaku dan tashi an yi baki"

Fareeha ta gyara dankwalin ta da hannunta wanda bata sa a cikin awarar ba tace "Su waye?"

Bai kula ta ba ya bude kofar falon Abba ya dan duba yaga komai tastas dukda baiyi tsammanin ganin akasin hakan ba don kullum se an share an tsabtace dukda ba'a cika zama a ciki ba sosai.

Fitowa yayi yace "Ki dauko ruwa ki kawo musu. Su Baba Habu ne"

Mikewa tayi tare da plate din awarar. "Su Baba Habun ne sai an shigo dasu? Se kace baki"

Ta mikawa Hafsatu plate din awarar sannan ta nade tabarmar hade da wanke hannunta.

Tana kitchen tana jera kofuna akan tray din da ta sako ruwa da Maltina taji shigowarsu.

Muryoyi uku taji, wannan ya sa ta gane su uku ne don a zaton ta mutum biyu ne.

Komawa fridge din Umma tayi ta dauko wata maltinar ta kara akai. Tunda Abba ya fara rashin lafiya kowa idan yazo gaishe su sai ya riko dan wani abu ya kawo, yawanci kuma Maltina din ake kawowa. Gata nan yanzu a dakin Umma himili guda.

Da sallama a bakin ta ta shiga falon.

Suka amsa mata a tare. Ta jiyo Baba Habu na cewa "Ai daga asibitin ma muke yanzu"

Kanta a kasa ta ajiye tray din a tsakiyar su don babu wani teburi a falon wanda zata daura a kai.

"Sannunku da zuwa" ta fada bayan ta mike tana kallon Baba Habu wanda ke zaune kujera daya da Ya Bilal. Ta waiga daya kujerar ma don ta gaishe su kawai ta tsaya cak!

Me zata gani haka?

Kallon wayar sa ma yake kamar bai ji shigowar ta ba, shi na gefen nashi ne wanda ranar ya kirata da 'Antinmu' shine ya amsa gaisuwar tata.

Bata iya sake cewa komai ba ta juya fuuuu ta koma falon Umma. Idonta har yaji-yaji yakeyi tsabar bacin rai.

Wai shin ana dole ne kam? Wannan wace irin masifa ce? Ace an hana mutum yayi numfashi ma?. Ba cewa tayi zata sanar da shi ba idan ta yanke lokaci, shine zai karkade kafafuwan sa ya wani biyota har gida?

"Lafiyarki kuwa?" Hafsatu ta tambaya ganin yanda ta shigo tana ta cika tana batsewa ita kadai.

"Ina fa lafiya" ta fada tana jijjiga kafa. Ita dai bata iya tashin hankali ba kuma bata son tashin hankali, amma a yanzu ji take kamar ta koma falon ta zazzage mishi duk wani abun da ke cikinta har sai yaji haushi ya tafi.

Tana cikin wannan tunanin Ya Bilal ya daga labule ya leko. "Zo" kawai ya ce da ita kafin nan ya juya ya bar falon.

Kamar bazata bi bayan shi ba. Sai da ta shaki numfashi tukunna ta daidaita bugun zuciyar ta sannan ta tashi ta fita. A kofar falon ta sameshi yana tsaye.

Ya kalleta tsaf sanye cikin hijabin ta sannan yace "Minti goma. Yanzu zamuje mu dawo" sannan ya mata nuni da falon Abban. Fuskarshi babu alamun dariya don haka ta shige ciki.

Nan ta fahimci su Baba Habu har sun bar falon ma, Mayen kawai aka bari shi kadai.

Eh Maye mana tunda batasan da me zata fassara abun da yake ba in bada maita ba.

Yanzu kam idon sa yana kanta har ta shigo ta zauna akan kujerar da ta fi nesa da shi. Hijabin da ke jikinta mai ruwan kasa ya kara haskaka ta ya fito da asalin kyauta dukda bata shafa komai a fuskar tata ba.

Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen

Wani ďan guntun murmushi yayi yana jinjina kanshi ganin yanda ta hada rai babu ko alamar murmushi a fuskarta 

Lallai ya jiko wa kansa aiki babba. Allah dai ya bashi nasara kawai.

"Ki dan saki ranki mana ko nima zan samu na shaki iska. The tension in the room is so thick"

Bata kula shi ba. Hadiye kalaman da take shirin amayowa take.

"Fareeha"

Yanayin da ya kirata yasa ta daga kai ta kalleshi. Idanunta suka sauka a cikin nashi. Nan taji wani abu kaman tartsatsin wuta ya watsu a duk ilahirin jikinta. Tayi saurin sauke su.

"Kiyi hak'uri. I'm really very sorry, amma hak'uri na ya kare"

A ranta tace 'nima nawan ya kare'.

Ya cigaba da magana. "Na so ace na baki lokaci kinyi tunani kamar yadda kika bukata amma kuma sai naga i'm running out of time..."

"Shine ka biyo ni har nan?" maganar ta fito a hasale.

Ya karya wuyansa, wanda hakan yasa ya kara fito da kyawunsa. "Na biyo ki daga wata kasa ma balle nan?"

Zuciyarta ce taji ta doka jin furucinsa.

"Dube ni nan" ya furta kalaman cike da umurni. Ai bata isa ta ki duban sa ba kuwa. Haka ta daga kai ta kalleshi.

"Ina zaman zamana, ban sanki ba, ban san da ke ba, Allah ya aiko sanadin daya sa naji labarinki, sannan Ya dasa min wani abu game da ke a cikin zuciyata. Ban taba ganinki ba Fareeha, ban san yaya kike ba; rana daya naji duk duniya babu wacce nakeson na kare, na share mata hawaye, na wanzar mata da farin ciki a rayuwarta, na mantar da ita bakin cikin da ta sha a baya, na So ta da zuciya daya, ba domin kowa ba sai domin Sa- kamar ke."

Wani abu ne taji ya wuce ta makogoronta wanda ya haddasa mata daukewar numfashi a lokaci guda.

"Haka nayi ta rainon wannan bakon al'amari a zuciyata har ranar da Allah yasa na sanya ki a cikin idona. A ranar da zuciyata ta bude min kofofin da bansan da su ba, ta raya wani abu a jikina da bansan cewa ya mutu ba. A ranar dana fara ganinki nasan this is it for me Fareeha. There's no going back."

Kankame hannun kujerar take don ji take kamar zata fadi kasa dukda kuwa a zaune take.

Ya Rahman Ya Rahim. Meke shirin faruwa da ita?

"Ba kece macen dana fara so a duniya ba, watakila kuma ba kece ta karshe ba, amma a halin yanzu ina jin wani abu game dake da ban taba ji ba, kuma bana so na dena jinshi ko da kuwa zai zama ajalina."

Saukowa yayi daga kan kujerar ya zo ya zauna a gabanta dabas, yana tankwashe kafafunsa.

"Gani nan nazo, I crossed the Atlantic and everything in between. Ina so a yau ki fayyace min ko zaki iya karban tayin soyayya ta ko kuma kina so na koma da aba ta"

Hawaye ne suka fara zubo mata, daya na bin daya. Bata san daga ina ba, bata san dalilin kukan nata ba, kawai taji tana bukatar yin hakan ne don zuciyarta ta cure waje guda tana barazanar fashewa.

**************
Not me swooning over my own character. Look at me just blushing up and down.

This Uncle Captain knows what he wants o. Let's see if our Adda also wants him.

Yanzu dai, sai an jima.

Ina jiran votes dinku da comments.

Taku a kullum,
Miryamah.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top