24.
24.
Murya kasa-kasa take karatun suratul Muzzamil. Idanunta wanda sukayi luhu-luhu saboda kukan da koyaushe yin sa take suna kan shafin da take karantawar.
A hakikanin gaskiya da can ita ba ma'abociyar karatun alkur'ani bane dukda ba laifi tana karantawa jefi-jefi, amma sanadiyyar faruwar abubuwa da dama a 'yan makoninn nan yasa ta rungumi littafin da dukkan zuciyar ta. Cikin ikon Allah duk sanda ta bude shi kuwa sai ta ji wata nutsuwa tana saukar mata, shiyasa tana jin ta fara tunane-tunane marasa amfani zata dauko ta fara karantawa. Gashi yanzu har ta kusa sauke shi a kwanaki kalilan.
Duk wanda ya shigo ya ganta zaiyi zaton cewa mutuwa akayi mata, kodayake abun da ya sametan za'a iya kiransa da kanin mutuwa. Ciwuka ne suka taru daya akan daya a cikin zuciyarta suka mata yawa, bata gama jinyarsu ba wasu sukazo suka sake hawa kai.
Tana ga kamar tayi kankanta dayawa ace tana fuskantar irin wadannan damuwowin a rayuwarta, amma kuma Allah ya riga ya rubuta hakan shine zai sameta a 'yan shekarun da take da shi.
Saidai gashi ta kasa nutsar da hankalin ta waje guda ta karbi komai a yanda yake. Kullum maganar da Anti Mami ke mata kenan, akan tayi hakuri ta rungumi komai a matsayin kaddara, amma ta gagara.
Cikin dare zata tashi tana kuka, ta rasa inda zata saka ranta taji dadi. Tunanin duniyan nan babu wanda bata yi, ta gudu ne ta je ta sake wata sabuwar rayuwar a wani wajen ko kuma ta hakura da rayuwar ne gaba daya ma kowa ya huta? Abun ya isheta.
Ba dama aga giftawar ta a unguwar sai anyi zancen ta, ko kuwa a mata kallon abar tausayi ko abar kyama ma wasu lokutan. Idan banda Maman Walid da Hafsatu, kowa a unguwar ya fice mata a rai tunda sunki yarda cewa ba'a mata abun da suke tunanin an matan ba.
Bugu da kari ga zancen fasuwar aurenta daya kara karade unguwar. Wasu ma har suna cewa bakin cikin hakan ne ya kwantar da Abban ta a asibiti.
Abubuwa goma da ishirin sun hadu sun jagule mata rai.
Ta rasa ta ina zata fara lallashin zuciyarta, da bata hakuri. To da wanne daya ma zata fara? Ciwon abun da aka mata, ko na rabuwar ta da Engineer ko kuma na mahaifinta wanda yake kwance ba'a san ko zai tashi ko bazai tashi ba?
Ajiyar zuciya ta sauke tana juya shafin zuwa shafi na gaba.
A dai-dai lokacin Anti Mami tayi sallama ta shigo dakin.
Tsayawa tayi a bakin kofar tana karewa Fareehar kallo. Duk da gajiyar data kwaso a makaranta sai taji kamar ta rufe ta da duka a lokacin.
"Adda lafiyarki kuwa?" ta fada a fusace.
Fareeha ta dago idanunta ta sauke akan kanwar mahaifiyar tata.
"Yau din ma bakiyi wankan ba wato?"
Ido Fareeha ta cigaba da zuba mata.
"Me kikeso ki zama ne Adda? Da wasu kalamai kikeso nayi amfani dasu wajen lallashinki?"
Ganin zazzafan kallon da Anti Mamin take mata ne ya sa ta saukar da idanunta ta fara watsa da yatsunta.
Doguwar riga ce a jikinta mai laushi wanda ke jikinta na tsawon kwana uku kenan yau. Gashinta da rabon da ya samu kulawa daga gareta ta tattare ta cusa a cikin wata hula wanda daga ganinta zaka san itama ta dade bata ga ruwa ba.
Sam Anti Mami ta kasa gane wannan sabon yanayin da Fareeha ta tsinci kanta a ciki. Ace mutum da hankalinsa da komai amma ya gagara kula da kansa? Tayi fadan tayi masifar tayi lallami amma Fareeha sai dai ta zuba mata ido kawai. Tun tana bata tausayi yanzu kam abun haushi ya fara bata.
Da taga bata da niyyar amsa ta ne ta juya ta fice a dakin cikin bacin rai.
Har Fareeha ta sauke ajiyar zuciya kawai taga an banko kofar dakin an shigo.
Tana daga ido sukayi ido hudu da Bilaal.
Yau kwanansa uku kenan da dawowa garin, ya tsaya rubuta jarabawarsa ta karshe ne don haka bai samu ya taho ba a lokacin da aka kai Abban nasu asibitin. Tun da kuwa yazo yake sintiri tsakanin asibitin da gida, don duk wani aike shi yakeyi. Yanzunma bata san cewa ya dawo ba don tun safe ya tafi asibitin.
Fuskar sa babu alamar dariya yace "Ki tashi kiyi abin da aka ce ko ranki ya baci yanzunnan"
Makogoronta ne taji ya ciko da wani abu me daci. Ta bude baki zata mishi magana kawai taji ta fashe da kuka.
Runste idonsa Bilal yayi don har cikin ranshi yaji zafin kukan da take. Bai iya rarrashi ba, bai san wasu kalamai ake amfani da su ba wajen yin hakan ba don haka cigaba da tsayuwa yayi a bakin kofar yana jira ta gama kukan sannan ta aiwatar da abun da yace ta yi din.
Ganin bashi da niyyar ce mata komai kuma bashi da niyyar tafiya yasa tayi kokarin tsaida kukan nata. Cikin sheshsheka take fadin "Ya Bilaal bana jin dadin komai wallahi. Ko na shiga bandakin sai naji kaman na cika ruwa a bokiti na tsunduma kaina a ciki har sai na dena numfashi"
Zuciyar shi ne yaji da kara bugu da jin kalaman nata. Me yake shirin ji?
Cigaba da magana take hawaye na sintiri a fuskar tata. "Nagaji Ya Bilaal. Nagaji wallahi. Nikam gwara ma na mutu da wannan....."
Bata kai aya ba ta ga wani hasken taurari a cikin idonta. Ta kai sakwanni biyar kafin ta gane cewa Bilal din dauketa yayi da mari.
Cikin kidimewa Anti Mamin ta shigo dakin don dama turo shi tayi yazo ya yi wa Farihar magana ita kuma ta tsaya daga falon, kawai sai taji tafi.
"Meye haka Bilal? Daga cewa kazo ka mata magana sai ka mareta?" Da sauri tayi kan Fareehar wacce ta fara shidewa tsabar kuka. Riketa tayi a jikinta tana lallashi.
Bilal yana huci yace "Kina jin abun da take fada kuwa? Wai so take ta kashe kanta? Ya Allahu!" hannunsa ya sa ya shafo fuskarsa da wani yanayi.
Anti Mamin ma razana tayi da furucin nasa. Ta kalli Fareehar dake cikin rikonta da take ta sharbar kuka ga kumatun ta daya tara jini a dalilin marin da aka sharara mata.
"Yanzu Adda ashe duk islamiyyar da kikaje ta banza ce da har zaki iya wannan furucin? Duk nasiha da ban bakin da ni da Umma muka miki ashe duk baki jimu ba? Yanzu bazaki karbi kaddara ba ki samar wa zuciyarki sa'eeda shine har kike tunanin kashe kanki bayan kinsan hukuncin da zakije ki samu a lahira idan kin aikata hakan? Bakiyi tunanin halin da zaki jefa Ummanki ba a ciki da kannenki dama danginki gabaki daya idan hakan ya faru? Ashe damuwar da Umma take ciki yanzu bata isheta ba sai kin kara mata wata akai?"
Zuciyarta ne take mata zafi kamar zata fasa kirjinta. Girgiza mata kai kawai takeyi saboda gani take Anti Mami bazata gane yanda takeji ba a lokacin.
Mikewa tayi tana hadiye wani kullutu a makogoranta. "Ki tashi ki shiga kiyi wanka yanzunnan. Idan kin ga dama kuma ki kashe kanki a cikin bandakin"
Tana fadin haka ta ja hannun Bilal da tun dazu yake huci suka fita a dakin.
Kukan ta cigaba dayi ko bayan sun fice. Sai dai da taga bazai fishe ta da komai ba ta tashi ta shiga bandakin.
Baza tace ga lokacin data dauka tana zaune dabas a kasan bandakin ba sai da taji hayaniyar su Inayah sun dawo makaranta sannan ta tashi ta wawwatsa. Ita kanta tasan kawai dai tayi wankan ne ba wai don ta fita ba ko wani abu. Ko mai bata shafa ba ta zira wata doguwar rigar ta dauko hijabi ta saka.
A tsakar gidan ta taddasu suna ta hidimarsu. Anti Mami na daga cikin kitchen Qulsoom kuma na bakin kitchen din tana daka abu a cikin turmi. Inayah da Ahmadi da Ya Bilal kuwa sun shimfida tabarma a tsakar wajen suna ta surutunsu, fitowar ta ya saka duk suka zuba mata ido.
Kallo daya Bilal ya mata ya hango shatin hannunsa kwance a fuskar tata wanda har yanzu jazur take, ya dauke kansa yana hadiye wani abu mai daci. Ta bashi matukar haushi a yau din, amma kuma ta bashi tausayi.
Da zaiyi ido hudu da yaran da suka zama sune musababbin faruwar komai, da yau saidai ya kwana a cell don kuwa ba zaiyi wata-wata ba zai aikasu lahira. Bai san ma ya akayi har yanzu bai aiwatar da abun da ya ke kudurin yi tun sanda ya sami labarin abun da ya faru da ita.
Ikon Allah ne kawai ya ke aiki a kansa don da ba dan haka ba, ranar daya shigo garin sai da suji ya tafka wannan mummunan aikin kafin ma ya iso gida. Amma cikin ikon Allah zuciyar shi sai ta ke samun sassauci duk lokacin da ya ganta, tausayinta da kaunarta duk sai ya danne duk wani haushi da zafin da ya keji.
Zama tayi itama akan tabarmar tana jingina bayanta da bangon sashen Abban tunda a kofar shiga falon nasa suka yi shimfidin.
"Adda kin warke ne?" cewar Inayah da ke taya Ahmadi jagwalgwale a littafin sa.
Fareeha ta kalleta tana tattare girarta. "Dama banda lafiya ne?"
"To meyasa kullum kike daki? Kin dena kulamu kin dena cin abinci kin dena wanka. Shine Ummu tace wai ko aljanunki ne suka tashi oho"
Wani irin kallo Fareeha ta watsa wa Qulsoom wacce tayi saurin shigewa cikin kitchen din tana mikawa Anti Mami abinda ta daka mata a turmin.
"Qulsoom" Fareeha ta kira rai a bace.
Lekowa tayi ta tsaya a bakin kofar ba tare da ta amsa kiran da aka mata ba.
"Yaushe nace miki ina da aljanu?" Ta kafeta da ido.
Qulsoom ta dan juya idon ta. "To naga abun naki ne yayi kama da na masu aljanu"
Yanzu kam Fareeha harararta take. "Bakida hankali wato. Irin wannan mummunan fatan zaki yi min?"
Ya Bilal yayi gyaran murya cikin yi musu kashedi. Yaga abun nasu yana neman ya zama fada.
Yi tayi kaman bata ji shi ba. "To tunda abun da kike min fata kenan, Allah ya mayar da shi kanki"
Zaro idanu Qulsoom tayi tana dafe kirji. "Auzubillahi!!. Adda meyayi zafi? Ni fa ba wai fata namiki ba kawai naga....."
"Kawai kinga me? Shikenan mutum baza'a barshi yaji da damuwar da take damunsa ba sai ace aljanu. Allah sai ya saka min. Wannan ma ai mugunta ne da......"
"Ya isa to!" Ya Bilal ya daga muryarsa saman nata. Shiru tayi amma wani irin tafasar da zuciyar ta ke yi ne yasa hawaye suka fara sintiri a fuskarta. Inayah kam gaba daya jikinta ne yayi sanyi ganin yanda furucinta ya kawo hayaniya a tsakanin 'yan uwan nata.
"Yanzu kuma meye na kuka? Dukanki akayi ko me? Shikenan ke ba dama minti minti sai kin zubda hawaye saboda an tattaro duk damuwar dake cikin duniyan nan an dora miki ko?"
Nan da nan ya hau ta da fada. Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ita kuwa bata fasa kukan nata ba. Anti Mami tana jinsu a kitchen ko lekowa bata yi ba. Ita kam dama ta soma gajiya, gwara Bilal din ya mammasife ta ko zata dawo hayyacinta. Haba! Wata guda kenan ana abu daya.
"Idan so kike ki hadiyi rai ki mutu sai ki hadiya mugani. Mu dinnan da kika gani ance miki muma abun be dame mu bane? Idan mukace zamu yi rayuwa yanda kikeyi ya kike tunanin abun zai kasance? Da ba a hakuri ana fawwalawa Allah komai da gaba daya duniyar ai ta kife. Kina dai ganin Anti Mami mijinta kacokam ta rasa, ya tafi ya bar ta da marayan da bai ma gama sanin dadin ubansa ba, kinga ta hau saman fanka ta lankaye kanta ne? Da haka kowa yake tada hankalinsa kina tunanin da Umma ta kai inda take yanzu a gidannan? Wani irin abu ne bata gani ba a rayuwa, amma gashi duk yazo ya wuce. Yanzu da kike ta daukan zafi wani riba kikaci?"
Nuna ta yayi da yatsar sa "Wallahi ki shiga hankalinki. Idan baki sawa zuciyarki ruwan sanyi ba kin nemi gafarar ubangiji, zaki shiga uku wallahi. Baki san wani alkhairi bane yake tattare da duk abubuwan da suke faruwa ba"
Kukan yana kokarin shake ta tace "Wani alkhairi ne yake tattare da shigar Abba coma?"
Kama baki yayi yana kallonta. "Keh! Kar na kara jin kin yi furucin nan. Zaki ja da ikon Ubangiji ne?"
Wani abu ta hadiya tana share hawayenta. Gaba daya ranta ya dagule ta rasa meye yake mata dadi.
"Kiyi maza-maza ma ki cire wannan tunanin a ranki kar ki nisantar da kanki daga rahamar Ubangiji wallahi. Kina jina ko?"
A hankali ta gyada masa kai.
"Tashi ki je ki wanko fuskarki kuma ki zo ki taya Anti Mami aiki"
Wunin ranar haka ta yi shi sam bata jin dadi. Da yamma da zai kai abinci asibiti tace zata bishi, kamar yace ta zauna sai kuma ya amince.
A napep suka tafi kowa da abinda yake sakawa a ransa.
Ko da suka isa ta ga Umma, sai taji duk wata damuwa ta gushe mata, tausayin Umman nata yana mamayeta.
Rike juna sukayi a jikinsu, dukda Fareehar tasha kashedi a wajen Ya Bilal din kafin su isa akan in ta sake ta yi kuka sai ya babballata. Haka ta shanye kukan daya taso mata, ta makale a jikin Umman nata.
Tare suka ci abincin, suna hira sama-sama don har yanzu Umman kawai ake bari ta shiga wajen Abba a ICU din.
Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar Maghreb ta dawo ta bar Ya Bilal din acan.
Bayan sunyi sallar Isha sai ga Anti Mami ta shigo dakin da waya a hannunta.
"Ga Uncle Captain zaku gaisa zai tambayeki jikin Abba" Anti Mamin ta fada tana mika mata wayar dake hannunta.
Da mamaki ta karbi wayar tana karawa a kunnenta hade da yin sallama. Daga daya bangaren ya amsa mata da sassanyar murya.
"Kuna lafiya?"
"Lafiya kalau. Yaya aiki?"
"Aiki Alhamdulillah. Ya jikin Abba kuma?"
Numfashi ta ja sannan tace "Da sauki mun gode Allah" ba don ko tasan da saukin ba ko babu, tana dai fatan hakan. Don har rana irin ta yau bai farfado ba.
"Allah ya tashi kafadun sa yasa kaffarane."
Runtse idon ta tayi don ta hadiye hawayen da suke barazanar zubo wa tace "Amin mungode."
Mikawa Anti Mamin wayar tayi ita kuma ta karba ta fita. Tunda Abban ya kwanta ko kuma tace tun da take ma a rayuwarta, yau ce rana ta farko da suka taba waya da shi. Duk da kusan koyaushe tana ji suna waya da Anti Mamin, sai dai kuma bata san meyasa taji hakan ya mata dadi ba.
Su dai kam Allah ya azurta su da kirki, tunda dai mahaifiyarsa tayi tattaki tun daga Kano ta zo duba su, ba dangin Iya balle na Baba, kwarai sun ji dadin hakan. Sai dai su mata addu'ar Allah ya saka mata da alheri.
Qulsoom ce ta turo kofar dakin ta shigo tare da Ahmadi. Bacci yayi a falo shine ta daukoshi. A shimfidin da aka masa a kasa ta ajiye shi a hankali ta juya har za ta fita sai kuma ta dawo.
"Adda" ta kira ta a hankali.
Dago idon ta tayi daga kan wayarta batare data amsa ba. Hira sukeyi da Sajida tana bata labarin marin da Ya Bilal ya sharara mata a yau din, ita kuma tana ta bata baki da addu'ar Allah ya tashi kafadun Abba.
Duk hidimar nan da ake, Fareeha bata sanar da Sajida cewa an fasa bikin nata ba, balle ma ta fada mata dalilin fasawar. Bata san ya akayi ta kasa furta wa aminiyar tata halin da take ciki ba. Kawai cewa tayi an daga bikin sai Abba ya samu sauki, wanda hakan yasa Sajida cikin farin ciki da fatan cewa lokacin da za'a yi tazo hutu gida kuma zata samu bikin.
Cigaba da kallon Qulsoom din takeyi wacce gaba daya fuskarta tayi narai-narai.
"Kiyi hakuri akan abun da ya faru dazu"
Kallonta take ta kasan idanu tace "Meya faru dazun?"
Qulsoom ta hadiyi wani abu me daci. "Da mukayi fada a tsakar gida"
Fareeha ta mayar da kallonta kan fuskar wayar ta "Ni banyi fada dake ba. Ki je ki ya wuce"
Ajiyar zuciya ta saki kafin nan ta kara da "To dan Allah Adda ki dena mana irin haka kinji? Muma fa hankulanmu sun tashi akan abunnan amma bamu dena rayuwa ba. Dan Allah ki sassauto kinji? Munyi kewarki"
Hawayen da suka taru a kurmin idonta ne ya saka ta kasa dagowa ta kalli kanwar tata. "To Qulsoom naji kuma nagode. InshaAllah komai ya wuce"
Murmushi tayi sannan ta mata sai da safe ta fita.
Tana fita Fareeha ta kifa kanta a pillow ta saki kuka.
Ita kam yaya zatayi ne? Ta yaya zata ce musu ta kasa rarrashin zuciyarta? Ta yaya zata fahimtar da su cewa bata san yaya zata zauna tana walwala da jin dadi ba bayan gaba daya rayuwar ta ta jagwalgwale?
A haka ta kwana tana rai babu dadi.
*******
Zufa yaji hannunsa yana yi a lokacin daya ga ta tunkaro inda yake. Daidai da rana daya bai taba tunanin cewa zasu sake haduwa ba har ma ta ganeshi. A hakikanin gaskiya ma ya manta da cewa akwai wata Rahma ma a duniya, sai yanzu da aka kwada masa kira a tsakiyar siyayyar da yake a shagon Target. Trolley din ta take turowa wanda ke shake da kayan yara da takalma tana karasowa in da yake tsaye.
Ba zai ce me yake ji a lokacin ba amma za'a iya alakan ta shi da tashin hankali. A ce duk girman garin New York, a rasa wacce zai hadu da ita a irin wannan wajen sai yayar Misriyyah?
Murmushi da yaga tana yi ne ya dan sassauto da tashin hankalin daya ji ya shiga ciki.
"Ashe kai dinne dai. Har ina tantamar ko ba kai bane nace dai bari na karaso" ta fada tana haki don da alama kayan data turo sun mata nauyi.
Shima murmushin ya sakar mata amma ko kadan bana jin dadi bane. "In flesh and blood" ya furta a hankali.
'Yar dariya tayi sannan suka gaisa.
"Ashe dama ana ganinku a wani wajen ba a filin jirgi ba?" tafiya ta cigaba dayi tana tura trolley din nata don haka shima ya bita.
"Mu din ba mutane bane?"
Har yanzu dai murmushi ne a kunshe a fuskarta "I'm just messing with you"
Sosa girarsa yayi ya ce "I know"
Cigaba da tafiya sukayi a cikin wajen suna dan taba hira kadan, don Rahma kam ba dai surutu ba.
Gaba daya ya tsargu da kansa. Kwata-kwata ya kasa sakewa da ita. Yasan dai duk yanda yayi kokarin boyewa Ammah alakarsa da Misriyyah to itama haka tayi kokarin boye wa 'yan uwan nata, amma sam sai yake ganin kaman Rahmar tasan komai kawai tana gwada shi ne.
Bai ankara ba, bai san ya akayi ba kawai yaji ya furta "Yaya kanwarki kuwa?"
Juyowa tayi ta kalleshi da wannan murmushin nata "Tana nan. Ta samu gurbin karatu a New Zealand, ta na can haka yanzu"
Gumi ne yaji yana tsatsafo mishi lokaci guda. Daman dagaske take da ta ce zata bar kasar gabaki daya?
"Daman bata gama karatu bane?" Ya samu kansa da yi mata wannan tambayar.
Cigaba da tura trolley dinta takeyi suna sake kutsawa cikin wajen saida takalma. "Degree dinta na uku kenan yanzu."
Sai a lokacin ya tsinkayi wani daci a tattare da muryar Rahmar, ai kuwa bugun zuciyarsa ta karu.
Karfin hali yayi yace "Ah lallai. Haka take da son karatu?"
Juyowa tayi ta fuskance shi da wani yanayi a fuskarta. "Ko kadan. Kawai dai ta dauke shi kamar hanyar samun mafita a rayuwar ta. Duk sanda ta shiga wata matsala, sai dai kawai ta tsiri tafiya karatu wani wajen. To yanzu ma abun da ya ke faruwa kenan."
Jijiyoyinsa yaji sun mimmike cikin wani irin yanayi mai rikitarwa. Kara damke trolley dinsa yayi don sai yaji kaman zai fadi a wajen.
"Ba yanda bamuyi da ita ba wannan karon don ta zauna, amma sam taki yarda. Iyayenmu suna so tayi settling waje daya, ko da kuwa batayi aure ba, ace dai tana da permanent residence. Amma yau tana can gobe tana can, abun babu dadi"
Yawun sa ne yaji ya kafe, ya rasa me zece mata daya.
"Dalilin dayasa ma bamu daga hankulanmu sosai ba, duk inda taje akwai wanda aka sani a kasar ko a garin. This time around, we don't know anybody in New Zealand. Ita kadan ta take zaune"
Hadiye wani abu me daci yayi yana so ya tattaro duk nustuwar sa ya bata amsa amma sai tace "Kayi hakuri ina ta maka babatu, ina baka labarin dai bai shafeka ba. Kawai abun ne ya dade yana damuna, sai kuma gashi naga fuskar da na sani, I couldn't help myself"
Murmushin da tayi mishi, irin sa shima ya mayar mata. Wannan karon kam har cikin ranshi yayi murmushin don tausayin ta ne ya kama shi sosai.
"Karki damu. I know how it feels."
Jinjina masa kai tayi kafin ta tsaya da tafiyar tata. "I'm this way" ta nuna masa hanyar dazatayi wajen cin abinci domin tun azahar ta shigo shagon, yanzu kuwa kusan uku ake nema.
Sallama sukayi, bayan ya bata hakurin rashin 'yar uwarta da kuma yi mata addu'ar fatan alheri.
Har ya koma gida, bai daina jin wannan dacin a zuciyar sa ba.
Ya cuci Misriyyah, shine kawai gaskiyar maganar. Amma shi kansa yasan da ya aureta, da cutar ta da zaiyi sai ya fi haka.
A farkon haduwarsu kam ta shiga ransa, amma daga ranar da suka kulla alaka a bisa tafarkin shaidan, ya yakice ta a ransa. Na dan wani lokaci kawai yakejin dadin kasancewa da ita, bayan nan kuma bayajin komai game da ita.
Kuskurene sun riga da sun tafka. Sai dai su nemi gafara wajen ubangiji, kuma su nemi samun rahamarSa, wacce bata yankewa. Shi yanzu fatanshi, Allah ya bashi ikon aiwatar da abunda yake niyyar yi, kuma Allah ya sa albarka a lamarin.
Sallar Maghreba ya gabatar, kafin ya jawo wayarsa don neman lambar Mami. Da ya duba lokaci, sai yaga karfe dayan dare ne a Najeriya, don haka ya hakura.
Gobe zai gama hutunsa, ya koma bakin aiki. Idan ya sake samun wani hutun, zai tabo ta yaji inda maganarsu ta kwana.
*********
Masha Allah Alhamdulillah. I have a feeling the book is coming to an end, ko me kukace? A tsaya in the next two chapters or do you want more drama🤭?.
Nagode da guddumuwarku.
Taku a kullum,
Miryamah.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top