22.
Godiya dubu dubu ga mabiya Wagga littafi. Idan baku ban san ya zanyi ba 💞.
22.
Bacci take so tayi amma abun ya gagara. Bugu da kari ga kanta dayake sarawa tun dawowarsu a asibiti a dalilin dinkin da aka mata a kan nata. Buguwar da kanta yayi ne ya haddasa mata fashewar kai saidai Allah ya takaita abun iya fatar wajen ya tsaya be zurfafa ba don har su x-ray sai da akayi mata don a tabbatar. Hakan yasa likita ya bata shawarar samun ingattaccen hutu amma da alama abun ba zai yiwu ba.
Mutane ne ke ta kai komo a cikin gidan nasu don suzo su jajanta musu, abunka da zance marar dadi, labari duk ya game gari. Yanzu da wani abun alkhairin ne ya same ta ba lallai aji shi ba kamar yanda kowa ke saurin bada labarin wannan abun alhinin.
Wasu kam har sun kara Maggi a kai. Dukda cewa duk zuwan da masu jaje zasuyi Anti Mami sai ta kara jaddada musu cewa ba abunda ya samu Fareehan don su Hafsatu sun cetota kafin samarin su samu damar yin wani abun, amma hakan bai sa sun dena yada labarin cewa anyi mata fyaden ba.
Hakan ba karamin tayar wa Fareehan hankali yayi ba, amma babu yadda ta iya. Bata isa ta hanasu fadan abun da sukayi niyya ba, sai dai tasan ko ba dade ko ba jima, watarana gaskiya zata fito. Tana fatan Allah ya wanke mata wannan dattin da aka yaba mata. Amma kam ranta ya sosu.
Babban abun daya fi damunta shine taradaddin da take kwana da shi take tashi da shi. Hankalinta sam yaki kwanciya. Gani take yi kamar in ta kwanta mutanen nan zasu lallabo cikin dare su zo har dakinta su yi mata abun da sukayi niyya.
Ko da Baba Zubairu ya iso garin a washegarin faruwar abun, baiyi wata-wata ba ya hado kan 'yan sanda aka shiga unguwar aka tattaro Nazee aka tafi station da shi. Sai da ya sha bugu sosai sannan ya fadi sunan abokan nasa da kuma inda za'a samesu. Sai da aka kamosu tukunna hankalin Baba Zubairu ya kwanta.
A halin yanzu ma jira yake Fareeha ta nutsu su je police station din ta bayar da nata statement din.
Ita kam bata san me zata ce musu ba. Ko labarin ta gagara bawa Engineer dukda dai Anti Mami ta yi masa sharhi. Jiya da ya kira fashe masa tayi da kuka, abun da bata taba yi masa ba. Sosai hankalinsa ya tashi. Karfin hali yayi kawai ya fara kwantar mata da hankali da fada mata kalamai masu tausasa zuciya har ta samu ta dena kukan. Ya jadadda mata cewa yana tare da ita a kk wani irin hali kuma yana nan zuwa Azaren don ya duba lafiyar jikinta. A haka suka rabu zukatansu cike da alhini.
Turo kofar dakin da akayi ne ya saka ta saurin rufe idonta. Koma waye idan yaga tana bacci zai juya.
Maimakon taji an koma sai taji gefen gadon ya dan lotsa alamar mutum ya zauna a kusa da ita.
"Fareeha?" Muryar Hafsatu ta jiyo ta kirata a hankali.
Bude idanuwanta tayi ta sanya su cikin na aminiyar tata. Ta dan saukar mata da murmushi wanda bai kai har zuciya ba. "Yaya kika kara ji?"
Kallon ta Fareeha ta cigaba da yi dan bata san wani irin bayani zata mata ba don ta gane yanayin da take ciki a yanzu.
Hannu ta sa ta dan shafa bandejin da ke kan Fareehan wanda aka rufe dinkin da shi zuciyar ta tana kara karyewa ta kara da cewa "Sannu kinji? Sannu"
Fareeha ta lumshe ido wanda hakan ya bawa hawayenta daman gangarawa gefen fuskarta. Ta ina ma zata fara mancewa da wanann al'amari bayan ga tabo sun bar mata? Sannan ga askin da aka mata a gefen kai duk dan a samu a mata dinki me kyau.
Sun cuce ta. Sun ruguza mata rayuwa.
Rungumeta da Hafsatun tayi ne ta gane cewa ashe ta fashe da kuka ne.
A haka Anti Mami ta shigo ta samesu duk su biyun sai kuka suke.
"Haba Hafsatu. Ke da zaki rarrasheta ki kwantar mata da hankali, shine kika biye mata kuke koke-koke? Kukan da ba zai kare mu da komai ba?"
Karasawa wajen su tayi ta banbaresu. "Dan Allah ya isa haka. In dai ba so kike ki kara wa kanki wani ciwon ba Adda ki dakata da kukan nan. Abu ne ya riga da ya faru, babu yadda muka iya. Amma kuma idan kika duba abunnan ta wata siga sai kiga yazo da sauki tunda basu samu damar yi miki abun da sukayi niyya ba, ashe wannan bai ishemu mu godewa Allah ba Adda? Ba dan Ya so ba akwai wanda ya isa ya ceto ki a wannan lokacin? Ai kuwa kinga ya kamata ki gode Masa ki kara gode Masa bisa wannan gagarumin taimako da Ya kawo miki da kuma jarabawar da Ya aiko miki da ita."
Kokarin tsaida hawayen ta take amma ta gagara saboda maganganun Anti Mamin kara karya mata zuciya suke.
"Ki kwantar da hankalinki kinji? Allahn daya sakaki a cikin wannan halin Shi zai fitar dake. Maza share hawayenki kije kiyi wanka. Baba Zubairu na tafe zakuje ku bada statement a police station"
Da sauri ta girgiza kanta wasu hawayen suna kara kwaranyowa. "Ni kam ba zanje ba Anti Mami. Bana son ganinsu. Bana son tunowa. Dan Allah kice bazanje ba. Ni bansan me zanje nace ba. Dan Allah...."
Ita kanta yanzu Anti Mami sai taji kamar ta fashe da kuka don wani tausayin Fareehan ne ya kara shigarta. Jawota tayi jikinta ta fara bubbuga bayanta cikin sigar lallashi. "Yi shiru to ya isa. Zan ce mishi a dan barki ki sarara ko?"
Girgiza kai ta cigaba da yi "Nikam a'a bazanje ba. Bansan me zance ba Dan Allah kuyi hakuri"
A haka suka wuni suna abu daya. Da Baba Zubairu yaga abun da gaske ne sai yace a barta kawai shi yasan yanda zasuyi da 'yan sandan.
Haka ta wuni ranar in banda sambatu babu abinda take. Sai da Umma da Anti Mami suka saka ta a daki suna ta rarrashi da Addu'o'i sannan aka samu ta danyi bacci. Kafin Maghreb jikinta yayi zafi sosai. Ai ba shiri suka sake komawa asibiti. Nan suka kwana sai washegari da aka samu zazzabin ya sauko sannan suka dawo gida.
Tun da tayi wannan zazzabin kuma abun mamaki sai taji zuciyarta ta dan sassauto, ga wata sa'eedah da ta shige ta. Haka ta dukufa da kiran sunan Allah tana nemon taimakonSa a karo na ba adadi.
Ita ma Umman da ta ga ta dan yi sanyi sai hankalin ta ya kwanta.
A iya shekarun ta babu kalar tashin hankalin da bata gani ba amma wannan ya shallake komai da ta taba gani. Ance mutum yana manta zafin nakudar daya sha da zarar ya haihu, amma ranar da ta ga Fareeha a cikin wannan halin sai ji tayi zafin nakudar da tayi a haihuwar ta ya dawo mata sabo fil. Fareeha ake wa dinki amma sai taji kamar fatarta ake yankewa ana ajiyewa a gefe. Bata san ma ya akayi ita batayi irin sambatun 'yar tata ba don tana ga kaman tafi ta shiga tashin hankali. Karfin Addu'a ne kawai da zuciya irin ta mahaifiya yasa bata karaya ba a gabansu, amma har ga Allah itama ta kusa zautuwa a lokacin da al'amarin ya faru.
Ba abun da za'a ce dai kawai sai dai ayi wa Allah godiya.
An dan kwana biyu kafin nan Fareeha ta fara warwarewa har ma take da dan walwalan yin hira da 'yan gidansu. Hafsatu ta kan shigo mata akai-akai ta duba jikinta ta kuma tayata hira idan sauran yaran sun tafi makaranta. Wasu lokutan ta kan taho mata da wani abun tabawa amma Fareehan bata iya ci.
Rama kam ta riga da ta yita a cikin 'yan kwanakin nan ga wani duhun da tayi wanda ita kanta bata san daga ina yazo ba. Da su Anti Bebi da Yusrah sukazo duba ta duk sai jikinsu yayi sanyi. Yadda ta rame sai kace tayi jinyar wata da watanni ne, har Anti Bebi ta fara tunanin ko ta dauketa su tafi Kano sai kuma taga rashin dacewar hakan tunda dai a halin yanzu babu abinda take bukata a kusa da ita kamar iyayenta da 'yan uwanta. A haka dai suka tafi suka barta cike da tausayin ta.
Alhamdulillah ta fara samun sassauci game da abubuwan da takeji a ranta, sai dai matsalar ta daya yanzu shi ne yanda har kamar rana irin ta yau bata saka Engineer a idonta ba kuma bata samu wayar sa ba.
Tana so ta kira shi amma zuciyar ta ta riga ta gama raya mata cewa ba ita yakamata ta kirashi ba tunda ita ce ke cikin yanayi na damuwa, ita ya kamata a kira aji yaya take.
Haka tayi ta sake-sake game da lamarin daga baya kawai ta yanke shawarar kiran nasa don taji dalilin wannan shariyar tasa, tunda dama ba yau ya fara ba.
Abun mamaki data kira sai taji wayar a kashe. Taso ta dan tada hankalinta akan abun don har ta fara tunanin ko wani abunne ya same shi, amma sai ta yi wa kanta fada, tashin hankali ba nata bane a yanzu. Don haka sai ta lallashi zuciyarta ta kuma cigaba da Addu'a Allah yasa komai lafiya.
Ranar da suka dawo daga warware dinkin nata kawai ta sami wayarsa. Kamar bazata dauka ba, don ta dan ji zafin share tan da yayi a cikin kwanakin nan. Ita a tunaninta ko da birnin Sin yake yaji labarin abun da ya sameta ai ya bar duk abun da yake ya taho ya duba lafiyar ta, koba komai yanzu dai kiris ya rage ta zama matarsa. Amma shiru bai zo ba kuma be kira yaji ya ake ciki ba. Har da wani kashe waya kuma.
Ranta babu dadi ta amsa wayar tasa. Sai dai shima daga bangarenshi ta tsinkayi wani yanayi daga yadda ya amsa sallamar tata.
"Yaya jikin naki?"
"Da sauki Alhamdulillah. Yau naje an cire min dinki"
A razane yace "Dinki kuma? Dinkin me?"
Tattare girarta da tayi waje daya a dalilin rashin fahimtar tambayarsa wanda ya haddasa mata wani radadi akan goshinta, ta dan runtse idonta tare da sakin goshin nata. "Ba nace maka an fasa min kai ba? to anyi dinki ne a wajen, yau aka cire" ta yi masa bayani a takaice. Ko dai ya fara tunanin a wani waje daban aka mata dinkin?
"Uhm"
Uhm? Abun da zai iya ce mata kenan a halin yanzu?
Ranta ne taji ya kara baci.
"Engineer" ta kira shi a hankali don bata son ta nuna bacin ranta a wannan lokacin, za ta iya fashewa da kuka. Abu na karshe kuma da take so tayi a halin yanzu kenan.
"Na'am"
"Meyasa ka kirani?"
Ya danyi shiru kafin yace "Dama ina so naji ya jikinki ne"
Ta so ta amayar masa da abunda ke cikinta a wannan lokacin amma ta hadiye. Sai yau ne yasan ya tambayeta ya jikin ta? Ko ba shi bane mutumin da yayi ta lallamin ta a waya yana rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta akan gashinan zuwa ba? Ko akan kunkuru yake dai yanzu yaci ace ya iso.
"Jiki da sauki. Nagode Allah ya bada lada" tana fadin haka ta katse wayar ta cillata kan gado. A haka zasuyi auren yana mata irin wannan halin ko in kula a lokacin da take bukatar kulawa? Lallai akwai aiki a gaban ta.
Bata kara bi ta kansa ba ta cigaba da sha'anin gabanta. 'Yan dubiya da 'yan gulma dai har ila yau basu dena zuwa ba. Yanzu kam har ta dena fitowa ma su gaisa. Idan tana falo taji an shigo sai ta yi sauri ta shige daki ta kulle har sai sun tafi ta fito. Umma data ga haka batai mata magana ba don itama abun ya isheta.
Wajen karfe tara suna zazzaune a falon Umma sai ga Abba ya leko. Suka mishi sannu da dawowa kafin nan Fareeha ta fita zuwa kitchen don hada mishi abincin sa. Tana ji Umma ta bishi falonsa suna kus-kus dinsu, abin har ya so ya bata dariya. Saidai yanayin data samesu a ciki bayan ta shiga falon ya sa ta fara tunanin wani mummunan abu ya faru.
Da sauri ta ajiye tray din abincin a tsakiyar falon da zummar juyawa ta fita amma sai taji Abba ya kira sunanta. Ba shiri ta juyo ta fuskance shi.
"Zauna" ya nuna mata gefen da Umman ke zauna wacce ta kauda kanta tana fuskantar window. Ko ba'a fada wa Fareeha ba ta san kuka take.
"Adda"
"Na'am Abba"
Sai da yayi shiru na tsawon wani lokaci kafin ya fara magana "Bansan da wasu kalamai ko da wani yare zanyi amfani wajen rarrashinki ba a halin yanzu, saidai in ce ki yi Imani da Allah ki yi Imani da kowacce irin kaddara. Idan kikayi haka, za ki ci riba me dinbin yawa"
Gyada kanta tayi a hankali "InshaAllah Abba"
"Ina so ki karbi abun da zan sanar da ke a matsayin wata jarabawa wanda da ikon Allah, Allah zai baki nasara a cikinta"
Kasa bashi amsa ma tayi saboda yanda taji bugun zuciyarta ya karu. Me ya faru yanzu kuma?
"Dazu da Yamman nan Bappan Faruk ya kirani a waya, sun janye batun aure tsakaninki da shi Faruk din"
Numfashinta ne ya tsaya cak!
Me take shirin ji?
"Kiyi hakuri Adda. Kiyi hakuri" abinda Abban ya karasa fadi kenan domin shima muryar sa ta fara rawa. Tsallake su yayi a falon ita da Umma ya shige dakinsa ya turo kofar.
Wani abu me nauyi taji ya dirar mata a cikin cikinta. Ta dauka a yanzu kam babu abin da zai kara girgiza ta saboda abubuwan da ta fuskanta a 'yan kwanakin nan, ashe kuwa da sauran ta.
Bata taba tunanin ko a mafarki cewa wannan shine sakamakon da zai biyo bayan abubuwan da suka faru ba.
Lallai Engineer ya bata mata rai kuma ta ji zafin abinda ya mata, amma ko da na minti daya bata taba tunanin rabuwa da shi ba ko fasa auren sa akan abun da ya mata domin ta riga ta karbe shi hannu bibbiyu kuma tayi shirin zama da shi a ko wani irin hali.
Shi ne zai mata haka?
Wannan shi ne tukwuicin soyayyar data nuna masa? Wannan ne sakamakon yarda da amintar da tayi da shi? Wannan ne ladan da za ta samu na mika masa gaba daya zuciyar ta?
Hasbunallahu wa niimal wakeel.
Hawayen taji sun taru a kurmin idonta tayi saurin barin falon don bata so Umma tagani, dukda ta riga ta san sai tayi kuka.
Tana shiga falon Umma tayi saurin daukar wayar ta akan kujera ta shige dakinsu.
Sintiri take a dakin tana kokarin kirar wayar a karo na ba adadi amma sam taki shiga. Sai da ta ga abun yana nema ya zautar da ita sannan ta ja gwauron numfashi ta sami waje ta zauna a bakin gado.
Tambayoyi ne fal a cikin kanta wanda bata da wanda zatayi wa su sai shi din.
Wani lefin ta masa ne ya fasa ko kuma akwai wani kwakwaran dalili? Ya fasa aurenta ne dindindin ko kuma na dan wasu lokuta ne tukunna za'a dawo da zancen? Yanzu yaya zasuyi da kayan dakin da Abba ya siyar da kadarar sa yayi mata su duk dan a fidda ta kunya? Yaya batun kudaden da Bappah Dattijo da Anti Bebi suka kashe wajen bada nasu guddumuwar? Me mutane zasuyi tunani kenan yanzu idan sunji cewa an fasa aurenta?
Kanta ne taji ya mata nauyi tayi saurin rike shi a cikin hannayenta.
Da wanne daya zata ji? Ciwon da ke jikinta da zuciyarta ko kuma da wannan ciwon da Engineer ya haddasa mata?
"Wayyo Allah na" ta furta a hankali yayin da hawayen da take ta kokarin matsewa tun dazu suka fata sintiri a fuskarta.
A take a wajen taji wata tsanarshi ya shige ta muraran. Taji dama ace yana tsaye a gabanta yanzu ta wawwanke shi da mari ta haddasa masa wani ciwon da zai bar mishi tabon da koyaushe ya kalla sai ya tuna da ita.
Numfashinta ne ya fara yin sama-sama, nan tayi kokarin daidaita shi amma hakan ya faskara. Sai ma wani duhu dayake kokarin lullube ganinta. Kafin ta san abun yi ta ji jiri ya fara dibanta.
A haka su Inayah suka shigo suka sameta ta sume a kasan kafet din dakin.
Anti Mami ce ta yayyafa mata ruwa sannan da taimakon Qulsoom suka ciccibeta suka daura akan gadon suka lullubeta ruf.
Ranar kowa ransa ba dadi ya kwana a gidan.
Washegari Umma na shiga dakin ta da safe ta ja ta tsaya turus ganin Fareeha tsugune a gaban wardrobe dinta tana ta shirga kaya a cikin ghana must go. Bata ma lura da Umman dake tsaye a bakin kofar ba sai jido take.
Da farko Umma ta gagara gane me ke faruwa sai da ta nutsu ta kalli kayan sai ta fahimci kyaututtukan da Engineer ne ya bata a tsawon lokacin da ya shafe yana neman aurenta. Turaruka ne wasu kwalin su ma ya malkwade tsabar ajiya, da takalma, da gyalalluka da kuma atampopi. Haka tayi ta watso su cikin ghana must go din, sai da ta gama ta zuge sannan ta jiyo suka hada ido da Umman.
"Umma ina kwana?"
A maimakon ta amsa gaisuwar ta sai cewa tayi "Ina zaki da wannan kayan?"
Daidaita tsayuwar ta tayi sannan tace "Zan kai tasha ne. Zan mayar masa kayansa"
"Adda" ta kira sunanta cikin lallashi.
"Umma dan Allah kar ki hanani. Wallahi bakiji yadda zuciyata take min ba, inaga idan nayi hakan watakila in dena jin wani radadin"
Umma ta girgiza mata kai. "Ba hanaki zanyi ba, amma dai kinsan yanzu bakya cikin cikakken hankalinki, fushi ya rufe miki ido don haka bana so kiyi wani abun da zakizo kina dana sani akai"
Shiru Fareehar tayi don bata so su tsaya suna jayayya da Umman.
"Shikenan tunda kin riga kin yanke shawara. Allah ya bada sa'a" haka kawai tace ta shige bandakin ta.
Da kyar Fareeha ta jawo ghana must go din zuwa falo sannan ta shiga dakinsu neman cellotape. Ta kuwa same shi a cikin shirgin litattafan Qulsoom. Nan ta dawo ta nannade jakar tas sannan ta samu wata paper ta rubuta sunanshi baro-baro da lambar wayarsa da kuma garin da za'a aika mata kayan, sai a can kasa ta rubuta tata lambar ko da kuwa za'a tuntubeta idan shi ba'a same shi ba. Tana gamawa ta shiga wanka.
Wajajen azahar sai ga kiran shi yana shigowa. Katse wa tayi sannan ta saka wayar a silent suka cigaba da hirar da sukeyi da kannenta kamar babu abinda ya faru. Da ya gaji da kira ne sai taga ya aiko mata da sako.
'An kirani a tasha akan naje na karbi sako daga Azare, naje kuma ban gane menene ba'
Murmushin gefen lebe tayi sannan ta tura masa amsa. 'Kayan ka ne. Ka bude ka gani'
Ba'ayi minti biyar ba kuwa sai ga kiranshi ya sake shigowa. Wannan karon dagawa tayi sannan ta shiga daki ta turo kofar.
Tana jiyo hucin sa daga cikin wayar, wani abun mamaki sai taji wani dadi a ranta.
"Hauwa what is this?"
"Kayan ka ne na dawo maka da su. Tun da yanzu ka yanke duk wata alaka a tsakaninmu, ban ga dalilin da zai sa na cigaba da ajiyan su a wajena ba"
"All these while Hauwa, bakiyi amfani da su ba, kaman dama jira kike....."
"Dakata" ta tsayar da shi "Don't make me look like the bad person here. Don't you dare!" Bata san ma bata da kunya ba se yau.
"Hauwa?" Shi kanshi mamakin ta yake a halin yanzu.
Bata amsa kiran da yayi mata ba ta cigaba da magana. "Kafin na katse don Allah ina so na san laifin dana maka har ka dauki wannan hukuncin a kaina. Idan kuma bani da wani laifi to ka bani kwakwaran dalilin dayasa kayi hakan"
Shiru ne ya biyo baya, ba wai don bai gane tambayar datayi masa ba, sai dan be san amsar da zai bata ba.
"Hauwa......" ya kira muryarsa cikeda roko da lallashi.
Ita kam ko a jikinta, don ta riga da ta kai gacci. "Ina sauraronka"
"It's complicated Hauwa. Bansan ta yaya zanyi miki bayani ba. So many issues, my family, Hajiya...."
"Kar ka bani excuses dan Allah."
Mamaki ne ya kara kamashi. Yaushe Hauwa ta fara masa rashin kunya har haka?
"To me kikeso na ce miki? An min karfa-karfa babu yadda na iya. Kisani cewa yadda kike cikin tashin hankali nima haka nake ciki Hauwa"
Jinjina kai tayi tana murmushi mai daci.
"A iya sanin da na maka Engineer ina tunanin babu wata karfa-karfar da aka isa a maka a kaina ba tare da ka turje ba sai dai don kaima ka riga da ka yanke shawarar rabuwa dani. Sai yanzu na fahimci hakan bayan nayi tunani akan abubuwa da dama.
"Lokacin da ka samu labarin abun da ya faru da ni, na yi imani akan cewa kaine mutum na farko dazaka fahimci halin da na shiga kuma kaji zafin danake ji fiye da kowa, kuma a hakikanin gaskiya hakan ka nuna min. Sai de bayan wasu kwanaki nasan ka shiga wasiwasi kala-kala akan gaskiyar abun da ya faru da ni din
"Bayan nan kuma danace an warware min dinki, na tsinkayi wani tashin hankali a cikin muryarka, wanda ya nuna alamun cewa ba'a goshina kayi tunanin an min dinkin ba, a wani wajen ne daban."
Runtse idanunsa yayi dayaji kalaman nata don kusan hakan yayi tunani.
"Ina so ka sani, iya gaskiyata na fada maka, kuma a duk zaman da mukayi da kai, dai-dai da rana daya ban taba boye maka wani abu ba ko kuma na maka karya. I know you know that"
"Hauwa...."
"Faruk" a karo na farko a rayuwar ta data kira sunansa kai tsaye wanda hakan ya girgiza shi matuka. "Na soka tsakani da Allah, na aminta da kai. Deep down in my heart nasan da wani abu makamancin hakan ya faru da kai, kaurace maka ko guje maka will be the last thing i will think of, balle kuma har na fasa aurenka. Alkawari ne ka dauka, kuma ka karya. Kaje can na barka da Allah, Zai yi min sakayya da mafi alkhairi. Abun da ya faru da ni kaddarace daga wajen ubangiji, kuma tana kan kowa.
"Abu na karshe da zan fada maka shine Nagode. Nagode sosai da irin kaunar daka nuna min wanda har ila yau babu wanda ya nuna min irinta. Ga kayanka nan na dawo maka da su, lefen naka ma don sunyi yawa ne banida isashen kudin mota don haka ka turo a dauke. Mungode sosai da dawainiya. Allah kuma ya sada kowa da alherinsa. Bissalam"
Hannunta har rawa yake a lokacin da ta katse wayar tana sulalewa a tsakiyar dakin. Sai a lokacin hawaye suka samu damar zubo mata.
Tayi kukan cin zarafin ta da akayi, da sharrin da aka mata a unguwa, da wulakancin da Engineer ya mata. Sannan kuma tayi kukan rashin masoyinta, wanda ta so shi da zuciya daya, ba dan wani abun hannunsa ba, sai don Allah, wanda ya dasa mata son shi a cikin zuciyarta.
Ta so suyi rabuwar mutunci ko don soyayyar da ke tsakaninsu a da, amma abun da ya riga ya faru ya faru, ba a maida hannun agogo baya.
******
Kwance ya ke akan gadon nasa yayi matashi da cinyar Umma, idanunsa a rufe suke amma hakan bai hana hawayen sa zubowa ta gefen kuncin sa ba.
A hankali ta saka hannu ta share su. Ita ma kukan take son yi, amma ita din wa zai lallashe ta?
"Haba Abban Bilal" ta furta a hankali "Yanzu idan Adda ta shigo ta ganka a wannan yanayin ita kuma tayi yaya kenan? Ashe ba kai bane kace ta karbi komai a matsayin kaddara ta fawwalawa Allah komai? Shine kai kazo ka tada hankalinka har ma da kuka Abba?"
Damke hannunta yayi wanda ta ke share mishi hawayen da shi yana maida numfashi. Shi ma kanshi bai san dalilin hawayen nasa ba, kawai ya tsinci kansa a wannan yanayin ne. Ba zai iya tuna lokaci na karshe da yayi hawaye irin haka ba, amma dai kam an jima sosai. Sai gashi yau abubuwa sun kwance mishi, ya rasa inda zai saka ranshi yaji dadi.
"Lami ni kaina bansan ya akayi hakan ya kasance a gare ni ba, ki yi hakuri na nuna gazawata"
Kara rike shi tayi a jikinta tana girgiza kanta dukda ba kallonta yakeyi ba. "Kar kace haka Abba. Kayi hakuri idan furucina ne ya haddasa maka wannan tunanin, kayi hakuri"
Haka ta barshi yayi kukan sa ma'ishi. Sai da aka kira sallar la'asar tukunna ya tashi daga jikinta ya shiga bandaki don yayi alwala.
Sai a lokacin itama ta samu daman yin nata kukan.
Allah yaga ni ta fara sarewa akan lamuran nan da suke ta faruwa babu kakkautawa. Tana ganin idan wani abun kuma ya sake faruwa to zai yi sanadinta, wa iyazubillah. Ta jure iya jurewa amma kam yanzu juriyar tata ta kusa karewa.
Tayi kokarin ta tsaida kukan nata kafin Abba ya fito amma kukan ya riga da yaci karfinta.
Ko da ya fito ya ga yanayin data shiga, karasawa wajenta yayi ya dan riketa a jikinsa na wasu 'yan lokuta kafin ya fice zuwa masallaci.
A tsakar gida ta samu su Inaayah suna shanyan uniform dinsu na boko.
"Sai yanzu kuka wanke unform din? Idan ruwa ya sauko basu bushe ba fa mai zaku saka gobe da safe?"
Bin ta kawai sukayi da ido basu ce mata komai ba har ta shige falon ta bar su a wajen. Suka gama su ka share wajen da sukayi wankin sannan suma sukayi alwala suka shiga ciki.
Ta idar da sallah kenan taji hayaniya a tsakar gida, a tunaninta ko su Inayan ne don haka bata bi ta kansu ba ta cigaba da Azkar dinta. Sai dai bata yi nisa ba taji an banko kofar dakin nata.
Tana daga kai sukayi ido hudu da Qulsoom.
"Umma. Umma kizo" ta fada muryarta cike da tashin hankali.
Dafe kirjinta tayi hade da kiran sunan Allah tana jira taji zuciyar ta ta dena bugawa.
"Kizo an kawo Abba ya fadi a masallaci. Baya numfashi"
*********
Hm! Men are what?
Please vote vote vote and comment.
Also, please follow my business page on Instgram @_aliyah_.co
T for thanks.
Taku a kullum,
Miryamah.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top