21.

Brace yourselves, this chapter is total chaos. You've been warned ⚠️ ❗❗❗.


21.

Kamar yadda sukayi, ranar asabar wajen karfe sha daya Fareeha ta shirya ta gangara gidansu Hafsatu. Dayake gidajen nasu yana da dan nisa, sai ta yanke shawarar ta hau abun hawa dukda cewa akwai hanya ta cikin layi, kawai dai bata son bin ta wajen ne saboda masu shaye-shaye sunyi yawa a ta wajen. Dama yaya unguwar tasu balle ka shige can cikin lungu?

Ko da ta isa, Hafsatu cikin murna ta tarbeta. Ta sameta tana aikin tsince shinkafa, don haka Fareehar ta zauna ta taya ta, suna yi suna hira. Bayan sun gama Hafsatu ta dora shinkafar a wuta; dama mamanta tayi miya da safe kafin ta wuce makaranta.

Sai da ta jira ta tuka tuwon suka ci sukayi sallah sannan suka nufi gidan lallen.

"Ni ban zaci gidan da nisa ba ai da mun hau napep" cewar Fareeha da ta ga tafiyar taki karewa.

Hafsatu ta yi 'yar dariya "Ke yanzu sai mu kashe kudi dan nan da can din? Ki bari dai ko a dawowa ne sai mu hau. Amma yanzu ai mun dan mike kafa."

Shiru kawai Fareeha tayi amma ba haka ta so ba. Ta dan ji sauki ma dayake garin babu rana sosai alamar zuwa yamma ko dare ruwan sama zai iya sauka.

Sun zo wucewa ta wani layi ne kawai Fareeha taji kamar an yafuto hijabin ta. Cikin sauri ta juya wanda yasa Hafsatun ita ma juyawa.

Wasu samari ne su biyu zaune akan dandamalin wani shagon saida provision suna 'yan zuke-zukensu. Su Fareeha ko lura basuyi dasu ba lokacin da suka zo wucewar.

Wanda ya yafuto tan ya dan daga mata gira "Ya ne? Ina zuwa?"

Wani kololon bakin ciki ne yazo ya tsaya a makogoranta lokacin da take kare masa kallo. Tsabar raini da hijabinta da mutuncinta amma shine zai yafuto ta saboda bashida kunya?

Ta bude baki da niyyar yi masa masifa taji Hafsatu ta ja hannunta tare da buga tsaki tana fadin "Dan iska kawai"

"Kinga abun da yasa nace mu hau abun hawa ko?" Fareeha ta fada bayan sun dan kara gaba da wajen.

Zuciyarta sai tafarfasa take saboda bacin rai. Rabon da a mata irin haka tun farkon tafiyar Ya Bilal rehab, kuma shi ma tun lokacin ba wanda ya kara tunkararta musamman ma da karatunta ya kankama a Kano, tunda ba ma wani ganinta suke ba balle su shiga sha'aninta.

Kuma tun da can dinma ba mai zuwa kusa da ita da kannenta saboda suna tsoron Ya Bilal din. Shine yanzu wannan ya samu damar jawo mata hijabi? Abun ya bata mata rai matuka

"Ki kyalesu da Allah. Saboda wadannan shashashun ne zamu fasa yawo a unguwa? Don sunga kaman ana jin tsoron su ne ai shiyasa suke ganin daman mutane. Amma in ka nuna musu baka tsoron su to shikenan. Ni kinga kowa ya tsare ni a hanya rashin mutunci nake kekketa masa."

Shiru Fareehan tayi kawai tana karanta Hasbiyallahu wa niimal wakeel a cikin zuciyarta don har yanzu tafarfasa takeyi.

Sun isa gidan lallen suka samu mutane da dama ana musu lalle wasu kuma ana musu kitso. Anan dai suka shaida wa Falmata akan lallai nanda sati uku masu zuwa zatazo ta yi wa Fareeha lallen ta na amarya, baki da ja. Falmata ta amince da hakan. Suka karbi lambar juna sukayi sallama suka dawo gidan su Hafsatu. Ko da zasu dawo Fareeha ta nace akan su hau Napep, haka Hafsatun ta hakura don taga ran kawar tata ya sosu sosai akan abun da ya faru dazun.

********

"How's the new place?"

Juyawa tayi tana yawata idonta a  dan falon nata wanda har yanzu bai amsa sunansa falo ba sai ma dai a kirasa da store saboda shirgin da aka jibge a ciki da kuma yanda komai yake a hargitse, hatta TV ma har yanzu yana kwali bata bude shi ba. Kujerun ma suna cikin ledarsu bata daye ba.

Gaba daya sai taji gidan ya mata girma ita kadai. Abunda ta dade bata ji ba shi takeji a kwana biyun nan; kewar mijin ta, rabin ranta, jigon rayuwar ta. Allah ubangiji ya masa Rahama. Da yana nan yanzu da ya gama kimtsa mata komai. Ko kadan baya so yaga ta tashi tana wani abun nan da nan zai karba ya tayata, ko da kuwa bai iya abun ba.

Wani abu ne ya taso yazo makogoranta tayi saurin hadiye wa kafin ta bawa Mu'azzam din amsa.

"It's empty" ta fada da wani daci a muryarta wanda ya haddasa wa Muazzam karayar zuciya. Ina ma zai iya zuwa ya yaye mata wannan kuncin da ya ke ji a cikin muryarta.

"Ammah" ya kirata a hankali da sigar rarrashi. "Ba sai dana ce ki jira ni ba? Gashi yanzu kin tafi ke kadai gidan duk ya miki shiru"

Ta gane sarai so yake ya dan rage mata zafin da ta ke ji, don haka ta biye mishi.

"Kai ma dai ka fadi gaskiya. Haushi kakeji yanzu baka da gurin zuwa cin abinci idan cefanenka ya kare"

Sukayi dariya.

Hira ya cigaba da mata yayinda ta tsallake tarkacen falon ta koma dakin datayi masauki. Nan din ma dai gashinan ne don har yanzu akwatunan ta suna nan shirge a tsakiyar dakin duk an bubbudesu. Sabuwar bedside lamp din data siya ma har yanzu tana cikin ledarta.

Waje ta samu a bakin gadon nata ta zauna.

"Mu'azzam ina maganarmu ta kwana?"

Ya dan yi shiru kafin yace "Wace maganar?"

Ta san ya gane me take nufi, kuma ta lura tun kafin tafiyar tata yake ta mata kwana-kwana akan maganar, amma yanzu ta ji bazata iya jira ba. Hankalinta sam bai kwanta ba tunda ta tafi ta barshi.

Ta san ba wai zamanta a can bane ko sa idonta ne zai hanashi aikata wani abun idan yayi niyya, Allah ne kawai zai iya kubutar mata da shi. Dukda hakan yanzu hankalinta ya karkata zuwa ga aurenshi.

Ta yanke shawara kawai idan basu daidaita da Mami ba ita da kanta zata nemo mishi wata. Kuma tana fatan a dace. Tana ga hakan ne zai wanzar mata da kwanciyar hankali a cikin zuciyarta.

"Ammah ina ta tunani akai" ta tsinkayi muryarsa daga daya bangaren

Ajiyar zuciya tayi. "I think I've given you enough time Mu'azzam.  Ko ni kakeso na mata maganar?"

Da sauri ya ce "Innalillahi!!! Ammah ki rufa min asiri"

Dariya tayi "To na rufa maka. Amma dan Allah ka daina jinkiri. Na dai fada maka da kai da ita baku cancanci bata lokaci ba. Idan abunnan zai yiwu sai a yi shi proper, idan ba zai yiwu ba kuma sai muyi adduar Allah ya hada kowa da rabonsa"

Muazzam ya mintsini hancinsa. "Ammah ki kwantar da hankalinki, everything will be okay inshaAllah"

Ko da suka gama waya sai ta tsinci kanta da samun raguwar abinda takeji a cikin zuciyarta na kadaici. Ta dan ji kuzarin data rasa a 'yan kwana biyun nan ya dawo mata don haka ta tashi ta fara kikkimtsa dakin nata.

Bata gama shirya kayan ta a wardrobe din ba har aka kira sallar la'asar don haka ta tsagaita ta shiga ta yi alwala.

Tana idar da sallah ta jiyo karar doorbell don haka taje ta duba taga ko waye don bata tsammanin kowa a wannan lokacin. Mutanen da suka san ta dawo kasar ma basu da yawa don tafi so sai ta gama settling tukunna ta sanar da kowa.

Ko da ta leka dan ramin da ke jikin kofan sai ta tsinci kanta da yin murmushi ganin wacce ke tsaye a bakin kofar tata.

"Yau ni da Mu'azzam ne a garin nan, sai ya fada min dalilin yamadidin da yayi da ni" ta fada yayinda ta bude kofar.

Anti Bebi tana dariya ta rungumeta. "Oho dai koma menene kwa warware, nikam na riga nazo kuma da tawaga ta na taho"

Tana fadan haka sai ga Fadila da Yusrah sun shigo su dukansu da ledoji da manya manyan food flasks a hannunsu. Driver dinne ya karasa shigo da sauran shirgin da suka taho da shi.

Suka gaggaisa yayin da Anti Bebi take kallon gidan.

"Masha Allah Mama Ammah, gida yayi kyau. Amma dan Allah meyasa bazaki kira azo a tayaki shirya shi ba?. Ina ke ina yin wannan aikin ke kadai?"

Daga kafadar ta tayi "Ba wani aiki bane ba fa. A hankali nake yin kayana, ba wai lokaci daya ba. In kuka bani nan da sati daya komai zai kammalu. Bana so na saka kowa dawainiya ne shiyasa."

Anti Bebi ta jinjina kai. "Kanina ya kyauta da ya fada min. Mama Ammah in bamu miki dawainiya ba wa za muyi wa? Mu da yakamata ace mun kimtsa miki gida tun kafin kizo, kina isowa sai shiga kawai?" Tana fadin haka ta cire mayafin ta ta daure shi a kugu. Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka hau aiki.

Falon suka fara gyarawa aka share akayi mopping sannan suka daddaye ledojin kujerun nata masu kyau. Aka shimfida carpet sannan shima TV din aka cire shi a cikin kwalin sa aka daura akan TV stand din.

Da suka kammala da falon sai Anti Bebi ta bar su da saka labule ita kuma ta shiga dakin Amman inda ta samu tana ta kiciniyar karasa shirya kayanta a wardrobe din.

Haka ta saka hannu ta tayata sannan suka zuge akwatinan suka saka daya cikin daya sannan suka daura a saman wardrobe din. Ta gyara mata gadon nata ta saka sabon bedsheet sannan ta share dakin. Lokacin data gama an riga an kira sallar Maghreb don haka ta shiga bandakin don tayi alwalwa. Nan ma sai da ta wanke shi tas sannan ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah.

Su Yusrah ma anan falon sukayi sallar saboda akwai guest toilet a falon. Bayan sun idar suka zauna suka ci abincin da suka taho da shi dukansu sannan aka cigaba da aiki.

Fadila aka bar wa gyara guest room din don babu wasu tarkace a ciki sosai sai Anti Bebi da Yusrah suka hau shirya kitchen din. Gas cooker ma sai a lokacin suka cire ta a kwalin ta. Anti Bebi na dariya tace "To Mama Ammah da bamuzo ba kam sai yaushe zaki fara girki a kitchen din naki?"

Itama dariyar take tace "Waya san min ne? Kinga tunda nazo siyan abinci nake" ta yi mata nuni da takeway packs din da ta wanke a safiyar ranar.

Ba su bar gidan ba sai wajen karfe goma da suka tabbata sun share mata ko ina kuma sun jera mata komai.

"Dan Allah gobe ki kwanta ki huta, zan aiko miki da breakfast. Maganar neman mai tayaki zama kuma ki barmin wannan. Zanyi waya da Ummata za a nemo miki a nan Misau din. In kuma kinfi son 'yar fesfes anan Kanon ma sai na sa a nemo miki" Anti Bebi ta fada da ta rako su waje.

"Ko daga Misau din ma aka samu babu matsala. Ni dai nafi son 'yar gida shine kawai."

"To ba matsala. Ki kwanta dai ki huta kinji?"

"Ai kun fini bukatar hutu ku da kuka sha aikin nan. Allah dai ya saka da mafificin alkhairi ya biya ku da gidan Aljannah"

Duka suka amsa da Amin sannan sukayi mata sallama.

Data shiga gidan nata sai taji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta. Sai a lokacin ta kara gode wa Allah da ya sa ta dawo gida kafin lokaci ya kure mata. Yanzu in banda dan uwanka waye zai bar abun da yake yi yazo ya maka irin wannan gagarumin taimakon? Ita kam tasan da basuzo ba sai tayi wajen sati uku bata gama kimtsa gidan nan ba. Amma gashi sun gama mata komai a cikin lokaci kalilan. Taji dadi kwarai. Hakan yasa ta tura wa Mu'azzam sakon godiya da kuma jan kunnen kar ya sake mata irin wannan ba zatan.

Su Anti Bebi suna isa gida ta tarar da Ashraf yana barin bangaren baban nasu. Fuskarsa babu wata annuri  ya musu sai da safe ya wuce sashen su.

Ko ba a fada mata ba ta san wainar da aka toya don haka tana shiga dakinta ruwa kawai ta watsa ta yi shirin kwanciya sannan ta wuce wajen Bappahn. Samu tayi ya idar da sallar shaf'i da wutr don haka ta duka ta dauki abun sallan nashi ta nade ta ajiye a ma'ajiyar sa.

"Yaya kuka sami Maman naki?"

Ta zauna a bakin gado tana cire hijabin data shigo dashi a jikinta. "Lafiya kalau Alhamdulillah. Sai dai mun je mun samu aiki tirim! Kasan ko gas cooker dinta ma sai mu ne da mukaje muka cire mata shi a kwali? "

"To meyasa bata fada miki zuwan nata ba, ai da kunje tuntuni kun kimtsa mata wajen"

"Nima fa abunda nace mata kenan. Sai tace wai bata son saka mu dawainiya. To in ba mu mata dawainiyar ba wa za muyi wa?"

Bappah ya danyi gajeren murmushi. "Allah sarki. Yanzun ma ai kun kyauta da kukaje. Allah ya bada lada"

"Amin"

Har ta kwanta sai ta tashi ta zauna. "Nikam Baban Samha ya kuka kare ne akan batun neman auren Ashraf? Mun hadu dazu a kofar gida sai naga kamar ranshi babu dadi"

Murmushi yayi yana zama a daya gefen gadon yace "Ba dole ranshi ya ki dadi ba nace ya hakura da rabin ransa"

Kalaman sa suka saka Anti Bebi dariya. "Kai dai ba'a barinka da zolaya. Gashi kuma baka fada min sakamakon binciken naka da ka saka akayi maka ba game da family din su yarinyar"

"Ni bansan ma me zance bane, gaba daya abun be min dadi ba. Kuma hankalina bai kwanta ba."

Nan ya shiga bata bayanin labarin da ya samu a kan mahaifiyar Wafiyyar, Hajiya Huda.

Abubuwan yawanci babu dadin ji amma musababbin abin da ya tada wa Bappahn hankali shine yanzu kusan shekaru goma sha biyu da suka rabu da tsohon mijinta amma har irin rana ta yau bata sake wani auren ba, kuma zaman kanta take a garin Abuja bata da mafadi babu wani babba namiji dayake kula da lamuranta, abun da taga dama kawai takeyi. Shi a ganinshi ko da kuwa bata da niyyar auren yakamata ace tana karkashin wani dan uwanta ko dan gudun maganar mutane.

Gashi ita ba aiki take ba ba sana'a ba kawai ta samu gida a Maitama tayi zamanta.

Wannan yasa mutane dayawa suke mata mummunan zato kala-kala tunda ba'a san takamemen abun da takeyi ba, gashi kuma mutane sunzo sun nuna sha'awar aurenta amma sam ta ki sauraron kowa, cin duniyarta kawai take da tsinke. In an kwana biyu ta kade jakarta ta keta hazo tace ta tafi Umrah, sai bayan wata uku take dawowa.

Anti Bebi ta kama habarta "Toh fa! Shi Ashraf din duk yasan da wannan dama?"

"Zai yi wuya ai ace bai sani ba. Shi yanzu yana ganin shine Knight in shining amor dinta, kowani tabo take dashi ya riga da ya kwallafa ranshi cewar auren ta da zaiyi shine zai ceto ta daga rayuwar datake.

Yana ganin kaman wadannan abubuwan baza suyi tasiri akanta ba tunda ba tare ta taso da mahaifiyarta ba, but he has no idea the influence a mother can have on her children. Ina tsoron abun da zai je ya zo"

Anti Bebi ta jinjina kai "Hakane kam. Amma yanzu kam tunda ya dage sai dai mu bishi da Addu'a. Allah yasa akwai alkhairi a ciki. Tunda dai kusan kaman Jihadi yake da niyyar yi"

Bappah ya yi ajiyar zuciya. "Ni a zatona idan nace mishi a'a to magana ta kare, amma sai ya ban mamaki danaga ya kafe."

Jikin Anti Bebi yayi sanyi. "Kayi hakuri Baban Samha. Kasan yaran yanzu ba kamar na da ba, sha'aninsu da wuya"

Murmushi yayi wanda bai kai har cikin ranshi ba yace "To yaya na iya tunda ya nace? Iya kaci na bishi da Addu'a kawai. Ina fatan Allah ya shige masa gaba, albarkacin son da ya ke mata na tsakani da Allah, Allah ya dube shi ya sa auren tan nan dayasa a gaba ya zame masa hanyar samun nustuwa da kwanciyar hankali a rayuwar sa"

Ganin yanayin fuskar sa sai ya kara karyar mata da zuciya. Tasan baiji dadin kafiyar Ashraf dinba, amma ita ma kuma bata so a zo ana takun saka akan maganar. Tasan Bappahn zai iya danne fushinsa akan komai, kuma idan yace abu ya wuce to ya wuce kenan, don haka addu'ar ce kawai mafita.

Hannunsa ta riko ta rungume a kirjinta. "Allah ya kara maka hakuri da juriya Baban Samha na. Allah kuma ya yiwa yaran mu albarka ya kade duk wata fitina a rayuwarmu"

"Eh wato kun hada kai ke da danki kun samu abunda kukeso ko, shine zaki min wani dadin baki. Duk nagane tactics dinki in gaya miki" ya wafce hannunsa yana kokarin nuna bacin ransa wanda daga ita har shi din sunsan akasin haka  yakeji a wannan lokacin.

Dariya tayi tare da sake riko hannun nasa. "In ban maka dadin baki ba wa zan yi wa?"

Haka ta cigaba da fada mishi dadadan kalamai har ya sassauto. Dama can ba wani hawa yayi ba, ran sa ne dai kawai ya sosu.

***

Shiru Fareeha bata ji daga Hafsatu ba har kusan wajen kwana biyar. Ta kira wayanta yafi a kirga amma baya shiga. Gashi sunyi akan zata rakata kasuwa ta karasa wasu siyayyar tata, ga kuma dinkunanta da bata karbo ba a wajen tela. Allah yasa ma ba wanda zata saka a bikin bane. Yayyen Umma ne suka mata kokari suka hada mata hana gori shine a ciki ta cire guda hudu ta bayar dinki inda Anti Mami kuma ta biya kudin dinkin.

"Yanzu bazaki jira Qulsoom su dawo a makaranta ba sai ta je ta dubo miki ita? Wai sai yaushe zaki nutsu ne ki zauna waje daya uhm? Sai yawo kike a gari kaman kinci kafar kare" Umma sai masifa take tana cizge kayan shanya daga kan igiya "Yan gurje gurjen dakikayi ma ai duk se ya kode a rana. Haka zakije musu dusu-dusu?"

Fareeha dake tsugune a bakin famfo tana karasa wanke-wanke tace "Umma dan Allah kiyi hakuri kinji? Hankalina baze kwanta ba idan ban je na ganta da kaina ba. Kuma kinsan Qulsoom da kalula yanzu idan ta dawo kafin tayi wanka taci abinci ma sai ta bata lokaci mai tsawo. Ni kuwa yanzun nan zan je na juyo inshaAllah"

"To waya ce ki wani tsaya wanke-wanke da ba kinje kin dawo ba sai kiyi wanke-wanken?"

"Umma ho!" tayi murmushi. Yau dai Ummar tata ta tashi a birkice don tun safe suke shan fada a gidan. Su Inaayah ma kafin su tafi islamiyyah sai da suka karbi rabonsu. "Kiyi hakuri dan Allah. Yansu zan kammala"

Ta gama ta dauki basket din kwanukan ta kai kitchen ta jingine sannan ta wuce daki. Kayan jikinta ta cire saboda dan jikewar da siket dinta yayi ta kasa ta saka wata doguwar riga.

"Umma yanzu zan je na dawo inshaAllah. Minti ashirin" ta fada tana kokarin saka hijabinta.

"To ki gaida Hafsatun da Mamanta duka"

Sauri ta yi ta zabgawa har ta isa bakin titi ta tari abun hawa.

Shagon Nasiru tela ta fara zuwa don karban dinkin nata. Tana zuwa ta samu kala biyu kawai ya dinka, na ukun ma sai a lokacin ake yankawa.

Ranta bai yi dadi ba haka ta tattara 'yan kala biyun ta ta sake hawa napep don zuwa gidan su Hafsatun.

Da ta isa gidan ta samu bata nan ta fita.

Maman su ta samu ita kadai don kannen Hafsatun ma suna islamiyyah duk makaranta daya suke zuwa tare da su Qulsoom da Inayaah.

"Yanzun nan zata dawo. Na aike ta gidan kanwata ne nan bayan layi ta karbo min kankara" cewar Maman Hafsatun a yayin da take shimfida wa Fareeha tabarma a tsakar gidan nasu. "Ki dan jira ta kadan"

Fareeha ta duba agogon wayarta. Allah-Allah take ta koma gida tun da dai da alamun Hafsatun kalau take tunda har aka aiketa.

Bata dade da zama ba kuwa sai gata ta shigo.

"Allah sarki Fareeha ta. Shine hadda tasowa ki zo ki duba ni?" Hafsatu ta fada bayan sun gaisa.

"To naji ki shiru ba dole nazo na gani ba? Hankalina fa har ya tashi"

"Iyyeh iyyeh. Ashe haka ake sona daman?"

Fareeha ta juya idanunta "Tunda lafiyar ki kalau nikam sai anjima" ta mike tare da daukar ledar dinkunanta.

Hafsatu ta riko hannunta. "Yi hakuri mana. Dadina dake saurin daukar zafi" ta jawota ta koma ta zauna "Kin ga wallahi gidan rasuwa fa mukaje shi ne aka sace min wayar tawa. Ina ta cewa nima yau zan shiga wajen naki amma abubuwa sun min yawa"

Haka dai ta samu ta jata da hira har ma ta nuna mata dinkunan data karbo. Sunyi kyau ba lefi. Da suka ji iska ta fara kada su ne Fareeha tayi saurin mikewa "Kinga kar ruwa ya tare ni a hanya bari na koma gida"

Hafsatun taso ta mata rakiya amma kuma dawowarta daga aiken Maman nata ta fita itama don haka gidan ba kowa se ita kadai.

"Ki samu dai kiyi welcome back na Sim dinki ki saka ko a wayar Mama ne sai muyi magana. Kinga ni ba sake ganina zakiyi ba kuma, don yanzu Umma har ta fara mita wai yawon ya isa haka."

"Ai gaskiyarta. Karki kode a rana Engineer yace ya fasa"

Fareeha ta kai mata duka ita kuwa tayi saurin tura kofar gidan nasu.

Girgiza kai tayi ta juya ta fara tafiya. Har ta kai bakin titi kawai ta duba taga ashe ta bar purse din ta a gidan su Hafsatun kuma kudin napep din ta na ciki. Ba shiri kuwa ta juya don komawa dan kamar yadda tayi tsammani hadiri har ya taso gadan-gadan kuma da alamu ruwa za'a sheka nan ba da jimawa ba.

Tana shiga layin su Hafsatun kawai taji an jawo Hijabinta har tana kokarin hantsilawa ta baya.

Gabanta ne yayi mummunar faduwa ganin mutum a gabanta yana kokarin hankada ta cikin lungu.

Tana kokarin samun madogara taji an sake janta ta baya kuma ta karasa shigewa cikin lungun. Saboda duhun da garin yayi sai taga kamar har dare yayi a lokacin dalilin rashin haske a lungu.

Kamar daga sama taji ance "Ni kika ce wa Dan iska ko? Yau zan nuna miki iskanci"

Bata samu daman juyawa ma taga ko waye ba taji an kare shake mata hijabin. Kafin tayi aune ya buga kanta da jikin ginin wajen sai da taga wani jan wuta a idonta. Wani zafi ne ya ziyarci kwakwalwarta hade da jiri daya kwashe ta duk a lokaci guda. Dayan ya sa kafa ya kwarfeta. Nan ta sulale kasa ta zube.

Tana daga ido ta gansu su biyu sun yo kanta. Ihu ta ke so ta kwala amma kamar an zare mata rai takeji. Haka taji sun dagata sunyi ciki da ita.

Warin daya ziyarci hancinta ya haddasa mata daukewar numfashi. Nan ta shiga karanta Hasbiyallahu wa niimal wakeel a cikin zuciyarta, kafin wani duhu ya rufe mata ido. Daga nan kuma bata san inda take ba.

Da Hafsatu tazo nade tabarmar da aka shimfida wa Fareehar ne ta hango purse din tata. Har ta fita zata bi ta dashi ta tuno kuma zata bar gidan babu kowa kuma tsakanin gidan nasu da bakin titi akwai rata don haka ta shiga makwabtansu don neman wacce zata tsaya a gidan nasu kafin ta je ta dawo. Dama yawanci haka sukeyi

Tana shiga kuwa ta samu wata yarinya Aisha tace mata dan Allah ta dan shiga gidansu ta zauna yanzu zata je bakin titi ta dawo. Fitowarta ke da wuya sai ga kaninta Yusuf ya rugo wajenta a guje.

"Har kun tashi islamiyyan ne?" Ta tambayeshi, ganin yanda ya taho hankali a tashe kuma sai ta sake masa wata tambayar "Meya faru ?"

Yana kokarin tsaida numfashin sa da gudun zuciyarshi yace "Na dawo karban kudin littafi ne kawai sai...sai....sai naga kawarki suna fada da wasu maza a cikin lungu"

Hafsatu ta dafe kirji hade da zazzaro idonta waje. "Fada kuma? Wace kawar tawa?"

"Adda Fareeha. Yayarsu Qulsoom"

Bata san lokacin da ta finciki hannunsa ba suka nufi hanyar daya nuna mata. Suna zuwa wajen suka ga wayam.

"Anan fa na gansu. Wallahi anan na gansu" Yusuf ya fada yana nuna mata dai dai wajen.

Kokarin daidaita zuciyar ta take don ta samu tayi tunani me hankali amma hakan ya faskara. Sai ma wani karin tashin hankalin takeji.

"To ko ta wuce gida baka sani ba?"

Addu'a take Allah yasa Fareehar ta gudu amma sai cewa yayi "Naga fa sun kwarfeta ta fadi kasa."

Hannu ta dora akanta yayinda hawaye suka cika idonta "To ba ka san suwaye ba su din?"

Girgiza kai yayi. "Watakil abokan Nazee ne"

Nazee? Nazee shahararren dan daban layinsu?

Kara sauri tayi ta nufi kofar dakin nasa wanda yake bayan wani shagon masu wanki da guga. Shagon nasu yana ta gaban layin ne, inda shi kuma dakin ya na daga ciki-ciki. Don haka duk abun da akayi ma basu da masaniya tunda ba akan Idon su akayi ba. Hasali ma basu ga wucewar Fareehar ba don kowa aikin sa kawai yakeyi.

Tana zuwa wajen bugun zuciyarta ya karu don ga warin takalmin Fareeha nan daya a yashe a wajen. Bata san lokacin da ta fara buga kofar ba da dukkanin karfinta tana jijjigawa. Amma ko gezau. Kofar ko motsi batayi ba, kuma babu wanda yake da niyyar bude mata ita.

Masu guga kam basu ma san me akeyi ba don sun kunna kida a shagon nasu yana tashi don haka basu ankara da cewa tana ta wajen ba ma sai da ta shigo shagon nasu a firgice.

Nan da nan daya daga cikinsu ya rage sautin wakar ganin Hafsatun a rikice don ya santa a unguwar. "Lafiya?" Ya tambaya.

Kuka take sosai tace "Kuzo ku balle min kofar dakin Nazee. Kuzo dan Allah"

Tsayawa sukayi suna kallon ta don kowa yasan cewa Nazee baya ganin mutuncin kowa a unguwar, yanzu akan wani dalili zasu balle mata kofar dakin sa yazo ya sassare musu hannu cikin dare?

"Sun shige min da 'yar uwata daki. Dan Allah kuzo ku tayani ceto ta"

Ai ba ta kara nanatawa ba duk su maza ukun suka fita a guje. Bugu biyu kofar ta balle kasa suka fantsama cikin dakin.

Hannunta rungume akan kirjinta tana taradaddin abun da zai faru sai gani tayi an fito mata da Fareehar ta a sume ga jini yana malala daga gefen kanta. Hijabin dake jikinta ta cire ta yafawa Fareehan don tuni suka yaga mata nata.

Duk nauyin Fareeha a ranar Hafsatu bata ji shi ba haka ta goye ta a bayan ta har bakin titin, masu guga suna biye da ita. Su suka tsare mata napep mutum daya a cikinsu ya shiga gaba ya dan rakube tare da mai napep din har suka karasa gidan su Fareehar.

Umma na kokarin tarar ruwa a buta don yin alwalar Maghreb kawai sai ganin mutum tayi hajaran majaran da goyo a baya. Dagowan daza tayi ne taga Fareeha a bayan Hafsatun. Butar dake hannunta ta fadi ruwa ya fantsame a tsakar gidan.

"Hafsatu?" Ta kira muryar ta cike da taradaddi. Bata tsaya jin me zatace ba ta karasa wajenta ta riko fuskar Fareehar. Jinin data gani ne ya tayar mata da hankali, a lokaci guda kuma wani karfin hali ya ziyarci zuciyarta.

Hijabinta dake lankaye akan igiya ta jawo ta sakawa Hafsatun wacce sai a lokacin ma ta lura babu hijabi a jikinta.

"Jirani nazo mu je asibiti" ta fada kafin ta wuce ciki tana kokarin hadiye kukan daya taso ya zo makogoranta ya kafe.

A daidai lokacin kuma ruwan sama mai karfi ya sauko.

****

Uhm. No words!

Drop your comments, make sure not to come for my head tho.

Taku a kullum,
Miryamah.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top