20.

Apologies for my silence. Life has been so busy, Alhamdulillah. Thank you all for your patience.

20.

Abu kamar wasa, wai yanzu saura wata uku bikin ta. Abun har mamaki yake bata.

Lokacin da su Abba suka saka rana wata takwas ta dauka abun ba zai zo da wuri ba. Har dariya ta rinka yi wa Engineer da ya nuna cewa shi kam wata takwas ya mishi nisa.

"Saurin me kake? Eight months kamar yau ne fa!"

Ai kuwa dai gashi har an cinye wata biyar. Allah mai iko.

Umma sai shiri ake tayi. Dama tun da can ta dan fara taron ta na kayan kitchen da sauran abun da ba za'a rasa ba sakamakon sana'ar saida kankara da ta fara a watannin da suka shude.  Abba ya siya mata 'yar karamar freezer (second hand) kuma Alhamdulillah tana samu ba lefi. A ciki ta dan samu ta sayi 'yan kayan robobi da sauran kananun abubuwa.

Yanzu da abu yazo kusa kam sai taro ya kankama. Sati biyun da suka wuce ma sukazo ita da Anti Mami, Fareeha ta musu rakiya kasuwar sabon gari suka kara yin wata siyayyar kayan kitchen din.

In banda ido babu abun da ta zuba musu, in suka tambayeta wani abun ma ko ya mata kyau gyada kai kawai takeyi. Da Bappah yaji labarin za su je kasuwan shima ya bata kudi yace ta kara akan siyayyar da za suyi. Haka ta bawa Anti Mami kudin ta ce ita bata san me zata siya ba. Gaba daya ji take kamar ba ita ba.

Gashi yanzu an fara zancen su gadaje da sauran abubuwa. Anti Bebi da Adda Samha sun je sun gano gidan da Fareehar zata zauna. A nan Kabuga ne babu nisa da gidan Maman Engineer din. Gidan sa ne kuma anan ya tare lokacin auren sa na farko. Dakuna hudu ne a ciki da parlor biyu da kitchen mai isashen girma.

Da suka dawo suka yi ta santin gidan.

Ba bata lokaci Bappah ya sanar da Abban nasu cewa zai yi gado daya da kujeru a matsayin guddumuwarsa idan yaso shi Abban sai yayi sauran kayan dakin. Hakan ya sa Abban ya ji dadi dan shi dama niyyarsa yayi gado daya da set din kujeru.

"Sauran daga baya su da kansu sa saka. Wanda aka samu ma Allah ya sa albarka" abunda yace wa Umma kenan da tace mishi daki hudu ne a gidan.

Yaushe zai fara yin wani gadaje uku? Ita Fareehan ina zata kai dakuna hudu ma? Shi kam da ba yaron bane ya gina gidan da ya ce a canja. Yanzu gado da kujerun ma da zaiyi sai ya hada da wata gonar sa ya siyar tukun. Duk wani kudin daya tara domin bikin nan ya kare a siye-siyen su carpets da labule da kayan kitchen da kuma dan karamin TV. A hakan ma ba'a zo maganar gaara ba tukunna.

Fridge da gas cooker kam tuni Anti Bebi ta siya ta ajiye mata su a gidan Samha. Lokaci kawai take jira ta fito dasu aje ayi jere.

Ita kam jikinta kara yin sanyi ma yake don ta kasa yarda wai ita ce zata yi aure. Ita ma yanzu zataje ta gina tata zuri'ar kenan?. Kullum tana cikin tunanin irin rayuwar da zata je ta fuskanta amma idan ta tuno Engineer yana tare da ita sai taji ranta yayi sanyi. Tayi imanin cewa zai kula da ita gwargwadon ikon sa.

Ita dai fatanta Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya Allah kuma ya basu zaman lafiya ya hada kansu.

"Yau baki da lectures ne?" muryar Anti Bebi ta kaste mata tunanin da ta fada. Ta dago kanta daga inda take tsugune a gaban wardrobe dinsu ita da Yusrah. Fadila ta bar musu dakin yanzu su biyu sai ta koma dakin Samha na da.

"Eh Mama" ta amsa a hankali. "Ina kwana?"

Gyara zaman dankwalin ta tayi ta amsa da "Lafiya. Me kuka dafa?"

Mikewa tayi tana ajiye mayafin da take nadewa akan gado tace "Danwake. Amma in akwai wani abin da kikeso zan iya dafa miki"

Dakatar da ita tayi tana murmushi. "A'a koma ki cigaba da aikinki. Bana jin cin komai ma. Bari na dan dama kunu"

Toh kawai tace ta koma ta cigaba da nade kayan da ta keyi tun dazun.

A kitchen Anti Bebi ta samu Amina tana ta faman wanke Wake don Alale sukayi niyyar yi da rana.

Ta gaishe ta cikin ladabi ta kuma amsa mata.

Maimakon ta hada kunun kamar yadda tayi niyya sai ta tsinci kanta da samun waje ta zauna.

Tunanin yanda zata fara sanar da Ashraf sakamakon maganar da sukayi da Babansa jiya da dare takeyi.

Sati biyu da suka wuce yazo mata da labari mai dadi. Ya ga wacce yakeso kuma yana so ta taya shi sanar da Bappah akan yana so aje a masa tambaya. Abun ya mata dadi matuka musamman da ya nuna mata hoton yarinyar. Tubarkallah Masha Allah 'yar fara kyakyawa da ita. Wafiyya sunanta.

Sun hadu a airport tun lokacin yana karatu a Jamus, ita da 'yan uwanta zasu je Umrah don haka transit ya hadasu a Qatar dayake jirgin da suka shiga kenan. Anan Ashraf ya ganta dayake shi ya samu delay din jirginsa a dalilin dusar kankara (snow) dake sauka a garin Munich don haka sun shafe lokaci mai tsawo suna hira da ita.

Da aka kira jirginsu Wafiyyar sai sukayi musayar lambar waya.Daga nan kuma shikenan abubuwa suka kankama.

Hankalin Anti Bebi ya kwanta sosai kan lamarin don haka batayi kasa a gwiwa ba ta sanar wa Baban nasa.

"Zanyi bincike tukunna. Ba zan nema masa aure ba bayan bansan wasu irin mutane bane" abin da Bappah yace kenan bayan sun gama magana.

Hakan kuwa aka yi. Sati guda tana jiran taji bayani daga gareshi amma shiru. Har ta cire rai kawai jiya da daddare sai gashi ya taso mata da zancen lokacin ta kai masa abincin dare.

"Da dai zai bi shawara ta ya nema a wani wajen amma banda ita" cewar Bappahn bayan ya gama koro mata bayani.

"Baban Samha sun dade tare fa da yarinyar. Wani abunne kaji?"

"Ki dai fada mishi abun da nace. Idan kuma ya dage sai ita din, sai mu bi su da Addu'a. Allah ya sa khair"

Dukda wannan furuci nashi, hakan bai hana jikinta yin sanyi ba game da lamarin. Taga kuma kaman dan nata yana son yarinyar matuka. Yanzu ta yaya zata karya masa zuciya? Gashi Bappahn bai sanar da ita sakamakon binciken da yayi ba, yana so sai yaji daga bakin Ashraf din tukunna.

Da taga zaman ba zai amfane ta da komai ba sai ta tashi ta hada kunun.

Wajen karfe sha daya Amina ta dawo daga markade. Fareeha ta fito ta tayata hada kullin suka daura alalen.

Sai bayan la'asar Yusrah ta shigo gidan duk tayi laushi.

"Gaskiya zanyi change of course" ta fada tana kwanciya ruf da ciki a kan doguwar kujerar da ke falon Anti Bebin.

Fareeha tayi dariya "Ki koma me?"

"Hausa. Ko Mass Comm"

Girgiza kai Fareeha kawai tayi taci gaba da danna wayarta. Sakonni ne suka shigo a group din department dinsu na Linguistics. Bayani ne akan test din da suke da ita gobe da kuma wasu assignments da aka bayar.

***

Shigowar sa gidan kenan don yana wajen aiki ya sami sakon Baban shi akan yana nemansa bayan sallar Maghreb.

Dayake ofishin su a Hotoro yake, ya saba yawanci idan an tashi yana zuwa gidan kanwar Anti Bebin da ke unguwar saboda yawan hold up din da ake samu a hanya da yamma, sai yayi Maghreb anan kafin ya karaso gida. Ganin sakon Bappah ya sa yau din be biya ta gidan Anti Balaraban ba, ana tashi kawai ya debi hanyar gida don yasan ba zancen komai zai masa ba illah zancen Wafiyyarsa.

Sarai ya sami sakon sa a wajen Anti Bebi da tace Bappan yace ya hakura, amma sam shi ya kafe yace lallai sai ita. Shi bai ga wani aibun ta ba kuma a shirye yake ya aureta ko da kuwa tana da wani abun kyama a tattare da ita ko wani nakasu, haka yake son abar shi.

Raka'a daya ya samu a masallacin unguwar tasu, wannan yasa Bappah ya riga shi shigowa gida. Da ya dawo ya samu yana waya a falonsa don haka ya shiga cikin gidan don ya sami abinda zai saka a cikinsa.

Fareeha ya samu a kitchen tana faman tuka tuwo. Daga inda yake tsaye ya hango cewa tuwon tamba ne. Yasan na Bappah ne amma shima kuma tuwon na masa dadi musamman idan da miyar yauki ne.

Juyowa tayi suka hada ido tayi saurin saukewa. "Yaaya sannu da dawowa" ta furta a hankali.

"Sannu Adda Amarya"

Murmushin gefen lebe tayi. "Kaima har da kai?"

Plate ya dauko a cikin kitchen cabinet din yana zarcewa inda yaga an ajiye warmers guda biyu "To ba amaryar bace?"

Murmushi kawai ta sake yi bata ce komai ba.

Ya lura dai kamar shi kadai ne bata son yiwa magana a gidan. Don lokuta da dama ya kan jiyosu ita da su Fadila idan suna hira, amma idan ya zo waje sai yaga ta yi tsit. Duk yadda Kuma ya so ya sake mata ita taki ta sake da shi. Tun abun na damunshi har yazo ya dena damun shi. Tun da dai ba gaba suke ba ai shikenan.

Shinkafa da miyar da ya gani ya zuba ya koma kan kitchen island din ya fara ci.

Ko loma uku beyi ba Anti Bebi ta shigo kitchen din rike da baby Noor yarinyar Samha da ba ta wuce wata biyar ba.

"Nan ka shigo ashe. Babanka yana ta nemanka"

Sauke spoon din yayi yana hadiye lomar tasa. "Ya gama wayan ne?"

"Eh ya gama. Barin ce kana cin abinci to"

Girgiza mata kai yayi hade da mikewa. Tare suka fita inda yaci karo da Samha tana shirin komawa gidan ta. Dama ta je biki ne dare yayi mata shine ta shigo tayi sallah. Suka gaisa a tsatstsaye ta wuce abunta shi kuma ya nufi falon Bappahn.

Bayan sun gaisa ya tambayeshi ya aiki da sauran al'amura sannan ya masa bayanin dalilin kiransa da yayi.

"Ka samu sako na daga wajen Mamanka?"

Ya gyada kai. "Eh Baba na samu"

Bappah ya jinjina kai. "Har yanzu kana kan bakanka?"

Ashraf ya gyada kai a hankali.

"Ina da tambaya guda biyu"

Shirun da yayi ne ya sa Bappah cigaba da magana. "Na farko, me ya jawo hankalinka zuwa gareta?"

Ashraf ya ja dogon numfashi sannan ya gyara zama. "Abu babba dai da ya ja hankali na shine dogaro da kanta da tayi da kuma zuciyar nema da take da shi. Kowa ya shaida Babanta babban dan kasuwa ne kuma mai kudi, amma hakan bai sa ta zauna tana jira a bata ba, ta tashi ta nemi na kanta kuma har yanzu ta na kan nema. Yanzu kusan shekara uku kenan da bude shagon ta datayi a Zoo road wanda take saye da sayarwa kuma Alhamdulillah abubuwa suna kara ci gaba sosai"

"Masha Allah" Bappah ya jinjina kai "Tambaya ta biyu, meyasa kake son aurenta?"

Dan guntun murmushi ya saki don bai tsammaci wannan tambayar daga wajen baban nasa ba "To kusan dai zance tausayin ta nakeji. Ta taso mamanta da babanta basa tare kuma sauran matan babanta basa nuna kulawa a gareta, ta rasa abubuwa da dama tun tana da karancin shekaru, don haka ina so in bata wannan abubuwan data rasa, in zama me share mata hawaye, in zame mata bango a rayuwarta, mai damuwa da dukkan damuwar ta, wanda zata kaiwa dukkan kukanta."

Bappah ya sake jinjina kai.

"Tausayi yana daya daga cikin abubuwan da ke kara karfafa aure. Kuma tausayi kan rikide ya zama so, amma hakan ba yana nufin idan kana tausayin mutum ba shine kana sonsa. Shin Ashraf, son yarinyar nan kake ko kuma tausayinta kake?"

Ya bude baki zaiyi magana Bappah ya dakatar da shi. "Sannan kuma kasani cewa so daban, kauna daban. In kana son ta don wasu dalilanka, to kana ga idan bata da wannan abubuwan zaka iya cigaba da sonta da martaba ta?

"Ina so ka nutsu kayi tunani. Shin wannan tausayi, da son da kakeyi mata, ya kai ga har kana ganin yakamata ta zama abokiyar rayuwar ka, uwar 'yayanka? Kana ganin kamar yadda zaka zame mata madogara haka itama zata zame maka? Kana da yakinin cewa zata mutunta iyayenka? Zata girmamasu? Zata zame wa kannenka babbar ya? Zata kula da su kamar yadda kaima zaka kula dasu?"

Fitilar da ke haska kwakwalwarsa yaji ta dauke dif. Yanzu me ya kawo duk wannan zantukan?

Yana son Wafiyya kuma so na fisabilillahi Fakat! Me kuma ya rage? Shi bazai tsaya tunanin da zai saka shi canja shawara ba. Ya riga da ya mata alkawarin aure, kuma shi bai cika son saba alkawari ba tunda wannan ba halin nagarta bane.

Kuma ko ba komai Wafiyya ita ma ta yi iya kokarinta. Ta jira shi lokaci mai tsawo har ya kammala karatun sa. Bayan nan kuma ta sake wani jiran har ya samu aiki ya fara tsayawa akan kafarsa don tun haduwarsu ya sanar mata cewa ba za'a barshi yayi aure a gida ba sai dai ya samu aikin yi. Hakan bai sa ta dena sonshi ba dukda tana da masu sonta wanda suka fishi shekaru da kyau da kuma kudi, amma ta dage sai shi. Ta shanye duk wata bakar magana da akayi ta mata a gida akan cewa kannenta sunyi aure sun barta ita kuwa tana nan tana jiran dan boko.

Shi ne bayan ta gama wannan wahalar akan shi ya zo yace mata ya fasa? Wannan shine karshen muguntar da zaiyi mata, kuma baya so ya kasance daga cikin wanda zasu sanya ta cikin kunci a rayuwarta.

"Na baka nan da dan wani lokaci" muryar mahaifin nasa ya dawo dashi daga tunanin daya fada "Ina jiran amsarka a karo na biyu"

"Nagode Baba" haka kawai yace ya sa kai ya bar falon. Abincin shi da Fareeha ta saka wani plate ta rufe gudun kar ya huce ya dauka akan counter top din kitchen din ya wuce boys quarters. Ko da ya shiga dakin sa sai ya ji baya son cin komai ma don jikinsa duk ya mutu.

Bandaki ya shiga ya watsa ruwa sannan ya dauro alwala. Yana fitowa yaji an fara kiraye kirayen sallar Isha. Kaya ya sauya zuwa marasa nauyi sannan ya fice zuwa masallaci.

***

Tana jiyosu daga daki suna magana kuskus shi da umman nasu. A zatonsu kowa ya kwanta don haka ba wanda zai jisu. Isowar Abban kenan daga Hadejia don har Umma ta cire rai akan yau zai dawo, sai gashi kuwa ya iso a daren.

Kiciniyar bude kofa ne ma ya farkar da Fareeha daga baccin data dan fara yi. Itama a ranar ta iso daga Kano dan shekaranjiya suka gama exams. Dayake hutun karshen session ne sai Bappah yace tayi zamanta a Azaren kawai har sai bayan biki tunda Kanon za'a kawo ta.

"Ka kwantar da hankalinka Abban Bilal, idan Allah yayi bazaka saida gonar nan ba bazaka siyar ba fa duk dabararka. Idan kayi hakuri sai Allah ya kawo maka kudin ta wata hanya. Mu godewa Allah ma da ta samu miji, shine muhimmi. Kuma yana da muhallinsa nasa na kansa. Tada hankalin mu akan kayan daki shine abu na karshe da ya kamata muyi"

"To haka za'a kaita empty? Ya dage yayi gininsa sai a bar mishi gida babu komi a ciki?"

Umma ta sake saukar da muryarta kasa-kasa amma duk da hakan dayake dare ne sai da Fareehan ta jiyo su. "Ya san da hakan ai tunda dai sai da ya fara zuwa gidan nan yaga yanayin gidan kafin ma ya ganta har ya bude baki yace yana sonta. Don haka dan Allah ka janye maganar zancen saida gonar nan tunda dai an rasa me siya. Iya abun da aka tara sai a mata gado daya da shi. Tunda Bappah yace zaiyi...."

"Yanzu ni a matsayin ubanta sai in mata gado daya kacal? " Abba ya fada da wani daci a muryarsa.

Hawaye ne suka fara zuba daga idanun Fareeha yayinda taji wani abu ya tokare mata a makoshi. Dama haka iyaye suke tada hankulansu su sadaukar da dukiyarsu don su sama wa yaransu farin ciki? Yanzu dama Abbanta gona zai siyar don kawai ya mata kayan daki? Ya Salaam.

Toshe bakinta tayi tana kokarin hadiye kukan nata. Allah ya so ta Anti Mami da Ahmadi sun tafi Jama'are gano Gwaggo don haka ita kadai ne a dakin.

Kasa tsaida hawayen tayi don zuciyarta zafi take mata. Ita kam zata iya hakura da komai a kaita daga ita sai kayan sawarta in dai sai Abba ya taba kadararsa kafin ya mata kayan daki. Ta yafe gadon ta yafe katifar.

Kamar yadda Umma ta fada Engineer ya san karfinsu kuma a haka ya ganta yace yana so don haka baya tsammanin zasu cika mishi gida da kayan alfarma. Tasan ko da ba'a kaita da komai ba hakan ba zai rage mata kima da daraja a idonsa ba don shi din mutumin kirki ne me dattaku.

A haka ta cigaba da sakar zuci har bacci ya dauketa.

Washegari ta tashi idonta sun kumbura suntum. Umma data ganta bata tambayeta me ya sameta ba don itama jiyan kusan kwana tayi batayi bacci ba ganin yadda Abban ya tada hankalinsa batun saida gona.

Gonar da zai siyar din a can Maigatari ne to an rasa  mai siyen ta anan kusa da garin, wanda suke da kudin siya kuma ta musu nisa sosai. To jiyan kan har yayi tunanin ko gonar Hadejian zai siyar tunda wannan din taki yiwuwa.

"Haba Abba. Gonar da muke ci muke sha a dalilinta? Ko ka manta cewa da taimakon Allah da taimakon Baba Zubairu da sudin goshi ka sameta? In ka siyar da ita muyi yaya kenan?" Abunda ta ce mishi kenan a jiyan da ya sake dauko maganar bayan sun kwanta.

Da karayar arziki ta same shi shagon sa na saida magunguna a kasuwa ya kone kurmus, tallafin da Yayan nasa ya iya bashi kenan, wannan gonar.

Daga hekta daya sai Allah ya sanya mata albarka har ya siye wasu 'yan hektocin dake kusa da nashi ya hada ta bunkasa. Kuma Alhamdulillah yana samun albarka daga wajenta ga shi kuma tunda shi Baba Zubairun harkar gona ya saka a gaba don haka yana duba masa gonar tasa akai-akai.

"Sai na koma chan Maigatari da noman" amsar daya bata kenan.

Dukda a cikin duhu suke sai da ya ji kaifin kallon da ta watso masa a lokacin. Ta yaya ma zai fara wannan zancen? "To idan auren Qulsoom ya tashi kuma fa? Sai ka siyar da ta Maigatarin kenan?"

Yayi shiru.

"Idan auren Inayaah kuma ya tashi sai a siyar da gidan nan kenan"

"Lami" ya kira sunanta cikin kashedi.

Ta numfasa. Ranta ya baci kololuwa, amma tasan kalamanta sun masa zafi.

Hannu ta sa ta dafa kafadarsa. "Kayi hakuri. Bana jin dadin tayar da hankalinka dakakeyi akan lamarin nan. Muci gaba da hakuri. Allah zai kawo mafita"

A haka suka bar maganan amma ko yau da safe da ta tashi taga yanayin sa, har yanzu hakalinsa bai kwanta ba.

Jiki babu kwari daga ita har Fareehan haka sukayi aikin gidan suka gama. Suna gamawa kuwa ta shiga dakinta ta dauko wani bokiti mai cike da ganyen lalle ta bawa Fareeha.

"Ki debi kofi daya ki tafasa a tukunya. In ya tafasa sai ki sirka kiyi wanka dashi. In kinyi wankan sai kizo ina jiranki"

Fareeha kamar ta daura hannu akai tayi ihu. Dama sai da Yusrah ta fada mata. Tana komawa gida za'a fara mata al'adu da jike-jiken shirya amarya. Kai subhanallah.

Ranta baya so haka tayi abunda Umman tace.

Bayan ta fito a wanka ta shirya Umman ta mika mata kofi ta ce ta sha. Madarar shanu ce tsabtatacciya wanda aka sakawa dakakken hulba.

Haka aka rinka mata har na tsawon sati biyu. Anti Mami ma data dawo ta hadata da scrubs iri-iri duk bayan kwana biyu sai ta yi.

Abun mamaki ita kanta sai ta fara ji da ganin canji a jikinta.

"Har an fara gyaran jiki ne mutumiyar. Kinga wani hasken da kikayi kuwa?" cewar Hafsatu a lokacinda ta zauna a gadon dakin su Fareehan.

Fareeha ta juya idonta. "Hadda ke kema? Nikam ba wani hasken danayi bana son sharri. Dama da haske na kuka ganni"

Hafsatu tayi dariya. "Gaskiya Engineer idan ya ganki ba zai gane ki ba. Ziza!"

Duka Fareeha ta daka mata a cinya. "Ya isa to. Idan zolaya ta kikazo yi to ki tashi ki wuce"

"Yi hakuri amarsu ta ango. Yaushe rabon da na sakaki a idona?"

Dayake calendar din makarantar su Hafsatun data su Fareehan ta banbanta, yawanci lokutan da suke hutu ita kuma Fareeha tana makaranta don haka sun jima basu hadu ba.

"Yanzu dai yaushe zamuje gidan lallen nan? Kinga ni bana so sai lokaci yayi muje kuma tace an riga anyi booking dinta"

Hafsatu ta kurbi zobon da Fareeha ta kawo mata a dazun. "Karki damu ai Falmata mutuniyata ce, kuma na dade da fada mata cewa ita zata miki lallen nan. Amma kamar yadda kikace kar sai lokaci yazo ta noke. Don haka wani sati kawai kizo gidanmu sai muje mu sameta"

"To Allah ya kaimu. Zan fadawa Umma"

"Ina nan zata zo ta miki?"

"Eh zai fi ai ko?"

"Gaskiya kam"

Haka suka cigaba da hirarrakinsu da tsare-tsaren abubuwan da zasuyi lokacin bikin. Walima ce dama kawai Fareeha ta tsara za'ai. In banda shi bata shirya wata bidi'a ba.

'Yan department dinsu ne suka tara mata guddumuwar dubu ashirin da hudu dayake kusan ita ce zata fara aure a cikinsu, don haka da wannan kudaden take da niyyar yin hidimar walimar. Ta san baza'a rasa abin da za'a kara akai ba amma da iznin Allah komai zai zo da wadata.

Hirar da sukeyi da Hafsatun bai sa ta dena tunanin zancen saida gonar da Abban yake da niyyar yi ba don yi mata gado da kujeru. Haka dai ta boye damuwar ta ta sake wa kawar tata fuska.

Bayan wasu 'yan kwanaki aka fara shiryar karban lefen Fareeha.

A satin daya gabata Anti Mami ta sanar da Umma cewa kanwar Maman Engineer din ta kirata akan zasu kawo lefen a karshen satin.

Ba gayya dayawa sukayi ba tunda ba auren farko bane a wajensu. Su biyu ne sukazo sai driver din daya kawo su. A hilux sukazo shake da kaya.

Anti Mami ne da yayyen umman su biyu, sai matar Baba Zubairu da Maman Walid ne suka tarbesu. Abinci mai sauki Umman tayi, sai matar Baba Zubairu ta taho da drinks da ruwa, Maman Walid kuma tayi snacks da zobo da kunun aya wanda aka basu suka tafi dashi a matsayin guzuri.

Kaya kam Masha Allah ba'a cewa komai, daman basu tsammaci kasa da hakan ba duba da yanda Engineer din yake da sakakken hannu da yawan ihsani. Amma hakan da yayin ma ya kusa shallake tunaninsu.

Haka Abba yasa kayan a gaba yana kallo da daddare bayan ya shigo. Dayake a falonsa aka karbi kayan don haka yana shigowa da su ya fara sallama.

"Ko zaki tayani shirya jakata? Gobe inshaAllah ina so na tafi Hadejia" abunda yace da Umma kenan data shigo masa da abincin sa na dare. Kallon daya mata ne ya tabbatar mata cewa har yanzu yana kan bakansa.

Bata bashi amsa ba ta karasa cikin dakin nasa. Tana bude wardrobe din nasa kuwa hawaye suka fara sintiri a fuskarta. Yanzu kam ta riga da ta gama karaya, Allah ne kadai gatansu.

Fareeha kam bayan ta dawo daga gidan Maman Walid data ga kayan sai jikin ta ya kara yin sanyi da lamarin. Sai ta samu kanta da kiran Injiniya don ta masa godiya.

"Ki rike godiyarki bana so" ya fada cikin zolaya.

"To in ba godiyar ba me zan maka?" Ta tambaya idonta cike da hawaye.

"Tsakanina da ke babu godiya Hauwa'u. Matsayinki a wajena ya wuce tilin akwatuna da duk wani abun duniya"

Hawayen da ta ke ta kokarin matsewa suka sauko kan kuncinta. Kalamansa sun shiga zuciyarta sun kwanta luf. "Nagode da irin son da kake min, ina kuma fata Allah ya bani ikon faranta maka fiye da yadda kake faranta min"

Engineer Faruk ya dade baiji addu'a ta ratsa shi haka ba, ko dan daga bakin Fareeha ne? Ko kuma dai don duk abun da ta fada yana tasiri a cikin zuciyarsa ne?. "Amin ya Rabbi Hauwa Kulu ta. Allah ya barmun ke"

Haka suka cigaba da hirarsu har sai da ta fara jin bacci tukunna ta mishi sallama.

Engineer ya sauke wayar daga kunnenshi sannan ya kashe motar tasa. Isowarsa gida kenan ya samu kiran nata, don haka yayi zaman sa a motar har suka gama hirar. Yunwa yakeji amma sam baya so ya katse musu tadinsu, don ma dai gimbiyar tasa ta fara jin bacci amma bai so su dena magana ba.

Makullin motar tasa ya saka a aljihun wandon sa na chinos kafin ya taka zuwa kofar da zata sada shi da falon gidan. A hankali ya tura kofar tare da yin sallama.

Sanyin AC ne da kuma kamshi mai dadi ya ziyarci hancin sa a lokacin da ya saka kafarsa ya shiga falon.

Ba wanda ya amsa sallamar tashi saboda babu kowa a falon don haka kai tsaye ya sake kutsawa cikin gidan wajen Hajiyar sa.

A dakin ta ya same ta ita da kanwarta Gwaggo Iyyaluwa da 'yar autar Hajiyar Hajar wanda sune tawagar kaiwa lefen.

"Ango kasha kamshi" Hajar ta fada tana murmushi yayinda Gwaggon nasa ta buga guda.

Dariya yayi cike da annashuwa amma ya lura da yadda Hajiyarsa ta dan kauda kanta ta bata rai, don haka sai ya tsagaita dariyar tasa.

Tun ba yau ba yasan hankalinta bai gama kwanciya ba akan auren nasa. Da ya zo mata da zancen maimakon ta mishi addu'ar sanya alkhairi da fatan dacewa sai ta haushi da fada.

"Yanzu Umaru duk fadin Kano ka rasa mata sai da ka luluka can wani garin da bamu san kowa ba?"

Nan ya shiga mata bayanin cewa yarinyar tana matsayin 'ya ne a wajen matar marigayi Mukhtar abokin sa.

"Dorin dosano" ta yatsina fuska. "Wannan hawa hawan dangantaka. Bama kanwar Muttarin ba, 'yar yayar matarsa fa. Uhm!"

Haka dai yayi ta lallabata har ta sassauto akan zancen don yanda yake jin Fareeha a ransa idan Hajiyarsa tace ya hakura to za'a samu matsala don yana ganin zai mata abun da bai taba mata ba kenan, wato kin jin maganar ta.

Shi a kullum farin cikin ta yake son gani, duk wani abu kuwa da zai bata mata rai to zai iya rabuwa da shi ko yaya yakeson abun kuwa. A karo na farko akan Fareeha yakejin kaman zai iya bijirewa Hajiyar sa. Addu'a yake kawai kar Allah ya kawo su wannan bigiren, a samu ayi bikin nan lafiya a gama lafiya. Kuma yana fatar Hauwa Kulun sa da Hajiyar sa su kulla kyakyawar alaka mai dorewa.

Da magana a bakinsa ya shigo dakin, saidai ganin yanayin Hajiyar yasa ya samu waje ya zauna hade da gaida Gwaggon nasa.

"Sannunku da dawainiya Gwaggo. Allah ya saka da alkhairi "

"To ai kaine da dawainiya Babana. Irin wannan kayan da ka sheka musu, Tubarkallah Masha Allah"

"A hakan ma dai sai da Hajiya ta rage" Hajar ta fada tana kallon Hajiyar tasu.

"Ni kar ki min sharri. Ba rage wa nayi ba, canja wa nayi"

"To Hajiya kin canja babban zani da karamin zani ai kam ragewa kikayi"

"Nikam kin maida ni sa'arki ko? Tashi ki bani waje"

Tana dariya ta bar dakin. Suma duk sauran dariyar sukeyi. Dukda abin beyi wa Engineer dadi ba amma sam bai bari ya dame shi ba. Don wani zancen zannuwa da kaya sunyi yawa ba abun tada hankali bane. Tun da dai an amince yayi auren ai shikenan, falillahil hamdh.

Haka dai suka shiga wata hirar daban don yaga kamar yau an tabo Hajiyar ta sa. Daga baya Hajar ta kawo mishi abinci ya ci ya musu sai da safe ya wuce sashen sa.

*****

Maybe, just maybe I might update another chapter within the week. Let's just hope everything slows down.

Taku a kullum,
Miryamah.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top