2.

Ummyasmeen read the first chapter, I had to update💫💫🔥🔥. I am shocked and happy at za same time. Wayyo excitement😭😭😭💐💐💐💐.

2.

Yadda Umma ta tafi ta barta a falon a durqushe a kan kafet din haka ta cigaba da zama tana sharar qwalla a hankali. Maganganun Umman sun sosa mata rai matuqa. Zuciyarta tana mata zafi sosai, amma Umma ta ce mata ta daure. Hakan zatayi. Ko dan Ahmadi ma zata cije ta shanye duk wani baqin ciki har sai an kamo bakin zaren.

Wasu hawayen suka sake kwaranyo mata yayinda ta tuno masoyinta kuma abar qaunarta, Mukhtar.

Shekaru hudu kenan da aurensu, auren da aka gina shi bisa soyayya da qaunar juna fisabilillah.

Sun hadu ne a garin Jama'are a lokacinda Mamin ta je bikin qawarta. Akayi sa'a kuwa shima Mukhtar din yana cikin abokan ango. Kallo daya ya mata a lokacinda suka je budan kai yaji gaba daya ta shiga ransa. Baiyi qasa a gwiwa ba kuwa ya biyo ta har Azare bayan bikin domin sanin gidan su da kuma nasabarta. Watanni biyar suka shafe suna soyayya kafin nan aka daura musu aure. A lokacin Mami batayi shekara da kammala secondary school ba.

A lokacin auren nasu Baffa Dattijo yake sanar da Mukhtar din cewar zai kyautu idan Mami ta cigaba da makaranta koda kuwa college of education ne. Mukhtar yayi maraba da shawarar kuma yayi alqawarin zai nema mata gurbin karatu da zarar sunyi aure.

Aurensu keda wuya ya fara shirye-shiryen maida ta makaranta. Labari ya iske mahaifiyar sa. Ai kuwa tayi tattaki tun daga Gamawa tazo ta tsige shi. Sam taqi yarda akan cewa Mami zata koma makaranta. A fadin ta, zata je ta hadu da shaidanun qawaye su hanata zaman aure. Babu hanyar da Mukhtar bai bi ba domin ya shawo kanta amma hakan ya faskara.

Daga baya dai da sauran dangi suka saka baaki sai ta yanke shawarar cewa idan Mami ta haihu ta kuma yaye dan, sai ta shiga makarantar. Mukhtar bai so haka ba amma babu yadda ya iya. Hakan kuwa akayi. A ka jingine zancen makaranta aka zuba wa Mami ido.

Shiru-shiru babu ciki babu labarin sa. Watanni suka shude har ana neman shekara.

Gwaggon Mukhtar ta sake zuwa ta tunatar musu cewa Mami ba zancen zuwa makaranta sai ta haihu.

Hankalinsu ya tashi. Mami tanason tayi karatu, ko don a gaba ta tallafa wa mijinta wanda yakeda madaidaicin qarfi. Shima Mukhtar din yana so tayi makarantar, ko da batayi aiki ba kuwa zata ilimantar da 'yayansu kuma hakan kamar wata garabasa ce a wajen sa.

Bayan shekaru biyu sun shude Gwaggon Mukhtar ta kasa zama zaune don haka ta yanke shawarar nemo wa Mukhtar wata matar domin ta lura cewa Mami juya ce, bata haihuwa.

Babu yadda Mukhtar baiyi da ita ba akan ya ganar da ita cewa ita fa haihuwa ta Allah ce. Babu mahalukin da ya isa ya sa ta auku idan Allah baiyi ba. Duk wasu hadisai da ayoyin Alqur'ani Mukhtar saida ya karantar da Gwaggo domin dai tayi haquri ta bar zancen qara aure. Da taga da gaske yake sai ta fashe da kuka, wai ya rainata ita zai mayar jahila har Allah Annabi yake karanto mata. Ta nuna mishi bacin ranta qarara kuma tace ya fita batason ta qara ganinshi.

Ya bata haquri amma tayi mirsisi akan hakan. Bayan kwana biyu ya sake dawowa neman gafararta kuma ya qara tunasar da ita akan cewa koya qara aure kobai qara ba idan Allah yaso zai bashi haihuwa kuma zai iya hanashi. Gwaggo ta dage akan sai yayi auren nan kafin nan zata yafe mashi cin mutuncin daya mata a cikin daaki.

Haka ya dawo wajen Mami fuska ba yabo ba fallasa ya zayyane mata komai. Ta tausaya mishi matuqa. Amma duk yadda kishinta yake ta qonata mata zuciya hakan bai hanata bashi qwarin gwiwa ba akan ya amince yayi auren. Baiso hakan ba, amma ta tilasta. Koba komai zai samu ladan bin umurnin mahaifiyarsa kuma suma zasu samu kwanciyar hankali a rayuwarsu.

Bayan wata uku aka daura auren Mukhtar da Zaliha. Aka kawota gidanshi a matsayin amaryarsa. Gwaggo farin ciki kamar ta zuba ruwa a qasa tasha.

Mami ta karbeta hannu bibbiyu dayake tsakanin shekarunsu babu wani rata sosai. Komai idan zatayi tare sukeyi. Ta rinqa janta a jiki har suka saba.

Tun Mukhtar baya kula Zaliha har yazo daga baya ya fara shiga sabgarta duk a dalilin Mami.

Tafiya tayi tafiya bayan wata shida da aurensu sai ga Zaliha da ciki wata biyu. Gwaggo kam farin ciki kamar zata taka rawa a tsakiyar kasuwa. Saidai tasa aka mata Masa tayi sadaka a masallacin unguwarsu.

Zaliha kam taga gata. Gwaggo sai nan-nan take da ita. Shima Mukhtar din duk ya tattara hankalinshi ya mayar akan ta. Motsi kadan yace "sannu dai. Kinason wani abun ne?"

Mami ma tun abun yana tokare mata maqogoro har tazo itama tashiga sahun masu kula da mai cikin. To abinda mijinka yake so ai Kaima saika soshi. Abinda basu sani ba a lokacin kam Mami itama tana qunshe da nata cikin wata uku. Ita kanta batasan tanada shi ba domin laulayin da tayi na lokaci qalilan ne kuma ma baikai ga taje asibiti ba balle har a gwada ta. Saidai data dade bataga al'adarta bane ta fara tuhumar kanta.

Cikin Zaliha nada wata uku tayi bari. Mukhtar har saida ya zubar da qwalla domin yaci burin ganin babynsa. Bayan an sallamesu daga asibiti Zaliha ta koma gidansu domin ta qarasa jinyar don har wankin ciki saida akayi mata domin incomplete miscarriage ta samu.

A wannan lokacin kuma hankalin Mukhtar ya dawo ga Mami har ya lura da wasu canje-canje a tattare da ita. Ya tambayeta ko tanada ciki tace batada komai. Aikuwa ya debeta sukayi asibiti. A ka tabbatar musu wata hudu. Duniyar Mukhtar ta dawo sabuwa fil. Kulawar daya nuna wa Zaliha a baya sai ta ninku akan Mami.

Zaliha kuwa tana dawowa daga jinya ta samu labarin cikin Mami. Sai baqin ciki yayi mata katutu a zuciya. Ta sa a ranta cewar Mami ce ta zubar mata da ciki domin ya zama ita zata fara haihuwa a gidan. Musamman ma data ga Mukhtar ya karkata akalar rayuwarsa gaba daya ya dora akan Mami da abinda ke cikin ta, sai ta qara gasgata lamarin.

Nanfa ta shiga qulle qullen yadda zata raba Mami da cikin. Hakan bai yiwu ba da ikon ubangiji. Mami ta haife dan ta a wata ranar asabar da asuba. Yaro fari sol mai kama da babansa. Yaci sunan kakan sa na wajen mahaifi wato Ahmad.

Maimakon Mukhtar ya qara nuna kulawarsa akan na baya tunda yaron ya zo, sai Mami taga kamar baya maraba da haihuwar ma sam. Kanta ya kulle. Meke faruwa to?

Gaba daya ya dauke mata. Idan ya shigo wurinta to tambayar ta zeyi ko suna buqatar wani abu, daga haka kuma sai yayi tafiyarsa. Ko Gwaggo ma da daa ta tsaneta yanzu kam sonta takeyi. Toh shi Mukhtar din meya same shi?

Bata dai ce mishi komai ba haka ta rinqa binshi da ido yana yanda yakeso a gidan. Da abin ya isheta sai taje gareshi domin suyi magana ta fahimta, amma sam bai bata fuska ba. Wai qarnin haihuwa take don haka idan ta dena sai suyi maganar. Mamaki ya cika Mami, amma batace komai ba. Ta zuba musu ido shida Zaliharsa.

Idan ya dawo a aiko koba girkin Zaliha bane wajen ta yake zuwa susha hirarsu. Watarana ma da abun tabawa yake shiga, idan sun gama lashewa akawo mata saura wai ladan ganin ido. Ita dai bata taba tanka musu ba, hankalinta gaba daya yana kan hasken idaniyarta wato danta. Kulawa take bashi sosai. Nan kuwa yaro yayi wayo bul-bul abunsa tubarkallah. Kyaunsa ya qara fitowa dadi da qari ga wasu dimples da Allah ya azurtashi dasu.

Kwatsaam watarana Mami ta fito a kicin da robar wankan Ahmad, tafasashen ruwa ne a ciki zata je bakin randa ta sirka, saiga Zaliha ma ta danno cikin kitchen din. Sukayi karo kuwa. Ruwan gaba daya sai a jikin ta. Zaliha ta tsala ihu, Mami kam sai salati da tsoro daya ziyarci zuciyarta. Mukhtar dake wanka a bandakin Zaliha yayi sauri ya watsa ruwa ya fito. Halin daya tsinci zalihar ya rikirkitashi. Ya sungumeta sai mota. A asibiti aka bata taimakon gaggawa. Allah yaso qunar ba sosai bane domin fatar bata duri ruwa sosai ba amma de kam tasha azaba.

Bai dawo gida ba sai bayan Maghreb domin a asibiti ya wuni wai shi a dole jinya yake. Ya sami Mami tayi jugum jugum tun safe babu abinda taci Ahmad dinma da qyar ta samu ta mishi wanka domin jikin ta yayi sanyi gaba daya. Gashi bata san halin da Zalihar ke ciki ba don shi madugun be dawo ya bata bayani ba.

Anan yace tana son kashe mishi mata don haka baze iya zama da ita ba ta tattare kayanta ta koma gidansu ya sawwaqe mata.

Hawaye suka zubo a idon Mami a lokacinda ta tuno irin cin zarafin da Mukhtar ya mata a wannan daren, har watso kayan ta yayi waje. Bugu da qari harda cewa tunda tayi yunqurin kashe mishi mata, shima wataran zata kashe shi. Oh duniya! Wai Mukhtar ne yake mata wannan kalaman.

Aka daga labulen falon aka shigo, wannan ya katse mata tunaninta. Ta share hawayenta.

Kishiyar Umma ce wacce suka kirada Mama Mariya ta shigo.

Mami ta gaisheta.

Fuska a yatsine ta amsa "Ke kuma yaushe a gari?"

Mami ta amsa da "Jiya nazo"

Mama Mariya ta gyara zaman mayafinta wanda yasha adon duwatsu. "Toh sannu. Ina Mai dakin?"

Kafin Mami ta yunqura ta kira Umma, sai gata ta fito a dakin.

"Gani nan" ta fada a taqaice.

Mama Mariya ta dan saki fuska irin na miskilai.

"Dama zan raka Abban Bilaal Hadejia ne shine na kawo maki makullina." Ta miqa mata wani dan key "wannan kuma sauran qwai ne nace kar na bari ya baci tunda kinsan ana zafi. Nace ko za'a dafa wasu Qulsoom" ta ajiye ledar qwan a gefen kujera.

Umma tayi ajiyar zuciya. Tirqaashi! Har yaushe suka fara 'yar rakiya? In banda munafurci irin na Mariya, salon ta haddasa mata hawan jini. Ta san sarai ba tare zasuyi tafiyar ba, itama wani wajen zataje, amma saboda kisisina shine zatace wai zata rakashi Hadejia. Oh duniya. Umma tayi ajiyar zuciya.

"Angode. Allah ya kiyaye hanya" abinda tace kenan kafin ta juyo ta koma daki. Ko kallon inda qwan yake ma batayi ba.

Mama Mariya ta yatsina fuska kafin itama tabar falon.

Mami ta bita da ido kawai.

Sai wajen Azahar Bilaal ya farka. Gaba daya baiji dadin jikin nashi ba. Kwanan cell yayi, bayan 'yan sanda sun musu shegen duka.

Da qyar ya lallaba ya miqe. Ya fito tsakar gidan ya tari ruwa a famfo. Wanka yayi sannan a gurguje yayi sallar asuba da kuma azahar.

Falon ya shigo domin neman abin sawa a baki. Babu kowa amma yana jiyo muryoyinsu daga daki suna hira. Idonshi suka qyallaro wata yamusashiyar dari biyar akan kujera. Aikuwa yayi wuf! ya dauketa. Baiko leqa wajen Umman ba ya suri takalmansa se teburin mai shayi.

Yaci yayi nak! Sauran canjin ya sayi abin maye.

Shinkafa da wake Umman ta dora ganin yaran sun kusa dawowa daga makaranta. Ko dan man da za'a yayyafa akan abincin basuda shi. Ta tuno dari biyar din da Abbansu Bilaal ya ajiye mata. Ta hau nemanta kuwa.

"Mami, nikam dazu ba a nan na bar kudi ba?" Umma ke tambayar Anti Mami lokacinda take daddaga cushion din kujerun falon.

Mami ta leqo falon.

"Eh dazu tana nan wajen inda Mama Mariya ta ajiye ledar qwai"

Umma tayi shiru tana nazari, kafin ta miqe ta leqa dakin Bilaal. Ba ya nan.

"Bilal baze dauke min kudi ba. Ban koya mishi sata ba." Abinda ta ayyana a ranta kenan. "Wataqil ta shige wani wajen"

Anti Mami ce ta taimaka ta siyo musu man da dan kudin dake wajen ta. Ta hado da cabbage da kuma busashen barkono. Ita ta daka yajin yayi laushi sosai sannan ta wanke kabejin ta yayyanka qanana. Koba komai abincin gidan ze danyi fasali yau.

Da sallama a bakinsu suka shigo gidan. Anti Mami ta amsa musu. Qamshin soyayyan mai ya daki hancinansu.

"Laaaa shinkafa da wake akayi yau?" Inji Inayaah a lokacinda ta cire hijabinta ta yi wurgi dashi a kan kafet. Qulsoom najin haka ta ruga zuwa kicin din domin ta gane wa idonta.

Fareeha ta harareta "Maza dauke hijabin nan ki shiga dashi kafin na saba miki"

"Ah ah Adda ayi haquri mana" cewar Anti Mami a yayinda take taya Inayaar cire socks dinta. "Bari ta ci abinci sai ta dauke ko?"

Fareeha ta zumbura baki ta wuce cikin dakin Umma. Ta samu tana sallah don haka ta dawo ta shige nasu dakin. Bayan ta ajiye jakarta a lungu gadon ta shige bandaki ta kimtsa. Ta shirya cikin wata doguwar riga me siririn hannu dai-dai shan iska domin kuwa ana zazzaga zafi a garin, Alhamdulillah.

Ta samesu a falo sunyi zuru-zuru suna kallon qaton tire din da Anti Mami ta shaqeshi da abinci.

"Adda ke muke jira fa" Qulsoom ta fada tana hadiyar yawu.

Sai tausayinsu ya kamata. Ta rausayar da kai a yayinda take kokarin zama kan kafet din.

"To ai da kunci abunku. Idan nazo na debo nawa"

Inayaah da tuni ta cika bakinta da abinci tace "To ai Umma tace mu rinqa cin abinci tare"

"Inayaaah ba kyau" Qulsoom ta kwabeta "ki cinye na bakinki kafin kiyi magana"

Umma ta fito daga daki ta samesu. Farin ciki ya mamaye zuciyarta ga 'yanmatanta suna cikin walwala da son junansu. Yau ga abinci isashshe sun samu harda qarin kabeji. Inama haka rayuwa zata ci gaba da gudana?

"Kai Umma an dade ba'ayi abinci me dadi a gidan nan ba. Ko wani abun ne ya faru?"cewar Inayaah lokacinda ta dawo daga kai tray din kitchen.

Umma ta murmusa. Yaro kenan. Wato sai wani abun ya faru za'aci abinci me dadi.

"Ba abunda ya faru Inah. Amma kince Alhamdulillah kuwa?"

Inayaah ta danyi shiru tana nazari? Ta ma ce Bismillah kuwa daza taci abincin? Balle kuma Alhamdulillah?

"Ban fada ba" ta fada tana yaqe haqorinta wanda ke da wawulo. Haqoran saman duk sun zube.

Umma tayi dariya.

"To ki godewa Allah. Kinga idan kika gode masa, to zai qara mana. Sai muyi ta girki me dadi"

Ranar Inayaah wuni tayi tana rera Alhamdulillah a cikin gidan. Idan wani abun ya dauke mata hankali, tana tuno da zancen Umma sai kuwa ta ci gaba da fadin Alhamdulillah. Su dai sauran sai dariya suke mata.

Bayan la'asar 'yayan Mama Mariya, Lawiza da qaninta Sufyan suka shigo sashen su Fareeha karban key. Umma ta dubesu a lokacinda take miqa wa Lawizar makullin.

"Ku kuwa ina kuka tsaya sai yanzu kuke dawowa?"

Sufyan yayi caraf yace "Ai mamanmu ne tace idan an tashi muje gidan Antinmu muyi wanka muci abinci kafin mu dawo gida"

Fareeha da ke tsaye a bakin qofar dakinsu tana daura dankwalin uniform din islamiyyarsu ta ce "Dayake anan din baza a baku abinci ba ko?"

Umma ta juyo ta watsa mata kallo "Wa ya sa bakinki a ciki? Nace dake ake?"

Ta dan sunkuyar da kai bata ce komai ba. Lawiza kuwa in banda harararta ba abinda take.

Umma ta dan dafa kan Sufyan tace "Toh Dan mamanshi daga yanzu idan kun dawo daga gidan Antin naku sai kuzo nan in qara muku ko?"

Lawiza taja hannun Sufyan "Mun qoshi" kawai tace sukayi fitarsu.

Umma ta bisu da ido.

A hanyarsu ta islamiyyah suka hangoshi shida abokan shashancinsa suna hira a gaban wani shago.

"Adda kinga Ya Bilaal can. Muje muce ya saya mana cingam?" Inayaah ta tambaya cikin zumudi.

Fareeha ta dauke kai kamar ba ta ganshi ba. Ta qara saurinta.

"Adda mana" Inayaah ta fadi cikeda shagwaba.

Fareeha ta watsa mata harara "Idan baki mun shiru ba zan mammake ki yanzun nan. Haa'an. Mutum se surutu kaman aku."

Qulsoom ta matse dariyarta yayinda hawaye suka ciko a idon Inayaah. Bata ce komai ba kawai ta cigaba da fadin Alhamdulillah.

Dama ita Fareeha kaf ajinsu qawarta guda daya, Hafsatu. Don haka da ta shiga ajin taga Hafsatu batazo ba, sai ta samu waje can lungun tabarma tayi zamanta.

Sam bata son shiga harkokin sauran. Yara qanana amma in banda zancen samari ba abunda sukeyi a aji. Ko kuma a kawo litaffin hausa ayi ta karanta wa. Wasu lokutan kuma basuda aiki sai zancen 2go. Ita Fareeha dama ba waya gareta ba, don haka bata ma san ya ake 2go dinba balle ta shiga cikin zancen nasu. Bugu da qari, Umma bata son karance-karancen littafin hausan nan. Hasali ma, in banda Magana Jari Ce da Iliya Dan Maikarfi, babu wasu litaffan hausa da ta sani. Ta balle aje ga saurayi kuma. Duka-duka shekarunta sha hudu a duniya, me ma ta sani. Domin haka babu category din daya dace da ita a ajin. Shiyasa suke rayuwarsu su biyu itada Hafsatu. Ba ruwansu da kowa. Abunda aka turosu makaranta suyi shi sukeyi. Wato karatu.

Da suka taso a islamiyyah saida suka tsaya gidan Maman Walid suka karbo awara. Dama jiyan ta ce wasu Inayaah idan sun dawo a makaranta suje su karba.

Ran Inayaah fari sol yau za'aci awarar Maman Walid. Suna shiga gida suka tarar da Baffa Dattijo yana alwala a bakin famfo zashi masallaci. Murna ya cika su. A tsaitsaye suka gaisa ya ce in ya dawo a masallaci sai ayi gaisuwar mai kyau.

Kwalin indomie, taliya, makaroni da na madarar ruwa ne suka musu salamu alaikum a lokacinda suka shiga falon. Fareeha ta tsaya turus tana kallon kayan.

"Umma wannan fa?" Ta tambaya

Umma dake qoqarin miqewa ta shiga daki ta amsa "Baffanku ne ya kawo". Suka hada ido da Inayaah, habawa Inayaah ta daka uban tsalle.

" Alhamdulillah. Allah mungode maka daka qara mana"

Dukkansu sukayi dariya.

★★

Kwance yake kan lallausan gadonsa, yayi ruf da ciki yana sharar bacci. Baccin daya dade bai samu ba. Zango biyu yayi tsakanin New York da Chicago, don haka a gajiye yake. Sanyin AC ya ratsa ko ina a dakin ga wani ni'imtaccen qamshi yana tashi ta ko'ina.

Aka turo qofar dakin aka shigo. Wannan ya saka shi farkawa amma bai bude idonshi ba. A hankali aka zare mishi fararen takalmansa. Socks ya biyo baya. Kafin nan kuma ta hayo gadon ta kwanta a gefensa. Ya dan juyo da fuskarsa kana ya bude idanuwansa. Caraf, ta cafkesu cikin nata. Kallon ya rikirkitashi. Yayi ajiyar zuciya.

"Welcome home" tace dashi tana mai murmushi. Zara-zaran yatsunta ta daura akan fuskarshi tana shafa sajenshi. "Nayi kewarka"

Har cikin bargonshi yaji kalamanta. Ya lumshe ido sannan ya sake budesu.

"Nima nayi kewarki Najma"

Qarar fashewar abu ne ya fargar dashi.

Firgigit ya tashi zaune, gaba daya ya jiqe da gumi kamar babu AC a dakin. Ya sa hannu biyu ya dafa kanshi wanda ke masa azababben ciwo.

"Ya Salaam" abinda ya iya furtawa kenan. Ya samu ya cire rigarshi saura vest mai guntun hannu.

A hankali ya sauko a gadon ya nufi hanyar kitchen inda yake zaton anan ya jiyo qarar.

A durqushe ya sameta tana faman share kwanon daya fashe a dazun.

"Ammi?" Ya kirata a hankali.

Ta juyo da sauri. "Ayya Mu'azzam, sorry to wake you. Wai zan maka heating lasagna ne kuma kaga dish din ya fashe"

Muazzam ya nisa.

A tsakanin 'yan kwanakin nan ya lura Ammin nasa tama fishi shiga tashin hankali. Batada aiki saidai ta sidado ta shigo gidan shi idan baya nan ta cika mishi fridge da abinci, ta mishi wanki, wasu lokutan ma har cleaning company take kira suzo su qalqale mishi gida. Duk don wai akan bashida me mishi yanzun. Ko ta manta cewar shima ze iya duk wannan ayyukan?

Ya dubi agogonsa. A wannan lokaci yakamata ace tana office.

"Ammi aikin fa?"

Ta zubda sharan yayinda take qoqarin nemo wani mazubin "Lunch break" ta amsa a taqaice.

Wannan lunch break din akwaishi da tsayi kuwa.

Ya zagaya ya isa gareta. Hannu biyu ya saka a kafadunta ya juyota gareshi.

Ta fuksanto shi, amma kanta a qasa.

"Ammi look at me" ya fada a hankali. Da qyar ta dago ta kalleshi. Idonta fal hawaye.

Yaji  wani abu na mishi zogi a zuciyarsa. Oh yaya zaiyi da Ammin nan nasa ne? Ya sarqe hannunta cikin nasa.

"Ammi I'm fine. Ki dena damuwa don Allah. Wannan sintirin da kike a kaina ya kamata ki tsaida shi haka. Kema fa kina buqatar hutu. Kin sani ko?"

"Muazzam in ba kula dakai ba waze kulamin dakai? Najma bata....." Sai kuma tayi shiru.

Muazzam ya furzar da iska.

"I'm a grown up Ammi. Ni zan iya kula da kaina. Dan Allah ki huta kema."

Ta share hawayenta. "Muazzam you are not fine. Kullum saika kira sunanta a cikin baccinka. Yau ma....."

Ya qara damqe hannunta.

"Ammi please. Stop"

Wasu hawaye suka gangaro mata.

"Muazzam ka dena volunteering a masjid, basketball dinda kake zuwa ka dena zuwa yanzu. When last did you go to the gym uhm? Ga plants dinka nan on the patio, if not for me nasan da sun mutu. You are not yourself. Na fada maka...."

"I'm not going to see a therapist Ammi!" Yayi furucin cikin zafin nama. "Abinda ke damuna ni kadai ya shafa, I don't have to empty my emotions in front of some psychopath."

Ya juya da zummar tafiya dakin shi. Ta riqo hannunshi. A hankali ta janyoshi jikinta, ta rungume shi. Nan hawaye sukace Salamu Alaikum.

Ta bubbuga bayan shi cikin tausaya wa dan nata tilo guda.

"Bance kaje gurin therapist ba Mu'azzam. You have me. Let's talk about how much you miss her over a cup of hot mocha ko kuwa?"

Ya qara qanqameta a yayinda kuka ya ci qarfin shi. Kai kawai ya gyada mata.

Ta jashi suka koma kan kujera.

****

What is your opinion on mother and son relationships that are soooo soo tight? Like Mu'azzam and his Ammi.

I think they're cute. I love people who are very close and extremely to their parents.

Na gode da guddumuwarku akan littafin nan. Allah ya saka da alkhairi.

Taku a kullum,
Maryama.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top