19.

Godiya dubu dubu for all the support. Miryamah loves y'all ❤



Ranta fari kal tana jiyosu suna magana, tasan kuma ba hirar komai suke ba hirar ta ne. Don yanzu ba shi da wanda yake kaiwa korafinta sai Mami. Ita har mamakin sabon da sukayi ta ke. Kodayake ita din ma cikin lokaci kalilan suka saba. Mamin ce akwai shiga rai Masha Allah.

Cigaba da yanka kankanar tayi yayinda dariyar Mu'azzam din ke shigowa cikin kitchen din nata. Allah yaga zuciyar ta taso ta mishi zancen Mami a lokacin da ta gama takaba, sai gashi su da kansu sun hada kansu. Allah kenan, mai yadda ya so a lokacin da ya so.

Falon ta dawo dauke da tray din kankanar tana tsallake kwalayen da suka babbaza a falon wanda ko ina ka juya su kake gani. Ba komai bane kuwa a cikinsu in banda shirgin ta da zata bayar, wasu kuma za ta tafi da su.

Alhamdulillah cikin watan da ya gabata ta gama hidimar paperwork dinta yanzu kuma sai shirin komawa gida. Bata zaci kayan nata na da yawa haka ba don haka ta dauka zata iya packing ita kadai. Sai kawai taga abun na nema yafi karfinta shi ne ta kira Mu'azzam din akan ya taho mata da boxes kuma ya zo ya tayata hada kayan.

Sunyi zancen cewa zata koma amma se karshen shekara. Yana zuwa yaga abun beyi kama da se karshen shekara zata koma ba ya kuwa shiga rokonta Allah Annabi ta taimaki rayuwarsa ta canja shawara. Sam taki sauraronsa don tunda ta samu stroke dinnan hankalinta gaba daya yayi gida. Shine dalilin da ya sa ya kira Mamin yana mata korafin abun da Amman ta masa, ita kuma tana bashi baki. Daga baya da taga abun nashi bana yi bane ta hau tsonakarsa wai ya cika shagwaba kaman wani baby. Dalilin dariyar tasa kenan ta dazu.

Mika masa tray din kankanar Ammah tayi tare da zama a kujerar da ke kusa dashi. Ya karba yana fadin "Yanzu ba za ki roka min ita ba ko?"

Daga daya bangaren Anti Mami tace "To me kakeso na ce mata?"

Ya dauki kankana guda daya ya jefa a bakinsa yana taunawa. "Kamar de dake aka hada baki ko Mamish? Kin mata alkawarin wani abu ne in ta je can din?"

Ammah ta girgiza kai tana hada wasu litattafai tace "Nikam kun manta cewa ina zaune anan ne ko me?"

Duk su biyun dariya sukayi sannan Anti Mami tace "Kaga sai anjima bacci nakeji."

Ya daga kai ya kalli agogon falon wanda ya nuna karfe uku na rana, hakan yayi daidai da karfe tara na dare a Nigeria.

Ba a son ranshi ba yace"To sai da safe. A gaida Big man"

"Gashi nan shima yayi bacci. A cewa Ammah ina mata sannu da aiki"

Dayake wayar a speaker ya saka sai Amman ta amsa da"Nagode Mami. Mu kwana lafiya"

Yana katse wayar ta juyo suka hada ido.

"Yanzu ba zaki hakura ba?"

"What is going on?"

Duk su biyun suka fada.

Kifta idonsa yayi yayinda girarsa ta hade waje guda don rashin fahimtar abinda take nufi. "What is going on where?"

Gyara zama tayi tana tankwashe kafarta tace "Tsakaninka da Mami"

Ya bude baki zaiyi magana ta dakatar da shi "Kafin kace komai ina so kasani cewa idan ba neman aurenta kake yi ba there's no point wannan hirarrakin da kukeyi here and there. Don't get me wrong, I am happy about your friendship. Ku biyun kun gane pain din da kuke ciki kuma kuna taya juna alhini da kokarin yin tawakkali, sai dai zama abokan juna kawai bai kamace ku ba.

In kasan  neman aurenta kake to kaji tsoron Allah Mu'azzam; ta rasa mijinta, abokin zamanta, jigon rayuwarta, ya tafi ya barta da maraya, don haka bata lokaci ba nata bane. Idan kana da wani nufi akanta, to ka sanar da ita. Idan ta amince maka ba wanda zai kaini farin ciki, amma idan aka samu akasin hakan, sai kayi hakuri. Idan kuma baka da wani nufi akanta, to a ja layi a haka please. Don dai gaisawa na sada zumunci ba laifi bane. Amma wannan shakuwar tayi yawa"

Jikinsa ne yaji ya masa sanyi lokaci guda.

Abubuwa dayawa suka hade masa a kansa.

Shi dai ba zai ce yana jin wani abu game da Mami ba wanda ya wuce mizanin daya ajiyeta.

Sun sami fahimtar juna a dalilin rasa abokan zamansu da sukayi. Bugu da kari Ammah tana da muhimmanci a rayuwarsu duk su biyun. Wannan ne ya kara musu dankon shakuwa.

Ta bangaren Mu'azzam yana jin tausayin Mami, dan abun kamar da sauki idan ance miji ne ya rasa matarsa. Amma idan mace ce, abun da wuya matuka. Balle kuma ga nauyin yaro. Ga makarantar da take zuwa. Don haka duk sanda ta zo mishi da wani korafi, ya kan nutsu ya saurareta don yasan hakan zai rage mata wani radadin da take ji. Hakan yana wa Mamin dadi don sabanin yadda idan tayi wa su Umma da sauran 'yan uwanta korafe korafe (ranting) suke bata hakuri da bata baki, Mu'azzam sauraronta kawai yake. Ita kuma abun da take so kenan, a saurareta. A barta ta amayar da abinda ke ranta. Ai tasan da hakurin ba wai bata san da shi bane, kuma tana yinsa, ita dai kawai tana so ta rage zafin abin da take ji ne. Kuma ta sami hakan a wajensa.

Takan bashi labarin abin da ya faru da ita a makaranta, ko wani kalubale da ta samu a makarantar ko dai wani abun da Ahmadi yayi da ya taba mata zuciya. Ta lura in dai abu ya shafi zancen Ahmadi to anan ne zataji yana bata hakuri yana kuma kara jaddada mata cewa yanzu matsayi biyu ne ya hau kanta a kanshi; uwa da uba, don haka ta dena karaya.

Amma de kam in de matsalar ta ce sauraronta kawai yake. In an mata wani abun da bata so ne zai ce su wance wance basu kyauta ba. Idan 'yan zolayar ta sa suna kusa kuma sai yace 'Gobe in kun hadu ki kwakule musu ido'. Yakan bata dariya sosai. Kuma hakan na rage mata radadin data samu kanta a lokacin da ta kira sa. Shiyasa yanzu ba'a kwana biyu in be kira ba to ita zata kira.

Hankalinsa ne ya dawo kan Ammah daya ji tayi gyaran murya. Kallon sa take tana jiran amsa daga gareshi.

Jan numfashi yayi yana jujjuya wayarsa dake kan cinyarsa yace "I will think about it InshaAllah. I will do the right thing"

Ta jinjina kai. Hada kayanta ta cigaba da yi. Sai kuma suka shiga wata hirar daban.






Ya shafe kwana biyu yana juya maganar Ammah a ransa.

Tabbas shima shakuwar da sukayi da Mami yana basa mamaki wasu lokutan, amma idan ya dangana abun da lamarin ubangiji sai yaji ba komai bane. Tana da muhimmanci sosai a rayuwarsa, saidai baya tunanin zai iya zama da ita a matsayin matarsa.

Matsalolinsa dayawa. Akwai abubuwa game da shi dayawa wanda bata sani ba, kuma yana jin kunyar ta san hakan. Bugu da kari yana ganin girmanta fiye da yadda take zato, don haka idan ya aureta yana ga kamar be mata adalci ba. Yana da tabo dayawa a zuciyarsa ga tarin laifukan da ke masa yawo a jinin jikinsa, bai kamata ace ta kasance da mutum irinsa ba a matsayin mijinta.

Abotarsu tsabtatacciya ce. Kuma sun samu fahimta akan abubuwa dayawa. Da ace a da ya hadu da ita watakila ya bude mata zuciyarsa. Amma yanzu kam zuciyar tashi ta riga da ta lalace, ko da ya bude mata ita ba abun da zata mora a cikinta.




Shirun da ta ji na kwana biyu ne yasa ta dauki waya ta kirasa dukda ba wani isashen data bane da ita. Kwanan nan ta sauke manhajar Imo a wayar ta don haka tana samun saukin kiransa, a madadin da da katin wayarta take kira.

Bata same shi ba, don haka tayi tunanin ko yana wajen aiki. Sai can dare wajen sha daya sai ga kiransa, har tayi bacci ma amma ringing din ya tashe ta.

"Mamish" ya kira a hankali. "Allah sa ban tashe ki ba"

Murya cike da bacci tace "Ka tashe ni mana. Ina wuni?"

Yayi 'yar siririyar dariya. "To ki koma ki kwanta. Sai gobe inshaAllah zan kira"

Ta shi tayi ta zauna "Kuna dai lafiya kai da Amman ko?"

Zuciyar shi ta kumbura da jin dadin nuna kulawarta a gareshi dama Ammansa. "Lafiyar mu kalau. Sorry I went MIA, ayyuka ne suka min yawa. Gashi Ammah ta sani a gaba kan packing dinnan nata."

"Allah sarki sannu. Allah ya baka lada"

Ya dan turo bakinsa kamar tana ganinsa yace "Ai duk ke kika jawo"

"Ni kuma? Danayi me?"

"Kinsani ai"

Tuni bacci ya wartsake a idonta. Sai sha biyu da ta ga hirar tasa ba me karewa bane tace ita kam zata koma ta kwanta tana da class karfe 10 washegari. Yayi mata Allah bada sa'a sukayi sallama.

Ya dade a zaune bayan sun gama wayar yana ta sakar zuci.

Kwana biyun nan in banda addu'an neman zabin ubangiji ba abinda yake yi. So yake hankalinsa ya nutsu akan sha'aninta, sai ya tambayeta idan akwai abinda take ji game da shi a zuciyarta. Komin kankantarshi, yayi alkawari in de akwai wannan digon son nasa a zuciyarta, to tabbas shi kuma da iznin Allah zai maye mata gurbin Mukhtar. Zai dage ya kokarta ya shafe duk wasu abubuwan daya ke ganin sun rage masa nagarta ya gina sabuwar rayuwa da ita. She is amazing and she deserves all the good things in life. Kuma inshaAllah zaiyi kokari ya faranta mata.

A bangaren Anti Mami kuwa, hankalinta ya gama kwanciya da lamarinsa. Dama ita kullum cikin addu'ar Allah ya mata zabi take. Da kam ta cire rai da sake yin wani auren, shiyasa ma kowa yazo cikin mutunci take sallamarsa tun kafin zance yayi nisa. To amma da Mu'azzam ya shigo rayuwar ta sai ta ke tunanin ko watakila alama (sign) ne daga wajen ubangiji. Don yanda abun yazo gadan gadan ita kanta ya bata mamaki. Gashi lokaci daya sukayi clicking.  Alakar da suka kulla ne yanzu har yasa ta fara tunanin ko zata iya ba wa zuciyarta dama ta fara son wani har ma tayi tunanin auren sa.

Matsalolinta yanzu biyu ne. Na farko babu wani tazarar shekaru a tsakaninsu mai yawa, don shekara daya da rabi ya bata. Ba abun damuwa bane a musulunce amma ita dai abun ya dan dameta kadan. Na biyun kuma wanda shi ne babbar matsalarta shi ne banbancin wayewa da ilimi dake tsakaninta da shi, da kuma rashin sanin wani matsayi take da shi a wajensa.

Mutumin da aka haife shi a turai, ya girma acan kuma rayuwarsa kacokam a can yayi, shin zai durkuso yayi rayuwa da wacce tafiya mafi nisa data taba yi a rayuwarta shine zuwa Kano? Shi da kasashen da bai je ba a duniya za'a iya kirga su da yatsun hannu, zamansu zai yiwu da wannan banbance banbancen?



●●●

Kwance take a daki tana kallon wani vedion girke girke a YouTube sai ga Yusrah ta shigo. Basu dade da dawowa daga zana jarabawar Post UTME ba a BUK din. Results dinsu na WAEC dana NECO duka sunyi kyau Tubarkallah Masha Allah. Hakan ya sa Bappah yaji dadi sosai.

"Adda" ta kirata a hankali tana zama a bakin gadon.

A hankali ta juyo ta kalleta ba tare da ta amsa mata ba. Yanzu kam har ya gaji da kwaban ta akan ta dena ce mata Adda, abun ya riga da ya shiga bakinta har ma ta yada wa sauran 'yan gidan. Yanzu hatta Anti Bebi ma Adda take kiranta.

"Wani abu ne zan gaya miki amma ina jin kunya"

Dariya tayi tana tafa hannu. "Yau kuma? Ni surukarki ce daza kiji kunyata? Abeg fada min menene?"

Yusrah ta cije lebenta tana kokarin boye murmushinta.

"Samir ne yace zai turo a masa tambaya"

Fareeha ta zaro idonta waje cike da mamaki. "Kai haba de?"

Samir din wani dan kawar Anti Bebi ne. Tun dama akan aiko shi gidan nasu to amma dai shi da Yusrahn basu jone ba sai kwanan nan. Yanzu haka soyayyar tasu bata fi wata shida ba. Yana kokarin kammala karatunsa na Masters kenan a BUK din kuma a cikin makarantar yake aiki shima.

Gyada mata kai kawai Yusrah tayi don ita kanta abun mamaki yake bata.

Rungumeta Fareeha tayi tana 'yar kara wanda za'a danganta ta da na murna ne.

"Kice biki zamusha nan bada dadewa ba"

Yusrah tayi dariya "Sai anyi naki tukunna ai"

Sati biyu da suka wuce Bappanin Engineer Faruk suka dibi hanya zuwa Azare don kai goron tamabayar Hauwa'u Fareeha. An karbe su hannu bibbiyu kuma an basu yarinya. Yanzu sa rana ne kawai ya rage sai a fara shirye-shiryen kai Fareeha gidan Engineer. Shi yaso ayi abun ne ma a cikin wata uku amma Abba yace a dan basu lokaci tukunna su shirya.

Fareeha ta dan harareta "Kika sani ko a riga yin naki?"

"Hakane kam. Amma fa ina tsoro"

"Tsoron me?"

"Kinga naga bamu dade da haduwa ba, akwai sauran abubuwan daya kamata nasani a kanshi shima kuma akwai abubuwan da bai gama sani akaina ba. Tsorona shine kar suna zuwa a basu don kinga Baba yana ganin mutuncin Mummynsu sosai sosai. Banaso a zo a samu matsala daga baya"

Fareeha ta jinjina kai. "Gaskiya kuma hakane. Amma dai shawarar da zan baki shi ne kicigaba da Addu'a kawai Allah ya miki zabi, sai kiga komai ya zo da sauki. Ko baku gama fahimtar juna ba idan akwai alkhairi sai kuyi aurenku kuma ku zauna lafiya"

"You see why I call you Adda ko?" ta fada tana daga mata gira.

Tureta Fareeha tayi tana dariya "Matsamun dallah"

Itama dariyar tayi. Da ta ga Fareeha ta koma ta kwanta tace "Kin manta ne zamuje gidan Adda Samha? Naga kaman ko shiryawa bakiyi ba fa"

Ajiyar zuciya Fareeha tayi tana kallon rigar da ke jikinta. Bodycon ce wanda ta daura wa Kimono a dazu da safen da zasuje jarabawa, data dawo kuwa ta watsar da Kimonon tayi kwanciyarta.

"Nikam na fasa fa. Bana jin fita kuma"

"Na dauka kin ce wa Engineer ya same ki a can"

Nan da nan ta tashi ta zauna. "Kinsan na manta? Bari inyi alwala kinga tunda la'asar ta kusa sai muyi sallah a can gidan Adda Samhan. Kar ya je bama nan yayi ta jira"

"Ah lallai" yusrah ta jinjina kai tana kallonta cikin zolaya tace "Zanzo na dauki course fa Adda"

Duka Fareeha ta kawo mata tayi sauri ta fita a dakin tana dariya.

A gaggauce ta shirya tayi alwala ta sanya Abaya baka ta dan gyara fuskarta. A adaidaita sahu suka tafi don babu mai kaisu a gidan kowa ya shiga sabgar gabansa.

Cikin murna Samhar ta tarbesu da dan tulelen cikinta. Sun samu tayi dambun tsaki wanda yasha kayan lambu don haka suka hau ci. Sun gama ana kiran sallah don haka Fareeha ta tashi ta sauke farali. Ba'a jima ba kuwa sai ga wayar Engineer din ta shigo.

Mayafinta kawai ta gyara ta fita ta shigo dasu. A dan varendah din ta ajiye musu kujeru shi da abokinsa Yusuf. Kamar yadda ta saba mishi ruwa da zobo da abin tabawa ta kawo musu. Bayan sun gaisa sai Yusuf ya tashi akan zai je ya dawo ya dauki abokin nasa daga baya.

"Amaryar Faruk" ya kira ta bayan tafiyar Yusuf din.

Ta dan sunkuyar da kai tana murmushi cike da kunya. "Ya faruk mana"

"Yanzu ni baza'a ce mun Angon Hauwa ba?"

Murmushi ta sake yi. "Da saura fa. Saurin me kake?"

"Dan dai ina jin kunyar Abba ne da binki zanyi muje wajensa a matso da bikin nan"

"Ashe dama kana jin kunya?"

Dariya ta bashi sosai. "Wato ni mara kunya ne kenan?"

"A'a ni bance ba" ta girgiza kanta da sauri. "Kawai de naga abubuwa da dama basa maka nauyin fada ne"

Gyara zama yayi yace "Kamar me da me kenan?"

Da dan harareshi. "Ka san me nake nufi"

"Kamar Sweetheart kenan? Ko idan nace my love?"

Da sauri ta rufe fuskarta. "Innalillahi Ya faruk. Ni kam sai anjima" tayi yunkurin tashi. Nan da nan shima ya tashi dukda dariyar da yakeyi.

"I'm sorry my darling. Maida wukar to"

Dagowa tayi ta sake mishi wata hararar wanda yayi wa lakani wa 'kallon so'.

"Oops" ya dan rufe bakinsa wai shi a dole yayi subul da baka, duk da da gangan ya ce mata my darling din.

Komawa yayi ya zauna. "To ai ke din ce idan muna tare gaba daya bakina bayi da control sai yayi ta biyewa zuciyata in yi ta fada miki kalamai iri-iri"

"To zuciyar tayi hakuri tana yi kadan kadan"

Ya kwantar da kafada "Ina zatayi hakuri bayan an ki mayar mata da martani?"

Sarai ta gane me yake nufi sai dai ta basar da shi ta shiga yi masa wata hirar.

A tsawon watannin da suka shafe suna soyayya daidai da rana daya bata taba furta mishi wata kalma ta so ba ko makamancin hakan. Wasu lokutan har yana tambayan kansa anya kuwa tana sonshi? Saidai idan ya kalli idonta ya na hango kaunar da ta ke masa a cikinsu, wannan shine ya kan dan kwantar masa da hankali. Matsalar da aka samu shi ne shi din ya kasance mutum wanda yake son tana ririta shi kamar yadda yake ririta ta. A dai barta da nuna kulawa da damuwa da abun da ya dame shi, amma kalaman so kam a bakin Hauwarsa bai taba ji ba. Dan I love you din dayake ce mata ma sai dai tayi murmushi kawai, in kuma 'yan soyayyar nata suna kusa tace 'me too' ko 'me more'. Pet names dinnan na zamani duk ba wanda ta ke kiranshi, kwanan nan ne ma ta dena ce mishi Engineer da ya nuna mata cewa baya so ko kadan, shi ne ta makala masa Ya Faruk. Amma ya dauki alwashi in dai sukayi aure, to wannan tsananin kunyar da rashin iya kalaman soyayya duk se yayi maganinsu.

Sai wajen karfe shida Yusuf ya dawo daukansa.

In da sabo Fareeha ya kamata ace ta saba, amma kullum yazo tafiya idan zai bata kyauta sai taji kamar kar ta karba saboda wani nauyi da take ji. Shiyasa duk yawanci abubuwan daya ke bata suna nan ta ajiye a wardrobe din Umma sai dai ta kallesu kawai don bata san ya zatai da su ba. Kayan ciye-ciye ne dai ita da kannenta sun cinye, amma su turare da atamfofi da Abaya da sarka duk suna nan ta jibge su.

Sai da sukayi sallar Maghreb sannan suka wuce gida dukda Samhar na ta rokon su wai su kwana mata sukace sukam basu zo da shirin kwana ba.

"Kuma dai zakuyi auren nan kwanan nan zaku dandana wannan abinda nakeji kuma inshaAllah ba mai zuwa gidajenku" ta fada bayan ta musu rakiya zuwa bakin gate.

"Adda Samha karki mana baki mana." Yusrah tayi saurin fada.

"Kiyi hakuri. Kinga bamu ce wa Mama zamu kwana ba mun barta ita kadai a gida" cewar Fareeha

"Wani irin ita kadai. Ga ta ga mijinta kuce wani ita kadai?"

Sun lura dai kamar harda sha'anin ciki a lamarin masifar tata don haka lallabata suka shiga yi da alkawarin cewa Yusrah zata zo ta kwana mata tunda Fareeha zata koma Azare washegari. Da kyar dai suka samu ta sassauto aka rabu lafiya.

Suna komawa gida Fareeha ta hau hada kayanta don da sassafe Bappah yace zasu wuce akan yana da Daurin Aure.

●●●●●

Abubuwa fa sai kara zama serious suke yi ya jama'a. Kaina ya fara kullewa😂.

Drop your comments abeg. They mean alot.

Taku a kullum,
Miryamah

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top