18.

Your comments and unwavering support on the previous chapter  drove me into writing this one. You guys are the absolute besssttttt💗❤. Allah ya bar mun ku Ameeen.






"Kun shirya?"

Bata dago ta kalleshi ba ma tana sake cusa pencil case dinta a cikin school bag dinta tace "Eh".

"Ina Yusrahn?"

Ita tunda aka ce shi zai maida su makaranta taji gaba daya ranta ya baci.

Bayan sun gama yanke shawara ita da zuciyarta akan ya kamata a tattara Ya Ashraf da komatsansa a aika su waje, amma ta yaudare ta ta je ta boye shi a wani lungun zuciyar wanda bata san da shi ba. Sai bayan an gama biki da suka dawo gidan Bappah ta ganshi sai taji son shi ya dawo mata sabo fil. Abun da ya kara sata taji ta tsani kanta saboda wannan wani irin masifa ne?

A da ta yi tunanin watarana hankalinsa zai karkato zuwa gare ta shiyasa ta bata lokaci tana ta renon sonshi amma yanzu da ta fahimci bata ma gabansa ba sai ta hakura ba? Sam zuciyarta taki yarda da hakan. Sai ma wasiwasi da take saka mata.

To wa ya ce miki ita din sonta yake? Kin ma san wacece ita? Don ya saka ta a wallpaper ba lallai son ta yake ba. Watakil ma ta mutu kawai yana so yana tunawa da ita ne. Wa iyazubillah.

Daga karshe kawai ta yanke shawarar rage haduwarsu a gidan. Tana tashi da sassafe zata fito tayi abubuwan da zatayi sai ta koma daki, har sai taji karar fitar motarshi a gidan sannan zata fito parlor. Duk inda karfe biyar kuma tayi zata sake komawa daki ta buya don tasan ya kusa dawowa gida.

Wasu lokutan idan ta manta bata shiga da wuri ba to tana jin muryarsa zata sulale ta gudu daki.  Kuma sai taci sa'a in de ta shigo daki ta buya kuma babu me nemanta balle ma ta fito ta ganshi. Hakan ya fi mata, don ya rage mata radadin da take ji a zuciyarta. Wasu lokutan ma in ta kwana biyu bata ganshi ba har ta na mantawa da sha'aninsa. Sai anyi rashin sa'a wani ya ambace shi ko kuma taga giftawarsa sai abun ya dawo mata sabo. Wannan wace irin masifa ce?

Gashi yanzu ya fito ya tsaya a kanta yana ta mata wasu tambayoyi, yana kara karya mata zuciya.

"Tana fitowa" ta amsa mishi tare da saba jakarta ta shige kitchen. Ba komai za tai a kitchen din ba kawai ganin sa ne bata son yi don a yanzu kam ji take kaman ta amayar masa da abunda ke cikin ranta ko zai fahimci irin rudanin da ta ke ciki. A yadda take jin tan nan da zai ce yana son ta koda na minti biyu ne to komai zai daidaitu a rayuwarta.

Nan da nan kuma ta kara jin haushin kanta. Shin Fareeha ke mayya ce?

Wasu hawaye ne masu dumi taji suna gangarowa kan kuncinta. Tun da abunnan ya faru take so tayi kuka ta kasa amma sai yau? Nan ta kife kanta a kan worktop din kitchen din ta kara fashewa da wani kukan.

Amina ce ta shigo ta kofar baya da shanya a hannunta ta same ta a wannan yanayin. Ta yi saurin isa gareta tana dafa ta. "Adda Fareeha meya sameki?"

Kokarin hadiye kukan take amma ta kasa. Kai kawai ta girgiza mata.

"Ko komawa makarantar ne bakya so?"

Ta sake girgiza mata kai hade da dagowa daga kifuwan da ta yi. Ta sa gefen hijabin ta tana share hawayen ta. "Nima ban san meyasa nake kuka ba fa" ta fada tana yin tsaki. Kwana biyun nan kam ta koyi tsaki abun har mamaki yake bata. Kuma duk lefinshi ne.

Ta karasa bakin sink ta bude ta wanke fuskarta.

"To kiyi hakuri. Ai komai ya zo karshe inshaAllah"

Murmushi tayi wa Aminan. "InshaAllah"

Bappah da Anti Bebi sunyi tafiya zuwa Kaduna a ranar, su Fadila da Baba Habu kuma sun riga da sun koma makaranta don haka Amina kawai sukayi wa sallama suka tafi.

A mota Yusrah suna ta hira da Ya Ashraf tana sanar mishi irin farin cikin da take ciki don ta kusa kammala makaranta.

Har suka isa bata ce uffan ba. Shi ya cika duk wasu takaddu da za'a cika sannan ya musu sallama. Ya bawa kowa dubu uku pocket money. Fareeha kaman bazata karba ba amma haka ta sa hannu ta karba tace tagode. Ta ja akwatinta tayi hanyar hostel dinsu.

Har dare ranta baki kirin. Sai da suka hadu da Sajida Modibbo ne take tambayar ta me ya sameta don sam bata san Fareeha da yin fushi ba. Kawai sai ta tsinci kanta da bata labarin komai tun daga farko.

Sajida tayi dariya da ta gama jin labarin.

"Dariya ma kike mun wato. Allah bakiji yadda nake ji ba" ta fada tana dan turo baki.

"Allah sarki Hauwi ta" Sajida ta rungumota tana sake wata dariyar. "Kawai de kin ban mamaki ne wallahi. I never knew you were a hopeless romantic"

Ta kwantar da kanta akan kafadar Sajidar. "Wannan ya ma fi karfin hopeless. Useless de. I'm a useless romantic"

Wata dariyar Sajida ta sake yi. "Ni dai abun da zan ce miki shi ne kiyi kokari ki cire shi a ranki. I know it's not going to be easy but ki kokarta. In ba haka ba wallahi ke zaki sha wahala tun da be ma san kina yi ba."

Fareeha de kawai turo baki tayi tana jin ta.

"Dan Allah kiyi kokari kinji?. Ki hada hadda Addu'a kuma. Nima zan taya ki"

"Uhum"

"Dagaske fa nake."

"Naji"

"Oh ni Sajida. Wai to meye ne ma kike so a tattare da shi?. Be miki tsoho ba ma? Shekara kusan nawa ya baki? Bakya so ki auri dan saurayi dai dai ke ne?"

Wata harara ta banka mata. "Ya Ashraf dinne tsoho?"

"Duk surutun nan danayi abinda kikaji kenan kawai ko?"


Da taimakon ubangiji da kuma goyon bayan Sajida ta samu karfin gwiwar fuskantar NECO exams dinta. Sati uku suka shafe sunayi kuma Alhamdulillah duk jarabawowin sun zo mata da sauki. Amma kam kana ganinta zaka san tana cikin damuwa don duk ta rame ta kode. Kawai daurewa take.

Ana jibi zasu kammala exams dinsu ta fara tattare kayan ta. Da ta zo kan litattafanta da take rubuce rubucen poems akanshi sai taji hawaye ya taru a kurmin idonta. Yanzu shikenan ba ze karanta duk wannan surutun data yi ba?

Hadiye kukan nata tayi ta dauko biro ta bude sabon shafi.

A karo na farko ta rubuta cikakken sunansa a littafin.

Dear Muhammad Ashraf Hussain,

Har ta kai aya bata bari hawayen sun zuba ba. Ta gama ta rufe littafin sannan ta dauko na baya da ta riga da ta cika su da poems da wasikun da duk shi ta rubutawa, ta hade su waje guda tana kallonsu. To yanzu konawa zatayi ko me? Amma duk wannan wahalar da ta sha zai tashi ba a komai ba fa kenan?

Daure su tayi a leda ta jefa cikin akwatinta sannan ta cigaba da tattara kayan ta. Idan ta koma gida ta nutsu zata san abin yi.

Ranar da suka rubuta final exams dinsu haka suka zauna a masallaci ita da Sajida suna ta kukan rabuwa. Sun zaci abun ba zai musu ciwo sosai ba tunda duk suna da lambar juna sunyi alkawari zasu na waya da chatting a koda yaushe zasu cigaba da zumuncinsu, amma sai yanzu ne da abun yazo su ka gane wautarsu.

Fareeha zata koma Azare, idan ta samu admission ne ma a BUK to zaman ta ze dawo Kano amma Sajida kam ta mata nisa. Dama ita gidansu a Yola ne, gashi kuma mahaifinta yace zai tura ta Canada karatu ita da dan uwanta Sajid wanda shima a yanzu zai gama makarantar Hassan Gwarzo. A ina zata sake ganinta?

Sai da aka zo daukan Sajidar ne ma suka samu suka sassauta kukan nasu amma kowacce idon ta ya kumbura suntum. Har bakin gate ta rakata. Suka rungume juna wasu hawayen na zubo musu. Maman Sajida tana murmushi tace "Rabuwa fa baya nufin mutuwa. In kunyi hakuri kun rike zumuncin ku sai ku ga Allah ya sake hadaku watarana"

A haka suka rabu kowacce tana zullumin kewar 'yar uwarta.

Bappah ne ya zo daukansu wannan karon kuma hakan ya mata dadi. Sai da ya tsaya ya musu siyayyar kaza da yogurt kamar yadda ya saba sannan suka wuce gida. Nan ma suka samu Anti Bebi ta shirya musu abinci kala-kala duk dan ta tayasu murnar kammala jarabawarsu ta karshe a wannan bigiren.

Da dare suna zaune a palo suna kallo sai Yusrah ke tambayar Anti Bebi "Mama nikam ina Yaya ne? Ban ganshi ba tunda muka dawo"

"Ya tafi Abuja documentation. Ya samu aiki satin daya wuce"

Yusrah ta fiddo ido cikin murna "Kai haba? Alhamdulillah. A ina?"

"NDIC" Anti Bebi ta amsa mata ita ma da murmushi a fuskarta. Ba wanda ya kaita jin dadin aikin da Ashraf din ya samu dukda sana'arsu ta printing tana rufa masa asiri amma wannan aikin zai kara tsayar da shi akan kafafunsa. Sannan kuma yanzu ta samu damar yi masa zancen aure.

"Kai ya kamata na kirasa na masa murna gaskiya"

Duk wannan abun da akeyi Fareeha na gefe tana jinsu. Ita dai fatan ta kawai ta samu ta gudu gidansu kafin ya dawo garin.

Haka suka shafe satin gaba daya ba abunda suke sai rama bacci da kallo.

Ranar da dare Bappah ya shigo yace Fareeha ta shirya washegari zasu wuce Azare. Yusrah tayi caraf tace ita ma zata je. Nan da nan suka shiga hada kaya. Anti Bebi ta shigo dakin tace "Yanzu haka zaku watse ku barni ni kadai a gidan nan?"

Yusrah tayi murmushi. "Ayyah Mama am, sati daya fa kawai zanyi in dawo"

Ta jinjina kai "To Allah ya kaimu"

Washegari basu bar Kanon ba ma sai wajen karfe biyu don Bappah ya je wani daurin aure. Anti Bebi ta cika su da tsarabar da zasu kaiwa mutan Azare. Ran su fari kal haka suka kama hanya.

Wajajen la'asar suka isa. Kai tsaye gidansu Fareeha suka nufa. Umma ta tarbesu cikin murna da jin dadi. Su Qulsoom sun ji dadin ganin Yusrah don lokacin da suka je biki sun saba da ita sosai.

Hutu yayi dadi don in banda aikin ziyara ba abunda suke. Yau suje gidan nan gobe suje can. Ga shi aka cika ta da kayan kwalama. Duk abunda tace tana kwadayi nan da nan Fareeha ta shiga kitchen ta yi mata shi. Idan na siyowa ne zata saka hijabi ta fita ta siyo mata. Ta zazzaga gari da ita har gidansu Hafsatu suka je. Da weekend kuwa suka hau mota ita da Yusrah da Anti Mami suka je Shira wajen Daada. Sosai Daada taji dadin zuwan Yusrahn don har da kukanta.

Hotuna kam an sha su ba'a magana. Don duk gidan da sukaje sai anyi hotuna da 'yan gidan. A cewar Yusrah zata ajiye don tarihi. Su kuwa suka cika ta da dinbin alheri. Kowa sai ya nemi abunda da ze bata ko wani abu da za ta kai wa Mamanta. Ta ji dadin hakan sosai.

Da sati ya zagayo sai taji kamar kar hutun ya kare. Anti Mami ta sa ta a gaba ta tsefe mata kai ta wanke mata shi sannan ta yayyafa mata kitso mai kyau. Dukda ba wani gashin kirki bane da ita amma sai kitson ya kara fito da kyaun gashin nata. Fareeha ce ta rakata wani gida a bayan layin su aka mata kunshi hannu da kafa. Ta fito walwal da ita kamar wata amarya.

"Yanzu Adda sai yaushe zaki zo Kano?"

Fareeha da ke tayata hada kayan ta tayi dariya. "Wato kema kin koyi ce min Adda ko? Ni ba Addarki bace"

" 'Yan gidanku sun koya min ya na iya?"

Ta girgiza kanta kawai. "Yanzu kam sai result ya fito watakila. Ko kuma dai in wani abun ya taso"
Da so a samu ne ma har illa masha Allah. Don yanzu Kano ta gundureta, bata son zuwa ko kadan. Sai dai in wancan mutumin ya bar garin gaba daya to watakil ta iya zuwa. Amma yanzu kam ita da Kano sunyi bye bye. Sai yanzu ma take kara jin haushin kanta da ta cike BUK. Da ta sani ATBU ta saka, ga ta ga gida.

"To Allah ya kaimu. Ai baze dade ba ze fito"

"Allah dai yasa muga alkhairi"

"Amin Amin"

Suka cigaba da hada kayan. Can kuma Yusrah tace "Naso dake zamuyi wannan azumin wallahi. Zamuyi missing dinki"

Fareeha ta harareta  "Ki ce dai zakiyi missing tayaki aikin danake"

Yusrah ta fashe da dariya tana rufe fuskarta da mayafin dake hannunta. "Kamar kin sani wallahi. Yanzu fa kinga Adda Samha bata nan kuma Ya Fadila ma ba lallai suyi hutu da wuri ba. Duk ni za'a bar wa aikin"

"To ai tunda ba mutane dayawa aikin ma bazeyi yawa ba. Abincin shan ruwan dan kadan ne. Daga ke sai Mama da Baba da Amina fa."

"Sai Yaayaa"

Ta jinjina kai tana hadiye wani abu mai daci dalilin ambaton sa da Yusrah tayi"To kinga. Still baku da yawa ai"

"To dan Allah kizo mana sallah mana"

Fareeha tayi dariya. "Chabdi. Tunda nake ban taba sallah a ko ina ba sai Azare, bana jin zan iya yi a wani garin. Se de ke kizo mana"

Yusrah ta zumbura baki "Ba lallai Baba ya barni ba"

"To nima ba lallai Abba ya barni ba"

●●●●

Sati daya da tafiyar Yusrah aka tashi da azumi. A dai dai wannan lokacin ne kuma Abba yayi wa Fareeha zancen Engineer Faruk. Bata yi mamakin hakan ba don lokacin da su Anti Mami suka je biki ta dan bata labarin abin amma sai ta watsar da zancen don a lokacin tana ta hidimar son wanda bai ma san tana yi ba.

"Ina so kije kiyi tunani akai tukunna kafin ki bani amsa. Ba zan ce mishi komai ba sai da amincewarki. In kinyi na'am to sai ace mishi ya zo ya ganki. In kuma akasin hakan ne sai a bashi hakuri. Bazanyi miki dole ba"

Kanta a kasa tace "To Abba. Nagode"

Nan to koma ta fara tambayar Anti Mami duk wani bayani akan sa.

"Gaskiya ba wani sanin sa nayi sosai ba. Amma ba laifi yana da kirki kuma yana da kyauta sosai. Baban Ahmadi ya ce min lokacin da suke makaranta ma abun shi na kowa ne, kuma in dai zai sayi wani abinci ko wani abu dai haka, baya saya wa kansa shi kadai sai ya saya wa sauran 'yan dakinsu."

Fareeha ta jinjina kai tana jinta.

"Na san dai da yana aiki ne a wani kamfani masu tsara gine-gine amma daga baya ya bari bansan ina ya koma ba. Kuma ya taba aure amma sun rabu da matar"

Fareeha tayi jimm. "Meya raba su?"

"Dama bata sonshi akai auren. Auren hadin gida ne"

"Allah sarki"

"Sai kuma me kikeson sani?"

Ta dan daga idon ta sama tana tunani. "Yana da yara?"

"Bayi da su"

"Su nawa ne a gidansu?"

Anti Mami tayi dariya. "A'a gaskiya ban sani ba. Nasan dai shi ne dan fari a wajen mamansa. Kuma gaskiya yana sonta sosai kuma yana mata biyayya daidai gwargwado. Kinga lokacin da yake aiki a Abuja duk sati haka zai wanke kafa ya tafi Kano wajenta."

Fareeha tayi murmushi. Hakan ya burgeta. "Allah sarki"

"Yayi miki ko kuwa?" Anti Mami ta tambaya tana daga mata gira.

Ta yi dariya tana kifa kanta akan pillow. Ita ma bata san koya mata ba ko be mata ba, kawai dai tasan  hanya ta farko da zata bi wajen manta Ya Ashraf shi ne ta fara sauraron wasu. Wala Allah a dace wani ya shige zuciyarta ta manta dashi kwata-kwata. Don duk rashin hankalinta tasan bazata iya auren wanda baya sonta ba ko kuma wanda bata so.

Bayan kwana biyu Abba ya kira don yaji amsarta sai ta rasa me zata ce masa.

"Kin dai amince kenan" ya fada da ya ga ta gagara magana. Tayi murmushi kawai bata ce komai ba.

"To shikenan. Allah ya tabbatar muku da alheri"

Can kasan makoshin ta ta amsa da 'Amin'

Ranar Jumu'ah sun dawo daga sallar Taraweeh kawai ta tsinci missed calls guda biyu a wayarta daga bakuwar lamba. Dama a gida take barin ta idan zasu tafi. Sai da ta shiga kitchen ta tattare sauran abincin da ya rage ta dawo falon Umma ta saka a dan karamin fridge dinta sannan ta shiga daki ta kira.

Da sallama a bakinsa ya amsa wayar. Ta jiyo wani farin ciki a tattare da muryarsa a lokacin da ya ambaci sunanta.

"Ina wuni?" Ta gaishe shi a ladabce.

"Lafiya kalau Fareeha. An sha ruwa lafiya?"

Babu bata lokaci Engineer Faruk Murtala ya gabatar da kansa tare da mata bayanin kudirinsa a kanta dukda dai tasan dalilin kiran nata da yayi.

Hira sukayi mai tsawo wanda ita kanta batayi zaton zasu dauki lokaci haka suna hirar ba.

Da ta fito falo suka hada ido da Anti Mami ta daga mata gira sai ta samu kanta da jin kunya.

"Kai Anti Maaaami" ta fada da sigar shagwaba tana rufe fuskarta. Anti Mami kuwa me zata yi in ba dariya ba.

"Yanzu ni me nace?"

"Nidai kawai ki dena min irin kallon nan" ta fada tana shigewa cikin kujera.

"To Adda ayi hakuri na dena. Next time de a ce wa injiniya ina gaishe shi"

"Anti Mami Allah nima zan rama"

"Me zaki rama?"

Fareeha ta yi shiru kawai ta girgiza mata kai. Tun dawowarta ta lura da wayoyin da Anti Mamin take da wani 'Uncle Captain' kamar yadda taji Ahmadi yana fada, ta so ta tambayeta a lokacin sai kuma ta bar zancen don Yusrah tana nan. Yanzu kuma bayan tafiyar Yusrahn sai ta watsar da zancen amma kuma tunda Anti Mami ta sata a gaba yanzu da tsokana to ita ma ta dauki alkawari sai ta rama.

Engineer kam ba ji ba gani Fareeha sai kara shige mishi zuciya take. Yarinyar akwai kunya ga nutsuwa. Sannan ya ga alamar kamar ba ta da hayaniya irin ta teenagers. Duk lokacin da sukayi waya kuwa sai ya samu kanshi cikin nishadi. Itama Fareehan haka ne daga wajenta don Engineer ba dai iya hira da zolaya ba. Kullum tana makale da waya suna hira. Idan bai samu daman kira ba kuwa to zata ga sakon shi. Yana nuna mata kulawa daidai gwargwado. Ya so yazo su hadu to amma yanayin aikin shi bazai bari yayi tafiya mai nisa ba amma ya mata alkawarin zai kawo mata ziyara lokacin sallah.

Ba za tace ta fara sonshi ba tukun, sai dai shi din ya fara shiga ranta saboda yanda yake damuwa da abubuwa dayawa game da ita da kuma kalar soyayyar da yake nuna mata wanda bata san ma akwai irin ta ba sai yanzun. Kullum tana cikin addu'a Allah ya cire mata son Ya Ashraf ta samu daman bawa Engineer gaba daya zuciyar ta tun da dai da alama shi ya rigada ya bata tashi.

An shiga goman karshe Ya Bilal ya zo gida hutun sallah. Fareeha sai taga gaba daya ya kara canza mata, ya zama wani shiru-shiru. Dama tun can da ba wai hira suke da shi sosai ba, to yanzun ma de idan suna aikin shan ruwa in yazo ya kafa kujera a tsakar gidan sai dai yayi ta binsu da ido idan suna hira. Ko an tsoma shi a ciki baya wani cewa komai.

Fita kam ya gagareshi, kullum yana gida. Don in ya fita to tabbas sai ya hadu da daya daga cikin abokan sa da sukayi shaye-shaye a da, kuma yanzu duk haushin sa sukeji tunda suka ga yaje rehab har ma ya koma makaranta. Hakan ya musu ciwo matuka.

Yana so ya je wajensu don ya jawosu zuwa ga hanyar tsira, amma yasan halinsu sarai babu wanda zai yadda da shi. Watakil ma su mishi duka idan yaje. Shiyasa ya zabi zaman gidan kawai. Allah Allah yake sallah tazo ya koma Hadejia. Nan ne kawai ya ke samun nutsuwa.

"Mami yakamata ku tashi fa in dai kuna so ku samu Idi" cewar Umma tana bubbuga kafar Anti Mami wanda ta sha lalle. Lallen da aka cire karfe ukun dare sannan aka sake shafa mata wani a hannu.

Ita mai shafawar wato Fareeha tayi wata doguwar mika daga inda ta ke kwance akan sallaya. Da kyar tayi sallar asuba don idon ta wani yaji-yaji yakeyi tsabar baccin da ya cika mata su. "Umma karfe nawa?"

"Bakwai fa har ta kusa. Yaushe aka gama abinci har kuka shirya kuka tafi?" Umma ta amsa mata tana fita a dakin.

"Nikam na fasa zuwa Idin ma" Fareeha ta fada tana sake kanannedewa cikin hijabinta.

Anti Mami ta tashi ta zauna tana mutsitsika ido. "Ai baki isa ba. Tashi zakiyi yanzu ma kuwa"

Da kyar a daddafe ta tashi ta gyara dakin ta share. Ta shiga dakin Umma ma ta share dukda su Inayaah sun kalkale shi don yanzu su ne masu kwana a dakin. Falo ta share sannan ta saka turaren wuta ta fito ta samesu a tsakar gidan.

Inayaah da Ahmadi ta samu sun saka plate din Masa a gaba suna ta ci, Qulsoom kuma an sakata sharar falon Abba. Umma na yanka cabbage, Anti Mami kuma na jajjagen kayan miyan da zatayi pepper chicken da shi. Dama tun jiya da daddare ta sulala kazar ta soya ta ajiye.

"Yanzu ni aka bar wa shinkafar kenan?" ta marairaice tana kallon Umma da Anti Mami.

Umma bata ko dago ta kalleta ba tace "Nan ba da dadewa ba daga Shinkafar har salad din babu me tayaki ke kadai duk zakiyi. Gwara ki koya tun yanzu"

Wata kunya ce taji ta lullubeta don sarai tasan me Umma take nufi. Sum sum ta shige kitchen ta fara aiki.

Zuwa takwas da rabi komai ya kammala.

Abba ya fito yace duk me zuwa Idi ya fito don sun makara. A gaggauce tayi wanka ta fito ko kayan sallar bata samu ta saka ba. Kawai wata boubou ta zumbula ta dauko hijabi ta bi su.

Bayan an sauko Idi suka zauna su duka a falon Abba aka zubo abinci a tray kowa ya sa cokalinsa ana ci ana hira, in ka gansu gwanin sha'awa.

Shiryawa tayi cikin atamfar da Abba ya musu duk su ukun. Dinkin riga da skirt aka mata wanda ya kara fito da kyau da cikar hallitarta. Ga shi atamfar ta karawa fatarta haske don dark brown ce. Dankunne da sarkar da aka siya musu da bikin Samha ta dauko ta saka. Ta dan shafa powder ta zizara kwalli a idonta. Lipgloss ta saka a labbanta kafin ta kawo dankwalinta ta daura. Wani vedio ta gani kwanaki a YouTube na daurin dankwali ta gwada kuwa sai gashi daurin ya mata kyau sosai.

Tana kunna data ta fara samun sakonnin barka da sallah daga shafukan sada zumuntarta. Kan sunan Yusrah ta shiga ta ga har ta turo mata hotunansu na sallah. Gaba daya gidan kowa ya hallara har Adda Samha ma tazo. Duk sunyi kyau Masha Allah.

'We miss you' Yusrah ta rubuta a kasan wani hoto da aka musu ita da Fadila da Samhan.

'I miss you too' ta tura mata sannan ta daga wayar ta dauki hoton kanta ta tura mata.

Yusrah tana ganin hoton ta danna mata kira. "Adda kinyi azumin nan kuwa? Kinga yadda kikayj kiba?"

"Ni ba nace ki dena ce min Adda ba?"

"Mchew. Ya riga ya bi bakina fa. Kinga yadda kika kara kyau?"

Fareeha tayi dariya "Bana son zolaya. Yaya kuke? Ya Mama da Ya Fadila da su Amina?"

Hira suka sha. Yusrah tana ta bata labarin yadda sallar ta kasance musu da kuma wuraren da zasuje a ranar. Har suka gama bata ambaci Ya Ashraf ba. Fareeha taji dadin hakan matuka.

Bayan sunyi sallama ta nemi Sajidarta. Bugu daya ta dauka.

"Hauweeeeee!" ta kira muryarta cike da farin ciki.

"Na'am Jeeeeee. Eid Mubarak"

"Eid Mubarak Habibty. Ina kwalliyar sallarki?"

Fareeha tayi murmushi. "Kema ina naki?"

"Na turo miki fa. Ki duba"

Bayan Yusrah babu wanda yake cika mata waya da sakonni da hotuna kaca kaca kamar Sajida. Wasu lokutan sai ta hau taga sako kusan ashirin daga wajen ta. Kuma ba wani muhimman abubuwa bane. Daga hotunan ta, sai hoton abinda taci, ko wani abu da ta dafa, ko taji ciwo, duk dai shirme. Shiyasa wasu lokutan ma ta gwammace suyi waya akan chatting.

"To zan turo miki. Ya Mama da Sajid?"

"Suna nan lafiya. Jibi zamuje mu rubuta IELTS. Ki tayani da Addu'a please"

"InshaAllah Jee. Allah ya baku sa'a"

"Amin Amin"

Suna gama waya da Sajida tayi tunanin kiran Engineer sai kuma ta fasa. Jiya yace mata yana hanyar Kano kuma da aka sha ruwa ta tura masa sakon ban gajiya amma bata samu amsa daga gareshi ba. Watakila ko har yanzu gajiyar bata sake shi ba.

Da akayi azahar suka tattara suka tafi gidan Yayar Umma, Mama Uwani. Nan sukaje suka samu an baje kolin hira don har jikokin Mama Uwanin sunzo. Basu dawo gida ba sai da sukayi la'asar.



"Adda" muryar Qulsoom ta jiyo kamar a mafarki. Sake gyara kwanciyar ta tayi akan doguwar kujerar. Tun da tayi Azahar take bacci don yau din ma sassafe ta tashi ta hau aiki don washegarin sallah ne suka fi yin baaki. Tana gamawa kuma sai ta tafi gidan su Hafsatu. To yanzu data dawo tana sallah sai kawai taji wata gajiya ta lullubeta.

"Adda manaaa" Qulsoom ta kara kira tana dan jijjigata.

"Menene?" Ta tambaya cikin rashin jin dadin katse mata baccin datayi.

"Anti Mami tace na taso ki. Kinyi bako"

Tashi zaune tayi cikin hanzari. "Bako kuma? A ina?"

"Kizo ki gani. Yana falon Abba" kawai Qulsoom tace tana ficewa daga falon Umman.

Cikin rashin fahimtar abun da ke faruwa ta sauko akan kujerar tana gyara zaman hijabinta.

"Ina zakije?" Anti Mami ta tareta a tsakar gidan da ta ga ta dauki hanyar falon Abban.

"Ba Qulsoom bane ta taso ni wai nazo nayi bako?"

"To shi ne zakije wajenshi haka buzu buzu bacci duk idonki?. Ga wani hijabinki yasha squeezing. Wuce muje daki" ta figi hannunta "Qulsoom ki dauki tray dinnan ki kai wa Engineer"

Qulsoom dake bakin famfo tana wanke-wanken kwanukan da aka ci abincin rana ta amsa da 'toh' sannan ta tashi.

Tura ta tayi bandaki tace ta wanko fuskarta sannan ta shiga duba mata kayan da zata saka. Wani leshi ta ciro wanda Bappah ya dinka mata tun sallar bara, sau daya ta saka bata sake sakawa ba kuma. Dinkin doguwar riga ce me dogon hannu. Ta dudduba bata ga mayafin daya dace da kayan ba don haka ta dauko a nata kayan.

"Ga wannan ki saka. Kuma ki gyara fuskarki dan Allah. Ki dan saka kwalli. Ina jiranki a palor"

Haka ta saka kayan tana ta zumbura baki don ita sam bata san da zuwan sa ba. Kuma ma bayan ya gama share ta ko amsa sakon ta beyi ba shine zai yi mata wani zuwan bazata.

Kasa daura dankwalin kayan tayi kawai taja tsaki ta yafa mayafin a kanta.

Da sauri tazo ta wuce Anti Mami a falon kar ma ta kirata tace wani abun beyi ba.

Sallama tayi ta shiga falon ya amsa mata cikin natsuwa. Sai da tayi ajiyar zuciya saboda wani daddadan kamshi da ya cika falon wanda babu tantama ta san shine yake yin wannan kamshin.

Kanta a kasa ta samu hannun kujera ta dan dofanu akai.

"Sannu da zuwa. Ina wuni?"

Engineer yayi dan siririn murmushi. "Laifin me nayi da ba za'a dago a kalleni ba? Wannan kwalliyar fa duk ke akayi wa ita"

Ta so tayi murmushi amma sai ta dake.

"Haba Hauwa kulu ta. Bansan ki da fushi ba. Ki fada min me nayi dan Allah kike fushi dani? Ko duk kunyar ce?"

Kamar ba za tayi magana ba kuma sai ta ce "Ba kai bane ka share ni". Ita kanta tayi mamakin yadda maganar tata ta fito da sigar shagwaba.

Shikuwa Engineer ya kara tsumbulawa. Nan da nan ya shiga aikin rarrashi. Ba yadda ta iya haka ta sake fuska suka yi hira. A ranar yakeso ya juya Kano don washegari zai koma wajen aikin sa.

"Na so ace hutun nawa mai tsawo ne don gaskiya ban gaji da kallonki ba"

Ta sa hannu ta rufe fuskarta tana dariya ciki-ciki. Wannan kunyar tata tana kara kumbura masa zuciya.

Ledojin daya rinka fitowa da su a boot din motar sa lokacin da tayi masa rakiya sai da suka bata mamaki har take tunanin ko dai hadda sakon wasu ne. To waya sani a garin kuma in banda su?

"Ga wannan babu yawa goron sallanki ne ke da su Inayaah"

Tsayawa tayi tana kallonsa sakeke. Duk wannan din? Ina zata kaisu? Shago zasu bude? Ashe da Anti Mami tace yana da kyauta bata mata bayani me kyau ba. Yakamata ace ta ce mata yanada mahaukaciyar kyauta don abun kam ya wuce tunanin mutum.

Kafin ta fara mishi bayanin cewa kayan sunyi yawa ma yayi sauri ya shige motarsa ya wuce. Haka ta dauko kayan niki-niki ta shigo da su cikin gidan.  Anan tsakar gidan ta zube su ta zauna ta zabga uban tagumi. Anti Mami ta fito ta ganta tayi murmushi. "Kadan ma kika gani in dai Engineer ne"

A daidai lokacin kuma Umma ta shigo gidan. Daren jiya anyi rasuwa a makota shi ne ta je ta'aziyyah daga nan ta tsaya gidan Maman Walid.

Anti Mami na ganinta tace "Umma an kusa fa a dauke miki Addarki"

**********

Toh fa! Ga Engineer ya na neman replacing crush dinmu, ga kuma hankalin Uncle Captain yayi wani wajen.

Who wants to know what's happening in New York though? Ni dai ina so naji wainar da ake toyawa tsakanin Anti Mami da Muazzamu, amma fa babu idea😂😂. Kuyi Addu'a Allah ya kawo basira.

Thank you guys for sticking to the story. Allahumma Barik ❤.

Taku a kullum,
Miryamah.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top