17.
Wayewar garin ranar Alhamis ya tsinci sakon Misriyyah a wayarsa. Tun kwanciyar Ammah a asibiti daya fada mata cewa yanzu bashi da lokacin da zasu zauna suyi magana saboda wasu dalilai, bai sake ji daga gareta ba. Hasali ma blocking layinta yayi din gaba daya hankalinshi yayi kan Ammah. Yanzun ma da bakuwar lamba aka turo masa sakon kuma bisa dukkan alamu ita ce.
I can't wait any longer for you to clear your head and sort your thoughts. Na so ace mun zauna munyi magana ta fahimta da kai amma baka bani wannan damar ba. Ina maka fatan alheri da samun nutsuwa a rayuwa don nikam na rasa tawa. I'll be leaving the country for a while and I'll not like to get in touch. Thank you.
Ya dan yi jimm yana sake karanta sakon. Ji yayi jikinsa ya masa nauyi. Yayi kokarin kiran lambar sai ya sameta a kashe. Ya gwada daya layin ta wanda yayi blocking din shima a kashe. To idan ya kiratan ma me ze ce mata? Bashi da wasu kalamai masu taushi da zai yi amfani da su. Bai san ma takameme me ze mata ba. Hakuri zai bata? Lallashinta zai yi? Oho.
Kwanaki biyu suka rage mishi kafin ya koma bakin aikinsa don haka yana so ya koma cikin karfin gwiwa. Baya bukatar wani damuwa ko tunani suzo su shige mishi jiki har ma yayi sanadiyyar sake faduwarsa gwaji.
Ajiyar zuciya yayi tare da goge message din a wayarsa sannan ya tashi ya shiga kitchen dinsa don hada abun shan ruwa. Yau da azumin nafila ya tashi kuma Alhamdulillah bai wujijiga shi ba.
Sandwich ya yi wanda yasha kayan lambu da kwai da tuna. Akwai sauran yam balls din da Ammah ta aiko masa ranar litinin da sukayi waya yace mata yana azumi, zai hada da shi ya sha ruwa. Yau ma yayi tunanin ko za ta mishi wani aiken amma shiru.
Yana tsaye anan kitchen din wayarsa ta dauku ruri da kiran sallan Maghreb daga Adhan App dinshi. Dabino ya tauna yayi addua sannan ya kora da orange drink.
●●●●●
A Kano kuwa Fareeha suna ta shirin zuwa gida don sun samu hutun intervals. Sun kammala zana jarabawarsu ta WAEC kuma Alhamdulillah suna fatan samun nasara mai dinbin yawa.
Hutun ya kama ranar Jumu'ah.
Suna tashi da safe kowa tayi duty din ta suka tattara kayayyakinsu zuwa bakin hostel ta yanda zai musu dadin dauka idan an zo daukansu. Bayan sun karya (dukda ba kowa bane yake karyawa ranar hutu) principal ta tarasu a dining hall din ta musu nasiha akan idan sun tafi hutu kar su shagala da wasu abubuwan, su tuna cewa wata jarabawar tana jiransu kuma.
Ko bayan an watse Fareeha da kawarta Sajida suka cigaba da zama a dining din suna 'yar hirarsu. Sai zuwa akayi akace mata wai anzo daukansu. Ta duba agogon cikin dining hall din taga har goma da kwata. Karfe goma kuma ake bude gate. Sun tsaya hira bata ma san har lokacin bude gate din yayi ba.
Nan ta shiga neman Yusrah don suje su dauko kayayyakinsu.
A class dinsu ta sameta itama anata hayaniya da kawaye. Tare suka karasa wajen reception. Suna zuwa kuwa suka ga Anti Bebi ce da kanta tazo. Da gudu Yusrah ta ruga wajen Mamanta ta kankameta. Fareeha ma murmushi ta saka wanda ya nuna jin dadinta.
Suka harhado kayansu suka jawo zuwa gate din. Anti Bebi ta gama signing abunda zatayi signing ta fito suka tafi.
Tana zuwa jikin motan kawai taji jikinta yayi sanyi. Ko ba a fada mata ba tasan shi ne a cikin motan. Kafin tayi wani abu Anti Bebi tace "Ashraf a bude boot"
Ta cikin motar ya bude sannan ya fito ya zagayo don yazo ya tayasu saka kayan a cikin.
"Yaya ina kwana?" Ita da Yusrah suka fada a tare.
"Lafiya kalau. Yau kuna ta jin dadi zaku tafi gida ko?"
Yusrah ce ta bashi amsa inda ita kuma Fareeha idon ta suna kasa. Cuccusa kayan ta tayi a boot din tayi saurin shiga motar.
Ya Ashraf dinta ya kara kyau Ya Subhanallah. Dan dai kar tayi karya ma da ta ce har kiba ya kara. Ga sajenshi da taga ya kara baki ya kwanta luf a gefen fuskarsa. Ita kanta mamakin kanta tayi yadda duk ta karanci wadannan abubuwan a tattare dashi a kallon da ta mishi wanda ba kai sakwan ashirin ba.
She is in trouble.
A mota Yusrah ba abin da take sai aikin surutu don ita ce a gaba, Fareeha kuma da Anti Bebi a baya. Sai dai ita Fareehan tana owner's corner don haka a hankali take satan kallon Ashraf.
Komai nashi ya burgeta. Daga shigarshi da yayi na kananan kaya, zuwa ga sassanyan kamshin turarensa da ya ke ta dawainiya cikin motan, da yadda yake juya sitiyarin motar da hannu daya. Duk sai taji ta sake lulukawa.
Sun dauka gida zasu wuce kawai sai suka ga Ya Ashraf ya dauki wata hanyar.
"Mama ina zamuje?" Yusrah ta tambaya.
Anti Bebi ta saki murmushi. "Surprise ne"
Basu ankara ba kuwa sai ganinsu sukayi a Beruit road. Nan Yusrah ta gano lagon abun, ta shiga ihun murna.
"Baban ku ne yace a siya muku waya gift dinku kenan saboda kunyi kokari a JAMB dinku"
Su suka zabi wayoyin dukda Anti Bebi ta tsaya akan kar su zabi masu tsada sosai. Infinix duka suka dauka. Ta Fareeha Red ta Yusrah kuma Black.
Daga nan shagon MTN suka wuce sukayi rajistan layi.
Ran su fari kal lokacin da suka shigo gida kowa tana fara'a. Suka saka wayoyin a caji sannan sukayi wanka suka ci abinci sannan suka zauna daddana sabbin wayansu. Dayake kowa yana makaranta don haka gidan shiru sai su kadai. Fadila ma ta sami gurbi a FUD don haka ita da Baba Habu suna can. Suna sa ran nan da sati daya za ai midsemester break zasu dawo don a fara bikin Adda Samhan da su.
Lambar Umma ta fara saving a kan wayar don tuni ta haddace kafin ta danna mata kira.
Da sallama Umma ta amsa wayar.
"Umma ina wuni?" Fareeha ta gaishe ta cikin zumudin son fada mata abin farin cikin daya sameta.
"Adda" Umma ta amsa da fara'a. "Har kunyi hutun ne?" Bata jin mamakin ganin kiran Fareeha da bakuwar lamba ba don inda sabo ta saba. In dai Fareeha ta samu waya to bini bini zata kirata.
"Eh. Umma albishirinki!"
Umma ta sake yin wani murmushin. "Goro fari tas!"
"Bappah ya siya mana waya yau ni da Yusrah"
"Ah ah ah. Masha Allah. Lallai Bappah ya gwangwaje ku. Allah ya saka masa da alheri"
"Amin Amin Umma."
"Allah sa ku mora. InshaAllah zan kira na masa godiya. Ki gaida Anti Bebin ko?"
"Zataji inshaAllah. Umma ina Anti Mami?"
Tun bayan ta gama takaban ta, ta so ta cigaba da zama anan Jama'aren amma duk sai taji gidan ya musu fadi ita da Ahmadi don haka bata dade ba ta tattaro ta dawo Azare wajen Umman. Bappah kuma yana ganin haka sai ya bata shawarar ta koma makaranta kawai. Tayi na'am da hakan. Babu bata lokaci ya biya mata kudin registration ta samu gurbi a College of Education Azare. Yanzu haka sun fara kenan.
"Ta na makaranta amma in ta dawo ita ma zan mata albishir"
"To. A gaida su Inayah"
"Zasuji. A cewa Yusrah ina tayata murna"
Har la'asar sai faman kiran mutane suke suce wannan ne lambarsu ayi saving. Yusrah kam ta dauko wayar Mamanta ta rinka daukar lambobin 'yan uwa da abokan arziki.
Da Anti Bebi taga abun yaki karewa tace in basu nutsu ba zata kwace wayoyin. Nan kuwa suka shiga hankalinsu.
Da Bappah ya dawo gida haka sukaje sukayi ta masa godiya shi kuma ya sa musu albarka.
Bayan sallar Isha ne Anti Bebi ta kirasu dakinta don su gwada dinkunansu na bikin. Kala hudu-hudu aka musu. Atamfa da za su saka ranar kamu wanda aka musu dinkin Borno style da ita, sai leshin su na dinner riga da skirt da asoken da zasu daura, da kayan da zasu saka ranar yini doguwar riga itama atamfa ce. Dangin mijin Samhan sun shirya gagarumin zaman Ajo a family house don haka an musu wani dinkin leshin ma da zasu saka a lokacin. Kayan duk babu wanda beyi kyau ba. Dinkin ya zauna musu cas cas a jikinsu. Anti Bebi ta kallesu su biyun ai se ta fara hasaso wa kanta shirin wani biki nan ba da dadewa ba. Ta saki dan murmushi tana zaro musu mayafan da ta saya musu wanda zasu dace da kayan nasu. Har takalmi da jaka ta siya musu.
Murna kam a wajensu ba'a cewa komai ranar. Sukam bajau da su. Ga sabuwar waya ga sabbin kayan fitar biki.
Da suka zo kwanciya Yusrah take ce ma Fareeha "Ni fa ina ga yau na ma fi Adda Samha jin dadin bikin nan da za'ayi. Zan iya cewa bata kaini farin ciki ba ma"
Fareeha ta fashe da dariya. "Ke kin isa ki fita jin dadi? Ita da zata auri wanda takeso."
"Nima wataran zan auri wanda nakeson ai" Yusrah ta fada tana jujjuya idanu.
Nan da nan Fareeha ta matsa kusa da ita tana zaro ido tace "Saurayi ne dake Yush?"
Yusrah ta kalleta ta danyi dariya. "Ke kin cika firgicewa wallahi. I was just stating the obvious"
Ta kankance idanunta a kan Yusrahn "Kiji tsoron Allah ki dena boye min. In akwai ma ki fada min"
"Yanzu dan Allah yadda muke da ke se inyi saurayi amma bazaki sani ba?" Yusrah ta tambayeta tana saka hularta ta bacci mai laushi. "Ai ban kyauta miki ba ace na boye miki irin wannan gagarumin abun ko kuwa?"
Fareeha ta jinjina kai tana jingina a jikin gadon. "Hakane". Sai kuma taji wani iri. Kamar ita bata dauki Yusrahn yanda ta dauketa ba don tana boye mata yanayin data ke ji a game da yayanta. To amma ai ba soyayya suke ba don haka ba laifi bane idan bata sanar da ita ba. To amma watakil idan ta sanar da ita Yusrahn ta tayata jawo hankalinsa zuwa gareta.
Haka ta kwana ta kulla wancan ta warware wancan.
Ran lahadi ita da Bappah suka wuce Azare akan sai su Umma zasu taho biki su taho da ita.
Taji dadin ganin 'yan gidansu kowa cikin farin ciki da nishadi. Ummanta da Abbanta kowa cikin koshin lafiya.
Su Qulsoom kam murna ba'a magana Addarsu ta dawo. Basu san cewa sunyi kewarta har haka ba.
Da suka ganta da sabuwar waya kam ai sai suka manta da sha'aninta. Aka kwakume mata waya sai game ake tayi. A shiga wannan app din a fita. Anyi hotuna sun fi dari. Gashi da suka gano wayar tana da front camera, selfie salamu alaikum. Ita kanta mai wayar ko hoto daya bata dauka ba amma har sun kusa cika mata waya. Sai dare ta shigo hannunta.
Ita da Anti Mami suka kwana a daki suka sha hirarsu har tsakiyan dare don washegari Anti Mamin bata da class. Da safe ita ta musu abun karyawa sannan tayi wanke-wanke. Tana gamawa sai ga Anti Mami ta fito da wankin Ahmadi. Haka ta zauna ta tayata ita tana wankewa ita kuma tana dauraya. Kafin Umma ta leko har sun kammala sun share tsakar gidan tsaf.
Ranar laraba sai ga wani abokin marigayi Baban Ahmadi ya kawo wa Anti Mami ziyara. Daman tunda akayi rasuwar yazo ya musu ta'aziyyah bai sake zuwa ba kuma sai de waya.
Fareeha ce ta shigo dashi har falon Abba ta kawo masa ruwa kafin Anti Mami ta dawo daga makaranta. Da ta iso suka gaisa cikin mutunci kuma ya tayata murnar cigaba da karatunta datayi. An kawo masa abinci amma yace sauri yake. Leda katuwa ya ajiye musu cike da kaya yace na Ahmadi ne sannan ya ajiye envelop akan ledar yace Anti Mami ta kara kudin transport na zuwa makaranta.
Bayan tafiyarsa da Umma taga shirgin kayan tace "To Masha Allah. Mami ko an kusa dauke mana ke ne?"
Anti Mami ta tabe baki. "Wa? Umma ai ni da aure kuma sai na kammala karatu na samu abun da zan rike dan maraya na tukunna"
"Ah ah kar kice haka. Allah dai ya zaba miki abinda yafi alkhairi kawai"
"To Umma. Amin"
Abun mamaki bayan kwana biyu sai ga wayarsa. Wai shi kam yaga Fareeha Kuma hankalinsa ya kwanta da ita.
Da ta fada wa Umma sai da tayi salati ta sanar wa ubangiji. "Adda dai?"
Anti Mami tana gintse dariya ta gyada mata kai.
"To nikam bansan abun cewa ba kuma" ta fada tana maida duban ta kan jakar da ta ke shiryawa na tafiyarsu Kano. Sam sam bata tsammaci hakan ba. Hasali ma jikinta ne yayi sanyi. Yanzu er yarinyar ta ta har ta kai matsayin a fara neman aurenta? Lallai lokaci na gudu. Kuma girma yazo mata. Nan bada dadewa ba kuma sai ce ta fara tara jikoki ko? Allah mai iko.
Ta dauka a iya nan zancen ya tsaya, sai ga shi mutum kam ya addabi Anti Mami da kira akan sha'anin Fareeha. Ita kuwa Anti Mami ta sake komawa wajen Umma.
"To ni yanzu me kikeso nace ne uhm?"
"In kin bada go ahead Umma ai sai a jona su"
Umma ta dan yi shiru. "Ya danyi hakuri ta kammala makarantar mana to. Saura de kadan"
Yadda Umman ta fada haka Anti Mami ta koma ta fadawa Engineer Faruk. Yace to a bashi izni ya zo ya gabatar da kansa a matsayin wanda yakeso ya nemi aurenta kafin ta koma makaranta.
"Wannan maganar kuma tafi karfina. Sai ki bashi lambar Abba" cewar Umma kenan da Anti Mami ta sake dawowa mata. Ita ma ta gaji da wannan aiki da take na masinja don haka ta bashi wayar Abba akan suyi magana.
Anan aka bar zancen suka tattara suka tafi Kano don bikin Adda Samha.
Gida kam ya cika tam! 'Yan uwa da abokan arziki kowa yazo taya Bappah da Anti Bebi murnar aurar da babbar 'yarsu. Tsabar yawar jama'ar gidan su Yusrah hakura sukayi da dakinsu suka bar wa baki. Gidan wata kawar Anti Bebin suka koma da kwana daga su har amaryar da sauran kawayenta.
Ranar Kamu da sassafe masu lalle sukazo suka musu lalle har da ita amaryar. Su an musu baki ita kuwa amaryar har da ja. Sai wajen sha daya aka cire mata tayi wanka sannan ta tafi wajen kwalliya ita da kawayenta.
Dakin taron ya cika makil da 'yan uwa da abokan arziki kowa yazo domin Samha ne. Decoration kam gashi nan ansha ko ina walwali yake. Caterer ma tazo da kulolinta shake da abinci kala da iri jira take kawai a bata izni ta fara rabawa.
Kawayen amarya ne suka fara shigowa dakin taron sanye da ankonsu wanda ya yi musu kyau sosai. Kowa ya gansu sai Masha Allah kawai yake cewa don duk cikinsu babu wacce batayi kyau ba. Amarya ce ta biyo bayansu tare da kannenta. Suma sun yi kyau sosai. Mai hoto yana ta binsu yana daukansu. Har mazauninta suka kaita sannan suka gyara mata rufin mayafin da aka rufeta dashi.
An kama amarya lafiya taro yayi kyau sosai. An ci an sha kuma an gwangwanje. Ba a watse ba sai wajen bakwai, kowa ya kama gabansa. Wasa-wasa aka kwashe amarya da kawayenta amma su Fareeha basu samu mota ba. Su waiga nan su waiga can amma basuga wanda suka sani ba wanda zai mai da su gida. Ita dai Yusrah wayarta ta mutu don tsabar hotuna da vedios din data ringa dauka.
"Ki kira mana Baba Habu dan Allah kiji ina yake"
Nan Fareeha ta gwada wayarsa. Ya amsa yace shi kam yana hanyar Mariri Mama ta sa ya maida mata wasu bakinta.
"To wai ita Ya Fadila haka ake? Wasa tare ci banban. Shine ta tafi ta barmu wato"
Fareeha tayi 'yar dariya tace "Bata tafi ba. Gata can" ta dan nuna mata ita da kuncin ta. Yusrah na juyawa kuwa ta hango wata me irin ankon su tana tsaye ita da wani mutum. Ta dan kara kura musu kallo sai taga tabbas kuwa Fadilar ce. Suna ta shan dariyarsu ita da mutumin wanda ya jinginu a jikin motarsa.
Nan ta hau salati. "La ila ha illallahu"
Fareeha ta gintse dariyarta.
"Yanzu ita ko tsoro bata ji? Idan wani ya ganta fa yaje ya fada wa Baba?"
"Ke kam dai ki rike bakinki kiyi shiru"
Suna cikin gulmar Fadilan ne suka ga mota ta tsaya a gabansu.
"Ku kuma me kuke anan har yanzu baku tafi gida ba?"
Ai nan da nan Fareeha taji bugun zuciyarta ya karu.
"Ya Ashraf bamu samu mai maida mu gida bane"
"Kaman ya baku samu me maida ku ba?. Yanzu ko adaidaita sahu baza ku iya shiga ba ku koma shine kuka tsaya a nan kuna jiran wa kenan? Kuma kuna gani dare kara yi yake. Kunsan wurin nan de ba wani tsaro bane da shi ko."
Idon ta yana kanshi yana ta sirfa musu fada amma abun mamaki ita fadan ma sai taji ya mata dadi. Wani abu taji ya kara lullube zuciyarta.
"Oya maza ku shiga mu tafi." Ya fada yana komawa cikin motar da niyyar jan kofar. "Ina Fadila?"
Ai sai suka shiga wukil wukil da ido. Yusrah ta daga kai ta kallo wajen da Fadilan ke tsaye akayi rashin sa'a kuwa Ya Ashraf ya bi inda ta kalla, ba shiri ya fito a motar ya wani rufe murfin da karfi. Taku biyu yayi sai gashi a gabansu.
Daga inda suke tsaye suna hango kalar tashin hankalin dake bayyane a fuskar Fadilan a dalilin ganin Ya Ashraf tsaye a gabansu yana huci. Kallonta kawai yayi sum sum ta juyo ta taho wajensu Yusrah.
"Sannu Ya Fadila" yusrah ta fada tana mata kallon tuhuma. "Yau kam de kin jawo mana masifa"
Fadila ta harareta. "Ki min shiru"
Fareeha kam idonta na kan Ya Ashraf da mutumin da Fadila ke hira dashi. Sai taga a nuste yake masa magana har ma sukayi musabaha kafin nan ya juyo ya dawo wajensu.
"Me kuka tsaya kallo?" Ya watsa musu harara wanda hakan yasa Fareeha yin murmushi. Sai taga ya mata kyau da hararar. He looks so cute.
Bude kofa sukayi suka shiga motar.
Ya juyo ya kallesu duk su ukun sun wani jeru a bayan motar.
Murmushin gefen lebe yayi. "Amma yaran nan kun rena mun hankali. Ni direbanku ne da zu ku wani shige baya ku kame? In mutum daya bata dawo ba wallahi juye ku zanyi in koma gida."
Suka kalli juna kowa tana tunani. Fadila ta girgiza musu kai akan ita dai bazata shiga gaba ba don yanzu zai yi ta mata fada ne har su isa gida. Yusrah kuwa dama ita ce a tsakiya don haka ta tsuke fuska karma a ce mata ta koma. Tana son Ya Ashraf amma duk randa ya birkice kuwa ko hanya bata so su hada.
Jiki babu kwari Fareeha ta bude murfin motar ta fito. Sai da ta ja numfashi kafin ta samu kuzarin bude kofar gaban motan ta shiga ta zauna.
Sun fara tafiya yace mata "Saka seat belt". Nan taji wani dumi ya cika mata zuciya a karo na biyu. Ta jawo a hankali ta makala.
Tafiya suke shiru in banda radio da ke ta tashin waka a hankali wanda aka saka a gidan radio. Sun zo wajen wasu shaguna Ya Ashraf ya ja ya tsaya.
"Minti daya" ya fada musu kafin ya fice.
Gaba dayansu suka saki ajiyar zuciya a lokaci daya. Hakan kuma ya sakasu fashewa da dariya.
"That was suffocating" inji Yusrah tana fiffita da mayafin ta. "Nikam ko anan ma a sauke mu dan Allah mu karasa gidan Anti Jamila"
"Au na dauka gida zamu je fa" cewar Fareeha tana juyowa ta kallesu.
"Yanzu yaushe zamu je gida kuma mu sake fitowa mu tafi gidan Anti Jamila?"
"Amma dai kunsan Yaya kam gida zai maida mu. Bana tunanin zai wani je gidan Anti Jamy"
Suka yi shiru.
Yusrah ta dan matso gaba yadda zata kalli Fareeha da kyau ta ce mata "Please in ya shigo kice mishi ya kai mu gidan Anti Jamy"
Fareeha ta fiddo ido waje. "Ni kuma? Ke meyasa bazaki fada masa ba.?"
"In ya hayayyako min fa?"
"To nima in ya hayayyako min fa?"
Fadila ta fashe da dariya. "Kunga muyi respecting kanmu kawai. In ya kai mu gida, mu nemi mai mika mu can din. In Kuma muka yi sa'a ya kaimu gidan Antin shikenan, falillahil hamdh."
"Gaskiya" Fareeha ta jinjina kanta. "Mu gode Allah ma da muka samu ya dauko mu"
Tana fadin haka sai gashi ya shigo motar. Nan da nan kamshin turarensa ya cika mata hanci.
Bai ce musu uffan ba ya kunna motar suka cigaba da tafiya. A ankare suke suna so suga wace hanya zai bi.
Kamar daga sama taga ya ajiye mata wayar sa akan cinyarta. Ta juyo ta kallesa a razane.
"Saka mun" ya fada yana miko mata katin wayan da take tunanin dazun da ya tsaya shi ya siya. A hankali ta sa hannu ta karba.
Hannunta na rawa haka ta dauki wayar. Dan madannin tagani a tsakiya ta danna, wayar ta kawo haske. Hoton data gani a matsayin wallpaper din wayar ne ya sata faduwar gaba.
Wata kyakyawar mace ce tsaye sanye da hijabi maroon wanda ya kara fito da hasken fatarta. Hannayenta wanda suka sha lalle ta ke kokarin rufe fuskarta da su. Fararan hakoranta ne suke nuna cewa murmushi take. Bata san lokacin da ta sake danna madannin ba, hasken wayar ta dauke.
"Yaya dai?"ya tambaya yana kallonta ta gefen ido.
"Na kasa budewa" ta fada da wata murya da bata san ko tata bace. Har yanzu zuciyarta bugawa take.
Mika hannu yayi ya karbi wayar sannan ya danne madannin tsakiyar, fingerprint dinshi ya hau ta bude.
Mayar mata yayi. Kamar bazata karba ba amma haka ta sa hannu ta karba. Da sauri ta saka masa katin ta mika masa wayarsa.
Tana ji yana mata godiya amma ta gagara bashi amsa.
Bata san ma lokacin da suka isa gida ba, kawai ji tayi su Yusrah suna bude kofa. Tana daga ido taga yayi parking a kofar gidan Bappah. Ita ma fitowan tayi suka shige ciki. Wani bakin ciki takeji da bata san daga ina ya taho ba.
A falon Anti Bebi suka samu ana ta cin abinci ana ta hira. Sama-sama ta gaggaishe su ta wuce dakin da su Umma suka sauka wanda shine dakin Adda Samha a da.
Tana shiga ta tsaya a bakin kofar ganin Umma bata dakin. Sai Anti Mami data gani suna hira ita da wata mata a dakin. A hankali ta juyo ta koma falon ta zauna. Bata ma da karfin gwiwar zuwa neman Umman nata. To in ta neme ta me zata ce mata ?
Ita kuwa Anti Mami suna dawowa a wajen Kamu ta shiga daki domin yin sallah. Tana idarwa sai ga Anti Bebi ta shigo, da alamu ita ma a lokacin ta shigo gidan dan ko kunce daurin asoken da aka mata batayi ba. Tana murmushi tace "Mami kinyi babbar bakuwa". Tana fadin hakan sai ga Mama Ammah ta shigo dakin.
Anti Mami bata san lokacin da ta rungume ta ba, hawaye suka fara sintiri a fuskarta. Ammah kuwa ba abunda take se dariya don tasan ta mata surprise. Duk wayoyin da sukayi a satin da ya wuce bata nuna mata cewa ma tana da niyyar zuwa bikin ba. Ita kuma Anti Mami bata tambaya ba don a tunaninta bazata zo ba saboda rashin lafiyar da tayi a kwanakin baya duk da ta samu sauki sosai sosai don yanzu kam maganar ta ras Alhamdulillah.
Hira suka sha sosai har da su Umman duka. Sai da ga baya suka fita suka barsu su biyun.
Ammah ta nuna jin dadinta kwarai don taga Anti Mami cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Bugu da kari ga karatun da ta keyi. Ta jinjina mata sosai kuma ta mata adduar Allah sanya alheri.
Bata bar gidan ba sai wajen karfe goma da Mu'azzam yazo daukanta. Wannan karon kam dashi akayi tafiyar don cewa yayi kafarsa kafarta. Da Anti Mami ta rakata kofar gida ta tsaya suka gaisa.
"Yau kam dai naga Maman Ahmadin da ta kwace min Ammah ta"
Anti Mami tayi dariya. "Ni na isa in kwace maka ita? Kai ne fa madubin zuciyarta "
Mu'azzam ya fashe da dariya har da sunkuyawa. "Ita tace miki haka?"
Ammah ta kallesu tana murmushi. Yadda suke zolayar juna kamar sun san juna tun da. Sai taji zuciyarta tayi fes.
Sukayi sallama Anti Mami ta juya ta koma ciki.
A daki ta samu Fareeha kwance a can lungun gado tayi shiru.
"Adda yaya dai?"
Girgiza mata kai kawai tayi. Yusrah ta shigo da roban zobo a hannunta.
"Fareeha kinci abincin?"
Sai a lokacin Anti Mami ta lura da plate din fried rice da salad din da ke kan dressing mirror din.
"Gashi can kuwa bata ci ba. Meya same ta ne?"
Yusrah ta zauna a bakin gadon ta dan kurbi zobon nata. "Nima fa bansani ba. Kawai muna dawowa daga wajen event din tace bata jin dadi. Da muka zubo abinci ma tace bazata ci ba shi ne Mama tace na kawo mata daki"
Anti Mami ta matsa kusa da ita ta dan taba wuyanta ko zataji da zafi sai taji ta kalau. "Adda menene? Ko gajiya ce?"
Ta daga mata kai kawai bata ce komai.
"To ki tashi mu tafi masaukin mu. Kinga dare yana yi. Kar a rufe gidan Anti Jamy bamu koma ba"
Sai a lokacin ta juyo ta kalli Yusrahn. "Wa zai kaimu?". Ji take in ta sake sanya Ya Ashraf a idonta to zata iya fashewa da kuka. In kuwa akace shi zai kaisu to ta fasa tafiyar. Anan zata kwana ko da kuwa a kasa ne.
"Baba Habu" ta bata amsa a takaice.
Saukowa tayi akan gadon tana daukan mayafinta da jakar ta. "Anti Mami sai da safe"
"To Allah ya kara sauki"
Har suka isa gidan Anti Jamy ba abunda take tunani sai hoton data gani a fuskar wayar Ya Ashraf. Shin wacece ita? Tun da har ya saka ta a fuskar wayar sa yana nufin cewa tana da muhimmanci a rayuwar sa kenan? Hakan Yana nufin koyaushe ya bude wayarsa sai yaga hoton kenan? Sai yaga wannan murmushin? To wacece ita?
Sai da tazo kwanciya ma abun ya fara bata haushi. Meyasa zata damu kanta? Dama a tunaninta santalelen saurayi kamar Ya Ashraf za'a ce bashi da wacce yakeso ko kuma ace ba wadda take son shi? Ita ma dai ta iya shirme.
Wani tsaki taja tana gyara kwanciyarta. Lokaci kuma yayi da yakamata ace ta cire shi a ranta tunda da alama bata da gurbi a nashi ran sai mai maroon hijab. Sai taji kuma ta tsani maroon color. Wani tsaki ta sake ja tana rufe fuskarta da bargo.
Haka ta kwana sam ranta babu dadi.
********
To dai Adda. Kema da kin hutar da zuciyar ki akan mutumin nan. Seems like Ya Ashraf has lost himself a crush.
How was the chapter? Hope you liked it.
I will be looking forward to all your comments.
❤❤❤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top