16.


"What?" Kallonshi take kamar ya samu tabin hankali.

Wani kololon bakin ciki ne ya taso ya tsaya a makogoronsa. In ta sake mishi wannan kallon to tabbas zaiyi wani abun da zai sa shi yin nadama. Ya dunkule hannayensa waje guda yana maida numfashi. "Bazan iya ba Misriyyah. Aure ba shi bane mafitanmu"

"In ba aure ba to yaya kakeso muyi?"

Ya bude bakinsa zai bata amsa kenan ya ji vibration din wayarsa a cikin aljihunsa. Cikin tunanin ko Ammah ce ke kira yayi sauri ya zarota amma sai yaga bakuwar lamba. Dukda haka dai ya amsa.

"Hello"

Wata baturiya ce tace "Is this Mr. Mu'azzam Kabir?"

"This is he"

"I'm calling from University Hospital. A Mrs Fatimah Kabir has just been brought in. You're listed as her next of kin"

Kafafuwansa ne yaji suna barazanar kin daukansa don haka yayi saurin tsugunawa kasa. "Is she okay?"

"She's had a stroke and is now in surgery. You need to come in"

Sake kankame wayar yayi ko zai samu saukin tashin hankalin daya samu kanshi a lokacin.

"Innalillahi wa inna ilaihi raajiun" ya furta a hankali kafin ya mike. "I'll be there" ya bata amsa sannan ya katse wayar.

Ko kallo Misriyyah bata ishe shi ba ya juya ya fara tafiya. Yana jin ta tana kiran sunansa amma yaqi ya juyo.

Bai san lokacin da ya shiga motar ba balle ma lokacin da aka saukeshi, shi dai kawai ya tsinci kansa a gaban counter din Emergency Department din asibitin yana tambayansu bayanin Amman. Ya samu cewa har a lokacin tana dakin tiyata. Suka mishi kwatance cewa ya haura sama ya jirata.

A iya bayanin da likitocin suka mishi, faduwa tayi a kofar wani shagon saida kayan masarufi. Jama'ar wajen ne suka kira 911 aka kawota asibitin. Kuma da aka mata MRI ne aka fahimci cewa akwai abunda ke hana jini isa kakwalwarta (clot) wanda ya haddasa daukewar numfashinta da amfanin dukkan gabobinta.

"We administered a mechanical thrombectomy which successfully pulled the clot out." Dr. Ezzeddin ya masa bayani.

Duk abunda ake cewa kawai jinsu yake amma ya rasa me ze ce. Shi dai burin sa kawai a fito masa da Ammansa lafiya.

Hawaye ne masu dacin gaske suka zubo masa a lokacin da ya ga yanayin da ta ke. Ko ba a fada masa ba yasan shi ne silar wannan halin data shiga don likitocin sunce suna ganin jininta ne ya hau.

Kwananta biyu kafin nan ta farka. Shi ta fara gani kuwa da ta farka.

Tana saka idanunta a cikin nasa babu shiri ya ji hawaye sun fara sintiri akan kuncin sa. Ya riko hannunta ya rungume a kirjinsa yana kuka mai tsuma zuciya.

"Ammah ki yafe min" ya furta yayinda kukan yake kokarin cin karfinsa.

Tunda suka hada ido ta dauke bata kara kallonsa ba kuma.

A haka likitan ya shigo tare da residents dinsa suka same shi yana faman share hawaye. Hakuri suka shiga bashi suka samu ya dan nutsu kafin suka mishi bayanin halin da Amman take ciki da kuma sauran gwaje-gwajen da za'a mata.

Likita ya mata physical exam don a gano ko akwai wani abu daya tabu a jikinta dalilin stroke din.

An yi rashin sa'a harshen ta ya kwanta don maganarta sam baya fita da kyau. Bayan nan kam komai na amfani, hannayenta da kafafunta duk sumul.

"Zamu fara speech therapy kai tsaye" likitan ya masa bayani cikin harshen turanci.

Duk wannan abun da akeyi, sam Ammah ta ki yadda su hada ido da shi. Idan ya mata magana ma saidai ta kalli wani wajen amma ba shi ba.

Ta kasa cire hoton dake yawo a kwakwalwarta a tsawon kwanakin nan. A bacci ko a farke in ta rufe idonta babu abun da take gani illa lokacin da Muazzam yake aiwatar da abun da ya haramta a gareshi ga wacce ba matarsa ba. Abun da yake kara kona mata rai shine shin wai meyasa tun yana saurayi beyi wannan shirmen ba, sai yanzu daya malllaki hankalin kansa yasan fari da baki?

Allah ya gani tayi iya kokarinta wajen tarbiyyarsa. Tasha wahala ta hana kanta bacci kuma ta hana kanta jin dadin wasu abubuwa na rayuwa duk dan taga ya zama mutum ingantacce. Tsoron ta daya kar ya kwaso hali irin na turawa don ya tashi tsulum cikinsu. Ta dage kwarai wajen karatun addininsa da cusa masa tsoron ubangijinsa a ransa. Lokacin kuwa daya zo mata da zancen aure yana dan shekara 24 babu wanda ya kaita farin ciki a rayuwa. Damuwarta dama shi ne kar ya fada halaka kuma sai Allah ya kawo mata sauki.

Amma sai yanzu, bayan duk wannan gwagwarmayar da ta sha, shi ne zai watsa mata kasa a ido? Ita kam baza ta iya hada ido da shi ba. Don a yanzu kam ma bata san me takeji a game da shi ba. In ta kuskura kuma ta mishi magana to zata fada mishi abinda zai dade yana sosa masa rai. Ba kuma ta son haka ya kasance. Ta fi son sai ta huce tukun.

Don haka share shin ne kawai mafita a gareta.

Sai da sukayi sati a haka.

Idan ya shigo da safe ya same ta ko ya gaisheta bata nuna alamun ta san da zamansa a dakin. Iyakacin hirar dayake da likitoci ne game da cigaban da take samu. Shi zai rakata wajen therapy ya kuma dawo da ita amma dukda haka ko 'uhm' bata cewa. Idan wani abu na mata ciwo ko tana so ta ci wani abu sai dai ta danna dan button a jikin gadonta sai nurse ta shigo taji ko menene.

Hakan yana sosa masa rai matuka don tana nuna mishi cewa shi da dutse basu da banbanci a wajenta. In banda haka, a duk fadin asibitin nan babu wanda ya cancanci ya fara sanin me ke damunta bayan shi, amma sam taki bashi wannan daman.

Abun duk ya bi ya isheshi.

Saukin daya samu shine idan sun danyi waya da mutanen gida suji ya jikinta, takan dan kalleshi ko kuma ta nuna alamar tana so ya bata wayan. Yawanci idan Anti Bebi ta kira in dai taji ita ne zata nuna mishi cewa tana so ta yi magana da ita dukda kuwa maganar ta ta har yanzu baza ka gane wasu kalmomin ba. In bacin haka kam bata ce masa komai.

Gyangyadi ya fara yi a kan 'yar kujerar daya saba zama a kai a dakin nata yaji karar wayar sa a jikin aljihun wandonsa. Yana dubawa yaga lambar Nigeria ce ya san cewa masu neman Ammah ne don yanzu da wanda ya sani da wanda be sani ba duk ta wayar sa ake kira aji yaya yanayin jikin nata yake.

Da sallama ya amsa dukda beji dadin katse masa baccin da akayi ba don jiya da daddare bai samu wani isheshen bacci ba. Yana sallar asuba kuwa asibitin ya taho.

Daga daya bangaren Anti Mami ta amsa masa sallamar hade da gaisuwa. "Ina wuni?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah" ya amsa yana dan sosa idonsa.

"Anti Bebi ce ta bani number dinka. Yaya jikin Amman?"

"Jiki da sauki Alhamdulillah. An kusa sallamarmu ma nan bada dadewa ba"

Kokarin boye hawayenta take da kuma saita muryarta don ta masa magana.

A satin da ya wuce ne taji shirun yayi yawa daga bangaren Ammah don haka ta gwada wayarta amma bata sameta ba don haka ta yanke shawarar kiran Anti Bebi taji ko lafiya. Ai kuwa labarin daya risketa ya matukar razana ta. Hankalinta ya tashi sosai. Ko bayan Anti Bebi ta turo mata lambar Muazzam din ji tayi kamar bata da karfin gwiwar kira don gaba daya zuciyarta ta karaya.

Kuka kam ta sha shi don abun ya taba ta sosai. Ita kanta tayi mamakin irin girgizar da tayi. Bata san shakuwar da sukayi da Amman ya kai har haka ba amma sai gashi cikin 'yan kwanaki ta shiga wani yanayi saboda alhinin abun.

Daga baya ne ta dan sami nutsuwa kuma ta gode wa Allah da abun a iya stroke din ya tsaya. Da Ammah ta rasa rayuwarta kam bata san yaya zata ji ba. Matar nan da ta debe mata kewa a lokacin da duniyar tayi mata fadi, ta taimaketa ta fito daga cikin duhun da mutuwar Mukhtar ya saka ta a ciki, ta sakata dariya da nishadi da dadadan labaranta a lokacin da tayi tunanin bazata kara dariya a rayuwarta ba; yau idan akace babu ita a duniya yaya zatayi?

Karfin gwiwar da taji ta samu ne a 'yan kwanakin nan ya sa ta dauki waya har ta kira Muazzam din. Amma kuma yana dauka duk sai taji abun ya dawo mata sabo.

Ta hadiye wani abu a makoshi kafin nan tace "To Alhamdulillah. Allah ya kara mata lafiya yasa kaffara ne"

"Amin Amin. Mungode" ya amsa mata.

Har zata katse sai kuma tace "Ka gaida Amman dan Allah."

"Zata ji. Wa za'a ce mata?"

"Mami. Maman Ahmadi" ta fada a takaice.

"Zan fada mata inshaAllah"

Sai wajen karfe tara Amman ta farka. Yau kam kafin ma tayi yunkurin kiran nrse din yayi sauri ya isa gareta.

"Ammah gani" ya fada yana kamo hannunta tare da taimaka mata ta tashi zaune. Da ido kawai ta nuna masa zata shiga bandaki don haka ya kama hannunta ya ja ta har bandakin. Yana tsaye a bakin kofar ta fito. Da alama alwala tayi don haka yayi saurin karasawa wajen jakarta da ya hado mata daga gida ya zaro sallaya da hijabinta. Ya shimfida mata sannan ya mika mata hijabin.

Sallar walaha ta gabatar.

"Nikam....ka....de...na...zu...wa....ai...ki...ne?"

Saida ya waiga yaga ko akwai wani a dakin bayan shi don ya tabbatar cewa shi takeyi wa magana. Da ya juyo ya kalleta zai iya rantsewa cewa ya ga giftawar murmushi akan labbanta.

"An bani hutu ne" ya amsa mata a hankali.

"Wa...ni...iri..n....hu....tu?"

Ya sosa girarsa. "I failed the mental health examination"

Kallonshi take a nutse. Kamar zata sake masa wata tambayar kuma sai ta fasa don yanzu maganar ma da kyar take yi. Da ba dan likitan ma yace tana kokarin yi ba ita kam da ta dan hakura da yinta na wasu 'yan kwanaki. Wasu lokutan har haki take idan ta furta kalmomi masu yawa. Abunda za ta fada da a sakwan goma yanzu sai ya kaita kusan minti daya kafin ta harhado kalmomin.

Mikewa tayi ta nade sallayar ta ta koma ta zauna a kan gadon.

A rashin son yankewar hirar tasu ne yasa shi fadin "Dazu wata Maman Ahmadi ta kira ta ce a gaishe ki"

Da sauri ta juyo ta kalleshi. "Yau....she?"

"Lokacin kina bacci"

"Shi...ne....ba...ka....ta...she..ni..
.ba?"

Sai kuma a lokacin yayi nadamar fada mata hakan don yaga kamar ranta ya baci. Baya kuma son hakan ko kadan. Ya samu ta sassauto ta fara kula shi ba zaiso abun da zaisa ta sake yin fushi da shi ba yazo ya gifta a tsakaninsu.

Nan da nan ya zaro wayarsa a aljihunsa. "Barin kira miki ita yanzu sai ku gaisa ko?"

Jinjina masa kai tayi alamar hakan yayi mata dadi.

Yana kira kuwa wayar ta shiga.

"Salamu Alaikum" Anti Mami tayi sallama.

"Wa alaikum salam Maman Ahmadi. Ga Ammah nan ta tada hankalinta wai sai kun gaisa"

Wata harara Amman ta watsa masa wanda ya saka shi jin nishadin da ya dade be ji shi ba. Ya mika mata wayar yana murmushi ita kuma ta wafce.

Dariya ta kwace mishi a lokacin da ya koma kujerarsa ga zauna.

Mamaki yake yanda yaga Ammah tana ta fara'a da kuma dagewa wajen yin magana da Anti Mamin. Shi dai tunda yake da ita bai taba jin ta ambaci wannan sunan ba dukda kuma ba wai yasan 'yan uwan nasa dayawa ba, yasan dai cewa wannan Maman Ahmadin ba danginsu bace.

Da kyar Ammah take hado kalmomin da zata kwantar wa Mamin da hankalinta. Hakan kuma ya kara saka Mamin kuka saboda yadda taga Ammah ta damu da ita dukda tana halin rashin lafiya. Wannan kulawar data nuna a gareta kadai ya isa ta ji ta shige mata zuciya.

A haka suka gama wayar kowa yana wa dan uwansa addu'a.

"Who is she?" Muazzam ya tambaya bayan ya karbi wayarsa a hannun Amman.

Ta dan tabe bakinta hade da gyara kwanciyarta a kan gadon. "Ba....ruwa...n...ka"

Ya girgiza kai yana dan murmushi. Abun yana masa dadi yanda take ta gwale shi don haka ya nuna alamun ta sassauto daga fushin da ta ke da shi. "Allah huci zuciyar Ammah ta"

Maimakon ta ba shi amsa ma sai ta juya masa baya tana rufe ido. Ko ba komai yau taji zuciyarta sakayau sabanin da da kullum ta ganshi sai ta ji ta cunkushe mata.

Bayan kwana uku aka sallamesu da sharadin cewa Ammah zata na zuwa speech therapy dinta tunda tana da sauran kusan sati biyu kafin su kammala session din nasu.

Hannunsu yana cikin na juna suka fito a asibitin. Ya tsayar musu da mota suka shiga zuwa gidan Amman. Hira ya ringa yi mata dukda ba ko yaushe take bashi amsa ba har suka isa.

Shi ya tsaya biyan mai taxi din da kuma daukar jakarta a boot din motar inda kuma ita ta wuce kai tsaye zuwa gidan don a zahirin gaskiya ta yi kewar gidan nata. Sam ba'a son ranta ta zauna har tsawon wannan kwanakin a asibitin ba.

Tana kokarin neman mukullin ta ne a handbag dinta sai taga kamar kofar gidan ma a bude take. Nan zuciyarta ta doka. Kar dai Muazzam ne ya manta be rufe mata gida ba daya zo daukan kayanta?

Cike da mamaki da tsoro ta tura kofar a hankali tana lekawa ciki. Gaba daya foyer din nata ya kaure da ihun 'surprise!!'. Sai da ta girgiza don ko kadan ba abunda tayi tsammani ba kenan.

Abokin Muazzam Mujahid ne ta fara hangowa tare da matarsa da 'yar su, sai makociyarta ta sama Mrs Wright wata dattijuwa wanda ke zauna tare da jikonkinta guda biyu Miles da Hannah, sai wasu abokan aikinta kuma guda biyu. Katuwar banner ce ta gani sun manna a hanyar shiga falon ta wanda ke mata maraba da samun sauki. Ga balloons nan duk sun cika ko ina.

Ta juya baya don ta tuhumi Muazzam kawai se ta ganshi rike da cake a hannunsa yana mata murmushi.

Kallon tuhuma ta masa inda shi kuma ya daga mata gira alamar 'yayi miki?'

An ci an sha kuma an yi wa Ammah fatan samun sauki. Har gifts suka kawo mata duk dan a karfafa mata gwiwa. Wani abun mamakin ma bayan kowa ya watse sai taga ashe har fentin falonta aka sauya. Ta san kuma ba aikin kowa bane sai na Muazzam.

Yana kitchen yana aikin saka sauran snacks din da suka rage da sauran cake din a cikin fridge ta shigo.

Ya juyo suka hada ido ya mata murmushi. Rashin mayar masa da murmushin ne yasa ya katse abinda yake ya taho zuwa gareta. Ya karanci duk abunda yake gani a kwayar idon ta.

"Ammah I'm sorry" ya furta a hankali yana saka hannayensa a cikin nata. "Na tuba. Na roki Allah gafara. Amma kema ina neman yafiyarki. Dan Allah ki yafe min."

Nan da nan hawaye suka fara sintiri a fuskarta. Kukan ta ya dade yana makale a wuyanta yau kam ta sake shi.

Ya jawota jikinsa yana bubbuga bayanta zuciyarshi tana mishi wani irin kuna.

Kuka take sosai hadda shesheka. Abun da Muazzam bai sani ba shi ne wannan kukan da take yana kara wanke mata sauran burbudin bakin cikin da take ciki ne.

Sai da tayi mai isanta sannan ya ja ta zuwa sink ya kunna famfon. Ta sa hannu ta wanke fuskarta sannan ya mika mata tissue ta goge.

"Ammah....."

Ta daga mishi hannu alamar ya dakata.

"Ya....wuce. Allah....ya...ya
..fe...ma...na....ga...ba...da...ya.."

Tana fadin haka ta juya ta wuce dakinta. Da zai bita sai kuma yaji ta turo kofar hade da saka key.

Jingina yayi a jikin fridge din yana maida numfashi. Ko ba komai dai ta ce ta yafe mishi. Yanzu abun da ya rage shi ne ya cigaba da kyautata mata fiye da yanda yake a da don ya gyaro alakarsu.

Da wannan tunanin ne ya gama tattare mata gidan tas. Ya tafasa ruwa ya saka mata a flask  don yasan idan ta tashi zata nemi tea. Ya gama tsaf sannan ya jawo mata kofa ya tafi.

●●●●●

I just realized that not every chapter has to be perfect so you guys should just manage this.

Thank you for your support and encouragement. Allahumma Barik.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top