14.

Littafi ne a bude a kan cinyarta. Duk wanda ya kalleta zaiyi zaton karatu take don gaba daya hankalinta yana kan littafin, amma a zahirin gaskiya tunani me zurfi take.

Tunanin Muazzam take da sauyin data gani a tattare dashi tun ba yau ba. Tsakaninshi da ita babu boye-boye don sun taso rayuwarsu daga ita sai shi. Mahaifinsa ya rasu tun yana karami don haka ita ta zame masa komai a rayuwarshi. Sunyi shakuwa matuka da babu abun da yake boye mata a rayuwarsa; ko ya boyen ma shi da kansa yake zuwa ya fada mata daga baya. Ita ce babbar aminiyarsa wanda tasan duka sirrikansa a fadin duniyan nan.

Ko lokacin da ya auri Najmah idan yazo wajenta neman wata shawara game da aikinsa ko abin da ya shafi lafiyarsa, sai tace masa yaje yayi shawara da matarsa tukun. Amma hakan bazai hanashi zuw washegari da wata matsalar ba. Ya riga ya saba ita ce komin sa.

Ita dinma kuma kusan hakan ne. Duk inda ta waiwaiya in tana neman shawara shi take fara kira. Shine abokin hirarta shine me bata shawara kuma shine babban abokinta. Kuma bata fata hakan ya canza a tsakaninsu.

Amma kwanan nan sai taga kaman akwai abun da yake boye mata. Da ta tambayeshi kuma sai yace mata babu komai. Ta hango rashin gaskiya karara a idonsa amma sai ta kyale tana jiran ranar da zaizo da kanshi ya sanar da ita abunda yake faruwa. Amma sai me? Shiru shiru har yanzu ranar batazo ba, har ta gaji da jira. Hankalinta kuma kara tashi yake don ta lura ko ma meye Muazzam yake ciki to ba alkhairi bane.

Bazatace ga abunda take tunanin shi ne matsalar ba amma har cikin zuciyarta tasan yana cikin matsala kuma yana bukatar taimako.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan ta lalubo wayarta dake gefen ta. Yau sati biyu kenan rabon da ta saka shi a idonta, abun da bai taba yi ba kenan a rayuwarshi. Baya sati bai leko ta duk kuwa irin matsin da ke cikin aikinsa. Amma ace har sati ba daya ba, har biyu, kwana goma sha hudu, amma babu labarinsa.

Kai tsaye kiran nata voice-mail ya shiga alamar cewa wayar tashi ma ba a kunne take ba.

Babbar magana.

Tashi tayi daga mazauninta ta nufi bandaki. Alwala tayi ta dawo parlon nata ta shimfida babbar daddumarta ta fuskanci gabas.

Sallar walaha ta gabatar sannan ta zauna ta danyi karatun alkur'ani ko zata samu nustuwa. Ta dan jima tana karatun kafin ta rufe ta daga hannunta ta fara Addu'a. Wayarta ce ta shiga ringing. Har za ta katse addu'o'in nata a tunaninta ko Muazzam dinne yake kira amma sai ta cigaba da zayyano wa Ubangijin Rahama matsalolinta kuma ta nemi taimakonSa a dukkan lamuranta. Tana idarwa ta jawo wayar sai taga Anti Bebi ce ta kirata.

Ta dan murmusa kafin ta kirata.

"Mama Amma am" muryar Anti Bebi ta jiyo daga daya bangaren. "Ina kwana ne ko ina wuni?"

Amma tayi dariya "Yanzu kam safiya ne anan. Yaya kuke?"

"Lafiya Alhamdulillah. Yaya kanina?"

Amma ta danyi Jimm kafin tace "Kwana biyu ban ganshi ba amma yana nan lafiya Alhamdulillah"

Anti Bebi ta yi ajiyar zuciya "Amma da dai ya dawo gida yanzu tun da shi kadai ne. Kema kina bukatar wani a kusa da ke ai ko kuwa?"

Ta danyi murmushi wanda yafi kuka ciwo. "To Bebi ai yanzu kam ya riga da ya saba da zama shi kadai. Kuma ni dinma na kusa dawowa gida inshaAllah "

"Kai haba? Gaba daya?"

Amma ta jinjina kai kamar Anti Bebin na gabanta. "Haka nake fata. Nayi applying for early retirement. Zuwa dai wata shekarar inshaAllah"

"Kai Alhamdulillah. Amma nayi murna. InshaAllah kina nan za ai biki"

"Ke kam dai har yanzu baki daina zancen bikin nan ba. Ni na dauka ma an fasa" Amma ta fada tana dariya.

Anti Bebin ma dariya take. "To Mama abinka da wanda bata taba yi ba. Duk na bi na kagu. Sati biyu ma da suka wuce gidansu yaron sunzo akan zasu kawo tambaya, kawai kuma sai akayi rasuwa"

"Subhanallah waye ya rasu?"

"Hmmm. Kin tuno kanwar Babansu Ashraf dinnan da kika ganta wancan zuwan naki?"

Amma ta dan dakata tana tunowa. "Kamar na tunata. Su biyu dai nagani lokacin"

"Eh dayar cousin dinsu Samha ce" Anti Bebi ta bata amsa "To wallahi mijin kanwar tashi ne ya rasu."

A daidai lokacin kuma fuskar Anti Mami ta hasko a kwanyar Amman. Tausayinta ta ji ya mamayeta.

"Allahu Akbar. Allah sarki baiwar Allah. Allah ya jikanshi da Rahama ya sa ya huta. Allah basu dangana"

"Amin Amin Mama"

"Yaransu nawa?"

"Yaronsu daya. Shekararsa biyu"

Wani abu ya soki zuciyar Amma. Taji mutuwar baban Muazzam ta dawo mata sabuwa a lokacin. Shekarun Muazzam din da kadan suka wuce hakan a lokacin. Ta tuno lokacin taji duniyar ta mata fadi, kamar bata da kowa a cikinta. Kadaici, da tsoro, da kewarsa duk suka hadu waje guda suka cunkushe a zuciyarta. Ga tausayin Mu'azzam. Tana tunanin yadda ze taso babu Uba. Gashi lokacin tana tsakiyar jarabawa tana aji daya a jami'a.

Wahala kam ta sha ta. Da taimakon Ubangiji ta samu ta karasa semester dinnan. Mahaifiyar marigayin ce ta zauna da ita a lokacin da tayi takaba har ta gama. Kusan ita ce ta reni Muazzam dinma don kwata-kwata sai taji ta kasa yi masa komai.

Da ta gama takabar kuma cikin ikon Allah taji wata nutsuwa da tawakkali ya saukar mata. Ta rungumi kaddara kuma ta kudiri niyyar tarbiyyantar da Mu'azzam da kula da shi har zuwa lokacin da Allah ya ara mata.

Wasu hawaye taji sun kwanta a kurmin idonta"Allahu Akbar. Gaskiya ta ban tausayi. Allah ya kara mata hakuri."

"Ameen Mama. Abun kam abun tausayi. Gata 'yar karama"

"Ayyah. Allah ya basu dangana"

Sai kuma suka koma wata hirar. Har sunyi sallama zata ajiye wayar sai kuma ta tsayar da Anti Bebin.

"In bazaki damu ba ko zaki turomin lambar Mami din in mata ta'aziyah?"

"Laa Mama ba komai. Barin turo miki yanzu ma. Allah bada lada"

Bata samu ta kirata ba sai da aka kwana biyu, don tana ta tunanin mai zata ce mata kuma da wasu kalamai zatayi amfani dasu wajen tausasa mata zuciya. Gashi ba wai sunsan juna sosai bane.

A haka dai ta yanke shawara ta kirata a yammacin wata ranar asabar wanda yayi daidai da bayan sallar Isha a Nigeria.

Anti Mami na kwance a dakinta taji wayarta ta fara ringing. Bacci takeso tayi don rabon data yi bacci isashshe har ta manta. Tun da akayi rasuwar Ahmadi ya birkice mata.

Maghreb tana yi zai fara kuka yana neman Babansa don kusan wannan lokacin yake dawowa daga aiki. Ya saba yana dawowa zai ruga wajenshi akan 'yan kananun kafafunsa ya rungume sa. Shi kuma baban sai ya daga shi sama yana hajijiya dashi suna dariya.

To yanzu ya kasa fahimtar dalilin dayasa baya ganin baban nasa a gida. Haka zatayi ta rarrashinsa amma ina. Sai da kyar idan bacci yaci karfinsa tukunna take samun lafiya. Gari na wayewa kuma haka zai fara nemansa.

Lokacin da ya fara ta dan samu taimako saboda 'yan zaman makoki da suka zo. Daga me goya shi sai me mishi wanka ko zaiji dadin jikinsa. Amma ana sadakar bakwai kusan kowa ya watse. Aka barta daga ita sai Fareeha sai Gwaggon Mukhtar.

Yanzun ma samu tayi Fareeha ta goye shi shine ta dan shigo daki kozata samu baccin ko da kuwa na awa biyu ne.

Kaman bazata ansa wayan ba daga farko. Tasan 'yan ta'aziyyah ne tunda kowa abinda ya ke kira ya mata kenan yanzu. Idan tace bata gaji ba tayi karya amma ba yadda ta iya. Sai da wayar ta kusa yankewa tukunna ta jawota ta kara a kunne.

"Salamu Alaikum"

Jin muryar babbar mace yasa Anti Mami saurin amsawa "Wa alaikum Salam. Ina wuni?"

"Lafiya Alhamdulillah Mami. Yaya kuke? Ya yaronki?"

Suka gama gaisawa sannan Amma ta mata bayanin ita wacece da kuma dalilin kiran nata.

"Ina rokon Allah ya baki ikon cin wannan jarabawar Mami"

Hawayen da basu gaji da zubowa daga idonta ba suka kwararo kamar an bude famfo. Wani abu ya tokare mata a makoshi.

"Bazance ina jin yadda kikeji ba amma naji kwatankwacin hakan a wasu shekaru masu yawa da suka wuce. Nasan akwai daci Mami, amma sai kin dage da Addu'a. Allah ya taimakeki ya baki tawakkali. Allah ya baki ikon rainon danku"

"Amin Amin." Anti Mami ta amsa tana share hawayenta.

"Ki dauki lokacin da Allah ya ara muku ke da shi a matsayin kyauta babba daga wajen ubangiji, kuma ki sa a ranki karbarshi dayayi a lokacin da kika fi bukatarsa hakan ba yana nufin ko Allah baya sonki bane. Karki manta Allah yana jarabtar wanda ya fi so ne"

Ammah ta shiga bata labarin yanda Baban Muazzam ya rasu, da halin da ta shiga ciki, da taimakon data samu daga wajen 'yan uwanta da 'yan uwan marigayin. Ita kanta batasan dalilin dayasa take bata labarin ba, kawai ta tsinci kanta da batan ne. Tayi mamaki kuma da batayi hawaye ba.

Lallai bature yayi gaskiya dayace time heals all wounds.

Da sukayi sallama sai Anti Mami ta nemi bacci a idonta ta rasa. Tashi tayi ta shimfida sallayarta dama da alwalarta ta Isha.

Nafiloli ta ringa yi ba adadi tana kai wa Allah kukanta a kowacce sujood. Har sai da Fareeha ta shigo ta kwantar da Ahmadi akan gadon sannan ta tsagaita. Jingina tayi a jikin gadon tana tasbihi da tahmidi wa ubangiji. 'Yar wayar da sukayi da Amman yanzu ya sa ta sanyi a ranta.

Wannan mutuwar jarabawa ce a gareta, kuma inshaAllah zata ci ta.

Washegari ta tashi ranta sakayau. Tayi wa Ahmadi wanka; abinda ta dade batayi ba tun da akayi rasuwar. Ta samu ankawo abun karyawa daga gidan Babban abokin marigayin. Doya ce soyayya da miya.

Kwana biyu baya iya cin abinci amma yau sai ta samu kanta da cusawa. Shima Ahmadi da ya ga tana ta ci sai ya zauna sukayi taci tare.


Abu kamar wasa duk bayan wasu 'yan kwanaki sai Ammah ta kirata su gaisa taji Yaya take. Wasu lokutan gaisawa kawai zasuyi sai ta mata sallama saboda tana wajen aiki. Idan da weekend ne wayar tasu takanyi tsawo.

Yawanci labari zata bata akan wani kalubale daya sameta bayan mutuwar Baban Muazzam da kuma yanda ta ci galabar abun. Takan dade kuma tana yi wa Mamin Addu'o'i da fada mata kalaman da zasu kwantar mata da hankali. Hakan yana mata dadi matuka.

Akwai dararen da zata farka cikin dare sai ta juyo da sauri ko zata ga Mukhtar din a kwance a bayanta, rashin ganinsa a wajen daya saba kwanciya zai sa ta fashe da kuka. Zuciyar ta ta cunkushe waje guda. Sai tayi tunanin ita ma Ammah haka taji da mijin nata ya rasu? To ta yaya ta wuce wannan bigiren? Anya ita zata iya kuwa?

Haka zata kwana tana zullumi har gari ya waye. Takanyi tunanin kiran Amman ko zata dan samu sassauci don labaran da take bata suka dan sanyaya mata zuciya, amma bata taba gwada hakan ba. Sau daya ta taba kiranta shima da tazo taga missed call dinta, sakwan aspirin sukayi kawai Mami taji katinta ya kare. Ai bata sake gwadawa ba.

Itama Amman sai ta nuna mata cewa tafiso ita ta rinka kiranta da kanta don yafi mata sauki.

A kwana a tashi zumunci mai karfi ya kullu tsakaninsu. Anti Mami sai taji kaman Allah ya sake bata kyautar wata mahaifiyar. Ko bayan Fareeha ta koma makaranta, bataji kadaici sosai ba saboda Amman. Sai ta dawo ma kullum take kira. Ahmadi ma har yazo ya saba da ita.

Karfe takwas tanayi wayarta zata fara kara. In bata kusa zai je da gudu ya dauko wayar ya kawo mata yana fadin "Mama Mma. Mama Mma" kamar yadda yaji mamanshi tana cewa Mama Amma. Takan bashi wayar yayi ta yi wa Amman gwalatun shi, ita kuma tana biye mishi.

*********

"Call me when you get home okay?" Ya fada yana shafa gefen fuskarta. Ta lumshe ido tana kara kwantar da fuskan nata cikin tafin hannunshi.

Duk lokacin da ta tsinci kanta cikin wannan yanayin dashi sai taji kamar kar su rabu, amma da zarar ta koma gida sai taji ta tsani kanta. InshaAllahu suna sake haduwa kuwa shaidan zai kada mata ganga sai ta manta duk wasu dalilai dayasa ta tsani kanta a baya.

Ta bude idonta hade da rike sitiyarin din motar yayar tata data dauko. "I will" ta bashi amsa a takaice.

Ya sunkuyo dai dai fuskarta ya manna mata lebbansa kafain yaja da baya yana jira taja motar ta wuce.

Sai da ta sakar mishi murmushi wanda ya sace mishi gwiwa kafin ta saka giya ta hau kan titin. Yana kallo tasha kwana kafin ya ja dan karamin akwatin sa ya karasa kofar gidan nasa. Tun da asuba ya tashi aiki kuma yana fitowa ita ya fara cin karo da tana jiranshi a wajen data saba jiran nasa.

Shi kanshi bai san ya akayi suka kawo wannan matakin ba a alakarsu kuma ba zaice ga dalilin da hakan ke faruwa ba, shi dai kawai yasan duk sanda suke tare tana sa shi nishadi kuma tana yaye mishi duk wani kadaici dayake ji.

Ya zura hannayensa cikin aljihunsa don zaro makullensa amma sai yaga a wangale kofar. Yana daga kai suka hada ido da ita yaji gaba daya gwiwowinsa sun sage don kallon datake masa ya firgita shi. Tsoro, tuhuma, tashin hankali da kuma karayar zuciya; su ya hango a idanun mahaifiyar tashi.

"Mu'azzam!!" ta kira sunanshi muryarta na rawa. "Innalillahi wa inna ilaihi raajiun"

Juyawa tayi da sauri ta shige cikin gidan, tsumman dake hannunta wanda take goge a dazun kafin isowarsa ta sulale daga hannunta ta fadi kasa.

Kaman an shuka bishiya haka ya tsaya a kofar. Shi bai shigo ba, shi kuma bai juya ya koma inda ya fito ba.

Ba zaice baiyi tunanin wannan ranar ba, amma bai taba tunanin haka zata zo mishi ba.

Ba karamin kokari yayi ba wajen boye alakarsa da Misriyyah. Sau da dama yakan samu kanshi wajen son ya furta wa Amman ko da kuwa sunanta ne amma se ya kasa. Dalilin dayasa ma ya rage zuwa wajenta kenan kwana biyun nan. Idan yaje kuma baya dadewa yake dawowa don sai ya ke ganin kaman zata ga sirrin dayake boyewa a kan goshinsa, ko ta jiyo a muryarsa, ko ta karanto a idonsa. Ya lura da irin kallon datake masa. Shiyasa baya yadda su dade tare. Idan ya kiratan ma haka ne. Nan da nan ya katse zai ce yana da aikin yi.

Shakuwar da sukayi da Mami ne ya dan rage mata zafin abun da take ji game da sha'anin Muazzam din. Sau da dama idan suna waya sai ta mance da duk wasu damuwowinta. Idan Ahmadi yayi wani abun dariyar kuwa sai ya tuno mata da Muazzam din lokacin yana karami.

Addu'a kam bata fasa yi ba. Kullum tana cikin rokon Allah ya dawo mata da danta, bata san menene ko wanene suka dauke mata shi ba, amma kam tana ji a jikinta ta rasa shi. Anyi mata musayar Mu'azzam dinta da wani. Don wannan kam bata sanshi ba.

Mu'azzam dinta yana sonta, yana kaunarta. Burnishi koyaushe ya faranta mata. In ba ya wajen aiki to yana wajenta. Ita ce ma take koranshi dan yaje wajen abokansa ko wasu uzurarrukan sa. Ba shi da wajen cin abinci sai a wajenta. Ba shi da abokiyar hira sai ita. Ba yi da wata aminiya sama da ita.

Sai gashi yanzu duk wannan abubuwan ya dena mata su.

Kewarsa da kadaicin data tsinci kanta ne yasa ta yanke shawarar tattaki tabar gidanta zuwa nashi gidan don suyi maganar fahimta. Ta fahimci cewa in ta zuba mishi ido abun kara jagule wa zaiyi, gwara su zauna ita da shi su san meye matsalar. Idan akwai abinda za'a gyara a gyara don ita kam ta gaji da wannan ciwon zuciyar.

Kwankwasawar datayi tayi ne ya ganar da ita cewa baya gidan. Ta tuno cewa yana ajiye spare key a kasan foot mat don haka tana dagata kuwa ta hango dan mukullin.

Abinda bata saba gani a tattare da muhallinsa bane ta gani bayan ta shiga gidan nashi.

Tarkace ta ko ina. Ga kaya akan kujera an cire an barsu. Socks har a kan dining table. Ga kwanuka anci abinci ba'a wanke ba. Gadon shi ba'a gyare ba.

Yaushe Mu'azzam ya zama messy?

Haka ta cire mayafinta da jacket dinta ta hau tattare gidan. Ta mishi wanke-wanke ta yi vacuuming sannan ta fara goge-goge.

Tana goge dining table dinne taji tsayuwar mota. Tayi tunanin ko shi dinne ya dawo. Da ta ji shiru bai shigo ba shine ta karasa bakin window taga mai ya tsaida shi, tana zuwa kuwa idonta ya gane mata abunda tayi dana sanin gani.

A yanzu ma datake tsaye a tsakiyar falon nashi, hawaye cike a idonta, rokon Ubangiji take yasa mafarki take.

Wannan wani irin mummunan mafarki ne?

Kaman daga can nesa take jiyo muryarsa. Nisan daya kara yi mata sai taji ya kai kamar kilomita ashirin, amma a zahirin gaskiya taku biyu zaiyi kawai ya iso inda yake.

Shi kanshi bai san ya akayi kafafunsa suka kawo shi inda yake a yanzun ba.

"Amma" ya sake furtawa. Da kyar kalmar take fitowa daga bakinsa. Gaba daya komai a jikinsa yaji ya masa nauyi ciki kuwa har da harshensa.

Ta juyo cikin sanyin jiki yayinda hawayen idonta suka gangaro kan kuncinta.

"Mu'azzam meyasa?"

Qwat! Ya hadiyi wani abu me daci.

"Meyasa sai yanzu?"

Ina ma kasa zata bude yanzu ta hadiye shi.

"Nagode wa Allah da Kabir bai ga wannan ranar ba. I'm glad he's not alive to witness this"

Ji yayi kaman sama ta rabe gida biyu kasan shi kuma tana amayar ta wuta.

*****

Ghen ghen times two😂. This was short and rushed but I hope you enjoyed it.

Please please vote and comment.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top