13.

Hazo ake na ban mamaki a garin dayake sanyi ya shigo gadan-gadan. Rigar sanyi ce a jikinta wacce takai har wuya (turtle neck) kalar sararin samaniya. Ta dora doguwar rigar atamfa mai guntun hannu don haka dogon hannun rigar sanyin ya fito. Kanta sanye yake da hular sanyi fara sai dankunneta fari na beads shima dayake ta lilo a kunnen nata.

Kunun gyada take hadawa. Jiya da suka dawo a makaranta da rana taji Anti Bebi tana zancen za'ayi kunun gyada da safe kuma sai taji kwadayin kunun ya kamata ita ma. Don haka tunda tayi sallar asuba sai tayi wanka ta fito. Ta samu Amina tana sharar falo ta tambayeta ko Mama ta mata zancen kunun tace a'a. Kitchen din ta wuce kai tsaye.

Bata san inda gyadar take ba amma a bincike binciken ta ta samo ta markadaddiya a store. Babu bata lokaci ta hau aiki.

A lokacin Anti Bebi ta shigo kitchen din. Har a lokacin idonta cike yake da bacci. Ko wanka batayi ba don rigar bacci ce a jikinta sai hijabin da ta dora akai.

"Ayyah Fareeha am. Da sanyin safiyan nan? Ke kam bakya gajiya ko?"

Tayi murmushi "Mama ina kwana?"

"Lafiya Alhamdulillah. Ke da kika dawo hutu zaki hau wani aiki? To meyasa baki taso Yusrah tazo ta tayaki ba?"

A jiyan aka basu hutun karshen shekara wanda ya kan kama daga tsakiyar December zuwa farkon January. Bappah ne ya zo daukansu shi da Ya Ashraf wanda hakan ya zame musu surprise don basu tsammaci ganinsa ba. Shima hutun yazo. Kwanansa biyu da zuwa kuma daya samu labarin za'a zo daukarsu yace ze biyo Bappan.

Yusrah kam tasha murna sosai dan bata shiri da kowa kamar yanda suke shiri dashi kuma tayi kewarsa sosai. Haka tayi ta mishi surutu a mota har sukazo gida. Ita kam Fareeha tun bayan gaisuwar da sukayi bata kara cewa uffan ba.

Har bayan sun dawo gida ma Yusrah bata barshi ya sararara ba. Duk inda yayi tana biye da shi. Har dare suka kai suna hirar yaushe gamo. Don Fareeha bata ma san yaushe ta shigo daki ta kwanta ba. Shiyasa ma yanzun bata tasheta ba don tasan bacci bai isheta ba sosai.

Ta dan rausayar da kanta tana murmushi tare da jujjuya gyadar da hannunta a cikin robar da ta saka wa ruwa "Mama bakomai wallahi. Ai aikin babu yawa"

Anti Bebi ta jinjina kai kana ta wuce wajen fridge inda ta saka naman kan data dafa jiya da daddare ta ciro shi.

Tukunya ta samu ta juye shi a ciki sannan ta dan kara ruwa akan ruwan romon dake jikinsa wanda yasha citta da daddawa kafin ta shiga saka mishi spices da markadadden kayan miyan da bata rabuwa da shi a freezer dinta koda yaushe. Farfesun naman kan takeson yi don aci da masa wanda tayi order tun jiya da yamma.

Tare suka cigaba da aiki suna dan hirarrakinsu. Yawanci Maman ce ma take tambayarta akan makarantar tasu ita kuma ta bata amsa.

Da sallama ya shigo kitchen din ta kofar baya. A tare suka amsa masa sannan Fareeha ta gaishe shi. Ya amsa hade da jawo wata kujerar tsuguno ya zauna akai.

Tunda ya shigo ta ji ta nemi nutsuwarta ta rasa. Ko a jiya ma da suka gaisa a harabar makaranta sai taji zuciyarta ta buga. Ta zaci ko zumudin zuwa gida ne ko kuma wani abu. Amma yanzu da hakan ya sake faruwa sai ta yadda lallai saboda shi ne.

To meyasa? Tsoronsa take ko me? To rabonta da shi tun yaushe har za ta fara tsoronshi? Dama can ba wani saninsa sosai tayi ba.

Da wannan sakar zuci ta juye gyadar a cikin tukunya sannnan ta daura ta akan wuta.

Hirarsu suke shi da mamansa, ita kuma ta kasa sukuni Allah Allah take ta gama aikinta ta bar kitchen din.

Suna haka sai ga Fadila ta shigo kitchen din itama. Waje ta samu ta zauna kusa da Ya Ashraf tana ta mutsutsuka ido.

"Mama ina kwana? Yaaya ina kwana?"

Suka amsa mata kowa da murmushi a fuskarshi.

"Jiya karfe nawa kuka kwanta ne naga daga kai har Fadilan duk idonku a kumbure?" inji Mama kenan bayan ta rufe tukunyar ta.

Ashraf yayi murmushin gefen lebe. "Dan ma ita ta kwanta da wuri. Ni da Yoosh fa sai karfe daya"

Mama ta jinjina kai. "Lallai a gaishe ku. To yau kam goma tana yi kowa ya nemi square root din sa. Tunda de ba nan kusa zaka tafi ba ai kuna da sauran lokacin yin hirar"

Wajen karfe tara masar ta iso. Kafin nan Fareeha da Mama har sun gama kunun gyadarsu da farfesu, Amina ta share ko ina ta goge sai kamshin turaren wuta gidan yake. Gaba dayansu a falon Mama suka hallara don karyawar.

Lokacin da Bappah yayi sallama ya shigo sai yaji zuciyarshi tayi sanyi. Gaba daya zuri'arsa a waje guda, cikin farin ciki da annashuwa. Samha ce kawai bata nan tana makaranta. A take yayi wa Ubangiji tasbihi tare da gode Masa a dalilin ni'imomin daya masa masu tarin yawa ciki kuwa har da iyalansa.

Sosai sukaci abincin don yayi dadi Masha Allah. Suna gamawa Yusrah da Fareeha suka tattare kwanuka zuwa kitchen inda Amina ta wanke sai Fadila ta sake shara falon Maman ta saka turaren wuta a burner don gaba daya kanshin farfesu kawai kakeji.

A falon ta zauna tana kallon wani film din India da akeyi a B4U, su Yusrah suna ciki suna wanka.

Bappah ne ya leko ya ganta. Ya dan sakar mata da murmushi a lokacinda tace 'Sannu Bappah'.

"Kinji ni shiru ban miki zancen tafiya gida ba ko?" Ya tambaya bayan ya dan dosanu a kan hannun kujera.

Ta girgiza kai tana murmushi.

Shekara daya da wasu watanni kenan tun sanda ta fara karatunta a Kano kuma kamar yadda Bappan ya tsara ana gobe komawa makaranta yake aikowa a daukota daga Azaren. Sannan idan anyi hutu kuma sai tayi kwana biyu a Kano kafin shida kanshi yake daukarta ya mayar da ita. Tun bata saba ba har ta zo ta saba yanzun.

"Ashraf ne yakeso shi ma yaje Azaren amma yanada wani uzuri gobe shine nake tunanin ko zaki jirashi jibi sai ku tafi duka hadda su Fadila ma?"

"Allah ya kaimu"

"Amin Amin. Amma fa in kin kosa ki tafi ki fada min gobe sai muje inshaAllah"

Ta rausayar da kai "A'a Bappah zan jirasu. Tafiyar zata fi dadi ma da su"

"To Alhamdulillah" ya jinjina kai "Allah ya kaimu jibin"

Bayan fitarsa kuma sai ga Anti Bebi ta shigo falon. Tayi wanka abinta ta shirya cikin rantsatsiyyar atamfa riga da zani sai mayafin ta data yafa kato wanda ya rufe mata dukka jikinta kuma ya dace da kalar atamfar tata.

"Yusrah tayi wanka?" Ta tambaya bayan ta zauna akan kujera tana sanya agogonta.

Fareeha ta mike "Barin duba"

"In batayi ba kice maza ta tashi tayi. Ina so ku min rakiya zuwa unguwa"

"Toh" ta amsa tana nufan hanyan corridor din.

A hankali ta tura kofar dakin da suke kwana duka su ukun. Tun tafiyar Anti Mami kuma Fareeha bata kara karambanin zama a dakin Samha ba dukda kuwa ba ita ta hanata ba. Dukda yawancin lokutan da take zuwa gidan ma Samhar tana makaranta amma sam sai taji kawai ta fi so tana kwana da su Yusrahn.

A zaune ta sameta tana shafa mai tana tayi wa Fadila surutu wacce ke ta danne danne a wayarta. Shigarta SS3 Bappah ya siya mata ita.

"Mama tace wai ki shirya zamu rakata unguwa"

Nan da nan ta fara murna. "Haba de? Ina zamu je?"

Drawer din da take ajjiye 'yan kyayyakinta a gidan ta nufa "Nima ban saniba". Wani hijabi ta jawo light blue ta saka sannan ta fita tana jiran Yusrahn.

Minti biyar sai ga Yusrah ta fito sanye da bakar Abaya mai manyan fulawowi wanda aka kayata su da duwatsu masu kyau.

Mama ta tsaya ta kalli shigar Yusrahn da kuma ta Fareehan sannan ta jinjina kanta.

"Yusrah dauko hijabi" ta fada a takaice.

"Mamaaa" Yusrah ta dakuna fuska "Abaya da hijabi kuma?"

"To ki canja kayan sai kisa wanda ake sakawa da Hijabi ko?"

Ranta bai so ba haka ta juya ta koma dakin. Mama kuma ta kudurta sabunta wa Fareeha kayayyakinta don sam bata ji dadin banbancin data gani a tsakanin Fareeha da Yusrahn ba a yanzun.

Sahad Stores suka fara zuwa inda sukayi dan saye-sayen abubuwan toilet da sabulan wanka masu kamshi, turaruka, shampoo, lotions da dai sauran abubuwan da baza'a rasa ba. Daga nan sai driver ya mikasu sabon gari inda suka yada zango a wani shagon undies.

"Kuna makaranta munzo da Fadila da Samha shi ne nace kuma in kun dawo se muzo a caccanza muku. Musamman ke Yusrah naga vests dinki duk sun dafe "

Yusrah ta sake turbune fuska.

"Bata wankesu da kyau ko?" Ta tambayi Fareeha wanda ta rasa abunda zata ce kawai sai tayi murmushi.

Anti Bebin ta lura da canjin da take gani a tattare da su. Ta ma yi mamaki da sai yanzu don sunkai SS2.

Undies masu kyau ta zaba musu kowa dozen dozen. Sai ta kara musu da rigar bacci kowa daddaya. Ita dai Fareeha kunya dukda mai shagon macece kuma tayi ta musu fara'a amma ita sam bata sake ba.

Daga nan Tarauni sukayi. Mama ta sayi vegetables da kaji sannan suka dawo gida a gajiye.

Sallah suka fara yi kafin sukaci abinci.

"Baba yace in ce muku fa zamuje Azare jibi zamu raka Fareeha" Fadila ta sanar musu a lokacin da suke cin abincin. Ita ta dafa. Shinkafa ce da miya sai salad din datayi me dan karen dadi.

"Dagaske?" Yusrah ta tambaya farin ciki fal fuskarta. Ita kam duk inda akace akwai yawo to tanaso.

Fareeha ta dan tureta. "Ayawo. Har kin fara jin dadi"

Sukayi dariya.

"Kinsan me nake tunowa? Akwai wani lokaci muna yara mun taba zuwa na manta bikin wanene. Ni da Aishan Baba Habiba tsabar yawo ingaya miki bata mukayi. Daga karshe dai wasu mutane muka samu mukace su kaimu fada don mun kasa gane ko ina."

Fareeha ta jinjina kai tana dariya. "Tab. To da yanzu ne kukayi haka wallahi sace ku za ai"

"Sosai ma" Fadila ta jaddada. "Yanzu duniya babu yadda. Kowa neman yanda zai cuci dan uwansa yake"

"Hakane kam. Ina Aishan Baba Habiba take yanzu kam?" Yusrah ta tambaya tana kurban ruwan data debo  a Kofi.

"Tayi aure da dadewa. Tana can Gamawa"

Yusrah ta dafe kirjinta. "Aure? Na shiga uku. Wannan 'yar mitsilar?"

Wata dariyar suka sakeyi. "Dan kin ganta 'yar karama kuma tana biye miki kuna shirme? Babba ce fa. Tayi kusan sa'an Baba Habu kawai de bata da girman jiki ne. Kuma ai kin dade baki ganta ba yanzu kam ta zama babba"

Da dare suna zaune suna kallo a falon Mama dukansu hadda Amina sai ga Ya Ashraf yayi sallama ya shigo. Nan take Fareeha taji faduwar gaba ta saukar mata. Turaren shi ya mamaye falon a yayinda ya samu waje ya zauna tare da mika ledar hannunshi wa Yusrah.

"Fruits ne ki wanke ki kawo mana"

Ta karba ta wuce kitchen da shi. Sake lumewa yayi cikin kujeran ya dora kafarsa daya akan daya sannan ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa.

Har Yusrah ta fito a kitchen din da tray din data sanya fruits din a ciki Fareeha ta gagara numfashi me kyau.

"Ku sauko muci" cewar Yusrah.

Apples ne da pears sai tangerine da kuma sweet melon. Duk ta yanka ta jejjera a tray din gwanin sha'awa.

Sukayi Da'ira a gaban tray din kowa yana daukar abunda ransa yakeso. Ita dai Fareeha tana can gefe tunda ta dauki slice din apple kwaya daya take ta gutsirarshi a hankali a hankali. Da kyar ma yake wucewa ta makogoranta.

Tafiyar tasu ta kama ranar lahadi. Tun a daren asabar ta shirya 'yan komatsanta. Mama ta bata sabulai da turaruka masu sanyin kamshi ta kaiwa Ummanta sai wasu dan kunne guda biyu masu kyau wa Inaayah da Qulsoom. Ranta fari kal ta kwanta tana jirar wayewar gari.

Tun kafin a kira sallah ma ita ta tashi. Sai da tayi wanka tukunna tayi sallah sai ta tashi Yusrah da Fadila suma sukayi wankan. A gurguje sukayi  breakfast indomie da shayi kowa ya hahharba saboda gidajen dazasuyi ziyara a Azaren dayawa kuma a yau din sukeso su dawo.

Karfe bakwai duk sun shirya abunsu suna falon Mama inda suke jiran Bappah ya fito ya sallamesu. Yusrah ce ta tayata jan akwatinta zuwa mota. Direban shima har yazo yana dan goge motar dukda mai gadi ya wanketa jiya da yamma.

Suna tsaye sai gashi ya taho ta hanyar da zata sadaka da boys quarters din. Yana cikin wata rantsatsiyyar shadda sky blue wanda ta kara fito da kyawunshi. Dama can kallon tsoro Fareeha take mishi don kusan duk lokacin da zasu hadu tazarar dake tsakaninsu babu yawa shiyasa ma bata iya daga idonta ta kalleshi. To amma yau da ta hango shi daga nesa sai ta kasa dauke idonta a kanshi. Sai taga kamar shi da Bappah ta kara fitowa. Kawai de shi yayi tsawon kafa dayawa ne har ma ya wuce Bappahn tsawo. Amma daga hasken fatar zuwa cikar fuskarshi da idanuwansa  zuwa sajenshi wanda ya kwanta luf a gefen fuskarshi, kana ganinshi kasan jinin Bappah Dattijo ne.

Cufflinks dinshi ya ke kokarin sakawa ga kuma hularsa daya makale a kasan hannunsa. 

Har ya iso gab dasu bata dena kallonsa ba sai da taji Yusrah ta gaishe shi sannan ta farga daga shagalar datayi.

Da sauri ta sauke idanunta a kanshi sannan itama ta gaisheshi. Ya amsa a takaice hadi da mikawa Yusrah cufflinks din nashi ta tayashi sakawa.

Murmushi ya mata bayan ta saka mishi sannan ya kafa hularsa a kansa. A daidai lokacin kuma Bappah ya fito daga gidan tare da Mama da Fadila. Suka gaisa.

Ya bada kudin mai da kuma kudin da za a sayi dan abunda za a kai wa 'yan uwa. Mama ta musu addu'ar Allah ya kiyaye.

Yusrah suka saka a tsakiya shi kuma ya zauna a gaba shi da direba.

Hira suke sama-sama akan gidajen dazasu je idan sun isa Azaren yayinda Fadila take musu list din wajajen da suka fi muhimmanci.

Har suka isa Fareeha bata furta kalmomi sama da goma ba. Duk tabi ta takure.

Gidansu aka fara sauketa, suka samu Umma ta shirya musu abin karin kumallo. Soyayyar doya da farfesun zabi. Sai kunun tsamiya mai shegen dadi. Haka suka zauna suka lashe tas.

Fareeha ta lura cewa bataga Inaayah da Qulsoom ba lokacin da suka shiga amma sai bata tambayi Umman ba saboda tana ta hidima da su Yusrahn. Sai da suka gama ta tattara kwanukan sai ta musu rakiya zuwa bakin mota.

Da Ashraf yaga kowa ya shiga ita ta tsaya sai ya leko da window. "Ba dake zamu tafi bane?"

Wani abu ne taji ya hau tsalle a cikin kirjinta a lokacin da tayi kokarin daidaita numfashinta. A iya 'yan kwanakin nan data sanshi in banda gaisuwa babu abunda ya taba hadata dashi. Zata iya rantsewa ma tace ya manta cewar da ita suka taho in ba dan ya ganta ba da suka iso don tun da aka fara tafiyar ko uffan bai ce mata ba. Idan hirar ta koma tsakaninta da Yusrah ko Fadila shiru kawai yakeyi.

"A'a" ta samu kanta da fadi.

"To wa zai rakamu duk sauran gidajen?"

Murmushi ne ya kwace mata wanda bata san daga inda ya taho ba. "Ai Malam duk ya sani. Shi ba bakon garin bane" ta fada tana nuni da direban.

Jinjina kai kawai yayi ya koma ya zauna. Su Yusrah suna daga mata hannu motar ta fice a layin nasu.

Kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ta tako daga kofar gida zuwa ciki.

"Umma naji gidan shiru ina su Qulsoom?" ta tambayeta a lokacin da ta tsaya a kofar kitchen din nasu.

Umma ta danyi murmushi tana kwashe sauran kunun data dama daga roba. "Mijin Mami ne dai bashida lafiya shine sukaje dubashi shi"

Gabanta taji ya fadi. "Me ya sameshi?"

Umma ta dago ta kalleta jin yadda hankalinta ya tashi. "Ba abun daga hankali bane Adda. Appendix aka cire mishi kuma jikin ma da sauki"

A hankali ta sauke ajiyar zuciya. "To Allah ya bashi lafiya. Yaushe zasu dawo?"

"Ameen. Abba yaje ya taho dasu. Tun ran Juma'ah suka tafi"

"Ya Bilal fa?" ta tambaya a hankali

Tun bayan dawowarshi daga rehab Abba ya yanke shawarar cewa ya bar garin tunda duk abokan shaye-shayen sa a unguwar suke kuma yana tsoron kar su maida shi cikin ruwa. Don haka aka samo mishi gurbi a makarantar Informatics dake kazaure. Idan anyi hutu kwana biyu kawai yake zuwa yayi a Azare sai ya koma can Hadejia wajen Baba Zubairu. Sai ya zama gonar Abban dake can yana zuwa yana taya Baba Zubairun kula da ita. Duk yadda Umma taso ta ganshi a kusa da ita amma haka ta hakura ta bawa zuciyarta hakuri cewar hakan shine mafi alkhairi a gareshi.

"Yana can Hadejia. Satin daya wuce yazo"

Kai kawai Fareeha ta jinjina. Rabon da ta saka shi a idonta har ta manta. Yadda makaranta ta boye shi itama haka makarantar ta boye ta.

"Allah sarki" ta furta a hankali.

Daga nan bata sake cewa komai ba. Akwatinta data jingine a tsakar gidan ta ja zuwa ciki. A falon Umman  ta bude shi ta ciccire komai. Ta cire tsarabarsu ta ajiye sannan ta tattare kayanta ta shiga daki ta jerasu a wardrobe wajen kayanta. Nan da nan ta gama unpacking shi kuma akwatin ta dora shi a can Saman wardrobe din.

Da ta dawo kitchen sai ta samu Umma tana jajjage.

"Sannu Umma" kawai tace ta kwashe kayan wanke-wanken da suke tarawa  a wata roba ta fito dasu bakin famfo. Ta koma kitchen din ta dauko robar soda.

"Adda kibari ki huta sai da yamma mana"

"A'a Umma. Ai wanke wanken ba yawa yanzu zan gama"

A haka suka gama aikin nasu gidan tsit kaman babu kowa.

Ta idar da sallar azahar kenan ta dan kwanta don bacci ne a idonta tunda bata samu tayi da safe ba.

A hankali Umma ta turo kofar tare da yin sallama. Idonta a rufe ta amsa mata tare da kara dukunkunewa a cikin hijabinta.

"Adda" taji Umman ta kirata a hankali.

Mirginowa tayi daga kan sallayan ta juyo suka hada ido. Sai taga hawaye a idon nata.

Take ta mike zaune. "Umma menene? Meya faru?"

Umman ta bude bakinta kaman zatayi magana kuma sai wani kukan ya kara tahowa ya toshe mata makoshi. Ta rufe idonta wanda ya bawa hawayen nata daman gangarowa kan kuncinta tana kankame wayarta da ke hannunta wanda a dalilinta labari mummuna ya risketa.

Tasha ganin Umman tana kuka kuma akoda yaushe tana shiga tashin hankali idan taga hakan. Ta dauka kukan ta ya kare sanda Abbansu ya samu lafiya Bilal kuma ya tafi rehab. Ashe da saura. Meke shirin faruwa?

Da rarrafe ta karasa wajenta ta dafa gwiwowinta tana duban ta. Ita ma kuka  take shirin yi.

"Ki tashi ki shirya muje jama'are. Allah yayiwa Mukhtar rasuwa"

Wata faduwar gaba da ta dade ba ta ji ta ba ne ta jijjigata.

Innalillahi wa inna ilaihi raajiun kawai ta furta kafin ta kifa kanta akan cinyar Umman a yayinda zafafan hawaye suka sulalo mata.

**********

Lokacin da Misriyya ta kirashi cewar tana kofar gidanshi bai yadda ba sai da yanzun ya ganta a tsaye sanye da coat dinta ja wadda ta kai mata har gwiwa. Bakin wando ne a jikinta (skinny jeans) da bakaken boots. Ta nannade kanta da wani bakin dankwali.

Sosai tai masa kyau musamman lokacinda suka hada ido ta sakar mishi murmushi. Jambakin dake lebbanta ya kara haskaka fararen hakoranta.

"Are you being serious right now?" Ya tambayeta a yayinda ya karaso inda take. Daga mishi kafadu tayi alamun dagasken take.

Sanyi ake zabgawa na ban mamaki domin numfashinsu har fitar da hayaki yake. Shi kanshi karkarwa yake saboda daga shi sai wata 'yar sweater ya fito. Kayan bacci ne a jikinshi don har yayi shirin baccin ma sai kawai yaga sakon nata.

Ta dunkule hannayenta wanda suke cikin gloves a gaban kirjinta. "Kai fa kace inde nazo zaka rakani" ta dan tabe baki alamun shagwaba.

Ya girgiza kai a lokacin da yaji zuciyarshi tayi tsalle.

Bai fi awa daya da suka gama waya ba ta ke sanar mishi cewa hasashen yanayi ya nuna cewa a yau ne kankara zata fara sauka a garin (first snow fall) na wannan shekarar. Ta nuna mishi cewa tana son taje Manhattan Bridge saboda taji labarin yanda yanayin yake idan kankara tana sauka saboda yadda aka kayata gurin da kyale kyale na shirin bikin kirismeti da sabuwar shekara. Ya fada mata cewa fita ita kadai cikin dare kuma a wannan yanayin ba abu ne me yiwuwa ba ne.

"To kazo ka rakani" ta fada tana dariya.

Shima dariyar yake lokacin da yace "In de kika biyo ta nan to zan rakaki"

A zatonsa ta fahimci cewa wasa yake da ya fadi hakan don bai yi tunanin zata baro inda take ta sake lulukowa unguwarsu ba a wannan daren. Amma kuma ashe ita dagaske take.

Ya sake girgiza kai yana kare mata kallo. Tunda yake bai taba haduwa da mace kamar Misriyyah ba. A da yana kwatanta ta da Najmah amma sai ya fahimci cewar ko kusa basuyi kama ba.

Misriyyah mutum ce wanda bature zai yi mata lakani da fearless. Bata da tsoro. Kuma a kowani hali ta tsinci kanta bata karaya. Tana da jajircewa da kuma dagewa. Sannan tana son yin abubuwa da dama har ma wadanda suke da hatsari.

A iya alakarsu kawai da bata wuce shekara daya ba yasan ta dirgo daga jirgi (sky diving), ta shiga ruwan da akwai sharks a ciki, ta shiga can kasan ruwa domin ganin halittun ciki (scuba diving), ta shiga kogo (caves) iri iri a kasashe daban daban, ta hau tsaunika kuma ta shiga jeji, ta ga abun da zata gani a duniya wanda bata gani ba kuma tana fata ta gani. Don haka zai iya cewa ma bai taba haduwa da mace irin ta ba.

Sai dai duk rashin jin tsoronta da jajircewarta da kaifin tunaninta ya kasa barinta ta fada mishi kalmar datake son fada mishi a duk lokacin da suke tare.

A cikin idonata yake ganin kaunar da take mishi tana yawo. A tausasan kalamanta kuma yana jin son da take mishi.

Shi kanshi yasan yana ji da ita sosai, sai dai baya tunanin ko ya shirya bude mata rayuwarsa don ta shigo cikin ta a matsayin abokiyar zama. Baya tunanin ya kai wannan bigiren a yanzu. A kullum yayi tunanin bude wa Misriyyah zuciyarshi sai yaga kamar yaci amanar Najmah ne.

Sanyin da ya ji ya fara ratsa kashinsa ne ya fargar da shi daga tunanin daya fada.

"Barin saka kayan sanyi in fito" ya fada kafin ya juya da sauri ya shige gidan nashi.

Har yafito cikin jeans da bakar coat da kuma hular sanyi tana tsaye a wajen tana jiranshi.

Suka fara takawa a hankali har sukaje karshen layin kafin nan suka sami taxi suka shiga.

Dayake gidan nashi babu nisa sosai da Brooklyn Bridge Park, nan da nan suka isa. Sun samu jama'a da dama a wajen don da alamu ba Misriyyah bace kawai ke da sha'awar ganin first snowfall din.

Daga inda suka tsaya suna hango Manhattan Bridge din wanda aka kayata shi da hasken lantarki iri daban daban. Ta mika mishi camera dinta tace ya mata hoto. Hakan kuwa akayi.

"Gaskiya baka iya hoto ba. Meye haka?" Ta fada a yayinda ta dudduba hotunan da yayi mata.

Ya sosa sajenshi yana dan murmushi. "A koya min to"

Ta dan juya idonta tace shima yaje ya tsaya a inda ta tsaya a dazun. Ta fara daukan hotunan kenan sai ga snow ya fara saukowa. Wata dariya me cike da annashuwa ta saki tana kallon sararin samaniya. Ran ta fari kal a lokacin.

Shi kuma ita yake kallo.

Abun farin ciki baya mata wuya. Kuma ba ta iya boye farin cikinta a duk inda take.

Jujjuyawa take ta bude hannuwanta tana jin saukar kankarar a fuskarta. Abubuwa da dama suna sakata nishadi amma wannan yana daya daga cikin wanda suka fi saka ta farin ciki.

Ta tsagaita hajijiyar da take ta juya don ta kalli Muazzam sai taga shima kallon ta yake. Kallon da aka dade ba a mata irin shi ba. Kallo me cike da sakonni iri daban-daban.

Bata san ya akayi ba, batasan lokacin da kafafunta suka dauketa daga inda take tsaye ba, bata san me ya shige kanta ba, kawai gani tayi ta shige jikinshi, tana mishi rikon da bata taba yi wa kowa ba.

****

Ghen ghen.....

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top