12.

I just want to say a big thank you to all of you who've been following this story despite how inconsistent I am. I really appreciate you guys. Thank you so much Allah ya saka da alkhairi Ameen. Sannan kuma ku sakani a addu'arku Allah ya sa na rinka updating regularly Ameen😅.

"I met someone" fadin Mu'azzam kenan bayan sun fara session din nasu na ranar shi da Doctor Brown.

Ta kalleshi cikin mamaki. Hakan ya saka shi murmushi. Cikin harshen turanci yace "Nasani Doc. Ni ma ban taba tsammanin hakan zai faru da ni da  wuri ba."

"An samu cigaba kenan" cewar Doctor Brown. Ta danyi rubutu a wata takarda tana murmushi. "Bani labari. A ina kuka hadu? Kuma a wani mataki alakar ku take?"

Ya sake nutsewa cikin lallausar kujerar da ke opishin Doctor Brown din. Zuwan nashi jefi-jefi ne. Wasu lokutan ma sai sakatariyarta ta tura mishi sako don ta tuna mishi da appointment din nashi. Wani lokacin yaje wani lokacin kuma yayi harkokin gabansa. To yanayin da ya samu kansa a watanni uku da suka wuce ya sa shi fara zuwa wajenta akai-akai.

Itama Doctor Brown din ta lura da canjin data gani a tattare da shi kawai dai batayi magana bane tafiso ta ji daga gareshi. Gashi kuma yanzu ya fada mata da bakinshi.

Idonshi ya yawata a opishin nata madaidaici wanda ta kayata shi da litattafai da kuma furanni masu sanyin kamshi. Ya fara bata labarin yanda Misriyya ta nemo lambar wayarsa a wajen Aishan Mujahid da yanda ba zato ba tsammani ta zame masa abokiyar hira.

Ta yi wa rayuwarsa shigan bazata. Don ko kadan bai saka ran zai sake ganinta ko ma yin magana da ita ba.

Sai ga shi duk lokacin da zai samu wani dan sarari zaka ganshi makale da waya.

"It feels like Najmah all over again" ya furta a hankali.

Yana lura da kallon da Amma take mishi kwana biyu. Tana so ta san me yake ciki. Tun da yake da ita kuma bai taba boye mata wani lamari game da shi ba sai wannan. Ya rasa meyasa ya kasa sanar da ita dukda yana ganin alamar kamar ta gane a idonta.

Fadawa Doctor Brown din ne yasa yaji kamar an rage mishi wani nauyi a kirjinshi. Kamar yana rike wani sirrin da yanzu ya samu damar furtawa.

"Hakan ya maka?"  Muryar Dr. Brown ta kutsa cikin kanshi.

Ya danyi shiru yana nazari kafin ya gyada kanshi a hankali.

"Kana hira da ita ne don kana sakata a gurbin Najmah ko kuma akwai wasu abubuwa a tattare da ita dayasa kake tare da ita wanda sam basu da alaka da Najmar?"

Ya dan yi shiru. "Bansaniba nima. Kawai tana saka ni dariya kuma tana sa na manta da dukkan wata damuwa ta. And she cares about me a lot" ya karashe yana tuno lokacin da ta tafi hutu Nigeria na tsawon sati biyu. Haka zata saka alarm ya tasheta karfe ukun dare wanda yayi daidai da karfe tara na dare agogon New York don tasan a lokacin ya dawo gida. A wannan lokacin tukin jirgin dayake na safe zuwa rana ne. Daga bakwai tayi to ya tashi amma kafin ya iso gida ya kikkimtsa yayi sallolinsa har taran tayi. Tunda ya sanar mata hakan kuwa sau daya shikenan koyaushe kamar agogo tara tanayi zai ga kiranta ya shigo. A lokacin yayi wanka yaci abinci har ya saka kayan bacci. Wasu lokutan yana makale da waya zaiyi bacci. Ita kuma sai ta tashi tayi sallar asuba.

Da ta dawo daga hutun nata haka ta ciko mishi jaka da kayan marmari irinsu kilishi, dambu, aya mai siga, gullisuwa da alawar madara.

Abun yayi masa dadi matuka don ko Amma dataje kwanakin baya in banda kilishi babu abun da ta kawo mishi wanda yake marmar. Haka yayi ta sanyawa Misriyyah albarka. Kuma a lokacin yaji zuciyarshi ta sanyaya da lamuranta.

"Ya maganar mu kuma ta keeping journal? Ka fara?" Doctor Brown ta tambaya tana katse mishi tunani.

A lokacin da ya fara zuwa wajenta farkon rasuwar Najmah, shawarar data bashi kenan.

"Duk abunda kakeji, duk wani yanayin da yazo maka da dacin da kakeji a ranka, da duk sauran abun da bazaka iya fada ba ka rubuta shi a wani waje ka ajiye. Zai rage maka radadin da kakeji na tabbatar maka da hakan. Dalilin dayasa kuma nace ka ajiye shi shine watarana zakazo ka karanta sai ka gane cewa you have come a long way after overcoming your grief. Zaka ji sanyi a ranka"

Yana tuna lokacin da ta furta mishi wadannan kalaman. Sau daya, a wata paper ya rubuta wasu kalmomi da basu da wata ma'ana domin yana kuka yayi rubutun. Ya ji sassauci a ranshi kam ba tantama, amma bai kara kokarin yin hakan ba.

Ya dan langwabar da kanshi yana kallonta da dan siririn murmushi a fuskarshi. "Na dauka mun wuce wannan matakin yanzu"

Ta girgiza mishi kai itama da nata murmushin. "Da sauranmu. Ina so ka fara ko sau daya a sati ne. Zuwa sau biyu, har ya zama kullum sai kayi"

Ya sosa sajensa yana harde kafafuwansa. "I'll try"

"Please do" ta fada tana cigaba da rubuce-rubucenta a file dinsa.

●●●

Dawowarsu kenan daga sallar azahar inda suka wuce dining hall domin cin abincin rana. Dayake yau din asabar ne Jollof rice aka musu da soyayyan nama kowa yanka daddaya.

Kowani table yana kunshe da mutum goma, a cikinsu kuma aka wakilta mutum biyu Table captain da kuma assistant dinta. Su ne suke da alhakin raba abinci wa 'yan teburinsu. Sannan idan kammala su wakilta mutum daya wanda zai tattare plates din ya kaisu wajen da ake wankewa.

Bakajin komai a dining din sai hayaniyarsu da kuma karar cokula suna kwaramniya da plates.

Wata 'yar SS2 wacce aka fi sani da Senior Hafsat Sharada wacce kuma ke rike da mukamin Labour Prefect ce ta taso tazo table din da Fariha take tace "Wacece Hauwa'u Abubakar?"

Fareeha ta dago ta kalleta da manyan idanuwanta. "Ni ce" ta fada a takaice.

Senior Hasfsat ta juya ta kalleta tare da hada girar dama da kasa sannan tace "Idan an gama cin abinci ki tsaya"

Bata yi mamakin jin hakan daga gareta ba dan ta san za'a rina.

Yau da safe da aka tashi General cleaning Room Captain ta basu aikin wanke laundry su hudu 'yan dakinsu. Ta dauki bokitin ta da tsintsiya ta wuce wajen Duty Prefect ta karbo omon da zasu wanke laundry din dashi.

Tana karasawa ta sami sauran ukun suna jiranta.Su duka ukun juniors din Fareeha ne. Ta ce su biyu su wanke se ita da dayar su dauraye su share. Hakan zefi musu sauri. Su ka yarda da hakan kuwa.

An fara aiki tiryan-tiryan kawai se daya daga cikinsu ta fara wanke uniform dinta bayan basu gama aikin ba.

Fareeha ta mata magana akan ta bari a gama sannan ta yi wankinta amma sai tayi kamar bata ji ta ba. Hakan ya bata mata rai don yarinyar da kadan tafi Qulsoom, kuma tana ganin Qulsoom bazata mata irin wannan abun da aka mata yanzun ba.

Bata sake cewa komai ba suka gama ita da sauran. Suna fitowa ta wuce wajen Matron ta kai karar yarinyar wanda har a lokacin wankin uniform din nata take. Aikuwa Matron din tana zuwa ta sameta ta dauke bucket din gaba daya da kayan wankin a ciki ta cilla su waje.

Fareeha batayi tsammanin abun da ze faru ba kenan. Ita dai ta kai kararta ne saboda a mata fada don tasan abinda tayi ba daidai bane. Lokacin yin duty ba lokacin yin wanki bane. Kuma ma suna wankewa tana kara bata musu da ruwan dattin wankinta.

Yarinyar sam bata ji dadi ba. Don kayan duk sun turbune a cikin kasa. Har kuka sai da tayi. Fareeha ta so bata hakuri amma sai ta kasa. Tunaninta ma kar a garin bata hakuri ta mata rashin kunya. Ita kuma abunda bata so kenan.

Abunka da makaranta 'yar karama kafin kace me labari ya karade makarantar akan abun da Matron tayi wa wata student. Dama yara tsoronta suke saboda tana da zafi sosai. Don wannan aika-aikar data yi bai bawa wasu mamaki ba.

Labari yazo wa Fareeha cewa Yayar yarinyar prefect ce a SS2 kuma tace sai ta (abun da malam ya hana fada).

Ko kadan bataji tsoro ko wani abu ba a ranta. Yarinya ce tayi laifi kuma ta kai kararta kuma an hukuntata dukda ba wannan hukuncin tayi tunanin za'a mata ba. To ita meye laifinta a nan?

Ta gama cin abincinta ta jira a kada kararrawar tashi a dining. Kafin ma a kada wasu 'yan SS2 sukazo suka tasa keyarta zuwa bayan dining din.

Senior Nafisa ita ce Head Girl din da aka nada sati uku da suka wuce a lokacinda aka karbe ragamar makarantar a hannun 'yan SS3 saboda a basu damar nutsuwa domin shirin zana jarabawarsu ta karshe (WAEC and NECO).

Tana zaune a kan dan dandamalin bayan ginin, sai wasu kawayenta guda biyu wanda su ba prefects bane sannan ita Senior Hafsat Sharada da dazu tazo ta kira Fareeha a dining. Bokitan ruwa guda biyu ne a gabansu.

"Reduce your height" suka ce mata nufin baze yiwu suna zaune ita kuma tana tsaye a kansu ba. Tsugunnawa tayi ba yanda ta iya.

"Who do you think you are?" Senior Hafsat ta watso mata tambayar.

Shiru ta musu don bata san ma wace amsa zata basu ba.

"Har kin isa ki sa a watsar wa kanwata da kayanta? Akan wani dalili? Me kike takama da shi?"

"Apologize" wata a cikin kawayen ta fada.

Fareeha taji wani abu ya makale mata a makogoro. Ta bada hakuri? Akan me? Ita me tayi?

"Au bazaki bada hakuri ba ko? Saboda kin ga kin kamo ni tsawo ko? To wallahi sai kinyi birgima a kasa kema. Yadda uniform dinta ya caccabe kema naki se ya cabe"

Tana gama fadan hakan sauran seniors din guda biyu suka fara zazzaga ruwan bokitin a kasar da ke wajen. Kan ta ce wani abu itama sun fara yayyafa mata ruwa a jikinta. Wasu hawaye ne taji sun taru a idonta lokacin da ta gano abun da zasuyi mata amma tayi saurin mai da su.

Bazata yi kuka a gabansu ba. Bazata bari su ji cewa sun ci galaba a kanta ba. Suyi duk abun da zasu mata amma bazata bada hakuri ba. In sunga dama su kasheta.

Ita kanta bata san daga ina wadannan tunane-tunanen suke zuwa mata ba. Amma kamar bacin ran data shiga ne duk ya jawo.

Ba suyi aune ba sai ga wasu jerin 'yan ajinsu Fareehan sun zo wajen a guje.

"Hauwa Abubakar." Suka kwala mata kira "Kizo Vice Principal tana nemanki. An zo miki"

An zo mata?

Wani sanyi taji ya mamaye gurbin dacin da taji a dazu. Waye ya zo mata? Wanene yazo cetonta?

Sai a lokacin Senior Nafisa tayi magana. "In kunsan karya kuke to ranku zai baci"

Da sauri sukace "Wallahi ba karya muke ba. Mun gansu. Babanta ne da yayanta"

Zuciyar ta taji ta doka mata. Yaya Bilal ne da Babanta sukazo?

"Muje mugani" cewar Senior Nafisa. Su dukansu suka dunguma zuwa reception. Yadda sukayi ayari zaka zaci duk sunsan wanda aka zo wa. Ga Senior Nafisa da tawagar ta ga kuma 'yan ajinsu Fareeha.

Tun kafin su karasa ma ta ke hango su su biyu a zaune a kan waiting chairs.

Babu tantama Abbanta ne. Ta gane shi da hularsa baka dayake yawan sakawa.
Wanda ta gani a gefensa ne ya saka ta ta kasa karasawa daf dasu.

Ya Bilal.

Ya rame. Amma cikin ikon Allah ramar ta masa kyau. Ga wani hasken shi da ya kara fitowa. Dama can kalarsu daya da Fareeha sai da rashin wanka da cakwakwiyar dauda duk tasa ya zama wani iri.

Yanzu kam ya fito asalin hallitarsa. Gashi ya sha aski da gyaran fuska. Yana sanye da kananun kaya. Sai idon shi daya makale da bakin gilashi.

Idan bazatayi karya ba sai tace Seniors din dake bayanta sun sauke ajiyar zuciya. Amma yanzu ba su bane damuwarta a halin yanzu.

Kafafunta sun mata nauyi, amma a haka ta jasu zuwa wajen mahaifin nata da dan uwanta da ta shafe kusan watanni takwas bata saka shi a idonta ba. Wata kewarshi da bata taba tunanin zata yi ba taji ta lullubeta.

"Adda" ya kira sunanta a hankali hade da sakar mata murmushi.

Sai taji wasu hawaye sun zubo mata.

Abba ne ya tashi ya rikota jikinshi.

"Lallai zanyi vedio na turawa su Inayaah. Har yanzu baki dena kuka ba Senior Adda?"

Fadin 'Senior' din dayayi ya sakata yin dariya.

"Abba sannunku da zuwa. Ina wuni?" ta tsinci kanta da fadi. Kafin ya amsa kuma duk sauran 'yan ayarin suma suka dunguma.

'Ina wuni' daga sama har kasa suka fara jero masa. Sai amsawa yake yana tambayarsu ya makaranta.

Sai da suka gama kwasan gaisuwa sannna suka jujjuya suka koma.

Abba ya dafa kafadarta. "Mamana kukan nan ya isa haka kinji?"

Ta gyada kai tana share hawaye da gefen hijabinta, amma hawayen sun ki tsayawa.

Komai taji ya dawo mata a lokacin. Kewar 'yan gidansu, kewar yayanta da batasan zata taba yi ba, cin zarafin da aka kusa mata-duk suka hadu waje daya suka shaqe mata makogoro. Kukan ne kawai da ta keyi yake sanyaya mata zuciya.

"Wannan din duk hawayen ne ko me?" Ya tambaya yana dudduba hijabinta dayaga ya jike da ruwan da dazu aka yayyafa mata.

Da girgiza mishi kai.

Ya dan bubbuga bayanta. "Ya isa to"

Suka zauna suka sakata a tsakiya.

Ta juya ta kalli Bilal a gefenta. "Ya Bilal yaushe ka dawo?"

Ya yi murmushi. "Adda ba gaisuwa?"

Ta langabar da kanta ita ma tana nata murmushin. "Yaya ina wuni? Kun zo lafiya?"

"Lafiya Senior Adda" ya fada yana dan tureta.

Suka fashe da dariya.

Yaushe rabonda suyi wasa da dariya haka ita da Ya Bilal? Shin a tunaninta ma wannan ranar zatazo? Maza biyu da sukafi kowa muhimmanci a rayuwarta, sun zagayeta, sun sakata murmushi, sun yaye mata damuwa na dan wani lokaci.

Idan batayi wa Allah godiya ba, wa zatayi wa ?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top