11.
"Good Afternoon passengers. This is your Captain speaking. I'd like to welcome you all on board United Airlines flight UA300 from New York to Chicago, Illinois. We are currently cruising at an altitude of 33,000 feet at an airspeed of 540 miles per hour. The time is 1:25pm. The weather looks good and with the tailwind on our side, we are expecting to land in Chicago O'Hare international airport approximately fifteen minutes ahead of schedule. The weather in Chicago is clear and sunny, with a high of 25 degrees for this afternoon.
If the weather cooperates we should get a great view of the city as we descend. The cabin crew will be coming around in about twenty minutes time to offer you a light snack and beverage, and the inflight movie will begin shortly after that. I'll talk to you again before we reach our destination. Until then, sit back, relax and enjoy the rest of the flight. Once again my name is Captain Mu'azzam Kabir and it's a pleasure to have you all flying with us"
Kamar kullum Muazzam ya gama jawabinsa kafin ya juya ya kalli abokin aikin nasa wato co-pilot dinsa suka cigaba da hirar da suka fara kafin tashin jirgi.
Haka suka cigaba dayi suna kuma musayar muhimman rahotanni da Air Traffic Control.
Muazzam zai iya cewa ba abunda yake bashi nishadi a wannan aikin nasa illa yaga yanda jirgin daya ke tukawa yana kutsawa cikin gajimare cikin sauki.
Abu na biyu daya ke saka shi nishadi shine duk lokacin da yake tukin yamma, yana son ganin yanda rana take faduwa.
Lokacin yana yaro yana tunani idan ya hau can sama zai hango inda rana take zuwa ta buya idan ta fadi, sai gashi yanzu yana kololuwar sama amma yana gani zata fadi kuma bai san ina ta buyan ba. Ikon Allah kenan.
Isarsu Chicago O'Hare international airport suka fara shirye-shiryen dawowa New York din da wasu fasinjoji daga Chicagon.
Yadda yayi announcement din nashi daga zuwansu New York haka kuwa ya kara yi ma anan din. Sai dai bayan sun sauka ne wata Flight Attendant tazo tace mishi ana son ganinshi.
"Wasu 'yan Nigeria ne" ta fada cikin harshen turanci. "Sun ji sunanka shine sukeso su ganka"
Ya saba da hakan. Ba sau daya ba ba sau biyu ba ana zuwa domin a ganshi. Dama shi dan Najeriya duk inda yaga ko yaji dan uwansa sai yaso an hadu an kulla zumunci musamman in ana kasar da babu 'yan Najeriyar dayawa.
Bugu da Kari kuma ba'a cika samun 'yan Najeriya masu taking jirgi ba da suke jan manyan jiragen kasar. Shi ne dalilin dayasa yawancin mutane sukeson su ganshi wasu lokutan ma har suyi hotuna.
Da murmushi a fuskarshi ya fito a cockpit din.
Su biyu ne a tsaye amma yana ganinta ya ganeta. Ita ma kallon sani ta mishi.
"We've met before" ta fada tana murmushi.
Ya jinjina mata kai. Dayar ta juya ta kalleta sannan ta kalli Muazzam din.
"Kunsan juna?"
"I saw him a gidan Aisha Bashir, lokacin party din Sister-in-law dinta" ta yi mata bayani. Sai kuma ta juya kan Muazzam din. "Sunana Misriyya"
Ya jinjina mata kai "Muazzam Kabir"
"Captain Muazzam Kabir" ta gyara mishi. Hakan ya sa su duka dariya. "Wannan yayata ce Rahma"
"We are so proud of you" Rahma ta fada da murmushi a fuskarta "Shekarata hudu kenan a America amma ban taba cin karo da pilot dan Nigeria ba dayake aiki wa american airline ba sai kai."
Ya dan jingina yana saka hannayensa cikin aljihun bakin wandon uniform dinsa wanda ya masa masifar kyau.
"Thank you. Amma ta ya akai kikasan ni dan Nigeria ne?"
"Ni ma ce mata nayi maybe dan India ne because of the Kabir amma bata samu nutsuwa ba sai da ta tambayi Flight Attendant din" Misriyyah ta sanar mishi.
Ya jinjina kai. "Lallai a gaisheki"
Kamar sauran 'fans' dinshi suma sun bukaci suyi hoto da shi. Bayan sun yi hoton kuma su ka nemi lambar wayarsa. Cikin mutuntawa ya nuna musu cewa ba zai iya basu ba amma zasu iya nemanshi a Facebook.
Haka suka rabu kowannensu da murmushi a fuskarsa.
Sai da sukayi handing over jirgin wa sabon crew din dasu ne zasuyi aikin dare sannan kowa ya kama hanyar gida.
A cikin taxi din ya samu sakon Ammi tana tambayar ko ya tashi a aiki. Ya mata amsa da ya na hanyar gida.
'Su Mamma sunzo. Can we meet up at their place?'
Sai da ya sake karanta sakon nata sau biyu don ya tabbatar da abunda ya karanta hakan ne. Yaji wani abu ya tokare mishi a makoshi.
Sun gaisa jefi-jefi da Mamma har ma da Na'ima bayan rasuwar Najman, amma bayan wasu lokuta ma sai ya daina daukar wayar tasu domin yanayin da ya samu kanshi a kwanakin bayan. Daga karshe yazo ya canza lamba. Tabbas ya samu emails din Na'iman kusan guda uku amma babu wanda ya mata amsa a ciki don bai san me zece mata ba. Haka ya goge su daga inbox dinsa ba tare da ya mata amsa ba.
Sai a lokacin yake jin bai kyauta musu ba ko kadan. Ba shi kadai ya rasa Najmah ba, su ma sun rasata.
Bai yi musu adalci ba daya watsar da su kaman basu da wani muhimmanci a rayuwarshi. Kaman ba su bane mutanen da suka fi kusanci da abunda yafi so duk duniya. Kaman ba su bane dangin hasken idaniyarsa.
Kanshi ya ji ya mishi nauyi don sai a lokacin ya kara ganin girman laifin daya aikata. Ya yanke shawarar koma meye zai biyo baya, dole ya wanke kansa kuma ya gyara kuskuren da yayi.
Da wannan tunanin ya karasa gida yayi wanka ya sauya kaya kafin nan ya sake fitowa.
Gajiya sosai ya ke ji kuma ba abunda yafi so yayi a lokacin kaman ya kwanta yayi bacci amma zuwa wajensu Mamman shine abu mafi girma a yanzun.
Apartment din nasu yana nan a Upper Manhattan. Nan suke sauka idan sunzo hutu. Kafin rasuwar mahaifinsu Najman, ya na da mukamin Consul General a Consulate General of Nigeria dake New York din.
Ko bayan ya sauka daga mukamin ya cigaba da zama a New York din yana harkokinsa na business. A lokacin ne Muazzam da Najma suka hadu a wani bikin sallah da 'yan kasar Nigeria a New York din suka hada.
A lokacin ta kammala High School kuma har ta samu gurbin karatu a makarantu biyu masu matukar kyau; Princeton University da kuma Columbia University wanda suna cikin manyan manyan makarantun da suke wahalar samu. Kwata-kwata bata hasaso wa kanta yin soyayya har ma ta kai ga aure ba a lokacin. Ita burinta kawai ta cigaba da karatu ta zama abin alfahari a wajen Mammanta da danginsu baki daya.
Kwatsam Mu'azzam ya shigo rayuwarta ba zato ba tsammani.
Wani dinkin doguwar riga aka mata a wannan sallar kuma tsawon rigar ta baya har jan kasa yake. Sai da Mamma tace kar ta saka rigar ta bari se an rage mata amma taki yarda. A haka ne Mu'azzam ya take mata jelar rigar a wajen taro wanda yayi sanadiyyar yin tuntubenta har kuwa takalminta me shegen kyau ya tsinke.
Sai da ya zaunar da ita a kujera mafi kusa da ita sannan ya bata hakuri. Kunya ta bi ta isheta a lokacin. Bata ma tsaya ta kalleshi sosai ba ta ce mishi ba komai.
Ashe ya lura da size din takalminta don haka ya fita a wajen taron ya zagaya unguwar har sai dai ya samu wani shago ya siyo mata wani silifas mai kyau.
Da ya dawo ma a zaune ya same ta a inda ya barta. Mamaki ya bayyana karara a fuskarta a lokacin da ya cire takalman a leda ya jera su a gabanta yanda zata ji saukin sakawa sannan ya dauki wanda suka tsinke din ya saka a ledar daya cire sabbin ya kulle.
Cikin minti biyu yayi ya gama amma abunda bai sani ba shine dan wannan abun da yayi ya samu waje ya cunkushe a zuciyar Najmah kuma ya zauna daram dam!
Maganar da sukayi bayan nan din takaitacciya ce amma bayan sun rabu duk sai taji ta kasa sukuni. Burinta kawai ta sake ganinsa. Ta yi ta tunanin yanda za su sake haduwa, ga New York babban gari ne babu tabbas din hakan zai iya faruwa. Gashi kuma ta kusa tafiya makaranta, zasu kara nisa da juna.
Kawai ta tsinci kanta da nemo lambarsa ta hanyar organizers din taron bikin sallan da sukaje domin ta san daya daga cikinsu. Yawanci idan anyi irin wadannan taron akwai littafi da mutane zasu cike wasu takaitattun bayanai a kansu domin ko da wani abun zai taso a nemo su cikin sauki. A haka aka zakulo mata lambarsa.
Ko bayan ta samu lambar sai da tayi sati biyu a wajenta kafin nan ta samu karfin gwiwar kira.
Bata same shi ba a lokacin saboda yana tsakiyar training dinshi a Washington na neman license din da zai tabbatar da cewa zai iya jan babban jirgi mai fasinjoji. Bai kuwa kirata ba sai bayan kwana uku wanda a lokacin Allah kadai yasan kalan tunanin da ta rinka yi saboda bata ji daga gareshi ba.
A ranar da ya kirata sai ta tsinci kanta cikin nishadi domin ta fahimci cewa shima kanshi cike yake da tunaninta.
"Bazan miki karya ba, I'm so glad you reached out. Babu irin tunanin da banyi ba ta yanda zan nemo ki. Gashi first name dinki kawai nasani"
Zuciyar ta ta cika ta kumbura a dalilin jin maganganun nashi.
Bayan sunyi hira mai tsawo ya sanar mata cewa zai kawo mata ziyara da zaran ya gama abunda ya kaishi DC din.
Abu kamar wasa zumunci mai karfi ya kullu a tsakaninsu dukda cewa sai da suka shafe kusan sati uku kafin suka sake haduwa. Waya ce sukeyi kullum dukda yawanci can cikin dare ne saboda Mu'azzam din bashida lokacin yi da rana a dalilin training din nasa.
A tsawon wannan kwanakin sai yaji yarinyar ta kwanta mishi a rai. Haka kawai yake samun kanshi cikin nishadi idan yayi waya da ita. Duk randa ya kwana ya tashi kuma bai ji daga gareta ba duk sai yaji garin ya mishi ba dadi, ga wani kadaici da yake mamaye zuciyar shi.
A haduwar su ta biyun kuwa bai yi kasa a gwiwa ba ya sanar mata da cewa yana sonta kuma aurenta yake son yi. Bata yi tsammanin abun zaizo da wuri har haka ba amma ta amince mishi. Bayan tafiyarta makaranta ya je ya samu Baban nata don a bashi iznin nema.
"Yanzu Najmah har ta isa aure?" Tambayar da Baban nasu yayi wa Mamma bayan tafiyar Mu'azzam daga gidansu.
Ta dan yi murmushi. "Shekara sha takwas fa Baban Na'ima. Ai bature ma ya bata lasisin tayi duk abun da takeso a wannan shekarun" ta fada tana zama a kusa da shi. "Kuma ni nayi murna da wannan lamari don gaskiya yaron kirki ne"
Ya juyo ya kalleta. "A ina kika sanshi?"
Ta yi 'yar dariya "Nikam tunda naga sun fara waya dare da rana na sa aka yi min bincike a kansa ai."
Baba ya gyara zama yana jinjina kai. "Bani labari"
Ko da Mu'azzam ya isa apartment building din nasu a yanzu, yana tuno lokutan da ya kan zo wajenta hira idan ta dawo hutu daga makaranta. A balcony yawanci suke zama inda take cika shi da labaran abunda suka faru a makaranta dukda yawanci ya sani don tana bashi labari idan suna waya. Ba ya gajiya da kallonta ko jin surutanta, yawanci ma idan yazo hira ita ce zatayi ta mishi surutu, shi dai a barshi da binta da kallo da lallausan murmushi dauke a fuskarsa.
Ba a bata lokaci ba bayan wata takwas aka daura musu aure. A lokacin Mu'azzam ya mallaki license dinshi har ya fara aiki da United Airlines.
Baya tunanin zai kara samun kanshi cikin farin ciki fiye da farin cikin daya tsinci kanshi a ciki a lokacin da akace an daura masa aure da Najmarsa.
Zuciyarshi ta mishi nauyi a lokacin da elevator din ya daukeshi zuwa Penthouse inda nan ne apartment din nasu yake. Ko da ya kwankwasa kofar, sai yaji gudun zuciyar shi ta dan ragu da wata nutsuwa ta saukar mishi da bai san ta inda ta bullo ba.
Addu'o'i ya karanto yana neman taimakon Ubangiji daya agaje shi wajen gyara alakar dayayi sanadiyyar ruguzawa.
********
Visiting dinsu na farko Fareeha ji tayi ta kagu taga 'yan gidansu musamman ma Umman nata.
Tun karfe goma aka bude gate aka fara tururuwar zuwa wa dalibai ziyara. Shiru-shiru har sha biyu ba su ga 'yan gidansu ba. Yusrah dai ta gaji da jira ta karbi wayar maman wata 'yar ajinsu ta buga wa Anti Bebi waya.
"Gamu nan kusa da BUK. Saura kadan mu iso" cewar Anti Bebin bayan sun gaisa.
Su hudu sukazo. Umman Fareeha, Anti Bebi, Fadila da kuma Anti Mami.
Fareeha har da kuka tsabar tayi farin cikin ganinsu. Katon kafet suka shinfida a can bayan classes dinsu suka zauna. Girki kala-kala Anti Bebi ta yi musu ga katuwar Ghana must go datayi musu shopping a ciki. Umma ma ba a barta a baya ba don ta kawo musu yajin tafarnuwa da dambun kazar da ta zauna ta tukeshi da kanta.
Hira suka sha sosai suka ci suka sha suka goge hakora. Bappah Dattijo bai samu damar zuwa ba don yayi wata tafiya zuwa Lagos don haka ta waya suka gaisa da shi. Ya tambayesu ya karatu kuma ya musu addu'ar samun nasara. Sun kira Abban Bilal ma. Shima Addu'ar ya musu.
Yusrah kam ance tayi baki ta rame don sam sai ta kasa sabawa da makarantar. Rawar kan da take da ma yanzu ya dan ragu. Fareeha ce dai ba wani canji sosai sai ma girman da Umman taga ta kara mata. Ta kara zama 'yan mata ga wani kyaunta da ya ke kara fitowa. Gashi sai taga kaman ta kara nutsuwa. Haka tayi ta bin ta da ido har suka zo tafiya.
Sukayi hotuna sosai a wayar Anti Bebi da ta Anti Mami kafin sukayi sallama. Anci sa'a dai Yusrah batayi kuka ba sai dai kana ganin fuskarta kasan bata so tafiyar tasu ba.
A haka suka dauko shopping din nasu niki-niki har hostel. Fareeha ce ta jera mata a locker sauran ta saka a akwati don sai taji bata da karfin yin wani abu don kewar 'yan gidan nasu ta isheta. Ta gama gyara mata akwatin tsab sannan ita ma ta wuce nasu dakin ta jejjara nata kayan.
Kwanciya tayi ta soma karanta wasikar da Qulsoom da Inayah suka rubuto mata.
Adda munyi missing din ki...
Kalmar data karanta kenan taji hawaye masu dumi sun jika mata kunci. Bata gane wasu abubuwan ma da suke fada ba a wasikar don idonta taf yake da hawaye. Haka ta rungume wasikar a kirjinta wani gunji kuka yana kubce mata.
A haka har aka kira sallar Maghreb. Ta tashi ta goge hawayenta sannan ta wuce laundry. Alwala tayi ta dawo ta dakinsu Yusrah ta samu itama tayi alwalar. Da hijabinta a hannu suka fice a hostel din zuwa masallaci.
Da aka idar ma hostel din suka dawo suka cinye sauran pepper chicken da aka kawo musu.
A haka rayuwar ta cigaba da tafiya har ranar hutun su ya zagayo.
Sai da tayi kwana biyu a Kano sannan suka taho Azare da Bappahn.
Ranar su Inayaah murna kamar su zuba ruwa a kasa su sha. Kasa zama suka yi suna ta sintiri Addansu ta dawo gida. Duk sai taga sun canza mata a 'yan watannin. Ga wata kiba da Inayaah tayi har ma tana so ta wuce Qulsoom.
Hutun sati uku aka basu don haka Umma tace su shirya suje Shira su je su gano Daada.
Hutun ya mata dadi matuka. Kwanansu uku a Shira suka dawo. Daada ta hada ta da kayan kwadayi su gullisuwa ne da su hallaka kwabo wai ta bawa kawayenta.
Hafsatu ma ta kawo mata ziyara. Wuni guda tayi a gidansu tana ta bata labarin makaranta da abubuwan da akayi tunda ta tafi. Sun sha hira sosai kamar kar su rabu. Sai taji dama Hafsatun ta dawo makarantarsu ita ma.
Bayan an dan kwana biyu Abba yace taje wa Anti Mami nan ma ta dan yi mata hutu. Abun ya mata dadi sosai.
Abban da kansa ya rakata har Jama'aren. Anti Mamin sun tashi a gidan da ta santa sun koma wani mai dan girma. Daki uku ne a ciki madaidaita da dan parlor. Ta samu ma an canja wa Anti Mamin kayan dakin nata. Kuma yanda ta sameta sai taga kamar tana cikin kwanciyar hankali. Hakan yasa taji ranta ya mata dadi sosai.
A kwananta na uku ne a garin Anti Mami ta shigo dakin da ta mata masauki ta sameta tana karatun littafin da yake sharhi akan Akhdari. Ahmadi na kwance a gefenta yayi bacci don tun la'asar yake goye a bayanta sai da Anti Mamin ta ce ta saukeshi kar kirjinta yayi ciwo.
Ta dan dafata tana zama a bakin gado. "Hajiya Adda"
Fareeha ta dago idanunta masu kyau ta saukesu a kanta. "Hajiya Anti Mami"
Sukayi murmushi su dukansu. "Wata magana ce a bakina"
"Ina jinki"
Ta dan gyara zamanta. "Ina tsoronki ne Adda. Kar ki gwale ni"
Fareeha tayi dariya. "Tsoro kuma Anti Mami? Dan Allah ki fada min meye?"
Anti Mami tayi ajiyar zuciya. "Kanin Uncle Mukhtar ne wanda suka zo shekaranjiya ne yace yana son magana dake shine nace barin ji daga bakinki tukunna"
Fareeha ta juya idanunta tana kifa littafin a kan pillow. "Oh ni Hauwa'u. Daga zuwana?"
Anti Mami ta dan dungureta"Eh daga zuwan naki. Lefine dan yaga ni yana so?"
"Nikam kice mishi a'a wallahi. Umma ma idan ta ji labari balbaleni zatayi. Karma Abba yaji labari. SS1 fa nake?"
"To ai ba aure aka ce zakuyi ba ko? Kawai dai zaku na gaisawa ne a samu fahimtar juna kafin lokacin yayi"
Ta girgiza kanta alamar bata son zancen.
"Nikam banaso"
"To Allah ya baki hakuri. Dama nasan gwaleni zakiyi."
Bata ba ta amsa ba har ta fice a dakin. Sai a lokacin ma take tunanin a ina ma ya ganta har ya ke wani cewa yana son ta. Ita dai a iya tunaninta a ranar data zo suna kitchen ita da Anti Mamin ya shigo da ledojin pure water guda biyu ya ajiye a store. Gaisuwa ce kawai ta gifta a tsakaninsu daga nan kuma bata kara saka shi a idonta ba.
Ita yanzu a 'yan shekaruntan nan yaushe zata wani tsaya magana da wani wai dan su fahimci juna?. Ai Umma tana jin labari ma zata hanata zuwa Jama'aren baki daya.
Allah de ya kyauta.
A haka ta kare iya kwanakin dazata yi ta dawo Azare. Tana dawowa kuwa ta fara shirin komawa makaranta.
Abun mamaki a unguwarsu ma sai taga ana ta bibiyar ta. Kamar ko da din basu san da zamanta bane sai yanzu dasuka dade basu ganta ba ko meye oho. Ita dai bata bawa kowa dama ba, bata ma nuna musu ta san abunda sukeyi ba. Hankalinta kacokam ta dauka ta mayar kan karatunta..
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top