10.

Wayarshi da take ta kuka babu kakkautawa ne yasa ya fito a wankan da wuri. Ba wai don ya gaji da jin dumin ruwan a jikinshi ba, sai dan kawai yasan Mujahid ne yake ta mishi wannan kiran.

Shi dinne kuwa. Yana goge fuskarshi da karamin towel ya amsa kiran ta re da sakawa a speaker.

"Ya akayi?"

Da ga daya bangaren Mujahid ke fadin. "Haba Malam. Tun dazu nake ta jiran kiranka inji ko ka kamo hanya amma shiru. Aisha har tayi fushi."

Ya danyi murmushi. "Karkayi mata sharri. Fushi ai sai kai"

"To naji. Kana ina?"

Zama yayi a bakin gadon yana ajiyar zuciya.

Zaiyi karya idan yace kwata-kwata bashida raayin fita yau. Kwanansa uku baya gida kullum yana zarya daga wancan gari zuwa wancan. Dan baccin dayake samu ba wadatacce bane.

A tunanin shi yau din in ya dawo gida yayi wanka da ruwa me zafi sai yayi bacci har sai ya koshi. Amma hakan be yiwu ba don yana fitowa a airport ya samu kira daga Mujahid akan yana gayyatar sa cin abinci a gidanshi. Kanwarshi ce ta gama karatun ta shine suka hada mata dan kwarya-kwaryar walimah. Bai so zuwa ba amma Mujahid ne. Ba ze iya ce mishi a'a ba.

"Ina gida. Amma ganinan ka bani minti talatin"

Mujahid ya jinjina kanshi. "Minti talatin bazai kawoka ba. Sai dai na ganka kawai"

"Amin hakuri"

"Kazo tukunna se a maka hakurin"

Yayi dariya. "To yallabai"

Sai da ya shafa mai ya feshe jikinshi da turaruka masu dadin kamshi kafin ya tsaya a gaban wardrobe din nashi yana tunanin me ze saka. A irin wannan yanayin yakan tuno Najmah.

Dama shi kayanshi jeans da t-shirt. To da zarar zai je wani wajen taro ko kuma zai fita da abokansa zata tsaya ta zaba mishi kayan da zai saka. Yana kiranta da 'personal stylist' dinshi. Domin duk kayan da ta dauko idan ya saka sai yaga sun mishi kyau. Ta san kayan daya dace da kowanni occasion. Kuma ta iya matching kaloli.

Allah ya mata Rahma.

Bai san ya akayi ba yaga ya jawo wata shaddarshi sky blue da rabon da ya sakata tun sallah. Rigar iya gwiwa ce me dogon hannu wanda aka tsukeshi don yana bukatar cufflinks. A nitse yayi shirin nashi. Yana gamawa kuwa ya kama hanya.

Tun daga kofar gidan Mujahid din yasan cewa suna alfahari da Salmah din domin gaban gidan yasha decoration da balloons Kala Kala. Ko ba komai ta fito da first class dole su gwangwaje ta. Shi ma ya tsaya ya siya mata wata sarka kafin ya taho. Abun da yasa ya kara yin lattin ma.

Ya daga hannu zai danna doorbell din kenan kofar ta bude.

Dara-daran idanuwanta ne suka fara mishi sallama kafin idanuwanshi suka fara yawo a kan fuskarta.

Tsayawa sukai suna kallon-kallo kafin ta farka daga duniyar da ta tafi.

"Sorry" ta fada tana 'yar dariya a yayinda ta matsa mishi don ya shigo ciki.

"It's fine" ya fada yana rabata ya shiga gidan a dai-dai lokacin da ita kuma ta fita.

Daidaikun mutane ya samu a falon ya dan gaggaisa da wanda ya sani kafin ya wuce backyard inda anan ne ake ta harkar.

Salmah din ya fara hangowa a cikin 'yan uwanta suna ta daukar hoto. Sanye take da doguwar riga ja wacce ta karbi farar fatarta. Tayi lullubi da wani dan siririn mayafi ja sai tiara ta daura akan mayafin.

Yana karasawa wajen Mujahid ya dan ture mishi kafada.

"Malan an tashi fa" ya fada yana hararsa ta gefen ido.

Murmushi yayi ya juya wajen Salmah din suka gaisa ya tayata murna. Ya gaida sauran 'yan uwan nata ma kafin ya tsaya shima akayi hoto dashi.

Teburin da aka ajiye tarin kyaututtukan da aka bata ya je ya ajiye nashi kafin ya nufi inda ya ga an ajiye abinci domin ya sa wani abu a cikin nasa.

Yawanci an cinye abubuwan. Ya dai samu salad da wata 'yar shinkafa da kuma wasu manyan manyan samosa da jikinshi ya bashi na mutan Indiya ne.

Cokalin roba ya dauka da kuma serviette.

Waje ya samu can gefe ya zauna yana ci. Mujahid ya taho wajenshi rike da kwalbar Snapple ya ajiye a gabanshi shi ma ya zauna.

"How far?" Ya daga mishi gira.

"Nice party" Muazzam din ya fada yana hadiye abincin shi.

"Duk Aisha ce ta yi wannan shirin. Amma aljihu na yayi kuka"

Suka kyalkyale da dariya. "But Salmah deserves it"

Mujahid ya jinjina kai. "Yes she does. Ita ta fara cin first class fa a dangin nan"

"Dukkanku mumu ne ashe" inji Mu'azzam.

Suka sake wata dariyar. Mujahid har da dan hawaye ma.

Ya kalli abokin nashi sosai. Ya ji dadin yanayin daya ganshi. Yayi fes kuma kamar ya dan kara kiba ma. Da alama ya dan fara samun kwanciyar hankali"You look good"

Mu'azzam ya dan juya idonshi alamar baya son zancen. "Kar ka fara"

Ya buge mishi fada. "No seriously. In fada maka gaskiya?"

Mu'azzam ya girgiza kai alamar baya son ji.

Mujahid din be biye mishi ba ya cigaba da magana. "Abun da ya sa na isheka ma akan kazo akwai wata kawar Aisha ne danakeso ku gaisa"

Wani kallo Mu'azzam din ya watsa mishi. Yayi saurin daga hannayensa alamar surrender.

"Maida wukar to abokina. Aisha advised me against it. Tace be kamata na matsa maka ba akan wannan lamarin in de har ba kai bane ka nuna son hakan"

"Allah ya mata albarka wallahi"

Mujahid yayi dariya. "Ameen. And on the brighter side ma, ta riga ta tafi. Tana tafiya ka iso so ka saki ranka. Bani da niyyar sake maka shishigi kuma"

Cigaba sukayi da wata hirar. Anan gidan Muazzam din yayi Maghreb sannan ya tayasu dan tattare wajen kafin shima ya kama hanyar tafiya. Aisha ta cika mishi leda da sauran snacks din da sukayi ragowa. Ya ji dadi sosai.




Fara'a ce shimfide a fuskarshi a yau din. Duk wanda kuwa ya hada hanya da shi zai fahimci cewa yana cikin nishadi. Abokan aikinsa ma hadda dan zolaya ko dai wata ya samu. Share su kawai yayi don bazasu fahimci yanda yakeji ba.

Ammansa ta dawo kuma bashida wani buri illa ya ganshi a kusa da ita. Rabon da tayi tafiya ta dade har haka tun lokacin bikinshi. Shi dinma kusan kullum suna tare. Bayan bikin ne ma suka taho shi da Najmah su ka bart a can ta karasa kikkimtsawa tayi sallama da 'yan uwa.

Dan karamin akwatinshi ya ja zuwa wajen airport din kafin ya tsayar da taxi ya shiga.

Wanka kawai ya yi a gidan nashi bai ma bi ta kan abinci ba ya sake ficewa. Ya tsaya ya sai mata flowers da kuma chocolate cupcakes. Kowa ya gansa abun da zai zo mishi shi ne zaije wajen matar sa ko budurwarsa. Shi kam gun Ammansa zaije. Matar da ta fi kowa da komai muhimmanci a rayuwarsa kuma wacce yake kauna da dukkan komai nashi.

Doorbell din da ake ta dannawa babu kakkautawa ne ya sa ta gane cewa shi ne.

Kwana biyun da ta dawo ba abunda take sai bacci saboda gajiyar da ta kwaso don haka ba ta sanar da kowa cewar ta dawo ba ma.

Bata taba tunanin haka tafiyar tata zata kasance cike da dinbin tafiye-tafiye daga wancan garin zuwa wancan gari. Amma an shafe shekara biyar rabon da ta saka kafarta a Nigeria. Anyi mutuwa Kala Kala da bukukuwa da kuma haihuwa. Haka ta bisu daya bayan daya tana ta'aziyyah da barkan da bata samu tayi ba shekaru da suka wuce. Dukda wasun ta yi su a waya amma tun da taje kasar haka taje dukka. Wasu wajajen ita ma in ta je sai a mata ta'aziyyar Najmah.

Ta sada zumunci kam yanda batayi tsammani ba kuma hakan sai ya samar mata da wata nutsuwa da bata san daga inda tazo ba. Taji dama da Mu'azzam dinta sukazo shi ma ya kwashi ladan.

Da murmushi a fuskarta ta karasa wajen kofar. Ko dubawa batayi ba ta bude. Bai kara ko minti daya ba ya rungumota.

Hawaye yaji sun taru a kurmin idanunsa a lokacin da ya gane cewa yayi kewarta ba kadan ba.

"Amma...." ya kira sunanta. Ya rasa mai ze ce kuma bayan wannan.

'Yar siriryar dariya ta saki tana bubbuga bayansa. "Na'aaaam"

Ya saketa ya dan sake kallonta da kyau. "Lallai Ya Bebi ta baki abinci kin koshi. Har kumatu kikayi Amma"

Ta sake wata dariyar tana jan hannunsa zuwa ciki. "Bana son sharri. Kwata-kwata kwana na nawa a gidanta."

Zama sukayi a falon nata a lokacinda ya ajiye kwalin cupcakes din daya siyo mata yana mika mata flowers din. Tashi tayi zuwa kitchen dinta domin neman vase dinda zata adana flowers din a ciki. Sai a lokacin ya lura da akwatinta ma a gefen kujera.

"Jetlag dinne har yanzu?" Ya tambaya a lokacinda ta dawo falon rike da kofin shayi guda biyu ta mika mishi daya.

Ta dan mutsutsuka ido tana murmushi. "Wallahi."

Ta bude kwalin ta dauki cupcake guda daya ta kai bakinta shi kuma ya kurbi shayin da ta bashi.

"Me aka kawo min?"

Ta dan kalleshi ta gefen ido. Hakan ya bashi dariya.

"Bayan ka ki rakani"

Ya sake dariya. "Ni fa ba kin rakaki nayi ba Amma. I had my reasons"

"To next year dai Bebi zata yi auren Samha sai ka shirya zuwa"

Ya zaro ido. "Wace Samhar?"

"Samha nawa ka sani?"

"Lallai abun ba wuya. Har ta isa aure yanzu?. A bikina fa befi wani SS1 ko 2 take ba a lokacin"

Amma ta fashe da dariya. "Kai Babana. Kai ma de auren wuri kayi shiyasa. Kuma yanzu in ka duba tsakanin bikinka da yanzu ai Samha ya ci ace itama tayi aure. Aji uku ta ke fa yanzu a jami'a"

Ya jinjina kai. "Masha Allah. Allah ya kaimu lokacin. Yaushe ne?"

"Ba a saka rana ba ma. Bebin ce dai she is so excited about it. Ba ma kowa ya san zancen ba nima dai ta fada min ne dan na zama cikin shiri"

"To Allah ya kaimu. Su Ya Bebi za'a aurar da 'ya ai ba zama"

Suka kyalkyale da dariya.

Ta ji dadin da yanzu Muazzam din yana sakewa yayi hirar aure ko wani abu makamancin haka ba tare da wani duhu ya gifta ta idonsa ba. Hakan ya mata dadi matuka.

Yanzu kusan shekara kenan da rasuwar. A ranta tana fatan cewa watarana Muazzam din zai sake bude zuciyarshi wa wata har ma yayi wani auren. Zama hakan babu dadi kuma tana mishi addu'ar samun wata abokiyar zaman. Lokaci kawai take jira kafin ta taso mishi da zancen.

Hira suka cigaba da yi suna cin cupcakes din suna shan shayin nasu. Kafin daga bisani tace zatayi unpacking.

Kwanciya yayi a gadon nata ita kuma tana bakin wardrobe din ta tana ta jera kayan. Na wanki kuma ta shiga toilet dinta ta zuba su a washing machine.

Bai bar gidan nata ba sai wajen tara da rabi. Hakan ma sai da ta takura mishi saboda hutun kwana daya kawai gareshi kafin ya koma bakin aiki.

Bayaso haka dai suka rabu.

Yana zuwa gida kuwa shafa'i da witr kawai yayi ya kwanta bacci. Dan wankan daren da ya keyi ma yau baya jin zai iya.

**********

"Ikon Allah Adda sai kace wanda akayi wa mutuwa?" Umman ta fada tana salati da sallalami. Zatayi karya idan tace bazata yi kewar 'yar tata ba amma wannan kukan da takeyi mai tsuma zuciya ya sa itama tana ji kamar ta daura hannunta a kai ta kurma ihu.

"To yanzu idan an miki aure kuma yaya kenan?" Cewar Maman Walid da ta jinginu a jikin shirgegen akwatin Fareehan.

Ai jin maganar Maman Walid din tayi kaman an watsa mata wuta don haka wani sabon kukan ta sake sakewa tana sulalewa kasa tana zama akan simintin tsakar gidan.

Umma ta saka hannu ta dagota ta rungumeta a jikinta. "Kukan ya isa haka Adda ko nima so kike nayi kukan ne uhm?"

Da sauri ta girgiza kanta amma hakan bai hana hawayen nata zuba ba.

"Ya isa dan Allah" ta sake nanatawa tana bubbuga bayanta. "Wannan rabuwar fa ba ta har abada bace. Karatu zakije. Ci gabanki ne kuma muma ci gabanmu ne. Dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji?. Kar ki bamu kunya"

Ta share hawayenta da gefen hijabin nata tana kallon Umman nata. "InshaAllah Umma. InshaAllah "

"Allah ya baku sa'a ya sa wa karatun naku albarka. Kuna cikin addu'a ta a koda yaushe"

Sake rungumeta tayi sai dai wannan karon bata bar hawayenta sun zubo ba.

Ta juya ta kalli su Qulsoom da Inayaah da sukayi jugum jugum a wajen. Suma da dukkan alamu sai yanzu abun yake zama a jikinsu. Addarsu zata tafi ta barsu har na tsawon wata uku. Wa zai na tashinsu a bacci? Wai zai na wanke musu uniform? Da wa zasu na zuwa makaranta ? Wa ze na raba su fada?

"Dan Allah kar ku na saka Umma yawan magana kunji?. Duk abunda tace kuyi kawai kuyi banda fada kuma"

Kai suka gyada mata kawai. Inayaah kam hadda dan guntun hawayenta. Ta rungumesu suma kafin ta nufi hanyar waje.

Abba kam tun shekaranjiya sukayi sallama don yana da tafiya zuwa Hadejia. Gonarsa da take can wanda Baba Zubairu yake duba masa zaije ya gano. Ya de mata alkawarin zai tsaya a kano a hanyarsa ta dawowa Kuma zai leko ta a makarantar.

Maman Walid ne ta ja mata akwatin har bakin mota. Direban yana ciki sai Baba Habu da ke tsaye a gefen motar. Tun dazu ya fito a gidan yana jira su gama sallama.

A tsakanin wata biyu zuwanshi Azare kusan sau uku kenan. Abunda be taba yi ba. Duk a sanadiyyar Fareeha.

A tsarin Bappah Dattijo baya bari yaransa mata suyi yawo da direba su kadai sai dai ya hadasu da wani na gida Babba. To yawanci duk yawon su Yusrah in dai da direba to shi ake sakawa ya rakasu. Amma sunfi fita ma da mamansu wasu lokuttan ko Ya Ashraf idan yana gari.

Dalilin dayasa kenan duk zuwan Fareeha da tayi zuwa Kano in ba da Bappah ba to za'a turo Baba Habu dan shine a gida lokacin.

Bacci ne me nauyi ya kwasheta tun kafin su wuce Jama'are saboda tsabar kukan da ta sha. Bata farka ba kuwa sai da motar ta tsaya a harabar gidan Bappan.

Yusrah ce tazo ta tarbeta da murna a fuskarta. Haka suka ja akwatin suka shige ciki. Anti Bebi bata nan ta je yinin bikin wata 'yar kawarsu shima Bappahn baya nan sai su kadai a gida.

Sai da ta ci abinci tayi sallah tukunna sannan Fadila ta kira mata Ummanta a waya. Suka gaisa ta sanar mata sun isa lafiya.

"Umma ki ce wa Anti Mami ta kira ta wayar Ya Fadila mu gaisa"

Umman tayi murmushi. Kwarai ta so ace sun tsaya sunyi sallama da Mamin amma tunda ba ita ke da iko a kan direban ba shiyasa bata ce musu su tsaya ba. Duk da kuwa tasan in ta sanar da Bappahn tana bukatar haka ba ze hana ba. Hasalima zai so ace dukkansu sunje su ga Yaya Mamin take tun bayar komawarta gidan nata. Domin gaba ki dayansu sunga abun al'ajabi a dangane da auren nata.

Mukhtar dai ya ce shi sam bai san lokacin da ya saketa ba kuma yana so ta dawo dakinsa. Su Bappahn dai sun ja mishi kunne sosai kuma su ka mishi naseeha mai ratsa jiki. Ganin cewa har yanzu Mamin tana son mijin nata shine ya Kara basu karfin gwiwar amincewa ta koma din dukda dama ta riga ta komu tunda bata gama idda ba kuma Mukhtar ya rigada ya firta cewa ta dawo din. Haka suka rakata da Addu'a suna fatan wannan ya zamo karshen dawowarta gida.

Tun da ta tafi kuwa kusan kullum sai Umman ta kira taji Yaya suke don sam hankalinta bai kwanta ba. Shi kuma Bappahn ta wajen Umman ya ke samun labari. Ya na so ya je ya dubata amma bayaso Mukhtar din yaga kamar ya takura musu.

Ya dai yanke shawarar duk randa hanya ta biyo da shi zai tsaya ya ganta din.

Umma ta yi ajiyar zuciya. "To inshaAllah zan fada mata. Ki gaida su Fadilan da sauran yaran duka"

"Zasuji"

Suna ajiyewa kuwa Antin Mamin ta kira. Gaisuwa sukayi mai tsawo. Suma Yusrah da Fadilan duka ta gaisa dasu kuma tayi wa Yusrah fatan alkhairi da Addu'ar Allah ya bada sa'ar karatu. Har Amina mai aiki aka kira ita ma suka gaisa.

Dayake Samha ta dawo daga makaranta sun dan sami hutun mid semester break, sai Fareehan kawai ta zabi ta zauna a dakin su Fadilan tunda dama washegarin zasu wuce makaranta da yamma.

Sai bayan Maghreb Anti Bebi ta dawo. Ta samu Samha da saurayinta wanda aka musu baiko a parlor. Bappah ya hana hirar waje ko ta mota. In baza'a shigo cikin gida ba a hakura.

Suka gaisa a mutunce ta wuce ciki.

A daki ta samesu su uku suna ta shirin goben. Suka gaisa da Fareeha ta mata ya hanya sannan ta mika wa Yusrah ledar da ta shigo da ita.

"Gashi ku kara a cikin kayanku kowa guda shida" tana fada ta fice a dakin.

Yusrah na leka ledar ta fashe da dariya. Ta mika wa Fareeha.

Kunya ce ta lullubeta sai ta tura ledar gefe.

Ko ba'a fada mata ba tasan menene. Tana gani a wajen Umma da Anti Mami kuma tasan amfaninshi tunda an musu a Home Economics. Lokaci ne dai bai yi ba da ita ma zata fara amfani da shi.

"Ki ajiye mana a akwatinki" ta fada wa Yusrah a hankali.

Yusrah ta sake fashewa da wata dariyar. Ita bata ga abun jin kunya ba. Ko ba dade ko ba jima ita ma watarana lokacin zai zo to meye na jin kunya? Abu ba ciwo ba ba komai ba?

"Ki na dai ji Mama tace mu raba ko?"

"In ina bukata zanzo wajenki in karba ai. Ki ajiye kawai. Ni akwati na ma ya cika"

"To sai kisa a school bag"

Fareeha ta mata wani kallo. Ta sake yin wata dariyar. Ita abun dariya baya mata wuya dama.

Haka ta yi ta zolayarta sai da Fadila ta sa baki sannan tayi shiru.

Gaba daya gidan aka dunguma kaisu don mota biyu sukayi. Bappah da Anti Bebi suna mota daya sai su yaran duka a mota daya. Har aka isa zuciyar Fareeha tana dukan uku-uku.

Suna tsaye Bappah ya gama cike-ciken da zai musu a matsayinsu na sabbin dalibai sannan akayi checking kayansu da littatafansu saboda a tabbata akwai komai. Fareeha tana A class Yusrah kuma tana B don yanda aka tsara makarantar A class sune 'yan Arts 'yan B class kuma 'yan Science.

An ci sa'a hostel daya aka kaisu sai da kowa da dakin da aka bata. Anti Bebi da Samha suka taya su jera lockers dinsu Fadila kuma ta gyara musu gadonsu ta sassaka musu bedsheets da pillow case.

Sai da suka tabbata sun gama musu komai sannan sukayi sallama. Sai a lokacin Yusrah ta gane cewa fa bazata kara ganinsu ba sai anyi hutu. Ai kuwa sai hawaye daya na bin daya.

Abun mamaki sai Fareeha ne ta ke rarrashinta. Ita kuma a lokacin sai taji ta gama kukanta a Azare. Idonta taji ya kafe.

Yusrah bata kara jin kewan gida ba sai da daddare da akayi lights out. Wani tsoro ta ji ya mamayeta. Da yanzu suna fada da Fadeelanta akan ta yaye mata bargo ko ta jibga mata kafa.

Wasu zafafan hawaye ne taji suna barazanar zubo mata.

Ta juya ta tofa Addu'a tana rokon Allah ya cire mata tsoron da takeji.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top