1.

Brooklyn, New York.

Litinin, 12th June 2012.

Hawaye ne masu bala'in zaafi suke zubowa daga idon Ibrahim Mu'azzam a lokacinda mahaifiyarshi dake gefenshi take qoqarin kwantar mishi da hankali. Sai dai kash! Itama kukan take don haka sai ta kasa lallashinsa domin itama a lokacin tana buqatar lallashi da ban baki. Zaune suke a waiting room din A&E unit din Parkway Hospital. Mintina talatin da suka wuce kenan aka sanar musu rasuwar matar Mu'azzam wato Najma wacce ta shaafe kusan kwanaki biyar tana fama da jinyar ciwon bronchitis.

Kuka sosai Mu'azzam din yake har da shesheqa. Wata nos ta qaraso wajensu fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce "Mr. Kabir, you may go in and take the body".

Jikinsa na rawa haka ya miqe ya bita zuwa dakin daukan gawa.

Gawawwaki ne gasu nan an jerasu a sahu kowa da sunansa da lokacin mutuwarsa a lankaye a jikin gadonsa. Dukkan gawawwakin na jiran family member yazo ya tafi dasu kamar yadda tsarin asibitin yake. Ya tsaya a kan gawar Najmar wanda tuni an rufeta a cikin wani silver yadi.

Name: Habib Najma

Age: 21

Time of death: 11:54am.

Abunda aka rubuta kenan a jikin gawar tata. Wasu hawayen suka sake kwaranyo masa. Ya kira sunan Allah tareda jan dogon numfashi kafin nan ya turata izuwa waje.

Ammah dake durqushe ta miqe ta nufo shi. Babu abunda bakinta yake furtawa sai 'Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un'. Ta sa hannu suka tura gawar tare zuwa waje inda motar daukan gaawa take. Basu zarce ko ina ba sai community masjid din da ke unguwarsu.

Da qarfe biyu bayan sallar Azahar aka sallaci Najma Habeeb kuma aka miqata izuwa ga makwancinta wato qabari. Mutane da dama wadanda ta qulla alaaqa da su a 'yan shekarun da tayi a garin sun hallacci jana'izar tata.

Babu abunda suke fada a kanta sai alkhairi domin Najma ta kasance mai faran-faran da mutane ga son taimako da girmama na gaba.

Kawayenta da sukai internship a United Nations headquarters tare sun zubda hawaye kuma sunyi kewarta matuqa domin ta riqe su kamar 'yan uwanta na jini.

Amma duk cikin ilaahirin mutanen nan babu wanda yaji mutuwar ta har cikin bargon qashinsa kamar mijinta kuma masoyinta wato Mu'azzam. Ji yake kamar an sa wuqa an yanke wani sashe na haqarqarinsa ne.

A lokacin ne wani zazzafan zazzabi ya rufe shi. Ya dawo da qyar ma yake numfashi. Hankalin Ammansa ya tashi. Kafin Maghreba tuni an kaishi asibiti. Ai babu shiri likitoci sukayi admitting dinsa. Ammah ta rasa mai ke mata dadi. Da rashin Najma zataji ko kuwa da Mu'azzam danta tilo guda?. Haka tai ta kaiwa da komowa a asibitin har sai da ta tabbata ya zama stable sannan hankalinta ya dan kwanta. Ta zaro wayarta domin sanarda mahaifan Najma rasuwarta amman sai ta rasa da irin muryar dazata fada musu. Ta yanke shawarar kawai tayi musu text message. Hakan kuwa akayi.

Bayan likitoci sun gama zurkuda masa allurai kuma an saka masa drip, wani nauyayyan bacci yayi awon gaba dashi. Ammah na gefensa tana karanta masa Suratul Baqara murya qasa-qasa. Bada jimawa ba itama baccin yayi awon gaba da ita domin stress yayi mata katutu a system dinta.

Ba ita ta farka ba sai qarfe daya na dare. Bandaki taje ta dauro alwala tazo ta gabatarda sallar Isha'i domin bacci bai barta tayi sallar ba akan lokaci ba. Tana idarwa ta dago wayarta dake kan kujerar datayi bacci akai.

Missed calls ne kaca-kace akai. 'Yan uwan Najma da mahaifanta sun mata missed calls kusan ashirin. Da suka ga sun kasa samunta sai suka mata message cewar zasu zo har New York din nan ba da dadewa domin suzo suyi wa Mu'azzam din ta'azziyah.

Ta amsa saqon nasu da yi musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya. Daga abokan aikinta har 'yan uwa duka kowa ya kira domin yayi mata ta'aziyya. Ta rasa yadda zatayi da sauran missed calls din kawai sai tayi replying messages din sannan ta kashe wayar.

Gari na wayewa kuwa dakin nashi ya cika da abokanshi daga aviation industry. Daga kan pilots zuwa flight attendants da ticketing officers kowa yana zuwa gaisheshi kuma ya masa ta'aziyyah. Saidai duk zuwan dasukeyi kwata-kwata baisan inda kanshi yakeba.

Ammah ce ke karban gaisuwan da kuma amsar bouquet of flowers din da ake ta kawo masa. Dama turawa kam ba dai son bada flowers ba. Haka dakin nashi ya cika maqil da flowers har Ammi ta rasa inda zata sakasu. A qarshe dai sai fitowa tayi daga dakin ta zauna a reception. Duk wanda yazo sai tace Mu'azzam is unconscious. Mutane kuwa basu daina zuwa ba har La'asar. Ai kuwa tana sallar La'asar ta koma gida tayi wanka ta samu taci abinci.

Saida Mu'azzam ya shafe awowi talatin da takwas kafin ya farfado daga yanayin daya fada. Yana bude ido kuwa babu abunda yake furtawa illa 'Najma'. Ammah ta tsaya a kanshi tayita tofa addu'o'i tana share mishi jiki da towel wanda ta tsoma a ruwan sanyi. Da qyar ta samu ya dawo hayyacinsa. Bayan nan kuwa sai yayi ta kwarara amai. Nurses duk suka rikice ana bashi taimako. Wasu alluran aka sake tsikara mishi sannan aman ya tsaya. Daga nan kuma baccin wahala yayi awon gaba dashi.

Ammah ji takeyi kamar an tattaro tashin hankalin duniya an yafa mata shi. In banda salati da kiran sunan Rabbil Izzati babu abunda takeyi. Hawayen ma kasa zubowa sukayi. Gaba daya jikinta ya mutu. Shin Mu'azzam dinma mutuwa zaiyi ya barta?

Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un.

Qarfe shida na safiyar ranar yayar Najma da mahaifiyar ta suka shigo qasar. Ko masauki basu wuceba kai tsaye asibitin aka kawo su. A help desk din suka tambaya aka musu kwatancen dakin Mu'azzam. Tun kafin su qarasa mahaifiyar Najmar wanda ake cewa Mamma ta fara kuka. Diyar ta dake gefenta ta kamo hannunta.

"Mamma please!" ta fada cikin murya mai rauni. "Ya isa haka. Idan Mu'azzam ya ganki a haka he will loose it. Ki daure. Do this for Naj. Please."

Da qyar Mamman ta hadiye kukan nata sannan suka qarasa dakin.

A yadda Amman ta barshi a haka suka sameshi shame-shame a kwance rai-kwakwai mutu-kwakwai. Duk ya rame a dan tsakanin kwanakin. Ga lebbansa sun bushe duk sunyi baqi ga wani wahalallen numfashi dake futa daga bakinshi. Duk wanda ya ganshi a wannan yanayin dole ya tausaya masa.

Mamma ta kasa daurewa, hawaye kam suka dinga sintiri a fuskarta. Na'ima ma kasa daurewa tayi. Sukayi ta kukan su biyu ba mai rarrashin wani.

Ammah ce ta turo qofar dakin ta shigo. Dawowarta kenan daga wajen doctor. Tana ganinsu taji wani abu ya tokare mata a maqogoro. Ta tattaro duk wani qarfin halin da ya rage mata ta fara rarrashinsu da ban baki. Da qyar aka samu suka daina kuka. Suka zauna dukansu jugum-jugum babu mai cewa kowa komai.

Baby din dake hannun Na'eema ce ta fara tsala kuka. Kamar ance wa Mu'azzam 'bude ido', ya kuwa bude su. Basu sauka ko'ina ba sai kan Na'eema wacce a lokaci guda ta rikide masa ta koma Najma.

Basu lura cewa ma ya farka ba saida na'urar dake nuna bugun zuciyarshi ta fara wani irin qara; alamar akwai matsala kenan. Ammi tayi firgigit taje gareshi. Jikinshi ya fara rawa, bai kuwa dena kallon Na'ima ba wacce ta tsaya cak ta kasa motsi saboda tsoro. Numfashin shi ya fara yin sama-sama.

"Mu'azzam. Look at me. Stay with me please." Ammah ta kama hannunshi ta fara tofa mishi addu'a. Nan da nan jikinshi yayi zaafi. Mamma ce ta fita da sauri ta kira wata Nos. Tana zuwa taga yanayin dayake jiki sai tayi allura a jikin ledar drip din da aka daura mishi.

Cikin ikon Allah kuwa bayan wasu dan lokuta sai ya dawo hayyacinsa. Numfashinsa ya dan dawo dai-dai. Nan bacci yayi awon gaba dashi. Ya shafe awowi masu tsawo kafin nan kuma ya farka. A lokacin jikin ya danyi sauqi kuma ya dena hallucinations din.

Mamma tazo kusa dashi tana mai murmushi wanda yafi kama da yaaqe tace "Mu'azzam ya jikin?"

Ya kalleta a lokacinda wata qwalla ta zubo masa. "I'm fine Mamma. Yaushe kukazo?"

Itama hawayen ne suka cika mata idanu. "Daga airport muka wuto nan..." sai kuma tayi shiru.

Mu'azzam ya juya idonshi zuwa ceiling din dakin. "Mamma ya haqurinmu kuma?"

Dukansu kallonshi suke cikin mamakin furta maganar da yayi. Basuyi tsammanin zai iya furta hakan ba duba da yanayin daya shiga saboda mutuwar.

Mamma tayi qarfin hali ta amsa. "Haquri ya zama dole Mu'azzam. Allah ya jiqan Najma ya saka mata da Aljannah"

"Al-Firdaus" Mu'azzam ya fadi cikin wata siririyar murya. "Mamma na yaafe mata komai wallahi. Insha Allah Aljannatul Firdaws zataje."

Ammansa ta shafa kansa "Insha Allah"

Kafin Azahar tayi har yana iya zuwa bandaki da kanshi ba tareda taimako ba. Ya dauro alwala yazo ya jero sallolin da suka kubce masa sannan ya hada da ta lokacin tareda nafilfili na neman gafara a wajen Ubangiji na rashin tawakkalin daya nuna hade da rokon Sa daya yafe wa matarsa dukkan kura-kurenta. Lokaci mai tsawo ya shafe yana ibadarsa. Bayan ya kammala Ammah ta zuba mishi abinci.

Ya karba tareda kallon jaririyar dake hannun Mamma.

"Mamma can I hold her?" Ya tambaya yana qura mata ido.

"Mu'azzam kaci abinci tukunna" ta fada tana murmushinta irin na manya.

Ya dan langabar da kai. "Please" ya roqeta. Bata iya ce mishi komai ba ta miqa masa baby din.

Dumin jaririyar ya ratsa jikinshi a lokacinda ya karbeta ya rungume ta a qirjinshi. Qamshin baby powder dinta ya doki hancinshi. Ya lumshe ido.

Ya tuno irin son da Najma takewa yara. Tanada burin ta cika mishi gidansu da 'yaya masu yawa da albarka. Amma Allah bai basu ba. Sun shafe shekaru uku da aure amma ko batan wata bata taba yi ba balle bari. Anje asibitin anyi gwaje-gwaje amma ba a gano wata matsala ba. Dukkaninsu lafiyansu qalau, lokaci ne kawai baiyi ba.

Ya tuno lokutan da zai sameta tana kuka a daki a kan rashin haihuwa. Ya sha nuna mata hakan bai dameshi ba. He is contented living his life with her by his side. A wasu lokutan yana tsokanarta yace "Kika sani ko Allah ne yake prolonging honeymoon dinmu?" sai ta zumbura baki "Wani irin honeymoon kuma? Nikam ya isheni I want babies".

Lokacinda Na'ima ta haihu kam abun sai ya qaru. Kullum tana cikin zullumi. Balle ma idan ta tuno cewa ta riga Na'imar yin aure amma gashi har ita ta haihu. Mu'azzam yayi iya qoqarinsa wajen lallashinta da nuna mata cewa rashin samun 'yaya bashi bane qarshen duniya. Ya sanar da ita cewa akwai lokaci, kuma lokacin na nan zuwa.

Saidai abinda bai sani ba shine, akwai lokaci, amma lokacin Najma Habib ya kusa qarewa a duniya. Gashi yanzu ta tafi, ba tareda ta haifa mishi babyn da take ta burin bashi ba.

Yaji kanshi ya fara mishi ciwo. Ya tallafo fuskar baby Hannoufah ya manna mata kiss a goshi.

Toh washegari da safe Mu'azzam ya daddage sai da aka sallameshi domin ya sami qarfin jikinshi. Dukda cewar likita ya bashi shawarar ya qarasa kwanakin da aka qayyade masa domin su cigaba da monitoring din condition din nashi, amma yaqi. Haka suka sallameshi tareda magunguna.

Sun koma gida zuciyoyinsu cikeda kewar Najma ta tausayin kawunansu. Shin yaya zasu cigaba da rayuwa babu ita? Musamman ma dai Mu'azzam.?
★★★

Azare, Bauchi.

12th June, 2012.

6:44pm.

Hawaye ne masu bala'in zaafi suke zuba daga idon Fareeha. Ta rasa gaba daya mai ke mata dadi. Tana jiyo masifar da mahaifinta ke zazzagawa Ummansu daga falo, abun babu dadin ji. Dawowarta kenan daga islamiyya ta tarar da abunda yake faruwa. Tsugune take a bayan qofar falon ita bata shiga gidan ba kuma bata fita ba.

"....ai duk ke kika sangarta shi. Gashi yanzu yazo ya kwaso miki bala'i. Sanin kanki ne bashi kadai bane daana don haka inada wasu nauyin a kaina. Kijeki tunda ke ce silar fadawarshi cikin wannan hali kisan yadda zakiyi ki fiddo shi. Ni kam babu nawa a ciki." Abinda Abban nasu yake fada kenan.

Can qasa-qasa Umman take magana murya a sarqe tace "Haba Abban Bilal. Ka dubi girman Allah ka taimaka mana. Idan ba kaiba wa zai taimaka mana?"

"Ohhhh sai yanzu kika san dani? Lokacinda kike zagawa a bayan idona kina zuwa wajen yayanki kina masa qarya yana baki hatsi da masara bakisan da ni ba ai ko?"

Umma tayi shiru zuciyarta tana tafarfasa.

Alhaji Abubakar ya daga murya. "Ba magana nake miki ba?"

Ta sunkuyarda kai. "Larura ce tasa naje wajen Yaya Dattijo. Nan ka tafi ka barmu babu ko sisi watanmu shida babu abunda zamu sarrafa. Takai takawo sai zannuwana da sarqoqina na sayar na sayo mana shinkafa da masara. Da suka qare kuma naje neman taimako"

"Uban waye ya saya miki zannuwan da sarqoqi? Bani bane?"

"Abban Bilal..."

"Yimin shiru. Maakira algunguma. Bazaki taba jin dadi ba harsai kinga kin baata min suna a wajen danginki ko? Don kawai suce na kasa riqeki da 'yayanki" ya ja dogon tsaki. "To kije ki tambayi kishiyar taki zata fada miki ita yadda nake riqeta. Saboda tafiki hankali kuma bata tona min asiri kamar yadda kika bankada min a bainar jama'a. To ki sani, idan baki canja wannan dabi'ar taki ba to fa saidai ki nemi wani mijin baniba"

Hawaye suka cika a idonta fal amman ta hanasu zubowa. Dayaga batada niyyar cewa komai sai ya miqe yana ta guna-guni.

"Haba! Mata sai kace alaqaqai. Tun da na aurota in banda asara da talauci ba abunda ya nane min. Ta zo ta haifa maka 'yaya duk babu mai qashin arziqi duk sai bala'i suke janyo maka. Wannan wacce iriyar masifa ce?..."

Haka har ya fita a sashen nasu yanata banbamin bala'i kaman sabon mahaukaci, tsabar bala'i baima lura da Fareeha dake labe a bayan qofa ba. Sai a lokacin Umman ta samu sararin zubda hawaye domin ta riga taci alwashin cewa bazai taba ganin hawayenta ba. Saida taci kukanta mai isarta sannan ta tashi a falon ta shige daki.

Fareeha da taji Umman ta rufo qofar dakinta sai ta lallabo ta shige nasu dakin. Ta cire hijabinta ta fada bandaki. Tsugunawa tayi a gefen bathtub din tayi ta kuka mai isarta sannan ta cire uniform din nata tayi wanka. Ta jiqa uniform din a cikin bucket kafin nan ta dauro alwala ta fito.

Qannenta mata guda biyu Inayah da Qulsoom suna homework dinsu a kan gado. Da alama shigowarsu kenan daga gidan maqociyarsu Maman Waleed. Yawanci acan suke wuni domin sun shaqu da matar sosai.

Qulsoom ta kalleta tace "Adda lafiya naga idanuwanki sun kumbura?"

Fareeha ta qaqalo murmushi wanda hausawa ke ce wa yafi mari ciwo tace " Qwaro ne fa ya fada shine idon yayi tamin zaafi. Da qyar na cire"

Dayake Qulsoom mai wayo ce sai tace "Kuma duk idanuwa biyun qwaron ya shiga?"

Fareeha ta juya mata baya a lokacin da ta bude wardrobe dinsu tana neman kayan sakawa.

"Ya Qulsoom ki koya min mana" Inayah ta fada yayinda taga hankalin yayar tata baya kan abunda suke yi musu.

Da Qulsoom taga Addan nata batada niyyar amsa mata tambayar data mata sai itama ta shareta ta cigaba da koya wa Inayah homework din ta.

Fareeha ta zaro wata baqar abaya wacce Aunty Hauwa dake Bauchi ta kawo mata a matsayin kunce. Ko dayake ma duka kayansu ma yawanci na kunce ne.

Umma batada isashshen kudin dazata saya musu sababbin kaya. Dama kuma Abba kam ba'a maganarsa. Idan sunsa sabbin kaya toh Sallah ne. Shima din Bappah Dattijo ne yake aiko musu. Wasu lokutan kuma idan Umma ta samu wasu 'yan kudade sai ta dinka musu.

A da can da take sana'ar saida 'yan kunne da kayan kwalliya ba laifi suna samu. Amman daga baya sai Abba ya hana wai mata suna shigo masa gida suna kafa dandalin gulma. Ba yadda ta iya haka ta daina. Ta dawo tana daura zobo da ginger tana baiwa wasu yara suna kai mata College of Education. Shi din ma dai Abba yace bayaso. Wai shazumami sun dameshi a gida saboda ana zubarda sugar idan anayin zobon. Haka ta haqura da wannan dinma.

Duk wata sana'a data kama to sai ya kawo wani dalili marar qwari da zai hanata. Idan ta nuna bazata daina ba kuma sai yayi mata barazanar saki. Yanzu kam haka take zaune tana jiran abunda Rabbana zai aiwatar a kanta.

Bayan Fareeha ta idar da sallar maghreba sai ta nufi dakin mahaifiyar tasu. A kan sallaya ta sameta tana ta Azkhar dinta. Ta sakar mata wani lallausan murmushi kai ba kaace itace tasha kuka a dazun ba.

"Adda har an dawo ne?" Ta tambayeta a lokacinda ta samu gefen kafet din ta zauna.

Fareeha ta gyada kai. "Eh Umma. Na shigo ai sai na samu kina bandaki shiyasa na koma nima nayi sallah". Idonta na qasa gudun kar Umma ta gane qarya take.

Umma ta jinjina kai "Ai har da zan aika a dubo min ke naga har Maghreb baki dawo ba"

Fareeha ta murmusa "To ina zanje a daren nan Umma?"

"Na sani ko kin shiga gidan Maman Walid?"

Fareeha ta dan bata baki "Kin manta Ya Bilaal ya hanani zuwa?"

Umma taji wani abu ya tokare mata maqogaro a lokacinda Fareehan ta ambaci sunan Bilal. Ta qaqalo murmushi tace "Kinsan basa jituwa da Maman Walid dinne shiyasa"

Fareeha ta dan gyara zama. "Wai Umma ina ma yake ne? Tunda na shigo ban ganshi ba"

"Kinsan Bilaal sai bayan Isha yake shigowa gida. Duk yadda akayi yana shagon su Turabi"

Fareeha ta jinjina kai. Sam! bata gamsu da zancen Umman nata ba. Dazu fa taji Umman tana cewa Abba ya taimaka mata akan shi Ya Bilaal din. Duk yadda akayi ya sake fadawa wata muguwar hanya ne. Ba tantama yanzu yana can kulle a police station.

Suka cigaba da hirarrakinsu kamar babu abunda ya faru a dazun. Bada jimawa ba Inayah ta leqo dakin tace "Umma mun gama homework din saura abinci"

Umma ta kalli Fareeha tace "Adda maza zuba musu abinci ko? sai ki duba homework din idan sunyi dai-dai in kuma ba haka ba ki gyara musu"

Fareeha ta amsa da toh kafin ta fice a dakin Inayah na binta a baya har kitchen din. Tuwon masara ne kamar kullum sai miyar kuka koriya shar da ita. Kana ganinta kasan ko isashen daddawa bata samu ba balle kuma kayan miya. Ta zuba musu a babban tire suka dawo falon su uku suka zauna suna ci suna dan taba hira. Khulsoom tana ta basu labari akan wasu qawayenta a makaranta masu bala'in qoqari. Fareeha sama-sama take jin hirar domin gaba daya hankalinta yana kan Ya Bilaal. Wai yaushe ne zai shiryu ya daina wannan harka tashi ta shaye-shayen miyagun abubuwa? Wani abu ya tokare mata maqogwaro ta kasa hadiye tuwon.

Tana iya tuno lokacinda Ya Bilaal din ya ga FGC. Bayan result dinsu ya fito ya samu A's da B's. Dama shikam Allah ya zuba mishi baiwa ta gane karatu. Kwata-kwata bai samu matsala ba wajen neman gurbin karatu a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi. Ya samu gurbi a fannin Electrical Engineering. Baffa Dattijo ne ya biya mishi ya tafi ya fara karatu.

Semestar farko  ya fito da GPA din 4.32. Umma tsabar farin ciki har kuka tayi. Baffa Dattijo ma yaji dadi sosai saboda baiyi asarar kudinshi ba. Duk wani baqin ciki da Umma ke ciki duk sai taji an yaye mata.

Bayan Ya Bilaal din ya koma zango na biyu ne ya hadu da wasu shaidanun abokanai suka saka shi a hanyar shaye-shaye da sauran abubuwan rashin da'a. Kafin kace me gaba daya ya lalace karatunma ya daina maida hankali. A qarshe dai a aji biyu sai korarsa akayi a makarantar saboda an kama shi da wasu suna satar amsa a dakin jarabawa.

Duk mafarkin da Umma take akanshi ya rusa mata shi. Ita a tunaninta shi zai zo ya cire su a qangin da suke ciki. Amma sai gashi shima ya lalace.

Yanzu a taqaice dai in banda yawo a cikin unguwa babu abunda yakeyi. Ko sana'ar kirki ma ya kasa yi. Ya zama abunda hausawa ke cewa 'zauna gari banza'. Umma dai babu abunda take mishi sai Addu'a domin shine kadai abunda zata iya masa. Bappah Dattijon ma yanzu ya zame hannunsa akan lamarinsa yace babu ruwanshi dashi tunda rayuwar daga zaba kenan.

Bayan sun gama cin abincin suka wanke hannayensu sai Fareeha ta dauko homework din nasu ta duba. Duk sunyi dai-dai.

Dayake Qulsoom ce babba da Inaya kuma ta fita aji a makaranta, yawanci ita take koya mata karatu. Ita kuma Qulsoom Allah ya zuba mata qoqari don haka ita ko taimako ma bata nema idan zatayi nata homework din. Saidai idan abun yafi qarfin qwaqwalwarta ne sannan take neman taimako a wajen Addanta ko Ya Bilaal.

Qarfe takwas dai-dai aka dauke wutar lantarki. Fareeha ta janyo lanter ta kunna musu a falon sannan ta tada kabbarar sallar Isha'i. Tana idarwa ta ce dasu Qulsoom suje suyi sallah suma. Suka wuce daki domin yin alwala.

Sallama a kayi a qofar falon. Fareeha ta amsa kaana ta bude qofar. Mamaki ne da farin ciki suka cikata a lokaci guda lokacinda taga qanwar mahaifiyarta wato Aunty Mami a tsaye a wajen.

Ta fasa wani ihun murna hade da rungumo Auntyn nata. Maimakon itama Auntyn ta rungumeta cikin farin ciki, sai ta fashe da wani matsanancin kuka. Sai a lokacin Fareeha ta lura da kayan da ta taho dasu.

"Anti Mami lafiya?" Fareeha ta tambaya lokacinda ta tallafo ta suka shigo falon. Ta kunto Baby Ahmadi wanda ke goye a bayan Aunty Mamin ta rungume shi.

Aunty Mami ta baje akan kafet din falon tana share hawaye. Umma dake daki ta fito tana salati domin ta jiyo kuka. Tana fitowa sukayi arba da Mami sai ta sake yin wani salatin.

"Mami lafiya a wannan daren? Wani abunne ya faru? Menene? Mukhtar ne? Wani abunne ya sameshi?" Umma ta jefo mata tambayoyi wanda a lokacin ta rasa bakin amsasu. Hawaye ne kawai ke sintiri a kumatunta.

Fareeha dai tana gefe zuciyarta sai dukan uku-uku take. Tunda suka taso tare da Aunty Mami gida daya bata taba ganinta a cikin tashin hankali ba irin na yau. A ranta ta ce 'Ko uncle mukhtar ne ya rasu to?'

Haka dai suka dunguma suna lallashin ta. Su Inayah ma da suka idar da sallah suka fito suka zuba mata ido. Saida tayi kuka iya son ranta sannan ta sanar dasu abunda yake faruwa. Mijinta ne ya danqara mata saki kuma ya koro ta gida. Dama tun tana 'yar qaramarta take zaune a wajen Umman. Hasali ma, a wajenta tayi aure. To tunda yanzu batada wajen zuwa sai nan din, shiyasa ta tattaro ta taho.

Umma da Fareeha sukayi jugum jugum aka rasa mai magana a cikinsu. Kukan Ahmadi ne ya dawo dasu daga kogin tunanin da suka fada. Aunty Mami ta karbeshi ta fara bashi nono.

Umma ta kalli su Inayah da Khulsoom tace "Ku tashi kuje kuyi brush ku kwanta. Gobe akwai makaranta". Babu musu suka miqe suka aiwatarda aikin da ta saka su. Fareeha itama dakin ta nufa domin bataga amfanin zamanta a falon ba.

Tana jinsu Khulsoom da Inayah a bandaki suna ta kiciniyar yin brush. Ta bude wardrobe ta dauko musu kayan baccinsu. Suna fitowa suka sanya kayan bacci suka hau gado sukayi addu'a.

Fareeha ta shiga bandakin ta wanke uniform dinta da dazun ta jiqa. Sannan itama tayi brush din. Ta fito falo da bucket din a hannunta. Umma da Aunty Mami sun shiga daki. Har yanzu tana jiyo kukan Aunty Mamin.

Ta fita waje ta shanya Uniform din nata a igiya. Ta dawo da datse kofar falon da mukulli domin kuwa Ya Bilaal bashida niyyar shigowa gidan a yau. Ko yana dashi ma ba sai 'yan sanda sun sake shi ba? Ta tsaya tana tunanin leqa dakin Umman domin tai mata sai da safe amma sai ta kasa domin bata so ta shiga ta sake kallon fuskar Aunty Mamin. Wani tausayinta ya qara kamata.

Ta koma dakinsu tayi shirin bacci. Ta hau gado domin yin baccin amma hakan ya gagara. Tunani ne fal a cikin qwaqwalwarta. Wai shin duniyar nan ina zata damu ne?.

Washegari da misalin qarfe shida da kwata na safe Bilaal ya shigo gida. Kana ganinshi zaka san ba'a hayyacinsa yake ba. Wani wari ne ke fita daga jikinsa. Fareeha dake tsaye a bakin famfon tsakar gidan tana tarar ruwa a bokiti saida taji amai yana qoqarin zuwa mata a lokacinda ya gifta. Ta runtse idonta tareda dora hannayenta akan qirjinta duk dan wai kar tayi aman.

Dakinsa ya dosa wanda ke can lungun tsakar gidan. Kafin ya qarasa kuwa ya yanke jiki ya fadi. Gaban Fareeha yayi saurin bugawa domin taji tsoro ba kadan ba. Maimakon ya miqe ya shiga dakinshi sai kawai ya gyara kwanciyarsa a wajen, ya fara bacci.

Aka turo qofar falon nasu. Umma ce ta leqo sanye da hijabi a jikinta da tasbaha. Ta tsaya tana kallonshi, zuciyarta tana quna. Wasu hawaye sukayi barazanar zubo mata amma sai ta tuno cewa Allah yayi alqawarin zai jarraba bayinsa ta hanyar dukiyoyinsu ko 'yayan su. Ita ga nata jarabawar kuma.

Ta nisa. Allah ya bata ikon cin wannan jarabawar. Ta share digon hawayen daya zubo mata kafin ta qarasa wajen shi.

Ta duqa ta kamo qafafunsa guda biyu ta jashi har cikin dakin. Wasu hawaye masu zaafi suka zubo wa Fareeha. Ta dauki bokitin ruwan tayi kitchen dashi. Anan ta tsuguna tayi ta kuka mai isarta. Mai yasa Ya Bilala bazai duba halin da Umma take shiga ba saboda shi bane? Ko dan ita ma yakamata ya nutsu ya daina shan miyagun qwayoyi.

Saboda sake nauyinshi dayayi gaba daya, hakan bai bawa Umma damar dora shi akan katifar sa ba. Don haka a shimfide a kan kafet din dakin ta barshi. Ta dan kalli dakin. Komai a hargitse yake, abun har ya bata qyama.

Ta dauko pillow ta tallafa daqyar ta daura masa kansa akai sannan ta lullube shi da wani tsohon bedsheet din data ci karo dashi a dakin.

Ta sake kallon dakin kafin nan ta hau tattare dakin. Duk wasu qullin ababen shaye-shaye saida tayi waje dasu. Da kwalaben maganin tari ne da wasu pills duka ta watsar. Ta share dakin tas! sannan ta fito.

Lokacinda ta koma cikin falon, su Qulsoom sunyi wanka sun shirya tsab cikin uniform dinsu. Suka gaisheta ta amsa ba yabo babu fallasa sannan ta qarasa dakinta.

Fareeha ta shigo da tire a hannunta. Kofunan shaayi ne guda uku akai sai wani dan mitsitsin biredi wanda da dukkan alamu bazai ishesu ba. Ta ajiye a gabansu.

"Maza kuci sai mu tafi makaranta" ta fadi bayan ta miqawa kowa kofin sa.

"Adda wannan biredin fa ya mana kadan" Qulsoom ta fada tana zumbura baki.

Fareeha tayi murmushi " Toh gashi kici harda nawa. Ni na fasa ci"

Inayah ta kalleta "Adda meyasa zaki bar mata?"

"Idan ana cin abinci ba'a magana. Oya kuyi sauri kar muyi latti"

Daga nan basu qara cewa komai ba.

Umma ta kalli Anti Mami dake duqunqune akan sallayar da tayi sallar asuba akai. Tausayin qanwar tata ya kamata.

"Mami, ya kamata ki tashi ki kimtsa. Kwanciyar nan ba abinda zai haifar miki"

Anti Mami tayi shiru bata amsa ba. Ahmadi dake kwance akan gado ya danyi motsi. Can kuma ya fara kuka wee-wee-wee. Umma ta daukeshi a hannu tana jijjiga shi amma yaqiyin shiru.

"Mami yunwa yakeji fa. Dan Allah ki tashi ki bashi abinci"

Mami ta miqe zaune. Idanunta sunyi luhu-luhu alamar tasha kuka.

"Umma nikam idan na yaye yaron nan yanzu nayi laifi?"

Umma ta zare ido. "Bakida hankali ne? Kwata-kwata watan sa nawa? So kike ya mutu?"

Mami ta fashe da wani matsanancin kuka.

"Toh Umma ya zanyi. Ta yaya zan raine shi ni kadai? Ba gwara na yaye shi ba na maida shi wajen ubansa ba? Zai samu kulawa acan Umma. Ko da kuwa za'a tsangwame shi saboda uwarsa bata gidan, nasan zaije makaranta mai kyau kuma zaici mai kyau yasha mai kyau....." Wani kukan ya qara zuwa mata ta kasa qarasa maganar tata.

Umma ta durqusa ta ajiye mata Ahmadi akan cinyarta.

"Mami shin wai Islamiyyar da kikaje duk a banza ta tafi? Kin manta da qaddara ne? Ko kuwa kin manta maganar Rabbil Izzati dayace Fa 'inna ma'al usri yusra? Ya kuma qara da Inna Ma'al usri yusraa. Allah ya mana alqawarin sauqi a yanayin tsanani. Don haka ki daina tada hankalinki. Allahn daya baki Ahmadi, shi zai baki ikon ciyar dashi da tufatar dashi da bashi ilmi mai amfani. Kuma ma naga ubansa ba mutuwa yayi ba yanada ransa. Toh yanzu da maraya yake fa? Ina zaki kaishi?"

Kalaman Umma suka sosa mata zuciya har ma ta daina kukan.

"Don haka inaso ki rungumi qaddara ki cigaba da addu'a. Insha Allah za'a samo bakin zaren. Idan Abbansu Bilaal ya shigo zan masa maganar tunda shine waliyyinki sai ya kira Mukhtar din suyi magana. Ki dena kuka kinji?" Ta dafa hannunta akan kafadar Mamin. Mami ta gyada kai tareda share hawayenta.

"Nagode Umma. Allah ya saka da alkhairi."

Umma ta mata murmushi kafin nan ta miqe ta fita.

Mami ta kalli dan jaririnta wanda har ya fara baccin wahala. Ta tallabo shi ta fara bashi abinci. Nan kuwa ya farka ya fara sha. Ta shafi kansa a hankali.

"Allah maka albarka Ahmad".

Su Fareeha basu dade da tafiya makaranta ba Abbansu ya shigo sashen nasu. Daman Umman ta aika masa saqo a waya cewar idan zai fita akwai wata maganar daza suyi.

Umma na zaune a falon tana jijjiga Ahmadi domin yayi bacci sai ga Abban ya shigo ko sallama babu. Ya tsaya a kanta.

" Gani nan. Ya akayi?"

Ta yi ajiyar zuciya. "Ina kwana Abban Bilaal?"

Ya yatsine fuska. "Lafiya. Nace menene kike nema na?"

"Bazaka zauna ba?" ta tambayeshi a hankali.

"Sauri nakeyi." Ya bata amsa kai tsaye.

"Toh idan ka dawo mayi maganar"

Ya kalleta a wulaqance. "Inada tafiya zuwa Hadejia bayan Azahar. Don haka koma meye zaki fada ki fadeshi yanzun nan. Ba lallai ki sake ganina ba nanda kwana hudu"

Wani abu ya tokare mata wuya. Wato sai ranar girkinta zai tsiri tafiya? Har na tsawon kwana hudu? Kuma idan ya dawo ya wuce wajen Mariya ko?

Ta gyara zama tareda rungume Ahmadi wanda tuni ya fara bacci.

"Dama Mami ce tazo jiya da daddare bayan ka kwanta. Sun dan samu matsala ne da maigidanta shine ya ce ta dawo gida. Shine nace ko....."

Yayi saurin katseta "Yace ta dawo gida? Kaman ya?"

Da qyar Umman ta iya furta "Ya saketa ne"

Abba yayi qwafa. "Toh don ya saketa sai ta dawo nan? Me take nufi kenan?"

Umma ta kalleshi cikeda mamaki.

"Abban Bilaal ina zataje idan ba nan ba?"

"Ubanta bashida gida ne?"

Maganar tasa ta sosa wa Umma rai ainun. Sarai yasan cewa Mahaifinsu ya dade da rasuwa kuma gidan ya zama na gado. Dayake abubuwanda ya bari a matsayin kadara ba wani abin azo a gani bane don haka bayan duk yaran gidan sunyi aure sai aka sanya gidan a haya. Duk bayan shekara ana raba kudin hayan wa 'yayan.

Umma ta daure fuska.

"Abban Bilaal wace irin magana ce wannan?"

Ya kalli agogon hannunsa. "Malama kina baata min lokaci. Ke kanki kinsan banida qarfin ciyar da Ku balle kuma an qaro mun wata. Kice mata ta tattara kayanta ta nemi gidan ba wannan ba. Na bata nan da kwanaki hudu kafin na dawo."

Yana gama magana ya zaro wata yamushashshiyar dari biyar ya ajiye mata a kan kujera.

Ta kalli kudin sannan ta bishi da "Angode. Allah ya kiyaye hanya"

Bai bata amsa ba yayi ficewarsa.

Idonta akan kudin. Ko me dari biyar zai musu? Rai har shida? Allah ya kyauta.

Mami ce ta fito daga dakin idonta taf da hawaye. Itai dai ba labewa tayi ba domin taji maganar su amma yanda Abban yake daga murya yana hayaniya zaiyi wuya maqota ma baza suji abinda yake fadi ba.

Gwiwowinta biyu a qasa ta sa sannan ta fuskanci Umma.

"Umma ina zanje?" Tambayar data mata kenan.

Umma ta kalleta cike da tausayinta.

"Mami ba inda zakije. Nan gidanku ne"

"Umma kinajin abinda yace fa." Hawaye suka fara sintiri a kan kuncinta. "Kwana hudu kawai ya bani" ta fashe da kuka.

Umma ta gyara wa Ahmadi kwanciya a kan cinyanta sannan tayi ajiyar zuciya.

"Ina sake tuna miki cewar Rabbil Izzati baya bacci. Yana sane dake da kuma danki. Don haka ki sallama mishi komai. Da ikonSa komai zai dawo dai-dai. Inaso ki kwantarda hankalinki kuma ki dena wannan koke-koken domin babu abinda zai haifar miki. Ahmadi yana buqatarki a haalin yanzu don haka ya dace ki tattaro duka nutsuwarki ki bashi kulawa. Kisan cewa Allah zai tambayeki ranar gobe qiyamah idan baki kula dashi ba. Mami, kiji tsoron Allah."

Da wannan ta tashi ta barta a wajen. Dakinta ta shiga ta kwantarda Ahmadi akan gado. Zama tayi a gefen gadon ta sauke ajiyar zuciya.

Innalillahi wa inna ilaihi raajiun kawai take ta furtawa.

*******
So how was the first chappy? Long right? I'd love to hear your opinions.

Taku a kullum,
Mairose.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top