JAWABIN MARUBUCIYA
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barkatuhu.
Ina mana maraba hade da fatan alkhairi. Da fatan anyi sallah lafiya.
Gani na dawo muku da wani labarin da kamar kullum ban san abunda zai kaimu ga cimmawa ba. Amma in sha Allah ina sa ran mu amfana da darrusan dake ciki mu kuma nishadantu.
Ba zan ce labarin MAIMAITA TARIHI ya fita daban ba, domin a hangen farko yayi kama da labari sassauka na yau da gobe, amma tabbas zan iya cewa MAIMAITA TARIHI ya taho mana da sabon sako. Allah Yasa ya samu karbuwa yanda ya dace.
Abu na gaba da nake son fada shine, wannan labari ne da zai rinka zuwa jifa-jifa ba kullum ba ko bayan kwana bibbiyu yanda sauran labarai na suke zuwa muku a wattpad. A hankali muna nisa ina kara yawan rubutun sai a sake samun yawan updates.
Don haka idan an ga na bada tazarar kwanaki, a saurara update na zuwa da yardar Allah.
Kamar kullum ina fatan samun goyon bayanku a wannan tafiyar da zamu fara.
Da fatar kun shirya haduwa da juyi-juyi na rayuwa? Domin abunda za a fuskanta a ciki kenan kamar kullum. (Uwar dukkan wani rikirkicewa 😜)
Da wannan nake so na ce muku wasu daga cikin babin labarin nan ne za a samesu a wattpad kyauta sauran na sayarwane inda za a samu dunkulallen labarin a matsayin littafi guda akan manhajar okada. Wanda zanyi bayanin yanda za a saya a karshen wannan littafin in sha Allah.
Ma'assalam.
Umm Yasmeen 💞
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top