BABI NA TARA
BABI NA TARA
ASSALAMU ALAIKUM,
EHEM EHEM 🙊
***AGUSTA, 1994
Wai ance karshen tikatuki tik! A safiyar yau dai cikin gidan Ambasada Usman Muhammad ya cika dam da 'yan uwa da abokan arziki domin bikin daurin auren Sufyaan da Maryama-Siddiqah. Wannan rana ta Asabar ta shiga kundin tarihinsu. Ranar da suka zama ma'aurata a idon duniya gaba ki daya.
Cikin gida dai ana ta hidima, a ci a sha a dauke.
Yayin da amarya take ta daukar hotuna da 'yan uwanta. Ana ta farin ciki har dai zuwa lokacin da goggoninta guda uku da yayun Hajja Nenne biyu suka saka amarya Siddiqah a gaba a dakin Hajja Nennen.
Kowaccensu ta dau lokaci mai tsawo tana mata nasihar zaman aure. Duk abubuwan da suka fada yawanci ta taba jinsu, amma yanzu da suke fada a dalilinta sai taji gabaki daya zuciyarta ta yamutse, kamar zata sare tace ta fasa a barta a gida. Bama kamar karamar cikin goggonin nasu, Dada, wacce ta fi kusanci da Siddiqah a dalilin son mutanenta.
Sai nanata wuta da aljanna Dada takeyi, da azaba da wuya da dadi da kuma hakkoki. Gaba ki daya sai da Siddiqah ta ji kamar ta ruga waje tace a tsayar da masu daurin auren su kunce. Daga karshe dai tana kuka sosai Raliya ta rikota suka wuce falon Baba, amma ganin yanayin da take ciki yasa Ambasada yayi murmushi yace, "Maryama ko ace masa ya tafi ne, ba yanzu ba? Gashi da kuwa har ya iso daukar ki, amma tunda ba kya so..."
Ware idanu tayi ba wai don jin za a ce Sufyaan ya tafi ba, sai don ji da tayi ance yazo daukarta.
"Baba daukana kuma?"
"Eh, Raliya, shiga ki fada musu a gama kimtsawa nan da awa daya, mijinta yana nan jiranta zasu tafi. Kunga doguwar tafiya ce a gaban su."
Siddiqah kam gwiwowinta biyu ta saka a kasa ta shiga kallon mahaifinta da 'yar uwarta cikin kidima. "Amma Baba an shirya masu kai amarya, cikin gidan a cike yake da mata masu son raka amarya." Ta ma mance a gaban wa take maganar ita dai kar a dauke ta.
"Banda abunsu a cika motoci aje rakiyar amarya, wani dawainiya zaku kara musu? Babu wanda zai raka amarya sai mata daya, na fadawa Gaggi zata shirya ta rakata. Idan ta dawo daga baya duk mai son zuwa duba Siddiqah a dakinta sai yayi zuwan kansa ya dubota. Amma tsarin mijinta shine, shi zai tafi da matarsa."
A wannan lokacin ne Siddiqah ta kara rushewa da kuka, shikenan ana cewa aure na dauke 'ya mace daga gidansu. Ganin karshen ma ba a za a bari tayi wa danginta ba, su je suga gidanta suji dadi a zo a fadawa Hajja Nennenta.
Ambasada ya dago kai ya dubi Raliya, yace "Jeki ki barni da ita."
Duk da hayaniyar cikin gidan bai hana Ambasada ya samu guri ya zauna ba, yace "Maryama, bude fuskar ki ki kalleni da kyau. Gashi, karba..." Robar ruwa ya mika mata sannan ya bata hankici yace ta goge fuskarta, sai da ta natsu ta daina kukan tukunna ya fara bayani.
"Bana son ki tashi hankalinki akan komai. Yau an daura aurenki, kuma ina so na shaida miki cewa daga wannan lokacin wani jayayya ko gardama da mijinki ba naki bane. Tsakaninki da shi kyautatawa da kuma bin umurninsa muddin ba akan abunda Allah Ya hana bane. Wannan shine abunda nayi ta fada miki tun ba yau ba. Kuma shi kika tashi kika ga iyayenki na yi.
"Kada ranki ya baci, in sha Allah kinyi dace da mutum mai karamci. Kuma kema ina alfahari da kyawawan halayenki, na san bazaki bawa kowa kunya ba, na san a nan inda muke watarana mijinki zai zo yayi godiya bisa halayenki na kwarai. Don haka ki kiyaye daga yau dinma kiyi yanda yake so, kinji ko? Ba komai bane wadannan abubuwan sai al'adunmu na gida ba addini bane bare ranki ya baci don ba ayi yanda ya kamata ba. Da kaina zan kawo miki Hajja Nenne har dakinki ta ganki kuyi hira idan tana jin yin hira ranar."
Lokacin ne Siddiqah tayi dariya cikin shesshekar ta sannan ta gyada kanta, "Na gode Baba, Allah Ya saka da alkhairi."
"Yauwa ko ke fa? Dakata bari na baki sakonki."
Ta dan saurara Baba ya tashi ya shiga ciki sai gashi ya fito, yana zama ya mika mata wasu kudade sannan yace, "Sakon Sadakinki ne daga hannun Sufyaan. Allah Ya baku zaman lafiya. Ki shiga ciki ku kimtsa, sai ku fito."
Siddiqa ta sa hannayenta biyu ta karba tana godiya.
***
Umma Gaggi na tsaye a kanta sai da aka saka mata dafaffen ruwan danyen ganyen lalle da magarya wanda aka surka da ruwan madarar turare ta shiga ta sake wanka, aka bata sababbin kayanta dinkin atamfar holland mai launin ruwan ganye da daurawa mai ratsin fari-fari ta saka, sannan aka shafe ta da turaren bakhoor mai sanyin kamshi. Lallenta yayi duhu a hannayenta da tafukan kafafunta sai sheki yakeyi.
Dankunnayenta wasu fararen seti mai kanana duwatsun da suke sheki aka zaba ta saka. Raliya ce da kanta ta nada mata lafayar ta a jikinta bayan Salmah ta kafa mata daurin da ya taho baya ya tokare, yanda koren lufayar zata zauna da kyau a saman kanta.
Fuskarta babu komai sai kwalli da hoda da man baki, amma ta fito das da ita.
Tana shigowa tsakar gida kuwa aka fara ribibin leken amarya. Tunda daga nan suka sauke mata rufin fuskarta ta yanda gurin da zata saka kafafunta kawai zata iya kallo.
Dakin Hajja Nenne kawai aka kaita ta mata addu'o'i ta kara jaddada mata hakuri musamman da zata je kan wata. Ta bi a sannu ta bi tsarin gidansu ta yi biyayya ga mijinta. Sannan tayi sallama da sauran matan da kannenta a tsakar gida. Abu kamar a fim, kan ace haka da haka wai har an dau hanyar shiga mota da ita.
Kofar wata farar Marsandi aka bude mata a waje, ita aka fara sakawa a cikin motar a gidan baya.
Kowa sai dagelgel yakeyi ana mika wuya daga kan dakalin kofar gidan don son a hango angon da aka ce shi da kanshi zai dauki amaryarsa.
Sai da ya sa hannu ya rufe marfin motar. Bayan an saka Siddiqah a ciki ne ta kyafta idanu, jin kamshin turarensa da tayi. Duk inda kamshinsa yake a duniya kuwa ita mai tantancewa ce. Bata ida mamakinta ba ya bude gurin zaman gefenta ya shiga ya zauna.
Direban da zai ja su kuma ya shiga gurin zamansa aka karasa sallama. Tunda taji muryar Sufyaan yana sallama da yayunta da suke kofar gidan ta dauke tsammanin shigowar Umma Gaggi motar kamar yanda aka ce mata zata mata rakiya.
Ga tabbacin dai shine a zaune a gefenta. Yaya akayi? Ina Umma Gaggin... Ta fara waige-waige da neman dabarar daga mayafinta na lufaya ne don ta leka abunda yake faruwa sai taji muryarsa mai zurfi daga gefenta yace, "Ki kwantar da hankalinki, zasu biyo mu a dayar motar."
Baki ta bude zatayi magana, sai ta rasa abun cewa.
"Malam Jibrin, bismillah, zamu iya tafiya."
Da misalin karfe hudu na rana suka dauki hanyar Jabbi Lamba da ita da sabon angonta, tare da sanin cewa yanzu amanarta tana karkashinsa, tare da fatan zai rike alkawarin Allah da ya dauka gaban shaidu na rike ta amana har iya karshen rayuwarsu tare.
"Sai nayi budan kai ne a nuna min fuskar Mar'yam di ta?" Muryarsa da taji kasa-kasa kusa da itane yasa taji wani abu ya tsirga mata daga tsakar kai har tafin kafafunta.
Da sauri ta daga kanta ta bangarensa.
"Kar zafi ya dame ki, bude fuskarki, mu biyu ne kawai babu me kallonki."
Maimakon tayi hakan sai ta samu kanta da tsumewa. Sai da ta jira ya sake magana sannan ta dan bude fuskarta dai-dai gwargwado ta juya tana kallon wajen taga, suna kutsawa cikin gari wurin neman hanyarsu ta fita daga garin Gombe inda zata bar tsohuwar rayuwarta ta fara sabuwa.
Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Me ake cewa na taya farin ciki bayan aure da larabci?"
"Nima ban sani ba." Ta fada da iyaka kokarinta na ganin bata nuna masa rashin jin dadinta ba na hana ta tafiya da Umma Gaggi. Yanzu haka su Baba kaf suka ganta dashi a bayan mota, haka zasu isa garinsu kowa ya ga sun fito tare, wane uwar kadadi. Farawa da bismillah kenan.
"Mar'yam fushi kikeyi dani?"
"Ka bar maganar kawai," ta fada a dakile.
"Hakan ne kenan. Juyo ki dubeni."
Tsam tayi taki ta bari muryarsa ta shafe ta. Amma ta san a gaban hadiminsa bazata iya gwasale shi ba. Don haka ta juyo ta furta masa ba yanzu ba yanda zai karanta a bakinta ba tare da sauti ya fito ba, hade da masa nuni da gabansu, alamar wanda ya kira da suna Malam Jibrin na iya jinsu.
Bai sake ce mata komai ba har suka bar cikin gari. Ita kuwa jin shirun da kadaici ya kara sawa taji kewar gida sosai. Gashi ta bar duk danginta a baya, wacce ta sani kwalli dayan ma an raba masu mota, ba tare da sanin daga ina ba kawai ta samu kanta da sheshshekar kuka. Tana ji Sufyaan ya dan kame a gefenta bata kirga iya lokacin da suka dauka a hanya ba sai ji tayi yace "Malam Jibrin idan mun dan matsa gaba kadan ka tsaya."
Bata ko kalli gefen da yake ba har sai da taji suna tsayawar da gaske. Bayan Malam Jibrin ya tsayar da motar, fita yayi daga ciki ba tare da Sufyaan yace masa komai ba.
"Siddiqah?" Yau kuma abunda zai kirata dashi kenan? Sai yayi tayi ai. Bazata kula shi ba kuwa.
Hannunsa ya sa a cikin nata a karo na farko tun saninta dashi. Sai da ta kusa shidewa saboda ya dauketa ba zata. Daurewa tayi ta runtse idanunta taki ta sake daga ido ta kalle shi ballantana fararen babbar rigar da ya saka domin daurin aurensu ya kawata mata shi a idanunta ta rasa mallakar kanta a gabanshi.
"Na so mu tafi a mota daya saboda akwai muhimman abubuwan da nake so mu tattauna sanin cewa idan mun isa bazamu samu lokaci ko sararin kebewa muyi maganar ba. Sai na fahimci ranki ya baci da yanda na tsara mana tafiyar. Idan kina so ki koma daya motar gasu nan sun tsaya a bayanmu, ba komai. Ki je ki, zamu yi maganar daga baya."
Shiru tayi tana auna maganarsa, sai ta fahimci shi din ya fita gaskiya, don haka ta dan turo bakinta gaba alamun dai ba wai saduda tayi ba, hakura tayi.
"Ba komai, mu tafi kawai." Ta fada kasa-kasa.
"Kin tabbata?"
Kanta ta gyada masa sannan yace "To da sharadin zaki daina kuka a motar nan, idan ba haka ba kuma zaki sa na rarrasheki a gaban Malam Jibrin."
Ware idanunta tayi, ta kara takurewa a jikin kofa, duk da cewa hannunta har yanzu yana cikin rikon na Sufyaan. Dariya yayi, sannan yace "A fada min amsar tambayata kuma."
Girarta ne suka tattare kafun ta tuno tambayar da ya mata dazu. Dan guntun murmushin gefe ta masa sannan ta amsa masa a sanyaye, "Mabrook."
Kankance idanunsa yayi yana mata kallon tuhuma.
"Meye? Da gaske haka ne."
"Koma dai menene, Allah ya karawa muryarki aminci. I love your voice, Mar'yam. Banki ki ci gaba da magana ba ko da mabrook kawai zakiyi ta fada." Kafun kalamansa su karasa ratsata, ya dan murza saman yatsunta sannan taga ya dubi waje. Amma bata kula da me yayi ba har Malam Jibrin ya fahimci sun kammala magana ba sai gani tayi an bude motar cikin sallama an shigo an tayar. Duk da ya dan bata sararin shan iska, ko kadan bai nuna alamun zai sake mata hannu nan kusa ba.
"Kamshinki ma haka." Ya rada mata daf kunnenta. Nufinsa yana son kamshinta ma. Eh tabbas da niyyar hallakata ai ya fito yau da safe, da ya fadawa Babanta haka ai da ba aje da nisa ba bare yayi nasara, da tayi zamanta a gidansu kawai kowa ya huta. Sai da ya gama kassarata da rade-radensa sannan ya juya ya fuskanci gabansa cikin kamewa tamkar ba shi bane yanzu ya gama hautsina mata duniyarta ba.
Sai da suka kara nisa sannan tace masa "Kace zamuyi magana."
"Ah! Maganarmu. Kar ki damu anjima kadan, in sha Allah."
***
Kofar gidansu Sufyaan abunda ta yi zato ne har ma fi. Ko da wasa iya labarin dayake bata bata taba tunanin akwai irin wannan gidan a irin kauye haka ba. Sun wuce wani wuri inda Sufyaan ya ce mata Sabon Gari sunan gun, sannan Wuro Modi kafun a farkon shigarsu garin Jabbi Lamba suka tarar da wani gidan mai a bakin hanya. Suna tafiya tana duban yanda kowa yake harkokinsa na yau da kullum, daidai tsakiyar garin suka tadda kasuwa inda shaguna suke jere akan hanya. Kowa na hada-hadar komawa gida domin duhu ya kawo kai. Wasu masallatai sun fara kiraye kirayen sallah.
Mutane akan mashin sai kai kawo sukeyi irin dai yanda ake zirga-zirga idan almuru ya kawo kai dare ya fara shiga.
Tafiya kadan suka kara suka shiga kwanar dama inda suka tarar da wani gida a bakin hanya mai farin fenti da bakin get. A hankali ta lumshe idanunta ta bude akan gidan. Ko da wasa bata kawo wa ranta nan zasu zo ba.
Zamananci gidansu Sufyaan yafi gidansu nesa ba kusa ba, duk da kuwa suma gidansu ana sashi a sahun gidaje saffa-saffa a garin Gombe. Tabbas taga alamar sa hannunsa a aikin tsara wannan gidan, domin ta san sai inda karfinsa ya kare wurin tabbatar da cewa masu yin sa sun bashi abu mai inganci kuma saukakka.
Sai dai madadin cincirandon jama'ar da tayi tsammani zasu samu a kofar gidan babu hakan, sai ma gefe dasu kadan inda mutane suke ta faman alwala cikin shirin sallar isha'i, butoci ne zube a harabar masallacin dake kofar gidan. Get aka bude masu inda Malam Jibrin ya soka hancin motar zuwa ciki.
Kafun su karasa tsayawa ya rada mata, "Idan kina so zaki iya rufe fuskarki kar su dameki."
Ai ba sai ya sake fada ba, tun kafun matan da suka doso motar tasu su iso inda suke a cikin mota, Siddiqah tayi saurin rufo saman lufayarta. Sai barka ake musu da isowa. Dakika kadan bayan shigowarsu, motar su Umma Gaggi ma ta shigo harabar gidan.
Ita ta sauko tukunna sannan ta tsaya a gangan Siddiqan, kafun wasu mata su iso su musu jagora zuwa cikin gidan.
Daga lokacin dai ta samu Sufyaan ya bar ganganta. Nan aka shiga da ita wani dogon falo wanda suka bulla ta ciki suka samu babban falo inda wasu mata ke zazzaune, sun kewaye wata dattijuwa fara tas ta sha mayafi na alfarma, hannunta rike yake da carbi tana ja. Da alama sun idar da sallah ne bata tashi ba a gun.
Masu guda nayi, masu cewa a bude fuskar amaryar su gani suna yi. Masu yiwa Sufyaan tsiya suna yi cikin mutanen da aka fi kira abokan wasa a al'adance.
Gaisuwa taji yana tashi a tsakani, Umma Gaggi ta amsa gaisuwar aka musu ban gajiya, sannan akayi addu'a sai lokacin aka bukaci a bude fuskarta, ita dai bata san yaya zatayi ba, don haka bata nemi ma ta dagawa kowa gaisuwa ba har yanzu kanta yana kasa.
Hakan yasa taji Hajiyar Sufyaan tayi fulatanci, tana cewa a shigar da ita ciki ta huta tukunna sannan su gaisa.
Hakan kuwa akayi aka sake debansu. A wurin saka takalma ne ta fahimci wacce take musu jagoran itama kamanninta sak Sufyaan amma ita fara ce tas, wannan yasa tayi kama sak da mahaifiyarsu.
Tafiya mai dan tazara sukayi kadan suka shiga wani get sannan aka wuce wata kofar ana isa kofa ta biyu taga an bude. Zuwansu nan bangaren ba a biyo bayansu ba kamar shigowarsu gidan. A ciki aka gabatar musu da abincin amarya da daki mai dauke da bandaki a ciki. An basu abun sallah sannan aka janyo musu kofar aka rufe. Siddiqah ta tsinkayi matar da ta kawo su wannan bangaren tana cewa wata budurwa ta tsaya a falo ko da zasu bukaci wasu abubuwan.
Ko ina sanyi da kamshi yakeyi an seta na'urar sanyaya daki yanda bazai musu yawa ba.
Ko da suka shiga cikin dakin da aka nuna musu, ta samu an shigo musu da jakukkunansu, biyu nata daya karamar ta Umma Gaggi kasancewar gabaki daya sauran kayanta, an wuce mata dasu Kano.
Kamar yanda dazu a mota Sufyaan ya shaida mata washegari zasu wuce Kanon da safe suma.
Sai da ya gama ja mata rai sannan ya sanar da ita ta kwantar da hankalinta, ta sawa ranta tamkar daga gidan Baba wani gidan Baban zata shiga, domin zai yi iya kokarinsa na ganin cewa ya kare mata martabarta amma sai tayi kokari ta taya shi yin hakan. Ya sanar da ita gun Hajiyarsa zai kawota su gaisa sannan su wuce Kano inda zata ga gidanta kafun su sake daukar hanya suyi wata tafiyar.
"Da fatan kina da juriyar zaman mota?" Ya tambayeta a karshen jawabinsa.
Karamin murmushi tayi sannan tace masa, "Zamu gani."
Bai matsa mata da surutai ba bayan fada mata sunayen garuruwa da kauyuka da yayi tayi a hanya tsawon tafiyar da sukayi na awanni. Bai dago mata maganar Amina ba ita ma kuma bata tambayeshi ko zasu hadu a nan ba ko kuwa sai a Kano.
Alwala suka fara yi suka yi sallolin maghriba da isha', sannan Umma Gaggi tace "A zubo miki abincin yanzu ki taba kafun a fara shigowa ko?"
"Cikina ya toshe Umma, barshi kawai sai anjima."
"Gajiyace, ko dan anjima sai ki daure kici kar yunwar tayi miki illa. Ga kayan marmari ko shi za a baki ki taba?"
Siddiqah ta san matan gidansu sarai yanda basa wasa da bawa yaransu abinci don haka ta san Umma Gaggi bazata taba barinta taji abunda takeji dashi ba har sai taga ta sa wani abu a cikinta. Wannan yasa ta karbi kayan marmarin ta dan taba kadan.
Ji takeyi kamar kayan cikinta zasu juye saboda taraddadi da rashin sanin abunda zai faru.
Suna sauraron azo ace su isa su gaisa da Hajiyar bayan sun gama hutawa sai gani sukayi Hajiya Amina ta shigo bangaren da kanta. Mata uku ke biye da ita, hayaniyar cikin gidan ya dan lafa ba kamar shigowarsu ba.
Siddiqah dai na lullube har kai, fuskarta a bude ta gaida su. Hajiya Amina tayi mata maraba hade da addu'o'i, batayi wata doguwar Nasiha ba illa cewa da tayi Allah Ya saukaka mata yin ibadar aure. Ya bata ikon bin mijinta yanda ya dace, ya kuma sa mata aminci a rayuwar da zatayi dasu Ya hada su da alkhairin juna.
Basu dade ba suka wuce.
Sai wuraren karfe sha daya da kwata Sufyaan yayi sallama a bangaren da suke, Umma Gaggi tana zuba gyangyadi a falo taji sallamar, ba shiri ta farka.
"Yaya gajiyarku, Umma?" Sufyaan ya tambaya yana zaune daga kan kafet bayan ta bude masa kofar ya shigo.
"Alhamdulillah, gajiya tabi lafiya."
"Ai hanyar tamu sai hakuri, ita take kara gajiyar tafiyar. Babu dai wani abu ko?"
"Alhamdulillah babu komai, yanzu su Hajiya suka tashi. Asma'u da Jamilah sun tabbatar bama bukatar komai sannan suka bar nan."
"To, alhamdulillah. Ban san ko kunyi maganar da ita ba, da safe idan Allah Ya kaimu zamu wuce Kano. Idan kin karasa hutawa, nayi magana da wanda zai mayar dake Gombe koda zuwa jibi ne, in sha Allah."
"To, jibi kuma? Goben ma ai yayi. Nisan da sauki ai. Tunda mukaje Birnin Kebbi ai sai wannan din naji shi da sauki."
Sufyaan yayi dariya. "To madallah, mun gode sosai Allah ya kara girma da lafiya."
"Ameen ameen."
"Sai da safe." Ya fada yayinda Umma Gaggi tayi caraf tace "Bari ayi mata magana mana yanzu ta tashi itama a nan din."
"A'a a barsu kawai idan sun shiga ne." Ya fada cikin sadda kai.
Umma Gaggi bata bi ta tasa ba ta mike da dan hanzari ta shiga cikin dakin da sukayi masauki domin kirar Siddiqan. Duk da taji yana cewa a barta kawai, ta san ai ba ita ya shigo sallama ba, matarsa ya zo gani.
"Tashi kije mijinki na falo yana jira."
Siddiqah kam sai da ta sha jinin jikinta amma bata bari hakan ya nuna ba, ta saka hijabin da sukayi sallah dashi sannan ta fito falon gurin Sufyaan.
Zama tayi a kafet ganin yana zaune saman kujerar da tafi kusa da bakin kofar fita.
"Anya za ayi tafiyar goben nan kuwa? Naga duk kin gama laushi daga yau."
Murmushi tayi sannan tace "Idan nayi bacci ai kawai shi kenan."
"To yayi kyau. A huta gajiya. Zanyi kokari zuwa karfe goma mu kammala da nan mu wuce in sha Allah. Babu komai ko?"
Kai ta gyada masa tace "Allah Ya kaimu."
"Yaya sashin naki yayi miki?"
Dama nan gaba daya sukutum din shi yake ta kira a matsayin dakinta? Ai wannan gida ne mai zaman kansa, tunda ga falo, ga babban madafi ga kofofi biyu da ta gani a rufe, wanda take kyautata zaton dakunan barci ne idan an hada da wanda suke ciki da Umma Gaggi guda uku kenan da wata rufaffiyar kofar da bata san ta mecece ba. A tunaninta nan ne gidansa na garin nasu. Ashe wai nan ne gaba ki daya nata dakin. To idan bai mata ba ai sai dai a kirata da butulu.
"Yayi, na gode. Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen, amma mun kusa mu fara fada idan kika faye yawan cewa kin gode."
Fara'arta ce ta fadada kawai kanta na kasa. Ya ce mata "Mu kwana lafiya."
Ta daga kai domin ta amsa kawai sai taji duminsa a kusa da ita, a hankali ya duka ya sumbaci saman kanta hade da shafar gefen fuskarta sannan ya fita.
Ta dade tana zaune a gun cikin tattaro bakin al'amuran da suka rinka faruwa da ita a yinin yau, sai taga haka zata kwana a zaune a gun bata fayyace me takeji a tattare da ita ba.
Numfashi ta sauke sannan tabi gurbin da ya shafa da nata yatsun ta lumshe idanunta kafun ta samu ta mike daga gun da ya barta. Tunda ba fahimtar komai zata iya yi ba, sai ta shiga ta watsa ruwa ta saka doguwar riga mai manyan fulawowi wanda ya faye laushi sannan tayi addu'a ta bi lafiyar gado.
Kamar yanda ta tarar da Umma Gaggi ta dade da lulawa nan tsakiyar kilishin dakin ko lullubuwa bata yi ba sai da Siddiqan ce ta shigo ta dan rufeta da mayafin da ta gani ajiye a bakin gado. Saboda ta san Umma Gaggi sarai ba abun mamaki bane gobe a tashi da ciwon qashi idan ta kwana cikin sanyin nan.
Da sassaukar ajiyar zuciya ta kufce mata lokacin da ta kwanta, bacci ne yayi awun gaba da ita.
***
Siddiqah amarya ta Sufyaan Barkindo Sajoh😍💃🏼
Shagali...😂
Ma'assalam
Umm Yasmeen💞
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top