BABI NA TAKWAS

Gombe, NAJERIYA.

YULI, 1994

Shigowan Tahir da sauri dakin Hajja Nenne ne ya ankarar da Siddiqah ta dago kai ta dube shi.

"Kai kuma fa lafiya kamar an koro ka?"

"Kinga Hajja?"

"Koma kayi sallama." Siddiqah ta fada tana kallon kaninta mai shekaru goma sha biyar wanda ya tara gashi a kansa da dogon wuyan da ya samu a sanadiyyar rashin ji da rashin natsuwa da kuma samartaka.

"Don Allah nayi a raina, nace miki kinga Hajja?"

"Ta shiga bandaki, menene? Kamar wanda zaka koma ciki, bazaka barta ta sarara ba."

"Ke ana nan duniya zata tashi baki sani ba, ana can ana miki kulli a gun Baba, Gwamma Hajja ta zo asan nayi."

Siddiqa ta kifta idanu, girarta suka cure guri guda. "Ban gane ba me yake faruwa?"

"Kawai dai..."

Tashi tsaye tayi ta juyo da shi yana fuskantarta. "Tahir, dubeni ka fada min me yake faruwa. Kar ka yarda ka tadawa Hajja da hankali."

"Batun fa shirin aurenki ne, wai kawai don Baba ya sa filinsa daya a kasuwa don ayi shirin biki shine suna can sun tada kayar baya. Wai idan ya saida filinsa a aurenki, su a auren yaransu me za a sayar? Don an ga kece 'yar dakin nan ta karshe da zatayi aure wai yana so ya karar da arzikinsa tun akanki kan a iso na yaransu da suke tasowa yanzu."

"Inji wa?"

"Hajiya Diddi mana tana can sai fade-fade takeyi, su Hajiya Maman ma ba wanda ya dakatar da ita. Ko da yake ta saba ai." Ya nade hannayensa saman kirji hade da kawar da kai cikin huci.

Da sauri Siddiqah taja kanin nata gefe tace "Kaga, kar ka yarda maganar nan ta dawo kunnen Hajja Nenne, kana ji na? Ni na san me zanyi, za a bar musu filinsu suyi yanda suke so dashi. In sha Allah Baba bazai daga komansa ya sayar ba."

"To da me za a yi auren naki? Ta ina zai fara tunda ana batun saura sati hudu yanzu?"

Murmushi Siddiqah tayi sannan tace "In sha Allah, bazamu ji kunya ba kuma bazamu tozarta ba. Hajja ta dade tana shirinta, kuma ni bani da wani dogon buri, kayan kicin kawai za ayi min. Sutura kuwa duk lokacin da Baba ya bamu kudi nakan saya na ajiye. Kuma Sufyaan yace ya saka komai a gidansa ko kujera ba ma bukatar mu kai."

Lokacin da shima ya fada mata haka har gardama sai da tayi sosai akai. Akan ya bari ita kam a gidansu ana yiwa kowa komai da yake bukata. Yace shi tsarin da yake bi kenan, yanda ya bada gida haka shi zai tanadi kayan cikin gidan. Don haka an fi sati da kammala kawo mata kayan dakinta a bisa yanda ya fada mata. Hatta launin kujerunta sai da ya kirata ya tambayeta abunda ta fi so.

Sai da aka kwana biyu ana kai ruwa rana sannan tace masa ta saduda ta zabi ruwan toka mai cizawa. To yanzu da hakan bata kasance ba wata rigimar ce kuma zata ballo a nan gidansu. Tunda dama anayi kasa-kasa Hajjan tana shanyewa. Amma tunda sun fito sunyi magana da kanta zata je ta samu Baba ta shaida masa yanda sukayi da Sufyaan.

Sai da ta jira yamma yayi sannan ta shiga falon Baba.

"Dama amare suna fita daga daki ne?" Baba ya tambaya cikin zolaya daidai lokacin da ya ajiye kofin shayinsa akan dan teburin kafa da yake kusa dashi. Yana zaune ne kan kujerar zaman mutum daya a falon.

Nan da nan Siddiqah ta kawo hannayenta ta rufe fuskarta. "Baba..."

Shima dariyar yayi sannan yace "Yaya shirye-shirye? Ana ta addu'a dai ko?"

"Eh Baba ina yi."

"Allah Ya shige mana gaba. Nayi magana da Raliya nace ta sameki a waya kuyi shawarar abun da ake bukata sai kuje ku saya a nan ko Kulsum ko su Fatima da Salmah su tayaki cefenen kayan naki."

"Uhm... Baba dama akan maganar ne nazo."

Tana ganin yanda ya mutskuta gaban kujerarsa yana sauraron ta. "Munyi magana da shi yace ya saka komai na kayan daki a gidan hatta labulaye akwai komai. Sai kayan kicin ne kawai za a saya."

Take ta ga sauyin da ya sauka a fuskar mahaifinta. Ta dade da sanin yanda Sufyaan yake ji da guntun taurin kansa da kafiya Babanta ya dama shi ya shanye shi. "Ke kika bukaci hakan a gurinsu?"

"A'a Baba, shine dai yayi tsarin hakan."

"To, duk da haka ai za ayi miki kayayyakinki yanda akayi wa kowa, tunda an riga an fara. Idan an kai miki su sai ya san yanda zai yi da su. Yanda yayin yayi kyau ya nuna sanin Ya kamata. Allah ya biyashi. Sannan suturu da wasu kayayyakin ma duk za ayi, sai kije kuyi shawara a madadin wasu manyan kayan da ya riga ya saya na dakin naki me kike so a saya miki?"

Tsam tayi, an dai gudu ba a tsira ba. Idan a madadinsa ne kenan duk da haka sai ya daga abu ya sayar.

Tun ba yau ba kowa ya shaidi mahaifinsu da takatsantsan, duk mukaman gwamnati da ya rike a kasar nan bazaka taba ganin wai ana facaka a gidansa ba, iyaka halaliyarsa yake ci. Ya taba fada musu a gun aiki har zundensa akeyi wai mai mayarwa gwamnati da canji cikin asusu.

Yakan ce musu ranar da ake kwashe masa ladansa don a biya bashin da ya ci a duniya suma suna ta kansu, ba mai tayashi biya a lahira. Don haka ya dade da gwadawa iyalansa wannan dabi'a ta kaffa-kaffa da abun duniya. To sai dai hali ne na dan Adam da burace-burace, idan wani yana da tsentseni wani an daura masa dogon buri.

"Baba hakan ma yayi bana bukatar komai."

"Maryama, ina da wadanda zan yiwa ne idan ba ku ba da 'yan uwana?"

"Baba ai ba sai an shiga matsi ba."

"A'ah babu wani matsi. Kuna sane ni duk iya aikina ban tara komai na gwamnati ba, ban ajiye kudi a banki ba bare wani abu amma Alhamdulilah muna da rufin asirin Allah. Akwai kadarorin da muka ajiye na halaliyar mu. Kar kiji tsoron wani abu ki je duk abunda kike so bazai gagara ba za a yi miki ayi wa 'yan baya. Komai ba sai Allah ya kai mana rai ba?"

"Haka ne Baba."

"To, kije kuyi lissafin komai."

"Na gode, Allah Ya kara girma da arziki. Allah Ya kara rufin asiri. Ya sa a mizani. Ya biyaka da mafificin alkhairi."

"Ameen Ya rabbi. Allah ya sa albarka a auren shine babban fatanmu."

Da wannan Siddiqah ta tashi daga falon. Sai taji ta samu sassauci daga kuncin da ta samu kanta a ciki dazu bayan ganawarta da Tahir.

Washegari taje gidan yarta Kulsum ta fada mata yanda sukayi da Baban game da shawarar abunyi.

"To kinyi magana da Adda Raliya ne?"

"A'a dama nace bari na fara samunku ku na cikin gari mu tattauna tukun."

"Wannan fagen ai na Adda Raliya ne, duk abunda tace ya zauna. Amma batun list kam zamu iya, inaga akwai wanda akayi nawa ban yar da shi ba, bari mu ci abinci sai na binciko shi."

Hakan kuwa akayi. Washegari duk suka hadu a gidansu ita da Kulsum da Fatima suka kira gidan Raliya a Potiskum suka saka ta a speaker aka yi ta shawara daga karshe dai suka tsayar akan za a saya mata setin gwal da kudin kayanta da ba a bukatar a saya.

"Na samu waya ma daga Adamawa cewa a karshen sati na sama kanwar Sufyaan din zasu zo domin kawo kayan auren."

"Kuma?" Siddiqah ta fada cikin ware idanu. "Adda Raliya ki dakatar dasu, yanzu ma yaya muka kare da Baba? Kin san baya son zancen kawo lefe kam kwata-kwata."

Kulsum ce tayi caraf tace "A'a ba a haka Siddiqah, ai akayi haka sai suyi tunanin a bati zasu sameki. Ki barsu su kai din tunda gidan Yaya Tijjani za a kai, sai a ajiye miki kayanki a can. Daga nan idan an gama biki sai a kai miki kayanki gidanki."

Fatima ta jinjina zancen, "Hakan ya yi. To batun kayayyakin da Baba yace za ayi su fa su kuma?"

Raliya ta sauke ajiyar zuciya, "A yanda dai ya min bayani, yace can Jabbi Lamba yana da gida inda yake sauka da iyalansa, kuma nan ne family house dinsu, saboda haka ya ware daki wa ita Siddiqan ma, kinga sai a mata jerenta na kayan da Baban zai mata a can gidan. Ko ba komai dai kowa zai san itama da gatanta."

"Shikenan ma tazo gidan sauki. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Jin duka sun shiga yin addu'o'i yasa Siddiqah ta rufe fuskarta da niyyar tashi a gun, "'Yar kwasti tana wani langabe wuya tana rufe idanu yanzu, kamar ba Allah-Allah takeyi ba ayi a kaita. Zaki sani ne ai wannan Sufyaan Sajon nakin sai kin kwala, 'yar nema." Kulsum ta fada tana dariyar Siddiqah.

Yayinda ta juya kan Fatima tana cewa "Kina jin harda cewa Baba wai a taimaka a saka auren kusa-kusa. Kiga kwanakinta uku dududu da dawowa daga makaranta sai ribibi takeyi kamar wacce ta kone a ka. Ko dan murmurewan da muka samu mukayi ba a barta tayi ba."

"Kai Fatima!" Kulsum ta fada amma itama dariyar takeyi. Aiko wannan ne ya koreta ta barsu suna kammala wayarsu da Raliya.

A lokacin ne ita kuma nata kawayen suka fara sintiri wurinta don shirye-shirye. Kai tsaye ta fada musu su gidansu ba abunda akeyi sai daurin aure.

Kamar yanda Sufyaan ya nema, suna gama jarrabawa, kamar wanda yake kan kaya ko numfashi bai bari tayi ba, ya aika gida batun saka rana. Tunda Baba ya san da zancen kuwa bai yi kasa a gwiwa ba yasa wata daya bayan gamawarsu. Nan ma sai da aka nemi alfarmar kari saboda ta samu ta murmure daga wahalar gama makaranta, amma fir Baba yaki.

Don haka ba wani shiri na azo a gani bane illa iyaka dinkunanta da ta bayar a mata na kayan sakawanta da sintirin kasuwa domin kammala abunda suka saura.

Hajja Nenne wannan karon bata tsoma baki ba don ganin su Salmah suna shirye-shirye, wannan yasa Kulsum ta dano baki gaba tace "Oh Hajja mune harda shan gwabji don munyi magana ina ce yanzu Siddiqah da kanta take zuwa kasuwa?"

Haka akayi ta mata dariya.

Kamar kuwa Kulsum ta san abunda ke ran Hajja Nenne, washegari Salmah ta gama shirinta don su fita ta biyo dakin Hajja Nenne sai sukayi kicibis a bakin kofa.

"To gata nan, tashi ki fita ki bita ki karasa kodewar, dama me ya saura? Sai mu debi kasusuwan naki mu kaiwa mijin naki ya san nayi dake. Ace mutum bazai natsu ba, sai yawo a rana, haka zaki karar da sauran kuzarinki ki isa babu armashi."

Tunda Hajja Nenne ta sauke aya a jawabinta, daga Salmah har Siddiqah hannu suka daura a ka kamar zasu nitse cikin kasa.

Sai da dare idan suka tuno maganar Hajja sai su tuntsure da dariya. "Kinga ta kanki Siddiqah, Hajja zuba miki idanu kawai tayi ashe cikinki take dashi. Yau ta haife ki."

Siddiqah tace, "Duk Adda Kulsum ce ta mana baki." Sai kuma suka fara dariya kasa-kasa suna kulle baki kar a jiyo su a tsakar gidan.

***

Kwanaki suna ta karatowa shiri yana kara zafi, zuwa yanzu an kammala hada duk abunda za a hada na tafiya a akwatin tafiyar Siddiqah. Fatima ce ta zo musamman ta zaba mata kayayyakin da zata fara amfani dasu a ranakun farkon amarcinta. A cewarta aka bar Siddiqah tayi zaben ba a san abunda hali zaiyi ba.

"Adda Fatima naga dai a yanda naken ya gani yake so, gwamma ya san abunda zai ci gaba da gani ko bayan auren."

"Ai baki isa ba, sai muzo mu miki duka idan bakya kwalliya."

Siddiqah tana shiru bata fada mata cewa ba sai sunje sunyi wannan aikin ba, don tun yanzu Sufyaan ya iya tambayar labarin lalle da kitso don haka ta san shima din mutum ne mai son gyara.

A can bangaren Raliya kuwa, baki ta samu na musamman inda kanwar Sufyaan, Jamilah ta taho da kaninsa daya, Muhammad Sani, hade da direba da motoci biyu shake da kaya.

Tun Raliya tana jira taga an hattama sauke kaya har ta koma kifta idanu. Ita dai basu taba ganin abu makamancin haka ba, sai gashi ana fidda bayanin kayan lefe akace akwatuna uku na cikin kayan na dangin Siddiqah ne duk a rabawa kowa.

Yau ga sabon abu, ita da ba a karbar lefe a gida, idan taje wa Baba da zancen kayan dangi da ita da kayan zai san nayi da su. Haka ta rinka saka tana warwara, bayan bakin sun koma washegari.

Kwana guda da Raliya tayi da Jamilah suka saba akayi hira cikin sakewa da jin dadin mu'amala. Da alama sun karbi aurensa da Siddiqan da aminci sabanin yanda take ta tunani ganin cewar ba ita bace matarsa ta farko. Kodayake su kam a gunsu zai zama Siddiqah da Aminar duk daya ne tunda su dai dan uwansu suka sani.

Bayan Raliya ta gama sake-saken ta ne, ta nemi shawarar maigidan game da yanda zatayi da kaya.

"Dama yaya kuka tsara?" Tijjani ya tambayeta.

"A'ah mu fa kaga bamu ce za a kawo wasu kayayyaki ba, niyyarmu sai a bar kayan a nan idan ya tashi sai ya aiko a debe mata su zuwa gidansa. Tunda su suka nuna suna da bukatar su kawo kayan wa danginta."

"To yanzu meye matsalar?"

"Kana ganin nan shirgi gudan fa wai kayan dangi ne, dama su haka mutanen garinsun suke tasu al'adar?"

Murmushi mai sauti Tijjani yayi, "To mutum yayi niyyar yi kam ai sai dai a barshi, kina magana har yanzu kamar baki san waye Sufyaan ba."

"A'a to har yanzu da sauran karatuna, yanzu fada min abunyi."

Tijjani ya nisa sannan yace, "Ki kira Baba kawai ki fada masa, muna zaune aka kawo kaya gashi harda na 'yan uwa anyi, baza a kawo natan ba kowa ya gani amma za a aika sakon dangi don kowa ya samu, ayi godiya a sa albarka."

"Nima dai sai an koma an min kayan dangi. Yau ga sabon abu a nan." Raliya ta fada cikin zolaya.

"Ke? Kin san kundunbalar da nayi na hada kayan naki ma kuwa? Ina ce har yau ado kikeyiwa dakin naki da setin akwatunan da aka miki? Tunda kike ina kika taba ganin irinsu a wani gida?"

"A'a adai yi mana idan ba tsoro ba."

Yana dariya ya sa hannu ya zagayeta cikin rikonsa. "Oho dai an bani mutum sukutum da guntun akwatuna na duk da haka."

Ajiyar zuciya sukayi idanuwansu na kan jerin kayan da ta shirga su a tsakar dakinsa.

"Allah Ya sa dai yau kar a min sambatun akwatuna anjima, don ke kadai nake so a kusa dani ba da jimawa ba." Tijjani ya fada daf kunnenta.

"Ni kam ka barni naji da kaina don Allah." Ta fada tana kokarin tureshi gefe cikin wasa.

Bandaki ta wuce ta tofar da yawu ta kurkure bakinta. Ita ta samu ma ayi bikin a gama lafiya ba tare da wannan sabon al'amarin ya mata katsalandan ba. Yanda ta ci burin auren Siddiqah sai gashi ya zo mata da laulayin ciki. Wanda abun godiya ne, tun bayan haihuwar Haneefa da shekara daya da tayi bari sai yanzu Allah Ya sake azurta su da samun karuwa. Don haka ga murna ga kuma tunanin yanda zatayi sintiri a haka.

Wannan yasa take ta boyewa Tijjani amma randa ya gano ta sai cewa yayi, "Da ma kin bar kunshe-kunshenki duk abuna bazan hanaki aurar da Siddiqah ba."

Wannan yasa taji kunya, amma daga ranar kuma komai ya koma daidai, suka hadu suna renon dan tayin nata. Duk da bata fadawa kowa ba tukun a gida.

Hakan kuwa akayi sai waya Raliya tayi gida ta fadi sakon Sufyaan kan cewa anyi akwatunan dangi. Baba ya gama fadansa akan dalilin karba, tace ai ko har masu kawo kaya sun isa gida lafiya jiya. Ba yanda ya iya haka yana ji yana gani da Raliya ta tashi tahowa biki ta taho dasu cikin gidan.

Yana ganin ana sauke kaya yace "Ashe kuwa wasu zasu shekara babu zanin daurawa daga gurina." Ya kalla ya sake yace "Sannunku da aiki ko? Da kyau. Ya muku kyau."

Duk aka saka dariya a tsakar gidan amma ana tunanin kar ya aikata da gaske. Duk da kasancewarsa mai zolaya wasu lokutan basa iya tantance yaushe yake zolayar yaushe yake zancen gaske har sai sun gani a aikace.

***

"Lailah! Ya salam. Don Allah ku bar mutum ya huta. Kun saka min ido da yawa. Ha'a!"

"Ina, ai yau kinga ta kanki a guri na. Allah Ya nuna min ranar da Siddiqah take lalacewa gurin magana a telefon da wani da namiji. Ina jawabin soyayya bata lokaci ne?"

"To sai kuma kiyi kasa-kasa ai kar Hajja ta jiki."

Tun dawowarsu daga kasuwa suka kule a dakinsu lokacin da kawarta ta kawo mata ziyara. Har yanzu mamaki bai sake jama'a da dama ba tunda suka ji labarin aurenta. Daga dangin Babansu har dangin Hajja Nenne, kasancewar a gidan Raliya suka fi haduwarsu da Sufyaan.

Lailah ma albarkacin tana ganin aike a makaranta yasa ta sani, idan banda haka Siddiqah bata taba fadan cikinta wa kowa.

"'Yar gari, na san kina Allah-Allah ki bar gidan nan ku samu free lokacin da muke school. Sheke ayarki kikeyi gidan Adda Raliya. Muna ta sake baki ashe abu sai nisa yakeyi. Ayi ta cewa 'Ni bazanci komansa ba' ashe ana so ana kaiwa kasuwane."

Siddiqah ta harari kawarta ta kut da kut tace, "Sai kuma kiyi ai tunda abun naki sharri ne. Ni bama ma kallon juna. Shi sabgoginsa yawa garesu bare mu hadu. Amma da yake sana'arki ce kulle-kulle sai kiyi tayi."

"A hakan kuma ya gani yace yana so ba. Gashi har mun shiga satin biki. Ni fa da Salmah ta fada min an saka aurenki sai da na kware. Ina tsaye sai da na zauna, Inna ta rinka tambayata ko lafiya, da kyar na bata amsa. Ta jera dani muka rinka mamaki. Iya saninmu kaf kilik kece baki kula kowa. Na zaci shima wannan din korar sa zakiyi ai. Muyi ta miki tsiya ashe ke macijiyar sari ka noke ce. Kallonmu kikeyi mu gama haukarmu ke zaki riga kowa fara aure."

Siddiqah ta kada idanunta tana murmushi. "Ke dai Lailah, idan abu dai Allah ya nufeshi sai dai kawai ayi shiru."

"Dakata, sake bani labarin yaya kuka hadu ma?" Siddiqah tayi dariya kawai ta girgiza kanta, don ta san tsiyar Lailah sarai, duk da ta san labarin kullum sai ta isheta da a sake badawa.

"Zaki yarda idan nace miki bai wuci watanni biyu ba da na fara ma tunanin da gaske zan iya aurensa? Duk watannin baya da ya diba yana sintirinsa na zaci bata lokacinsa yakeyi ni kaina, zaiyi ya gama ya kwashe kayansa."

"Ke! Siddiqah! Bana son kasada, watanni biyu sai kace ke 'yar sadakah? Me zakiyi da gaggawa haka? Lalle mutumin nan ya illata maki zuciya."

Siddiqah ta bude kwalbar Limca da karfen budewa ta tsiyayawa Lailah abunsha mai sanyi cikin kofin silbar da ta ajiye. "Kina magana sai kace baki san Baba ba? Ai kinga bayan zuwan da yayi makaranta ya shaida min manufarsa, mun hadu a gidan Adda Raliya sau da dama. Wataran yazo naki kulashi wataran yazo yaki nemana. A nan Gombe ma ya zo sau biyu. To ai tunda Baba yaji daga gurin Yaya Tijjani ya fito, yace Tijjani ba mutumin banza bane, bazai kawo wanda ba na gari ba don haka ya turo magabata ayi magana."

"Amma dai kin tabbatar ya kwanta maki a rai Deeqah?"

Murmushi Siddiqah tayi da ta tuno zancenta da Sufyaan.

Ranar da suka dawo daga makaranta bayan sun zana jarabawarsu ta karshene ya kira gidansu da yamma. Murnar gamawa yayi mata sannan ya mata ban gajiya. Yana karewa ya ce, "Kar ace nayi azarbabi da na taho gobe. Amma wasu ayyukan sun sha min kai. Congratulations."

Murmushi tayi tace, "Na gode. Ai baza kayi laifi ba."

"Dakata dai kiji tukunna sai kice haka."

"Ina sauraro."

"Kin tuna lokacin da kika fada min labarin kawarki Umut 'yar Turkiyya da kuka zauna tare a Saudiyyah?"

"Eh, na tuna wani abu ne?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Babu, kawai dai nayi la'akari da cewa kina da passport dinki kenan, don haka nayi magana da Hashim nasa ya karba min shi a hannun Baba za a sabunta miki shi. Ina fatan banyi laifi ba?"

"Ni kuma? Yaushe akayi hakan?"

"Kuna makaranta, kar ya zama babu lokaci bayan kin dawo shiyasa nayi hakan."

"Me zakayi kai kuwa da passport dina?"

"Me akeyi da passport?"

Da farko bata fahimci manufarsa ba don haka tayi shiru tana ta sauraron ya karasa jawabinsa amma ta san shi sarai wasu lokutan idan ikon ya motsa, bai cika son dogon surutu ba.

"Akwai tafiyar da na shirya mana. Zamu tafi bayan kwana uku da aure, in sha Allah."

"Amma da baka..."

"Shh. Mar'yam ina so duk wani abunda kike so na rayuwa su faru dake a lokacin da muke tare, saboda bana so ko dakika daya ya kubce na farin cikinki wanda ban gani a tare da ke ba. Don haka wannan ma tare zamuyi. Na riga na gama komai. Allah dai kawai ya kaimu lokacin lafiya."

A maimakon ta samu bakin amsa masa sai ji tayi hawaye na gangara a kumatunta. Ita sam ba mai saurin kuka bace. Amma bata san yanda akayi Sufyaan ya yi nasarar isa cikin kirjinta ya tabo zuciyarta ba. Irin wadannan kalaman ba kasafai ya faye fadinsu ba, amma duk lokacin da ya fada ta san hakikanin gaskiyarsa yake fadi.

Sai lokacin ta san hawaye ne na kawa zucin abunda Sufyaan yake haddasa mata a wannan lokacin. Tunda take bashi labaranta na kuruciya bata taba tunanin wasu ababen ma yana hankalce dasu ba, domin wasu zubin gani take kawai zai dauka haukarta take shirga masa, ashe duk yana sane. Ya bata mamaki kwarai da hatta sunan kawarta na yarinta Umut 'yar kasar Turkiyya bai mance ba. A wannan lokacin Sufyaan ya kara samun wuri na musamman a cikin zuciyarta.

"No gode, Allah Ya nuna mana lafiya." Amsar da ta bashi kenan.

Yanzun ma nisawa tayi ta kalli Lailah zuciyarta fal da annashuwa, "Kin san yanda kike ji idan kinyi addu'a kika tashi daga gun sallarki da cikakkiyar yarda cewa Allah Ya amsa addu'arki? To haka na ji dangane da hukuncin auren Sufyaan da na yanke. Akwai wata natsuwa da ta shigeni dangane da zabensa da nayi. Saboda na san don Allah nake da niyyar aure don nayi ibada, a iya hange na zan ji dadin yin wannan ibadar tare dashi.

"Saboda zuwanshi kai tsaye da batun aure yazo, bai zo da niyyar wasa da hankali na ba. Na san akwai bangarensa da zan zo na saba dashi na koyi aiki dashi a hankali kamar yanda shima dole wasu abubuwan nawa sai ya yi hakuri dasu. Wannan dalilin yasa na san bani da haufi."

A wasu lokutan takanyi tunani ko taji tsoron zuwa da zatayi ta tarar da tsarin rayuwar da ya riga ya saba da shi, sai dai tana da yaqinin cewa tabbas Sufyaan mutumne da take ga zai iya tsayawa kan gidanshi, taga kuma alamar hakan. Bisa yanda ta kula dashi baya wasa da al'amarin iyalinsa ko kadan.

"Da kyau! In sha Allah zai kasance alkhairi gareki. Saboda ko ba komai ke ta kwarai ce kuma Allah zai dubeki. Hadaku zai yi gida daya da matarsa ko kuwa?"

"Yana da gida a Kano tunda harkokinsa sunfi yawa a Arewa yanzu, yana kokarin barin can Legas. Saboda haka nan gidansa na Kanon zamu zauna, in sha Allah. Amma kowace mata da bangarenta."

"Shikenan za a daukewa su Hajja Nenne ke."

Siddiqah tana dariya ta duka kanta ta rufe. "Kai to ma sha Allah, Allah Ya kade fitina Ya tabbatar da alkhairi Ya kuma hada kawunanku. Allah kuma Ya sakawa malam Sufiyaanu da alkhairi, ko ba komai ya ciri tutan namijin da aka so a cikin maza."

Dundu Siddiqah ta zage ta dakawa Lailah a gadon bayanta, ita kuwa sai dariya take mata. Zukatansu fal da farin cikin sabuwar rayuwar da Maryama-Siddiqah zata fara.

***

Assalamu alaikum, I hope we are all good, today is Friday, let's not get carried away please, Let's recite surah Kahf and say the salatunnabiyy.

Please say a prayer to my Uncle, Bappah Uthman, he passed away on Wednesday evening 19th August, 2020. May Allah forgive his shortcomings, and give his family the fortitude to bear his loss.

Jazakumullahu khairan.

Ma'assalam

Umm Yasmeen.💞

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top