BABI NA HUDU



Potiskum, NAJERIYA

OKTOBA, 1993.

Kirar sallar assalatu ne ya sa Siddiqa ta farka a razane. Jin kirar sallar da tayi yayi dai-dai da duhun kan da ta samu kanta a ciki sanadiyyar abunda ta gani kan ta bude idanunta daga wannan baccin.

Hakan ya janyo mata wani saran kai mai azabtarwa. Ba shiri ta wuce falo neman magani. Ruwa ta kora bayan ta hadiyi kwayar paracetamol. Ita ko yau wani irin mafarki ne wannan mai tada hankali?

Salmah na ganin lokacin da 'yar uwarta ta dawo dakin bayan ta dauro tata alwalar.

"Lafiya Siddiqah?"

A firgice Siddiqah ta juyo tana duban Salmah, zama tayi tukunna a bakin gadon sannan ta sharce gumin da ta ji ya tsattsafo mata a saman gira da saman labbanta. A hankali ta shiga maida numfashinta.

"Ba komai, wani irin mafarki nayi."

"Kiyi addu'a ki yi sadaqa anjima, in sha Allah babu komai. Na tara miki ruwan dumi a buta naji yau garin da dan sanyi."

Gyada mata kai kawai Siddiqah tayi. Yaya zata dubi Salmah tace mata taga mijin aurenta a bacci, cikin mafarki? Ita kanta da tunanin ya ziyarceta sai ta jishi banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Ita ba kasafai ta cika yin mafarke-mafarke ba. Amma wannan mafarkin ya mata tamkar da gaske ya faru ba a mafarki ba.

Kai sai take jin kamar har sunan shi ya fada mata, amma kafun ta rike sunan har ta farka. Sai dai abu guda da ya tsaya mata a rai shine sautin muryar mutumin da ya ambaci kanshi gareta a matsayin mijinta. Ba tantama duk inda ta ga wannan mutumin tsaf zata gane shi ko da yake muryarsa ta fi daukar hankalinta amma ta ga kamannin sanma da siffarsa.

To ma wai banda shirme irin nata, ina take da tabbacin akwai irin mutumin a rayuwar gaske bare ma har ta hadu dashi? Don kawai ta ganshi a mafarki wannan ba shi yake nufin akwai shi a zahiri ba. Sai dai furucin da ya mata a cikin mafarkinta shi ne ya tsaya mata a rai.

Batayi tsammanin a cikin manemanta akwai mai wannan muryar ba. Don haka shawarar Salmah tabi kawai tayi sallah ta zauna tayi ta adhkaar cikin fatan Allah Ya mantar da ita wannan mafarkin.

***

Tun da safe suka tashi da shirin komawa makaranta. Suna cikin hada kayayyakinsu cikin akwatunansu na gwangoro Haneefa ta shigo dakin da gudunta. Raliya ce ta shigo bayanta tana cewa ta bata abunda yake hannunta.

"Hanee, me kika yiwa Mamanki?"

"Aunty Siddiqah boyeni." Abunda kawai take cewa kenan tana gudu tana zagaye Siddiqah. Nan Siddiqah tajiyo karar leda ana mutsukkashi, tana ganin abunda ke hannunta ta san gudun me Haneefa takeyi.

"Adda Raliya ayi hakuri zamu bayar."

"Wa yace ta dauki biscuit bata tambaya ba? Yau sai na karba na dura mata ta hanci."

"Wayyo Mama kiyi hakuri." Ta fada tana haki. Siddiqah na dariyarsu ta boye Haneefa suka roki Raliya ta hakura amma tace baza a bada Biscuit din ba yanzu.

"Kun kammala shirin naku ko? Baban Haneefa zai turo Babangida daga ofis yazo ya maidaku cikin makaranta."

"Mun gama. Amma Salmah dai tana bandaki ta shiga wanka."

Raliya ta juya idanunta, "Salmah kam ko dawisu albarka wurin gayu. Sai ta sarara haka ai tunda makaranta zata koma."

Siddiqah tayi dariya. "Yanzu ko zakuyi fada ashe. Ina ga yau wanda akeyi da shi ne zai zo shiyasa ta kasa zama tun safe kamar kifin tarwada sai shiga ruwa takeyi."

Raliya na dariya amma Siddiqah ta kula kamar tana so tace mata wani abun sai kuma ta fasa.

"Adda Raliya?"

"Shikenan dai, sai daga baya, yanzu ki kwankwansawa wancar kifin ta fito haka nan ta shirya kar ku makara. Kinga har karfe uku ya wuce."

Wai kura zata cewa kare maye, Siddiqah tana sane da irin gayun Yarta Raliya yanda Salmah take bata lokacinta wajen caba ado haka Raliyanma. Tana cikin yaran dakin Hajja Nenne da suka fito farare tas. Ta kasance mai tsawo da kira mai daukar hankali, jikinta ya nuna alamun murmurewa a gaba kadan.

Duk da dukkansu sun dauko kyaun Hajja Nenne da suffar fulani, Siddiqah ta san kaf dakin ba wanda ya kamo Raliya son ado da kwalliya wanda yake kara hasko kyaunta a kodayaushe.

Ko mijinta Tijjani ya shaida hakan motsi kadan ya dawo gida. Wasu lokutan har kunya suke bata don baya jin shakkun yana shigowa gida ya ja hannunta su zauna daf jikin juna suna hirarsu wani lokacin ma a daki zasuyi zamansu sai dai kaji tashin dariyarsu.

Rayuwarsu kwarai yake bata sha'awa.

Murmushi Siddiqah tayi ta kada kanta sannan ta isa kofar bandakin bugun da tayi wa kofar ko waye a kusa sai ya razana.

"To Hajiya a fito a koma inda ba a da wayo." Tana jiyo gunagunin Salmah daga ciki wai 'zata sa ta fito da kumfa a jiki'. Siddiqah ko ta guntse dariyarta.

Can falo ta koma ta tabbatar, ta kwashi su dakan kanzo da su cincin dinsu duka aka saka a jakar bagco. Jiki a sanyaye suka koma makaranta lokacin da Babangida direba ya iso gidan.

***

"Maryama-Siddiqah Usman Muhammad!" Kirar da aka kwadowa Siddiqah daga bakin hostel sai da ya zaburar da ita. Malam Mahammadu dai wannan kira ya kusa ya saka shi juyi a makwancinsa. Ko menene haka na gaggawa? Kira babu kakkautawa?

Sati biyu da dawowarsu makaranta kenan har sun soma sabawa da yanayin zaman makarantar bayan hutun da suka sha don haka bata san me tayi ba da za a mata irin wannan nema haka. Don dai ta san ba ranar ziyara bace. Kuma in har ziyara ce, ana kirar Siddiqah ake kirar Salmah.

Turus! Ta tsaya da ta ga Salmah ta karaso tare da Mamande, wacce take ta haki tsabar sauri.

Kallon Siddiqah ya koma ga Salmah cikin daurewar kai, "Lafiya? Waye ke nemana?"

"Ke dai taho mana ki gani. Kya tsaya a nan kina tambaya?"

"Don Allah bar wasa ki fada min. Kun tsinka min zuciya da firgici."

"Ziyara aka kawo mana, ki taho." Salmah ta fada hade da riko hannun Siddiqah.

"Amma dai Maryam-Siddiqah Usman aka ce ake nema?"

Mamande dai ta sake jaddadawa, "Tabbas sunce ace muku Yayunku ne."

Salmah ta daga mata kafadu alamun ba na fada miki ba.

Daga jin hakan shi kenan hankulansu yayi gaba, saboda tsabar farin cikin ganin mutanen gida sun zo musu. Duk da sati biyu kenan da dawowarsu daga gidan.

Duk yanda akayi daga Gombe ne, tunda can ne basu cika zuwa hutu ba sai idan dogon hutu aka bayar.

Sai dai suna isa wurin da ake nemansu suka dan rage sauri game da kallon juna saboda sam basu fahimci ko waye mamallakin motar ba. Wata bakar jif ce sai kyallin sabuntaka takeyi. A iya tunanin Siddiqah bata san wani wansu ko dan uwansu da irin wannar motar ba. Asali ma bata taba ganin wani wanda ta sani da irin wannan motar ba.

Amma daga ganin fuskar da ta bayyana bayan an zuge gilas din baya sai Siddiqah ta fadada fara'arta, sai kuma ga mijin Adda Raliya ya fito daga mazaunin direba. "Yaya Tijjani, Kawu Aliyu? Daman kune kuka zo?"

Murmushi wanda ta ambata da Kawu Aliyun yayi yace, "Karamarsu babbarsu yau dai gamu a makarantarku, yaya karatun dai? Sai a soke sunana daga black book yau nima na zo ziyara."

"Lafiya, kalau yaya gida? Yaya su Adda Raliya da su Antu?" Ta fada cikin tambayar labarin matansu.

Lokacin ne Salmah ta dan saki jiki ta gaishe shi itama don Kawu Aliyu wani kanin Hajja Nenne ne. Dai-dai lokacin ne idanun Siddiqah suka fada kan mutumin da ke zaune gefen Tijjani a gidan gaba wurin zaman fasinja.

Mutumin yayi shiru bai ce komai ba tunda suka iso, hakan yasa taji wani iri a take kuwa ta gaishe shi. Sai dai ko kan ya kai ga bude baki ya amsa mata taji bugun zuciyarta ya kara sauri nan da nan, don haka ta dan rage kaudinta na ganin kawunta wanda rabon da ta ganshi kusan shekara guda saboda shi a Fatakwal yake aiki, bai cika zuwa gida ba.

Mutumin na amsawa kuwa sai da 'yan hanjin Siddiqah suka kada saboda ta dade bata ji murya mai razanar da mutum sannan a take kuma ya bi ya natsar da shi irin wannan ba. Dai-dai lokacin ne idanunta suka koma gefen direban inda Tijjani ke tsaye bayan ya bude marfin motar. Salmah ce ta cece ta daga wannan mutumin dake zaune cikin mota daf da su. Kafun Siddiqah tayi wani katabus Salmah tace, "Yaya Tijjani dama kuna hanya? Adda Raliya bata baku sakonmu ba?"

Dariya yayi ya rufe marfin motar. "Ke Salmah karatun kike yi ko kin tsaya cinye abincin makarantar? Naga ko Siddiqah baki samma ba, gashi tayi fingil da ita ke kuwa sai habaka kikeyi."

Murmushi Salmah tayi cikin jin kunya sannan tace "A'a ka jira na gama paper zaka ga cin tuwo, don gwamma ka daure buhuhhunan gidan ka."

"Ah, lallai Raliya sai ta shirya kenan." Kallonsa ya mayar kan Siddiqah sannan ya yafito ta kadan, ta koma ta daya bangaren da yake tsaye. Kallonta yayi yace, "Gurinki fa muka zo Siddiqah tare da abokina kuma abokin kawunki, da fatan babu damuwa?"

Hmm! Ai ita faduwar gaban da zancensa ya haddasa mata ya wuce labarin damuwa ya kusa sanyata a doguwar suma. Ita dai 'yar Siddiqah da ita ce aka yi mata ayari guda! Bayan Ayari ma, tare da Kawu Aliyu da Baban Haneefa, ta san koma menene yake faruwa a nan ya wuce tunaninta.

Tunaninta kuwa shine abu na farko da bata son tarowa saboda halin da ta samu kanta a ciki.

"Baban Haneefa, ni kuma?!"

"Eh, wannan abokina ne Sufyaan gunki yazo don ku tattauna. Bari mu barku ku gaisa ko?"

Jiki a sanyaye ta sauke kanta kasa. Bata tuna sanda ta amsa masa tayinsa ba, sai ji tayi gurin yayi tsit, alamun Salmah aku ta yi gaba da su Yaya Tijjani da Kawu Aliyu.

Sai ji tayi an bude marfin mota an fito. Mutumin nan dai Sufyaan wanda ta sha jin labarinsa amma ko kadan bata taba haduwa dashi ba wai shine yau yazo su tattauna. Me zata tattauna ita kuwa da abokin Baban Haneefa?

Tana sauraron ta ganshi ya tsaya a gabanta sai gani tayi ya jeru da ita inda take lafe jikin gefen motar don ta samu tallafi, tunda kafafunta ba lallai bane su iya aikata mata aikin riketa tsaye. Sufyaan dai ya jinginu a nan hade da harde hannayensa saman kirjinsa.

A sannu ta ja da baya kadan ta bada fili a tsakaninsu. Bata san ko hakan da tayi bane ya sa shima ya matsa ya bude kofar direba ya zauna a ciki.

A kaikaice ta dago idanu ta kalli sashin da yake zaune daga cikin motar.

Tabbas dogon mutumne karfaffa, sannan kuma ba yaro bane. Tunda ta san sa'an su Yaya Tijjani ne. Yaya Tijjani ko ya bawa Adda Raliya shekaru goma Adda Raliya kuwa tana bata shekaru takwas rus! Saboda haka akalla Sufyaan zai bata shekaru sha takwas zuwa ashirin.

Ita damuwarta daya, tunda suka zo da kaudinta ta iso na murnar ganin kawunta ba tare da sanin suna tare da bako ba sam. Gashi shi bai wuci kalamai biyu ya furta ba, wai kuma wurinta ya zo. Sai lokacin ta yi hamdala da ya kasance uniform dinta mai zani ne a jikinta ba dangalelliyar doguwar rigarsu ba.

"Afwan, assalamu alaikum Mar'yam. Da fatan zuwanmu bai takura ki ba?" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai take nanatawa a zuciyarta. Domin ita kam gani takeyi kawai Baba ya sani an gama nata ya kare. Itace yau tsaye da namiji a gaban su Baban Haneefa? Rahoto ya isa gun Baba an gama kawai.

Shikenan zasu mata aure!

A take girarta suka hade guri guda cikin farguwa da wani al'amari. Ina ta san mutumin nan?

Ya nanata sallamarsa sannan ya duba gefen da take tsaye yana neman ganin yanayin fuskarta da ta dukar tana kallon yatsun kafafunta. Ganin tayi shiru yasa yace "Sunana Sufyaan Barkindo Sajoh, amma an fi kirana da SBS."

Nan take Siddiqah ta dago a razane cikinta yayi wani kugi domin kuwa ba abunda ta tuno illa mafarkinta na sati biyu da suka wuce. Tabbas bazata tuna inda ta san mutumin nan ba domin kuwa bata sanshi ba. Shine mutumin da ta gani cikin mafarkinta! "Ya subhanallah! Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Kawai ta samu kanta da nanatawa. Yaya za ayi hakan ya faru? Me yake faruwa da ita?

Yaya zata yi mafarki da sunan mutum sannan bata taba ganinshi a rayuwarta ba har sai bayan sati biyu sannan ya shigo rayuwarta? Shi kenan mafarkinta zai zamo gaskiya kenan? 'Sajoh zai cinyeki ne?' Kalaman da ya furta mata kenan a cikin baccinta. Amma yanayin da sukayi maganar ya zo mata ne tsab tamkar ita matarsa ce shi kuma mijinta suna cikin raha da annashuwa.

Sam wannan taswirar taki ta bace mata daga gani. A dan tsakanin kwanakin nan wataran har takan rufe idanu ko zata tuno sashin mafarkin, a tata wautar ma idan ta kwanta har fata takeyi ta ci gaba a inda ta tsaya a wancan mafarkin ko zata ga abunda zai faru.

Tunda duk iyaka tunaninta na duniya bata taba kawo cewa shi wancan mutumin na mafarkinta da gaske mutum bane a zahiri. Gashi sunansu daya, kamanninsu daya, muryarsu daya.

Jiri ne taji yana shirin kwasarta ta kara dafa gefen motar. Shi bai sake ce mata komai ba haka nan ita bata san me zata ce masa ba. Rabonta da ta tsaya da wani da namiji ta mance. A kalla an bawa shekaru biyu baya. Me ta sani a lokacin? Me ta sani a yanzu?

Ita bata ma san me ake cewa ba idan an tsaya. Shi kuma da ya kawo kanshin yaki ya ce komai. Gashi su Yaya Tijjani basu dawo ba. Da ta dan samu karfin gwiwa ta dan dago ta kasan idanunta don ta dubeshi sai ta samu idanunsa suna kan itatuwan da aka jera a farfajiyar filin makarantar. Kamar mai nazari.

Shin ita ya dace tayi magana ko shi? Idan itace me ya dace tace? Me ake cewa bako idan ya zo?

"Sannu da zuwa." Sai da ta fadi hakan kuma ta runtse idanunta tamau saboda bata san ko yin hakan azarbabi bane.

Furuncin tan ne kuwa ya dawo da hankalin Sufyaan kanta sannan ya nisa. Tamkar irin ya gamsu da nazarin da ya kammala yi dinnan.

"Mar'yam." Yanda yake raba tsakanin sunanta ya dan dakata kan ya karasa shi yafi tsaya mata a rai. Kifta idanunta tayi jin ya sake kirar sunan nata. Watakila shima ya rasa abun fada ne. Musamman da ta ga hankalinsa ya koma hange-hangensa, da alama abokan tafiyarsa yake nema. "Bari zamu barku haka ku koma karatunku, Allah ya taimaka Ya bada sa'a. Zaki iya bani dama na nemi izinin magana dake wurin mahaifinki?"

Ya Rabbil- alamina!

Da alama tara duka zancen bakinsa yayi sai a karshe ya sakar mata su. Domin ita kam bayan wannan batun nashi sai ta rasa ta cewa. To me zata ce? Yana zuwa gun Baba ta san mafarkin ta ya zama gaskiya an gama.

Idan ta hanashi kuma bata san me zatace da Yaya Tijjani ba. Amma a hakikanin gaskiya zata so taga iya gudun ruwan wannan abun al'ajabin da ke faruwa. Shin Sufyaan mutum ne ko aljan? Wannan zalamar ce ta ingiza ta ta fara marmarin ta bashi dama ya isa wurin Baba.

A daya bangaren kuma idan tace ya isa gun Baba bata san komai game dashi ba. Baba na iya cewa ya ma bashi auren azo a daura. Maimakon hakan ya bata tsoro sai ta samu kanta da fatan hakan ya zamo gaskiya. Ya Salam! Yau me ya same ta?

"Baki ce komai ba, Mar'yam."

Sai a lokacin ta dago idanu ta dubeshi fararen idanunsa ne sukasa taji tamkar bugun zuciyarta daya ya tsallake. Sun fada cikin kwarminsu kadan masu duhu, wanda ya sake fasalta tsawon hancinsa da ya lankwaso kadan a karshe. Kana ganinsa kaga bafulatani usul. Yo ina zata kai mijin da ya nemi ya zarceta a iya ado da kuma kyaunma? Da shi mace ne kam ai sai ta Allah.

"Uhm. To."

Murmushi yayi mai dan sauti. "Uhm. To? Naje na samu Baban?"

Bakin dankwalinta ta kama ta rufe idanunta.

"To shikenan. Naje nace ina so na auri Mar'yam?"

Da sauri ta wangale idanu ta hau girgiza masa kai. "Don Allah kar kace. Idan kace zaiyi auren a lokacin."

Sufyaan ya saukar da ganinsa daga gareta fuskarsa kunshe da murmushi. Sai lokacin ta kula da zolayarta yakeyi.

"To, je kiyi karatu. Nazo ne mu gaisa ki san da zamana. Idan kin dawo hutu sai muyi magana sosai ko?"

Kai ta gyada masa kamar kadangaruwa.

"Amma kar kace..."

"Bazance masa aure ba. Amma kin dai san abunda ya kawo ni kenan ko?"

"To kai din waye?"

Murmushi yayi sosai sai da hakoransa suka nuna, ya daga kai ya kalleta idanunsu suka hadu sosai da sosai.

"Nine mijin Mar'yam-Siddiqah, in sha Allah." Ya furta a tausashe.

Idan da ya ce ta aureshi a tsaye a gun a take zata ce ta amince, tsabar yanayin yanda muryarsa ta iya bada umarni mutum kuma yaji yayi na'am nan take.

Tabbas idan kowa nada baiwa kebantacciya a duniya, to baiwar Sufyaan Barkindo Sajoh shine sace zukatan mutane. Domin ita kam ba tantama tana ga ya yi awun gaba da tata zuciyar ba tare da ta san komai game da shi ba baya ga sunansa da fasalinsa. Ba wai kuma sace zuciya a fagen soyayya ba, a'a ya zame mata ne tamkar linzami duk inda yayi nan zata yi ko don a zauna lafiya.

Ko da bai sace zuciyarta a fagen soyayya ba ta san babu dan Adam da zaiyi nasarar sarrafa tunaninta cikin kankanin lokaci irin wannan Sadaukin bafulatanin. Kullum takan yi ikirarin ita bata da hali irin na wasu daga cikin mata na wofantuwa a cikin soyayyar da take karewa a waje idan anje ciki a rasa tudun dafawa. Amma tabbas yau kam Sufyaan yayi awun gaba da hankalinta. Tun wuri kuwa gwamma ta tunasar da kanta wannan mutumin abun tsoro ne ba abun a tattala a so ba.

"Kin amince nazo ko?"

Wai shi baya gajiya ne? Ta san maganinsa kuwa indai yace shi naci ya sa a gaba. Don haka ta gyada kanta.

"Kiyi magana naji."

Yo ai dole tayi maganar. Ina ita ina musawa? Sarkin bada umarnin duk duniya ya bada oda. "Na amince."

"Ga 'yan biyunki can ta gama nuna musu makarantar nan a zagaye na uku. Kafun ta idar da na hudun bari mu dakata haka nan. Kar mu kara wahalar da ita."

Wato yana nufin Salmah kenan. Bata gyara masa kurensa na cewa Salmah 'yan biyunta da yayi ba ta barshi a hakan. A sannu zai gane. Koda kansu daya, kowaccensu da kamanninta. Salmah na da zagayayyen fuska kuma tafi Siddiqah hasken fata, yayinda Siddiqah ta fita tsawo, tsawon hanci da kuma bakar fata.

Sufyaan yana fadin hakan ya mike ya bar kujerar direban. Ya zaga kujerar baya ya fiddo wasu kyawawan ledoji masu taushi da kala sannan ya dago ya mika mata su.

Bata yi tsammanin ya sake maida hankalinsa kanta ba amma ji takeyi kamar idanunsa suna tafiya a jikinta. Yau wannan mutumin anyi maye a gun. Tana zaman-zamanta yazo zai wargaza mata lissafi.

Kafun ta ce wani abu sai ga su Yaya Tijjani sun dawo wurinsu har ana sallama.

Ledojin hannunta dai shake suke da makulashen su cakulet da kayan dadi irin na marmarin dan makaranta. Amma Allah sutru bukwui taci abun hannun saurayi. Bare wannan mai fitowa a mafarki kafun ya iso da kansan. Yazo ya kwashi abunsa idan ta tara masa.

***

"Ban gane baza a ci ba. Malama idan baki ci bamu guri, ai idan ma abu a ka zuba mu bazai kama mu ba, tunda mu dai ba Siddiqah bane. Kunga, Lailah, Ruqy miko farantin can kiga na mana kasafi. Har jus din gwangwanin ma bazaki sha ba? Hala allura yayiwa jus din."

"Ni dai Sally na kama ledar." Ruqayya ta fada tana jujjuya leda mai taushin da daga gani daga kanti mai tsada yayi tattaki ya iso har kwanarsu a dalilin Siddiqah.

Siddiqah kam kwafa tayi. "Kuyi tayi dai, zaku sani ai idan kuka ci masifa."

Tunda su Yaya Tijjani suka tashi Siddiqah take jin kamar ba a kan kafafunta take tafe ba. Wannan al'amari ya tsorata ta ba na wasa ba.

Hakan ne yasa tun a daren tayi kyakkyawar alwala ta buga nafilarta ta nemi tsarin Allah daga sharrin wannan mutum mai rikitar da tunani da fitowa a mafarkai.

Salmah kuwa tun akan hanya take wuntsule-wuntsule don neman jin me suka tattauna har tsawon awa guda. Siddiqah ta dubeta shekeke yanzu nan wai tsayawarta da Sufyaan har sun shafe awa guda suna tare? To ai bai wuci jumloli shida suka furta ba. Sauraro da kalle-kalle da buge-bugen zukata ko tace zuciya su suka cika lokacin.

Hodijam! Tana da aiki a gabanta.

***

A hanyarsu ta komawa Sufyaan yayi tsam cikin tunani. Tabbas zuciyarsa ta bashi kyakkyawar shawara domin kuwa gani daya yayi wa Maryama-Siddiqah yayi na'am da zabinsa ko da yake Tijjani ma yana da hannu daidai wa daida.

Wannan yasa ya kara godewa Allah ranar da ya budi baki ya kalli abokin nashi ya shaida masa bukatarsa na son kara aure.

Gashi hakan yayi sanadin zuwansu domin su dubo Siddiqah sannan ya gabatar mata da kanshi. Kai yau kam da ya ganta sai ya kara sanin cewa bazai yi zaben tumun dare ba cikin ikon Allah domin kuwa ta hada yawancin abubuwan da yake so yaga matarsa tana dasu.

Wato kulawa da abu, kuzari, natsuwa da kuma ilimi don daga dan kankanin zancen da sukayi da kuma ganin da ya mata ya san Maryama-Siddiqah yarinyace mai kwazo, yana son kuma uwar 'ya'yansa ta kasance mai kwazo. Yana son abokiyar zamansa ta zama wacce zata rinka gogayya dashi a fagen ilimi da sanin rayuwa.

Musamman da ta nuna masa cewa bata san ko shi waye ba, yaya zata amince dashi? Wannan ya gwada masa ita mace ce mai zurfin tunani.

Tunda ya kawar da wannan daga zuciyarsa sai ya samu sukunin gudanar da harkokinsa. 

***

DAN DAN DAN 

Siddiqah kina ruwa, wannan bawan Allah ya saka ki a to-do list dinsa.🙊🔥

Sufyaanu mai bayyana a mafarki. 🏃🏾‍♀️🤣

Ma'assalam.

Umm Yasmeen💞

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top