BABI NA GOMA SHABIYU


Dai-dai lokacin wasu mata biyu suka fito daga madafin dake dan karamin falon da suka shiga yanzu. Dayar tana sanye da koriyar riga ta shadda da aka mata dinkin bou-bou.

Bata kai Iyami haske da tsawo ba amma yanayin jikinsu zai zo daya, itace Iyami ta nuna tace "Siddiqah, wannan itace abokiyar zamata Haajar. Wannar kuma itace Aisha matar Lawan." Ta fada tana mai nuna matar da take sanye da riga da zani na jan batik. 

"Sannu da zuwa, barkanku da hanya." Haajar ta fada cikin fara'a hade da rungumeta. Aisha ma ta mata irin gaisuwar.

Sun zauna aka gaisa sannan Iyami tace "Ina fata bazaki damu ba, zamu dan karasa a nan kafun cikkunansu su fara kirar ciroma. Yanzu kya ji kira iri-iri."

Siddiqah tana murmushi tace "Ba komai me za a yi na saka muku hannu?"

"A'a kinga salon ki hadani fada da SBS, ba abunda zan saka ki yi."

"Aunty Iyami, kiyi hakuri muje. Ba komai da gaske, ba zai san ma na motsa ba."

Suna dariya Haajar tace "Da kyau Baban Hameeda ya gamu da gamonsa. Shigo 'yar uwa ki ga. Aikin mutanen namu tamkar ta masarauta guda."

Suna dariya suka shige ciki, ba tare da ta cire abayarta ba ta karbi abunda zata taya su dashi, ana hira suna yanke-yanke da dafe-dafe. Kafun ace me sun harhada abunda ya saura na shirin abincin nasu na dare.

Daga hirar su ne Siddiqah ta fahimci Iyami mutumiyar jahar Kano ce kuma auren gida sukayi da Dawuud. Sannan daga ita har da Dawuud 'ya'yan sarauta ne daga gidan sarautar garinsu suka fito. Yayinda kuma Haajar 'yar Katsina ce shekarunsu biyar da aure da Dawuud.

Aisha da Lawan kuma dukkansu mutanen Adamawa ne. Akwai kyakkyawar mu'amala tsakaninsu da iyalan SBS don haka bata zake ba ganin yanzu shigowarta cikinsu. A hankali zata karance su.

Sai dai ba abunda ya mata dadi kamar yanda suka karbe ta hannu bibbiyu. Duk da cewa dukkansu sun girme ta sosai a kalla Iyami zata yi sa'ar Raliya, Haajar ce ma take ga zata iya bata shekaru hudu zuwa biyar.

Bayaga zancen Iyami a shigowarta gidan babu wanda ya ambaci Amina ko kuma ya nuna mata wariya. Har suka zauna aka ci abinci a tire guda, suna ci suna hira suna karawa bayan sun sallami yaransu da kuma mazajen nasu.

Sunyi hira sosai suna bata labarin farkon zuwansu duka. Hakan yasa itama ta fada musu nata labarin zuwan, cikin 'yar wayewarta ta dauke fada musu yanda ta lalace a kallon haske da tayi tangararau lokacin saukarsu a birnin Khartoum.

Sun dan jima suna hira a nan sannan suka koma masaukinsu.

***

Suna shirin bacci ne Sufyaan ya tambayeta ko taji dadin ziyarar tasu.

"Maa sha Allah, dukkansu suna da kirki da faram-faram, banji tamkar a yau kawai na san su ba."

"Na kuma sanki da kamewa idan kin hadu da sabbin mutane har ma wanda kika dade tare da su din sai ranki ya dauki mutum kike bin ta kansa."

Bude baki tayi cikin mamaki, sai Sufyaan yayi dariya, "But, that's saying a lot akan haduwarku da su Iyami. Hakan na nufin kece kika bude musu da kyau har suka ji dadin sake miki suka karbe ki hannu bibbiyu. Naji dadin hakan kwarai."

Ganin yanda bai boye mata abunda yake ji ba game da hakan yasa tace, "Hala abotanku ya dade sosai?" Duk da yace sunyi makaranta tare ba kowa bane zakayi karatu dashi ku shaku irin wannan shakuwar dasu. Ta shiga cire dankunnayenta tana sauraren amsarsa.

"Tare muka taso, kusan za a iya cewa amintaka ce a tsakaninmu."

Kai ta jinjina, fara'arta na makale a fuska. Zata kwanta ne ta tuna batayi alwala ba ta mike ta shiga bandaki.

Sai da ta kwanta tana shirin rufuwa ta kula da idanun Sufyaan a kanta. Don haka tace "Na'am?" A tunaninta ya mata magana ne bata ji shi ba.

Girgiza kai kawai yayi murmushi yace "Allah Ya kara miki albarka da kokari kan dabi'unki kyawawa, Mar'yam."

Rufe idanu tayi jin addu'ar da ya mata ta shiga yin murmushi.

"Nima bari nayi alwalar sai na zo a kara min karatu."

Ware idanunta tayi tace, "Karatu kuma? Ni kuma me na sani da baka sani ba?"

Zama yayi a bakin gadon yace, "Ki bari idan na gama daukan darussan zan fada miki su daya bayan daya. A ina kika koyi yin alwala kafun bacci?"

"Babu, kawai dai na san a gida Baba yakan ce damu kar mu taba kwanciya bamuyi alwala ba sannan kar mu yarda sallar shafa'i da wutri su wuce mu duk rintsi ko me mukeyi a ko ina muke a duniya, babban asarar da zamuyi shine mu bari sallar wutri ta shige mu."

"Madallah da Baba, kwarai ina godiya Allah Ya saka mishi da mafificin alkhairi. Ya sada mu duka a aljannah, kwarai ya mini kokari sosai."

Yana gama fadan haka ya shiga yayi alwalar sannan ya dawo ya kwanta a gefenta hade da jawo ta jikinsa. "Kin san fa'idar yin wannan alwala ta bacci?"

Siddiqah ta dan tabe baki cikin alamar nazari sannan tace, "Yana hana dai mugun mafarkai..."

"Da me kuma?"

Zuwa yanzu ta saba da yanayin hirar Sufyaan, shi mutum ne mai matukar son jin ra'ayin mutane game da abubuwa, don haka a kullum baya ingiza nashi ra'ayin a kan mutane, ya faye tambayoyi ne ba don ya kure mutum ba, sai don ya karanci mutum da kyau. A iya saninta da shi ta fahimci hakan. Don haka ta saba da siffar hirar su ta tambaya da amsa.

"Shikenan iya abunda na sani."

Murmushi yayi ya sumbaci goshinta, wanda ta jishi har tafin kafafunta. A tunaninta zuwa yanzu yaci ace ta saba amma duk sanda ya rike ta sai taji wannan ziryar a ilahirin jikinta.

Bayan ya dago ne yace "To zan fada miki fa'idar yin wannan alwalar kullum guda daya amma da sharadin kema kullum zaki na koya min sabon karatu."

"Allah, ni dai ba abunda na sani. Kai da ka girma gaban Kawu, ko ba cewa kayi shi malami bane da yake raye?"

"To ce miki akayi malamai basa tafiya karo ilimi? Bare Dan malam? Ai kinga sai da karin karatu ake kara sani."

Lumshe idanunta tayi ta sauke ajiyar zuciya. "To naji, amma idan ban san karatun ba zan ce ban iya ba."

"Hakan ya wadatar. Kin ga, dalili na biyu shine a halin yanzu duk wani shaidani ya nisance ki, haka ya nisance ni a dalilin alwalar da ke tare damu, saboda annabi SAW yace 'duk wanda ya kwanta da alwala yana da mala'ikan da zai kasance dashi iya tsawon daren yana cewa Ya Allah ka yafewa bawanka ya kwanta cikin yanayi na tsarki.' Hakan ya sa ko a lokacin bacci ko wajensa yake da kyau mutum ya zauna cikin alwalwa a kodayaushe. Kin san me hakan yake nufi kuma?"

Kai ta girgiza masa. "Yana nufin muna tare da albarkar Allah. Babu komai a tsakaninmu a halin yanzu sai alkhairi da falalar Ubangiji."

Shiru tayi zuciyarta tana ta balli-balli cikin sauraren ci gaban bayanin nasa sai taji yayi shiru. Ta dago idanu ta kalle shi a hankali, "Shikenan, na gama nawa darasin saura naki."

"Meye tambayarka to?"

Zai fara magana ne tayi sauri ta rufe masa bakinsa da 'yan yatsunta, "Kar ka min dariya idan ban sani ba fa."

Murmushinsa mai sauti yayi sai da ta ji shi har cikin ranta kafun yayi magana, "Me kika fi so a tare dani?" Ganin ta kifta idanu, yasa Sufyaan ya rage muryarsa kadan ya sake cewa, "Me kika fi so na miki?"

Da farko bata fahimci komai ba, sai a hankali manufar tambayarsa ta sauko mata. Ya Rabbal 'alameena! Yau ga mutum a nan!

Kirjinta ne ya shiga bugawa babu kakkautawa, yayinda jikinta ya hau rawa. Yau kam ta mutu murus! Sufyaan ya hallaka ta har 'bargo. Yaya za ayi ta fara irin wannan babban zancen da shi? Dama irin abun da ya sa ta amince dashi kenan? Yau har tsawon kwana nawa zasu dauka suna karatun fa'idar alwalar bacci? Wasu irin karatu zai nema daga gurinta tunda a ranar farko an fara da irin wannan? Yau tata ta sameta.

"Ina sauraren ki." Ya fada kasa-kasa dai-dai kunnenta cikin muyarsa mai zurfi.

Ai yau dai kam sai dai a kankareta daga inda take, rufe idanu zatayi tayi tamkar tayi bacci ko me zatayi? Idan dai Sufyaan ne ya rinka mata wannan tambayar kenan har sai ta rasa inda zata saka kanta.

Don haka ta nisa. Idanunta a rufe ta isa daidai kunnenshi amma maimakon ta ce masa komai sai ta shafi gefen fuskarsa da numfashinta bata tsaya ba har ta dawo da kanta kan kafadarsa. Cak ta tsaya da ta fuskanci abunda yasa ta aikata dai-dai lokacin da ya riko hannunta cikin nasa.

An kusa wullata gidansu yau kam. Amma cikin tsananin mamaki mai kaduwa, sai ji tayi ya maimaita mata abunda ta masa yanzu.

"Sai me kuma?" Ya rada mata a hankali. Tana da tabbacin ta narke sai dai a kwashi ruwanta kawai.

Yau me ta sayawa kanta?!

***

Da sassafe ta fito wajen otel dinsu ta zagaya titin unguwar da sukayi masauki. Anan ne ta kara ganin yanayin yanda mutanen garin suke gudanar da rayuwarsu. Tana jin labarin tafiya a kullum, sai kuwa taga tabbas tafiya mabudin ilimi.

Jakuna ne taga suna ta wucewa kowanne da keke a bayansa a daure. Ga tulun dalma nan a jere a jikinsu. Kowani abun hawa ana bi gida-gida suna sayar da madara. "A fito a sayi madara. A sayi madara." Ta dai fahimci wannan kam.

Haka nan suka bata sha'awa ta bata lokaci sur tana ta kallonsu har sai da ta gaji don kanta ta hantsi yayi nisa sannan ta koma masaukinsu na otel. Sufyaan na dawowa tace masa "Don Allah gobe mu fita da safe idan ba abunda zakayi?"

 Ita kanta bata san tambayarta ta fito a marairaice ba, sai da ya kankance idanunsa ya dubeta da kyau, "Kina da wurin zuwa ne?"

Rufe idanunta tayi da tafukan hannunta sannan tace, "A'ah jakkan nan nake so nayi ta kallo na ga daga ina suke fitowa."

Sufyaan ya daga girarsa sama yana jira tayi dariya tace wasa takeyi, sai yaga babu alamar hakan a tare da ita, asali ma jira takeyi ya amsa mata bukatarta. "Jakkai dai?"

Ta gyada masa kanta, Sufyaan yayi murmushi yace "Jakuna ake cewa."

"Oh to jakuna. Ba ka ga suna burge ka ba?"

A maimakon taga yayi dariya sosai yanda tayi tsammani, sai ya mata murmushi idanunsa suna kyalli yace, "Shiga ki shirya ki zo."

"Yanzu?"

"Ke kam dai jakuna kike so ki kalla, ina ce?"

Da sauri ta gyada masa kai.

Tana shiga ciki ta kimtsa ta saka wata doguwar riga mai ruwan daurawa da zanen fulawowi bakake, ta rufe saman kanta da mayafi har ya sauko ya rufeta sannan ta dauki madubin idanunta masu rage karfin rana da ya sayo mata ta saka ta daura siririn agogonta ta rataye jakarta mai dogon igiya sannan ta fito falon otel din nasu ta same shi a nan.

Kare mata kallo yayi kamar zai ce wani abu sai kuma ya nisa ya mike ba tare da yayi magana ba.

Suna fita wurin adana motoci suka nufa, inda suka samu motar wani basudane da Dawuud ya hadasu da shi zai na kaisu wurare mai suna Zaki. Tun da suka shiga motar Zaki, bata tambaye shi ina zai kaita ba. Ita dai nata idanu, ana tafe tana kalle-kallen ababen dabi'u da al'adu na mutanen Khartoum.

Abunda ta fara kula dashi shine yanda suke da soyayya da shayi, domin duk inda suka gitta sai taga masu shayi, kuma babban abunda ya dauki hankalinta shine kasancewarsu mata da lufayunsu a jiki. Wurare da dama kuwa hayaki na tashi, ga maza nan wasu na kan kujerun roba suna rike da kofunan su wasu na tsugunne a gefe wasu ko suna zazzaune kan gadajen bono da aka musu shimfidi masu launuka daban-daban suna zuke-zuke daga jikin wani bututu. Haka dai tayi ta kallon ababen da suke baki a gareta.

Duk inda suka gitta kamshi ne ke tashi na musamman.

Lokacin da suka fita rana bata karasa faduwa ba, suna wuce bas-bas masu launin daurawa da masu fararen launuka kan hanya, sai takeji kamar birnin Legas suka koma.

Suna tafiya a sannu sai ta kula sun bar cikin birni sun fara shiga wani bangare na wani karamin gari, can kuma suka shiga wani guri mai yashi, idan za a danganta gurin da inda suka fito to sai dai a kira nan da ruga ko karkara.

Ai tun kafun su kawo wurin take ta ganin wadannan jakunan suna ta wuce su a hanya. Har kan titi suna nan dai-dai kan kwana. A wannan karkarar mai cike da gidajen kasa suka tsaya inda mutumin da yake musu jagora, Zaki, ya ci gaba da musu bayani, "Na san zasuyi murnar zuwanku." Siddiqah dai taga fara'arsa taki ta kare. Don haka ta kalli Sufyaan.

"Na fada masa ina so ya kawo mu inda zamu samu ganin 'jakkai', yace idan na amince zai kaimu gidansu suna dasu da yawa, mahaifinsa yana sana'a dasu."

Idanunta ta ware, "Hn! Dama ka san da hakan kace mu tafi?"

"Sai da muka fito kasan otel mukayi maganar da shi. "

"Da ina zaka kaini to?"

Murmushi yayi, "Duk inda manmu ya kare."

Tana dariya ta girgiza kanta.

Hannun Siddiqah na sakale cikin na Sufyaan suka ratsa yashin nan, ita ko jin zafin garin ma bata yi murna fal ya cikata, sai kallon cicirandon dabbobi iri-iri takeyi. Wani gida sukayi sallama inda Zaki ya shiga jagoranci da bayani, har dakin kakarsa sai da ya kaisu suka gaisa ya kuma ce Sufyaan mutumin maigidansa ne, wannan kuma amaryarsa ce.

Tsohuwar da taji Zaki yana ta kira Habboba ta shiga jero musu addu'o'i, Maman Zaki kuma tana lullube da lufaya wanda ta saka shi saman riga sakakkiya da fatari. Sai dariya take musu tsananin farin ciki ya cika su.

Tun kafun dan jagorarsu Zaki, ya yi bayanin musabbabin zuwansu an cike gabansu da shayi da kofuna kanana akan tire. Nan da nan aka rinka sauke ababen tarba ana haba-haba da su kamar an sansu dama.

Da kanshi mai gidan wanda ya kira kansa da Mu'ammar, ya debe su ya nuna masu dabbobin kiwonsa. Yana alfahari da aikin da yakeyi na sayar da madara a gari. Sai da rana ta gama faduwa har ma sukayi sallarsu sannan suka yi musu sallama.

Matar Zaki ta hadasu da madara ta tsaraba jarka guda. Banda wanda aka basu tare da abinci dazun.

Girgiza kanta tayi tace "Da kin barshi, ai mun sha a nan ma mun gode." Da ta fara larabcin ta dai carke ta mance wasu kalmomin don haka ta dubi Zaki don yayi agaji.

Sai Sufyaan ya dubeta yace, "Ba komai ki karba ai tayi niyya, ba a mayar da hannun kyauta baya."

Haka dai ta amince ta karba, Matar ta jinjinawa Sufyaan don ta fahimci shi yasa Siddiqah karbar kyautarta.

Ita tunaninta, mutane basu san da zuwansu ba, sun masu tarba ta musamman sannan ta buge da karbar musu abun sana'arsu?

Zaki ne aka bari da jido jarkar madarar. Suka dauki hanyar komawarsu. Ai kuma ba ayi nisa ba, Siddiqah taji cikinta ya juya. Nan da nan zuciyarta ta hau zafi.

"Siddiqah, lafiya?"

Kai ta kada masa take ta addu'ar suje masauki lafiya.

Cikinta ta damka da hannunta yayi saurin cewa Zaki ya dan hanzarta zuwa masauki. Ai ko suna shiga dakinsu bandaki ta wuce ta fara hararwa sai da taji kamar duk hanjinta zasu fita.

Sai da ta kurkure bakinta ta mayar da numfashi sannan ta dago kanta, Sufyaan kuwa yana rike da kafadunta har ta samu natsuwa. Shi ya tattaro mayafinta dama da jakarta lokacin da ta rugo a guje. Yanzu kuwa yace mata sannu sunyi dubu.

Da ta dawo dakin zaunar da ita yayi yaji tana maida numfashi.

A hankali ya dubeta yayi murmushi yace "Yau kin san kin sha madara. Saura muje wurin masu biredi gobe ko?"

Tana dan tura bakinta tace "Don Allah a zubar da na jarkar da suka bamu, bana so na tuna sunan abun."

Sufyaan yana dariya yace, "Babu inda za a kaishi, shi zan na sha kullum."

Idanunta ta waro hade da yin sabon yunkuri da sauri ya taro ta amma sai ya ga ta zauna, "Basu dafa da kyau ba fa."

"Haka suka ce miki? Saboda baki saba sha bane. Camel milk ce."

"Hum'um sai dai kayi ta shan kayanka to kai kadai. Ni kam kar ka kara kira min sunan abun."

Har dare sai zolayarta yakeyi, "Siddiqah 'yar fulani mai madara." Amma hakan bai hana ya kaita asibiti ba aga ko da matsala a tare da ita, an tabbatar masa lafiyarta kalau sannan suka koma gida.

Washegari a kan tsibiri suka riski bullowar rana. Ta zaci wasa Sufyaan yakeyi da ya ce mata ta tashi su fita tun kafun ayi sallar asuba. Wanka kawai sukayi hade da alwala. 

Ya dai dauki abun sallah don haka hankalinta ya dan kwanta, amma ta rasa gane inda zasu je da asubar fari.

Tana kallon Zaki a tsaye gurin motarsa sai ta san lalle fitar zasuyi, amma kallon Zaki sai da ya tuna mata da cikinta a daren jiya. Yana mata fara'a, dole ta sakar masa da fara'a ta amsa gaisuwarshi.

Suna tafiya har suka isa kan wani tsibiri. A can sukayi sallar asuba, tana jira taji bayani daga Sufyaan amma bai ce mata komai ba har suka kammala adhkaar dinsu. Ita dai sanyin yanayin garin ne ya mata dadi, dadin karawa suna zaune ne kusa da ruwa don haka babu zancen zafi irin na garin a wannan lokacin.

"Daga idanunki ki kalli can."

Ya fada yana kallon saman kanta, don haka ta dan juya, sai da ta kankance idanunta lokacin da ta ankara da rana ne yake bullowa.

Yanzu dama duk wannan uban sammakon da suka doka don su ga wannan ne?

Bata idda tunaninta ba, taga Sufyaan ya mikawa Zaki kamarar hannunsa yace ya dauke su a hoto.

Zuwa yanzu ta gama lakantar Sufyaan da son daukar hotonsa, ko dai ya musu su biyu ko ya bayar a dauke su ko kuma ya sa ta dauke shi ko kuma lalle ya sa ta tsaya ya dauke ta itama.

Don zuwansu kasar nan ma cikin kwanaki uku kacal sai da ya tambayi ko akwai dakin daukar hoto nan kusa.

Ana daukar hoto tana juyawa taga yanda launukan suke gaurayewa cikin juna, rana na bullowa cikin hikimar ubangiji.

"Tunda kin zana faduwar rana a sararin hamada, saura bullowar rana a saman teku." Ya fada yayinda idanunsa suke kanta.

Tab har yanzu bai mance da zanen da ta fada masa tanayi ba lokacin da yake neman aurenta farko-farko? Kodayake a sannu sai da ya sa ta bashi wannan zanen.

Watakila shine dalilin da yasa ya saya mata kayan zanen da ke zaune a falonta na Kano a halin yanzu.

Haka suka zauna a gurin har ranar ta gama tasowa. Sannan suka tafi yawo a bakin tekun suna 'yan hirarrakinsu, tana kallon wasu daga jama'ar garin a zazzaune kan 'yan kujerun roba suma sun fito shan iskar duniya yawancinsu da kofunan shayi a hannayensu.

Nan suka karasa wurin masu shayin da suke jejjere a bakin tekun, inda suka tsaya, Sufyaan ya saya musu fanken da ta ga an turbude shi cikin suga, wanda taji ya kira zalabiya, sannan aka saka musu gahwa. Nan suka samu wuri suka zauna suka karya.

Ita dai Siddiqah gani takeyi kamar ruwan zai hadiye su ganin girmansa a gabanta. Amma taga kowa harkarsa yakeyi ko a jikinsa.

Daga nan gidan tarihi Zaki ya ce zai wuce dasu, hade da bayanin yafi dadi a dauki hanya da wuri. Ashe shi yasan dalilin fada musu haka, domin tafiya ce mai tsawo sukayi na kusan awanni biyar sannan suka isa.

Tun akan hanya Siddiqah ta fara hango Dala masu yawa ita duk iya jin labarinta kasar Misra ce take da Dala sai gasu yau ta gansu masu yawa a kasar Sudan.

Lokacin da suka isa wurin zuwan su ne Siddiqah ta dubi Sufyaan tace masa, "Me yasa baka taba fada min son tafiye-tafiye da bincikenka ya kai intiha ba?"

Dariya yayi sosai yace, "Ina baki wahala ko?"

Daga kafadarta tayi tana murmushi ta saka gogul dinta  masu duhutace "Nima ina jin dadin tafiyar, Allah Ya sa kar wannan abun dai ya ruso a kanmu, wai nan gurin zamu shiga?"

"Zo ki gani."

Kallonsa tayi kamar mai tambayar ko ya san abunda yakeyi. Haka suka tadda wani mutumi mai farin gashi da babban farin rawani akansa shine dan jagorar da yake bayani a wannan wurin, shi ya isar da su kasan wannan tsohon wuri mai kama da kofar kabarin.

Itadai fatanta a gama a fito lafiya.

Sai dai ko da suka shiga abunda ta gani a ciki yasa ta mance a ina ma take. Gashi nan zanunnuka ne da sukayi shekaru aru-aru a wurin da kayan tarihi iri-iri duk a tare a ciki. Mance kanta tayi tana dube-dube.

Daga karshe dutsen Barkal suka hau inda suka hango jerin Dala da ma tekun nil. Sai da sukayi tilis suka karasa garin Karima.

Sai yanzu t afahimci duk Sufyaan ya tsara wadannan ababen tun kafun fitowarsu ne. Tunda har jakarta an sauke daga bayan motar Zaki. 

Nan aka basu wurin hutawa, ga faranti nan an shake shi da gyada mabanbanta da su dabino ga butar gahwa nan duk kan teburin. Sai da suka ci abinci sannan aka karasa dasu dakinsu.

 Ajiyar zuciya tayi cikin jin dadi da ta hango shiryayyen gado. Ba tare da wani dogon bayani ba ta mike akai. Sai daga baya ta tashi ta watsa ruwa tayi alwala. Can da yamma farfajiyar wurin suka fito suka zauna kan wasu kujeru, suna hirarsu har aka kawo musu abincin dare.

A wannan yinin Siddiqah taji zuciyarta ta cike fal da wani farin ciki marar misaltuwa. Wannan yasa washegari suna komawa masaukinsu tayi abunda bata taba yi ba.

Kan yatsun kafafunta ta tsaya cikin dagelgel hade da sa hannayenta saman wuyan Sufyaan ta masa kawanya, ta riko sa cikin jikinta. A hankali ta samu kanta da juyawa kadan har labbanta suka kai kasan kunnenshi ta kai masa 'yar karamar sumba.

Da sauri ta sake shi ta sauka zata juya, sai riketa yayi gam ya hanata juyawa. Murmushi ya mata yace "Nine da godiya, Mar'yam. I had a wonderful time."

Itama murmushin ta mayar masa ta sauke ganinta kasa.

***

Jakar hannunta ta fara shigarwa cikin motar sannan ta shiga ta zauna, Sufyaan ya shigo ta daya kofar. Cikin 'yan kwanakin nan daga taga Zaki ta san dawar garin. An samo sabon wurin da za a kaisu ne. Kama daga gidan kifi, zuwa Qasr alJamhuuri, Shara'an Nile, wuraren shakatawa, da gidajen hutu har jami'arsu sai da Zaki ya kaisu.

A takaice dai sai da Sufyaan yasa taji son garin ya ratsata da kyau, yanda ko zama akace tazo tayi na dindindin bazata ji wani haufi ba.

***

Wadannan kwanaki da suka dauka a kasar Sudan ba karamin kusanci ya kara mata da Sufyaan ba, a nan ne ta kara fahimtar shi mutum ne mai asalin sauki da kulawa da kuma nuna kauna muraran muddin ka fahimce shi. Duk lokacin da zai fita daga masaukinsu sai ya dawo mata da cakulet saboda ya san tana so. Wasu lokutan ita yake dauka suje manyan kantunansu ta zabi ababen da take so.

A wannan 'yan kwanakin idan da rayuwa zata tsaya cak to da zata iya cewa, zummar ganin inda labarinta ko mafarkinta da Sufyaan ya nufa ya kaita ga cimma kamilalliyar rayuwa.

Saboda a nan ne ta mance duk wata damuwa da rayuwa bayaga rayuwarta da Sufyaan, ta mance da batun Amina da tunanin irin zaman da zasuyi, ta mance batun yankakkiyar soyayyar da bata da tabbas. Ita dai kawai a yanzunta take rayuwa.

***

Ana washegari zasu tafi ne suka hadu a gidan Lawan akayi 'yar kwarya-kwaryar liyafa ta tafiyarsu. Wannan karon fir suka hana Siddiqah aikata komai, nan suka cika su da nau'ukan abinci ciki kuwa harda wani abu da taga sunyi shi kamar kosai an saka ganyen parsley wanda suka kira 'da'miyyah, taji dadinsa kwarai har ta nemi su fada mata yanda sukayi shi.

Bayan sun bar gidan Lawan ne ya kaita kasuwa don tayi sayayyar tsaraba ta komawa gida. Nan Zaki ya kaisu Souq Libya yace nan zasu fi samun kaya sosai. Ita har mamakin yanda shiga kasuwa baya damun Sufyaan takeyi. Tashinta ta san mata ke zuwa kasuwa a gidansu don haka take mamaki.

Amma a al'amari na Sufyaan Barkindo Sajoh ta soma sanin ta shirya kanta domin amsar dukkan abun mamakin da zai fito daga gareshi.

Tunanin Maryama-Siddiqah daya ne, shin idan sun koma gida haka rayuwa zata ci gaba da gudana musu?

Ajiyar zuciya tayi tare da fatar ko za a samu wani sauyi na kasa ko al'ada ko tafiya, Sufyaan ya zauna a matsayinsa na Sufyaan dinta.

***

Ehem ehem... Siddi Mama next level things.🙊🔥 The whole Sufyaan is now hers. Amina...🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️.

Da fatan kuna lafiya, ma sha Allah. Allah Ya sake dawo da mu Juma'a. Sai mu gode maSa mu kuma ci gaba dai da neman falalar da ke cikin ranar. Allah sa mu dace ameen.

An gama watayawa za a koma gida, me ke tafe wa Maryama-Siddiqah? 🤔

Shin tsoronta zai zamo gaskiya ko kuwa dai haka za a ci gaba da tarairayarta? Yanzu dai muka soma labarin nan. 

Ababen mamaki da nishadi da kuma ban tausayi suna nan tafe a gaba. Kowa ta shirya a kuma rike guzurinmu na kullum.

(Kwalin tishu fefa.🙊🤣 )

Ma'assalam.

Umm Yasmeen.💞

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top