BABI NA GOMA
Capital Ehem Ehem 🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️
Mun dau hanyar Kano!🤣
***
Lokacin da suka dauki hanyar Kano, wuraren karfe sha daya saura na safe ne, saboda duk yanda Sufyaan yaso su tafi karfe goma sai da Hajiya Amina ta sa ya dakata saboda bakin da suke son su ga Siddiqah kan su wuce.
Sunyi bankwana da duk 'yan uwan Sufyaan da suke nan. Inda kanwarsa wacce Siddiqah ta fahimci itace Asma'u ta gwada mata waye ne waye.
Akwai Yaya Gimbiya wacce take zaune kan kujera lokacin da suka shiga falon da safe, duk da kasancewarta suna kama da Sufyaan hatta launin fatarsu mai dan duhu, bata da fara'ar sauran yaran Hajiya Amina. Hatta mazan sai da suka shigo aka gaisa.
Bayan sun fita an yi hotuna kadan suka kara masu fatan alkhairi sannan suka dauki haramar tafiya.
Ita dai Siddiqah tayi kasake tana ganin yanda kowannensu babu abunda ya barwa dan uwansa, sai dai wata ta fi wata hasken fata ko wani yafi wani girma a shekare. Amma 'yan gidansu Sufyaan kama sukeyi sosai. Ta tsinkayi kaunar junansu muraran a tare da su.
Guzuri aka musu na nama da gasassun zabbi da ruwan sha, harda jarkokin tataccen madarar shanu hade da wasu kayan cimar na fulawa da su cingam da goro duk aka shake musu boot dashi saboda hanyar da zasu dauka.
A safiyar ne sukayi sallama da Umma Gaggi, inda itama zata koma Gombe bada jimawa ba wannan yasa itama bata kara tsawon lokaci ba suka dauki hanyarsu ta komawa.
Tafiyarsu ta sha banban a zuwa Kano daga zuwansu Jabbi Lamba ganin yanzu bata kuka sannan kuma hankalinta yana kan labaran da Sufyaan yake kara bata dangane da 'yan uwansa da suka hadu dasu a yau din. A wani zubin kuma yakan bata labarin ziyarar da ya taba kaiwa garuruwan da suka gani a hanya.
Can kuma yace itama idan anzo garin da ta taba zuwa ta bashi labari.
"Kai dai ka ci gaba da labarin, ni ko na je ban san ta ina zan fara ba. Ballantana banda Potiskum ina na taba zuwa?"
Murmushi yayi ya kara rage sautin muryarsa, "Daga yau kema sai kice kinje Jabbi Lamba."
Dariya tayi har hakoranta suka fito. Bayan sun tsaya a hanya sunyi sallolinsu sun koma mota ne Sufyaan ya dubeta yace "Akwai bacci a idanunki, ki huta tukun sai mu ci gaba da bayanin anjima."
Zata musa masa ne, hamma ya zo mata don haka sukayi dariya su duka biyun. Bata san lokacin da ta sulale barin jikinsa ba tayi baccinta mai tsawo sai da ta farka ta jita a jikinsa ta san a hakan tayi bacci, ko dai a haka ko kuma shi yasan yanda akayi ta isa gurin. Da sauri ta shiga kimtsawa hade da dan taba gefen bakinta kar tayi yawun bacci bata sani ba. Yanda ta gajin nan hala har minshari ta yi ta masa.
Don haka ta zauna kikam taki yarda ta sake gyangyadawa, sai dai ya fizge ta ta kara gyara zamanta.
Ajiyar zuciya yayi a gefenta yace, "Kar ki damu bakiyi sosai ba. Malam Jibrin baiji ba."
Ware idanu tayi da sauri ta juya tana kallon wajen tagar motar. Ai har suka shiga cikin garin Kano wajen karfe tara taki yarda ta kalleshi, sai da yace wasa yake mata batayi minshari ba tukunna ta saki jiki.
Amma duk da haka ba wai ta yarda dashi bane.
***
Kamar yanda ta fadawa Sufyaan, tsakaninta da Kano lokacin da Babanta yake Ambasada idan zasu tafi Saudiyya, don haka ta dau shekaru bata je garin ba. A lokacin da suka rage tafiya alamun sun shiga cikin gari sosai, bata san wace hanya suka dauka ba bare ta san sunan unguwar da suka dosa. Can taga sun iso wani gida wanda wutan waje jajaye ne amma ba a wadata wajen da haske sosai ba bayaga ta wurin mashigar motoci.
Koda suka shiga cikin farfajiyar gidan idanunta ne suka ware saboda gari guda ta gani a ciki. Ta rasa irin jawabin Sufyaan, idan ya tashi sai yayi ta cewa dakin ta ko bangarenta. Bata gama fita daga al'ajabin gidansa a Jabbi Lamba ba ga nan ya kawota wani gari guda.
A kiyasin ta tsakanin sashi da sashi da ta gani a cikin farfajiyar wannan gidan yaci a gina wasu irinsu guda takwas.
Juyawa tayi ta kalleshi sannan ta mayar da kallonta ga inda suka nufa a fakaice. Zai iya yiwuwa shi da kannensa ne cikin gidan, ko kuwa shi da wani abokinsa suke amfani da gidajen.
Don haka batayi saurin yin tambaya ba. Da kyar idanunta suke buduwa don gajiya. Amma haka ta daure ta fita daga motar lokacin da suka tsaya.
Bata san labarin kayanta ba, tunda suna sauka Sufyaan ya nuna mata hanyar da zasu bi zuwa ciki.
Kai tsaye kofofin ciki ya shiga budewa. Da farko daki ya fara nuna mata sai da ta ajiye jakar hannunta sannan ya fita daga dakin. Bandaki ta shiga ta rage mararta ta dauro alwala sannan ta fito.
Dakin ta tsaya karewa kallo. Komai a saukake yake amma mai kayatarwa. Gadon dakin yana daf da kasa sannan kan gadon ya faro ne daga dungu daya zuwa daya dungun. A jikinsa kuma akwai ma'adana 'yan kanana da wasu durowowi, Sannan akwai wutace guda biyu a madadin yanda ake daurawa a durowar gefen gado wannan a jikin gadon akayisu. Har rediyo akwai shi a makale jikin wannan kan gadon.
Kanta ta jinjina sannan ta fiddo da hijabinta daga akwati. Tana shirin ta tambayeshi ina ne alkibla ta samu ya riga ya shimfida mata abun sallah. Alamar ya dawo bayan ta shiga alwala kenan.
Ko da ta idar da sallolinta, taga bai shigo ba, sai ta shiga da kayan wankanta bandaki da su brush.
Taji dadi da ta samu har ruwan yayi zafi don haka ta gasa jikinta sosai sannan ta fito ta shirya cikin wata duguwar riga yalwatacciya launin kasa mai haske da aka mata ado da zanen fure manya ruwan hoda.
Daya kofar da take cikin daki ta bude sai ta kula ya bulla wani daki ne don haka ta ja da sauri ta rufe. Ta dawo ta bude daya bangaren inda ta samu kayayyakinta da ta riga ta bayar aka taho dasu tun ranar Alhamis. Duk gasu nan a jere cikin akwatuna, daya bangaren wadrobe din kuma wasu sabbin bakaken akwatuna ne bisa dukkan alamu sune kayan lefenta, don bata taba ganin akwatunan ba tunda aka kai gidan Raliya.
Ta san aiki ne turum a gabanta, gashi yace ta kwana da shirin wata tafiyar zasu sakeyi washegari Litinin.
Sallamarsa taji a bakin kofa taji zuciyarta ta tsinke, sai da ta dan furzar da numfashi sannan ta samu natsuwar amsa masa sallamar.
"Idan kin kammala ga abinci an shirya mana."
Kai ta gyada masa kawai amma bakinta ya gagara motsi. Shima da alama ya kammala sallolinsa har ma ya watsa ruwa don ba kayayyakinsa na dazu bane a jikinsa, wata farar jallabiya mai wando ce a jikinsa.
Yanzun wani kamshi yakeyi daban da wanda ta saba ji daga gareshi, kawar da kanta tayi da wuri ta wuce inda yake, wanda a take ta kusa tayi dana sanin yin haka. Ta mance da manufarsa tun jiya da safe inda yake ta aikin wassafa mata tunani da ilahirin zuciyarta.
Yanzun hannunta ya rike, ta dawo da ganinta gareshi. Ba tare da yace mata komai ba taga ya sa hannu kan mayafinta da ta mance shi kan kafadarta ya daura mata akai "Yau akwai staff a gidan, basu tafi ba tukunna." Bayan ya fadi hakanne ya mata murmushi suka fita daga dakin.
Amma ita kam kunyace ta kamata kamar ta nitse kasa, kardai yayi tunanin ta bude kanta don ya gani ne da gangan. Ita da ko a cikin gida da dan mayafi take yawonta? Oh! Yau taga bone.
Ita dai ko wace dakikar da ta dauka tare da Sufyaan Barkindo Sajoh, mamakinta ne yake kara karuwa. Amma zuwa yanzu ta fahimci yin shirunta shi ya faye mata, idan ya so da kanshi ya bude mata komai. Don yanzu gani takeyi tamkar bata san da waye take zaune a gefenta ba.
Shin wannan ne mutumin da yaje gidan Adda Raliya yake cin suyar dankalinta, mutumin da yake sawa ta masa gashin kaji tana cewa bazata yi ba alhali shi mai iya daukar 'staff' ne na wucin gadi don su shirya masa abinci a gidansa? Wannan ne mutumin da yaje gurinta ta ruga a guje ta barshi har sai da ya gaji da zama ya koma inda ya fito?
Wani babban abu ta hadiya wanda ta tabbata ba romon kazar da take sha bane.
"Munyi waya da su Raliya sunce a gaishe ki, Tijjani yace gobe zasu koma in sha Allah sannan su Umma Gaggi sun isa lafiya suma."
Murmushi ta kakalo don ya kore rudanin da take ciki. "Alhamdulillah Allah Ya saukesu lafiya."
Nan ya shiga mata hira irin tasa, wacce jifa-jifa ce, kuma shi yake mata tambayoyi ita kuma tana bashi amsa idan ta sani.
"'Yan biyunki tana can tana kewarki ko?"
"Wa? Salmah? War haka ta jere kayanta a sashin saka kayana, ta baje komanta a ko ina, dama tace na takura mata. Amma na san tayi kewata zata yi ta kallon hotunan da mukayi kan na taho idan an kaisu gida."
Dariya yayi sosai har ma yasa itama ta dan saki jikinta suka kammala cin abincin su.
"Kina so kiga gidanki yanzu ko sai da safe?"
Zata iya gani yanzun ma, amma bata san me zata tarar ba. Sai dai kuma a daya bangaren bata ma so ta ambaci kalmar bacci a kusa da shi. Kamar ya kula da hakan ne yasa bai ma jira amsarta ba. Ya yi gaba yana magana, idan tana so taji abunda yake fada kuwa dole ta bi bayanshi don baya daga muryarsa.
Babban falo ne, sai dakin cin abinci, madafi, dakinta da wani dakin da ya nuna mata a matsayin nasa wanda ta kula shine wanda yake jikin nata tunda kofar ta bulla cikin sa. Sai wani dakin kuma daban daga an shigo falon ta gaba. Can ciki kuma kofar karshe karamin falo ne mai doguwar kujera daya, da kujera mai tsawo guda daya da teburi mai tsawo a kan teburin ne idanunta suka tsaya cak!
Manyan fararen takardu ne akai da wata bakar jaka mai siffar akwati, tun kafun ta bude tayi hasashen menene a ciki don haka ta daga idanu ta kalleshi da alamar tambaya, yana gyada mata kai ta rufe bakinta da hannayenta.
Setin fensura ne ya saya mata da kaloli na yin zanen ta. "Ban san me zan ce maka ba..."
"Kar kice komai, karamar kyautace, your wedding present. Duk lokacin da bana nan sai a zauna ayi ta zane ko?" Juyawa barin damansu tayi taga kusan rabin bangon wannan falon irin kofar gilas din nan ne da take hango shuke-shuke daf bakin gurin, babu inda zata fi son kasancewa irin wannan dakin da alama.
"To ni kuma babu abun da na kawo maka a matsayin kyautar ai."
Ta fada tana ta tunanin abunda ya dace itama ta bashi.
Fadada murmushinsa yayi yace, "Kar ki damu, tunda aka ce min Mabrook ya wadatar. Idan na tuna wani abunda nake so zan fada miki."
Tana jin hakan sai dadi ya cika ta fal. Wutar falon ya kashe sannan ya riko hannunta cikin nasa suka koma babban falon, fitowarsu ta kula da babu kwanukan da sukayi amfani dasu kan teburin sannan an rage karfin wutacen falon. Ko hakan na nufin mai aikin sa ne ya shigo ya kwashe kwanukan abincin ya fita?
"Bayan na kammala karatuna na digiri a QS na danyi aiki na shekara biyu kafun na koma nayi masters a kan ilimin tsare-tsaren birni (Urban Design) wannan ne sanadin samun aikina a Lagos."
Dago kanta tayi tana dubansa tare da tattare girarta cikin rashin fahimtar dalilin wannan hirar.
Murmushi yayi mai sauti sannan yace, "Naga yanayin da kika shiga tun isowarmu gidan nan, wannan yasa nake so na fahimtar dake game da wasu abubuwa, sannan na fiddake daga rudanin da kike ciki."
Ta bude baki zatayi magana, Sufyaan ya kada mata kansa kadan. Don haka ta zauna a gefensa inda ya nuna mata kan kujerar falon.
"Ina gamawa na samu kwangila da jahar Legas inda muka musu wani aiki na tsare-tsaren birni."
Haka ya ci gaba da mata bayanin yanda kudaden da aka biyasu na wannan kwangilar da su yayi amfani, shi da wasu abokan aikinsa suka fara kasuwanci. Kafun kace meye ya kirkiri nashi kamfanin ya fara budawa. Inda yafi bada karfi kan harkar gine-ginen gidaje da shaguna. Ko da babban birnin kasa ta koma Abuja can ma ya samu karin ayyuka da wasu kwangilolin. Daga nan babu kama hannu yaro wa Sufyaan Barkindo Sajoh.
A lokacin da duniya ta bude baki tana mamakin yanda dan Malam Barkindo mai koyar da yara karatun allo kuma magatakardar sakateriya yayi kudi lokaci guda, Sufyaan kwana yakeyi yana tsare-tsaren harkokinsa yanda komai zai tafi masa dai-dai gwargwado yana kuma rokon Allah ya fiddashi kunyar duniya da lahira dangane da sabuwar rayuwar da ya samu kanshi a ciki.
Bayi da wani dogon buri da ya shige kar ya taba rasa iko akan karan kansa ko wani al'amari da zai saka wadanda ya damu dasu da wadanda yake so a cikin hatsari. Bayan ya fadi hakane Siddiqah ta ciri kai ta dube shi, amma bai mata karin bayani akan dalilin da yasa yake da muhimmanci a gare shi kar ya rasa wannan 'control' da yake magana akai ba.
A yanda ta fahimta, Ya fawwalawa Allah rayuwarsa amma bai kwanta bacci ya jira yaga faruwar canji a rayuwarsa ba. Ya saka gumi da damtse don ganin babu abunda za a ce ya rasa saboda rashin gogewa da hanyar duniyar zamani ko kuwa rashin ilimi.
Tun yana yin hakan a matsayin hanyar samun mafita, gareshi da 'yan uwansa har yanzu hakan ya zame masa wani bangare na ginshikin rayuwarsa. Ya fada mata a karan kanshi ya kara samun yaqinin cewa duk abunda Allah Ya rubuta naka ne zai zo ya sameka inda kake matukar kaima ka tashi nemanshi.
"Don haka Mar'yam, ko yanzu da na ga kallon da yake idanun ki, na san ba na yanke hukunci akan ko ni wanene bane, sai na neman karin bayani dangane da abunda na rageki dashi ban fayyace miki ba na daga rayuwata lokacin da naje neman aurenki."
Janyo ta yayi barin jikinsa ya rike ta da kyau sannan yace "Kar ki bari wani abu daga cikin dukka wadannan ya dauke miki hankali, Mar'yam. Kar kuma kiyi tunanina da wata siga ta daban. Ina so har kullum ki sanni a matsayina na Sufyaan da yaje Potiskum don neman aurenki. Kar duk wani abunda zaki gani wanda na mallaka ya tsone miki idanu. Ina so ki sani ko wani kwandala, ko wani gini ko wani fili ko wace sana'a da nake yi da jinina da gumina na gina shi daga tushe. Kin fahimta ko?"
Kai kawai ta gyada masa tana lumshe idanunta lokacin da gashin idanun suka kwanta saman dan kuncinta sai da Sufyaan yaji zuciyarsa ta motsa.
"Na san kina da zurfin tunani, kuma kin san duk wanda ya dauka wani abunda ya mallaka zai bashi wani matsayi na musamman a duniya ko a gurin Allah bai fahimci rayuwa ba, muddin ba ta hanyar kwarai yake amfani da wannan damar ba. Domin yanda akayiwa ran dan Adam ajali, haka akayiwa dukiya wa'adi, haka akayiwa arziki wa'adi akwai ranar yinta akwai ranar kuma da kaf zasu iya karewa. Ko a tafi a barsu ko su tafi su bar mutum."
Siddiqah ta jinjina kanta jin bayanansa, dai-dai lokacin da ya kai labbansa ya sumbaci tsintsiyar hannunta kan inda jijiyarta ke bugawa.
Ba tare da ta iya daurewa ba ta samu kanta da lumshe idanunta, ta zuki numfashi. Zuciyarta kuwa ta tabbata yana jin karar bugunta a cikin kirjinta, musamman yanda barin jikinta yake kwance akan barin nasa jikin.
"Mar'yam, Ina sane da komai na nemi aurenki. Ban kuma saka kaina a yin hakan ba sai da na bincika komai akanki na san kuma irin gidan da kika fito gidan girma ne. Kowa ya bada shaida kan mahaifinku da dattakonsa. Don haka nake tsammanin na samu kwatankwacin hakan daga gurinki. Ina son ki gina soyayyata a zuciyarki a matsayina na Dan Malam Barkindo. Ki sakawa ranki duk randa babu wadannan abubuwan ni naki ne haka kema tawace. Kar muyiwa juna ha'inci a cikin zamanmu, idan kika kiyaye hakan in sha Allah zan zame miki garkuwa da ginshiki har karshen rayuwata."
Hawaye ne ya jika mata idanuwanta, ta ja numfashi dai-dai inda kanta ke kwance jikin wuyansa. Har sai da taji alamar ya zuki nashi numfashin da sauri sannan ta bude idanunta. Lokacinne ta ankara da yanayin da suke kishingide jikin juna.
Da Siddiqah ta motsa a cikin rikonsa, Sufyaan yaji ilahirin jikinsa ya tsumu da kusancinta da taushin fatarta da kuma sassanyar kamshin dake fita daga jikinta. Kara shigar da ita yayi cikin jikinsa har sai da yaji ya kure gurin da zai iya sakata a zahirance ba tare da yaji mata rauni ba.
"Baccin ya zo ne?" Ya tambaya a muryar da bai tantance ko tashi bace ko kuwa.
Da sauri Siddiqah ta maida kallonta kan yatsunta da suke rike cikin juna. Ba tare da ya ce mata komai ba ya ja hannunta zuwa dakin da yake gefen nata dakin.
Jinin jikinta bai gama komawa seti ba bare ta samu damar karewa dakin kallo da kyau, ta dai san akwai sanyi dai-dai gwargwado da yake shigowa ta tagar dakin a dalilin ruwan sama da akayi hala a yinin ranar. Don har zuwa wannan lokacin, iskar damina tana kada labulayen dakin.
Babu shirgi da yawa bayan setin gado mai duhun launi sai teburi da kujerar rubutu da karamar na'urar sanyaya ruwa.
A nan dube-dubenta ya tsaya saboda Sufyaan ya umurceta da suyi sallah don su samu su kwanta.
Amma a iyakan sanin Siddiqah, ita dai wannar sallar daga bayanan da ta sha ji daga ajin malam zuwa gun kawaye ba ta bacci ba ce. Sai dai haka ta daure bata sa gudu ba ta bi bayansa sukayi nafila. Bai tsawaita musu addu'o'i ba bayaga na larabci da taji yayi wanda a cikin littafin addu'o'in da Raliya ta bata ta fahimci ita akeyiwa sabuwar matar da aka aura don neman alkhairinta da neman tsari daga sharrinta.
Ita dai tamkar an zare mata laka ta gagara cewa uhm bare uhm-uhm, duk kuwa bin diddiginsa da tambayoyin da yake mata, amsa daddaya take iya bashi har sai da ya shiga nuna mata matsayinta a ransa.
Sufyaan dai duk iya yanda ya so ya kyaleta ta huta daga gajiyar hanyar da ya san ta kwasa a cikin ranaku biyun nan sai da ya faskara, musamman yanda ya bude mata cikinsa kan ababen da suka shafi rayuwarsa da ta shude. Lokuta irin haka kuma shi kansa ya san abubuwan da suke faruwa a tare dashi inda yake rasa karfin mallakar kansa da abunda yake ji a cikin zuciyarsa.
Shekarun da dama amma har kullum hakan ne yake faruwa. Don haka da ya sameta yanda yake so ya nuna mata cewa a gurinta yake samun kamilalliyar natsuwa iya yanda zai iya nunawa ba tare da ya bata tsoro ba. Domin shi kanshi al'amarinsa da Maryama-Siddiqah tsoro yake bashi. Yanda a lokaci kalilan komai nasa ya canza. Musamman idan tana tare dashi akwai wani bangarensa da ya aminta da ita fiye da zatonsa, fiye da yanda yake tunanin zai iya aminta da duk wani wanda ya shigo rayuwarsa a bayan faruwar abun.
Sassauci daya da ya samu, shine na tunanin jirginsu zuwa Legas ba da safe zai tashi ba, don ya san a cikin daren nan mai dimbin albarka, zai yi wuya ya samu hutun da yake bukata a wadace. Duk da kuwa yayi iyaka kokarinsa ganin cewar ya bar Siddiqah ta samu nata hutun.
***
Ba kallon razana tayi wa tazarar dake tsakanin sashi biyun ba a daren jiya. Ta tabbatar da hakan ne a lokacin da suka fito da rana domin tafiyarsu. Zuwa yanzu ta fahimci nan ne sashin Amina.
Duk labaran da ya bata a hanya jiya sai da ya san yanda akayi ya kaucewa batun Amina, sai yau da safe, suna karyawa yace mata "Idan mun isa Lagos can gida zamu kwana kafun lokacin flight dinmu da safe in sha Allah."
"To." Tace yayinda ta ci gaba da cin abincinta a hankali. Wannan yana nufin tana gaf da haduwa da Amina kenan.
A safiyar tunda ta tashi take ta aikin hada kayan da za tayi amfani dasu. Yace ta dauki kaya marassa nauyi sosai sannan wanda zasu isheta kwanaki goma a wadace. Ko da ta gama hada kayan, bata zauna ba shirga wasu kayan nata tayi cikin wardrobe dinta yanda idan sun dawo daga tafiyar bazata sha wahalar fara shirya dakin ba.
Da ya tashi hada nashi kayayyakin, kirarta yayi dakinsa yana mika mata abubuwan da ya zaba tana sakawa a cikin jakarsa.
Ta san yayi haka ne don ta fara kula da irin tsarinsa da abunda yafi so. Hakan ya mata dadi.
Ko da ta fito zuwa kicin da zummar taga ko akwai kayan abinci ta sarrafa zuwa abun karyawa, sai ganin rufaffun kwanuka tayi alamun an girka an ajiye. Kayayyakin da suka kawo jiya kuma duk an shirga su a babban friza da karamr na'urar sanyaya ruwa.
Sai lokacin ta tuna ya ambaci masu masa hidima a gidan. Ko daga wani madafin aka dafa aka kawo? Oho! Bata tambaya ba.
Bayan sun kammala karyawane ya shiga cikin gari ya dawo domin tafiyarsu.
Karfe uku na rana jirginsu ya tashi daga birnin Kano, tunani daya ne ya cika zuciyar Siddiqah. Yaya haduwarta da Amina zata kasance?
***
EHEM... SBS mehn🙊
DAN DAN DAN.
Amarya tana hanya Aminatu sai a shirya💃🏼
Ma'assalam.
Umm Yasmeen💞
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top