BABI NA BIYU

KASHI NA BIYU


A WANI WURI CIKIN NAJERIYA.

DISAMBA 2013-- 2:34 p.m.

"Yallabai kayi hakuri an samu kuskure ne wurin buga lambar kan takardar (typing slip number) amma In sha Allah yanzu nan za a gyara, kafin nan ku dan jira a VIP lounge (dakin hutawan baki na musamman)"

Wani kallon uku saura kwata ya buga masa sannan yace, "Nayi maka kama da wanda nake da lokacin jiranka? Ku mutanenmu haka kuke sam baku san muhimmancin aikin ku ba bare ku iya bi da kwastomas. Ka san kuwa waye kuke batawa lokaci? Kaima ka san SBS yafi karfin ya tsaya bin flights dinku, idan banda akasin da aka samu..."

"Ayi hakuri yallabai..." Amma kafin mutumin nan mai farar jumfa da koren igiyar da ta rataye takardar shaidar cewa shi ma'aikacin filin jirgin ne ya ida bada hakuri kakkauran mutumin nan ya ci gaba da surfa masa masifa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.

Daga bayansu sukaji wata murya mai cikakkiyar zurfi da kauri ya fidda kalami a tausashe, "Bilyaamin, yaya akayi ne?" Mutumin ya fada hade da zare tabarau din idanunsa masu dan duhu, wanda da gani ka san don su rage karfin rana ne aka sanya su daga can saman siraran hannunsu an rubuta CD daga collection din Dior homme.

Da sauri wanda aka ambata da sunan Bilya ya fara cicciro kwalakwalan idanunsa yana fadin "Yallabai, mutanen nan mana wai a kasar nan ba wanda zai yi aikinsa da kyau? Common ticket ba za ayi printing details ya fito daidai ba sai an samu kuskure?"

Murmushi yayi yana dubanshi ta kasan lumsashen gashin idanunsa hade da soke hannunsa guda a aljihunsa na gefen wandonsa, kallo daya yayi wa mutumin ya fahimci sunansa "Banda abunka Bilyaamin ai da yaci ya sake buga sabo, Alhaji Labaran, kayi hakuri je ka gyara aikinka." Mamaki ne tsantsa ya kama wannan ma'aikacin.

Cikin dariya gutsirarra irinta mai amsa laifinsa, ma'aikacin yayi godiya sannan ya wuce domin yin abunda aka saka shi, cikin mamakin yanda wannan gawurtaccen mutumin ya san sunanshi ya manta fedes da ID card a gaban rigarsa, tsabar rikicewa;

Duk da cewa yaransa ne sukayi wannan kuskuren amma ya zama dolensa ya gyara da hannunsa saboda ko bai fada ba yasan SBS VIP ne don haka nan da nan ya koma inda suke zaune a dakin hutu ya basu takardar, zuwa lokacin daukacin jama'ar da zasuyi boarding jirgin IHANAMS AIR Boeing 737-36N sun gama shiga saura su.

Tafe suke har cikin jirgin Bilyaamin na rike masa da akwatin na'ura mai kwalwarsa, banda wannan bayi da wasu kaya, tamkar ba tafiya ya taso ba, ba kuma tafiya ya nufa ba. QS SBS kenan.

Tunda suka shiga bangaren business class suka samu zama Bilyaaminu ya ci gaba da zayyanawa mai gidan nasa ayyukan dake gabansu. Wanda tsaurinsu ya karu a sanadiyyar matsalar da jirgin mallakar kamfaninsu ta samu, hakan ya haddasa suka kara kwana guda a garin ba tare da sun shiryawa faruwar hakan ba.

Shiru yayi ya kura masa idanu yatsansa daya na kan labbansa masu duhu da taushi, yayinda sauran tafin hannun nasa ya tallafo fuskarshi, cikin alamar saurare da dukkan hankalinsa, amma duk da wannan da alama ba ya cikin nishadin sauraren abunda daya daga cikin Manajojinsa Bilyaaminu ya zo masa dashi. Can ya nisa yace "Bilyaamin, ka saurara zuwa anjima duka zamuyi wannan bayanin. Yanzu ina bukatar nazari kan wasu abubuwan."

Baki a bude cikin tsantsan mamaki Bilya yace "Yallabai, ba wai shisshigi ba amma lafiya kuwa? Ayyukan nan fa sun haura mana kai sai mun sa raarar lokaci domin mu kamo abunda mukayi asara daga wannan lokacin, musamman batun sabbin softwares da za a fitar cikin makon nan. Zaid ya kirani da wasu karin bayanai akansu."

"Duk mu bar wannan ranar Alhamis ina da abunda ya taso min a cikin garin Damaturu saboda haka bazan yi komai ba a ranar can zan tafi, in sha Allah."

Agogonsa ya kalla sannan yace "Yallabai yau Talata, tuni lokaci ya tafi." Kallo daya SBS ya masa ya gyara murya hade da hadiye busasshen yawu ya kada kai. "Ba damuwa to zan cire Alhamis idan ka gama sai mu tafi Gombe ta can, Juma'a sai mu wuce Lagos idan Allah Ya kaimu batun kayan Alhaji Farouk."

"Banda Juma'a." Sufyaan ya fada tamkar hankalinsa ba ya cikin jirgin tare da gangan jikinsa.

"To... amma komai zai kwabe..."

Sauke hannunsa yayi ya makale shi cikin danuwansa hade da nisawa yayi magana tamkar ba shi bane yanzu hankalinsa yayi nisa, "Me kake yi komai zai kwabe? Ka tabbatar ba abunda ya canza. In fact, cancel all my meetings (a takaice ka soke duk wata ganawata) daga nan zuwa sati biyu, na damka maka komai zuwa lokacin da zan kammala abun da na saka a gaba."

Hannu ya sa zai yi bayani har ya bude baki kuma sai ya rasa abun fadi. Don haka ya rufe, ya yi dai shiru ne saboda ya rasa gane wani irin abu ne da muhimmancinsa har ya kai maigidansa zai shure duk abun da yake gabansa wanda zai janyo musu asara ta kudi makudai domin ya cimma wannan.

Ganin ya bude na'urarsa yana wani abun yasa Bilyaaminu ya fahimci ba a gayyatarsa don haka shima ya shiga nashi taitayin ya nemi abun debe lokaci zuwa sanda zasu sauka a filin jirgin Nnamdi Azikwe international Airport dake birnin tarayya, Abuja.

***

Da tunanin Hajiyarsa ya shiga cikin gidan. Yau ma dai ya sake gwada sa'arsa ko zata amince ta dan huta idan ya kawo ta asibiti. Daga jin ya ambaci zata huta idan ta zo, Hajiya Amina ta kafe fafur ta fasa ganin likitan, zata je asibitin cikin Girei.

Wannan gwagwarmayar ba yau aka fara ba. Yayi iya yinsa daga shi har 'yan uwansa abun yaci tura. Har takai ya sako nata 'yan uwan don dai ta amince ya kaita gidansa amma duk taki wayon. Don haka wannan yasa kodayaushe yake yawan zuwa dubota da zaran ya samu sukuni.

Su takwas ne a cikinta; kasancewarsa babba yasa duk wani taimako da ta san zata bashi na tallafi kama daga kudin hannunta ko shawarwari da kuma addu'o'inta to ta bashi wannan gudumawar domin ya taso ya tallafawa na bayansa, kuma Alhamdulillah. Likkafa ta ci gaba domin babu gatan da bai samu ba haka babu wanda baya nuna mata.

Kwarai ta ga jarabawa iri-iri bayan rasuwar mahaifinsu, Malam Barkindo Sajoh, wannan yasa dukka 'ya'yanta babu wanda ta mashi sake tun tasowarsu, a tsaurare suka santa haka bata wasa mace ce mai kamar maza, wanda bai sani ba bazai taba dauka cewa hannun mace suka taso ba, duk da kasancewar akwai sa idanun baffaninsu daidaiku.

A dakin Hajiyarsu Kafin Sufyaan ta haifi wani yaron da satinsa biyu a duniya ya koma sannan Allah ya bata Sufyaan bayan shi akwai Yaya Gimbiya Fatima, wacce kowa Yaya Gimbiya yake kiranta saboda ta amsa sunan yar babansu, Sai Jamila sannan Sagir, Asma'u, Maryam, Muhammad Sani sai kuma autanta Ruqayya.

Yana da kanne biyu a wurin matar babansu Zainab da Maimunatu. Su su goma ne a gidansu, kuma kwarai suna da hadin kai domin duk bayan wata uku zuwa hudu sukanyi taro domin tunkarar matsalolinsu da magance su ko ta hanyar tallafi na kudi ko na shawarwari.

Kwarai jinin Sufyaan ya hadu da na kanwarsa Asma'u domin ko bata fada ba kowa ya san itace 'yar gaban goshinsa. Shi kuwa yana duba yanayin ta ne yanda Allah ya sa take da son mutane da kuma son yiwa nata sai dai Allah bai azurta mijinta da wadata ba kaman na sauran 'yan uwanta, duk da yana musu alkhairai masu dimbin yawa idan ya tashi nata yana fin na kowa.

Hatta sana'ar da mijinta yakeyi a garin Bauchi shi ya tusa jarin ya bashi, dai-dai gwargwado yana samun alkhairi a kai. Kuma kaf cikin kannensa gidanta ne kadai idan ya je yake tube takalma ya shiga har dakinta ya zauna suyi hira, yaci abinci sannan ya kama hanya. Sauran sai dai mazansu suce yanzu Hamma yazo ya gaishe ku ya bar kuma sako, sai sunci sa'a zai sa a kirasu su gaisa dashi.

Sufyaan yana da tsantsan ra'ayi da tsayuwa kan batu guda daya haka nan akan gaskiyarsa zai iya fada da koma waye, baya son ha'inci baya kuma yarda ya ha'inci wani, yayi amanna da komai zai samu a duniya zai iya samunshi ta hanyar kwarai ba sai ya zambaci wani ba. Wannan dabi'a tasa yasa yake da wuri na musamman a zuciyar mahaifiyarsu kuma wannan dalilin yasa ya ke da tarin makiya a wani bangaren.

Dabi'arsa ta tsayuwa kan gaskiya daya da batu daya da ya furta ne yake saka shi tuhumar kansa a lokuta kamar yanzu, wanda ya hakikance ya fadi iya abun da ke ransa, sai dai sam tunda yake a duniya bai yi tsammanin ya taba yin hukuncin da yaji ya takura kansa irin wannan ba, abu daya yake fadawa kanshi ya samu sukuni wato "Ita gaskiya daci gareta." Don haka dole ya daure ya dau matakin da ya fi cancanta.

Sai dai yana shiga cikin gidansa a birnin tarayya ya gagara samun sukuni. Wannan dalilin yasa ya san zama bai ganshi ba. A take ya kira direbansa.

"Malam Yakubu, ka kwana da shiri, da safe zamu dauki hanyar Gombe, in sha Allah."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya danna maballin jikin remot domin dumama dakinsa. Bayan yayi sallah ne ya nisa tare da samun sassauci, ko ba komai gobe war haka idan Allah Ya so yana tare da yaransa. 

***

Gombe, NAJERIYA

1990

Suna zaune a falon Ambasada Usman gaba dayansu ana hira wani kaset din Indiya suke kallo, duk da shi hankalinsa yana kan littafinsa. Su Siddiqah ke ta faman kankare masa dandurof, don dama wannan kam aikinsu ne, har juyi-juyi yaran sukeyi ya basu kanshi ayi ta jagwalgwalawa, matan ma duka suna zaune ana hira, jefi-jefi.

Shigowar yayansu Salman ne ya sa Siddiqah ta zabura, domin kuwa dazu yake shaida mata zasu zo da abokinsa. Tace masa bata so don ta zaci tsokanarta yakeyi. Kaf gidan tsiya yaran suke mata wai mai tsoron samari. Tunda Baba ya ritsata bata sake tsayawa da kowa ba, duk da kuwa shi kanshi Abdullan ba wai ya sarara mata bane, lokaci zuwa lokaci yakan aiko mata gaisuwa da wasiku.

To ga Yaya Salman kuma da tashi matsalar, Mukhtari wai sunan abokin nasa, yanzun ma da ta ganshi kai tsaye yace "Siddiqah fito ki gani."

A darare ta kalleshi ta dubi bangaren da su Baba suke zaune, ido ya mata sannan ta tashi sumu-sumu ta dauko mayafinta tabi bayanshi "Yaya Salman, Allah idan Baba ya ritsani kai zan nuna."

"Naji, bazaki dade ba kawai gaisawa zakuyi zai koma makaranta."

Abun da ya daure mata kai shine tana fitowa taga tamkar ta san Mukhtarin nan a wani wuri, sai can abun ya fado mata, ashe tafe da Abdullah suka taba zuwa wurinta. Har ma Abdullan ya nuna shi a matsayin dan Baffansa.

Kwarai ya bata mamaki amma bata fadawa Yaya Salman ba. Sai da suka gaisa ne yace "Yaya hutu dai?"

A tsume ta amsa masa, sannan tun lokacin duk abun da ya tambaye ta sai dai tace masa uhm ko uhm-uhm. Daga karshe ko gajiya yayi oho masa ji tayi yace "Naga kamar kin gaji, bari na barki haka."

Ba wani bata lokaci ita kuwa ta juya tayi ciki don daman kamar an daura ta kan 'kaya.

Ba a dade ba kuwa ya sake zuwa wannan karon sun gaisa dai amma bata cewa komai, zuwan shi na uku ne yace mata "Ni ko ina neman shawara."

Kanta na kasa tace masa "Ni kuma na baka shawara?"

Murmushi yayi yace "Kwarai kuwa, haka nan naji zaki iya bani mai fa'ida. Kinga yanzu na kammala diploma na da poly Bauchi, ina tunanin na fara aiki ne ko kuwa na nemi gurbin karatu a jami'a nayi digiri na?"

Siddiqah taji dadin tambayar da ya mata ko ba komai abu idan dai ya shafi ilimi nan tafi kauri don haka a karo na farko da bata ji haushinsa ba tace "Eh to gaskiya ni a ganina ba gwamma ka karo karatunka ba, kaga idan ka soma aiki sai kayi 'yar gaba daya kawai. Amma yanzu idan ka fara karban albashi kaji dadin jikinka karatun ma sai ya maka wahala."

Shi kanshi Mukhtarin yaji dadin shawararta kwarai. Don haka yace hakan za a yi.

Bata bari ya sauke numfashi ba tace "Kuma, ina so na fada maka gaskiya tsakani da Allah ni bazan iya auren ka ba, saboda ko dan uwanka bai fara zuwa wurina ba ni ba yanzu zanyi aure ba sannan kuma ina ganin girmanka don haka bazan tsaya bata maka lokaci ba."

Shiru yayi yana nazarin kalamanta. "Ni a tunanina ai kowa ya iya ruwa ya fishhe shi ko ba haka ba?"

Lallai ma mutumin nan ya faye son kai, wanda zai iya cin amanar dan uwansa kam bata yi tsamman zai iya rike matarsa da aminci ba don haka bata ce masa komai ba, tun da ya tafi wannan ranar kuwa ko an ce mata ana mata magana bata saurarensa.

Yanzu shirye-shiryen komawa makaranta suke ta yi, kuma ko shi Abdullan ma da ya dawo bata bashi fuska ba. Don haka su Hajiya Salmah ne masu manema kala-kala. Sai dai idan bata fita ba sai tayi sabo.

Ba abunda yake damun Siddiqah irin tunanin komawa makaranta saboda zangon da ya gabata an dan taba rikici a makarantar tasu.

Suna zaman-zaman su a hostel wani yammaci, karatu ma takeyi ta baza littafai kan gado tana kwasar hadda bayan ta kammala kwafe note dinta, domin ita ce gwanar yiwa 'yan aji note kan allo daga baya ta zo tayi nata.

Kamar da wasa suka fara jiyo ihu da hargowa, ko kan su fito farfajiyar ma sai gani sukayi kura na tashi ko ina, nan da nan suma suka fito. Gudu kawai akeyi duk da basu san me ya janyo wannan rikita-rikatar ba suma suka bi sahu, kai tsaye hostel din su Fatima suka nufa, don gwamma a gudu tare a tsira tare.

Shigarsu dakinsu suka samu wata kawar Fatiman su wacce kullum basu rabuwa Lubabatu, ita kam har da suma don tana da ciwon asma. Hankalinsu kwarai ya tashi, a nan ne suka samu labarin yanda rikicin ya taso.

Abun dai ya soma kaman da wasa tsakanin yara musulmai da kiristoci, sai ga abu ya girmama har sai da aka nemo 'yan sanda, sai wurga tiya gas ake tayi ko ta ina. Garin gudu kuwa wasu sun fadi wasu an tattake su.

Aka kwashe marassa lafiyan da wadanda suka ji rauni sai asibiti.

Nan da nan gari ya dauka, wanda iyayensu suke kusa suka zo suka tafi da yaransu, sai ga su Siddiqah fuska duk kozai-kozai an sha kuka don tashin hankali, da kafa suka bar makaranta har zuwa gidan Raliya.

Kwana biyu tayi a kwance da wata muguwar zazzabi don tsabaragen tsoro da razana, don ko yanzu ta tuno ranar sai ta girgiza. Wannan yasa take ta tunanin komawa. Ba daman tace da Baba ya canza musu makaranta ba zai amince ba, ko da yake yanzu kam suna daf da gamawa ganin saura abun da bai wuci shekaru biyu ba.

***

Wannan komawar tasu kuka takeyi wiwi kamar sabon shiga, har ta sa Hajja Nenne goge kwalla, ita kam makarantar dole ne ma? Ta fada a ranta amma ta san ma gwamma kar ta furta domin kuwa ta san kwarai yanda mai gidan nasu ya dauki neman ilimi da muhimmanci.

Kuma bazata ce ta ga laifinsa ba, tunda idan dai kana son samun daukaka da ci gaba to abu na farko shine ka nemi ilimi.

Ko ita nan aka ce ta samu ilimin zata nema, don aurenta da Ambasada ne har yayi sanadin ta dage wurin koyan abubuwa duk da kan suyi aure tana zuwa makarantar yaki da jahilci a zauren Malam Bunu dake unguwarsu.

Don har wasika ta iya rubutawa ta kuma karanta. Wannan yasa taki ta karaya da taga hawayen Maryama-Siddiqah, aka hada musu duk kayan bukatunsu suka koma makaranta.

A hankali kuma abunka da yau da gobe, suka kara sabawa komai ya ci gaba da tafiya kamar da. Salmah dai itace 'yar ribibi, don har yanzu Siddiqah ba wai tana sakewa bane cikin mutane, idan kana son jin surutunta to sai a daki kawai zaka jiyo ta.

Wataran 'yan dakin su zagayesu wai su koya musu larabci. Kasancewar basu watsar ba tun dawowar su Saudiyya.

Har wannan lokacin Siddiqah bata faye tarukucen kawaye ba, kawarta daya da ta rika da muhimmanci tun zuwanta makarantar dai Laila ce kuma har yanzun da ita take yi. Da yake itama mai son karatunce sai tafiyarsu tazo daidai da Siddiqah.

Haka rayuwa ta ci gaba da gudana musu har lokacin da zasu bar aji biyar zuwa shida a makarantar.

**

Legas, NAJERIYA

JANAIRU 1994

Cikin falon shiru tamkar babu kowa, sai karar na'urar sanyaya daki da ke ta faman fita, sai dai ko kadan wannan karar bata ratsa kunnen sa ba bare kuma ya yi tasiri a kwakwalwarsa, domin ransa fal ne cike da tunani.

A take a lokacin kuwa ya yanke shawarar abunda zai yi da rayuwarsa, ba wai da bayi da abun da yake yi da ita bane, a'a yanzu ne ya sama mata hanyar da ta daidaitu da kwanciyar hankalinsa.

Kai tsaye dakinta ya shiga, amma bai ji mamakin ganinta da yayi ba cikin kyakkyawar shiga na shirin bacci, komai a dakin kamshi yakeyi, littafi ne a hannunta kamar kullum.

Wannan zai bayyana dalilin rashin isarta falon ta taya shi hira kamar yanda ta saba. Murmushi yayi, sannan ya karasa cikin dakin inda kafafunsa suka luntsume cikin lallausar kilishin da ke shimfide a kasa.

"Amina, yau littafi ya shiga tsakaninki da SUFYAAN." Itama murmushin takeyi daga kwance, sannan tace "Saura kadan ne yasa nayi tunanin na karasa sai na sameka. Amma tunda ka shigo shikenan."

Hannu ya sa ya ajiye littafin a gefe sannan ya zauna a gefenta. Bai san ya shiga wani tunanin ba sai da tace "Lafiya dai Baban Hameeda?"

Numfashi ya ja sannan ya sauke, "Lafiya kalau, wasu al'amura ne kawai."

Nan da nan ta tashi zaune tana kallonsa cikin damuwa da yanayin da ta ganshi a ciki "Ya wuce wannan," ta fada tana neman idanunsa da yake ta kokarin kawar dasu "Yaa Allah, lokaci yayi ko?"

Kai ya gyada mata hade da kokarin riko hannunta cikin nashi. Ko da wasa bai taba tsammanin abun da ya biyo baya ba, amma tana aikatawa ta matsa nesa dashi, wani lafiyayyiyar mari ta shimfida masa a fuska.

"Amina!" Ya fada cikin kakkaurar murya.

"Ka tafi kawai Sufyaan, bazan iya saka a idanu na ba."

Yana ganin yanda kamanninta suka sauya lokaci guda duk ta birkice sai yaji tausayinta ya kamashi, "Amina, ki tsaya na miki bayanin komai a tsanake, ina so fa ki san babu abun da zai canza. Kamar yanda na daukar miki alkawarin duk lokacin da hakan ya taso bazan boye miki ba, hakan kema kin san da niyyata tun ba yau ba, don haka abu daya da zakiyi shine ki natsu ki kwantar da hankalinki. Zan baki lokaci kiyi tunani da sassanyar zuciya."

Mikewa yayi zai bar dakin kwarai ya so ya zauna ya lallasheta saboda ya san tsakaninsu, amma kuma bazai iya ganinta cikin wannan halin ba.

Amina kam ta daskare wuri guda tana nanata abun da ya fada cikin kwakwalwarta. "Ka manta komai, kana magana tamkar ba kai ba! Ashe dama za ka iya min haka da gaske? Har ka ga wacce zata iya fina ka wulakantani dominta?"

***

Amina kyakkyawar mace ce, wacce sam bazaka ga tsufanta da wuri ba, fara ce sol mai matsakaicin tsawo, ta gogu kwarai da ilimin boko da na addini dai-dai gwargwado, sannan ga wayewan da ya shigeta a dalilin yawace-yawacen kasashe da sukeyi da mijinta.

Auren soyayya sukayi na kuruciya da Sufyaan kuma kwarai ta san yanda yake ji da ita, amma tun shekarar su ta farko da aure ya taba fada mata shi kwarai yana sonta, amma idan lokaci ya zo to bazai boye mata ba zai kara aure don yana sha'awar ajiye mace fiye da daya.

Kuma iya zamanta dashi ta fahimci dalilinsa, sai dai dai-dai da rana guda bata taba yarda cewa da gasken zai iya mata kishiya ba, domin yanda Sufyaan ya dauko duniya ya sa mata a kasan kafafunta.

Yaransu hudu dashi a shekarunsu goma da aure. Amal, Hameeda, Sultaana da Firdausi. Yara gwanin sha'awa kyawawa son kowa... ta haifa masa sannan yau ya dubeta da wannan mummunar batu da ta fi mutuwa daci?

Ranar Amina bata runtsa ba, da sassafe ta hada jakarta da ta yara. Sufyaan kuwa ya gama shirinsa yana shirin ya isa ya ga yanda ta kwana ne, suka hadu a falo inda take janye da akwati a hannu daya dayan hannunta kuma tana dauke da karamar 'yarsu Firdausi.

Cikin kidima Sufyaan ya dubeta "Amina, lafiya meye hakan kuma?"

Dariyar takaici tayi sannan tace "Lafiya kake tambayata? For God's sake zaka kawo min wata tayi invading rayuwarmu har sai ka tambayeni meye hakan yake nufi? Of course, gidanmu zan tafi." Ta fada cikin daga murya fuskarta tayi jawur kaman gautar da ta sha rana.

Da sauri Sufyaan ya isa gareta, ya sunkumi akwatin ya shigar dakinta ya janyo kofa, ya kama hannun yaran biyu masu wayo ya yi waje dasu babbar na biye dashi a baya. Bai tsaya ko ina ba sai bangaren mai aikinsu Umma Balki.

Tana hucin numfashi idanunta jazur ya dawo ya sameta a falon. Bai ce mata komai ba baicin rikota da yayi ya ja zuwa kujera ya zaunar. Kukan da takeyi ne ya hanata fita daga rikonsa. Amma ji takeyi kamar ta soke shi saboda tsabaragen haushinsa da takeji.

"Saurareni Aminatu, don Allah na rokeki ki kwantar da hankalinki, maganar nan ba yau muka fara ta ba fa. Ina son ki bani dukkan goyon bayanki. Nan ne kawai zanyi abun nan cikin kwanciyar hankali ba tare da ganin na cutar da ke ba, duk da dai babu cutarwan a ciki. Amma don Allah ki maida jakarki."

"Wacece yarinyar? Na santa? A nan garin kuka hadu?" Tambayoyin da ta jero masa kenan cikin tashin hankali.

Sufyaan ya shafo saman kanshi sannan yace "A'a baki santa ba, in fact, nima ban santa ba don bamu hadu ba tukun."

Wata irin dariya tayi cikin kuka-kuka ta-ce "Sufyaan, yanzu ka zabi macen da baka hadu da ita ba a kan zaman lafiyarmu da kai?"

Hannu yasa ya tallafo habarsa sannan ya furzar da numfashi, ya riko hannyenta cikin nasa. "Ko kadan ba haka bane, na fada miki ne saboda na yarda cewa zaki bani dukkan goyon bayan da nake bukata, saboda mu fuskanci wannan tare. A tunanina fada miki kafun na fara neman zai sa ki samu mindset din hakan ki kuma tayani addu'ar samo miki abokiyar zama ta gari."

Hawaye na bin fuskarta tace "Ban san son da kake min karya bane sai yau, idan banda haka yaya za ayi ka fuskanceni da maganar nan kayi tunanin hankalina bazai tashi ba? Ina sonka da yawa, Sufyaan, bazan iya jurewa ba. Ka san ma yanda kake a raina kuwa?" Fashewa tayi da kukan da ya soki Sufyaan a zuciyarsa.

"Do it please. For me?" Ya fada cikin kaskantar da kai. Yana ga rabon da yayi wa mutum magiya irin yanda yakeyiwa Amina yanzu ya manta. To amma shi Sufyaan Barkindo Sajoh ne ba kasafai ake sashi a wurin da zaiyi wa mutum magiya ba, sai dai ran gimbiya ya motsa dole yayi rarrashi.

"Bazaka fasa ba kenan?"

Shiru yayi yana kallonta wannan ya bata amsar tambayarta don haka ta ture hannayensa daga cinyarta ta daga Firdausi ta wuce ciki.

Tun daga ranar ya kara shiga tsaka mai wuya, ga harkokinsa da suke bukatar natsuwa gashi ya rasa natsuwarsa gaba daya.

Shi dai bai san matar da zai aura ba, amma ya ji da ma ya bari sai ya samu matar tukun kan ya tada wannan rikincin a gidansa, a tunaninsa Amina zata fahimci komai ta amince, domin kuwa lokaci na farko da ya dago mata zancen sam bata daukeshi da zafi ba.

Bazai manta ba har ce masa tayi zata rinka rakashi zance, ashe abun ba haka bane.

Wasa-wasa sai da ya dangana da yiwa mahaifin Amina magana domin ya sa baki a lamarinta, don ta daina shiga sabgar yaran ma gabaki daya, wai ba dasu ta zo gidan ba idan ya auro matar so sai ta kula masa da yaranma.

Gabaki daya ta caza masa kai, Alhaji Mansur ya nemeta a kan waya kasancewar shi yana Kano, a sannu ya kara rarrashinta ya kara mata tuni da cewa "Amina, mutum mai son kai baya taba ganin daidai a rayuwarsa fa aje-aje.

"Tunda ya riga ya gwada miki bukatarsa, ki bi shi a sannu sai ki ga kin mori zama dashi, ai maganin zama da mutum shine ka san yaya mutumin nan yake, akwai wacce zata zo ta fiki sanin waye mijinki? Sannan kar ki manta fa kema mahaifiyarki a bayan wata tazo.

"Shin da ana kin karin aure da ke an haife ki?" Bai jira amsarta ba kasancewar tana kuka "Kinga ai ba zancen ka 'ki wa dan uwanka abun da kai ka so wa kanka. Don haka ki jure kiyi hakuri ki ci gaba da bin mijinki, don kullum gidanki yana ban sha'awa yanda baku samun sabani, amma kar ki soma yanzu. Allah yayi muku albarka."

Ita ta san dama sai da ya hada baki da Abbanta tukunna yasa ya kirata idan banda haka yaya ma za ayi Abba yana ji yana gani za a cuceta ya dau waya ya kirata yana mata wa'azi?

Sufyaan fa da yaga ba sarki sai Allah, gashi da shi da yara an barsu sai azabtuwa sukeyi nan ne fa ya gwada mata idan tayi gaba abun da zata rasa. Ya nuna mata shima namijin duniya ne, kuma inda ya kwareta ya san yanda take mutuwar son shi.

Ba shiri kuwa ta sassauto ta bi hanya. Tun lokacin kuwa bai sake dago zancen ba, kai bai ma fara neman matar ba har watanni biyu suka shude.

***

Heheheehe... 

Ga dai SBS ya shigo gari. (2013) Ga can Siddiqah kuma ta arce. 🙆🏽🔥

Ga nan kuma SBS yana neman matar aure (1994) Ga nan Siddiqah kuma tana gudun maza. 

Mu tona? 🙊

Ga dai labari ya fara tahowa. Da fatan ana kula da ranaku, kun san yanda kwanakin wata suke da muhimmanci a labaran da nake zuwa muku dasu. A ci gaba da lura. 

Read between the lines and join every matching date. Na barku da aiki laaafiya. 

Sai gani na gaba...

Ma'assalam

Umm Yasmeen.💞

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top