BABI NA BIYAR
Gombe, NAJERIYA.
DISAMBA, 1993.
"Adda Siddiqah kije falon Baba ana nemanki."
A razane Siddiqah ta juya bakin kofar dakinsu, jin muryar kanwarta Ameerah lokacin data bada sakon.
"Ni kuma?"
Umma Gaggi ce ta daga labulen dakinsu tace "Sai kije kiji waye ne ai."
Cikin sanda da taraddadi Siddiqah ta mike domin taje amsa wayar. Sai dai fitowarta ne yasa ta fahimci me ya haddasa Umma Gaggi bata ce ta daga kan wayar da ke falonsu na cikin gida ba ta bari Ameerah ta kirata cikin kebanta.
Tunda ake a gidan babu namijin da ya taba yin waya dominta domin bata taba bada lambar gidansu ba. Sai gashi yau an kirata.
"Ameerah waye akan layi?"
"Kan layi? Bako kike dashi fa. Ya turo daga kofar gida shine Yaya Hashim yace a bude masa falon Baba ya shigo."
Nan take Siddiqah taji cikinta ya zagwanye kamar kafafunta zasu narke. Yau abun ya girmama, bata san wani wanda zai iya samun kwarin gwiwar zuwa har cikin gidansu don ya ganta ba tunda dai bata bada damar hakan ba sai... Turus tayi ta tsaya, haka tunaninta ya tsaya cak!
Lokacin da ta tuno zancenta da Sufyaan a makaranta kusan watanni biyu da suka shige. Tabbas ya shaida mata zai nemi izini gurin Baba domin ya zo ya ganta.
Kardai shine?
Dafe kirji tayi ta shuri silifas dinta, ko tsayawa batayi ta kimtsa kanta ba, mayafinma na kan igiya ta sura domin ta ganewa idanunta ikon Allah.
Tana bude kofar ta shiga, sallamar ma sa'a akayi tayi shi saboda sabo da yi. Aiko Zaune a cikin daya daga cikin kujerun falon Baba, Sufyaan Barkindo Sajoh ne cikin manyan kaya na wani yadi marar nauyi farare tas! Hade da farar hula. Falon ya cike kaf da sassanyar daddadan kamshin da bata taba ji ba.
Bata san me ya shige mata kai ba kawai ita dai ta samu kanta da togewa a bakin kofa ta kura masa idanu kafun ta sura ta juya a dari ta saka gudu ta bar falon bata tsaya ko ina ba sai dakinsu ta maido kofa ta rufe, harda saka makulli. Kirjinta sai balli-balli yake mata.
Ina! Sam bata shirya ganinsa ba yanzu. Me zata ce masa? Wai dama da gasken yake yi son tan yakeyi kuma zaizo gidansu?
Tabdi, ai sai dai ya gaji da zama ya tafi ita kam ina ita ina wannan mutumin? Ta san dai da iya tata wayewar sannan tana alfahari da cewan zata iya shiga ko ina ba tare da taji kunya ba wajen iya magana da turanci, hausa harma larabci mai dan fasali amma iyaka yanda ta ji labarin Sufyaan Barkindo Sajoh ai kwata-kwata hanyarsu bata hadu ba. Hanyar jirgi daban da ta mota.
Mutum idan ya daura maka idanunsa sai numfashinka ya sarke ina ga batun zaman tare na dindindin. Zata kar kanta da kanta ma kenan.
Tana ji ana ta kwatsamniya a cikin gida, amma ganin har minti ashirin sun shude ba wanda yazo cigiyarta a daki ya shaida mata cewa bai fadawa kowa cewa ta gudu ba.
Wata ajiyar zuciya ta kawo ta sauke. Wata kunyace ta lullubeta, saboda a hakikanin gaskiya bata san yaushe ta arce ba.
Duk da ta ji kunyar amma gwamma da hakan ya faru, shima dai ya fahimta hankalinta bai kai aure ba tukunna. Tana 'yar yarinya kankanuwa da ita. Bare ma Baba ya fada shi a nashi ra'ayin yaransa mata su kai shekaru goma sha takwas kafun ya musu aure yanda aka yiwa su Adda Kulsum saboda a cewarsa ko ba komai yarinya ta kara sanin ciwon kanta.
Tunda ko ta taba masa halin ai bazai yarda ya auri yarinyar da har yanzu bata wuce gudu ba a cikin gidansu.
Sai da taji an fara kirar sallar magariba kuma su Sadiya suna gaf da shigowa daga Islamiyya yasa ta bude dakin a hankali ta leko farfajiyar dake tsakiyar sashin dakunan su, nan taga kowa na hidimarsa. Sai lokacin ta kawo ajiyar zuciya ta sauke.
***
Potiskum, NAJERIYA.
DISAMBA, 1993.
Hankalinta yayi nisa wajen zanen da takeyi na tasweerar da ta makale a idanunta taki fita tunda ta ga wurin a kan hanyarsu ta dawowa Potiskum daga Gombe inda suke shirin komawa zango na biyun karshe, bataji lokacin da Raliya ta zauna a gefenta ba. Sai muryarta taji.
"Ma sha Allah wannan zane yayi kyau tamkar mai hankali ce tayi shi." Lokacin ne Siddiqah ta ciro kai ta dubeta.
"Adda Raliya mai hankali kuma?"
"Iyi mana. Kinga yanda yayi tsari kuwa?"
"To ni din bani da hankalin ne Adda Raliya?"
Daga kafadunta tayi na nuna alamar rashin sani. "To wa ya san miki ne kam? Tunda haka wasu dabi'un naki suke nunawa. Yanzu ashe don tsabaragen rashin hankali, Sufyaan ya niki gari ya taso daga Legas har Gombe domin ganinki sai ki kama ki ruga da gudu don kin ganshi? Wannan wani irin rashin hankali ne? Wallahi na zaci kin bar yayin wannan kauyancin. Naso ace Baba bai fita ba a lokacin yasa ki fita a dole muga ta tsiyar. Wani irin abu ne hakan kuma kika koyo? Sam bai dace da ke ba."
Siddiqah ta turo bakinta gaba sannan ta ajiye fensir din ta a gefen daya wanda yafi duhun wanda yake ajiye a kan teburin zanenta.
"Adda Raliya ba haka bane fa. Wallahi ni mutumin ne kawai..."
"Mutumin yayi me? Ji wani zance, shi din daga jeji ya fito ne ko cinyeki zaiyi da bazaki tsaya ku gaisa a mutumce ba ki saurare shi zaki wani falfala da gudu?"
Da sauri Siddiqah ta kalli bangaren da 'yar uwarta ke zaune cikin ware idanu. "Yaya akayi kika sani?"
Girar Raliya suka tattare guri guda cikin rashin fahimtar kanwarta tan.
"Yaya akayi kika san cewa hakan ne? Cewa yayi 'Sajoh zai cinyeki ne'?"
"Lafiyarki kuwa yarinyar nan?" Raliya ta dubeta da kallo na duhun kai cikin kiftawar idanu. Sai da Siddiqah ta lumshe idanu ta girgiza kai.
"Adda Raliya mafarki nayi yana ce min "Sajoh zai cinyeki ne"?"
"To ba dole kina irin wadannan mafarkan ba, kina ganin mutane kina gudu kamar kinga dodonni."
"Baki gane ba Adda. Nayi mafarkin fa sati biyu kafun haduwarmu. Ban taba ganinsa ko jin muryarsa ba, bare na san yanda fasalinsa yake. Nayi mafarkinsa sak. Ba dole nayi ta gudu ba idan na ganshi."
Raliya ta kai hannu ta tallafo goshinta. "Amma Allah Ya yaye miki wannan shiriritar. Ni Sufyaan din ma nafi tausayi indai a haka yake son ya kwashi shirmenki. To ya wuci kinji muna hirarsa ne da Baban Haneefa abun ya tsaya miki a rai?"
"To wa ya fada min yanda muryarsa take indai hakane?"
"Watakila kin taba daukar wayarsa da ya kira gidan nan mana."
"Fasalinsa fa yaya akayi na san tsawonsa, da yanda idanunsa suke da tsarin gashin fuskarsa?"
"Ke ni bana son shiririta. Na dai fada miki ki bar halin kauyanci. Kuma ina son na fada miki, Ya kira gidannan ya ce a rokeki a kuma fada miki zai sake zuwa, yana hanya yau don haka kar ki razana ki gudu idan kin ganshi."
Ware idanu sosai Siddiqah tayi kamar zasu fado. "Yau-yau dinnan?"
"Eh."
"To ai ban shirya ba."
"Hakan yasa zaki ajiye fensir ki taso muje ki shirya masa abun tarba. Kuma da Haneefa zan hadaki ta rakaki wannan karon gudun kar a taba dan hali."
"Bani da abunda zan saka ni kam da ya yi zamansa. Makaranta fa zan koma. Idan Baba yaji zai mana fada Adda daga ni har ke."
"Iyye! Yanzun ba sutura bane a jikinki? Ke nifa bana son shashanci, wallahi sai na kira Hajja na fada mata abunda kikeyi. Tun yaushe kowa ya san matsayarsa amma ke ki tsaya ki kula mutum daya kwakkwara ya gagareki. Ki duba kiga Salmah yaushe-yaushe ta hadu da Farouk har ya je ya gaida Baba. Ya kuma amince kuna gama jarabawa a fara maganar aure amma ke kin tsaya mutanen kwarai sunzo kina musu yawo da hankali. Kin san yawan shargullan mutumin nan kuwa ya ke barin komai don ya zo gurinki?"
Siddiqah ta girgiza kanta. Amma bakinta bai mutu ba tace, "To ai Adda Raliya abu mai muhimmanci ne ake kashe masa lokaci ayishi. Yaga zai iya ne."
"Oho, ashe kin san kina da muhimmancin a gunshi kenan."
"A'a bani ba dai, aure yake so ai shiyasa yakeyin hakan. Duk lallami ne ba wani abu ba. To ba sai ya zabi irinsa ba? Me yasa sai ni?"
"Ba kya sonshi ne?"
Tambayar ta saka ta a tsakiya, domin bata san wannan amsar ba amma sai ta samu kanta da jin wani iri da ta auna kalaman Raliya a ranta. Zata iya kula wani daban bayan Sufyaan ya shigo rayuwarta? Ita kam bata san ma menene son ba ai bare idan ya sameta ta san shi takeyi.
Tana zaman-zaman ta 'yar daidai da ita ya zo ya bata mata sha'ani da tunaninta. Ita ina namiji yake gabanta bare aure bare auren mutum irinsa?
"Ba wai bana sonshi ba ne ba wai kuma ina sonshi ba, ban san komai fa akanshi ba."
"Abu mai sauki, idan yazo anjima sai ki tambayeshi duk abunda kike so ki sani game dashi."
"Tab! Idan yace na faye kwakkwafi fa?"
"Sai kice idan bai amsa ba ke ba kya yi."
Siddiqah ta kyalkyale da dariya. Ai ko ya amsa batayi akai gaba. Wannan odar tasa ina zata iya masa? Bayan ta tsagaita ne ta dubi Raliya sannan ta riko hannayenta.
"Na gode Adda Raliya, na san kina hakan ne don kina sona da alkhairi, ki tayani addu'a kinji? Amma wannan kam na bar wa masu shi kayansu."
"Kar kice dai haka. In sha Allahu har addu'ar daina gudu zan na miki, yanzu tashi mu fara aiki kinga kar ya iso ba a shirya masa komai ba."
"Me zamu mishi to? Ni fa kinga yanda yaken nan zai iya muyi ne ma yazo ya gwasale mu yace shi baya ci."
Raliya tayi murmushi, ta gane duk dungun da kanwar tata takeyi, amma ko zatayi yaya sai ta zanta da Sufyaan. Domin yanda Siddiqan ta fada ne, alkhairi take sonta dashi.
Siddiqah sarkin aiki, babu kyuya a sha'aninta sam-sam. Aiki idan dai an saka mishi suna to wuyan ta fara shi ne, cikin kankanin lokaci ta kammala. Duk da aikin da ta dukufa akai bataji balli-ballin da kirjinta yake mata ya ragu ba.
Yau kuma dodon nata ko da me yake tafe oho.
***
Ta kasa cewa komai haka ta kasa karasawa cikin falon, shi kuwa da alama yana sauraren yaga me zatayi ne domin a tsanake yake dubanta ko kadan bai nuna alamun damuwa da yanayinta ba.
Sallamar da taji ne a bakin kofar da ta jona cikin falon da kofar gida yasa tayi saurin kyafta idanunta, ta shaki numfashi sannan ta samu damar sulalewa a kasa daf da daya daga cikin kujerun falon.
"Ina wuni Yaya Tijjani?"
Cikin fara'a Tijjani ya amsa mata gaisuwarta. Sufyaan ko bai dauke idanunsa a kanta ko na dakika ba, hakan yasa tana dago idanunta tar a cikin nasa suka fada. Da alama dai tuhumarta yakeyi. Me yasa zai tuhumeta? Da ya san yanda ta tsorata ranar da ganinsa da bai tuhume ta ba. Don haka baza ma ta nuna ta damu da wani kallonsa ba.
"Ni kuma rowar gaisuwar ake min ne Mar'yam? Ko yauma guduwan zakiyi?"
Ikon Allah! Ta zaci ranar gigicewa ce ya saukar mata da abunda taji sanda mutumin nan ya ambaci sunanta. Amma yau kam ta tabbata wani sabon salon ya koyo duk don ya gama da ita ya cuceta. To ina babban mutum ina tsayawa koyan kirar sunan mace? Daga dukkan alamu practice yayi tayi har ya iya.
"Ba haka bane ba fa..."
"Yaya ne to, Mar'yam?"
"QS bari na zo. Ku gaisa da kyau kafun nan." Tijjani ya fada yayinda ya mike daga kujerar.
Da sauri Siddiqah ta dago idanunta, a tunaninta zaman Tijjanin zai dan fi sassauta mata halin da ta shiga, amma ai zama cikin daki daya da wannan mutumin babban hatsari ne, musamman da ya iya tsare ta da idanunsa ta gagara hada kwakkwarar kalma daya. Gashi shi kuma bisa dukkan alamu ba magananne bane bare yayi mata labari. Sai uban tambayoyi kamar dan jarida.
Sufyaan kuwa sai da ya saurara Tijjani ya bar falon ya shige ciki sannan ya nisa. "Na fara shirye-shiryen auren fa. Da fatan kema kin fara."
Hodijam! Haka ake yi ne dama? Daga cewa na gani na yaba sai aure? "Ni kam ba abunda na fara."
Murmushi yayi. "Kodayake naga guduna ma akeyi nayi tunanin hakan."
Hannu takai ta rufe fuskarta bayan ta runtse idanunta.
"Ina wuni?" Ta fada don ya rabu da wancan batun haka nan.
"Naki na amsa. Sai da na roka?"
"Kayi hakuri, kawai dai hankalina ne yayi gaba."
Murmushi mai sauti ya danyi sannan yace "To na hakuran. Me da me akeyi na shirye-shiryen?"
"Nima ban sani ba, Hajja Nenne ce takeyi idan yayuna sun tashi aure. Mu bama komai, tace bai kamata mu san abunda akeyi ba sai an hada."
"Kin amince amma zata zaba miki abunda zai amfane ki ai ko?"
Kai ta gyada masa. "To baki fada min ko na miki ba, ko kuwa dai kina da wanda kike so ne?"
Rufe idanunta tayi da tafukan hannayenta. "Mar'yam, kalla, dubeni nan."
Ta zaci ya fada ne don ta saurareshi amma sai ta kula jira yakeyi ta kalleshin. Wai ita bai san me hakan yake mata bane? A hankali ta dago kai ta kalleshi. Kwayar Idanunsa masu duhun qahwa ne wanda suke cike da ilimi da tsantsan hikima da fasahar iya bada tsoro ya sakar mata.
"Kinga, nan da 'dan lokaci kadan idan mun daidaita zaki zama ni in zama ke, ki fada min abunda yake ranki kar ki boye min, kinji ko?"
"Toh."
"Toh meye?"
"Nima dai ban sani ba."
"Baki san abunda yake ranki ba? Ko baki san me ya kamata ki fada ba?"
"Duka biyu." Ta maida ganinta kasa. Kallon ya isa haka nan kar ya zaci ko na maita ne yanzu kam take masa.
"To kina so ki san meye a raina ko kuma na barshi kar na fada?"
A hankali ta gyada masa kanta.
"Ban taba tunanin wata 'ya mace har ya shagaltar dani daga tunanin matata ba sai a kanki. Haka ban taba samun rashin sukuni ba har sai na zo na ga mutum irin yanda nake samun rashin sukuni akan ki. Mar'yam kina da wuri na musamman a tare dani. Ina kuma fatan kema ki sama min wannan gurin a taki zuciyar."
Ba tare da ta shirya ko tayi niyya ba numfashi ya kufce mata ta ware idanu. Ai kam dai ta san ya kamata yana da mata, amma bata san me yasa da ya zo gabanta sai take ji ta mance duniyar kaf ma bare ko ita wacece ko shi wayene. Ko meye matsayinsa a wajen kofar falon nan.
Kana dai ganin Sufyaan kaga wayeyyen mutum wanda ya gogu da sanin duniya, sannan ba laifi yana da kamala sosai hatta furucinsa kamar yana sarrafa yanda zai fiddashi ne daga adadin kalaman zuwa tsarin tasirinsu ga mai saurare.
Amma banda salo na yaudara ina ita ina dauke masa hankali daga matarsa? Ya bada kowani misali mana meye sai ya sharara mata karya babba dashi sannan ta yarda?
"Baki ce komai ba."
"Uhm."
"Ke bakya tunani na?"
"Na kanyi." Ta furta a sanyaye. Gwamma ta fadi gaskiya. Hala ya rage wani abun kan ya zautar mawa iyayenta da ita ya musu asara.
Murmushin Sufyaan ne ya fadada jin furucinta, abu guda da ya kula da Maryama-Siddiqah shine yanda bata boye iya hakikanin gaskiyarta. She is too innocent in that regard. Ba boye-boye, duk da karara ya kula da rashin sabonta da zance irin wannan da da namiji amma hakan sai ya kara kayata masa ita. Domin zai so ace shi ya rene ta da yanda zata san menene so, yanda zata kula dashi ya kuma tarbiyyartar da ita da nashi irin soyayyar.
Don haka rashin gogewarta a wannan fagen ba karamin guri ya share mata a zuciyarsa ba ya sama mata muhalli na musamman.
"Me kike tunawa game dani?" Ya tambaya.
"Kawai dai..." 'yan yatsunta ta shiga murzawa cikin juna.
"Sau biyu muka hadu kuma sau uku kacal kika kalleni da naje makarantarku, kodayake haduwarmu ta biyun tserewa kikayi da kika ganni."
"A'a fa ba haka bane."
"Oh sau daya ne ma ashe kika kalleni."
Siddiqah dai ta fahimci me yake son yi mata, don haka ta kau da zancen. "Yaya gun su Hajiya?"
Bata san ko haka yake kirar mahaifiyarsa ba amma ta so ta tuna jin hakan a gun Raliya.
Sufyaan ya kure idanunsa ya rankwafo gaban kujerar. "Suna lafiya. Daga gurinsu nake, tace a gaida ki."
Da sauri ta dago ganinta gareshi, "Ni kuma? A ina ta sanni?"
"Na je na fada mata na samu matar aure ne na kuma bukaci ta saka albarka a neman. Ta min addu'ar samun nasara sannan na taho nan."
"To ina amsawa. Na gode."
"Tunda kin yi na'am kinga addu'ar Hajiya ta soma karbuwa kenan saura naje na samu su Baba."
"Nifa ban sanka ba har yanzu."
Wannan murmushinsa mai sautin ya sake yi. "Kar ki damu, zan sanar dake ko ni waye a sannu. Amma ina so kan ki san ko ni waye ki gwada aunawa zuciyarki ko zata aminta da wannan bakon. Yanda bayan ko kin san ni waye zaki iya sanin ko zaki iya rayuwa tare dani. Me kike so ki sani game dani?"
Kanta ta gyada daidai lokacin da ta masa wata tambayar. "A ina kake da zama?"
"Lagos. Amma ina da gida a Kano da wasu gurare daidaiku. Zamana yafi yawa a Lagos inda iyalina suke."
Siddiqah ta waro idanu. Saura kiris ta masa wata tambaya amma ta matse, Raliya zata bata wannan amsar ba tare da ta matsa lamba ba.
"Zaki iya barin su Hajjanki ki bini mu zauna a can?"
Shiru ta danyi kadan cikin nazari sannan tace, "To baka ci abincin ba dai."
Idanunsa ya kai ga jerin kwanukan da ta shirya akan darduma kafun isowanshi. "Sai idan zaki saka min da kanki."
Bata ce komai ba ta tashi ta janyo plate ta fara saka abincin. Duk abunda sukayi ta saka masa kadan-kadan a kai sannan ta matso dashi kusa da inda yake ta ajiye masa dan farantin da ta saka su cokula a ciki.
"Tunda kika cika kuwa sai kinci kema. Kuma ina jiran amsar tambayata."
"Ni kam na ci nawa tun dazu, wannan naka ne."
"To na gode, zanci amma a bani labari."
"Labarin me?"
"Koma na menene, makaranta, gida duk abunda kike so."
Ganin tayi shiru tana nazari yasa yace mata "Me kikeyi kafun nazo yau?"
"Uhm, nayi zane da safe sannan na taya Adda Raliya aiki ni da Salmah, sai muka shirya jakar tafiyarmu."
"Tafiya?"
"Zamu koma cikin makaranta gobe in sha Allah." Kanshi ya gyada dai-dai lokacin da ya kai cokalin shinkafa bakinsa.
"Me kika zana?"
"Faduwar rana ne a sararin hamada." Ta fada a sanyaye, bata cika son yin labarin zanenta ba, ta daukeshi ne a matsayin abun da take kebewa tayi don ya taya ta hira da zurfin tunani. Ba ta rinka fadawa mutane masu bata tsoro labari ba.
"Za a nuna min?"
Kai ta gyada masa. A haka ya ci gaba da cin abincinsa, jifa-jifa yana watso mata tambayoyi. Ita kuma cikin wani hukunci na ubangiji bata iya musa masa komai. Ta gagara gane wannan al'amarin.
"To na gode da girki Mar'yam. Allah Ya saka da alkhairi. "
"Ameen."
"Idan zan sake zuwa zaki sake min irin wannan gashin naman, yayi dadi sosai."
"Nifa gidan ba nawa bane sai abunda suke dashi nake dafawa."
Sufyaan yayi dariya sosai. Bata taba jin yayi dariya irin haka ba. "To shikenan naji, zan kira in advance, sai a shirya da kyau ko?"
"Hmm." Kawai tace.
"Ina 'yan biyunki? Kirata mu gaisa duka. Naga kullum ba a rabaku, Haneefa ma ta gudu tunda muka gaisa bata dawo ba."
"Tafiya zakayi?" Siddiqah ta tambaya, tana mai fatan hakan. Amma sai ta samu kanta da cewa duk lalacewar zancensu akalla dai tana dan kara fahimtar shi wani irine.
"Ko zaki min masauki?"
"Ni Maryama! Masauki dai? Ni kam ba ruwana. Ka gaida mutanen gidanka."
Kafun ya ce meye ta mike tsaye. "Siddiqah." Ya kira sunanta. A hankali ta juyo gareshi.
"Muna nan da ke. Cikin kwanaki kadan, in sha Allah sai kin rasa inda zaki sakani don tattalina da zaki rinka yi."
"Tabdi jam. Lalle ma. Nifa bana son maza."
Dariya ce ta kubcewa Sufyaan wanda baiyi niyya ba. "Barka na, ko ba komai yanzu na tabbatar cewa bani da competition na samu fili free parlour nayi yanda nake so."
"Zaka sha jira ashe." Ta furta kasa-kasa ba tare da sanin ya jita ba.
"Da sauki idan a karshen jirar za a tarerayeni a yi maraba dani."
Kaji mutum dai wani babba dashi wai a tarairayeshi. Ita fa kanta ma ya fara ciwo ne, da ya samu ya tafi ta huta.
"Allah Ya kiyaye hanya."
"Ameen na gode, Allah Ya bada sa'ar makaranta."
Ba tare da tace masa komai ba, ta juya tayi cikin gida.
Sai da Salmah ta kwala mata kira ne Siddiqah ta taho falon da sauri. Nan sukayi turus suna kallon kallo.
Kudine masu yawa har dubu biyar a ajiye akan wani kwali mai girma a jikin takardar an rubuta. Mar'yam. A daya takardar kuma kan karamin kwalin an rubuta 'yan biyun Mar'yam.
Sai dai Salmah bata jira ta cewarta ba tayi tsalle ta hau bude kwalin da sunanta ke kai. Baki a bude ta shiga ciro kayan masarufin dake ciki wasu 'yan ubansu masu kyau da inganci.
Siddiqah ta ciro kai ta sake duba falon ta tabbatar ko ya tafi ko yana nan. Sai dai banda sauran kamshinsa babu komai a falon. Haka suka tattara falon suka dauki kayan da ya kawo musu sukayi ciki dashi.
Ko bude nata kwalin batayi ba Siddiqah tace Raliyah ta raba musu da Haneefa da Salmah, bata son komai a ciki. Kudi kuma tace a ajiye masa abunsa duk randa bata aureshi ba yazo neman abunsa akalla zata mayar masa da kudinsa.
Kallonta suka tsaya yi shekeke kamar notin kanta ya kunce. Amma kan tace kobo Salmah ta janyo wata ledar chocolate ta fara masa aiki.
Duk yanda Siddiqah take son cakulet masu gyada da inibi ga kuma Dabinon da aka cusawa gyada aka dumulmule su da cakulet, haka ta kawar da kanta ta bar karamin falon, ita dai kam bazata taba cin abun hannunsa ba. Ba abunda ya kaita.
***
Hohoho!🔥 🙊
Uhum... inji Uwar gulma da tayi abun kunya. Ba magana...🤣
Me zamu tarar a gaba? Mu fada mata? A;a mu dai bari ta gano hehehe.
Ma'assalam.
Umm Yasmeen💞
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top