BABI NA BAKWAI


Gombe, NAJERIYA

1994

Tunda Siddiqa ta fuskanci abun na Sufyaan ba mai karewa bane sai ta daina ma batawa kanta lokaci gurin neman yakice shi daga rayuwarta. Ta dai san idan tana makaranta baya damunta, iyaka dai idan suna zo gida duk sati biyu sai yazo ya ganta. Ko yanzu da zasu koma zangonsu na karshe su zana jarrabawa sai da ya zo ya mata nasihar karatu sai kace shi takeyiwa karatun.

Ya gama zakuwa da ta dan haska masa matsayinsa a rayuwarta, daga gani ba ataba cewa ba a son shi bane shiyasa yabi ya damu. Itama lokuta da dama takan rasa me yake tsaida ta. Sai dai kamar yanda ta fada ta fi son komai zatayi ta shiga ciki idanunta a bude tangararau. Bata son jeka nayi ka ko azo ana jeka ka dawo.

Don haka ne wancan zuwan nashi da yayi ta gagara hakura ta fiddo abunda yake damunta dangane da shi tun farkon haduwarsu. Wanda a hakikanin gaskiya shi ya hana ta bude zuciyarta ta bawa Sufyaan wurin zama kamar yanda ya bukata.

"Kina da tambaya?" Ya nanata zancenta. Jumfa ce a jikinsa ruwan kasa mai cizawa an mata aikin hannu da bakin zare ba tare da an cika rigar da aiki ba. Haka nan yake saka kayansa komai a saukake. Tamkar kayan nauyi suke masa idan ya sa masu girma.

"Eh."

"Ina sauraronki."

"Ka taba ganina a wani waje banda gidan Adda Raliya? Nufina kafun kazo makaranta ka ganni da farko."

Shiru yadan yi hade da kura mata idanu sannan ya nisa. "A'a. Amma jikina ya bani na kusa haduwa da matata. Hakan ya dauki tsawon lokaci har sai randa na daura idanuna akan ki. Wani abu ne kika gani?"

Da sauri Siddiqah ta kada kanta. "Babu komai. Na gode da ziyara a gaida mutanen gida."

Yafito ta yayi yana zaune daga kan kujerar falon, hade da fadin, "Zo nan, ina zakije? Yaya zaki dauko magana kuma ki bar zancen rabi da rabi?" Kallonsa tayi wani irin dama da guntun haushinta, ya saka ta girkin abincinsa ta sha wuya. Amma nan take tayi dana sanin daura idanunta a kansa, don duk masifar da ta tanada bacewa tayi bat kamar ba ita bace me bitar abunda zata fada masa idan ya iso.

"Kawai dai..."

"Zauna ki fada min."

A hankali ta nemi wuri a kan kafet din falon ta zauna. "Kaga ba, tun kafun kazo makarantarmu ni na taba ganinka."

Kansa ya mayar baya yana kare mata kallo cikin tsananin mamaki. "Zai yiwu mana, a gidan Raliya."

"A'a."

"To wannan yana da alaqa da dalilin da yasa kike ta bani wahala? Saboda ke kika fara ganina ba ni na fara ganinki ba?"

Siddiqah ta dukar da kanta kasa ta shiga wasa da 'yan yatsunta, "A'ah, saboda ba a zahiri na ganka ba a cikin bacci ne."

Girarsa duka biyu suka tashi sama cikin tsananin mamaki. Yana nazarin kalamanta. "Idan na fahimce ki da kyau, a mafarki kika fara ganina?"

A hankali ta gyada masa kanta.

"Shiyasa kika ce ina baki tsoro?"

Da sauri ta daga kanta, ta mance yaushe ta furta masa hakan amma tabbas abunda ta fara ji game da shi bayan burgewa shine tsoro.

Murmushi yayi sabanin yanda tayi tunanin zai yi idan yaji dalilinta. "Mar'yam kenan, ai dan Adam yana mafarki a shinge uku ne, ko dai mafarki mai kyau daga Allah ko kuwa mummunar mafarki daga shaidan ko kuwa mutum yayi mafarkin abunda ya riga ya saka a ransa."

"Tunda ban taba ganinka ba shiyasa nayi tunanin ai ba abunda na sakawa raina bane."

"Me yasa shaydaan to?"

"Na'am?"

"Me yasa kika zabi cewa mafarkinki daga shaydaan ne ba daga Allah ba?"

Siddiqah nan da nan taji kunya ya rufeta. Hakan na nufin ta masa mummunar zato kenan fa tun kafun ta san shi waye. 

"To ai lokacin ban san ka ba."

"Kin san cewa mutane na kwarai masu gaskiya wasu lokutan sukan yi mafarkin abu ya zama gaskiya? Hala mafarkin da kikayi bushara ce daga Allah. Don haka kar ki sakawa ranki wani abun da zai dameki. Tunda kince lokacin baki sanni ba, yanzu fa da kika sanni me zaki ce game da hakan?"

Bayanin da ya mata ne taji ta gamsu da hakan, duk da yanda ya nemi ya sakata a fagen da bata san ko ta kai matsayin wurin ba, wai 'mutanen kwarai' ita ina ta kai har wannan matsayin?

"Zan kara baka dama idan bakayi fushi ba sai mu fahimci juna da kyau. Tunda bayan nayi mafarkin ai nayi sallah na roki zabin Allah." Duk da a zahiri dai neman tsari tayi daga sharrinsa, tana tunanin shima bawa Allah zabin ne ai.

Murmushi yayi idanunsa tar akanta. "Mar'yam, na dade banji kalaman da suka faranta min rai ba irin wannan. Ni kuma a shirye nake da na sanar dake duk wani lungu da sako na rayuwata har sai kin gamsu."

Hakan kuwa akayi, domin tun wannan lokacin iyaka kokarinsa Sufyaan yakeyi don ganin sun samu kyakkyawar fahimtar juna.

Siddiqah dai a dan tsakanin nan da ta tabbatar da Sufyaan bai zo da niyyar yaudarar ta ba kuma mafarkin da tayi bayi da alaqa da cewa shi din wani irin mutum ne, ta bar kanta ta dubeshi da idon basira domin ta fahimci ko shi waye, wanda a farkon zuwansa har ga Allah bata bari tayi wannan nazarin ba. Kawai kallo take masa na kura yaga nama.

Amma yanzu ta fahimci cewa Sufyaan Barkindo Sajoh, tsayayyan mutum ne mai matukar kwarjini, muddin ya shiga wuri kuwa ko ba asan shi waye ba, yakan samu kulawa ta musamman da wata girmamawa daga al'umma.

Ta kuma fahimci daukar hankalin mutane da kuma rikesu akan tsarinsa wata baiwace da Allah ya masa, tun kafin ya taka mukamin da ya kai yanzu.

Kamar yanda ya shaida mata shi bafulatanin jahar Adamawa ne daga asalin garin Jabbi Lamba cikin karamar hukumar Girei. Ya fada mata iyayensa gaba da baya mutanen garin ne.

Koda zata ture asalinsa a gefe, Sufyaan yana da wani irin launin fata mai sa mutum ya mance iyakacin kurewar launin da zai fidda shi daga sahun bakake ya fada sahun farare, ma'ana shi ba fari bane tas! Amma yana da murjajjen fata da kallo daya zaka masa ka san cewa tabbas ma'abocin jikin nan hutu ya sani gaba da baya.

QS Sufyaan Barkindo yayi fice wurin sanin sirrin abun da ya sa a gaba, ya san tattali. Ya san yanda yake bi da abokan kasuwancinsa haka abokan hamayya.

Tana hankalce da yanda yake gudanar da hakan. A iya lokacin da ya dauka yana zuwa gurinta don ya fayyace mata ko waye Sufyaan, baya boye mata komai ciki kuwa harda sashin kasuwancinsa jifa-jifa.

Abunda bata fahimta ba, yana kokarin ganar da ita koda sama-sama ne. Sai itace ma wataran take ce masa bata gane komai da yake fada. Sai yayi dariya yace "Wataran zaki gane."

A lokuta da dama sirrin kyau da rashin tsufanshi yana daure mata kai ganin yanda harkalla da zirga-zirga bai kamata ace sun bashi damar samun lafiyayyen fasali da sura ba. Amma duk da kasancewarsa bayi da rama, sam babu alamar tumbi a tare dashi.

Ko dayake ta san yanda ya dauki nau'ukan abincin da yake ci da muhimmanci ko wannan kadai zai sa ya zama mai kyakkyawar sura. Don a halin yanzu haka shekarun Sufyaan Barkindo Sajoh na haihuwa Talatin da bakwai a duniya. Zancen dai gaskiya ne yanda tayi hasashe lokacin da ya fara cewa yana sonta. Da kanshi ya tabbatar mata shekaru ashirin rus yake bata.

Yana da fuska mai tsawo da madaidaita labba masu taushi wanda gashin bakinsa ya hade da gemunsa ya wuce zuwa inda mahadin sajensa ke kwance lub a gefen fuskarsa sai sheki yakeyi.

Idanuwansa manyane da suka daidaitu a ramukan idanun. Sun dan zurma ciki saboda tsawon hancin da ke shimfide a fuskarsa.

Duk da bai cika saka kayayyaki masu tsada na wucin hankali ba, ta kula Sufyaan mutum ne mai tsantsan tsabta da kuma iya ado.

Ko wace mace ko burinta ta samu miji tamkar SBS. A cewar Salmah kenan zamanin da take mata wa'azi ta daina yiwa Sufyaan wulakanci.

Daga yanda yake mata hirar yaransa kuwa ta fahimci shi mutum ne da ya shaku da iyalinsa baya bari komai ya gitta a kan lamarinsu duk da babban abu guda da SBS ya sani shine ta ina suka fito ta ina za a zubasu; wato harkar kudi, kwarai baya bari nemansu su shiga hakkin iyalansa da danginsa.

Kullum tana ganin yanda yake sintirin zuwa dubo mahaifiyarsa. Da wuya ya shafe sati hudu bai je ya ganta ba.

Tsaurarren mutum ne ta waje, baka sanin lokutan da suka dace da saukinsa don haka kowa ya kasance mai takatsantsan dashi. Sai dai duk da tsaurinsa mutumne a wani fagen mai kankan da kai domin ko kadan abun hannunsa basu rufe masa idanu ba. Zai dai neme su amma baya takama wa duniya da su.

Ina zata taba tunanin bayan irin abun da ta shuka masa zai ci gaba da lallabata yana bin yanda take so? Ba ita kadai ba harta Haneefan Raliya idan yazo tana ganin yanda yake mata komai a tsanake yake hira da ita tamkar babban mutum ba yarinya mai shekaru biyar ba. Yana mutumta kaf 'yan uwanta.

Tazo kuma ta fahimci cewa tsaurinsa da kuma tsare gidansa da yakeyi, halittarsa ce da ta riga ta game da shi. Ba ita kadai yake shukawa halin nasa na iko ba.

Abunda yafi burgeta dashi shine yanda yake ganin martabar mahaifiyarsa. Domin a cewarsa itace Uwarsa itace kuma Ubanshi ita ta bashi rayuwarta har ya tako matsayin da yake a yau, domin kuwa da bata daura shi kan hanyar bi da rayuwa a sannu ba, ko kuwa ta gwada masa idan yana da gaskiya ya hakikance kan hakan har ya cimma burinsa ba da baya tsamman ya iso haka.

Allah ne ya nufe shi da zama abunda ya zama yau, ta hanyar mahaifiyarsa Hajiya kamar yanda suke kiranta.

"Mahaifinmu kuma Malam Barkindo kafun ya rasu, magatakarda ne a sakateriya ta karamar hukuma sannan kuma yana koyar da karatun allo idan ya taso aikinsa. Ban taba ganin Kawu yaje wani wuri ba bayan ya taso aiki. Kullum yana gida wannan yasa muka shaku sosai dashi. Ya rasu ina aji uku a makarantar sekandire."

Siddiqah ta nisa hade da yin addu'a wa mahaifinsa. Ta kula da yanda idanunsa suka sauya lokacin da ya fara ambaton mahaifinsa.

Tabbas ita bata san zafin rashin mahaifa ba, amma ta san a yanda takejin nata a ranta ranar da za a ce babu su Allah ne kawai zai fisshe ta. Don haka ta tausaya masa kwarai.

"Yanzu kin gamsu da ko wanene Sufyaan? Da fatan baza a sake tserewa da gudu ba idan an ganni?"

Hannu ta sa ta rufe fuskarta. "To mana ka daina. Ai nace kayi hakuri."

"A hada min zobo mai dadi sai na hakura."

"Cin hanci kenan fa."

"Ko kinfi so a biyani ta wani gurin sai na biki bashi?"

"A'a. Na gode ai na fada maka kai abun tsoro ne kaki ka yarda."

Yana dariya yace "To kije ki huta zancen yau ya isa haka. Sai na sake zuwa in sha Allah. Gobe da safe ni zan wuce."

"Lagos din zaka koma?"

"A'a ina da daurin aure a Kano, za kiyi min rakiyane?"

"Naga alama kafun ayi auren nan dai kana so Babana ya yanka maka ni."


Jin ta ambaci kanta a matsayin tasa ba karamin tsayawa Sufyaan yayi a rai ba, bai san lokacin da ya tsayar da ganinsa a kanta ba, "Kin san ma'anar abunda kika fada yanzu kuwa?"

Tana murmushi ta rausayar da kanta gefe. "Ni din na ce wani abu ne?"

Yana dariya yayi kwafa yace. "Zakiga aiki da gamawa kuwa."

Ai kuwa ta gani. Domin bayan kwana biyu da tattaunawar su da Sufyaan, suna zazzaune a falon Baba tare da 'yan uwanta a Gombe, Baba ya shaida musu cewa "An zo anyi tambayar auren Siddiqah jiya da yamma."

Bayan su Umma Gaggi da su Hajiya Mama sun gama addu'o'i da san barka ne ya nemi ganawa da Siddiqan.

"Salmah kema dakata tunda tagwayenki ce, sai ki tayata zama."

Tunda Baba ya fara magana, Siddiqah ta gagara sanin ta ina take numfashi. Shikenan ta faru ta kare anyiwa mai dami daya sata. Yanzu anyi tambayar, Baba har ya bada kenan? Yanzu ta kusa zama matar Sufyaan kenan?

"Yawwa, kamar yanda na fada muku an turo nemawa Sufiyaan aurenki Maryama, shin kin san da maganar?"

Kanta na kasa ta gyadawa Baba, duk da bata san aika-aikar da zai aikata ba kenan da yace mata zata ga aiki da gamawa. Bata isa ta karyatashi a idanun Baba ba. Zuwa yanzu ta dan samu natsuwa da Sufyaan wannan dalilin yasa ta amince ta san da batun tambayar.

"To yayi kyau, duk da dai na yi muku sha'awar ku cika goma sha takwas kafun na aurar daku irin yanda nayiwa su Kulsum da Fatima don ku kara mallakar hankalin kanku, tunda miji yazo kam kuma ai babu zancen jira. Sai kije a sha bakwai din. Duk da Tijjani ya masa shaida ta kwarai, ina da mutane na a can Adamawa na sa a min bincike dangane da shi Sufiyaan din. Da kuma inda yake aiki. Idan har na gamsu sai na basu amsa a sanya lokaci."

Fat! Fat! Fat! zuciyarta takeyi har ya kai aya. Sai da taji ya ambaci sunan Salmah sannan ta samu ta ja numfashi. "Ke ma Salmah yanzu ne kike so ayi maki auren?"

Dadin Siddiqah da Baba kai tsaye yake maganar sa ba abunda ya dameshi, wasu sukance shi ta dauko a fadin abunda ke ranta kai tsaye.

Salmah nan da nan ta hau noke kai. "Kwanaki naji ance Hamza ya zo gurinki ko? Yaron wajen Yaya Habu."

"A'a fa Baba, an canja shi yanzu wani ne sunanshi Farouk, ba har sunzo sun gaisheka ba?"

Baba yayi dariya sosai. Don a fili Salmah bata iya boye zalamarta idan tana son abu. Bare ta san Babansu abunda ka amince da farko to babu zancen kazo kace ka canza shi din yake so ka tsaya a kai.

"Shikenan, Maryama sai kuje ku fara shirinku na mata, na san ana bada amsa zasu bukaci a daura auren don na ga alama mai yi da gaske kikaje kika samo. Musamman ya roki alfarmar a saka lokaci kusa-kusa, inji 'yan aikensa."

Siddiqah kam kunya kamar ta nitse cikin kasa da gudu ta tashi ta bar falon. Inda ta tabbata har gari ya waye zancen aurenta za a kwana yi a gidan.

Zuwa lokacin da yawa 'yan gidansu sun san da batun Sufyaan domin da ya zo wurinta har cikin gida ya shigo ya gaishesu sannan ya tafi. Ga ihsani da yake musu ko yazo ko baizo ba wannan zaunanne ne sai sunga aike. Tun Siddiqah na fushi har ta fahimci haka Allah yayi shi, shi din mai yi ne.

***

Yauma Sufyaan ne ya kirata suna gaisawa yace mata "Na dauka hutunku ya kare ai. Yaya naji kuna gida kuma?"

"Eh ya kare, muna dai jiran Baba ne ya yi mana aike dangane da shirye-shiryen komawa."

"A'a, me yasa za a jira Baba? Me ya saura na shirin komawar?

Siddiqah kam shiru tayi don ta san shi da naci sai ya nemi sani ko a wani wurin.

"Mar'yam, tambaya na miki."

"Babu kawai dai... normal shiri ne dake hutun komawa extension ne yanzun ba dogon hutu ba."

"Normal shiri?"

"Eh."

"Naji. Gobe akwai wani yaro Bilyaamin zai zo. Zai kawo miki sako. Kuyi duk shirin da ya dace ku koma makaranta. Bana son zamanki haka a gida."

Juya idanunta tayi, "Meye, saboda kar wani abokin Yaya Tijjani ya ganni yace shima yana so?"

"Siddiqah!" Ya fada a tsaurare. Sai kuma taji ya dan furzar da numfashi.

"Kinga idan kun koma kuka yi karatu da kyau, kikayi jarabawa chances din cin jarabawanki da kyau zai karu. I only want the best for you. Kinga kina gamawa sai muyi aurenmu ko?"

"To ai ni har yanzu bakaji nace maka zan aure ka ba."

"Kin gan ki ko? Naga alama kina son bulala. Ki daina wannan zancen."

Dariyarta ta datse don kar yajita. "To ai gaskiya ne. Karya kake so nayi maka?"

"Allah, zaki sa na bar duk abunda nakeyi na zo inda kike."

"Ko ka zo ai ka san ba abunda zai canza."

"Kamar da gaske. Na dai fada miki ku zauna cikin shiri. Duk wani abunda kuke bukata kuyi shi a wadace ku koma makaranta."

"Sai kawai nacewa Baba saurayina ya mana shirin makaranta ko? In fada maka ba a shiga hurumin Babana, idan ka masa aikinsa sai ya gamu da kai."

Dariyar da taji ta kwace masa ne ya bata mamaki. Sai da yayi sosai sannan yace "Mar'yam, yaya zanyi dake idan ban aureki ba? Kin gama shiga raina ta ko ta ina. Shi Baban ai zamuyi tamu maganar dashi babu ruwanki. Ke dai jeki kiyi karatu. Ban yarda a bawa kowa fuskar yin magana ba kuma. Kin san ni yanzu dan gatan Baba ne, shi ya dafa min baya. Ya san da zamana."

"To Dokaji."

"Lalala, me kikace?"

Da sauri Siddiqah ta kife kan layin. Tayi murmushi mai sauti, tana juyawa tayi kicibis da Salmah wacce ta hau jujjuya mata gira tana mata signa.

"Iyye iyye, ta Sajohn ba. Zaki kama ki mana bakin ciki, dalla ki barshi yayi abunda yayi niyya wata gulma wai shiga hurumin Baba. Idan Baban ya aiko ai mayi wani abun da na gunshi. Zaki wani tsaya mana jan aji. Ai ni Farouk bana wani masa fulakon nan."

"Sannu marokiya, sai ya ce ki biya shi ai, zaki sani."

***

Tunda magabatan Sufyaan suka samu amsa daga wurin Ambasada Usman Muhammad, labari ya karade dangi batun auren da Sufyaan yake da shirin yi. Yayin da wasu ke taya sa murna wasu mamakin dalilin karin aurensa sukeyi ganin yanda ba a taba jin kansa da matarsa ba, wasu kuma cewa sukeyi kash! Inama da sun san yana da muradin karin aure da 'ya'yansu suka turo ya aura. Duk dai kowa da nasa tunanin.

Shi kuwa Sufyaan sai hamdala yakeyi komai yana tafiya yanda yake so. Ta bangaren Amina dai bai samu matsala ba, bayaga kin yarda ta koma Kano da tayi wanda ya san a hankali zai lallabata ta koman. Musamman idan ya gwada mata can tana kusa da iyayenta da 'yan uwa zata fi jin dadin hakan.

Don haka bai daga hankalinsa a kan wannan ba, sanin halinta sarai idan ya nuna tsarinsa ne hakan ko don ta nuna bacin ranta sai ta hana kanta tunani mai fa'ida tayi abunda zai zo ya dameta. Wannan yasa yace "Shikenan, ku zaku iya zama a nan zuwa lokacin da yara zasu gama school session, idan kin canza ra'ayi kafun nan to, idan baki canza ba sai ku ci gaba da zama a nan abunku."

Ya ga mamakin da ya zanu a fuskarta amma sai ta buge da cewa, "Eh, dole kace mu ci gaba da zama tunda yanzu harkokinka duk sunfi yawa ta can ai zaka zauna da zabin ranka mu kuma ko oho dole kace mu zauna a Lagos din. Ai kana da abokan hulda a Kano masu makarantu, kayi magana kawai yanzun nan a samawa yara slots. Tare zamu koma ba zaman da zamuyi."

Yana jin kalamanta, yayi siririn murmushi, amma bazaiyi kasada har ta gani ba, domin Amina nada kaifin basira yanzu-yanzu zata dago shi. Yayi mamaki ma da ta bi tsarinsa, idan banda kishi ya rufe mata idanu ya san da tuni ta dago shiri ya mata.

Idan ya hadasu gari daya hakan zai fi masa sassauci duba da irin tsarin da ya sa a gaba dangane da kamfaninsa. Tunda tuni ababensa na Kudu sun fara kankama dole ya tsaya akan bangaren da ake gudanarwa ta Arewa domin shima ya habaka ya kafu. Ya sayar da wasu hannun jarinsa, ya kara karfi kan ababe uku wanda ya kula a shekaru kadan masu zuwa su zasu mamaye duniya idan Allah ya yarda. Yanzu ya rike harkar gine-gine, man fetur da gas, sai bangaren shiga da fitar kaya a kasar. A hankali kuma zai bada kofar karo wani sabon abun da yake ga za a samu alkhairi akai sosai.

Da wannan tunanin ya ci gaba da shirye-shiryen aurensa da Maryama-Siddiqah.

***

Wedding bells, anyone?

Maryama-Siddiqah da mijin mafarkinta🙊

Ma'assalam

Umm Yasmeen💞

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top