8.









KADUNA.
DECEMBER, 2003.




Sannu a hankali motar ta tsaya gaban wani madaidaicin gida a unguwar dosa. Yaran da gudu su ka sauka su ka yi cikin gida suna ihun murna sun gane an zo gidan kakanninsu.

Umma ta yi murmushi tana kallonsu. Itama a hankali ta bude ƙofar ta sauka. Ta ƙarewa gidan na su kallo. Yau gata ta dawo cikin shi. Da tsakaninta da shi sai ziyara. Ko a mafarki bata taɓa zaton zata dawo gidan iyayenta da zama ba.

Rayuwa kenan.

Samarin unguwa suna ta gaisheta, su ka kama aka shiga da kayayyankin ciki. Ko tsinke bata bari a Kano ba. Komai ta kwaso ta bar ta dabo har abada kenan. Kayan gado su tuni su ka iso. Bata san ina aka saka su ba sai ta shiga zata gani.

Wata biyu kenan da ta kira Baba Malam tana kuka ta ce mai ita gida take so ta dawo. Ta daɗe tana saƙa hakan a zuciya daman, to zuwan Musa ne ya sa ta amayar da abunda ke ranta.

Zaman garin ya isheta bata ga amfanin cigaba da zama a chan ba tunda wanda ya yi sandin komawarta garin ya tafi ya barta. Ga ƙaninshi ya saka gaba yana neman illata su.

Alamarin Musa ya daina bata mamaki. Mutum ne da son abun duniya ya rufe mai ido a shirye ya ke da ya yi komai akan abun duniya. Shi yasa kafin ya ja mata asara ta tattara ta bar mai garin gaba ɗaya.

Yanzu bata da wata alaƙa da garin Kano, sai dai wani ikon Allah kuma.

"Umma mu shiga ciki."

Muryar Maryam ta dawo da ita daga zurfin tunanin da ta faɗa. Umma ta ƙaƙalo murmushi tana shafa kan ʼyarta. A ciki duk tafi nuna damuwa akan dawowarsu nan.

Hannunta ta kama su ka shiga ciki. Ta iske Mama da Baba a tsakar gida sun fito tarban su, Zee da Safiya suna ta zubawa Baba Malam surutu.

Ganin iyayenta ya sa Umma jin kwalla ya tarun mata a ido. Ko shekaran nawa a duniya kai ƙarami ne gaban iyayenka. Ganin su kaɗai ya sa wani irin sanyi ya lullbeta kaso babba daga cikin abubuwan da ke damunta sun tafi.

Har ƙasa ta tsugunna ta gaidasu. Mama ta kauda kai tana share hawaye ganin yanda Sa'adatu ta koma kaman ba ita ba.

"Mu shiga ciki, sannun ku da zuwa. Kun kwaso gajiya." Baba ya ce rike da Bashir a hannu.

Falon shi su ka isa inda abinci ke jiran su. Jamila ta zubawa kowa ta miƙa mai.

"Sannu da zuwa Umma."

"Lafiya lau Jamila mun same ku lafiya?"

"Lafiya lau Umma. Bari in dauko kunun aya na san ya yi sanyi yanzu."

Kaɗan Umma ta tsakuri abincin hankalinta na kan yara da ke ta tsalle abun su. Ko a iya haka ta san dawowansu gida ba kuskure bane. Rabon da taga yaran sun saki jiki haka an kwana biyu. Maryam ce kaɗai damuwarta, yanzu haka ma wasa kawai ta ke yi da abincin gabanta.

Bayan sun gama cin abinci Mama ta ce ya kamata su watsa ruwa su kwanta su huta. Umma ta miƙe zata shiga ɗakin Mama, Mama ta ce a'a ba nan ne masaukin su ba.

"Firdausi dauko kayan ku biyo mu da su. Ke kuma mu je."

Cike da tambayoyi fal a rai Umma ta bi bayan Mama. Gidan na su babban ne ba laifi sashe uku ne. Ɗaya na Baba Malam da ya ke ta gaba sai kuma ta ciki sashe biyu na matan gidan wato Mama da Gwaggo. Tunda Allah Ya yi wa Gwaggo rasuwa sashenta ya zamana babu komai sai kaya da ake ajiyewa.

To bangaren Gwaggo Umma ta ga sun nufa. Mama ta sa mukulli ta buɗe. "Fara shiga Sa'adatu."

Umma ta yi sallama ta shiga. Baki buɗe ta karewa wurin kallo kaman ba shi bane ya yi shekara da shekaru ba'a zauna ciki ba. An gyara shi tsaff an mai sabon penti kujerunta na Kano an jera su cikin falon. Ido cike da kwalla ta juya ta kalla Mama.

"Mama...."

Mama ta yi murmushi ta ida shigowa cikin falon. Sauran ɗakunan su ka shiga. Gadajen suma an jera su tsaff. Kaman an ɗauko gidanta na Kano ne an ajiye a nan. Ɗakuna uku ne a sashen sai falo ɗaya. Sauran kayanta da ba su samu wuri ba kuma an adana mata su.

Yaran nata shige ta fice a wurin. Wuri an yi mai gyara an yi penti gwanin sha'awa. Bashir ya gama guje-gujen shi ya dawo wurin Umma.

"Umma nan ne sabon gidan mu?"

Umma kai kawai ta iya gyada mai saboda tana buɗe baki kuka ne zata fashe da shi. Idan ba iyaye ba waye zai maka irin haka?

Bayan sun gama ganin ko ina yaran su ka yi tafiyarsu ya rage saura Umma da Mama. Umma Sa'adatu ta kamo hannuwan mahaifiyarta gam cikin nata.

"Mama nagode, Allah Ya saka da alkhairi. Allah Ya biya ku da jannatul firdaus, nagode Mama."

"Ameen. Ya isa haka kar ki sani kuka," Mama ta ce tana murmushi. Itama idanunta sun yi ja. "Share hawayen Sa'adatu. Ya isa haka."

Umma ta sa hannu ta share fuskarta amma hawayen basu daina zuba ba. Mama da sauri ta fita dan zuciyarta gaba ɗaya ta gama karyewa. Allah Ya basu ikon kula da su yanda ya kamata.  Da ran su 'ya'yan Ahmad sai dai su yi kukan kewar shi amma ba dan sun rasa wani abu a rayuwa ba.

Umma ta yi kuka sosai kafin ta shiga ta watsa ruwa. Sai bin ɗakin take yi da kallo. Ɗaya daga cikin akwatin da ta zo dasu ta buɗe ta ciro files guda huɗu. A hankali ta saki ajiyar zuciya tana tuna lokacin da Ahmad ya bata ajiyar takardun, ashe duk shirin mutuwar shine ya ke yi basu sani ba.

Yau ya shekera ɗaya da rasuwa. A kwana a tashi babu wuya wurin Ubangiji. Shekaru biyun nan sun zo mata da chanje-chanje masu wuyar ɗauka. Shekarar da ta gabata kaman haka duniyarta ta ruɗe, ta rasa Ahmad. Wannan shekarar kuma gata ta dawo gidan iyayenta da zama.

Alhamdulillahi Ala Kulli Halin!

Takarɗun ta ɗauka ta nufi bangaren Baba Malam. Ta same shi a falo kishingiɗe yana kallon labarai. Ganinta ya sa shi miƙewa ya zauna.

Umma ta zauna kusa da shi a ƙasa. Kanta ta kifa kan kafafuwanshi. Baba ya yi murmushi yana shafa mata kai. "Nagode Baba. Nagode."

"Bar yi mun godiya Sa'adatu. Dena kukan haka nan, ya isa. Kin dawo gida, kuka ya ƙare. Babu wanda zai shigo nan ya yi barazanar illata ki."

Ran Baba Malam ba ƙaramin baci ya yi ba jin abunda Musa ya yi. Washegarin ranan da Sa'adatu ta kira shi ya sa aka fara gyara cikin gidan. Niyarsa su dawo cikin satin sai dai saboda yanayin aikinta ba su samu sun taho ba sai yanzu. Yana raye babu wani da ya isa ya cutar mai da ɗiyarsa. Har sai inda ƙarfinsa ya ƙare wurin basu kariya da duk abunda ya kamata.

Da kyar Umma ta samu ta saita kanta. Files ɗinnan ta ciro ta miƙawa Baba.

"Ne mene ne wannan Sa'adatu?" Ya karɓa yana dubawa. Kai ya dago ya kalleta bayan ya karanta ya fahimci na meye.

"Na rasa Ahmad. Amma ina da kai Baba, ina da Mama, dan haka da sauran gata na a duniya. Wannan dukiyar da marigayi ya tafi ya bari ne. Kai na ke so Baba ka kula dasu, kai kaɗai ne baza ka cutar da ni ba Baba. Dan Allah kar ka ce baza ka karɓa ba."

"Sa'adatu..."

"Dan Allah Baba. Kai kaɗai zan ba hankalina ya kwanta. Dan Allah ka riƙe su a wurin ka."

"To. Allah Ya bani ikon riƙe amana."

"Ameen Baba, nagode. Allah Ya saka da alkhairi."

Tun farko da ta yi hakan wata ƙila abubuwa da yawa basu faru ba. Gidan su na Kano tare da taimakon ASP Zubairu an saka shi a kasuwa. Niyarta idan aka saida sai ta samu fili a nan garin ta siya. Gudanar da shaguna kuma ta ɗamkawa shi a hannun ASP Zubairu.

Ta daɗe a falon Baba har Mama ta zo ta same su. Haƙiƙa iyaye rahama ne.

A daren ranan Umma Sa'adatu ta kwanta ta yi barci. Rabon da ta yi barci irin haka ta manta.

Rayuwa ta cigaba da tafiya inda suka yi settling a garin Kaduna. Ta kai takardunta da yawa asibitoci neman aiki sai dai har yanzu ba'a dace ba. Yaran ta saka su makaranta private daidai gwargwadonta. Makarantan kuma na kusa da gida a ƙafa su ke zuwa ko a nan an rage kashe kuɗin mota. Islamiya ma a nan cikin unguwa take.

A hankali har suka saba da zaman nan ya zame musu jiki. Gida mai mutane da yawa ko ba komai zai ɗauke maka kewa saboda mutum rahama ne.

Har yanzu aikin Umma babu labari. Duk asibitin da taje sai su ce zasu nemeta daga nan kuma ta ji shiru. Abun ya fara damunta dan bata saba zama hakanan ba. Kuma ba son zama wuri ɗaya ta ke yi ba. Tafi son ta samu abun yi saboda zama wuri ɗaya na saka ta tunane-tunane daban daban.

Ta samu Baba Malam da Mama akan tana so ko teaching ne ta fara kafin Allah Ya sa a samu aikin asibitin. Su ka nuna hakan ma ya yi. Cikin ikon Allah tana kai takarɗunta makarantun aka dauketa aiki a wuri uku. Daga ƙarshe ta yanke hukuncin karɓan aiki a makarantan su Maryam saboda yafi kusa kuma albashin su babu laifi sannan ga ragi da zata samu sosai a matsayinta na ma'aikaciyar makarantan. Zata riƙa koyar da Science a junior secondary sai Biology a senior secondary.

Da safe tare su ke tafiya makaranta in an tashi ma su dawo tare sai dai idan Umma ta tsaya meeting ɗin malamai.




***




Maryam na da wuyar sabo shi yasa har yanzu bata yi ƙawa a makaranta ba. Ko break aka fita wurin Safiya ta ke tafiya su ci abinci tare ko ta tafi ajin Umma ta yi zamanta har sai an buga kararrawa.

Yanzu ma an fito break yara nata wasa tana zaune a kan wani dakali tana kallon su. Sai ta ji kewar babbar ƙawarta Bilkisu Kabir.

Zama ta ji an yi a gefenta. Da ta juya ta ga wata ʼyar ajinsu ce a wurin. Babu wanda ya ce wa wani komai su ka cigaba da zama a wurin har lokacin break ya ƙare.

Maryam ta miƙe ta kakkabe bayan rigarta da ya yi ƙura. Yarinyan gefenta ta sa hannu ta taya ta inda bata hangowa. "Nagode." Ta ce a hankali.

Tare su ka koma aji. Ita dai Maryam taga duk inda ta bi yarinyan ke bi, har yasa ta fara tunanin ko binta take yi. Ashe row dinsu ne ɗaya. Maryam tana gaba ita kuma yarinyan na baya dayake tana da tsawo.

Maryam ta maida hankalinta sosai kan karatu dama chan ita mai son karatu ce. Tunda Mama ta ce mata hanyar da zata sakawa Abbanta shine idan ta maida hankalinta a makaranta da kuma yi mai aduu'a ta ƙara ƙarfin dammaranta.

Tana missing Abbanta sosai. Wani sa'in ma bata san lokacin da hawaye suke fara zubowa daga idanunta ba. Umma ta ce mata a aljannah kaɗai za su sake haɗuwa dan haka kullum ta yi sallah sai ta yi addu'a Allah Ya haɗata da Abbanta a aljannah da Inna tare da Umma da sauran 'yan uwanta.

Da aka tashi makaranta malamai nada meeting a maimakon su tafi yanda Umma ta ce sai suka zauna jiranta. Idris, Zee da Bashir nata wasa a playground ɗin makarantan, Maryam da Safiya kuma na zaune ta gefe kan wani tebur.

Akwai wasu yaran da suma iyayensu malamai ne da wanda ba'a zo daukan su ba. Sun haɗu ana ta wasa. Safiya ma ta gaji da zama ta shiga cikin tseren da ake yi sai ya rage saura Maryam ita kaɗai a zaune.

Maryam ta ciro sauran biscuit din dake jakarta ta buɗe. Yarinyan da ta zauna kusa da ita ɗazu ta gani zaune ita kaɗai. Ba tare da ta yi dogon tunani ba ta miƙe ta koma kusa da ita. Suna haɗa ido su ka yi wa juna dariya. Maryam ta miƙa mata biscuit din ta ɗauka.

"Sunana Maryam."

Yarinyan ta yi murmushi. "Hamida."

"Kema mamanki na meeting ne?"

Hamida ta girgiza kai. "Ba'a zo dauka na bane."

Safiya ta iso wurin da gudu tana haki ta kamo hannun Maryam. "Yaya mu je ki shiga team din mu."

"Toh tsaya kar in faɗi," Maryam ta yi dariya. "Zo mu je Hamida."

Sun sha tsalle-tsalle har aka zo daukan Hamida su Umma kuma suka gama meeting ɗin.

"Toh sai ku zo mu tafi ai," inji Umma. Kai ta girgiza ganin yanda Zee, Idris da Bashir su ka yi dukun dukun.

Kan su ta kaɗa su ka kama hanyan gida. Yaran nata bata labarin abun su ka yi a makaranta. Umma na jin su tana murmushi har su ka iso gida.

A soro suka samu Baba Malam a zaune. "Ƴan makaranta sai yanzu?"

"Meeting muka tsaya Baba. Ina wuni."

"Lafiya lau. Ku shiga ciki, kun kwaso gajiya. Wannan dai sai sun yi wanka."

Umma ta yi dariya. "Gaba ɗayan su ma Baba."

Bangaren Mama ta fara shiga ta iske ta yi baƙi. Umma ta zauna aka gaisa sannan ta nufa bangarenta. Kamar kullum abinci na jiranta a falo. Ita kam bata da abun cewa sai Alhamdulillah. Dawowarta gida ya yaye mata damuwa da dama. Kowa na gidan na koƙarin ganin ya kyautata mata da marayunta. Sai dai su yi kewar Ahmad saboda sabo amma ba dan sun rasa komai ba.

Akwai abubuwa da dama da take son sanar da shi sai dai mutuwa ta yi musu iyaka. So dayawa sai tagama kudirawa a ranta bari in faɗawa Ahmad sai ta tuna ya yi mata nisa, nisa na har abada. A irin lokutan nan ne mutawarshi ke dawo mata, ta yi kuka ta godewa Allah da ni'imar da Ya yi mata.

"Umma," Maryam ta kira tana bude ƙofar ɗakin. Sai da gaban Umma ta faɗi saboda wani lokaci har muryarta kaman na Abbanta.

"Maryam mene ne?"

"Ba komai, naga ba ki fito kin ci abincin bane."

"Yanzu zan fito Yaya, shiryawa na yi. Ku har kun ci abincin?" Maryam ta gyada kai. "Bari nima in je in ci to."

Maryam bata bi bayan Umma ba ta yi zamanta a ɗakin. Wata jaka ta janyo ta ciro photo albums ɗin da ke ciki. A hankali ta riƙa buɗewa tana kallo hotunan da ke ciki. Tun daga kan bikin Abba da Umma har zuwa sunan ta da na Bashir duka akwai hotunan a liƙe.

So dayawa idan aka nemeta aka rasa tana ɗakin Umma tana kallon hotuna. Kallonsu na tuna mata da labarin da Abba ke bata a hanyar makaranta. Wani lokaci ta yi dariya wani lokaci kuma ta yi kuka.

Hotan su na ƙarshe da Abba kafin ya rasu ta kalla ta sake kalla. An dauka hoton ne bayan dawowar Inna gidan su. Musamman Abba ya ce su shirya zai kira mai hoto. An sha hotuna ranan kuwa, bayan an dauka kowa da kowa aka kuma yi ɗaya bayan ɗaya.

An ɗauketa ita da Abbanta suna dariya ya dauketa gaba ɗaya wai ai bata da nauyi.

"Yaya?" Muryar Umma ta firgitar da ita da sauri ta kulle album ɗin.

Umma bata ce mata komai ba ta zauna kusa da ita ta karɓa album ɗin. Daga farko ta fara budewa tana yi tana nuna duk wani hoto dake ciki tana bata labarin abunda ya faru a lokacin.

A hankali Maryam ta daura kanta kan cinyar hannun Umma su ka cigada kallon hotunan.

***

Maryam yanzu bata da ƙawa da ta wuce Hamida komai a ka yi sai kaji ta kira sunan Hamida. Har yan gidan su ka fara tsokanarta ƙawar Hamida.

A sanadin ƙawancen su har Umma da Maman Hamida su ka zama ƙawaye suma ya zamana ana zumunci tsakanin gidajen biyu sosai.

Wannan yasa da Maman Hamida ta samu Umma akan tana so ta kai yaran wurin wasa ƙarshen mako Umma bata hana ba ta ce dai zata fara faɗawa Baba. Da ya ji ya ce sai sun dawo.

Ana gobe za'a je wurin wasan nan dai Zee bata runtsa ba. Ita da ake fama da ita kafin ta tashi a barci ranan ta riga kowa tashi.

Anti Jamila ta ce, "Anya Zee baza a fasa zuwa da ke ba kuwa? Wannan zagwaɗi haka."

Duka aka yi dariya. Mama ta ce, "Jamila ki kyaleta."

Ƙarfe sha ɗaya motar gidan su Hamida ta iso lode da yara. Dayake harda cousins din Hamida. Maman Hamida ta shigo ta gaisa da su Mama. Zee na ganinta ta yi waje. Haka aka kwashe su gari guda.

Ranan sun yi having fun sosai. Maryam mai yawan shiru-shiru sai aka sameta itama ta saki jiki ta shiga cikin yara.

Basu suka koma gida ba sai yamma liƙis. Maman Hamida ta haɗo su da tarkacen yara da kwalam da maƙulashe shaƙe a leda.

Ranan ne karan farko da Maryam ta ji gwara da su ka dawo Kaduna





You guys aren't commenting🥲🥹


~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top