6.









All the fathers we have lost, Allah Ka jiƙansu da rahama, Ka sa sun huta. Allah Ka haskaka ƙabarinsu, Ka sa chan ya fi musu nan. Ya Allah Ka sa aljannah ce makomarsu. Allah Ka jikan musulmai gaba ɗaya. Mu kuma da muke raye Allah Ka sa mu cika da kyau da imani.

Ameen





Rayuwa na da abun tsoro. A cikin lokaci kaɗan komai ya ke chanzawa.   Gaba ɗaya duniyar bata tabbas sai abu ɗaya. Abu ɗaya da dayawa mutane kan manta da shi.

Mutuwa.

Allah Ya ce 'kullu nafsin za ikatul maut; ko wani rai sai ya dandana mutuwa'

Mutuwa ce kaɗai matabbaciyar al'amarin da se ta faru da kowa. Kowa lokaci kawai ya ke jira.

Umma ba zata iya cewa ga abunda ya faru ba bayan Zubairu ya sanar da ita. Kawai ta farka ta ga mutane a kanta ana kuka ana yi mata firfita.

Ganin kukan da su ke yi ya tabbatar mata ba mafarki ta yi ba.

"Ya mutu ko? Ya tafi ya barni ko?"

Dagaske Ahmad ya tafi ya barta. Kuka ta fashe da shi da ya taɓa zuciyar kowa a wurin.

Juyawa ta yi taga Maryam jikin wata mata tana kuka. Ganin ʼyarta ya sata sake fashewa da kuka saboda kaman an ajiye mahaifinta ne a wurin.

Shikenan, yanzu shikenan Ahmad ya tafi ya barta. Ba zata sake ganinsa ba, ba zata sake jin muryarsa ba.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!

Yaran huɗu su ka fado jikin mahaifiyarsu. Umma ta sa hannu ta rungume su tana kuka. Awannin kaɗan da su ka wuce haka mahaifin su ya rungume su cikin farin ciki da so da ƙauna. Ana sallama sai ya dawo ashe tafiyar ta shi ta har abada ce.

Sake rungume yaran ta yi zuciyarta na wani irin ƙuna da ciwo mara misaltuwa. Yanzu shikenan sun zama marayu. Ita kuma ta zama bazawara. Bangon su ya faɗi. Sun rasa jigon rayuwarsu. Ahmad ya tafi ya barsu.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!

Kaicho!

Kaicho! Mutuwa mai yankar ƙauna. Mutuwa mai raba mahaifiya da ɗanta. Mutuwa mai raba mata da mijinta. Mutuwa mai raba uba da yaransa.

Babu wanda bai tausaya musu ba a wurin. Inna ta dafa kafaɗar Umma. Tsohuwar ta yi dauriya. Ita ke basu haƙuri.

"Ya zamu yi? Lokaci ne ya yi."

Gidan ya cika da jama'a ana ta zuwa ta'aziya. Umma kai kawai ta ke iya ɗagawa. Hawayen sun daina zuba amma da ka ganta kasan kukan zuci take yi. Kukan da ya fi ko wanne ciwo.

Yaran na zaune gefenta ba su motsa ba tunda ta farfaɗo daga suma da ta yi. Manyan Maryam, Safiya da Idris sune su ka fahimci me ake ciki. Zee da Bashir sun ga ana ta kuwa amma basu fahimci na meye ba.

Sallama aka yi cikin falon. Umma na ganin mahaifiyarta da ƙannenta ta sake fashe da wani kukan. Mama—mahaifiyarta ta rungumeta tana shafa mata baya, itama hawayen take yi. Allah bai bata haihuwar ɗa namiji ba, Ahmad ne ya maye wannan gurbin. Yaro mai hankali da natsuwa, mai girmama manya.

Wayyo mutuwa, shikenan ta raba Ahmad da Sa'adar shi.

"Dole mu yi haƙuri Sa'adatu. Allah da Ya fi mu son shi ya amsa abinSa. Addu'a zamu yi ta mai. Halayensa na gari su bi shi. Allah Ya jiƙan Ahmad da gafara. Allah Ya bashi ikon amsa tambayoyin ƙaɓari. Mu da ya tafi ya bari da kewa Allah Ka bamu juriyar rashi, Allah Ka sa mana dangana a zukatan mu. Yara da ya bari Allah Ka yi musu albarka, Ka albarkaci rayuwarsu, da su da sauran iyalansa. Ki yi haƙuri Sa'adatu, ki yi haƙuri."

"Ameen..." Umma ta yi ta nanatawa. "Ahmad mutumin kirki ne. Idan ta shine da duniya ta zauna lafiya. Ba zaka taɓa ji ya samu sabani da kowa ba. Ko ka bata mai rai cikin ʼyan mintina zai sauko. Wayyo Ahmad. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil! Ya Allah!"

Ƙasan hijabinta ta saka ta rufe fuska jikinta na rawa da tsananin kukanta.
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil..."

Ƙannenta biyu Firdausi da Jamila ke ta bata baki. Su uku ne wurin iyayen su, Umma ce babba. Bayan nan mahaifinsu Baba Malam ya shigo inda ya yi wa marigayi addu'a mai tsawo.

A Kaduna hatsarin ya faru. ASP Zubairu aka fara sanarwa shi kuma ya nemi Baba Malam tunda a garin ya ke.

Mutanen falon aka ce su bada wuri za a shigo da gawa saboda makusanta su yi mai sallamar ƙarshe. Nan wuri ya ƙara ruɗewa da kuka musamman da aka shigo da makara.

A hankali aka buɗe fuskar. Umma na hawaye tana kallon shi. Kaman ka taɓa shi ya buɗe ido, sai dai ya tafi, tafiya ta har abada. Jikin shi babu ko kwarzane ɗaya. Bai ji ciwo ba da ya yi hatsarin. Internal bleeding ya samu da ya zama ajalinsa. Ko asibiti ba a kai ba rai ya yi halinsa.

Umma da Inna tare da yaran su ka yi mai addu'a mai tsawo.

"Wayyo mutuwa, ta tsallake tsohuwa ta ɗauki yar0," inji Inna ta share kwalla. "Da ni kika ɗauka kika bar Ahmad."

"Umma Abba barci ya ke yi?" Zee ta tambaya a hankali.

"Abba ya rasu Zainab. Ya tafi ba zai sake dawowa ba."

Maryam ta runtse ido kafin ta buɗe su a hankali. Addu'o'in da ake musu a islamiya su ta yi ga karantawa. Abbanta ya tafi ba zai sake dawowa ba. Hawaye ne suke gangarowa fuskarta babu ƙaƙƙautawa.

Iyalan Arc. Ahmad sun yi mai sallamar ƙarshe kafin a kai shi gidan gaskiya. Da aka zo fita da gawar Zee ta yi maganan da ya sa kowa kuka a wurin.

"Umma ina za su da Abba? Barci fa ya ke yi, kuma zai tashi ai."

Anty Firdausi ce ta riƙo Zee jikinta tana rarrashinta.

Dumbum jama'a sun halacci sallar jana'izar Arc. Ahmad. Kowa ya buɗe baki halayensa nagartattu ya ke faɗi. Arc. Ahmad ya samu yabo mai kyau.

Shikenan Arc. Ahmad ya isa gidansa na gaskiya. Adadin shekarun da ya diɓo kenan. Mai gadin maƙabartan da aka kai shi ya yi ta jinjina kai. Ya daɗe bai ga taron jama'a haka ba. Tabbas mamacin nan mutumin kirki ne.

Bayan an kai shi Musa da ASP Zubairu su ka shigo sannan su ka nemi ganawa da Umma. Musa jiki ya yi la'asar. Idanuwansa sun nuna kukan da ya sha.

"Akwai wanda kika sani da ya ke binsa bashi?" ASP Zubairu ya tambaya.

Kai Umma ta girgiza. "Babu. Sai dai shine ke bin wasu bashi ma."

ASP Zubairu ya gyada kai. "Alhamdulillah. Ki yi mun list ɗin sunayen su."

Ta ce to sannan ta koma ciki.

Umma Sa'adah kwana ta yi sallah. Idan ƙafafuwanta su ka gagara ɗaukanta sai ta zauna ta yi zikiri. Kasa zama ɗakin Arc. ta yi dan gittawansa ta ke gani idan ta rufe ido. Gaba ɗaya gidan da zata iya fita da ya fi mata. Ko wani lungu da saƙo na gidan na tuna mata da masoyin da ya tafi ya barta ita kaɗai cikin duniyar nan mai faɗi.

Ya zata fara rayuwa ba tare da Ahmad ba? Ba zata iya ba. Shekarun su goma sha biyar da aure, yau ta wayi gari babu shi.

Amma dolenta ta daure, dole ta yi juriya saboda marayun da ya bari.
Ahmad bai haɗa son yaransa da na kowa ba. Ya zama dole ta kula dasu yanda ya kamata. Babban burinsa a kullum be wuce rayuwarsu ta inganta ba, ta yi kyau su samu ilimi na arabi da na boko.

Ƙofar ɗakin aka turo Maryam ta shigo ta zauna gefen Umma. "Ya aka yi Maryam? Wani abu ya same ki."

Ta girgiza kai tana tura kanta jikin mahaifiyarta. "Na kasa barci Umma."

Umma ta gyada kai ta sa hannu ta gyara zaman Maryam a jikinta. Cikin surorin da tasan Maryam ta haddace ta janyo. Suna ta karatu har barci barawo ya sace Maryam ɗin. Umma ta ɗaurata kan gado sannan ta dawo kan abun sallah.

A haka ta wayi gari.

"Ki daure ki ci abinci," Mama ta ce tana miƙa mata plate ɗauke da tuwo.

Abunda Ahmad ya fi son ci da safe kenan. Dumamen tuwo da kunun tsamiya. Hawaye su ka fara zubowa babu shiri. Yana chan yau ya yi kwanan rami. Shikenan duk wani gata ya ƙare kuma.

Kai ta girgizawa Mama. "Ba zan iya ci ba," ta ce cikin muryarta da kuka ya dasar.

Har aka kwana bakwai ƙafar mutane bata ɗauke ba. Ana ta zuwa gaisuwa har daga wasu garuruwan. Abokan aikinsa ma sun zo mazan su da matan su harda shugaban wuri da ya kira ya sanar da shi batun zuwa Kuwait ƙaro karatu. Mutuwar ba ƙaramin girgiza bawan Allah nan ta yi ba.

"Ahmad is one of a kind. Haƙiƙa mun yi rashi babba. Allah Ya jaddada rahamarSa a gare shi. Allah Ya raya abunda ya tafi ya bari."

Ba su bar wurin ba sai da suka ajiye musu kuɗi sannan ka kwalaye da buhunan kayan abinci. Yawanci duk wani aboki na Arc sai ya yi ɗaya daga cikin abubuwan nan, ko ya bada kuɗi ko ya kawo kayan abinci.

Daganan ƙafa ta fara ɗaukewa aka bar mukasanta da tsananin ƙewa. Ba mutuwar akewa kuka ba, sabo akewa.

Arc. Ahmad ya tafi ya bar wawakeken giɓi a zukatansu.

Firdausi ƙanwar Umma aka bari ta zauna da su. Itace ƙarama a gidan shekarunta sha takwas. Ita ke kula da komai na gidan, Umma bata iya komai kullum tana ɗaki da charbi a hannu. Wani lokaci sai dai ka jiyo sautin kukanta. Inna ke shiga ɗakin ta yi ta bata baki.

"Ki yi haƙuri Sa'adatu. Ki yi haƙuri. Wa ya isa ya ja da ikon Allah? Allah da Ya fi mu sonsa ya karɓa abunSa. Ki yi ta mai addu'a. Ahmad ya samu kyakkyawan yabo. Chan ya fi mai nan."

Gidan ya koma shiru. Yaran duk walwalarsu ta tafi. Makaranta ma da kyar su ka koma musamman Maryam. A hankali wasu abubuwan su ka fara komawa yanda su ke da.

Saidai har abada iyalan Ahmad ba za su taɓa iya komawa rayuwarsu ta da ba. Babban jigonsu ya tafi, bangon su ya faɗi.

***


"Umma mai za'a dafa?"

A hankali Umma ta daga kanta dake yawan sara mata ta kalli ƙanwarta. "Komai ma ki ɗaura Firdaus."

Firdausi ta gyada kai ta bar ɗakin yayarta ta nufi kicin. Watan ta biyu kenan a Kano. Kullum tausayin Umma ƙaruwa ya ke a zuciyarta. Ta chanza gaba ɗaya kaman ba ita ba. Ɗan jikin da ta ke dashi yanzu babu, duk ta rame. Allah sarki rayuwa.

Yaran sun kusa dawowa dan haka da sauri ta ɗaura girkin. Jollof ɗin shinkafa ta dafa bayan ta gama ta zuba a kula. Inna ta fara kaiwa. Tsohuwar ta yi mata godiya. Itama tun bayan rasuwar Arc jikinta ya ƙi daɗi, yau lafiya gobe babu.

"Sannu Firdausi, Allah Ya yi miki albarka."

"Ameen Inna."

Ƙarfe uku yaran su ka dawo daga makaranta. Me napep ne ya sauke su. Maryam ta kalla inda Abba ke ajiye motarsa kafin ta kauda kai da sauri.

"ʼYan makaranta an dawo," muryar Anti Firdausi ta dawo da ita hayyacinta. "Maza ku je ku cire kaya ku zo ku ci abinci."

"Ni na ƙoshi," Maryam ta ce a hankali.

"Haba Yaya Maryam, me kika ci da kika ƙoshi."

Sunan da Anti Firdausi ta kirata da shi har tsakanta. "Bana jin yunwa."

Firdausi ta saki ajiyar zuciya. "To shikenan, anjima sai ki ci."

Kaya ta chanza zuwa uniform ɗin islamiya. Tana gama shiryawa ta ji sallamar ƙawarta Bilkisu ta biyo mata. Anti Firdausi ta ce tazo ta ci abinci ta zuba musu tare da Safiya. Bayan sun gama cin abinci Anti Firdausi ta ce zata raka su makaranta, haka kawai ta ji sha'awar taka ƙafarta.

Fitar su babu ɗaɗewa Baba Musa ya iso gidan. Tun bayan an gama zaman makoki bai wuce sau uku ya zo gidan ba. Yana ta sallama ba'a amsa ba. Ya juya zai tafi kenan Umma ta fito sanye da doguwar hijab.

Bayan sun gaisa ya tambayeta ina Inna ta sanar da shi tana barci. Hakan ya yi mai daidai. Zama ya gyara yana kallonta ƙasa-ƙasa. "Dama batun rabon gado ne ya kawo ni."

Umma ta dago kai da sauri ta kalle shi.

Musa kuwa ko a jikinsa. "Mun yi magana da limamin unguwar mu gobe zai zo sai ki tattaro duk wasu takardu da kika san da su dan ayi a raba kowa ma ya huta."

Umma ta girgiza kai. Hali zanen dutse, bata yi mamakin furucinsa ko kaɗan ba. "Shikenan, amma sai ka jira sai na sanar da wakilai na nima."

"Wasu irin wakilai kuma, har sai yaushe za a raba gadon ne wai. So kuke yi kwanciyar ƙaɓari ya ki wa ɗan uwa na daɗi."

"Ahmad na chan cikin rahamar Ubangiji. Bashi ne ke hana bawa kwanciyar ƙaɓari ba gado ba kuma Alhamdulillahi bai mutu da nauyin kowa a kansa ba. Rabon gadon ba haka ake yinsa ba kara zube, addini ya tanadar mana dan haka idan zaka jira to, idan ba zaka iya ba kuma ya rage naka."

Umma na gama magana ta yi shigewarta. Lallai mai hali baya fasawa. Shi damuwarsa kenan. Ita da za'a karɓa dukiyar a dawo mata da Ahmad ɗinta da tafi kowa farin ciki a duniyar nan.

Da kyar ta samu network ɗin magana da Baba Malam a waya. Basu da kowa a nan Kano da zai wakilce ta. Ta san halin Musa, cin dukiyar marayu ba ƙaramin aikinsa bane. Dukda gado ba wani albarka ne da shi ba, bs zata bari dukiyar da Ahmad ya samo da guminsa ta hanyar halal su tafi a banza ba.

"Kar ki damu Sa'adatu, zan yi tunani a kai sai in sanar da ke."

"To Baba. Sai anjima."

Zama ta yi a ƙasa tana ƙarewa ɗakin kallo. Akwatin Arc. da aka ciro daga motarsa. Ta kasa taɓa kayan. Ganin zuciyarta na neman dena aiki ya sa ta fita ɗakin da sauri ta koma falo.

A falon ma bata tsira ba. Rayuwar da su ka yi cikin gidan ke yi mata yawo a ka kaman vidiyo.

Muryar Firdausi ce ta dawo da ita hayyacinta. "Umma Inna tun ɗazu ta ke barci bata ci abinci ba. Ko ina tada ta?"

"A'a, kyaleta. Tana ta complain ɗin rashin barci dama."

Da dare su ka haɗu a falon cin abincin dare. A lokaci irin haka sun fi tunawa da marigayi. Suna yi mai addu'a kullum su ka taru haka. Wani lokaci kuma hakan yana zama fami a garesu daga nan su yi ta kuka abun tausayi.

Yau dai Inna ce ke jan hiran. Tana ba yaran labarin kuruciyar mahaifinsu. Chan kuma sai ta fashe da kuka.

"Wayyo Ahmad, ɗan albarka ne. Allah Ya jiƙanka da rahama Ahmad, muna kewar ka sosai."

Daga nan kuma kowa ya fara kuka babu babba babu yaro sannan babu mai rarrashin wani.

Mutuwa kenan, mai yankar ƙauna.

Bayan zuwan Musa gidan maganar gado da sati ɗaya ASP Zubairu ya zo gidan. Bawan Allah baya sati bai zo ba ko ya yi musu aike. Kayan cefane ma da Umma ta bada a siyo dawo mata da  kuɗin ya yi sannan ya ƙara wasu a sama ya ce ta riƙe.

A kullum Umma ta ji sallamar shi sai gabanta ya faɗi. Duk zuwan da ya ke yi sai dai ya gaisa da Inna da yaran, ita bata taɓa fitowa ba. Amma yau ASP Zubairu ya nemi ganinta.

Da doguwar hijabin da su ka kasance kayanta a yanzu ta fita ta same shi zaune kaman ranan da ya zo mata da labarin da ya juya mata duniyarta gaba ɗaya.

Bayan sun gaisa ASP Zubairu ya sake yi mata gaisuwa. "Ya haƙurin mu?"

"Mun gode Allah."

"Allah Ya jiƙansa da rahama."

"Ameen Ya Allah."

"Babu wani abu da kuke buƙata ko?"
Kai Umma ta girgiza. "To Masha Allah. Dalilin neman ki shine in sanar da ke na gama karɓo kudaden marigayi da ke hannun mutane. Sannan na tattaro kan kadarorin shi wuri ɗaya."

Umma ta gyada kai. "Kwanaki Musa ya zo...." yanda su ka yi da shi ta faɗa mai. Idan ba shi ba bata san wa zata sanar ba. "Ka ji yanda mu ka yi dashi. Sai dai har yanzu ban wasu wanda zai wakilce ni ba. Ina tsoro kar Musa ya kwari marayun nan."

ASP Zubairu ya gyada kai. Allah sarki. Ahmad kaman ya san baya da sauran kwanaki da yawa. Ya faɗa mata yanda su ka yi da marigayi da takardun da ke hannun shi. "Idan babu damuwa ni zan wakilce ki da yaran. Musa ba zai yi nasara ba."

Umma ta ce ta gode amma zata fara sanar da mahaifinta tukun. ASP Zubairu ya ce duk yanda su ka yi sai ta sanar da shi.

Umma ta sanar da Baba Malam ya ce hakan ya yi idan har ta yarda da shi Zubairun. Umma ta sanar da shi marigayi baya da amini da ya wuce shi.

"To shikenan Sa'adatu. Allah Ya yi miki albarka. Kuna nan lafiya dai ko?"

"Lafiya lau Baba."

"Madallah. Alhamdulillah. Ki sa Allah a ranki kin ji ko. Allah Ya baki juriya da dangana."

"Ameen Baba."

Daga nan su ka yi sallama. Maryam ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Wasu lokutan Umma bata son kallon fuskarta saboda tsantsan kama da ta ke yi da mahaifinta.

"Umma in kawo miki kwadon zogale?"

"Ina kika samu zogale Maryam?"

"Inna ta aika a siyo mata."

Umma ta girgiza kai. "Na ƙoshi."

Maryam bata juya ba sai ta samu wuri ta zauna kusa da mahaifiyarta. A haka Safiya ta leƙo ta same su. Itama ta samy wuri ta zauna. Da ɗaiɗai da ɗaiɗai duka yaran suka shigo su ka zauna tare da Ummansu.

Ganin su haka ya karyawa Umma zuciya. Yaranta sun zama marayu da ƙananan shekarunsu. Dole ta ɗaure ta jure ba dan ita ba dan amanar da Ahmad ya tafi ya bar mata.



















Wayyo Abba🥹💔 Zan yi missing Arc💔

The saddest chapter I have written in a while💔

Allah jiƙan wanda suka rigamu gidan gaskiya. Mu kuma Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.

Ina son jin ra'ayoyinku. Leave a comment below.

Nagode.


~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top